Kenza eBookz

Sahr khulaiyd complete - Chapter 16

Sahr khulaiyd complete - Chapter 16

Sahr khulaiyd complete Chapter 16: Sahr khulaiyd complete Chapter 16. "And I'll slap u hundred times idan ka sake fad'in irin munanan maganganun nan a…

4,468 words

"And I'll slap u hundred times idan ka sake fad'in irin munanan maganganun nan a kanta, baka da hankali neh kake fad'an haka akan 'yar uwarka? Kuskure ne ta riga da ta aikata, duk da cewa ni kaina ina fushi da ita ba zai sa inji irin kalamun da kake fad'i a kanta bah, am a mother kuma mothers are supposed to be shields for their children, babu uwar da zata so wani mummunan abu ya samu y'ay'anta, I admit tayi laifi but ya wuce tunda muka gano gaskiya, and I bliv she have learnt her lesson. Ka kalli halin da take ciki, sannan kake roka mata abun da yafi haka? When did u became this heartless? Saboda ni d'ana Khulayd da na sani yana da k'yak'k'yawan zuciya, yana yiwa kowa fatan alkhairi, yana da tausayi, amma kai" ta fad'a ne tana nunashi da yatsa sannan ta cigaba " Kai ba Khulayd d'ina bane, I don't know u" ta sake fashewa da matsanancin kuka.

Murmushi Khulayd yayi, har yanzu hannunshi na kan kuncinshi, runtse ido yayi saboda kalamun Mami sun mishi tsauri, juyowa yayi yana fuskantarta yace "Mami am still your son, ni ne Khulayd d'inki kuma har yanzu ni mai tausayi neh kamar yadda kika sanni a baya, kalamun da kika ji ina furtawa daga kasan zuciyata suke, kuma I know you'll understand me idan kika ji dalilin fad'an haka da nayi" shiru yayi na d'an wani lokaci tukunna ya d'ago yana kallon Neenah, yace

"Am sorry Neenah, yau zan bud'e sirrin da kika dad'e kina rufewa, u fooled us all along don kina gani kamar Allah ba zai toni asirinki bah, zan fad'a yau, kuma yanzu, in front of everyone musamman Mami da precious"

Stretching hannunta Neenah tayi, tana hawaye sosai tace "No, please Mr Omair kada ka min haka, I beg u don Allah ka rufa min asiri, wayyo Allah na!"

K'in kulata Khulayd yayi, ya dawo da kallonshi kan Mami, yace "Mami, I know you'll be wondering meye Precious tayi da har tayi deserving a sace ta?, zaki ke tunanin wace mace ce zata aikata wannan mummunar aika-aikan akan mace y'ar uwarta? Neenah a nan" ya fad'a ne yana nunata, yayin da ita kuma ta kawar da kanta gefe ta runtse ido sosai, ta cigaba da kuka, ji take yi kamar ta tsaga kasa ta shiga don kunyan abunda ta aikata, Khulayd yace

"Ita ce tayi planning komai da komai, ita ce tayi instigating Barr Zayyad akan precious, to cut d long story short, ita ce tasa yayi abducting precious kuma tasa yayi raping d'inta"

Da mamaki dukkansu suka juya suna kallon Neenah, kowa ya kasa gaskata abun da Khulayd ya fad'a duk da sun san cewa bazai musu karya bah, ganin kowa kallonta yake yi yasa Neenah sunkuyar da kai kasa, rawa bakinta keyi, bata iya furta komai bah sai "Am sorry!", a fusace Mami ta juyo tana nunata da y'atsa tace

"Neenah you!? Ki fad'amin k'arya yake yi."

Posted on : Sunday Date. : 15th April, 2018 Time :06:01pm Written by : Seemby luff😘

© *SEEMBY LUFF* 😘

⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff* 😘 page *67* ⚜

Shiru Neenah tayi bata ce komai bah, a fusace Mami tace "Neenah tambayarki nakeyi, ki fad'amin cewa ba gaskiya Son yake fad'a bah" Neenah ta d'ago kanta a hankali tana kallon Mami, tace "Mami am sorry, don Allah ki yafemin, wallahi son zuciya da sharrin shaid'an ne suka tunzurani har na aikata haka, am sorry mother!".

Jiki babu k'wari Sahr ta k'arasa kusa da gadon, kallon Neenah take yi kamar yau neh ta fara ganinta, fuskarta d'auke da tsananin Mamakin abunda taji data bakin Khulayd, kafad'an Neenah ta rik'e dukka biyu ta shiga jijjigata, kamar wata sabuwar mahaukaciya ta fara magana cikin kuka "Adda Neenah ki kalleni, ni ce fah Sahr, ni ce kid sister da kika fi kowa sona, am that little baby whom u watched while growing up, ni ce wannan yarinyar wacce bakya iya bacci har sai nayi, meyasa zaki so lalata min rayuwa? Meyasa zaki so ganin rayuwata ya salwanta? Me na tare miki a rayuwa Adda Neenah? Fyad'e fa kika sa ayi min, kina son rabani da abunda yafi muhimmanci a rayuwata kawai don kiyi satisfying selfish interest d'inki, toh me hakan zai amfaneki dashi?" Ta k'are maganan tana kan jijjigata.

Babu abunda Neenah ta fad'a mata, tun da Sahr ta fara maganan ma kanta na kasa don ba zata iya d'ago kai ta kalleta bah, kunyan abunda ta aikata ma ba zai barta ta kalleta bah, a harzuk'e Sahr ta d'ago fuskanta, tana kallon cikin idonta tace "Ki amsamin Adda Neenah, ki fad'a min dalilin da yasa kika tsaneni har haka, ki fad'amin" jijjigata ta cigaba da yi har sai da Neenah'n ta fara cizar leb'b'anta saboda zogin da kafarta ke yi, da sauri Nailah ta k'arisa wurin gadon itama ta janye Sahr ta rungumeta, gam Sahr d'in ta rik'eta tana rusar kuka kaman ranta zai fita, rarrashinta Nailah ta soma yi yayinda itama take hawaye "Shhhh! Kid sister, ya isa haka, ki daina kukan haka nan don Allah, isn't it obvious saboda Ya Khulayd ne tayi miki duk wad'annan abubuwan? In da ni ce ke wallahi bazan yi kuka bah tunda bata yi nasara a kanki ba."

Shiru Neenah tayi na d'an wani lokaci kafin tace "Na farko, duk wasu makircin da ta rika shukawa bai sa Ya Khulayd ya daina sonki bah, sai ma ninkuwan da sonki yake yi a cikin zuciyarshi, na biyu kuma Barr Zayyad bai yi nasaran k'wace maki budurci bah duk da cewa hakan taso, don haka ni sam ban ga abin kuka a nan ba."

Saketa Sahr tayi, tana kallonta da rinannun idanunta wad'anda suka k'ank'ance saboda kuka, da dashashshiyar murya tace "Adda Nailah ba zaki gane bane, ya zama min dole ne kawai inyi kuka, abun da ciwo a ce y'ar uwarka ta jini tana son salwantar da rayuwarka, ki duba kiga yanda na d'auketa a zuciyata, ina matukar sonta fiye da yadda kike tsammani, she's like a second mother to me, ta raineni tamk'ar ita ce ta haifeni, bana tab'a iya jurar ganin b'acin ranta, zan iya sadaukar mata da komai nawa, zan iya sadaukar mata da raina idan tana son haka, ban san me yasa na kasa sadaukar mata da Ya Khulayd ba, ko don saboda shine farkon d'a namijin da na fara so a rayuwata ne? Me yasa ta kasa fahimtar haka? Me yasa ta kasa fahimtar cewa ina sonshi fiye da tawa rayuwar bah? Me yasa ta kasa fahimtar cewa ba zan tab'a iya rayuwa a duniyar da babu shi a cikinta ba? Wannan wace irin mahaifiya ce da bata son farin cikin y'arta? Sune tambayoyin da idan na tuna, suke sakani kuka Adda Nailah"

Sake rungumeta tayi, yayinda ta kwanta a kan kafad'arta tana rusar kukanta, shafa kanta Nailah ta shiga yi a hankali tana "Shhh! Ya isa haka, kada ki sawa kanki zazzab'i saboda kukan nan."

Shiru kowa yayi a d'akin, babu abunda ke tashi sai sautin kukansu, jan jiki Neenah tayi ta fisge k'arin jinin, tana son sauk'owa daga saman gadon, basuyi aune bah suka ji ta fad'o k'asa, wani k'ara "Arrrgghh!" Ta saki mai cike da azaba, da gudu Mami ta karaso wurinta tana son d'agata, bata ma san har taje wurin bah, tausayin y'ar tata take ji can k'asan zuciyarta duk da cewa bata jin zata iya yafe mata nan kusa, d'aga mata hannu Neenah tayi alamar kada ta tab'ata, tace

"A'a Mami, ki k'yaleni don ban cancanci tausayinki bah, nasan cewa duk abunda ya sameni ni naja wa kaina, am the architect of my own problems, na kasance mai son kai kuma mara tausayi, ku kuma duk da haka kuna nuna min tsantsar kauna, ban cancanci soyayyarku bah, ban cancanci hawayen da kuke zubarwa a kaina bah, kamata yayi ku kyaleni in sha wahalana ni kad'a, ji nake yi da ma mutuwa nayi, da yafi min sauk'i akan irin kunyar da nakeji yanzu"

Mami ce ta tari numfashinta da cewa "Ai ba kece da izinin rayuwa da mutuwarki bah" ta fad'a ne tana d'auke kanta gefe.

Sanyi Neenah taji a ranta, saboda ta san har yanzu akwai burbud'in sonta a zuciyar Mami, rik'e hannun Mami tayi gam tana son fad'a mata wani abu, k'ok'arin fisge hannunta daga rik'on Mami ta fara yi, sai dai Neenah tak'i ta saketa, juyowa Mami tayi tana kallon Mr Abeed wanda kamar babu shi a d'akin, girgiza mata kai ya shiga yi alamar kada ta fisge hannun nata, jiki babu k'wari ta k'yaleta amma sai ta d'auke kanta da barin kallonta, sanya hannu Neenah tayi ta juyo da fuskar Mami, d'ago hab'arta tayi tana y'ar murmushi tace

"Mami, nasan yanda yanzu kike ji a ranki, tun tasowarmu ni da kannena, kin fi shan wahala a kaina, tun a wancan lokacin ni ce nake baki matsala, har na girma na mallaki hankalin kaina baki tab'a nuna gazawarki a kan tarbiyyata ba, baki tab'a nuna gajiyawa ba. Sai dai ni na kasance hasararriyar y'a, y'ar da bata bin umurnin mahaifiyarta, y'ar da take bijirewa mahaifiyarta don son zuciyarta, na sani I've never been a good daughter, kawai zuciyarki irin na jarumar uwa ne ya hanaki nuna min haka, kinsha wahala a kaina Mami, kin sha zubar da tsadaddun hawayenki a kaina wanda sam bai kamata bah Mami, you deserve to be happy but all I do is bring sadness into your life mother, ban cancanci hawayenki ba mahaifiyata, mutuwa ne kawai ya cancanceni."

Kuka ne ya k'wace wa Mami, da fari ta busar da zuciyarta da idanunta, sannan ta nuna ba zata karaya ba, amma sai gashi kukan yaci karfinta, maganganun Neenah sun matuk'ar karya mata zuciya, kuka ta shiga yi sosai tana sobbing, girgiza mata kai Neenah ta shiga yi, yayin da itama hawayen yana wanke mata fuska "Don't cry mum, kar kiyimin kuka, ki....." Bata k'arisa ba itama kukan ya k'wace mata, kukan ta shiga yi kamar ranta zai bar jikinta, kusan mintuna goma suka d'auka suna aikin kuka, da k'yar kuma da rawar baki Neenah tace

"Kiyimin aikin gafara Mamina, na tuba wallahi na gane kuskurena, ki yafemin ko na samu salama a cikin hargitsatstsiyar rayuwata, pls forgive me mom, forgive me please" d'aura kanta tayi a kafafun Mami ta ci gaba da kuka, d'ad'd'aya Mami ta d'ago tana kallon duk wanda ke cikin d'akin, babu wanda bai yi k'walla bah, kowa ta kalla sai ya gyad'a mata kai alamar ta yafe mata, hnnunta na rawa ta d'agoshi, da k'yar ta iya d'aurawa akan Neenah dake kwance kan kafafunta, a hankali tace

"Its okay, na yafe miki d'iyata, na yafe miki duniya da lahira"

D'agowa Neenah tayi cikin tsananin farin ciki ta rungume Mami, rik'eta itama Mamin tayi kamar zasu shiga jikin juna, cike da murna Neenah tace

"Thank you Mum,I love you so much" Da gudu Nailah ta Sahr suka k'arisa wurinsu suma, rungume juna sukayi duk su hud'un suna kuka, k'aran bud'ewar kofan da sukaji ne ya sasu d'agowa su kalli wurin, likita suka gani sanye da kayan tiyata, ga nurses a bayanshi suma duk a cikin shirin tiyatan suke, ga kayan aiki sun turo akan wani tray mai taya, cire gilashi likita yayi daga idanunshi yace

"Inaga har kun cinye lokacin da aka baku, ko zaku iya fita yanzu? Saboda lokacin tiyatan yayi"

K'in kulashi sukayi, har yanzu manne suke da juna, ganin haka yasa Neenah murmushin karfin hali, tace

"Its okay" tana magana, tana binsu d'aya bayan d'aya, tana share musu hawaye, "Ku daina kukan haka nan, babu abunda zai faru da yardar Allah, am going to be fine okay. Ku dai kuje waje kuyi ta addu'ar Allah yasa a gama lafiya, kunji?"

Gyad'a kai suka shiga yi mata, amma idanunsu bai daina zubar da hawaye ba, kama fuskar Nailah tayi ta sumbaci goshinta, haka ma Sahr da Mami, a sanyaye suka mik'e suka nufi hanyar waje, dama Mr Abeed da Khulayd tuni sun fita abunsu, Mami a gaba, Nailah na biye da ita, sai Sahr a baya.

Har sun isa bakin k'ofa Neenah tace "Kid sis"

Juyowa Sahr tayi, tana kallonta, sunkuyar da kai Neenah ta sake yi tace "Am sorry, don Allah ki yafe....."

Da gudu Sahr ta isa wajenta ta toshe mata baki, girgiza mata kai ta shiga yi tana hawaye tace "Shhh! Adda Neenah, wallahi na yafe miki, I hold no grudges against u, ke y'ar uwata ce and I'll never stop loving you" share mata hawaye tayi, sannan itama ta sumbaci goshinta tace

"Ina fatan tiyatanki ya zama nasara" daga haka ta mik'e, tayi ficewarta

Posted on : Wednesday Date. : 18th April, 2018 Time : 02:15pm Written by. : Seemby luff

© *SEEMBY LUFF* 😘

⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff*😘 Page *68*

Sahr na gama fad'in haka, ta juya tayi ficewarta. Murmushi Neenah tayi tana share hawaye, at least yanzu hankalinta a kwance yake tunda ta nemi yafiyan kowa, da taimakon nurses aka samu aka maidata saman gado, sake d'aura mata jinin akay tukunna aka sauya mata kaya zuwa na tiyata, bayan lokaci kad'an aka fara.

Tarar dasu tayi dukkansu suna zauneh a reception, babu wanda ke cewa komai a cikinsu, they all look worried tun bama Mami bah, har yanzu bata daina hawaye bah, dube-dube ta fara yi a cikin reception d'in don bata ga Khulayd a wurin bah, can waje ta hangoshi ta window yana tsaye shi kadai, bata ce da kowa komai bah ta fita daga reception d'in zuwa wurinshi.

Har ta isa kusa dashi bai sani bah, hankalinshi gabad'aya baya tare dashi don yayi zurfi cikin tunani, completely lost in his thoughts, murmushi tayi tukun ta d'an tapping kafadarshi tace "Jaan"

A d'an tsorace ya juyo, duk da yaji kamar muryanta ne, "umm" yace kawai, ya juyo yana kallonta

"Me yasa kazo nan ka tsaya kai kad'ai? Tunanin me kakeyi haka? U seemed lost in your thoughts" ta tambayeshi tana kallonshi

"Precious, ina tunanin rayuwa ne kawai, ta yaya mutum zai zama mara imani haka, har yanzu I can't believe Neenah ta aikata haka, she's very heartless" ya bata amsa, bai ko juyo ya kalleta bah.

Shiru tayi tana nazarinshi, tasan cewa tunanin da yake yi kenan, tun da ta ganshi tsaye all alone tasan cewa bazai wuci hakan bah, d'agowa tayi ta sake kallonshi kafin ta sauk'e ajiyan zuciya, tace "Jaan"

"Umm" ya sake cewa, wannan karon ma bai kalleta bah

"Look at me" ta buk'ata

A hankali ya juyo ta inda take amma bai d'ago kai bah, a kasa kanshi yake. Saka hannu tayi kasan hab'arsa ta d'ago da fuskarshi, shima d'in idanunshi ya d'ago a hankali ya zubasu cikin nata yana kallo, kasa resisting kallon tayi don haka tayi saurin sadda kai k'asa, tace

"Jaan ni inaga kaman komai ya wuce, Adda Neenah y'ar uwarmu ce, ba zamu yar da ita don ta aikata haka bah, idan zaka duba zuwa yanzu tayi nadama, kuma ta nemi yafiyarmu, I think you should also forgive her and let it go, let bygone be bygone pls."

Shiru yayi yana kallonta na tsawon mintuna biyar, murmushi yayi yace "To naji precious, duk yadda kikeso haka za'a yi, kece da ni ai"

Rik'e hannunta yayi yace "Zo mu koma ciki y'ar kanwata" duk suna murmushi, suka koma ciki wurin su Mami.

Nan suka yi sallan azahar da la'asar, kowa hankalinshi ya tashi ganin tun lokacin da aka shiga tiyatan, har zuwa wannan lokacin bai k'are bah, sai kusan karfe biyar likitan ya fito, cire gloves dake hannunshi yayi, ya jefa cikin waste bin dake ajiye gefe guda, k'arasa yayi gaban wurin wanke hannu da aka tanadar, ya dauki wani disinfectant ya wanke hannunshi, tsoma hannu yayi cikin aljihunshi ya ciro handkerchief yana goge hannu dashi, sai da ya tabbatar ya dawo normal self d'inshi tukun ya fito haraban reception d'in.

Kusan a tare suka mik'e da suka ganshi, Mr Abeed ne yayi saurin k'arasawa wurinshi yana tambaya

"Doctor, how did it go? Da fatan an kammala babu wani matsala ko?"

Dafa kafad'anshi likitan yayi, yace

"It was very successful, babu wani abunda ya faru, don haka karku damu. Yanzu dai nurses sunyi transferring d'inta zuwa d'akinta, tana buk'atan hutu yanzu har sai tayi regaining consciousness tukunna za'a bari ku ganta"

Hand shake sukayi exchanging, godiya Mr Abeed yayi wa likitan, daga bisani ya wuce office d'inshi all tired and exhausted, babu wanda ya tambayi Mr Abeed abunda likitan ya fad'a, saboda komai a kan kunnensu aka fad'a. Duk da cewa likitan ya tabbatar musu da cewa babu matsala, har yanzu hankulansu bai kwanta bah, all they want is to see her, ganinta kawai suke buk'atar yi don su tabbatar da maganan likitan gaskiya neh.

Juyowa Mr Abeed yayi, yace

"Toh dai kunji abunda likita yace, its obvious ba zamu samu ganinta yanzu bah, I suggest wasu su tafi gida suyi preparing abinci, sannan a taho da abubuwan da za'a buk'ata, kai Khulayd" ya fad'a yana kallonshi, ya cigaba

"Ka tafi da Nailah da Sahr, am sure this isn't their first time na zama a asibiti don haka kun san abunda ake buk'ata, ni da sister zamu zauna kafin ta tashi."

Turo baki Sahr tayi gaba, tayi narai-narai da idanu kamar wacce zatayi kuka tace

"Allah ni Uncle ba zani gida bah, nima inaso inga Adda Neenah in ta tashi, am not going anywhere"

Ta fara bubbuga kafanta a k'asa, nan take hawaye ya fara wanke mata fuska, da gaske ta soma kukan tana ta fad'in ita kam ba zata tafi ko ina bah, rai a b'ace Mami tace

"Ke, zan sab'a miki fah, ya kike neman maida kanki wata k'aramar yarinya ne wai? Abu kad'an kiyi ta bubbuga kafarki kina turowa mutane baki kamar jab'a?, toh wa kikeso yaje gidan idan ba ke bah? Zaki wuce ne ko sai na b'allaki, kin girma amma sam baki sani bah"

Kuka sosai Sahr ta k'ara fashewa da, ta dad'e rabonta da Mami tayi mata fad'a haka, sai faman murza ido takeyi tana rusar kukanta.

A fusace Khulayd ya fincikota, yace

"Zaki wuce ne ko sai na b'ata miki rai, dallah wuce mara kunya kawai"

Jiki na b'ari tayi gaba, har tana neman yin tuntub'e don batayi tsammanin Khulayd zai mata haka bah, d'auka tayi zai rarrasheta yanda ya saba amma sai ya basar da ita, k'arasawa tayi wurin motan ta tsaya, ganinta a wurin yasa Khulayd saurin k'arasawa yayi unlocking motan, bud'e mata gidan gaba yayi yana k'ok'arin bata hak'uri, saurin shigewa ciki tayi ta ja k'ofan ta rife "bamm!" Har sai da ya tsorata.

Girgiza kai yayi yana y'ar murmushi, a zuciyanshi yace

"What a little lioness" sannan ya zagaya shima ya shiga, dama Nailah tun d'azu ta shiga abinta, daga haka suka tafi.

Duk abunda sukayi, a idon Mami da Mr Abeed, y'ar dariya Mami tayi don abun ya bata kunya da dariya, cike da neman magana tace

"Hmm, a haka wai za'ayi auren?"

"Very soon ma kuwa" Mr Abeed ya bata amsa a takaice.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°••••••••••••••••••••••••••••••°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

A mota, shiru Sahr tayi kamar bata ciki, had'e rai tayi don kada ma Khulayd ya samu damar yi mata magana, lokaci-lokaci yakan juyo ya kalleta, sannan ya maida hankalinshi kan driving da yake yi, Nailah dake baya duk tana lura dasu, sai ta gimtse baki kawai tana dariya.

Ganin shirun yayi yawa , Khulayd ya yana ta kallonta da wutsiyan ido, chan ya fara wak'a da hausa, bai ma iya ba don shi ba ma'abocin jin wak'ok'in Hausa bane

"Wasu ma fushi bai karb'esu bah, amma sai faman daddagewa sukeyi, wai a dan dole suna fushi"

Kusan sau biyar yake maimaita haka, amma Sahr k'in kulkashi tayi, yi tayi kamar bata san yana motan bah, kawar da kanta ma tayi gabad'aya tana kallo ta window, gani yayi fah da gaske yarinyar nan fushi takeyi dashi, yace

"Ni wallahi shirun nan ya isheni, mutum ma bai iya fushi bah amma sai yayi? Yanzu nima da nayi fushin za'a fara yimin magiya da kuka"

Nan ma banza tayi dashi, gyara madubin sama yayi ta yadda zai kalli Nailah da kyau, yace

"Kina ji ne sis Nailah, wannan yarinyar dole inyi mata kishiya tun kafin ayi auren, ko ma a daura rana d'aya, kinga duk sanda take fushinta sai in tafi d'akin waccar, musha love d'inmu kafin ta sauk'o"

"Aikam Ya Khulayd, wannan shawara tayi sosai, akwai kanwar k'awata zan baka sai ka had'asu, dama su k'awaye ne kaga zaiyi dai-dai" cewar Nailah

"Wallahi baku isa bah, Jaan ni ce fa precious d'inka, kake magana sake aure tun baka aureni bah?" Fashewa tayi da kuka sosai wanda yasa Khulayd da Nailah da sun sanin yin maganar ma, rarrashinta ya shiga yi yana bata baki, da kyar ya samu ta hak'ura akan yarjejeniyan zai siya mata chocolate da ice cream, share hawayenta ta shiga yi tana ajiyar zuciya.

Sai da suka biya, ya siya mata chocolate da ice cream d'in as promised, tukun suka wuce gidah, Nailah sai kallonsu takeyi tana jin dad'i a ranta.

Posted on. : Saturday Date. : 21st April, 2018 Time. : 09:50pm Written by. : Seemby luff😘

© *SEEMBY LUFF* 😘

⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff*😘 Page *69*⚜

Tun a cikin motan ta b'alle marfin ice cream ta fara sha, kallonta Khulayd yake yi har ya kusa manta cewa driving yake yi, yana kallonta like its the first time he had seen her, abubuwa dayawa yake sakawa a cikin zuciyarsa. Nailah duk tana lura dashi, ita kuma Sahr bata ma san yana yi bah, shan ice cream d'inta takeyi tana tand'e baki, duk abunda tayi k'yau yake masa, ji yakeyi kamar ya tsayar da motan so they could have a romantic moment.

"Ya Khulayd a maida hankali kan hanya dai, kar wannan kalle-kallen yasa kazo ka bugamu" cewar Nailah

Sosa k'eyarsa yayi yana murmushi, sam ya manta ma Nailah tana motan, ajiyar zuciya yayi sannan a zuciyarshi yace

"Thank God, I haven't done anything stupid" daga haka bai sake waiwayowa ya kalleta bah, maida hankalinsa yayi akan hanya duk da cewa zuciyarsa yana tunzurasa ya kalleta d'in, har suka isa gida babu wanda ya sake cewa komai. Horn Khulayd yayi lokacin da suka zo k'ofan gidah, da gudu-gudu maigadi ya wangale gate d'in suka shigo, a parking lot ya tsaya da motan yana ajiyar zuciya, Sahr bata yiwa kowa magana bah ta bud'e marfin motan ta fita tana ta santin ice cream d'inta, zamewa y'ar gyalen data yafa yayi amma ita kam bata lura bah, tafiyan ta kawai takeyi tana b'are ledan chocolate, fitowa Nailah tayi itama ta wuce abinta ta bar Khulayd yana k'okarin locking motan. Har ya zo zai tafi yaga gyalen a yashe a k'asa, da sauri ya d'aga kanshi yana kallonta, yaga sai tafiyanta takeyi, doguwar rigan data saka ya zauna mata dab'as a jikinta, still yayi a wurin yana kallon spotless bayanta daga nesa, kamar an mintsilesa ya sunkuya a d'auki gyalen sannan yayi saurin bin bayanta.

Har kusan ture Nailah yayi, sahr ta shiga k'ofa kenan yayi saurin jawo hannunta suka shige corridor dake parlor'n, a tsorace ta d'ago tana kallonshi don bata yi tsammanin har yazo kusa da ita bah, zata yi magana yayi saurin rufe mata baki da hannunshi, kallonshi kawai takeyi bata san meye nufinshi na yin haka bah, shima kallonta yake yi from head to toe yana numfashi sama-sama, sai da yayi kusan minti biyar yana kallonta kaf tukun ya d'auke hannunshi a kan bakinta "Precious wallahi hak'urina ya fara k'arewa, I can't control myself anymore, ganinki kullum yana sani tunani sosai, banso in aikata wani abun da ba shi bane a kanki sam, kece kad'ai macen da na kasa tattara kaina a kanta, my feelings for you increases with each passing day kuma hakan yana so yafi k'arfina, please talk to Mami, ni kuma I'll talk to Papa don ayi auren nan da wuri, in ba haka bah...." Kamo hannunta yayi, ya d'aura dai-dai saitin k'irjinsa yace

"Precious kiji yanda zuciyata ke bugawa kamar zai faso k'irjina ya fito, hakan zuciyata ke bugawa whenever am with you."

Shiru Sahr tayi still da hannunta a saman k'irjinsa, babu k'arya kam zuciyarsa na bugu da sauri-sauri, tayi kusan seconds arba'in kafin a hankali ta sauke hannunta, sunkuyar da kanta tayi don da ace zata iya d'aura hannunsa a kan k'irjinta, hak'ika da yaji yadda itama zuciyarta ke bugawa duk lokacin da suke tare, rungume hannu yayi a k'irji ya jingina da bango yana kallonta bai ce komai bah, zame jikinta tayi kawai ta bar wajen, da y'ar gudunta ta haura stairs zuwa d'akinta, ajiyar zuciya yayi sannan yayi murmushi don yasan kunyansa takeji sosai, ba don haka ba she could have expressed what she's feeling too, a fili yace

"Insha Allah you'll soon be mine, ina jin hakan a jikina" daga nan shima ya haura sama abunsa.

Bayan ita da Nailah sun d'an huta, suka sauya kaya zuwa mai sauk'i sannan suka wuce kitchen, abinci mai rai da lafiya suka girka suka zuba a flask, har sun kammala komai sun share kitchen zasu fita, sai Nailah taji Sahr tace

"Inna lillahi"

Da sauri ta juya don a zatonta b'arin abincin tayi, har tsinkewa zuciyarta yayi don ta matuk'ar gajiya, ganin Sahr tsaye ta b'ata rai da basket na abincin a hannunta yasa tace

"Lafiya naji kina Inna lillahi? Wallahi d'auka nayi kin b'arar da abincin nan"

"Adda Nailah, mantuwa fa mukayi bamu kad'a wa Adda Neenah kunun alkaman bah, kinsan its her favorite kuma am sure she's gonna ask for it when she wakes up"

B'ata rai Nailah tayi bata ce komai bah, a wahale ta koma cikin kitchen d'in kamar zatayi kuka, d'aura basket d'in Sahr tayi a saman fridge, ta k'arasa wurin drawer ta fara bud'esu tana duba alkama, cikin kankanin lokaci suka kammala had'a kunun, daga nan Nailah ta bar Sahr a kitchen d'in ta wuce d'aki abunta, sai da Sahr ta juye kunun a wani flask d'in sannan ta wanke tukunyan da sukayi amfani dashi ta mayar dashi locker. A nan kitchen d'in ta bar abincin tayi d'akinta, toilet ta fad'a da sauri ta watsa ruwa ta fito, simple gown ta saka sannan ta d'auko hijabinta mai hannu ta saka, kusan a tare suka sauk'o da Nailah, tarar da Khulayd suka yi zaune a parlor yana jiransu, da sauri Sahr ta fad'a kitchen ta d'auko basket da flask na kunun tafi fito tana

"Jaan mun gama fa, mu tafi koh?"

Mik'ewa yayi yana murmushi ya k'araso gabanta, bai ce komai ba yasa hannu ya k'arb'i flask na kunun tukun yace

"Lemme help you"

D'agowa tayi ta kalleshi itama da murmushi a fuskarta, haka suka wuce yana gaba tana biye dashi a baya, har zuwa wurin mota, sai da ya bud'e mata ta shiga tukun ya ajiye mata flask dake hannunshi, ya zagaya ya shiga suka wuce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull