Kenza eBookz

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 9

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 9

Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 9: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 9. Duk abin da ake Nasir yana ji, kawai murmushi yake saki…

3,357 words

Duk abin da ake Nasir yana ji, kawai murmushi yake saki jin Baba ya ce ta ba Nasir haƙuri a kan kunnensa ya ji haka ta buɗe baki ta bashi haƙurin cikin dashashshiyar muryarta, sannan Baban ya ce ta ba Nasir wayar tana jin yadda ya ringa ba Nasir haƙuri tamkar zai ari baki yana ta yi wa Nasir ɗin godiya kamar wanda ya masa kyautar kujerar makka.

Juyawa kawai ta yj ta koma kan sallayar ta fara sallar magriba, tana saddaƙarwa da cewa wannan gidan auren kamar kurkuku yake a wajenta, sai dai ta san ba za ta dawwama a haka ba akwai ranar ƙin dillacin ta san ko ba jima ko ba daɗe sai Allah ya mata sakayya a kan zalincin da Nasir yake mata, ko da bayan ranta ne kuwa.

Bayan ta yi har isha'i ya zo ya buɗe store ya ɗakko mata taliya rabin leda ya miƙa mata, karɓa ta yi ta nufi kicin ɗin ta shiga kunna gawayi don mahaifiyar Nasir ta yi uwa da makarɓiya ta hana ta kunna gas ɗin da Nasir ya saya tana amarya ɗan ƙarami, ta ce ita Sadiya bata dace da amfani da Gas ba saboda a gidansu da icce ake amfani. Dakyar ta samu gawayin ya kama ta ɗora tuwan zafi ta dawo falon, sai ta ji kamar ta rufe ido ta buɗe ta ganta a wata duniya daban. Tun da ya bata taliyar ya fice, ta gama dafawa ta soya manja ta zubo abincin ta ajiye ta ɗauki Kalifa ta ke ta wanke masa ido da baki tuni ya ware don dama yunwa yake ji, haka yake cin abincin kaɓr me saboda yunwa, ita kuwa kaɗan ta samu ta ci shi ma duk babu daɗi.

Haka ta yi shimfiɗa ta kwantar da Kalifa ta shiga ta yi wanka tare da ɗauro alwala ta saka rigar bacci marar nauyi ta yi addu'a ta kwanta har lokacin Nasir bai dawo ba, ganin an kawo nepa ta tashi ta saka cajin wayarta ta koma ta kwanta tana rungume da filo tana ta tunanin lamarin gidan aurenta, rana zafi inuwa kuma ƙuna, hawaye yana ta bin kumatun ta mafita take nema ita dai da za a ji damuwarta a magance mata da da daɗi amma babu mai saurarenka iyayenka kawai burinsu ka zauna a ɗakin miji daɗi da wuya ko da kuwa a wulaƙance ne. Tana ta wannan saƙa da warwarar bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita.

Nasir sai wajen ƙarfe goma saura ya shigo gidan, yana can majalisa da abokai ana ta hira, yana shigowa ya rufe ƙofar gidan ya shigo gidan yana wani bada faɗi, sai kuma ya ga baiwar tashi bata ma falon tsire da coca colan da ya shigo da su ya zauna ya baje a falon ya cinye a shanye lemon ya tashi ya bar mata takarda da robar a wajen. Bayan ya gama abin da zai yi ya saka hannu a aljihu ya fito da wani ƙullin ruwan magani a farar leda ya tula ya shanye ya fito ya jefar da leda, kayansa ya cire daga shi sai singlet da ƙaramin wando ya haura kan gadon bayan ya kashe gabaɗaya fitilun. Kasancewar Kalifa a ƙasa take masa shimfiɗa a kan ƙaramar katifa da yake gidan ciki da falo ne, sai kicin da banɗaki kawai sai kuma ɗaya part ɗin inda ciki da falo sai ɗaki ɗaya wanda an fara ginin an kai linta amma ba a ƙarasa ba. Yana hawa gadon ya kwanta ya miƙa hannu ya shiga tashin Sadiya, cikin bacci ta ji yana buga mata ƙafa ta ɗago jajayen kumburarrun idanunta ta kalle shi ta cikin ɗan hasken farin wata da ya ratso ɗakin.

Cike da gadara babu tausasa murya ya ce

"Haƙƙina na zo karɓa" Ranta ne ya sosu wai mutumin da ya gama ci mata mutumci har marinta ya yi amma yanzu kuma ya zo da wata buƙata, a kasalance irin na wanda yake cike da bacci da gajiya ta ce

"Dan Allah Abban Kalifa ka mini lamuni yau wallahi ba na jin daɗin jikina" Kamar wanda ta watsa masa wuta haka ya zaburo mata ya ce

"In baki taliya ki cika ƙundunki ki shi ne tawa buƙatar ba za ki biya min ba? To in dai wancan taliyar da na ga kin ajiye mini a ƙaramin filas ce kike yi wa ki je ki ɗauka ni nama da lemo na sha, idan kin cinye sai ki zo ina jiranki da alama ƙoshi ne baki yi ba shi ya sa kike mita" Cike da ƙosawa da kalamansa ta ce

"Ni ba yunwa nake ji ba kawai dai zuciyata ce babu daɗi"

Zaune ya miƙe ya saka hannu ya daki kan katifar kan gadon ya ce

"Ko zuciyarki da daɗi ko babu wannan ke kike sakawa kanki kuma ke kika ga za ki iya, ni dai yanzu haƙƙina dole ki bani tun da sadaki na bayar" Tun da ya yi wannan furucin bata ƙara furta komai ba ya cire kayan jikinta, babu wani ɓata lokaci ya shiga biyan buƙatarsa ya daɗe yana abu ɗaya sai da ya gaji don kansa ya ƙyaleta, ita kuma tana kwance kamar gunki don dama babu wani abu da take fuskanta a lamarin don damuwa ta gama yi wa zuciyarta katutu, shi kuma lamarin mu'amalar aure ana son gabatar da shi a lokacin da ake cikin walwala farinciki haɗe da annashuwa.

*IBRAHIM*

Kafin ya ƙarasa gidan su Jidda ya haɗa uban gumi sharkaf abin ka da wanda ya saba rayuwa cikin AC gida AC mota AC office ma AC.

Ko da ya zo bai ƙarasa saitin gidan ba daga ɗan can gefe ya tsaya yana hangar ƙofar gidan, sai lazimi yake a zuciyarsa, yana addu'ar Allah ya sa ya dace.

A can cikin gida kuwa Aliya ce take gwada wata doguwar rigar abaya maroon da takalmi haɗe da wata jaka sai murna take tana cewa

"Gaskiya Kasim ya iya zaɓe"

Umma ta yi karaf ta ce

"Wannan ai za a je da shi, kin ga duk da ba mai arziƙi ba ne ai yana da wadatar zuciya, daga ganinsa irin mazan nan ne masu bautawa mace, kika dai yadda yake miki wahala komai ya samu ke yake yi wa"

Aliya ta ce

"Umma ai wanna da kike gani bawan mace ne"

Umma ta ce

"Ai tun da dai yana da karatun digirinsa digirgir kuma yana da ƙashin arziƙi daga gani, gashi yana sonki yana bauta miki tabbas in kika aure shi kakarmu ta yanke saƙa, wuyarta ya samu aikin gwamnati da takardun nan basa ai shi kenan kin zama babbar mace" Wani uban tsalle Aliya ta daka tana murna tana sanar da Umma Kasim ɗin ma ɗazu ya ce zai saya mata sabuwar waya. Da gayya suke ta maganganun nan da yada magana duk abin da suke Jidda tana jin su, ita damuwarta ma da jiya da daddare Abba ya tara su ya ce kowacce ta fitar da miji shi bai san cewa Jidda bata da wani tsayyaye ba, ita kuma tana jin nauyin sanar da Abban.

Ta yi nisa a tunani Umma ta ƙwalla mata kira, tana fitowa ta saka ta wankin kaya, haka ta karɓa don dama yau Ummar ce ta hana ta zuwa islamiya saboda aikin gidan. Aliya ce ta gama saka kayan gabaɗaya a leda ta cewa Umma za ta je gidan su Amatullahi ta kai ta nuna mata Umma ta ce

"Yawwa maza kula ki je ki nuna mata kin kece raini kuma kina da mijin da xa ki aura na nunawa sa'a" Ta faɗa tana kallon saitin Jidda da ta duƙufa wajen wankin zanin Ummar. Ko da Aliya ta ɗauki ledar ta fito ƙofar gidan, Ibrahim daga can inda ya tsaya ya hango ta, kasancewar bai shaida ta ba sai ya taho domin yana son ya tambaye ta ko Jidda tana ciki, bai gane ta ba sai da ya zo dab da ita, ita kuma Aliya a lokacin da ya ƙaraso tana ƙoƙarin kara waya a kunne don Amatullahi take kira za ta ce mata gata nan za ta nuna mata kaya. Ganinsa ya sa ta fasa kiran wayar ta kashe tana ƙare masa kallo, tabbas ko daga bacci ta tashi ba za ta kasa shaida wannan fuskar tasa ba.

Fuska ta yatsina tana masa kallon ƙwaf, shi kuma gabaɗaya kansa ya kulle da ya ganta don tabbas ya shaida ta ita wacce ta ciwa direbansa mutunci ranar nan. Gabaɗaya ma sai bakinsa ya ƙi bashi haɗin kai wajen yin sallamar da ya yi niyyar mata, bare a kai ga tambayar da zai mata a kan Jiddar tana cikin gidan.

Aliya kuma sai ta shiga masa wani kallon raini tana yatsina, gabaɗaya sai ya tsargu da kallon nata amma sai bai ce mata komai ba, cike da mamaki da gatsali ta ce

"Oho sai yanzu na je ghana, kai duniya mutane sai a barsu, wato dai Allah ya tona maka asiri ashe dai ganin kana da kyau shi ya sa kake aron mota da kaya masu kyau kana yaudarar ƴaƴan mutane ko? Har da aron direba da yake janka a mota, wato ka zaci ba zan gane ka ba, to ta Allah ba taka ba wannan ai kai ne a wanki gara!" Ta faɗa tana wani zagaya shi, gabaɗaya sai Ibrahim ya kasa magana ita kuma ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har da faɗin ɗan talaka dama bai iya samun wuri ba wato har da cewa wa yake nemanta lokacin da ta je wajensa a motar ashe dai duk kanwar ja ce shi ma dai talaka ne bai ajiye ba bai bayar ajiya ba.

Shi dai yana kallon ta tsabar mamaki ma ya rasa mai zai ce.

Ganin haka sai ta ce

"Shi ne ka lallaɓo koɗaɗɗun ƙafafunka da wasu tsoffin kayanka sa suka gaji da wanki, to wallahi ni na fi ƙarfinka ne, kar ma ka ɓata lokacinka wajen mini magiya ko roƙona don ina cikin mutanen da suke cewa da wuya ta kar su ai gwara daɗi ya kar su"

A can cikin gida kuwa Umma ce ta ce Jidda ta ɗauki bokiti ta fita famfon waje ta ɗakko ruwa ta ƙarasa wankin, da yake ruwan ya ƙare, duk da akwai mai ruwan da yake kawo musu ruwa amma saboda ta ga Abba ba ya nan ta aike ta ɗakko ruwan, haka ta ɗauki bokitin ta fito ba don ta so ba.

Aliya tana cikin masa wannan maganar har wani nuna shi da yatsa take a daidai nan ne Jidda ta fito, sai da gabansa ya buga da ya ganta sanye take da wani blue ɗin hijabi har ƙasa hijabin yana da hannu sai bokiti a hannunta fuskarta babu walwala. Tun da ta fito kallo ɗaya ta musu ta wuce da yake wajen famfon kusa da gidan da yae kusa da gidansu ne ta tara ruwan ta ciko ta ɗakko.

Ta zo za ta shige gida ganin abin da Aliya take yi wa Ibrahim sai ta ce

"Haba Aliya, a titi kike wannan ɗaga muryar?"

Cike da ɗaga murya ta ce

"An yi ɗin uwar pan shishshigi" Juyawa ta yi ta shige gidan, shi kuma kallon ta kawai yake yana son ganin gudun ruwanta, sai da ta gama masa ɗiban albarka ta ce

"To a yi gaba ko a samu wata dai amma wannan Aliyar sai Kasim!." Tana faɗa ta juya ta tafi tana wani juya mazaunan da su da babu duk ɗaya.

Gefe ya koma yana ƙarewa jikinsa kallo yana mamakin cewa kenan dai shi talaka a wajen wani shi ba komai ba ne, sannan wasu suna ganin duk rashin mutuncinka in har kana da kuɗi to kai mai kirki ne in kuma baka da shi da kai da babu duk ɗaya, dama ya fahimci cewa Aliyar nan ƴar son banza ce don ranar ma a idanunta ya ga son banza ƙiri ƙiri.

Ko da ta je gidansu Amatullahi nan ta shiga bata labarin Ibrahim suka ringa zaginsa suna ce masa matsiyaci, Aliya ta ce

"Oh har zan ce in yi saki na dafe da Kasim ɗina ashe dai ba arziƙi ba ne yake kirana tsiya ce"

Amatullahi ta ce

"Humm! Ba ke kike cewa wani kyakkyawa ba ne"

Aliya ta ce

"Ke dai bari a yau na gane cewa duk arahar kunu ta banza ce in babu gaya a ciki" Suka ci gaba da ɗaga kayan Kasim suna zuba masa albarka.

Fitowar Jidda za ta ƙaro ruwa sai ta gan shi jingine da bango, amma sai ta masa kwarjini ya kasa mata magana har sai da ta ciko bokoti tana ƙoƙarin ɗakkowa ya ƙarasa wajen ya ce

"Kawo in taimaka miki" Kawai da ta juyo sai ta kasa hana shi kwarjini ya mata ta ga yana da kima da kuma kamala. Ɗakko mata ruwan ya yi har ya kawo ƙofar gidan, kasancewar ya saba ruwa a banɗaki sai dai ya tara ya yi wanka tunaninsa zai ji nauyin bokiti amma da yake soyayya yake yi wa bauta sai ya ji ko alamar nauyi babu kamar dai ya ɗauki bokiti mai auduga ne. Yana zuwa ya ajiye ya ɗago yana kallon ta cike da jin daɗin abin da ya mata ta ce

"Sannu da ƙoƙari na gode ƙwarai"

Wani daɗi ne ya cika shi kamar ya taka rawa jin muryarta tana masa godiya da jinjina masa.

Har za ta ɗauki bokitin ta juyo ta ce

"Don Allah ka yi haƙuri abin da Aliya ta farfaɗa maka" Yana jinjina dattakon ta ya ce

"Ni dama ...am dama ke zan ce ta yi min magana da ke shi ne ... Ya faɗa yana inda -inda

Cike da mamaki ta kalle shi tsantsar mamaki yana bayyana a kan fuskarta ta ce

"Ni kuma?" Ta faɗa zuciyarta tana bugawa da ƙarfi, ta san dai jiya ta yi ta addu'ar ita ma Allah ya fito mata da mai son ta wanda zai aure ta ya riƙe ta da daraja idanu ta ɗan runtse ta buɗe ta ce

"Lafiya dai ko?"

Yana kallon yanayin ta ya ce

"Na zo don in bayyana miki soyayyata wallahi ina ƙaunarki da gaskiya tun daga ranar da na fara tozali da ke" Ya faɗa zuciyarsa tana zillo kawai gani yake ba za ta amince da shi ba saboda kyaun da yake da shi tun da da kunnensa ya ji ta ce bata son mai kuɗi kyakkyawa.

Jidda kuwa jikin ta ne ya fara rawa kasantuwar abin ya zo mata a bazata, kuma dai mutumin ya birge ta musamman da ta ga cin mutuncin da Aliya ta masa bai biye mata ba duk da bata san abin da ya haɗa su ba sannan da taimakon ta da ya yi ya ɗaukar mata ruwa.

Rasa amsar da za ta bashi ya sa ta ce

"Sai na yi tunani tukunna"

Wannan furucin nata ya saka shi a wasi-wasi amma ya danne ya ce

"Babu damuwa Allah sa ki yanke abin da ya fi zama alkairi " Yanayin yadda ya yi maganar ya sa ta ji wani iri kamar dai bata kyauta masa ba kamar dai bai ji daɗin furucin ba.

Bata ce masa komai ba ta sunkuya ta ɗauki bokiti har ta fara tafiya ya ce

"Jidda" Har tsakiyar kanta ta ji kiran sai ta ji tamkar shi kaɗai ne ya iya kiran sunanta daidai, sai dai bata san dalilin hakan ba, juyawa ta yi bayan ta ajiye bokitin ta ce

"Na'am" Ta faɗa idanunsu suna sarƙewa da juna da sauri ta yi saurin kawar da nata, kasancewar sai ta ji kallon da idanunsa suka jefe ta da shi ya sha bamban da kallon kowane mutum.

Iska ya ɗan hurar daga bakinsa ya ce

"Ki daure ki bani phone no ki" Kamar ba za ta ce komai ba har ya cire rai za ta bashi sai ya ji ta fara karanto masa, nan ya shiga rubutawa a ƙaramar wayar da ya taho da ita. Tana gama faɗa masa va tare da ta jira cewarsa ba ta juya ta ɗauki ruwan ta shige gidan.

Tsabar murna bai san ya isa bakin titi ba don ko wahalar tafiyar ba ya ji, wani irin farinciki da yanayi marar misaltuwa da yake ziyartarsa, haka ya yi kwanan farinciki amma dai ya kasa kiran wayarta don sai ya rasa mai zai ce idan ya kira.

Bayan kwana biyu, har lokacin bai koma gidansu ba kuma bai kira ta ba, sai dai yana ta dakon soyayyarta. A ɓangaren Jidda tun daga wannan ranar ta ji ta damu da Ibrahim sai dai rashin kiranta a waya sai ta ji duk babu daɗi, tun tana jiran kiransa har ta cire rai, da ko baƙuwar no ta gani sai ta yi tunanin shi ne har dai ta cire rai daga kiran nasa. Sai da aka yi sati sannan watarana da yammaci yana zaune a ƙasan wata bishiya a wata unguwa yammaci ne mai cike da ni'ima sassanyar iska tana kaɗawa, yana zaune saman motarsa ya kamo sunan ya shiga kiranta, Jidda tana hura wutar da take tuwon dare ta fara jiyo ƙaran wayarta, amma bata je ta ɗakko wayar daga ɗaki ba. Har kiran ya tsinke bata je ba, Ibrahim kuma sai ya fara wata zufa hankalinsa ya tashi ya fara tunanin ko dai ta yanke shawara marar kyau a kansa, kuma da ya yi tunanin ai bata san numbersa ba sai ya ji hankalinsa ya ɗan kwanata a ƙara gwada kiran.

Tunanin ta ma ko Salama ce ita ce idan ta fara kira bata san ta daina ba, hakan ya sa ta iza wutar ta nufi ɗakin, tana ɗaukan wayar ta ga baƙuwar no dama gidan babu kowa sai ita kaɗai duk sun fita gidan biki. Bata san mai ya sa ba amma sai da gabanta ya faɗi tana dannawa ta ƙara wayar a kunne.

Sassanyar muryarsa mai amo mai daɗi da ita ya fara mata sallama, idanu ta lumshe kaɗan ta buɗe su bata san dalili ba amma sai ta ji ta yi farin ciki da kiran, bata san ko don ta daɗe tana jiran ya kira ta ba ko kuwa mene ne oho.

Amsa sallamar ta yi sai ya ce

"Sunana Ibrahim ni ne kika ba numberki ranar da kika ɗauki ruwa" Wani murmushi ya kuɓuce mata marar sauti a zuciyarta tana raya da a ce ya san cewa bata da wani saurayi da bai wahalar da kansa wajen tuna mata ranar da suka haɗu ba.

Cike da murnar da bata bari ta bayyana ta a fili ba ta ce

"Na gane ka"

Ya ce

"Ya batun tunanin kin yanke hukuncin"

Ta ce

"Hukuncin me?"

Ya ce

"Hukuncin na cancanta ki kula ni ko ban kai ki kula ni ba" Maganarsa ta bata dariya hakan ya sa ta dara har yana iya jiyo sautin dariyar ta cikin wayar.

Jingina ta yi da bango ta don dama a tsaye take ta ce

"Ban amince ba" Gabansa ne ya buga da ƙarfi a take ya ji gabaɗaya hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi, ɗan walwalar da ya tsinci kanaa sanadin magana da ita duk sun gaushe.

Bata tantance ba ta ji saurin maganarsa cikin tashin hankali yana cewa

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"

Bata san dalili ba sai ta ji zuciyarta babu daɗi ta ji duk ta damu da yanayin sa ya shiga bata san lokacin da ta ce

"Da wasa fa nake maka na amince" Daga ita har shi dariya ce ta ƙwace musu.

Sun daɗe suna hira kamar sun saba daga bisani ta ce masa aiki take saboda ta ga abin nasa ba na ƙare ba ne, wayar ta ajiye ta fita ta ƙarasa tuƙa tuwon, sai bayan ta kallama aikin ta yi wanka ta zo ta ɗauki wayar ta yi saving no da IB tana ta maimaita hirarsu a zuciyarta.

Washe gari tun da asubar fari Aliya ta ishe ta da cewa saura sati guda a kawo mata kayan saka rana, amma Jidda ta yi kamar vata ji ba daga ƙarshe ta ce Allah sanya alkairi amma sai Aliya ta ce baƙin ciki take. Ita kuwa ko da Abba ya sake tambayarta sai ta ce za ta turo wanda zai gaishe shi ya ce za a aiko suna shiri ne daga haka Abban bai sake tambayarta ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull