Kenza eBookz

Sahr khulaiyd complete - Chapter 15

Sahr khulaiyd complete - Chapter 15

Sahr khulaiyd complete Chapter 15: Sahr khulaiyd complete Chapter 15. 'Dagowa D. Ahmad ya yi ya kalli Barr Zayyad yana neman k'arin bayani, da ya fahimci…

4,366 words

'Dagowa D. Ahmad ya yi ya kalli Barr Zayyad yana neman k'arin bayani, da ya fahimci haka ya ce " Neenah na son wanda kanwarta ke so kuma shi wannan mutumin zuciyarshi tafi k'arkata ga karamar, so she wanted her out of the way", da mamaki D. Ahmad ya ce " She could have killed her tunda tana son ta bar hanyarta, tunda ita ta tsaya tsakanin su, me ya sa ta zab'i ta sace ta?" " Saboda na nuna ina sha'awar kanwar" cewar Zayyad, rungume hannu a k'irji D. Ahmad ya yi ya ce " Toh ni abunda ya d'aure min kai shine, meye zaku yi benefiting a ciki, both of u, what's d plan?" "Fyade" kawai Zayyad ya fad'a, wannan karon shima yana kallon cikin idon D. Ahmad, " Fyad'e kuma?, but me yasa" D. Ahmad ya tambaya a takaice, Barr Zayyad ya ce " The plan was, idan nayi mata fyad'e sai in nuna ina neman aurenta, kaga tunda abu ya shiga tsakanin mu ba za'a hana auren mu bah duk da cewa zan fuskanci hukunci then, sai a had'a aurenta da shi fiancée'n kanwar", "wai ni tukunna ma, waye shi guy d'in neh?" " Mr Khulayd Abeed Omair" cewar Barr Zayyad, " turkashi, ashe duk a cikin gida d'aya neh matsalan" cewar D. Ahmad, daga haka bai kuma cewa komai ba, ya fice zuwa inda su Khulayd ke tsaye bayan ya tabbata yayi gathering enough evidence, tun d'azu kallonsu sukeyi ta glass dake a jikin d'akin, sai dai ba sa iya jin maganarsu, bayan ya isa wurinsu bai ma yi magana bah Khulayd ya ce, " Detective koh ka iya ka samu information kan wacce suke aiki tare? Am eager to knw wace irin mace ce mara imani haka, sannan kuma me ya sa za ta aikata haka, do I even know her?" Khulayd ya k'are maganarshi da tambaya, shiru D. Ahmad yayi na d'an wani lokaci kafin ya ce " I dunno if I should tell u this, amma in dai sanin ta ne, u knw her very well" eagerly Mr Abeed ya ce " Detective ka fad'a manah kawai we can handle it, besides bai kamata ka b'oye mana komai bah" " Huh, d lady behind this is, MISS NEENAH MUKHTAR, your niece"

Munzo gangara fah fans, a gurguje tunda kunce inyi in karisa.

Posted on : Saturday Date : 7th April, 2018 Time: 03:15 pm Written by : Seemby luff😘

© *SEEMBY LUFF* 😘 ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff*😘 Page *64*⚜

Juyowa both Khulayd da Papanshi suka yi suna kallon juna disbelievingly, tsawon mintuna biyar suka d'auka babu wanda ya iya cewa komai, da kyar Khulayd ya ce " Neenah? I could have known this long ago" ya sake kallon Papanshi ya ce " Papa, dama Neenah zata iya zama mara imani haka? Har zata iya sakawa a yi kidnapping k'anwarta sannan a yi mata fyade? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'uun, wace irin duniya ce wannan?" Mr Abeed bai iya cewa komai bah saboda he's in a very deep shock, Neenah da yafi kowa sonta a cikin 'ya'yan k'anwarshi, ita da yake gani ta fi kowa hankali a cikin su ita ce tayi haka, duk tambayoyin nan a cikin zuciyarshi yake yin su.

A zuciye Khulayd ya bar wurin ya nufi mota, Mr Abeed ganin yadda Khulayd ya wuce ya sa yayi sallama a gurguje da Detective Ahmad Jalaaluddeen, ya ce " Detective zamu yi magana idan na isa gida, I have to follow this boy don na san zai je ya aikata wani abun da ba shi baneh" yana gama fad'in haka shima ya wuce, da sauri-sauri ya karasa wurin motan ya tarar har driver ya yi starting motan, babu shiri shima ya fad'a ciki suka nufi gidah. A motan huci kawai Khulayd ke yi yana ta cizar lips d'inshi, gani yakeyi driver'n baya sauri don he's eager ya ga kanshi a gida, buga bayan seat d'in driver'n yayi yace "ka k'ara speed u fool, in kuma ba zaka yi tuk'in ba ka fitar min a mota mts!" Papanshi ya juyo yana kallonshi yace " ka kwantar da hankalinka mana son, komai zai zama tarihi watarana, just thank Allah that basu ci galaba a kanta bah, shine kawai abun yi".

" In k'wantar da hankalina fa ka ce Papa? Ai babu k'wanciyar hankali a wurina sai na ga an yanke musu hukunci dai-dai da abun da suka aikata, I don't care da cewa Neenah 'yar uwata ce tun da she have the mind to think of such evil, she deserves no mercy" Mr Abeed bai sake cewa komai ba suka cigaba da tafiya.

*NEENAH* Shiru tayi a bayan motan, idanunta a lumshe kamar wacce take bacci amma ba baccin take yi bah, sake-sake kawai take yi a cikin zuciyarta na yanda zata kauce wa wannan abun da ta aikata, ta san cewa zuwa yanzu Mr Abeed da Khulayd sun gano cewa ita ce musabbabin faruwan duk abubuwan da suka samu Sahr, sai da suka fara biyawa ta gidan wata k'awarta tukun suka kama hanyar zuwa Kaduna. Da speed sosai driver'n yake tafiya don ta ce tanaso su isa Kaduna da wuri duk da cewa sun bar gida a makare, 'Kiiiit' driver's yayi k'okarin jan brake saboda ganin wani mota ya tunkarosu kuma daga gani ya k'asa controlling motar ne, k'okari kawai yake yi ya kauce amma kafin yayi hakan abunda yake tsoro ya auku, abun mamaki driver'n yana nan a cikin motan amma Neenah dake zaune a baya kuma a honest corner ta fita tun daga bayan through glass na gaban motan ta fad'o waje, nan take d'ayan motan ya wuce kan kafafunta.

Da kyar driver'n d'ayan motan yayi iya k'okarinshi ya tsayar da motan a gefen hanya suka firfito tare da passengers d'inshi, motansu Neenah kuwa tuni ya shiga cikin jeji sannan da taimakon wani gungumen itace motan ya samu ya tsaya. Kwance take tsakiyar titin cikin jini, babu alamar numfashi a tare da ita, kanta suka yo dukkansu har da nata driver'n saboda kwata-kwata bai ji ciwo bah, wad'ansu na d'aura hannu a kai, wad'ansu kuma suna ta fad'in " Inna lillahi wa inna ilaihi raji'uun" k'okari driver'n d'ayan motan yake yi ya k'ira ambulance yayin da driver'n Neenah ke k'okarin neman Mami a waya.

Kusan sau uku yake k'ira bai samu lambar Asibitin bah sai a na ukun, suna d'auka ya fad'a musu cewa akwai accident daya faru babu nisa da garin, sannan ya fad'a musu ana neman taimakon gaggawa, daga nan ya k'ira police station saboda gudun kada a k'i karb'an Neenah a asibitin ba tare da police report bah.

Mami na zauneh a parlor tana jiran Nailah ta kawo mata abunda ta aiketa d'aukowa a d'akinta, tun da Khulayd da Papanshi suka fita daga gidan hankalinta yak'i kwanciya, burinta kawai su dawo ta ji daga bakinsu abunda ke tafiya, wayarta dake ajiye gefenta ne ya fara k'ara, dubawa tayi ta ga new number yasa tayi ignoring bata d'aga bah, Neenah dake saukowa daga stairs har ta ji k'aran wayan Mami, da sauri-sauri ta k'arasa saukowa tana

" Mami baki jin wayarki na ringing ne, ko bacci kike yi a zaune neh?" Ta tambaya demanding an answer, 'yar tsaki Mami ta yi "mts" sai dai kafin ta sake cewa komai wayanta ya sake fara ringing, har ya kusa tsinkewa tukun ta d'aga bayan Nailah tayi insisting kan cewa ta d'aga d'in, "Assalamou Alaikoum wa rahmatullah" ta fad'a tana sauraren ta ji abunda maishi zai fad'a, daga d'ayan b'angaren aka amsa sallamar, sannan mai maganan ya ce " Hajiya, Bala direba ke magana" Mami ta d'an sauke ajiyar zuciya tace " Toh Malam Bala ina jinka, har kun isa Kadunan neh? don na sanka da gudun tsiya, kuma ga Hajiyar taka itama mai son gudu ce".

Daga d'ayan b'angaren driver'n ya fashe da kuka " Ina fa muka isa Kaduna Hajiya, an samu matsala neh don ko gari ma bamu bari bah" yadda yake maganar yasa hankalin Mami ya d'an tashi, gashi ta ji kamar kuka yake yi, "Malam Bala lafiya kuwa nake jin muryanka kamar mai kuka? Wace irin matsala kuka samu haka? Idan na mota ne ai sai ku dawo kawai babu d'aga hankali" cewar Mami, dagewa Malam Bala yayi ya ce " Hajiya wallahi hatsari munkayi, sai dai ni ban ji ciwo bah amma Hajiya Neenah ta ji rauni sosai, ina gani ma kamar ta rasa kafafunta duk guda biyun".

Mik'ewa Mami tayi daga zaunen da take yi tace "What?" Daga haka wayan ya sulale k'asa, sauri Nailah tayi itama ta mik'e daga nata kujeran zuwa wurin Mami tana tambayarta meke faruwa, k'asa cewa komai Mami tayi sai " Inna lillahi" da take fad'a, tsugunnawa Nailah tayi ta d'auko wayan Mami dake kasa tayi unlocking sannan ta shiga call log d'inta, number'n data gani a sama tayi dialling, ringing biyu aka d'aga daga nan ta fara tambayan meke faruwa, zaman dirshan tayi lokacin da ya sanar da ita abunda ke faruwa.

Da k'yar ta iya tambayan a wani asibiti aka tafi da Neenah, bayan ya sanar da ita ta mik'e ta haura sama da gudu, jim kad'an ta dawo rik'e da abayanta da kuma hijabin Mami sannan da makullin mota, mik'awa Mami hijabinta tayi amma bata ko kulata ba, jikinta ya gama mutuwa bazata iya yin komai bah, Nailah da kanta ta saka mata hijabin sannan ta ja hannunta suka fita zuwa Asibitin.

Horn driver'n Mr Abeed yake yi a bakin gate, da gudu mai gadi ya taso daga kan bencin da yake zaune ya wangale gate d'in yana washe baki, suna shigowa driver'n bai ma gama tsayuwa ba Khulayd ya bud'e motan ya fita zuwa ciki, kusan minti hud'u ya d'auka a ciki sannan ya fito yana tambayan mai gadi ina mutanen gidan

" Eh to, naga sun fita kuma ga dukkan alamu babu lafiya" cewar mai gadin, ciro waya Mr Abeed yayi ya dialing number'n Mami sau uku amma bata d'aga bah, Nailah ya shiga k'ira ringing uku ta d'aga, before he could say anything Nailah ta ce " Uncle, Neenah just had an accident, yanzu haka muna hanyar zuwa Asibitin" daga nan ta fad'a masa sunan Asibitin ta kashe wayarta.

Hula Mr Abeed ya cira yana firfita da, ganin haka Khulayd ya tambaya " What is it Papa?" Sai da yaja dogon numfashi kafin yace " Your sister had an accident" a razane Khulayd ya ce " Wacce daga ciki?" A hankali Mr Abeed yace " *NEENAH*"

posted on: Tuesday Date. : 09th April, 2018 Time. : 10:00pm Written by : Seemby luff😘

© *SEEMBY LUFF* 😘

⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff* 😘 Page *65*

Khulayd ko a jikinshi jin abunda Papanshi ya fad'a, sai ma harzuk'owa daya sake yi yana ta huci kamar zaki, jinginuwa yayi da karfen jikin parking lot d'in, idanunshi sun kad'a sunyi jajur.

Mayar da hulanshi Mr Abeed yayi, ya bud'e motar ya shiga sannan ya umarci direban da ya koma cikin motan su wuce Asibiti. Yadda ya fad'a haka direban yayi, bayan ya shiga har yayi starting motan yana reverse, Mr Abeed yaga cewa Khulayd bai da niyyan shiga motan, sauk'e gilashin motan yayi yana kallon Khulayd d'in na 'yan wasu seconds kafin daga bisani yace

" Wai me kake yi ne a tsaye? Ba zaka je Asibitin bane? Ko baka ji nace 'yar uwarka tayi hatsari bah?" Yana gama fad'in haka ya d'aga gilashin.

Bai ko motsa a wurin ba, shiru yayi yana jin wani zafi a k'asan zuciyanshi, wai shin me ma zai kaishi ganinta ne? Gaskiya in ba don Papanshi ba, ba zai je ba. Kamar baya son tafiya haka ya zagaya, ya b'ude motan a hankali ya shiga.

*A Asibiti, Sashen taimakon gaggawa (Emergency)*

Ana kai Neenah asibiti, a sashen taimakon gaggawa aka kaita sai zubar da jini take yi, duk jinin ya b'ata cikin asibitin, kai tsaye d'akin tiyataa aka wuce da ita ana k'ok'arin ceto rayuwarta, numfashi (oxygen) aka fara saka mata sanadiyyan rashin numfashin da take yi.

Sai da likitan ya tabbatar numfashinta ya zama dai-dai tukunna ya fito wajen ward d'in don duba ko akwai danginta da suka zo, fitowarshi yayi dai-dai da shigowan su Mami cikin ward d'in, tana ganinshi tayi saurin isowa wurinshi tana

" Likita yaya 'yata take? Ina fatan babu abunda ya samar min ita?" Tana maganan ne tana hawaye

K'ok'arin k'wantar mata da hankali likitan ya fara yi ganin yadda duk ta bi ta d'aga hankalinta, sai da ya sauk'e gwauron numfashi tukun yace " Ki kwantar da hankalinki Hajiya, babu komai Insha Allah, ki biyoni ofishi na muyi magana don ba'a son hayaniya a nan"

Yana gama fad'in haka ya wuce, itama Mami tana share hawaye da k'asan hijabinta ta bishi a baya, ta bar su Nailah a tsaye a wurin saboda an hana kowa shiga.

Suna isa ofishin, likitan ya cire farin riganshi na sama ya rataye akan hanger, komawa yayi ya zauna kan kujerarshi tukun ya nunawa Mami kujera, yace " Bismillah Hajiya, zauna" zama Mami tayi kamar yadda ya buk'ata kan kujeran dake fuskantar nashi, yace

" Toh a gaskiya Hajiya, yanayin 'yarki babu sauk'i saboda ta zubar da jini sosai, as we speak yanzu haka ana buk'atan jini leda biyu a d'aura mata kafin ayi tiyata".

Da sauri Mami ta d'ago kanta tana kallonshi da idanunta da suka rine don kuka, tace " Likita wani tiyata kuma za'a yi mata?" Sai da Likitan ya d'an girgiza kanshi tukun yace

" Gaskiya Hajiya ba zan b'oye miki bah, kafafunta duk guda biyun sun samu rauni sosai wadda da k'yar idan zata sake iya tafiya, tiyatan da za'a yi saboda a yanke kafafun ne, gudun kar ciwon ya zo ya zama illa ga sauran b'angarorin jikinta".

" Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai Mami take nanatawa yayin da ta fashe da matsanancin kuka, Likitan bai so dakatar da ita ba don shima da yaga Neenah sai da yayi 'yar hawaye. Sai da Mami tayi kukan mai isanta tukun ta shiga share fuskarta, a hankali likitan yace

"Hajiya, yanzu fa ba lokacin kuka bane, abunda ya kamata kiyi yanzu shine ki nemo wanda zai yi donating jinin, dats in akwai mai irin jininta a gida, idan kuma babu sai a siya a nan ma'adanar jininmu, sabida fa idan babu jinin am afraid, tiyatan ba zai yiwu ba".

Mik'ewa Mami tayi jiki babu k'wari, bata ce da likitan komai ba ta fita ta bar ofishin, a hankali take tafiya kamar bata son yi, ji take yi kafafunta duk sun yi mata nauyi, isowarta yayi dai-dai da isowarsu Khulayd wurin, da 'yar gudu suka k'arasa wurinta ganin yanayinta, suka fara tambayarta abun da likita ya fad'a.

Zubewa kasa tayi, tayi zaman dirshan a wurin ta k'asa cewa komai, binsu kawai take yi da idanu hawaye na cigaba da bin gefen fuskarta, Mr Abeed ne ya sunkuya yana kallon kanwarshi da tausayinta fal zuciyarshi, a hankali ya shiga share mata hawayenta amma sun k'i tsayawa, ganin haka yasa ya dafa kafad'arta ya fara magana cikin nutsuwa

"Sister I know u are feeling very bad da jin abunda likita ya fad'a miki, sai dai bana tunanin zai miki k'arya saboda aikinshi ne, wat I want u to remember is, komai da kika gani ya faru ko yana faruwa, k'addara ne daga Allah, mai yuwa akwai musabbabin faruwanshi, a ko da yaushe mutum ya samu kansa cikin mummunan yanayi, yayi k'ok'arin mik'awa Allah lamarinsa and he'll surely make everything okay".

Numfashi sosai ta sauk'e tukun tace " Likitan ya ce ana buk'atan jini leda biyu kafin ayi tiyatan" da sauri Nailah ta sunkuyo tace " Mami wani tiyata kuma?"

Fashewa da kuka ta sake yi tace " Ya ce sai dai a yanke kafafunta duk guda biyun saboda ko an bari, sai dai su zama illa ga sauran gab'ob'in jikinta" sunkuyowa Sahr tayi itama, ta rik'e Nailah da Mami suka cigaba da kuka.

Mr Abeed duk hankalinshi ya tashi, duk da abunda Neenah tayi bai ji sonta ya ragu a zuciyarshi bah, kukan da suke yi har haushi yake bashi, " Duk kuyi shiru mu yi tunanin wa zai bayar da jinin nan" cewar Mr Abeed a fusace

Kamar an ce su kalleshi, gabad'aya suka juyo suna kallon Khulayd, har Mamin dake kuka kamar ranta zai fita. Ganin ido ya mishi yawa yasa yace

"Wai meye haka duk kuna kallona, ba dai cewa zaku yi ni zan bayar da jinin ba ko?"

Mik'ewa Sahr tayi cikin hanzari kamar an mintsileta ta k'araso gabanshi, kamo hannunshi dukka biyu tayi sannan ta d'ago kai tana kallonshi, a nutse tace

" Jaan ka manta cewa blood group d'in mu d'aya dukkanmu?" Gyad'a mata kai yayi, bai ce komai bah, hakan ya bata daman cigaba da maganarta " Jaan please, ka yarda a d'ebi jininka a saka mata, ka ga you'll save her life, nasan cewa kana fushi da ita due to some reasons, amma ita kanwarka ce, ba zaka tab'a iya goge hakan ba, kayi saboda Allah, kaji Jaan?."

Marairaicewa tayi, wasu hawayen na cigaba da bin kuncinta, " A ina za'a d'ebi jinin?" Kawai ya fad'a, daga nan aka k'ira nurse tayi directing d'inshi zuwa laboratory, bayan an gama d'iban jinin aka nuna mishi gado a nan cikin lab d'in ya kwanta don gudun kada jiri ya d'ebeshi.

Lumshe idonshi yayi kamar mai bacci, dukkansu suka dawo jinyarshi kamar shine mara lafiyan, sai sannu Sahr take yi mishi.

Tafiya da jinin akayi zuwa d'akin da Neenah take, bayan anyi gwaje-gwaje an tabbatar cewa baya d'auke da wani cuta, da kanshi likitan ya d'aura mata jinin, wani ikon Allah, d'igon jinin Khulayd na shiga jikin Neenah ta bud'e idanunta.

Posted on Friday Date. : 13th April, 2018 Time. : 02: 40pm Written by : Seemby Luff😘

© *SEEMBY LUFF*😘

⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby Luff*😘 Page *66*⚜

Tashi tayi daga kwancen da take yi ta zaunah dab'as akan gadon, zaro idanunta tayi tana dube-dube a cikin d'akin. A tsorace likitan ya matsa baya yana kallonta cikin tsananin mamaki, tunda ya zama cik'ak'k'en likita har zuwa yanzu, bai tab'a had'uwa da irin haka bah, ba wai saboda jinin wanda aka d'aura mata yana da karfi bane, sai dai yana gani kamar akwai wani babban al'amari a tsakaninsu. A irin wannan situation d'in, yana yin wuya patient ya dawo dai-dai saboda sai jinin yayi circulating, sannan ya gaurayu da asalin jinin jikinta tukunna zai fara aikawa brain sak'o, don haka sai ya d'auki lokaci mai tsawo, a b'angaren Neenah ko d'igon jinin Khulayd kawai yasa ta taso daga trauma da take ciki, kasa yin komai likitan yayi, kawai ya tsaya kallon ikon Allah. Fisge-fisge ta fara yi kamar wata sabuwar mahaukaciya, k'ok'arin fisge k'arin jinin da aka yi mata ta fara yi, da sauri likitan ya matso kusa sannan ya rik'e hannunta gam, k'wala wa nurses kira ya shiga yi suka shigo d'akin cikin hanzari, daga nan ya umurcesu da su rirriketa gudun kar tayi nasaran fisge k'arin jinin, yadda take yi yasan idan an k'yaleta zata iya ji wa kanta rauni. Da k'yar suma suka samu suka danneta saboda tana yi ne da dukkan karfinta, alluran bacci likitan ya ja a cikin 2mil syringe yayi mata, luuu ta koma ta kwanta, ba'a d'au lokaci ba bacci ya d'auketa.

Gyara zaman abun k'arin jinin hannunta likitan yayi, sannan ya matsa wurin sandan da aka rataye ledar jinin a kai, ya d'an k'ara tafiyan jinin saboda yana gani kamar yayi slow dayawa. Har d'igo na biyu ya sauka cikin jikinta, haka ma na uku, d'igo na hud'u na sauka Neenah ta sake bud'e idonta kuma ta tashi ta sake zama kamar d'azu, wannan karon bata wani fisge-fisge, sai dai bin d'akin da take yi da kallo na tsawon wasu mintuna, ji take yi kanta na sarawa kaman zai fashe, ga nauyi da jikinta keyi kaman an d'aura mata gungumen itace. A hankali ta rufe idanunta tana son tuno abunda ya faru, ita dai tasan she is on her way to Kaduna, kuma tana zaune a bayan mota ita kad'ai tana taunar chewing gum, sai kuma taji wani k'ara mai firgitarwa wanda hakan yasa tayi k'ok'arin duba meye dalilin wannan k'aran, bayan nan kuma bata sake sanin inda kanta yake bah. A razane ta bud'e ido, bata sauk'esu ko ina bah sai akan kafafunta, kallon kafafun sosai take yi ganin yanda aka rufesu cikin wannan farin abun, hawaye ne masu zafi suka fara bin kuncinta, hankalinta gabad'aya ya tashi, " No" ta fad'a tana girgiza kanta, k'ok'arin motsa kafan ta shiga yi a tsorace amma abun ya ci tura, ji take yi kamar kafafun ma basa jikinta k'wata-k'wata, "NO!" Ta sake fad'a da karfi kuma wannan karon kuka take yi sosai, " This can't be, wallahi bazan tab'a zama gurguwa ba soboda ba'a haifeni haka ba, sai nayi tafiya wallahi, sai nayi tafiya."

Juyowa tayi tana kallon likitan da tun d'azu ya koma baya yana kallonta, da hannunshi rungume a kan kirjinshi, murmushi ta shiga yi tace " Kai, nasan kai doctor ne ko? Kuma a asibitinka nake ko?" Sosai ta bashi tausayi, hakan yasa ya gyad'a mata kai kawai don har idanunshi sun kawo k'walla, babu alamar wasa a fuskarta tace "Ai babu abunda ya samu kafata ko?, ai kace zan yi tafiya kamar yadda nakeyi ko?"

Matsowa kusa da gadon likitan yayi, yama rasa ta ina zai fara yi mata bayani, yanke shawaran rarrashinta kawai yayi, don yana gani bai kamata ta san abunda ke faruwa ba alhalin tana cikin wannan yanayin. "Shhhh, don Allah ki k'wantar da hankalinki Miss, I promise you komai zai tafi a hankali idan akayi maki tiyata" cewar likitan, kamar tunzurata yayi, a fusace tace " Answer the damn question doctor, am I going to be fine Girgiza kai ya fara yi mata don baya tunanin zai iya cewa komai, sosai ta sake fashewa da kuka tana k'iran sunan Mami, " ina Mamina take, doctor inaso inga mahaifiyata, call my momma for me", k'in motsawa likitan yayi, yana ta aikin kallonta, da taga cewa bai da niyyan yin abunda ta fad'a yasa ta kai hannunta kan abun k'arin jinin da akayi mata, d'ago kai tayi tana kallonshi a cikin ido tace " Wallahi idan baka kira min Mami ba zan tuge wannan abun, sannan kuma in kashe kaina kowa ma ya huta".

Ganin yadda take maganan da iya gaskiyarta yasa likitan ya nufi kofa, kamar baya son zuwa lab d'in, don yasan cewa suna ganinshi zasu baibayeshi suna tambayan yaya jikin Neenah, jiki babu laka ya isa wurin lab d'in, ai ko Nailah na ganinshi ta window ta tashi da sauri ta isa bakin kofa tana " Doctor yaya take? Ba dai wani abun ne ya faru da ita ba ko?" Suna jin ta ambaci doctor, duk suka mik'e zuwa wurinsu, kowa da tambayar da yake jefa mishi, har ya rasa wanne zai amsa, daga karshe d'aga musu hannayenshi yayi yace

"Duk ku k'wantar da hankalinku, babu abunda ya sameta, she just want to see her mother"

Mantawa ma Mami tayi kan cewa likitan ya san ita ce mahaifiyar Neenah, nuna mishi kanta da hannunta ta shiga yi tana "Ni ce mahaifiyarta, ni ce", tana maganar ne tana hawaye, kafin likitan ya sake cewa komai, har Mami ta tureshi tayi gaba abunta.

Mr Abeed ya ja likitan gefe, yace "Doctor, muma zamu iya ganinta kuwa, wallahi muna so mu gantan", girgiza kai likitan yayi yace "Am afraid, ba zaku iya....." Mr Abeed bai bari ya k'arashe zancen ba, yace " Doctor sai fa kayi hakuri, bazan iya jurewa ba, sai na ganta" yana gama fad'in haka shima ya wuce. Nailah da Sahr na ganin haka suka mik'e suma suka bishi, haka Khulayd duk da jirin da yake ji, ya sauk'o daga kan gadon a daddafe, ya fita.

Mami na bud'e k'ofan, idanunsu yayi karo da juna, tsayawa tayi a bakin kofan tana kallonta yayin da kuka ya k'wace mata, saurin toshe bakinta tayi, tana k'ok'arin mayar da kukan "Mami ki fad'amin gaskiya, is everything okay? Zan sake tafiya kenan daga yau? Nasan ke mahaifiyata ce, baki tab'a yi min k'arya bah, kuma nasan baza ki yimin yanzu bah don haka ki fad'a min" cewar Neenah Da gudu Mami ta k'arasa wurin gadon ta rungumeta suka cigaba da kuka, kuka sosai suke yi babu mai rarrashin wani a cikin su, "Mami me ya saki kuka? Ai lafiyata kalau kuma babu abunda zai sameni?" K'in kulata Mami tayi ta cigaba da kukanta, d'an tureta Neenah tayi tana mata kallon tuhuma, rai a b'ace tace "Mami ki amsani mana, am I going to be alright?."

Duk basu san ma ya baro lab d'in ba, sai ji suka yi yace "U will never be okay Neenah" duk suka juyo suna kallonshi, fasawa tsakaninsu yayi ya shiga cikin d'akin, tsayawa yayi a bakin gadon ya rungume hannunshi a kirjinshi, cigaba da maganarshi yayi " Ai daga yanzu kin zama gurguwa har karshen rayuwarki kenan, ba zaki sake tafiya bah Neenah, hakan da kika ga ya faru dake shine ake k'ira sakayya, da kin d'auka zaki yi duk irin muguntan da kika yi ta shukawa and get away with it? No way, ai hakan ma kad'an ne a wurina coz I really hoped Allah will punish u far more than making u crippled, ke mace ce mara Imani, mara tausayi, mai son kai, u re so selfish dat u want everything good for yourself, d worst of it ma har da kanwarki ta jini kika so yin mugunta, I really wished bakya cikin y'an uwana, I hate you so very much kuma......"

Bai gama ba yaji saukan mari a gefen fuskarshi na dama, a ranzane ya d'ago yaga ko waye ya shammaceshi da irin wannan marin, ga mamakinshi yaga Mami ce. Da mamaki yake kallonta, don bai tab'a zaton ita ce tayi marin ba, dafe kuncinshi yayi da both hannayenshi yana kallonta, sadda kai yayi bayan ya gama kallonta na tsawon wasu seconds yace "Mami kece yau kika mareni? A iya tsawon rayuwata, tun da nasan kaina baki tab'a d'aga min hannu ba bare har kiyi tunanin bugu na, sai yau don na fad'i gaskiya? Don na fad'i abunda ke cikin raina?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull