Kenza eBookz

Sahr khulaiyd complete - Chapter 13

Sahr khulaiyd complete - Chapter 13

Sahr khulaiyd complete Chapter 13: Sahr khulaiyd complete Chapter 13. Tun daga ranan Khulayd bai sake bari sun had'u da Sahr bah, kwata kwata kallon zargin…

4,476 words

Tun daga ranan Khulayd bai sake bari sun had'u da Sahr bah, kwata kwata kallon zargin da take yi mishi yana sashi zama uncomfortable shiyasa yayi deciding har sai ranar da zai cire zargin dake tsakaninsu daga zuciyarta bazai bari su had'u bah, decision d'in daya d'auka wasn't an easy one coz its eating him up amma bai da wani sauran hanya. Gabad'aya hankalin Sahr yakai makura wurin tashi, duk hanyan da tabi don ta ganshi abun yaci tura. Ba kamar ta gama yafe mishi abunda ya aikata bah amma tana matukar bukatar ganinshi, she never thought abun zai kai har haka if she chose to abandoned him but it appears to be very difficult, duk ta rame ta lalace har ta fita kamanninta. Zauneh take kan gado tasa fuskanta cikin kafadunta tana kuka data saba, tun tashinta daga bacci bata ko sauka akan gadon bah kuma bata da niyya, tura kofar d'akin Neenah tayi ta shigo tun daga bakin kofan ta tsaya tana kallonta, jin kamar an bud'e kofa yasa Sahr ta d'ago taga ko wanene, da sauri ta mayar da fuskarta inda ta cirosu don ji takeyi kamar ta shake Neenah yanzu, sam bataso ta ganta domin a ganinta da Neenah bataje d'akin Khulayd a wannan ranar bah he wouldn't have tried to rape her, ko kayan dake jikinta a ranar bai kamata taje d'akin Khulayd dashi bah idan har ya zama dole toh she should have wore a hijab, yar Neenah ta karasa wurin gadon ta zaunah Sahr bata sani bah sai ji tayi an dafata, da sauri ta ture hannun Neenah daga kafad'anta ta ja baya kamar wacce bata santa bah, ajiyar zuciya Neenah tayi da d'an murmushi tace "haba kid sister umm, meyasa kike yiwa kanki haka ne wai? Abu ya dad'e da faruwa but u couldn't get over it, kar kixo fa ki sawa kanki ciwo don tunani da rashin cin abinci, ko ni da am d victim I've long forgotten about it tunda it wasn't my fault, he couldn't stand seeing me the way he did perhaps dat was y he tried to rape me". Kasa daurewa Sahr tayi da maganganun da Neenah take fad'a, a fusace ta d'ago kanta da fuskarta daya zama ja tana kallon cikin idonta tace "And what the hell took u to his room da wancan kayan Addah Neenah, idan shi ya nemi kije d'akinshi ai sai kisa something decent, u couldn't have go like that ko ba haka bah?" Ta tambaya ba tare da ta cire idonta a cikin na Neenah'n bah. Sadda kai kasa Neenah tayi tana kame kame tace "bbbbb.... Ba haka bane kid sister, ya kirani a landline and he sounded urgent shiyasa na damu inje, I thought ko babu lafiya neh dats y" "Ko dama hakan neh Addah Neenah zaki iya saka hijabi akan kayan ai ba saikin canza bah, with wat u were wearing ba Yaya Khulayd ba ko wani namiji zai iya shiga wani yanayi. It wasn't his fault daya kasa controlling kanshi but yours tunda ke kika bashi daman aikata haka and something isn't right at all here, idan Ya Khulayd was desperate to talk to someone then zai zama Mami ce ko ni, let's just say 'Mami' don itane mutum d'aya da yake iya bud'e mata sirrin zuciyarshi kuma ya nemi shawararta, d last time I checked baku ma in good terms dashi bare har ya kiraki wen he needs someone to talk to, can u explain this to me?" Sahr ta tambayeta tana jiran amsa, mikewa Neenah tayi daga zaunen da takeyi zuciyarta na tafarfasa sai huci takeyi tace "I beg your pardon miss, karki ga don nazo d'akinki ki gayamin son ranki manah, last time I checked nima am older than you, but keda Nailah kun zab'i ku rainani ku d'aukeni ba a bakin komai bah and u choose to respect her more than u do me" ta d'an numfasa kafin tace "now listen and listen good, I owe u no explanation regarding this, raping nawa neh yaso yayi kuma ko ku yarda ko karku yarda ya rage naku I don't give a hurt about it, banzaye kawai" tana gama fad'in haka tayi ficewarta tare da slamming kofar 'banng'. Mami na zauneh sanye da medicated glass d'inta tana duba wasu takardu Khulayd ya turo kofar dakin ya shigo da sallamarsa, ta amsa sallamar saidai bata d'ago ta kalleshi bah ya samu wuri kan sofa ya zaunah yana jiranta ta karisa. Bayan ta gama ta cire glasses d'in ta ijeshi kan side drawer ta juyo tana kallonshi, "sannu da aiki aunt" ya fad'a yana d'an murmushi, itama murmushin takeyi tace "yawwa son, ya akayi neh?" Komawa kusa da ita yayi a bakin gadon ya kamo hannayenta both yace "Aunt, nasan har yanzu u re suspicious of me kan maganan Neenah duk da kin tabbatar min cewa kin aminta dani kuma kinsan bazan iya aikata hakan bah but, duk lokacin da kika kalleni I feel guilty, somewhere in your heart kina zarginah, somewhere in your heart kina gani kamar ni naso aikata hakan" kafin ya cigaba Mami ta katseshi "son na aminta da kai like I said, but kasan its natural mutum ya rika feeling haka a zuciyarshi especially a situation d'in da aka kasa gane mai gaskiya a tsakaninku, not only u ita kanta Neenah am suspicious of her, abunda dai na sani akwai ranar da gaskiya zaiyi halinshi, at times shaidan zai iya sa mutum ya aikata abunda zuciyarshi bayaso daga baya kuma yayi nadama don haka don't blame your aunt son, kaaji" gyad'a mata kai yayi kamar karamin yaro yace "I understand aunt, shiyasa na yanke shawarar fito da mai gaskiya da mai rashinta a cikin mu, kuma nayi miki alkawarin cewa bazaki tab'a kamani da laifi bah" "kamar yaya fah?" Mami ta tambaya demanding for an answer, Khulayd ya murmusa kafin ya fad'a mata abunda zatayi daga haka ya fice ya barta tana jinjina lamarin. *later that day*

Kwance yake kan gadonshi yana ta faman kallon ceiling, a hankali ya tashi zauneh ya fara kokarin cire jallabiya da yake sanye dashi har ya gama cirewa ya ajiye a gefenshi ya rage daga shi sai singlet da gajeren wando, matsowa yayi kusa da drawer da landline ke ajiye akai ya d'aga yana son danna digits na d'akin Neenah sai dai ya manta, sanya yatsan shi yayi kan lips d'inshi yana son tunawa yace "my digits end with 0, Neenah's should end with 1 tunda shi aka fara bashi kafin ita thought dukkansu digits nasu d'aya neh and only d last digits differs" dannawa ya shiga yi ya kara a kunnenshi, chan kusan kiran ya kusa yankewa ta d'aga tace "hello Mr Omair" ta wani juya muryanta da wani irin salo na musamman, shi kuwa Khulayd runtse ido yayi yana kokarin danne zuciyarshi don muryanta tamkar guba neh wa kunnenshi, da kyar ya iya daidaita kanshi yace "Neenah I need u in my room now pls" murmushi Neenah tayi tace "Mr Omair lafia, kasan fa last time dana je d'akinka ya jawo maka matsala tsakaninka da Bby doll d'inka, baka gani akwai matsala idan ta sake ganina?"..... "I really don't care anymore Neenah, yanzu dai ke nakeson gani" cewar Khulayd, cike da jindadi tace "toh Mr Omair ganinan zuwa" har zata katse yayi saurin dakatar da ita da cewa " please do wear a sexy outfit, I liked d one u wore d oda day" yana gama fad'in haka ya katse kiran ya koma ya kwanta tare da lumshe idanu yace "Ya rabbi forgive me". Bayan Neenah ta ajiye wayan tayi ihu ta daka tsalle tace "YES, finally he'll be mine forever, karka damu Mr Omair, I'll give it to you whichever way u want it and after today you will never think of another woman other than N E E N A H"

Written by: Seemby luff😘 Posted on: Thursday Date: 15th march, 2018 Time: 12:30pm

© *SEEMBY LUFF*😘 [3/22, 6:23 AM] 0mmer Farouk: ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff*😘 Page *58*⚜

Wani shu'umin silky gown ta saka duk yabi shape d'in jikinta ya fitar da every corner dake jikinta, tayi packing gashinta one side sannan ta feshe jikinta da Arabian perfumes mostly Oud masu dad'in kamshi, ta d'auko lallausan slippers ta saka a kafarta ta fita bata ko fargaban zata had'u da wani, kai tsaye ta nufi balcony da zai sadata da d'akin khulayd, da wani taku da yafi kama da wahainiya ta isa door step d'inshi, saida ta tsaya ta sake gyara zaman rigan a jikinta tukunna ta murd'a handle d'in ta shiga babu ko sallama. Yadda yake tun d'azu akan short da singlet ta tarar dashi kwance saman gadonshi, jin an tab'a kofar yasa yad'an d'ago dukda yasan ko wayene, runtse idanunshi yayi ganin irin shigar da tayi, "she looks damn hot" ya fad'a a zuciyarshi sannan yace "ya Allah ka kareni daga sharrin shaid'an, ya Allah am doing dis in defence of my self ya Allah ka taimakeni kasa in fi karfin zuciyata" har Neenah ta karaso bai sani bah don har lokacin idanunshi a runtse suke, kamshin perfume nata neh ya tabbatar mishi da cewa she's close to him, ya bud'e idanunshi a hankali ya saukesu a kanta, zauneh tayi a bakin gadon ta d'aura kafarta na dama akan hagu with a smile on her face tace "Mr Omair u wanted to see me, is anything the matter?" Tab'e baki khulayd yayi kamar baison magana tukunna yace " ba komai Mrs Mukhtar, I just want to make it up to u, I've realised how foolish i was to have turned down your offer gashi yanxu precious taki believing d'ina duk da cewa ban aikata abunda take tuhumata akai bah, nayi iya kokarina in fahimtar da ita cewa abunda idanunta suka gani ba gaskiya baneh but all my efforts were in vain, so sai nayi tunanin gara inyi sai tayi punishing d'ina da tushe, besides your re such a beautiful lady" ya mika mata hannunshi ta rike tare da d'agata yana juyata daga tsayen da take yace "ba kowani namiji baneh zai kalleki sau d'aya bai sake na biyu bah" daga kafanta ya fara gani yana d'agowa da hankali ya tsaida idanunshi kan waist d'inta, bugawa yad'anyi da hankali yace "just d way I like it" ya cigaba da d'ago idonshi har ya tsayar dasu kyam akan kirjinta, zuciyarshi ne ya fara bugawa da sauri sauri kamar zai b'alla kirjinshi ya fito, da sauri ya kawar da kanshi gefe yana cewa "A'uzubillah" ya mike shima suna facing junah, "All I want ryt now is you Neenah, nothing matters anymore" ya fada yana kallon cikin idonta, wani fari tayi da ido tana yauki tace "your wish is my command Mr Omair, yau ina cikin farin ciki mara misaltuwa tunda zan kasance da wanda zuciyata ya d'ad'e yana marari, koda yau kad'ai ka kwanta dani kayi dumping d'ina bazan gushe bah zan zauna cikin farin ciki iya tsawon rayuwata don zanyi alfahari da cewa na tab'a sharing wani abu special da wanda nakeso, bare kuma nasan you won't dump me after dis koh Mr Omair?". Girgiza mata kai yayi yana murmushi yace " never Mrs Mukhtar, tayaya zanyi dumping macen da ta yarda ta shayar dani farin ciki? Tayaya zan watsar da macen da ta yarda zata bani jikinta a kyauta ba tareda taji fatgaban mai zai iya biyo baya bah? Tayaya zanyi dumping macen da tayi downgrading kanta to dis level a gabana don soyayya? Zuciyata bazata tab'a bari inyi miki haka bah Neenah, zuwa yanxu na yarda cewa kece macen da take tsananin sona duk fad'in duniyan nan" saida yad'an yi murmushi shu'umi kafin yace " would u mind if I see naked?" Ko d'ar Neenah bataji a zuciyata bah tace "I wouldn't mind Mr Omair, I'll do wateva pleases u" babu shiri ta watsar da slippers na kafanta ta fara kokarin cire rigan jikinta, abu kad'an ya hana khulayd ganin kirjinta sabida ko bra bata saka bah, banke kofar akayi from nowhere, da sauri Neenah ta sauke riganta ta juya taga ko waye keson b'ata wannan moment d'in, sai ganin Mami da Sahr tayi a tsaye fuskarsu d'auke da mamaki marar misaltuwa, matsawa gefe khulayd yayi ya hard'e hannunshi kan kirjinshi yana kallonta a yayin da ta shiga yin kallon kallo da Mami da Sahr.

Kuyi min afuwa babes, d page is kinda short, but nasan zaiyi gingering naku kad'an.

Posted on Tuesday Date: 20th march 2018 Time:05:04pm Written by Seemby luff😘

© *SEEMBY LUFF*😘 ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff*😘 Page *59*⚜

A fusace Mami ta karaso gaban Neenah without uttering a word da iya karfinta ta wanke fuskanta da wani mari mai rud'a mutum, a rud'e Neenah ta dafe kuncinta tana ji kamar tsinke namañ fuskanta akayi don zafi ta d'ago kai tana kallon Mami tace "Mami me nayi kuma kika....." Bata karasa abunda takeson fad'a bah ta sakejin saukan wani marin a d'ayan b'angaren fuskanta, dafe kuncin ta sakeyi nan take hawaye ya fara wanke mata fuska, cikin tsiwa tace "wai ni Mami me nayi ne kam kiketa marina continuously without asking me or even allowing me to explain? Ni a iya rayuwata da girmana you've never raised your hands on me talk more of hitting me mom, kamata yayi ki tambayeni meke faruwa ko kuma meya kawoni d'akin Mr Omair, koda ma baku zo nan yanzu bah I was going to tell u abunda ke faruwa da kudirin Mr Omair a kaina" nan take ta fara kokarin juya maganar zuwa wani direction. Sahr ce tayi interrupting d'inta cikin b'acin rai tace "meye Mr Omair yayi kuma this time Adda Neenah? Yau d'in ma yayi forcing d'inki zuwa d'akinshi and he's trying to rape u again right? Gashi u look very sexy in this dress, did he also forced u to wear it? C'mon ki fad'a mana Adda Neenah". Hard'e hannu Sahr tayi kan kirjinta itama tana jira taji me Neenah zata fad'a kuma yau, kuka Neenah ta hau yi babu kakkautawa tace "he he he threatened to fire me from work idan ban bashi had'in kai bah, kuma yace dama tun farko he never loved kid sister ni yake so, ni kuma I so much love my job bazan iya barin OGC bah dats y I agreed" ta matso gaban Mami dake tsaye tun d'azu speechless ta rike hannayenta dukka biyu tace "believe me mother, Wallahi am saying d truth, threatening d'ina yayi" fuske hannu Mami tayi daga rikon da tayi mata ta sake sauke mata wani marin a karo na uku, idanunta sun kad'a sunyi jajur zuciyarta na tafasa ta kalli Neenah a cikin ido tace "this is for lying to my face Neenah, am very disappointed in you, d'abi'arki is very disgusting Wallahi. Yau d'innan kin tabbatarmin da cewa nayi hasarar tarbiyyan dana sha wahala ina baki da 'yan uwanki, all dis years da mahaifinku ya bar duniya nasa effort sosai wajen ganin cewa kun samu ingantacciyar tarbiyya, I raised you girls single handed ba tare da taimakon ko da 'yan uwan mahaifinku bah amma shine sakayyan da zakiyi min?" Hawaye masu zafi neh suka fara zarya a kan kumatunta taci gaba "Wallahi nayi dana sanin haihuwarki Neenah, how I wish da b'arin cikinki nayi mutane su gaisheni bayan wani lokaci in manta da yafi min alkhairi". Da sauri Khulayd ya karaso gaban Mami ya d'aura hannu akan bakinta yana girgiza mata kai yace "No aunt, please don't say this, abunda kike cewa bazai kareta da komai bah saidai ya b'ata mata rayuwa, u re a mother aunt u shouldn't be saying this, ni dai nayi haka neh don inyi proving innocence d'ina a gabanki of which I did, bazan tab'a iya jurar ganin zargina cikin kwayan idonki bah amma kamata yayi kiyi mata addu'ar shiriya ba na tab'ara bah" d'aga mishi hannu tayi alamar ya dakata tace "no son, Wallahi nayi dana sanin haihuwarta, she's a disgrace to this family" daga haka bata sake cewa komai bah ta juya tayi ficewarta daga d'akin. Taafi Sahr ta farayi tana murmushi tana yiwa Neenah kallon sama da kasa tace "Well done Adda Neenah, well done. Lallai kin iya juyarwa mutum tunaninsa, kinyi nasarar cusamin zargin wanda nakeso a cikin zuciyata, kinsa ina yi mishi kallon macuci kuma mayaudari alhalin sam ba halinshi baneh, abunda kawai kika kasayi shine cire sonshi daga zuciyata saboda the bond is very strong that it cannot be broken this easy, da har ina tunanin sadaukar da soyayyata ga 'yar uwata domin a ganina u love him more than I do but kin san me? U don't deserve this, c'mon Adda Neenah am your blood sister fah, how could u even think of doing this to me, why??" Itama ta kare maganar tana hawaye. Kallon Neenah Khulayd keyi tun d'azu a kyamace yace "well, am so sorry sexy Mrs Mukhtar it was all a setup and am happy it worked, at least yanzu za'a daina zargina kan abunda ban aikata bah kuma ki sani, koda babu riga na ganki bazan tab'a jin sha'awarki bah coz I hate u so damn much". Juyawa Neenah tayi tana hararan Sahr na d'an wani lokaci don ta kasa cewa komai sannan ta juya kan Khulayd shima tana cizan leb'b'e, a sanyaye ta juya ta fita daga d'akin. *Sahr-Khulayd* Neenah na fita Khulayd ya juya da barin kallon Sahr, a zuciyarshi kuma yana jindadi at least yanzu precious d'inshi zata daina fushi dashi and everything will be back to normal between dem again. A hankali Sahr ta tattako ta tsaya dap bayanshi, so takeyi tayi tapping d'inshi a kafad'a amma da zarar ta kai hannunta sai kuma ta sake saukewa, sau uku takeyin haka daga karshe kawai taja dogon numfashi tana murmushi kamar yana ganinta, cikin 'yar siririyar muryanta tace "Jaan" shiru yayi mata kamar baisan dashi takeyi bah, kusan sau 4 take kiranshi amma yayi banza da ita, murmushin ta sakeyi don tasan dalilin kin kulata da yayi laifinta neh tace "Jaan am sorry, Wallahi situation dinne yai min tsauri and I've never experienced this my whole life, gabad'aya tunanina ya jagule bansan wanda zan yarda dashi a cikinku bah, ban tab'a yarda cewar Adda Neenah zatayi downgrading kanta har zuwa level d'innan bah, ban tab'a zaton zatayi kokarin kwace min farin cikina bah duk da cewa Adda Nailah taso ta ankarar dani, haka kuma kaima ban tab'a yarda zaka iya kwana da blood sister na ba. Try and understand me Jaan wallahi duk da faruwan wannan abun daidai da rana d'aya sonka bai tab'a raguwa a zuciyata bah, am having the best experience of new life with u Jaan and u re the best thing that has ever happened to me, kayi hakuri da rashin yarda dakai da nayi nasan na bata maka rai, I knw I shuld have believed u wen u said u didn't do it saboda banga komai a idanunka bah sai zallar gaskiya, please forgive me Jaan, please" ta kare maganar tayi narai narai da ido kamar zatayi kuka tana son jin abunda zai ce amma duk maganganun data fad'a baisa ya juyo bah haka kuma bai kulata bah, hakan yasa kawai ta fashe mishi da kuka don shine iyakan option da take da.

Written by seemby luff😘 Posted on Monday Date:26th march 2018 Time:12:14pm

© *SEEMBY LUFF*😘 ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff* 😘 Page *60* ⚜

Babu shiri Khulayd ya juyo yana mai jin haushin kanshi, meyasa baya iya banza da ita na tsawon lokaci neh, meyasa baya iya jurar jin kukanta neh, kamar zaiyi kuka yace "karki ma fara precious, kinsan fah banason kukan nan so meyasa kikeyi um?" Cikin muryanta na kuka tace "toh ba kai baneh inata magana tun d'azun kaki kulani, ko kallona ma bakason yi bayan kuma hakuri naketa baka, I said am sorry" fusgar da iska yayi yana kallon yanda bakinta ke motsi da shagwab'anta, shikam yanason komai game da yarinyar nan, "toh kuma sai aka ce miki sai kinyi kuka kafin na kulaki, wai meyasa kikeson kuka neh bby doll" ya tambayeta yanaji kamar ya had'iyata ya huta, turo baki tayi zuwa gaba tace "saboda nasan bazaka iya jurar jin kuka na baneh nayi and it seemed d only option I had, ai yanzu gashi ka kulani koh" murmushi yayi "it seemed d only option I had" ya kwaikwayi maganarta yad'an shafi gefen fuskanta yace "u just knw my weak point, kuma kin iya sanyani farin ciki koda a wani irin yanayi yakeh, I Luv u precious soo very much" ya kare maganar yana kallon cikin idonta, saurin sunkuyar da kanta tayi don bazata iya kallon cikin idonshi bah sannan kasa kasa tace "and I you Jaan" d'ago chin d'inta yayi yana kallonta tayi saurin rufe idonta gam "ban yarda da wayon nan bah, ki fad'a to my hearing cewa kina sona kema" kamar bazata ce komai bah, shiru yad'an gifta nadan lokaci a d'akin kafin daga bisani tace "I love you too Jaan" tana gama fad'in haka babu shiri yaji ta zille ta fice da gudu tana dariya, dariyan ya shiga yi shima ya koma bakin gado ya zube yana "I love this girl, she finally made me laughed after some days of sadness... Thank you for the gift Ya Rabbi" ya fad'a tare da kwanciya da bayanshi yana kallon ceiling.

Neenah tana komawa d'aki ta buga kofar bangg kamar zata b'alleshi, watsi ta farayi da duk wani abun da ta gani a cikin d'akin tanayi tana huci, hawaye kuma na cigaba da zarya gefen kumatunta, surutai kawai take tayi without even knowing wat she's saying, duk abunda yazo bakinta kawai furtashi takeyi " Wallahi Mr Omair kai nawa ne ni kad'ai, if I can't have you then no woman can, u re mine, u belong to me" daukan abun rataya jakakkuna tayi ta buga mirror dashi ai kuwa ya tarwatse sai karan zubewan glasses kawai akeji a d'akin, duk tabi ta sauya lokaci guda ta koma kamar zautacciya, tsayawa tayi turus tana bin d'akin da kallo tama rasa meye zatayi ta hango wayanta ajiye kan bedside drawer kuma da shi take nema, d'aga kafarta tayi da niyyan zuwa ta d'auko wayan taji ta taka wani broken glass ya soke mata kafa a bazata, kara ta saki "Aaarrgggh" ta zube a wurin tana jin zogin har kwakwalwarta tayi shame shame hawaye da majina duk sun wanke mata fuska, kamar wacce tasha wani abun maye ta fita hankalinta tace "Mr Omair idan ban sameka bah zan iya yin hauka, wallahi zanyi hauka". Akan kunnen Nailah ta fad'i maganar daidai lokacinda ta shigo d'akin, da mamaki take kallon d'akin yanda Neenah tayi kaca kaca dashi, tab'e baki tayi tace "mafarin haukan kenan ai big sister, kin ma yi haukan tunda ga d'akinki yai kama da na mahaukatan, sai ma uncle Abeed yazo an gane cewa da hannunki cikin abducting na kid sister zaki karisa haukacewan, as your sister I'll advice u tun wuri ki cire Mr Omair daga ranki coz he'll never b yours, from wat am seeing ma zan iya cewa you re just lusting after him" ta kare maganar tana d'an kokarin shigowa cikin d'akin, tsorata tayi lokacinda idonta ya sauka kan kafar Neenah dake ta zubar da jini, babu shiri ta karasa tare da durkusawa a wurin tana "OMG Neenah u re bleeding, garin yaya kikaji wannan raunin? D blood is too much" ta fusge d'ankwalin kanta da nufin tare jinin don babu wani abu a kusa, mika hannu tayi da niyyan rik'e kafar Neenah ta daka mata wani tsawa tace "don't touch me with those filthy hands, kamar kin damu dani when u guys treat me like am not part of you, banason munafurci karki tab'ani". Murmushi Nailah tayi, tayi kamar ba da ita Neenah ke magana bah ta shiga d'aure mata kafan tace "Mu bamu k'i ki bah Neenah, halinki neh kawai bamuso kuma ya zama dole a fad'a miki gaskiya komai d'acinta don baki fi karfi bah, yakamata ki saduda ki zubar da makaman yakinki don alama ya nuna cewa baza ki ci nasara bah, what baffles me most is idan na tuna cewa wanda kikeyi domin shi d'in ma bai sonki, hasalima ya tsaneki amma kike kokarin cusa mishi kanki, ki sauya tunani don Allah don wannan sam batai bah". Ture hannun Nailah Neenah tayi dajin kalamunta ta nuna mata kofa da yatsarta tace "zoki fitar min daga d'aki marar hankali kawai, just get out" mikewa Nailah tayi tace "dama ai zan fitar miki daga d'aki tunda ba mu biyu baneh akai, I just came to check on u neh dama danaji karan fashewan glasses kuma yanzun ma na taimakeki neh saboda bazan iya kyalewa baneh, zuciyata ba irin taki baneh daya riga ya bushe" tana gama fad'in haka tayi waje tana "Mr Omair dai kid sister yakeso, so deal with it".

Mami na komawa d'akinta direct wardrobe d'inta ta wuce ta b'udeshi, ba jimawa ta fito da wani babban enlargement na hoton mijinta, a hankali ta mayar da wardrobe d'in ta rufe sannan tahau kan gadonta can kusurwa taje ta zaunah, daga hoton tayi ta kura mishi ido yanda yake murmushi a jikin hoton, yatsanta tasa tana d'an goge gefen fuskarshi wasu sabbin hawaye suka sake fara racing akan fuskarta, saida tayi kukan mai isarta tukunna tayi murmushi tace "I really wished u were alive, I really wished u haven't left me all alone in this world, naso ace kana raye kuma tare muka baiwa 'ya'yanmu tarbiyya, na tabbata da kana raye abubuwan da suke faruwa duk bazasu faru bah, yau gashi ina zubar da hawayena dalilin kuncin da Neenah ta jefani wanda nasan da kana raye u could have taken care of it all, I really missed u hun, I missed u" ta rungume hoton tana cigaba da kukanta saidai wannan karon babu kakkautawa. Turo kofan d'akin Sahr tayi da 'yar sallamarta ta shigo d'akin ta hango Mami can kusurwan gado tana kuka, babu shiri ta haye saman gadon itama da niyyan petting Mami ta karb'e enlargement dake hannunta idanunta ya saukan kan kyakkyawan fuskar mahaifinsu, nan take hawaye ya cika mata ido itama ta rungume hoton tana "I missed u dad" bayan wani d'an lokaci ta ajiye hoton a gefe ta kira sunan Mami a hankali, d'ago kai Mamin tayi da fuskarta daya riga ya kumbura don kuka ta kalli 'yar tata, girgixa mata kai Sahr ta shiga yi tana goge mata fuska da hannayenta tace "Don Allah Mamina ki daina kukan haka nan ya isa, please" Murmushi Mami tayi da dashashshen muryanta tace "kinga halin da 'yar uwarki takeson jefani koh little princess, Neenah nason kasheni" da sauri Sahr ta katseta da cewa "Shhhhhhhh! Karki fad'i haka Mamina, come here" ta bud'e mata hannu bayan Mami ta shiga ta rungumeta.

Posted on Monday Date : 26th march 2018 Time: 06:00pm Written by : Seemby luff😘

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull