Kenza eBookz

Sahr khulaiyd complete - Chapter 11

Sahr khulaiyd complete - Chapter 11

Sahr khulaiyd complete Chapter 11: Sahr khulaiyd complete Chapter 11. "Can I feed her and make her take d medicines please aunt, zan tabbata sai ta sha" ya…

4,500 words

"Can I feed her and make her take d medicines please aunt, zan tabbata sai ta sha" ya tambaya whole heartedly. Haka yayi ta magia, babu ynda Mami ta iya dole ta yarda ta mik'a mishi tray d'in, har ta juya zata tafi sai kuma ta dawo tace

"Bawai ina doubting d'inka baneh son, but honestly banason zamanka da little princess alone kuma a keb'e considering d fact that both of you are in love, duk yadda kuka kai ga d'auke kai fah watarana fah shaid'an zaici galaba akanku har kuzo Ku aikata abunda haramun neh fah".

Khulayd ya tsugunna ya ajiye tray dake hannunshi a kasa, sannan ya mik'e ya sake dafa kafad'unta yace "Look at me aunt" Mami ta d'ago tana kallonshi, yace

"Aunt, kinsan irin soyayyan da nake yiwa baby doll ba krya baneh, I love her so much aunt as much as I love my own life, inaso kisan cewa ko babu dangantaka tsakina da ita bazan tab'a cutar da ita bah,trust me aunt I'll neva behave stupidly with her" ya rike wuyanshi ya cigaba

"I swear aunt, ina tsananin controlling kaina when it comes to her, and I assure you nothing like that will ever happen".

Mami ta numfasa sosai feeling at ease, tace

"I trust u son, more than u could eva imagine, kayi hakuri da maganganun dana d'auko, kawai don in tunasar dakai neh saboda shaid'an yakan fi karfin mu.. Its okay, zanyiwa yayana magana akai so we could arrange things and get u married" ta karashe maganar tana dariya tare da d'an bubbuga fuskarshi, ta wuce.

Khulayd ya taking deep breathe kafin yace "Huh... At last".

Turo kofan yayi a hankali ya shiga d'akin. Kwance ya ganta a tsakiyan gado ta dukunkune waje d'aya, he knows she wasn't sleeping don haka ya karaso cikin d'akin, ya ajiye tray'n kan bedside drawer sannan ya dawo ya zaunah bakin gadon.

"Baby doll" ya kira sunanta a hankali. Ta mirgino tare da juyowa ta kalleshi without saying a word Yace

"Tashi kici abinci kinji"

Babu musu ta tashi ta zaunah, Khulayd ya d'auko tray'n ya d'aura kan gadon ya bud'e plate d'in ya fara bata abincin a hankali, sosai taci har saida tace ta koshi don kanta, ya ajiye finger spoon dake hannunshi ya d'auko magungunan ya b'ab'b'alla mata, ya mika mata glass of water babu musu ta karb'a tare da had'iye maganin ta mik'a mishi cup d'in, yace

"Dats my baby, yanzu kwanta kiyi bacci kinji"

Ta gyad'a mishi kai ta kwanta, ya jawo duvet ya rufeta da sannan ya tsaya yana kallonta for some seconds yace

"Would you mind if I kiss u?"

Tayi saurin jan duvet d'in ta rufe kanta gabad'aya, yayi dariya yace

"Just kidding yarrr, sleep like a baby, gud nitee" ya kashe mata bedside lamp d'inta ya juya yayi hanyar waje. A hankali ta lumshe idanunta tace

"Gud night Ya Khulayd"

#TEAMSAHRKHULAYD❤

© *SEEMBY LUFF*😘

⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜

By *Seemby luff*😘

*PAGE 51*

⚜⚜⚜⚜⚜❤⚜⚜⚜⚜⚜

*Saturday_*

Ya ya kama weekend neh, tun 7am 'yan matan Mami suka wuce gym don yin weekend activities d'insu, Nailah ta kalli Sahr tace "Princess ya naga Ya Khulayd bai zo bah, kodai jikinshin neh haryanzu? U better go find out and see don na damu fan". Neenah dake chan gefe tun d'azun bata kulasu bah sai yanzun tayi interfering, ta hararesu dukkansu kafin ta katse Nailah "And why on earth will she do that huh, idan yayi deciding bazai zo bah its none of your business, ni ban cika son mutum me kaud'in tsiya bah wallahy" ta sake hararanta a karo na biyu taja tsoki sannan ta cigaba da abinda takeyi. Nailah tayi murmushi tace "I wonder wa yake kaud'i a tsakanin mu, nidai bazan fad'i komai gaban princess bah bt pls ki rika tauna magana kafin ki fitar, don't push me to the wall Adda Neenah" Sahr ta bubbuga kafafunta a kasa tace "Meyasa kuke yawan fad'a neh wai, I suggest idan kuna da problem kuyi solving a tsakaninku, chacar baki bai karb'eku bah sam". Neenah tace "Yimin shiru Miss right, waye ma ya saki cikin maganar mu, learn to shut up when your elders are having a conversation kina jinah" daga nan Sahr tayi shiru bata sake cewa komai bah.

⚜⚜⚜⚜⚜❤⚜⚜⚜⚜⚜

*Khulayd* Kwance ya kan tangamemen gadonshi, farkawanshi kenan saidai bai iya ya tashi daga kan gado bah, idonshi a lumshe ya mirgino yazo bakin gadon, a hankali ya bude idonshi ya d'aura kan wall clock. 10am ya gani da sauri ya tashi har yana neman fad'uwa yace "Sh*t am late again" ya fad'a toilet da gudu yayi wanka ya fito, a gurguje ya kammala komai ya sanya kayan gym d'inshi ya fito, bai bi ta d'akin Mami ya gaidata bah direct gym ya wuce. Yana karasowa ya hadu da dukka 'yan matan Mami sun gama activities nasu na ranan zasu koma ciki, kusan a tare Neenah da Nailah suka gaisheshi, babu yabo ba fallasa ya amsa su idonshi akan Sahr. Cikin girmamawa da ladabi ta gaidashi

"Lafiya kalau babynah, har kinji saukin da zakizo gym? " ya tambaya yana bid'ar amsa, kanta a kasa tace "Naji sauki fah ya Khulayd, besides ina bukatar in d'anyi exercise don in warware da wuri" Yace "Yeah u are right, jeki huta dai yanzun I'll join u for breakfast soon" ta wuce shima ya shige ciki.

*10:30 AM*

Minti talatin 30 kawai Khulayd yayi a gym ya dawo d'aki ya sake watsa ruwa da sauri ya sauko kasa zuwa dinning room ya tarar kowa is present, shi kad'ai kawai ake jira. Sahr ce take serving kowa abinci ta fara baiwa Mami nata, ta d'auko plate tayi serving na Neenah then Nailah, lastly ta d'auko plate na Khulayd ta d'ago ido tana kallonshi, ya sakar mata murmushi itama haka, without knowing ta buge kagarta da kujeran dinning d'in ta saki plate d'in ya fad'i kasa, ta saki kara jin zogin da kafar ke mata tayi saurin sunkuyawa ta rike kafar, harda d'an jini ta gani ta rufe idonta gam tana "Auuchh, akwai zafi".

Ture kujeran da yake zauneh akai Khulayd yayi ya mik'e ya karasa wurinta da sauri yana tambaya "What happened Bby"

"Ya Khulayd buge kafata nayi, yana zafi sosai" Khulayd ya d'auke hannunta data rufe ciwon dashi yana gani "OMG you are bleeding" ya fad'a cike da damuwa, Mami ce ta katseshi tana cewa "karka damu son, I'll take care of her".

Da haka Nailah ta d'auko first aid box aka wanke ciwon akayi dressing, da kyar ta yarda taci abinci tasha magani don zogin da kafar yake mata. Bayan ta gama shan maganin tacewa Mami zata koma d'akinta, da kyar da d'ingishi ta haura stairs zuwa d'akinta.

Bayan kusan awa biyu, Sahr na kwance a d'akinta, tashi tayi ta zaunah bakin gado ta d'auki wayanta, contact d'in Khulayd tayi dialing ta kara a kunnenta. Yana kwance shima a d'akinshi idanunshi a lumshe yaji wayarshi tana ringing, ignoring yayi without even looking at d phone har kiran ya katse, sake fara ringing wayar tayi a karo na biyu, Khulayd ya tashi fuskarshi a tamke yakai hannunshi kan wayar dake kan side drawer yana kallon screen d'in. Sunan da ya gani neh yasa ya receiving call d'in da Saudi "BBB... Babynah ya akayi, bacci nakeyi and I didn't heard d phone ringing, so meya faru are u missing me already"

A d'ayan b'angaren Sahr tayi 'yar karamar dariya tace "Yeah nayi kewarka, but dalilin kiranka shine I want us to meet at d garden bayan la'asar, inason muyi spending lokaci tare don bamu zaunah ba tunda na dawo, I want us to talk" Shima Khulayd dariyar yayi yace

"Yes Ma, your wish will always be my command.. Luv yhu" ya katse wayan.

⚜⚜⚜⚜⚜❤⚜⚜⚜⚜⚜

*Bayan La'asar*

Kananun kaya Khulayd ya saka ya feshe jikinshi da perfumes masu kamshi yayi styling gashinshi, wayarshi dake akan gado ya d'auka da nufin fita Neenah ta turo kofar d'akin ta shigo, juyowa Khulayd yayi yana kallonta totally speechless yana tunanin meya kawota kuma yau. Karasowa tayi cikin d'akin ta kallonshi daga sama har kasa tace "Umm Mr Omair, I can see you are dressed up and ready to go somewhere, and to tell u what, you look very cute" duk maganganun da takeyi bai ko kulata bah sannan bata ga mood d'inshi ya canza bah, hakan ya bata daman cigaba da magana Tafiya takeyi tana zagayeshi tace

"Mr Omair bansan meyasa bah but na kasa daina sonka, sau da dama ina tirsasa zuciyata amma na kasa especially now dana ganka, everything about u is 'wow, your hair, eyes, nose, small lips and this wide chest... Just like I want it" zata kai hannunta kan kirjinshi yayi saurin tureta ta fad'i kasa

"Don't dare touch me with dos filthy hands of yours, if u dare try it aswear....."

Tashiwa tayi tana kallonshi cikin ido hawaye na wanke mata fuska tace "What if I do? Me zakayi min Mr Omair? Mari, duka ko kasheni zakayi" ta matso gabanshi tace "Ka kasheni, ka kasheni Mr Omair at least zai fimin sauk'i akan irin wahalar da soyayyarka yake bani, I'd rather die Mr Omair" ta fashe da matsanancin kuka kamar ranta zai fita

"Mr Omair bansan me zan maka bah, na baka zuciyata da rayuwata gabad'aya amma har yanzu bai isheka bah, And now am willing to give you my body if that's what you want, am ready"

Dariya Khulayd yayi yace "So this what all this is about right, kwana dani kikeson yi Neenah shine kike nunamin maitarki a fili koh" shiru tayi bata amsa ba

"Tambayarki nakeyi Neenah" ya fad'a da karfin gashe har saida taji kamar ta saki fitsari a wurin, gadan gadan yayo kanta ya turata ta fad'i akan gado, yace

"You want to have s*x with me right, well zan baki wanda bazaki tab'a mantawa bah har karshen rayuwarki" ya b'alle bottons d'in rigarshi ya cire ya wurgar, ya cire vest shima ya wurgar. Zuciyar Neenah ya fara bugawa kamar zai b'alle ya fad'o kasa, Khulayd ya matukar bata tsoro, jikinta neh ya fara b'ari tana girgiza mishi kai amma baya jinta, saima kokarin yage rigar jikinta yakeyi, ya fita a hayyacinshi idonshi yayi jajur.

⚜⚜⚜⚜⚜❤⚜⚜⚜⚜⚜

*Sahr*

Tayi shirinta cikin simple outfit tayi applying light makeup, tayi rolling d'inta mai kyau ta d'auki wayarta ta shiga kiranshi amma baya d'agawa, tunani tayi tace gara ta dubashi a garden, ta wuce ta tafi but couldn't find him there sai tayi deciding ta dubashi a d'aki, komawa tayi ta nufi d'akinshi, tana isa ba ko knocking ta murd'a ta shiga,,,, me zata gani

*Sahr-Khulayd Neenah*

Khulayd ta gani yana kokarin yaga rigan Neenah, he's forcing himself and is trying to rape her

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai Sahr ta iya furtawa da karfi, d'aura hannunta tayi akanta ta sulale kasa tana hawaye, da sauri Khulayd ya ture Neenah da har rigarta ta yage jikinta na mugun b'ari, ta tattaro rigar tana kare kirjinta ta fita tana sauri.

Saka vest Khulayd yayi yazo gaban Sahr dake tsugunne tana kallonshi hawaye na wanke mata fuska, niyyar dafe kafad'unta yayi ta koma baya da sauri tana mishi kallon total stranger, Khulayd ya matse idonshi gam ya bud'e yace

"Look Bby doll, wallahi its not what u think.... I can explain, don Allah ki saurareni" Da hannu Sahr ta katseshi ta mike tana share hawàyenta tace "Baka da abunda zaka fad'amin Ya Khulayd, bazan tab'a yarda da kai bah" ta b'ude kofar tare da banging tayi tafiyarta.

#TEAMSAHRKHULAYD

© *SEEMBY LUFF*😘

⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜

*By Seemby Luff*😘

*PAGE 52*

⚜⚜⚜⚜⚜❤⚜⚜⚜⚜⚜

Buga kofar Khulayd yayi da karfi yayi zaman dirshan a wajen, ya rike kanshi dake baraxanar tsagewa don ciwo yana tunanin ta yaya zai fita daga wannan rikitaccen al'amarin

"Neenah why? Why are u doing dis to me, why do u want to destroy me" ya fad'a yayinda zuciyarshi ke tafarfasa.

⚜⚜⚜⚜⚜❤⚜⚜⚜⚜⚜ *NEENAH*

Tura kofar d'akinta tayi ta shiga ta mayar da kofan ta kulle, dariya ta fara sosai harda hawaye tanayi tana karasa yaga rigar jikinta, saida tayi mai isarta ta juyo tana kallon hoton Sahr dake ajiye saman gadonta, haye gadon tayi ta d'auko hoton tana shafawa a hankali tace "Poor kid sister, am sorry I had to do this cos dis was my plan, na fad'a tun baya cewa Mr Omair nawa neh ni kadai kuma babu mahalukin da zai shiga tsakanina dashi in kyaleshi, it isn't my fault kid sis soyayya ce kuma kinsan soyayya baya sanar da ranar shigan shi da zan iya hana zuciyata fad'awa tsundum cikin sonshi, and now I can do anything, I mean anything to have him even if it means killing someone, babu wanda rayuwarshi ta dameni sama da nashi, I don't care if dukkanku zaku mutu neh so long as zan zaunah tare dashi. Ta numfasa kafin tace

"I know you must be wondering ya akayi nasan zaku hadu da so called Ya Khulayd d'inki a garden, I'll do you a favour and tell you exactly wat happened... Nayi deciding in dubaki a d'akinki saboda ciwon da kika ji wurin dining d'azu, as if I care" tayi dariya "Na tura kofar d'akinki a hankali and u didn't even noticed coz u were talking on d phone so, I paid attention and DAT was how I came to know, so ya kikaga plan d'in nawa? Superb right" ta wurga hoton har saida ya fad'i ya tarwatse a kasa, mikewa tayi daga kan gadon feeling extremely happy tace

"Mr Omair, yanzu zanga yanda zaka fitar da kanka outta dis mess, would u go on your knees everyday and begging dat stupid sister of mine ko kuwa zaka zo inda za'a soka for eternity don yanzu kid sister bazata tab'a yarda da kai bah no matter how hard you'll try... The game begins now" ta sake tsuntsurewa da dariya.

*SAHR*

Shiganta d'akin ta zube nan bakin kofa tana rusar kuka, tuge rolling d'inta tayi ta yasar da gyalen ta tuge ribbon data packing gashinta da shima ta wurgar, ta hargitsa gashin kanta lokaci guda ta zama kamar wata psycho sabon kamu. Kukan ta rika yi har sai da taji kanta yana sarawa , har muryanta ya dashe gabad'aya sai sheshsheka zaka iya ji tun tanayi da karfinta, cusa kanta tayi cikin kafafunta ta zurawa tiles ido

"How could u betray me like this Ya Khulayd, I've loved you beyond imagination, na baka rayuwata, na yarda kuma na aminta da kai and now, saida ka bari nakai kololuwa wurin sonka, sai da ka bari na raini zuciyata kuma ta girma da sonka, sai da ka bari na amintar da zuciyata kuma na ginata kan son zama dakai har karshen lokaci, saida ka bari nakejin zan iya mutuwa duk ranar da bana tare da kai ko soyayyarka, saida ka bari nakejin babu wanda yake da muhimmanci a rayuwata sama da kai and you betrayed my trust, ka rusa duk wad'annan abubuwa cikin mintuna da basu wuci biyar bah" ta sake fashewa da sabon kuka cike da takaici and heart broken.

*KHULAYD*

Kin tashi yayi a wurin yana tunanin yanda zai b'ullowa al'amarin don baya tunanin zai iya jurar rashinta a daidai irin wannan lokacin, gashi Mr Abeed zaizo next week saboda a fara investigating kidnapping d'inta da akayi, yasan zata basu necessary details kan wanda suka aikata haka but shi kad'ai zata ita opening up mishi duk abunda ya faru gashi yanzu Neenah ta b'ata komai. Iskan dake shigowa d'akin neh yaji yana wuce gona da iri, juyowa yayi yana kallon yanda curtains na d'akin suke firewa kamar zasu tuge daga jikin karfen da aka makala su, from no where yaji muryar da bazai tab'a mantawa bah, muryar da yake tsananin bukatar taimakonshi yace "Hello friend, its been a while bamuyi magana bah, looking 4 help?" Muryan ya tambaya

Wani ajiyan zuciya Khulayd yayi feeling at ease yanzun da akwai my taimaka mishi, dube-dube ya shiga yi a d'akin yace "I really need help, wallahi am in a deep shit, ta d'auka ina......" Muryan ya katse mishi zancenshi da cewa "Ta d'auka you were trying to rape her elder sis, nasan komai. So yaya zaka fuskanci wannan al'amarin?"

"Dats d problem damn it, kwakwalwata bata aiki yanzu, am nt tinking straight... Please help me find a way out of this please" Khulayd ya fad'a cike da damuwa, kana ganinshi kasan yana cikin matsananciyar damuwa. "Well I suggest u shld go talk to her now, abari ya huce fah shike ....." Cewar muryan, lokaci d'aya iskan ya daina blowing wanda hakan ya tabbatar wa Khulayd duplicate d'inshi ya tafi.

Buying idea'n cewa yaje ya sameta Khulayd yayi, ya mike ya karasa wurin gadon ya d'auki shirt d'inshi daya wurgar ya sanya, jikinshi a sanyaye ya fita daga d'akin zuwa d'akinta.

*SAHR-KHULAYD*

Da fargaban abunda zai tarar idan ya tunkareta ya shiga da sallama a bakinshi, nan inda take kasan floor ya ganta kuma ya tabbata taji shigowarshi amma ta watsar, tattaki yayi a hankali ya karaso gabanta ya tsugunna yana sauraron sheshshekan kukanta, rasa abunyi da maganar dazai fad'a mata yayi, a d'an tsorace ya kira sunanta "Baby doll" yayi shiru yana jiran ta amsa saidai taki kulashi, d'ago kanta tayi da idonta da suka kumbura tana kallonshi, gashin kanta duk ya baje kan fuskarta, daga ta cikin gashin yana iya hango tsabar ja da idonta yayi. Kai hannunshi yayi da niyyar gyara mata gashin nata taja baya a tsorace, a nutse yace "Please precious don't do this to yourself, ki yarda dani abunda kika gani wallahy ba gaskiya baneh, akwai misunderstanding anan so please ki bani dama in kawar da zargin da kikeyi, ki yarda dani bazan tab 'a cin amanarki ko da da wata ce talk less of your blood sister, I love you so much that ....." Katseshi tayi ta hanyar cewa

"Don't you dare utter those words to me, ka saurari kanka manah Ya Khulayd, kanaso in yarda cewa abunda idanuna suka gani karya neh is that what u r saying? Ya Khulayd you tried to rape my sister, kasan abunda hakan yake nufi kuwa?"

Da karfi yace "no I didn't" har saidà ta razana, Sahr tayi murmushin yak'e, tana kallon cikin idanunshi tace "Kasan me? This conversation is over, we are done"

Har kashin zuciyarshi yaji furucinta na karshe ' _we are done_', cikin rashin fahimta yace "What do u mean _we are done_, ban fahimçeki bah baby doll"

"Ina nufin soyayyarmu ya kare, Its over between us, baka chanchanci soyayyata bah tun farko, I was blind to have fallen for someone like you macuci mayaudari,,,, idan baka da abunda zaka fad'a mai amfani ka fitar min a d'aki, zayyi magana tace

"I said get out" ta fad'a da karfin gaske, lokaci guda ta birkice mishi tana nuna mishi kofa da yatsarta, da mamaki kwance kan fuskarshi yake kallonta

"Ko ki yarda dani ko a'a, ban aikata bah, and no matter wat happened I'll always love u" daga haka ya fita ya barta, ta sake zubewa kan floor ta fara sabon kuka.

Heart breaking right?💔 Oh poor Khulayd, I wonder wat he's going through right now

#TEAMKHULAYD❤

© *SEEMBY LUFF*😘 [3/22, 6:22 AM] 0mmer Farouk: ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ By *Seemby-luff* 😘 *page 53*

Komawa d'aki Khulayd yayi ya zube kan gado ya d'aura both hannayenshi a kanshi don ji yakeyi kan yana barazanar fashewa, zogi sosai zuciyarshi keyi haryanzu ya kasa gaskata abunda yake faruwa don gani yake kamar a dream land yake ba reality bah, kalmarta na karshe neh yake ta yawo a kanshi, " *we are done* ", yanzu har abunda ya faru yakai wanda precious d'inshi zata rusa soyayyar da ya dade yana ginawa a cikin zuciyarta, didn't she believed in him, didn't she trust him like she used to say??, duk tambayoyin nan yanaso ya yimata su neh kuma yana bukatar amsoshinsu daga gareta saidai yasan bazai tab'a samun amsoshin bah with wat just happened. "Noo, we can't be done precious, we are meant to be together and our love is too far from coming to and end, ke tawace ni kadai and I'll do anything to win your trust back" surutun da yake tayi kenan ya fad'a kan gado yana runtse ido, a hankali siraran hawaye suka fara zarya a gefen fuskarshi.

Yini yayi a d'aki shi kad'ai yana ta faman tunani, har zama yayi kamar wanda ya shekara yana ciwo duk yayi wani iri, har lokacin lunch yayi baiko yi tunanin sauka yaci abinci bah. Duk sun hallara a dining don lunch, harda sahr data sha kukah idanunta suka kumbura sosai, a hankali ta janyo kujera ta zaunah kusa da Nailah, Mami ta kafeta da idanu tun shigowanta tace "Little princess meya faru neh na ganki wani iri duk kin zama kamar mai ciwo, ga idanunki a kumbure kamar wacce tasha kukah, what's wrong?"

Kamar bazata bud'e baki tayi magana bah tace "ba komai Mami, cikina neh ke ciwo shiyasa nayi kukah"

"A'ah Sahr kar kiyi min karya, nasan abunda ke saki irin ciwon cikin da zakiyi kuma and looking at d calendar zakiga cewa time d'in bai zo bah so tell me what's wrong with u will u?" Mami ta karisa maganar tare da tsareta sosai

Marairaicewa Sahr tayi kamar zata yi kukah tace "believe me mum, maybe I ate sumtin am allergic to shiyasa ya sani ciwon cikin" From nowhere Nailah tayi interfering "and what's dat thing u ate dat u're allergic to kid sister don ban tab'a sanin kina da allergy da wani abu bah",, Da taga zasu dameta da tambayoyin da bazata iya amsasu bah ta mik'e kawai ta haura sama, a nan neh Mami da Nailah suka gane akwai wani abu a kasa musamman idan sunyi la'akari da cewa Sahr bata tab'a reacting haka bah kuma bata karya, toh meyasa zatace cikinta na ciwon alhalin ga damuwa kwance a kwayoyin idonta, "Mami ki kyaleta kawai zan bincika manah meke damunta" cewar Nailah.

Ajiyar zuciya Mami tayi duk da cewa abun ya dameta ganin halinda autarta take ciki, "shi kuma yayan naku meya hanashi saukowa yaci abincin?, ko zaki duboshi neh Nailah?" Mami ta tambaya, "a'a Mami dadai kin kyaleshi don kinsan bai cika son yin lunch bah, maybe sai dinner kinsan d'an naki akwai shegen ra'ayi" Nailah ta bata amsa a takaice "Eh hakaneh fa kuma" cewar Mami, daga haka suka cigaba da cin abincinsu babu wanda ya sake cewa komai, Neenah kam dama kamar bata wajen, saidai wanda yayi magana ta juya ta harereshi.

⚜⚜⚜⚜❤⚜⚜⚜⚜

*08:30 pm, same day*

8:30 Mami ta kirasu zuwa dining don dinner, har Sahr tayi ignoring kiran da Mami tayi mata don bata da appetite, she don't think she'll eat anything amma sai ta deciding taje kawai don idan taki zuwa tayi inviting more questions daga wurin Mami, sum sum ta mike ta fitoh daga d'akinta zuwa balcony, a hankali ta juya ta juya tana kallon balcony'n d'akin Khulayd, haka kawai ta tsinci zuciyarta da kwad'ayin son ta ganshi, tana masifan son ta d'aura kwayan idonta a kanshi ammah sai ta tuna incident na d'azu, da sauri ta wuce ta nufi stairs ta sauka zuwa wurin su Mami.

"Wai meya rikeki neh tun d'azu ana jiranki kin wani makale a d'aki, kinsan na tsani in kira mutum ya ajiyeni ina jira koh" Mami ta kama bambami

"Am sorry mummy" kawai ta fad'a tayi zamanta kamar d'azu kusa da Nailah, haka kawai ta tsinci kanta da kyamar zama kusa da Neenah, duk abunda takeyi Mami na lura da ita kuma tanaji a jikinta something isn't right, bayan anyi serving kowa, suka fara ci banda Sahr da ba abunda takeyi banda wasa da abincin, bata kai koda loma d'aya zuwa bakinta bah, da abun ya ishi Mami a fusace tace "Sahr y did u lied to me earlier?, meyesa zakice ba abunda ke damunki bayan u don't seem alright... Okay mu kaddara d'azun kin fad'i gaskiya kuma na yarda dake, yanzun fah? Y are u not eating??"

Kukah sosai Sahr ta fashe da kamar dama jiransu takeyi suce wani abu, "y won't all of u leave me alone, banason magana daku harda Yaya Khulayd d'in, I so much hate his guts" tana gama fad'in haka ta ture plate dake gabanta har saida ya fad'i kasa ya tarwatse ta mike tayi tafiyarta. Ba Mami da Nailah bah, har Neenah saida ta tsorata da action na Sahr amma ta tab'e baki kawai don tasan abunda ke faruwa..

"I wonder what had happened between those two" Nailah ta fad'a tare da mikewa itama tabi bayan baby sister'n ta tabar Mami awajen tana jimami, hakan yasa tayi tunanin cewa akwai nasaban hakan da rashin zuwan Khulayd lunch d'azu gashi ya sake skipping dinner yanzu, yanke shawarar zuwa d'akinshi taji daga bakinshi abunda ya faru.

⚜⚜⚜⚜❤⚜⚜⚜⚜

*Sahr*

Tura kofar d'akin tayi ta shige tare da slamming kofar ta zube kasa ta fara rusar kukah, takaici neh makil cike da zuciyarta, all her life bata tab'a son wani d'a namiji bah, bata ma san soyayya bah sai akanshi amma ya rasa sakayyar dazai mata sai cin amanah, "Ya salaam" ta furta cikin kukah, bata masan Nailah ta shigo bah "Ya Allah ka ciremin soyayyar wannan bawan naka daga zuciyata kafin ya zautar dani, Ya Allah ka musanya min soyayyarshi da mafi alkhairi a gareni" ta runtse ido sosai tana cewa *na tsaneka Yaya Khulayd, I hate you"

"And why will u hate him?" Ta tsinkayo muryan Nailah a bayanta, bata ko damu da cewa Nailah'n taji furucinta bah, a hankali Nailah ta dawo tana fuskantarta ta tsugunta tare da tallabo hab'arta ta d'agota suka koma bakin gado, a hankali ta fara goge mata hawayen dake zarya akan kuncinta tana kallon cikin idonta tace "Baby sis, whatever happened nasan cewa bah laifin Yaya Khulayd baneh kuma decision dakike neman yankewa yanzu isn't right, u have to seek for solution and to find a solution saikin sharing da wani, ba lallai baneh sai ni but u have to talk it out so u can be relieved, kiyimin magana baby sis, meke faruwa?"

Hannu Sahr tasa tana share hawayenta kafin tace

"Adda Nailah munyi planning had'uwa nida ya Khulayd a garden so I went there but couldn't find him, sai nayi deciding in dubashi a dakinki na dawo ciki, Adda Nailah u won't believe what I saw, Yaya Khulayd neh forcing himself on Adda Neenah, fyad'e yakeson mata wallahi na gani da idanunah" ta sake bursting into tears

Murmushin yake Nailah tayi tace "haba, bazanyi mamaki bah, biri yai kama da mutum.... NEENAH WHY?" D'agowa tayi ta sake kallon Sahr a karo na biyu tace "And you believed what u saw? Kina ganin Yaya Khulayd zai iya aikata hakan akan neenah? Think about it sis, Yaya Khulayd ba irin mazan da kikeh tunani baneh bazai tab'a aikata haka bah, ki tuna fah basa ma jituwa bare har irin haka ya shiga tsakanin su and now kina blaming poor Yaya Khulayd bakya blaming 'yar uwarki" Da sauri Sahr tayi interrupting "but Addah Neenah bazatayi haka bah, she won't"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull