Sahr khulaiyd complete - Chapter 14
Sahr khulaiyd complete Chapter 14: Sahr khulaiyd complete Chapter 14. Ga wad'anda suke cewa suna nemana kuma basa samuna, zaku iya dropping messages d'inku…
4,454 words
© *SEEMBY LUFF* 😘 ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff* 😘 Page *61* ⚜
Saida sukayi kukan mai isarsu kafin Sahr ta breaking hug d'in tana goge fuskarta ta sauka daga kan gadon tayi waje, tana komawa d'akinta tayi zaman dirshan bakin gado, gabad'aya bata jin dad'in yanda zaman gidan ya koma kamar gaba akeyi, tadai san cewa abu mai kamar wuya neh ta kyale Khulayd ma Neenah after all what happened, zaiyi matukar wuya ta iya rayuwa babu shi, komawa tayi ta kwanta tana tunane-tunane har bacci ya d'auketa. *Monday, 04:20pm*
Dai-dai karfe 04:20 na yamma jirgin yayi landing cikin airport d'in, Khualyd da kanshi yazo d'aukan papan shi, tsaye yake a arrivals yana ta dube-dube cikin passengers da suke saukowa bayan kamar minti biyar ya hango Mr Abeed yana saukowa daga matakalan jirgin a hankali cikin takunshi na kasaita kanshi a k'asa har saida ya karasa saukowa tukun ya d'ago kanshi, cikin hanzari Khulayd ya d'an d'aga hannu kamar yana waving, Mr Abeed na ganinshi ya saki murmushi yana kallon d'anshi ciki da soyayya, shima Khulayd d'in murmushin yakeyi ya karasa yayi hugging papanshi, rikeshi Mr Abeed yayi yana d'an shafa bayanshi a hankali kusan seconds goma suka d'auka a haka kafin suka sake juna, "Welcome dad" Khulayd ya fad'a lokacinda suke kokarin karasawa inda ake sauke luggage, " Thanks son" kawai Mr Abeed daga nan suka d'auko luggage d'in suka wuce wurin mota, a baya driver ya b'udewa Mr Abeed ya shige Khulayd kuma yana kokarin bud'e gidan gaba ya zauna, "come and sit next to me" Mr Abeed ya fad'a yana nuna mishi gefenshi, ajiyar zuciya Khulayd ya saki sannan ya mayar da kofan front seat d'in ya rufe ya koma baya ya zauna kusa da mahaifinshi.
Shiru neh ya wakana a cikin mota na d'an wani lokaci kafin daga bisani Mr Abeed yace " so, me ake cikine game da maganan abduction din, shin kun zaunah da ita yarinyar ka samo wani information as to who is behind it?", girgiza kai Khulayd yayi alamar a'a yace " na d'an bata tym ta huta neh dad, naga kamar it isn't ryt in fara bincikenta after all what she went through, kaga yanzu ko wanda ya aikata abun zai sakankance coz zaiga kamar we've let go of it sai muzo mishi a bazata... That's wat I thought". "Umm, not a bad idea" cewar Mr Abeed sannan yace " we'll talk about it anjima after isha' prayer" Khulayd yace "hakan ma yayi" haka suka rika hira har suka isa gida. Nailah da sahr tun bayan azahar suke kitchen suna ta faman girke-girke bayan sun gama suka jere komai kan dinning suka koma don kimtsa kitchen din, jin tsayiwar mota yasa sahr ta wullar da mopper dake hannunta ta fice da gudu har ta kusa fad'i ta nufi harabar gidan, isowarta yayi dai-dai da tsayuwar motan a parking lot tayi saurin bud'e b'angaren da uncle d'inta ke ciki ta fad'a motan kawai sai a jikinshi tana "oyoyo sweet uncle", rungumeta yayi yace "oyoyo Mami's little princess, har yanxu kina nan da halin naki koh? Don't u knw you re now a grown up" mak'ale kafad'a tayi tad'an tura bakin tace "I knw manah uncle, amma a wurinku ai am still a baby koh" dariya sosai yayi yad'an ja kumatunta yace "shegen wayon tsiya ne dake 'yar autar Mami... Of course u re my baby, our baby". Nailah dake tsaye a bayanta tace "toh malama ai saiki matsa muma mu samu damar yi masa barka da zuwan koh, ko uncle d'inki ke kad'ai ne aka fad'a miki" ta kare maganar tare da janyota zuwa gefe, da shagwab'a Sahr ta fara bubbuga kafafunta a kasa tana "uncle ka ganta bah", dariya sosai Mr Abeed yayi wannan karon yace "duk kuyi hakuri ai zan fito kuma ba ina nan bah, we'll all spend some quality time together" Sahr bata sake cewa komai bah ta rungume hannayenta a kirji tayi narai-narai da ido kamar zatayi kuka tana kallonsu, fitowa Khulayd yayi ya tsaya a gefenta yace " ni baza'ayi min oyoyon baneh, ko papa kawai kika gani a nan" kin kulashi tayi tayi banza dashi, murmushi yayi yace "ni ne fa jaan d'inki kike banza dani, yanzu idan na rama anjima you'll start crying" nan na batace komai bah, d'auke kai Khulayd yayi zuwa gefe yace "zan rama neh" babu shiri tace "Ya Khulayd fa bada kai nake fushin bah, da uncle da Nailah nakeyi kaga sun kyaleni sunje gefe suna ta firansu" kin kulata yayi shima ya d'auke kai, rike kafad'anshi tayi ta d'an girgizashi tace "Ya Khulayd am sorry", b'ata rai sosai yayi kamar da gaske ya juyo baya ko murmushi yace "and what happened to 'Jaan'?" Sai da ta yi ajiyar zuciya tukun tace "am sorry Jaan" ta rike kunnenta, Khulayd ya sake fuska babu yabo babu fallasa yace "zanyi hakuri amma akwai condition", d'agowa tayi tana kallonshi tace "which is?" Kamar bazaiyi magana bah kafin daga bisani yace " kiyi pecking na" babu shiri Sahr ta zaro ido waje kamar zasu firfito tace "a nan?" Ko a jikinshi yace "a nan manah kuma yanxu" turus ta tsaya kallonshi tama kasa cewa komai kawai kallon mamaki kawai take mishi, daya ga bata da niyyar yin abunda ya bukata yace "don't just stand there staring at me, kiyi kawai ko kuma inyi fushi dake neh yarinya" suna kan haka Mami ta fito harabar gidan itama da murmushi tana kokarin b'oye duk damuwarta kada d'an uwanta ya gani a fuskarta, tun fitowarta ya kafeta da idanu ganin yanda ta rame tayi fayau da ita kamar wacce tayi ciwo har ta karaso bai d'auke idanunshi a kanta bah, tun kafin tace wani abu yace "kinyi jinya neh my dear sister? Naga u look palled kuma kin rame compared to d last time I came, ko akwai wani damuwa neh da kika k'i fad'amun?" Murmushi tayi tace "ai saika bari mu karisa ciki tukun kayi min wad'annan tambayoyin, yanzu dai u re highly welcome, nasan ka gaji don haka mu shiga ciki so you'll freshen up and eat your food okay, den komai sai ya biyo baya" "I asked you something kuma kina maganar cin abinci? Just look at yourself sis, u don't seem alright, ki fad'amun meke damunki?" Mr Abeed ya sake tambaya a karo na biyu, jan numfashi Mami tayi ta fusgar tukun tace "toh Yaya tunda u insist zan fad'a maka, na d'anyi zazzab'i neh na kwana biyu but am feeling much better now coz my son here has taken a very good care of me" ta kare maganar tare da shafar gefen fuskan Khulayd, ajiyan zuciya Mr Abeed yayi yace "are u sure kinji sauki?" Tace "am very sure Yaya" daga haka suka d'unguma zuwa ciki. Koda suka shiga Mr Abeed baiga Neenah bah hakan yasa ya tambaya "where is my favorite girl, I haven't seen her tunda naxo" kusan sau uku ya tambaya amma amsar da ake bashi d'aya neh "bamu san ina ta shiga bah" bai kawo komai a ranshi bah ya wuce masaukinsa kawai don hutawa.
*After Isha' prayer*❤ Kowa ya hallara wurin dinning don cin dinner amma banda Neenah da tun d'azu ta sa kafa ta fice daga gidan kuma har yanzu bata dawo bah, Mr Abeed ya b'ude baki da niyyar sake tambayansu inda taje tun safe saidai baima yi maganar bah yaji muryanta da ihu tana "uncle" tayi saurin karasowa ta rungumeshi ta baya duk da yana zaune, fad'ad'a murmushi yayi ya riketa shima yana "my favorite girl, ina kika shiga neh naketa tambayarki tun d'azu, meyasa kika jira har war haka a waje" kujeran kusa dashi taja ta zauna tare da riko hannunshi tace "uncle office name nd inada ayyuka dayawa akan desk d'ina shiyasa naga yakamata in rage, kasan yanda aikin namu yake balle kuma being a secretary to d CEO is a very difficult task" ta kare maganar tana kallon Khulayd, harara ya wurga mata babu shiri ta d'auke idonta a kanshi, cikin jindad'i Mr Abeed yace "this is why u re my fev, kina bawa aikinki muhimmanci... Keep it up" "awwn thanks uncle" Neenah ta fad'a daga haka Sahr ta mik'e tayi serving abincin kowa ya fara ci, babu wanda ya sake cewa komai.
*After dinner* Duk suka koma parlor bayan sun kammala cin abincin, Khulayd da Papanshi suka zaunah a couch d'aya, Mami da Sahr ma akan d'aya sai Neenah da Nailah kuma kan different couch. Mr Abeed yayi gyaran murya yana kallon Sahr yace "little princess muna sake godewa Allah daya kwaceki a hannun mugayen mutanen da suka saceki and we re happy u came back home safe and sound, mun barki neh iya tsawon wannan lokacin don ki huta kuma ki cire abun a ranki kafin mu fara bincike, toh Alhamdulillah yanxu nasan kin samu isashshen hutu don haka lokaci yayi da zamuji ta bakinki, ko kinsan wanda ya aikata hakan a kanki?" Gyad'a kai Sahr tayi jikinta duk ya fara rawa don bata tab'a tsammanin za ayi mata tambayar nan yanxu bah, ita a zatonta komai ya wuce, a hankali tace "na san wanda ya aikata hakan a gareni Uncle saboda bai tab'a b'oyemin kanshi bah dai-dai da rana d'aya" duk hankalin kowa ya koma kanta barin ma Neenah da tunda Sahr ta fara maganar zuciyanta yake bugawa, "ko kinsan dalilin da yasa basu bukaci kud'i (ransom) bah iya lokacinda suka rikeki?" Cewar Khulayd "Bana tunanin cewa suna bukatar kud'i neh, akwai wani manufa da kudirin da suke dashi a kaina saboda sau da dama yakan zo min da wannan kudirin" cewar Sahr, shiru tad'anyi nad'an wani lokaci kafin taci gaba "I always heard him talking to someone whom I believed to be a lady on d phone, saidai bansan ko wacece bah amma inaji a jikina akwai bakinta a ciki" Mr Abeed have "Masha Allah, ko zaki iya sanar damu wanene? Idan kuma saninshi a fuska kawai za'a iya kiran mai zane idan yaso saiki kwatanta masa ya zana", da sauri Sahr tace "no, we don't need that uncle, nayi mishi kyakkyawan sani don ko a mafarki bazan tab'a manta fuskarshi bah kuma babu wanda yake zaune a parlor'n nan da bai sanshi bah" duk suka fara kallon juna kowa yana wondering waye wannan mutumin, Neenah kam yanxu bugun zuciyarta ya karu fiye da d'azu, kamar zai b'alle k'irjinta ya fito, Mami ce tayi karfin halin tambayan Sahr "wanene haka princess, kince duk nun sanshi... Who could that be?" Kamar bazata ce komai bah, maganar ya zo musu a bazata yayinda tace " *BARRISTER ZAYYAD NEH*"
Posted on Monday Date: 02- April- 2018 Time: 09:00pm Writer: Seemby luff😘
© *SEEMBY LUFF* 😘 ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff* 😘 Page *62*⚜
Mik'ewa both Khulayd da Mr Abeed sukayi cikin tsananin mamakin furucinta, "Barrister Zayyad" Khulayd ya maimaita yanajin zuciyarshi yana tafasa, "Yes, barrister Zayyad, and d reason why he didn't asked for ransom is yanason kwana da ni neh kawai" da fashe da tsananin kuka tace "he tried to rape me sau uku" wannan karon har Mami saida ta mik'e tsaye, da karfi Khulayd yace "What? Rape fah kikace" gyad'a kai kawai Sahr tayi batace komai bah hawaye na cigaba da bin kuncinta, da gudu Khulayd ya haura sama jim kad'an ya dawo rike da car key bai ce dasu komai bah ya nufi hanyar waje, Mr Abeed yace "and where do u think u are going in such a hurry?" Khulayd bai ko kulashi bah ya cigaba da tafiya, a karo na biyu Mr Abeed yace "I asked u something" huci Khulayd yakeyi bayajin zai iya cewa komai, da kyar ya iya tattaro 'yar nutsuwa yace "gidan Zayyad zaani" "kayi masa meye" cewar papanshi "bazaka d'auki law a hannunka bah coz if u do kaima zaka zama mai laifi, ka bar masu aiki suyi aikinsu". "But dad how dare he, how dare he to even think of coming close to my woman, she's mine dad, she's mine baxan tab'a kyaleshi ba wallahi, idan na had'u dashi I'll kill him wit my hands aswear" kusa dashi Mami ta matso tare da dafa kafad'anshi tace "calm down son, nasan yadda kakeji amma kamata yayi mubi komai cikin hankali, kana fa jinta tace there is a woman involved, idan ka kashe shi how re we supposed to find out whom she is... Come and sit" Mami ta jawo hannunshi ta dawo dashi cikin parlor'n sannan ta zaunar dashi, wurin fridge ta nufa ta bud'e ta ciro chilled water na faro ta tsiyayo mishi a cup ta kawo, mik'a mishi tayi tana kallonshi batace komai bah yasa hannu ya karba, saida yasha kusan half d cup sannan ta koma ta zaunah duk kowa yayi shiru a cikin parlor'n. Tunda Mami ta zaunar dashi Sahr ta kafeshi da idanu, bata tab'a jin sonshi irin yanda takeji yau bah, gaba d'aya komai ya koma mata kamar sabo, jikinshi neh ya bashi ana kallonshi ya d'ago kai a hankali da jajayen idanunshi ya zuba cikin nata, batayi kokarin sauke kanta bah wannan karon itama tana kallonshi a cikin ido, sun d'auki lokaci a haka kuma tun d'azun basuyi noticing Mami na kallonsu bah, its like sun ma manta akwai Mami da Mr Abeed a parlor'n, Nailah ma kallonsu take tana murmushi kafin daga bisani ta mike taje gaban Sahr tace "kid sis xo muje muyi wata 'yar magana" bata tsaya jin me xatace ba ta ja hannunta suka wuce. Sai a sannan Khulayd ya dawo hankalinshi yana d'ago ido sai a cikin na Mami, gabad'aya kunya ya rufeshi don yasan tabbas ta gansu, mik'ewa yayi shima yana 'yar mik'a da hamma yace "Aunt, papa ni zanje in kwanta, am feeling sleepy sosai" "kodai kana korar kunya da hauka bah" cewar Mami, nunawa yayi kamar baisan inda zancenta ya dosa bah yace "korar kunya da hauka kuma aunt, me nayi neh?" Saida Mami tad'an murmusa tukunna tace "now u re pretending kamar bakasan me nake cewa bah, I saw u two ai" sosa keyanshi yayi da key dake hannunshi yama rasa me xai fad'a, Mr Abeed dake zaune tun d'azu yana kallonsu cike da farin cikin zamantakewarsu yace "I can see my son is so much in love, nayi maka alkawarin muna gama magance wannan matsalar xamu fara shirin aurenku tunda ma abun yaxo da sauki, na gidah neh" Khulayd baisan lokacinda ya karaso gaban Papanshi ya rungumeshi bah, harda pecking d'inshi a kumatu yace "thanks dad, u re d best" itama Mamin zuwa wurinta yayi pecking forehead d'inta yace "nyt aunt" daga haka ya haura sama cike da farin cikin furucin mahaifinsa. A fusace Neenah tabar parlor'n har tana jan tsoki, sam maganar da akayi bai mata bah, bama wannan bah, babban tashin hankalinta shine tasan cewa idan akayi nasaran cafke Barr Zayyad tofah itama asirinta zai tonu, tafiya kawai takeyi tana tunanin mafita. Kasa bacci tayi a daren sai juyi takeyi a saman gado tana sakawa da kuncewa daga karshe ta yanke wani shawarar da tabarwa zuciyanta ita kad'ai har bacci ya d'auketa. Nailah da Sahr suna isa d'aki suka zube nan kan two seated sofa dake gefe, kallonta kawai Nailah keyi batace komai ba bayan ita tace xasuyi wata magana, kallon neh ya ishi Sahr tace "Addah Nailah me nayi kike kallona haka bakya ko kyaftawa, I tot u said zamuyi magana neh, y ain't u talking" Nailah tace "dole in janyeki daga parlor'n mana kid sis, mamaki fah kika bani" cikin rashin fahimta Sahr tace "mamaki kuma Adda Nailah, toh menayi na mamaki kuma" har fuskanta ya fara komawa na tausayi, babu alamar wasa a fuskan Nailah sam tace "wai ma yaushe kika koma marar kunya neh kam, gaba d'aya kin biyewa Ya Khulayd ya cire miki wannan kunyar da kike dashi, I had to take u away saboda irin kallon juna da kukeyi kamar zaku cinye kanku kun ma manta Mami da Uncle suna parlor'n, shin kuwa ko kinsan Mami na kallonku. Wai ma tsaya, yaushe kika koyi kallon cikin idon mutum har na tsawon lokaci haka neh" Nailah ta tambaya tana wondering, "soyayya ce (littafin Maryam Abdulrahman, u guys should try reading it saboda its interesting and educative) ta koyamin Adda Nailah" tana gama fad'in haka ta b'oye fuskarta a cikin hannunta cike da kunya don bata ma san sanda ta fad'i haka bah, "iyye, lallai yarinyar nan kinfa girma, a'a u ain't d kid sister I used to knw wannan kam babba ceh, karki damu burinki yana gab da cika, everything will soon b over Insha Allah" cewar Nailah, daga nan suka d'anyi sisterly hiransu, da hamma Nailah ta mik'e tace "ba naje na kwanta kid sis, Allah bacci nakeji" Sahr tace "aikam kinajin bacci don gashi har idanunki sun k'ankance, tnks 4 ur tym" sunkuyowa Nailah tayi ta sumbaci Sahr a goshi sannan tace "nyt kid sis" tana magana tana tafiya, cikin muryan bacci itama Sahr ta amsa mata da "nyt", bayan fitan Nailah Sahr ta sauya outfit d'inta zuwa nighty ta haye saman gado, addu'ar kwanciya tayi daga bisani ta kashe wutan d'akin ta kwanta.
Khulayd na komawa d'aki baiyi tunanin kwanciya bah, bathroom ya nufa ya d'auro alwala ya dawo cikin d'akin, darduma ya shimfid'a yayi nafila raka'a biyu sannan bayan ya idar yayi addu'o'inshi yana mai godiya ga ni'imomin ubangiji, ya dad's zaune kan darduman har saida ya fara jin nauyayyen bacci tukun ya mik'e ya koma kan gado ya kwanta, tunane-tunane yayi tayi kan irin abubuwan da suke faruwa, a take ya zama moody daya tuna maganar precious d'inshi cewa Barr Zayyad yaso ya mata fyad'e, kamar an mintsileshi ya mirgina zuwa d'ayan side na gadon inda landline ke ajiye, d'agowa yayi ya jingina da jikin gadon sannan ya d'auko landline d'in ya ajiye saman cinyarshi ya fara dialing digits din d'akinta. Baccinta har ya fara nisa taji ringing, mirginawa itama tayi zuwa other end na gadon idanunta a rufe ta mika hannu ta d'auko, karawa a kunnenta tayi da wahalalliyar murya tace "Hello" Gabad'aya sai yaji veins d'inshi sunyi weak, nan take muryanta ya saukar mishi kasala da kyar ya iya cewa "precious" a lokacinda muryanshi ya doki kunnenta sai ta nemi baccinta ta rasa, gyara kwanciyanta tayi sosai sannan tace "Jaaaan, bakayi bacci bah" "Precious ya za'ayi in iya bacci when I can't get u off my thoughts"
"Nima da tunaninka na kwanta Yayana" ta fad'a a takaice, saida ya d'anyi shiru kafin yace "about dazu, kince Zayyad tried to rape u, did he in anyway....." Bata bari ya karisa fad'in abunda zai ce bah tace "Shhhhh Jaan! Babu abunda ya fara coz nayita addu'an Allah ya kareni idan har ina ajiye kaina wa mijina kuma don shi nakeyi and he did, he protected me from his evil plans, Ya Khulayd ni takace kai kad'ai, I promise". Wani nauyayyen ajiyan zuciya Khulayd ya saki baima san me zaice mata be coz he's overwhelmed, "thank u precious, thank h so much" kawai ya iya fad'a, a hankali tace "now u can sleep don na tabbata abunda ya hanaka bacci kenan" 'yar murmushi yayi yace "not until kin fad'amin abu mai dad'i", rufe idanunta tayi don muryanshi yasa taji wani electrification daga kai zuwa tafin kafa, cikin wani romantic voice tace "I love u Jaan, so much" ta d'anyi shiru, can tace "Muahh, a kumatu fah amma" yadda tayi maganan serious ta bashi dariya sosai, da kyar ya iya controlling dariyan yace "um um, nidai a lips nakeso ayi min, in kuma baza'ayi ba shikenan ko wannan ma bazan karb'a bah" da sauri tace "no way, nyt" tayi hanging up tana dariya, shima dariyan yakeyi a chan, that night dai sun kwanta full of each other's thoughts.
Posted on Thursday Date: 05-04-2018 Time: 01:02am Written by: Seemby luff😘
© *SEEMBY LUFF* 😘
⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜ Written by *Seemby luff* 😘 Page *63* ⚜
Washegari da safe bayan sun kammala breakfast misalin k'arfe tara da rabi, suna zaune a parlor Neenah ta fito da trolley cike makil da kaya, saida ta karaso cikin parlor'n tace "Mom, Uncle ni na wuce kaduna coz inada assignment a chan" A wulakance Mami ta kalleta daga sama zuwa k'asa tukun tace "and u couldn't even inform me tun jiya, sai da kika kammala shirinki kin ja akwati tukun zaki ce min kin tafi? Zaman kanki kikeyi ne kam" sai da Neenah ta d'an yarfe hannunta a iska tace "Ban sanar dake ba saboda nima I was informed late kuma dole in isa Kaduna a yau d'innan" kallonta kawai Khulayd ke yi da mamaki saboda ya san babu wani assignment a office da zai kai ta Kaduna, sai dai idan wani abunta take son zuwa yi". Mr Abeed ya yi gyaran murya "Uhum uhum" ya ce " Neenah ko da a ce aikin office neh ya kamata ki sanar da mahaifiyarki tun jiya, u just don't do things d way u like, ai baki da wani sama da ita, kada ki sake yin haka" Mami bata ce komai bah haka ma Neenah ta ja trolley d'inta ta fita tana taunar chewing gum.
K'arfe goma dai-dai Mr Abeed da Khulayd suka fice zuwa investigation bureau, bayan sun samu zama da in-charge d'in wurin gabad'aya mai suna Ahmad Jalaal, Mr Abeed yayi mishi bayani dalla-dalla sannan bayan ya gama aka bukaci Khulayd ya yi k'arin bayani tunda he's present tun da abun yake faruwa, bayan an kammala d'aukan statements Ahmad Jalaaluddeen ya ce " Toh Mr Abeed na saurari bayananku duk da cewa yanzu mun san suspect d'in but still sai mun yi involving police a ciki, our job is only to investigate then, sai mu bar police su tsare suspect kafin court tayi passing judgement, I believe ka san haka" gyad'a kai Mr Abeed ya yi yace " Sosai ma kuwa, dats y nake son bin abun yadda ya kamata" Ahmad Jalaaluddeen ya ce "Very well den, yanzu zan tura ku da yarana guda biyu zuwa station daga can sai ayi abunda ya kamata" bayan ya kammala yi musu bayani ya tura su tare da wasu agents zuwa station. A can station d'in ma kusan abunda suka yi a investigation bureau haka suka yi, after following due processes aka had'a su da officers biyu suka wuce gidan Barr Zayyad. On reaching there, Khulayd da Papanshi kad'ai suka shiga cikin harabar gidan suka bar sauran a waje, Barr Zayyad na zauneh a kan d'aya daga cikin couches na parlor'n ya yi receiving wani k'ira da aka sanar da shi ana neman shi urgently a court, suit kawai ya cire a wardrobe bayan ya shiga bedroom d'insa sannan ya d'auki car key d'inshi da ke ajiye gaban mirror ya fito, hankalin shi kwance ya ke locking kofar gidan yana yin 'yar wak'a, cikin zafin nama Khulayd ya karasa wurin da Zayyad ke tsaye kawai sai ji yayi an daafa kafad'arshi, juyawar da zai yi ya ji sauk'ar punch a fuskarshi da karfin gaske har sai da hakorinshi d'aya ya fad'i kasa, nan take bakinshi ya fara zubar da jini. A razane Barr Zayyad ya dafe bakinshi sannan ya d'ago kai yana kallon Khulayd, dak'ewa yayi ya tufar da jinin da ke bakinshi yace " Arrrgghh, that was hard man, meye ...." Bai gama karisa maganar ba Khulayd ya sake punching nashi a karo na biyu, yace " This is for trying to touch my woman" sosai Zayyad ya ji zafin bugun, da k'yar ya iya bud'e bakinshi yace " Am not surprised at all, na dad'e ina sauraren zuwan wannan ranar don na san cewa ba zaku barni bah" suna kan maganar Mr Abeed ya k'araso wurin su without uttering a word shi ma ya wanke fuskar Zayyad da tagwayen mari wanda suka gigitashi, " And this is for breaking my trust" daga haka Khulayd ya k'ira officers d'in suka yi arresting nashi, tasa keyarshi suka yi zuwa mota, daga nan suka wuce da shi.
*Investigation Bureau* Investigation room aka wuce da Barr Zayyad, bayan mintuna kad'an Ahmad Jalaaludden ya shigo tare da wasu agents da suka rufa mar baya, zama Ahmad Jalaaluddeen ya yi kan d'ayan kujeran da ke fuskantar na Barr Zayyad, shiru ne ya wakana a d'akin na d'an wani lokaci kafin Ahmad ya ce "Barrister Zayyad koh?" Ya tambaya ne yana kallon cikin idon Barr zayyad d'in, k'in kulashi Zayyad ya yi, D. Ahmad ya yi wata karamar murmushi ya ce " As a barrister, kasan implication na abunda ka aikata?" Wannan karon ma banza da shi Zayyad yayi hakan kuma ya sanya D. Ahmad k'ulewa, da karfi ya buga table d'in da ke tsakiyar su da karfi har sai da Zayyad d'in ya tsorata, " ka amsa min tambayata damn it, kar ka maida ni maras hankali mana ina tambayarka ka wani yi banza da ni" cewar D. Ahmad, " Na sani" Barr Zayyad ya bashi amsa a takaice, "Very good, kai barrister neh mai zaman kansa and yet kai ne ka ke karya doka, why is that" girgiza kai barrister Zayyad ya shiga yi full of regrets, sai da ya sauke wahalallen ajiyan zuciya tun ya ce " instigating d'ina aka yi kuma dama ina da sha'awar yarinyar sai aka kwad'aitar min da ita" mik'ewa D. Ahmad ya yi daga kujerarsa ya dawo ya zauna kan table d'in a gaban Barr Zayyad yana nazarinshi, jim kad'an yace " Instigation, oh I see. Toh waye wannan daya tunzuraka ka aikata hakan? Atunanina tunda kayi karatun da ya kai ka ga zama barrister, babu wani d'an adam da zai rinjayeka har ya kai ka ga aikata irin wannan mummunan abu" " Huh" barrister Zayyad ya ce, sannan ya d'aura " She's a lady" "wow, interesting" cewar D. Ahmad " Abun na yi ne ashe, may I know waye wannan macen?" " Miss Neenah Mukhtar" barrister Zayyad ya bashi amsa, " Umm, Neenah Mukhtar... Toh meye alakar ta da kai da kuma yarinyar da kayi abducting?" D. Ahmad ya tambaya, barrister Zayyad ya fara bayani " Toh ni dai bani da alaka da ita, illa iyaka ni ne lauyan kamfanin kawunta Mr Abeed Omair, and she happens to be the secretary to d CEO. Ita kuma yarinyar da nayi abducting k'anwarta ceh ta jini, I mean mahaifi da mahaifiyarsu d'aya" " Inna lillahi wa inna ilaihi raji'uun" D. Ahmad ya fad'a tare da dafe kanshi, mik'ewa yayi ya koma kan kujerarshi full of wonders ya ce " blood sister, but why? Me yasa zata so a sace 'yar uwarta ta jini,Ya salam" murmushi barrister Zayyad ya yi kafin ya ce " Soyayya".
Chapter notes and social links
Ga wad'anda suke cewa suna nemana kuma basa samuna, zaku iya dropping messages d'inku a whatsapp inbox d'ina ta wannan number'n *08060522342*, tnk you all for d supports, ina sonku dukka irin sosai d'innan❤❤❤ #ONELOVE #TEAMSAHRKHULAYD