Kenza eBookz

Sahr khulaiyd complete - Chapter 17

Sahr khulaiyd complete - Chapter 17

Sahr khulaiyd complete Chapter 17: Sahr khulaiyd complete Chapter 17. Wurin parking Khulayd ya nema lokacin da suka shigo haraban asibitin, da k'yar ya…

4,361 words

Wurin parking Khulayd ya nema lokacin da suka shigo haraban asibitin, da k'yar ya samu guri ya ajiye motan don yawan motocin masu ziyara da suka cika asibitin makil, kamar d'azu ya d'auki flask na kunu, ita kuma Sahr ta d'au basket suka jera suna hira abunsu, suna shiga cikin ward d'in yayi dai-dai da fitowan likita daga d'akin Neenah, sanar dasu yayi cewa zasu iya shiga su ganta yanzu, mik'ewa Mami da Mr Abeed sukayi kusan a tare suka isa bakin k'ofan. A hankali Mr Abeed ya murd'a hannun k'ofan ya kutsa kai ciki, Mami na biye dashi a baya, sai kuma su Khulayd, Sahr da Nailah, zaune take kan gadon ta kura idanunta a kan k'ofa, kafafunta dukka biyu an rufesu da farin bandage saboda an yankesu har iya gwiwa, ganin Mr Abeed yasa ta fashe da wani matsanancin kuka tana

"Uncle, ka dubi yadda favorite d'inka ta koma, yanzu am a cripple with no legs duk kuma sanadin abubuwan dana aikata mara k'yau"

Kuka take yi sosai kamar ranta zai fita, sake basket na hannunta Sahr tayi suka k'arasa ita da Nailah wurin gadon, babu shiri suka haye saman gadon, rungumeta suka yi duk su biyun suna rusar kuka. Tsayuwa Mami tayi still a wurin ta kasa koda motsawa, kallon Neenah take yi kawai da tausayinta fal zuciyarta, kasa hana hawayen tayi su zubo, toshe bakinta tayi da dukka hannayenta tana kuka mara sauti, a wahale Neenah ta d'ago kanta tana kallon Mami

"Mami kin tausayamin koh? Bazaki matso kusa dani in rik'eki bah mahaifiyata? Kukan da kika yi ya isa haka nan"

Mik'o hannayenta tayi wa Mami alamar tazo, kamar batason tafiya take yi har ta k'araso wurin gadon, bata damu da ta k'arb'i hannun da Neenah ke bata bah, a hankali ta d'aura hannunta saman kafafun Neenah, hawayenta na d'iga kan bandage dake rufe da kafarta, girgiza kanta ta farayi tana tafiya da baya-baya har ta isa kofan d'akin, da sauri ta bud'e ta fice waje, a nan ta zube tana kukanta har ta tara y'an kallo.

Matsowa Mr Abeed yayi shima kusa da gadon, ya d'aura hannunshi a kan Neenah yana shafawa a hankali yana rarrashinta. Tsaye Khulayd yake nan kusa da bakin k'ofa rungume da hannayenshi, tun shugowarsu yake tsaye a wurin yana bin duk wanda yayi magana da kallo, a hankali Neenah ta kai idanunta kanshi, bayan hannu tasa ta share hawayen fuskarta, murya a d'an d'age tace

"Mr Omair kai ba zaka iya yafemin ba koh?"

Shiru tayi kaman mai jiran amsa, sai dai Khulayd bai ce da ita komai bah, kallonta kawai yake yi, murmushi tayi kad'an sannan ta cigaba

"Nasan cewa zai yi wuya ka iya yafemin abubuwan dana rik'a aikatawa a kanka da kid sister, I can understand the pain I've caused you, nayi k'ok'arin rabaka da farin cikinka ko ta halin k'ak'a, wanda har hakan ya jawo kayi jinya a asibiti"

Kuka ta fashe da, batason tuna abunda suka faru a baya sam saboda yin hakan tamkar tana fame ciwon dake dunk'ule a zuciyarta neh

"Mr Omair don Allah, find a place in your heart and forgive this sister of yours, wallahi nasan idan har baka yafemin bah bazan tab'a fita daga k'uncin da zuciyata ke ciki bah, ba don ni bah, ka duba condition d'ina ka yafemin and I promise you, haka ba zai sake faruwa bah."

Shiru tayi ta k'ura mishi idanu, shi d'in ma ita yake kallon, maganganunta sun matuk'ar karya mishi zuciya amma ya kasa furta komai, kamar statue aka ajiye a wurin, tasowa Sahr tayi ta k'arisa wajenshi, kamar wani k'aramin yaro ta ja hannunshi yana biye da ita har zuwa bakin gadon tukun ta sakeshi ta zauna. Nailah ce ta mik'e a hankali ta dafa kafad'anshi tace

"Ya Khulayd na san kana da k'yak'k'yawan zuciya, bai kamata a ce ana abu d'aya tuntuni bah, we all know cewa Neenah bata yi dai-dai bah but, mahaliccin mu ma mukan masa laifi, wani abun ma ko kare ba zai shunshuna ba amma haka zai yafe mana saboda mu samu rabo ranar kiyama, toh idan har Allah zai yafe mana laifukanmu su waye mu y'an Adam da ba zamu yafe wa waninmu bah? Please brother forgive her not for her sake, but for Allah's, for Mami, for Uncle, for me and for your precious kid sister,please."

Yanzu kam ba zai tab'a iya k'in yafe mata bah, not after ta ambaci Allah da kuma sunayen mutane mafi soyuwa a wurinshi, ciro handkerchief yayi daga aljihunshi ya share zufan da ya k'eto mishi, a sanyaye yace

"Na yafe mata, Allah ya yafe mana baki d'aya"

Cike da farin ciki suka amsa da "Ameen"

Dirowa Sahr tayi daga saman gadon, flask na kunun ta d'auko ta sake dawowa wurin gadon tace

"Adda Neenah mun kad'a maki fav kununki, zaki sha?"

Gyad'a kai ta shiga yi tana fare hawayenta, jinta take yi kamar sabuwar mutum as she's so overwhelmed, bud'e flask d'in Sahr tayi ta d'ebo kunun a cup, dama sun dafa da sugar don haka cokali kawai ta jefa a ciki, matsowa kusa da Neenah tayi tace

"Yau ni zan baki a baki"

D'ebo kunun tayi a cokalin ta kai bakin Neenah tana "aaaa", da murmushi Neenah ta bud'e bakinta tana karb'a har tasha rabin cup din tace ta k'oshi

"A'a baki k'oshi bah, sai fa kin shanye, bari kiga na baki" cewar Khulayd, haka yayi ta bata har ta shanye tas, da handkerchief d'inshi yayi amfani ya goge mata bakinta, dad'i sosai Mr Abeed yaji seeing the family united once again, bayan an k'irawo Mami neh Mr Abeed yace

"Labari mai dad'i zan fad'a muku, next week insha Allah zamu tafi neman auren Sahr a wurin dangin mahaifinta, sam banaso bikin ya wuce wata d'aya"

A bazata maganar yazo wa Khulayd, babu shiri ya rungume Papanshi very tight, Sahr kuma mik'ewa tayi ta fice daga d'akin da tsananin kunya, a zuciyarta kuwa this is d best news she has ever received.

Posted on. Tuesday Date. 24th April, 2918 Time. 10:30pm Written by. Seemby luff😘

© *SEEMBY LUFF* 😘

⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff*😘 Page *69*⚜

Tun a cikin motan ta b'alle marfin ice cream ta fara sha, kallonta Khulayd yake yi har ya kusa manta cewa driving yake yi, yana kallonta like its the first time he had seen her, abubuwa dayawa yake sakawa a cikin zuciyarsa. Nailah duk tana lura dashi, ita kuma Sahr bata ma san yana yi bah, shan ice cream d'inta takeyi tana tand'e baki, duk abunda tayi k'yau yake masa, ji yakeyi kamar ya tsayar da motan so they could have a romantic moment.

"Ya Khulayd a maida hankali kan hanya dai, kar wannan kalle-kallen yasa kazo ka bugamu" cewar Nailah

Sosa k'eyarsa yayi yana murmushi, sam ya manta ma Nailah tana motan, ajiyar zuciya yayi sannan a zuciyarshi yace

"Thank God, I haven't done anything stupid" daga haka bai sake waiwayowa ya kalleta bah, maida hankalinsa yayi akan hanya duk da cewa zuciyarsa yana tunzurasa ya kalleta d'in, har suka isa gida babu wanda ya sake cewa komai. Horn Khulayd yayi lokacin da suka zo k'ofan gidah, da gudu-gudu maigadi ya wangale gate d'in suka shigo, a parking lot ya tsaya da motan yana ajiyar zuciya, Sahr bata yiwa kowa magana bah ta bud'e marfin motan ta fita tana ta santin ice cream d'inta, zamewa y'ar gyalen data yafa yayi amma ita kam bata lura bah, tafiyan ta kawai takeyi tana b'are ledan chocolate, fitowa Nailah tayi itama ta wuce abinta ta bar Khulayd yana k'okarin locking motan. Har ya zo zai tafi yaga gyalen a yashe a k'asa, da sauri ya d'aga kanshi yana kallonta, yaga sai tafiyanta takeyi, doguwar rigan data saka ya zauna mata dab'as a jikinta, still yayi a wurin yana kallon spotless bayanta daga nesa, kamar an mintsilesa ya sunkuya a d'auki gyalen sannan yayi saurin bin bayanta.

Har kusan ture Nailah yayi, sahr ta shiga k'ofa kenan yayi saurin jawo hannunta suka shige corridor dake parlor'n, a tsorace ta d'ago tana kallonshi don bata yi tsammanin har yazo kusa da ita bah, zata yi magana yayi saurin rufe mata baki da hannunshi, kallonshi kawai takeyi bata san meye nufinshi na yin haka bah, shima kallonta yake yi from head to toe yana numfashi sama-sama, sai da yayi kusan minti biyar yana kallonta kaf tukun ya d'auke hannunshi a kan bakinta "Precious wallahi hak'urina ya fara k'arewa, I can't control myself anymore, ganinki kullum yana sani tunani sosai, banso in aikata wani abun da ba shi bane a kanki sam, kece kad'ai macen da na kasa tattara kaina a kanta, my feelings for you increases with each passing day kuma hakan yana so yafi k'arfina, please talk to Mami, ni kuma I'll talk to Papa don ayi auren nan da wuri, in ba haka bah...." Kamo hannunta yayi, ya d'aura dai-dai saitin k'irjinsa yace

"Precious kiji yanda zuciyata ke bugawa kamar zai faso k'irjina ya fito, hakan zuciyata ke bugawa whenever am with you."

Shiru Sahr tayi still da hannunta a saman k'irjinsa, babu k'arya kam zuciyarsa na bugu da sauri-sauri, tayi kusan seconds arba'in kafin a hankali ta sauke hannunta, sunkuyar da kanta tayi don da ace zata iya d'aura hannunsa a kan k'irjinta, hak'ika da yaji yadda itama zuciyarta ke bugawa duk lokacin da suke tare, rungume hannu yayi a k'irji ya jingina da bango yana kallonta bai ce komai bah, zame jikinta tayi kawai ta bar wajen, da y'ar gudunta ta haura stairs zuwa d'akinta, ajiyar zuciya yayi sannan yayi murmushi don yasan kunyansa takeji sosai, ba don haka ba she could have expressed what she's feeling too, a fili yace

"Insha Allah you'll soon be mine, ina jin hakan a jikina" daga nan shima ya haura sama abunsa.

Bayan ita da Nailah sun d'an huta, suka sauya kaya zuwa mai sauk'i sannan suka wuce kitchen, abinci mai rai da lafiya suka girka suka zuba a flask, har sun kammala komai sun share kitchen zasu fita, sai Nailah taji Sahr tace

"Inna lillahi"

Da sauri ta juya don a zatonta b'arin abincin tayi, har tsinkewa zuciyarta yayi don ta matuk'ar gajiya, ganin Sahr tsaye ta b'ata rai da basket na abincin a hannunta yasa tace

"Lafiya naji kina Inna lillahi? Wallahi d'auka nayi kin b'arar da abincin nan"

"Adda Nailah, mantuwa fa mukayi bamu kad'a wa Adda Neenah kunun alkaman bah, kinsan its her favorite kuma am sure she's gonna ask for it when she wakes up"

B'ata rai Nailah tayi bata ce komai bah, a wahale ta koma cikin kitchen d'in kamar zatayi kuka, d'aura basket d'in Sahr tayi a saman fridge, ta k'arasa wurin drawer ta fara bud'esu tana duba alkama, cikin kankanin lokaci suka kammala had'a kunun, daga nan Nailah ta bar Sahr a kitchen d'in ta wuce d'aki abunta, sai da Sahr ta juye kunun a wani flask d'in sannan ta wanke tukunyan da sukayi amfani dashi ta mayar dashi locker. A nan kitchen d'in ta bar abincin tayi d'akinta, toilet ta fad'a da sauri ta watsa ruwa ta fito, simple gown ta saka sannan ta d'auko hijabinta mai hannu ta saka, kusan a tare suka sauk'o da Nailah, tarar da Khulayd suka yi zaune a parlor yana jiransu, da sauri Sahr ta fad'a kitchen ta d'auko basket da flask na kunun tafi fito tana

"Jaan mun gama fa, mu tafi koh?"

Mik'ewa yayi yana murmushi ya k'araso gabanta, bai ce komai ba yasa hannu ya k'arb'i flask na kunun tukun yace

"Lemme help you"

D'agowa tayi ta kalleshi itama da murmushi a fuskarta, haka suka wuce yana gaba tana biye dashi a baya, har zuwa wurin mota, sai da ya bud'e mata ta shiga tukun ya ajiye mata flask dake hannunshi, ya zagaya ya shiga suka wuce.

Wurin parking Khulayd ya nema lokacin da suka shigo haraban asibitin, da k'yar ya samu guri ya ajiye motan don yawan motocin masu ziyara da suka cika asibitin makil, kamar d'azu ya d'auki flask na kunu, ita kuma Sahr ta d'au basket suka jera suna hira abunsu, suna shiga cikin ward d'in yayi dai-dai da fitowan likita daga d'akin Neenah, sanar dasu yayi cewa zasu iya shiga su ganta yanzu, mik'ewa Mami da Mr Abeed sukayi kusan a tare suka isa bakin k'ofan. A hankali Mr Abeed ya murd'a hannun k'ofan ya kutsa kai ciki, Mami na biye dashi a baya, sai kuma su Khulayd, Sahr da Nailah, zaune take kan gadon ta kura idanunta a kan k'ofa, kafafunta dukka biyu an rufesu da farin bandage saboda an yankesu har iya gwiwa, ganin Mr Abeed yasa ta fashe da wani matsanancin kuka tana

"Uncle, ka dubi yadda favorite d'inka ta koma, yanzu am a cripple with no legs duk kuma sanadin abubuwan dana aikata mara k'yau"

Kuka take yi sosai kamar ranta zai fita, sake basket na hannunta Sahr tayi suka k'arasa ita da Nailah wurin gadon, babu shiri suka haye saman gadon, rungumeta suka yi duk su biyun suna rusar kuka. Tsayuwa Mami tayi still a wurin ta kasa koda motsawa, kallon Neenah take yi kawai da tausayinta fal zuciyarta, kasa hana hawayen tayi su zubo, toshe bakinta tayi da dukka hannayenta tana kuka mara sauti, a wahale Neenah ta d'ago kanta tana kallon Mami

"Mami kin tausayamin koh? Bazaki matso kusa dani in rik'eki bah mahaifiyata? Kukan da kika yi ya isa haka nan"

Mik'o hannayenta tayi wa Mami alamar tazo, kamar batason tafiya take yi har ta k'araso wurin gadon, bata damu da ta k'arb'i hannun da Neenah ke bata bah, a hankali ta d'aura hannunta saman kafafun Neenah, hawayenta na d'iga kan bandage dake rufe da kafarta, girgiza kanta ta farayi tana tafiya da baya-baya har ta isa kofan d'akin, da sauri ta bud'e ta fice waje, a nan ta zube tana kukanta har ta tara y'an kallo.

Matsowa Mr Abeed yayi shima kusa da gadon, ya d'aura hannunshi a kan Neenah yana shafawa a hankali yana rarrashinta. Tsaye Khulayd yake nan kusa da bakin k'ofa rungume da hannayenshi, tun shugowarsu yake tsaye a wurin yana bin duk wanda yayi magana da kallo, a hankali Neenah ta kai idanunta kanshi, bayan hannu tasa ta share hawayen fuskarta, murya a d'an d'age tace

"Mr Omair kai ba zaka iya yafemin ba koh?"

Shiru tayi kaman mai jiran amsa, sai dai Khulayd bai ce da ita komai bah, kallonta kawai yake yi, murmushi tayi kad'an sannan ta cigaba

"Nasan cewa zai yi wuya ka iya yafemin abubuwan dana rik'a aikatawa a kanka da kid sister, I can understand the pain I've caused you, nayi k'ok'arin rabaka da farin cikinka ko ta halin k'ak'a, wanda har hakan ya jawo kayi jinya a asibiti"

Kuka ta fashe da, batason tuna abunda suka faru a baya sam saboda yin hakan tamkar tana fame ciwon dake dunk'ule a zuciyarta neh

"Mr Omair don Allah, find a place in your heart and forgive this sister of yours, wallahi nasan idan har baka yafemin bah bazan tab'a fita daga k'uncin da zuciyata ke ciki bah, ba don ni bah, ka duba condition d'ina ka yafemin and I promise you, haka ba zai sake faruwa bah."

Shiru tayi ta k'ura mishi idanu, shi d'in ma ita yake kallon, maganganunta sun matuk'ar karya mishi zuciya amma ya kasa furta komai, kamar statue aka ajiye a wurin, tasowa Sahr tayi ta k'arisa wajenshi, kamar wani k'aramin yaro ta ja hannunshi yana biye da ita har zuwa bakin gadon tukun ta sakeshi ta zauna. Nailah ce ta mik'e a hankali ta dafa kafad'anshi tace

"Ya Khulayd na san kana da k'yak'k'yawan zuciya, bai kamata a ce ana abu d'aya tuntuni bah, we all know cewa Neenah bata yi dai-dai bah but, mahaliccin mu ma mukan masa laifi, wani abun ma ko kare ba zai shunshuna ba amma haka zai yafe mana saboda mu samu rabo ranar kiyama, toh idan har Allah zai yafe mana laifukanmu su waye mu y'an Adam da ba zamu yafe wa waninmu bah? Please brother forgive her not for her sake, but for Allah's, for Mami, for Uncle, for me and for your precious kid sister,please."

Yanzu kam ba zai tab'a iya k'in yafe mata bah, not after ta ambaci Allah da kuma sunayen mutane mafi soyuwa a wurinshi, ciro handkerchief yayi daga aljihunshi ya share zufan da ya k'eto mishi, a sanyaye yace

"Na yafe mata, Allah ya yafe mana baki d'aya"

Cike da farin ciki suka amsa da "Ameen"

Dirowa Sahr tayi daga saman gadon, flask na kunun ta d'auko ta sake dawowa wurin gadon tace

"Adda Neenah mun kad'a maki fav kununki, zaki sha?"

Gyad'a kai ta shiga yi tana fare hawayenta, jinta take yi kamar sabuwar mutum as she's so overwhelmed, bud'e flask d'in Sahr tayi ta d'ebo kunun a cup, dama sun dafa da sugar don haka cokali kawai ta jefa a ciki, matsowa kusa da Neenah tayi tace

"Yau ni zan baki a baki"

D'ebo kunun tayi a cokalin ta kai bakin Neenah tana "aaaa", da murmushi Neenah ta bud'e bakinta tana karb'a har tasha rabin cup din tace ta k'oshi

"A'a baki k'oshi bah, sai fa kin shanye, bari kiga na baki" cewar Khulayd, haka yayi ta bata har ta shanye tas, da handkerchief d'inshi yayi amfani ya goge mata bakinta, dad'i sosai Mr Abeed yaji seeing the family united once again, bayan an k'irawo Mami neh Mr Abeed yace

"Labari mai dad'i zan fad'a muku, next week insha Allah zamu tafi neman auren Sahr a wurin dangin mahaifinta, sam banaso bikin ya wuce wata d'aya"

A bazata maganar yazo wa Khulayd, babu shiri ya rungume Papanshi very tight, Sahr kuma mik'ewa tayi ta fice daga d'akin da tsananin kunya, a zuciyarta kuwa this is d best news she has ever received.

Posted on. Tuesday Date. 24th April, 2918 Time. 10:30pm Written by. Seemby luff😘

© *SEEMBY LUFF* 😘 ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜

Written by *Seemby luff*😘 Page *70*⚜

Tun daga wannan lokacin wasan b'uya ya fara tsakanin Sahr da Khulayd, sam bata so su had'u, wani masifar kunyanshi ta tsiri ji, duk inda taje kuma tasan zasu had'u tana matukar k'ok'ari taga ta guje wa haka, gaba d'aya yabi ya tada hankalinsa, ji yakeyi kamar zuciyarsa ya daina bugawa saboda rashin ganinta, ba wai ma kawai ya ganta bah, yanaso su tattauna muhimman abubuwa game da aurensu tunda yaga kamar Mr Abeed baison a d'auki tsawon lokaci, duk yabi ya canza, he isn't his normal self, idan ka gansa zaka san tabbas ak'wai abunda ke damunsa a zuci. A hankali ya turo k'ofan d'akin ya shigo da sallama a bakinsa, kamar dama ba son shigowan yake yi bah don a zatonsa ko da ya shigo bazai ganta bah, tana zuba kunu a cup don Neenah ta buk'ata, yi tayi kamar bataji shigowansa ba bare kuma ta amsa sallamarsa, still tayi a wurin ta k'asa juyowa don batayi tsammanin zai shigo yanzu bah, runtse ido tayi sosai, zuciyarta kuma ya fara bugawa kaman zai b'alle k'irjin ya fito. Tun shigowarsa idonsa ya sauk'a a kanta, nan da nan zuciyarsa data daina bugawa ta fara harb'awa, ganin ta k'i juyowa yasan bataso ya sameta a nan ba, duba d'akin ya shiga yi ya hango Mami can lungu tana laziminta, Neenah kuma shiru tayi a kan gadon da idonta a lumshe, rai a d'an b'ace ya k'arasa daf bayanta ya tsaya, tsananta bugu zuciyarta yayi don she can feel him very closed to her, rawa hannunta keyi lokacin da take k'ok'arin gauraya kunun da tea spoon, kamo hannunta yayi cikin zafin nama ya juyo da ita har ta kusa fad'i kasa ta saki y'ar k'asa "Auuuchh, Ya Khulayd zan fad'i fah" Ko a jikinshi abunda ta fad'a, kallonta ya shiga yi daga sama zuwa k'asa, sannan daga k'asa zuwa sama, sunkuyar da kai tayi duk jikinta na rawa, tasan zuwa yanzu tayi punishing nashi to the highest order tunda kwana uku tayi tana b'oye masa, cikin tsananin fushi yace

"Precious look at me" ya d'ago hab'arta da k'arfi ba tare da ya damu da ko zataji ciwo bah, runtse idonta tayi bata sake ta kalleshi bah

"Ki fad'amin dalilin da yasa haka kawai ki tsiri wasan b'uya dani, even after knowing how much am going to suffer without seeing u, haba precious, bak'ya tunanin cewa kwanaki uku sun min yawa? Just tell me idan bak'ya son auren ne coz na lura tunda Papa ya ambaci 'aure' kika fara guduna... Tell me, are you giving up on us?"

Sai mutsu-mutsu take yi tunda ya rik'eta, tambayar da yayi neh yazo mata a bazata, wannan wace irin magana ce, sosai taji babu dad'i, bud'e baki tayi da nufin magana, Mr Abeed ya turo k'ofan yana magana a waya, ganin irin rik'on da Khulayd yayi mata yasa ya sauk'e wayan da sauri ya k'araso wajensu, janyeta yayi daga rik'on yana "Have you gone crazy, so kake ka b'allata ne da irin rik'on nan? Nifa ban fahimceka ba, haka zakayi idan an muku auren? I've been observing you, you ain't nice to her sam sam, wai meke faruwa ne?"

Ja da baya Khulayd yayi ya rungume hannu a k'irji, ita kuma still tayi a wurin da kanta a sunkuye tana hawaye

"Papa, ita zaka tambaya ba ni bah, ta fad'a maka meye nayi mata take avoiding d'ina tun ranar da ka ambaci aure, bata tunanin halin dana shiga na rashin ganinta ne? Idan auren ne bataso fyn, ni sai in nemi wata in aura ai" ya k'are maganan kamar zaiyi hawaye, idanunsa sun kad'a sunyi jajur. Sheshshek'ar kukanta neh kawai ke tashi ta k'asa cewa komai, sai bata baki Mr Abeed yake yi amma tak'i yin shiru, Mami kam ko a jikinta, laziminta take yi hankali kwance ko kallon inda suke bata yi bah, tausayi sosai ta bawa Neenah yasa a hankali ta bud'e idanunta tace "baby sis" kamar dama jira takeyi ta ambaci sunanta, da gudu ta k'arasa ta haye kan gadon, ta zube jikin Neenah tana kuka tama manta da cewa jinya take yi, rarrashinta Neenah ta shiga yi tana bata baki, da k'yar ta samu tayi shiru. Shiru shima Khulayd d'in yayi daga tsayen da yake, yanzu kam ta tada masa hankali da kukan da take yi, sai dai b'acin ranshi ya hanashi yi mata magana, sosai b'uyan da take mishi ya dameshi, har ya fara tunanin ko wani abun yayi mata yasa take haka, tab'e bakinshi yayi ya kawar da fuskarshi daga b'angarensu, har ya fara yin zurfi a tunani muryan Papanshi ya dawo dashi

"Ba sai ka auri wata d'in mu gani bah, ai dai ba kai zaka d'aura wa kanka auren bah?, aure da y'ar auta kam babu fashi"

Dariya sosai maganar ya bashi, girgiza kai kawai ya shiga yi ya fita waje yana dariya.

K'wanakinsu uku a asibitin Neenah ta d'aga musu hankali, wai ita ta gaji da zaman asibiti tana son komawa gidah, babu yanda likitan ya iya, dole ya basu sallama ganin yanda duk suke kula da ita, sam basa barinta da damuwa bare har ta d'aga hankalinta, suna matuk'ar k'ok'arin sata farin ciki da kuma mantar da ita abunda ya faru har ta kammala 3 days treatment d'inta, tattarawa suka yi suka koma gida akan yarjejeniyan cewa zata ke zuwa checkups after every 1week. Horn sukayi a bakin gate Maigadi ya bud'e, har k'ofan shiga parlor driver'n yayi parking, Mr Abeed da Mami neh suka fito kusan a tare, da sauri ya zagayo b'angaren Mami don ya tayata su fito da Neenah, a hankali suka kwasheta da nufin shiga da ita, turus suka tsaya suna kallon abun mamaki

*WELCOME BACK HOME NEENAH* suka gani a rubuce jikin k'ofan parlor'n, anyi decorating da flowers da balloons masu kyau, Nailah da Sahr ne suka fito daga cikin parlor'n cike da murna, kusan a tare suka ce "Welcome back home sis" murmushi kawai Neenah ta saki, hawaye suka fara bin kuncinta, gaba d'aya farin ciki ya baibayeta ta rasa yadda zatayi expressing, cike da jin dad'i Mami da Mr Abeed suka kinkimeta, sai ji suka yi Khulayd yace "Not so fast aunt, ai baku ga tawa bazatar bah" da sauri ya shige ciki, jim kad'an ya fito da wheelchair modern mai tafiya da kanshi, "Surprise" ya fad'a yana dariya, toshe baki Neenah tayi kawai tana hawaye, bata tab'a tsammanin haka a wurin Khulayd bah, bama ita kad'ai bah, dukkansu sai da sukayi mamakin wannan k'yautan, k'arasawa yayi da taimakon Papanshi suka d'aurata akan kujeran, matsa wani button Khulayd yayi kawai kujeran ya fara tafiya da kanshi, rungumeshi Mami tayi speechless "Allah yayi maka albarka Son, may u always be successful in life" ta fad'a tana bubbuga bayanshi, "Ameen sweet aunt" ya amsa lokacin da yake k'ok'arin breaking hug d'in, da sauri yabi bayan Neenah don har ta kusa kaiwa gate, she was very happy har ta k'asa controlling kujeran, tsayar da ita yayi ta hanyar rik'e kujeran sannan ya sake pressing wani button, sunkuyawa yayi yana kallonta yace "You like it?" G'yada kai ta shiga yi ta kasa b'oye farin cikinta tace "I love it Mr Omair, thank you very m....." Bai bari ta k'arisa ba yace "Shhhh! We'll have a serious fight duk lokacin da nayi miki abu kika sake godemin, am your brother so bana buk'atar godiyanki,,, one more thing, kar ki sake cemin Mr Omair, call me Ya Khulayd kamar yadda kowa ke k'irana, kinji?" G'yad'a kai tayi tace "naji, Ya Khulayd" duk sukayi dariya, nuna mata buttons d'in ya shiga yi har sai da ya tabbatar ta gane tsab tukun yace "Jeki wajen su Aunt toh" Kamar yadda ya nuna mata haka tayi, tana zuwa wajensu Mami tayi pressing button d'in aiko sai kujeran ya tsaya, da murmushi ya k'araso wajensu ya tsaya yana kallonta, bayan hannunta tasa ta share hawayen dake zubo mata babu dalili, k'iransu da hannunta ta shiga yi tana "Come give me a hug" da gudu Nailah da Sahr suka rungumeta suna dariya, karyar da wuya Khulayd yayi kamar zaiyi kuka yace "Ni banda ni koh sis?" Kamar dama jira takeyi ya fad'i haka, bud'e mishi hannunta tayi ta inda ta rungumi Sahr, a hankali ya taho ya rik'eta, ta mayar da hannun ta rufe.

_2 weeks later_❤

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull