Sahr khulaiyd complete - Chapter 18
Sahr khulaiyd complete Chapter 18: Sahr khulaiyd complete Chapter 18. K'arfe tara da rabi, Mami da k'awarta, Khulayd, Mr Abeed da wasu abokanshi guda biyar…
4,483 words
K'arfe tara da rabi, Mami da k'awarta, Khulayd, Mr Abeed da wasu abokanshi guda biyar suka kama hanyar garin mahaifinsu Sahr, dama tuni Mami ta k'ira ta sanar dasu zuwan da zasu yi, dalilin zuwan Mami kuwa shine ta sanar dasu baki da baki gudun fitinarsu, su kuma Mr Abeed da tawagarsa zasu neman auren Sahr ne. K'arfe 2 dai-dai suka shiga cikin garin, direct kofar gidan suka yi parking suka sauk'a. A nan zauren gidan aka tarb'i su Khulayd, ita kuma Mami da k'awarta suka wuce cikin gidah, bayan y'an gaishe-gaishe Mami tace "Dama gani nayi ya dace in zo da kaina in sanar daku maganan auren nan" daga nan tayi musu bayani cewa d'an yayanta ne ke son auren Sahr, wata daga cikin k'annen mahaifinsu Sahr d'in tace "Ashe dai da sauran mutuncinmu a idonki, ashe dai muna da amfani? Ai ca nake tunda kin kwace y'ay'a kin girmar, haka zaki d'aura musu aure ba tare da dangin ubansu bah" "Kinci gidanku, wannan wace irin magana ce?" Cewar wata dattijuwa dake zaune kusa da Mami, da ganinta kasan ak'wai alakar jini tsakaninta dasu Sahr saoda suna mugun kama "Inna ai gaskiya na fad'a" cewar wannan matar, wacce aka k'ira da Inna tace "Yimin shiru mutuniyar banza, kar na sake jin kin bud'e bakinki a nan", ita dai Mami batace dasu komai bah, sai bin duk wanda ya tofa albarkacin bakinshi kawai take yi da kallo.
A b'angaren su Mr Abeed kuwa, bayan sun kammala gaisuwa suka bayyana dalilin zuwansu, sosai suka samu k'arb'uwa a wajen y'an uwan mahaifin Sahr, tun ba ma da Mr Abeed ya sanar dasu cewa d'anshi ne ke son auren, "Aaa Allah shi sa albarka, ai wannan lamari yayi kyau, wato kun san shi aure ana buk'atar bincike da makamantan haka, amma tunda yazo mana gidan sauki Alhamdulillah, babu bukatan a tsawwala abu, inda sadaki sai a biya kuma a sa rana, kunga kun ragewa kanku tafiya biyu" cewar wani da aka k'ira da Malam Sa'eed. Sosai Mr Abeed ya ji dad'in maganan Malam Sa'eed, dama shima hakan yake so ayi, negotiating akayi kan kud'in sadakin, Khulayd a aljihunshi ya ciro dubu d'ari biyu, nan yayi wa Papanshi magana a kunne, ajiye kud'in Mr Abeed yayi a gaban Malam Sa'eed yace "Ga dubu d'ari nan kamar yadda kuka buk'ata, wannan kuma a sai goro" "Toh, ayi haka kuwa? Kai Allah shi sa albarka" cewar Malam Sa'eed, karaf ya kwashe kud'in ya watsa a aljihunsa, bayan sun kammala ne Khulayd ya k'ira Mami ya sanar da ita cewa sun gama, sannan yace su fito su kama hanya don yamma tayi. A mota neh Khulayd ke sanar da Mami abunda ya wakana, shiru tayi kawai tana jinjina lamarin, a ce kud'in sadakin yarinya zasu karb'a su sa a aljihu? D'aukan waya Khulayd yayi ya shiga message, ya fara typing sak'o. Sahr na zaune bakin gado, fitowanta daga wanka kenan taji sak'o ya shigo wayarta, tana ganin 'Jaan' har jikinta rawa yake yi ta bud'e sak'on, tun bayan fushin da yayi mata akan b'oye mishi da take yi bai sake kulata bah, bud'e content d'in sak'on tayi, a hankali ta fara karantawa
" _Precious_ _guess what? Yau na biya sadakinki and you'll be mine soonest, in the next two months_ _I love you so much_ ❤"
Wani ihu ta saki out of happiness ta rungume wayan a kirjinta, sai yanzu tasan dalilin tafiyarsu Mami, dama ce masu suka yi zasuyi wata y'ar karamar tafiya neh, d'ago wayan tayi ta sumbata idanunta a lumshe tace "Am looking forward to seeing that day, I love you more Ya Khulayd d'ina.
© *SEEMBY LUFF* 😘 *SAHR-KHULAYD* written by *Seemby luff* 😘 Page *71*
*Wannan shafin naki neh matar Yusleem (Miss Xoxo)* Thank you for everything, I heart you irin sosai d'innan ❤❤❤❤❤
Sai kusan 6pm suka shigo gari, bayan Khulayd yayi parking, a gajiye Mami da Mr Abeed suka shigo parlor, babu wanda ya tsaya neman abinci duk da cewa yunwan suke ji, d'aki kawai kowannensu ya nufa don watsa ruwa. Tunda taji horn daga gate ta daka tsalle daga saman gado ta diro kasa, gashin kanta duk a barbaje bata yi combing ba ta d'auki y'ar karamar gyale kawai ta rufa, da gudu-gudu ta fito daga d'akinta ta nufi stairs har ta kusa bangaje Mami dake zuwa d'akinta a gajiye, "Mamina ahlan, sannu da dawowa" kawai ta fad'a ta cigaba da sauk'owanta, tsayawa tayi a bakin kofan parlor'n inda ta tabbatar in ya shigo zai ganta, rungume hannu a k'irji tayi tana murmushinta mai kyau. Sai da Khulayd ya tsaya locking na motan tukun ya kamo hanyan shigowa, rik'e yake da car key yana wak'a yana spinning car key a iska, zuwa yayi zai shige parlor ya ganta tsaye tana ta faman murmushi, kaman tunda yake bai tab'a ganin mai kama da ita ba haka yayi, shareta yayi kaman ma bai lura da murmushinta bah ya cigaba da tafiyarshi, mamaki sosai Sahr taji, irin wannan shariya haka kaman ba shine ya tura mata da sak'o d'azu bah, da gudu tabi bayanshi tana "Jaan". Kusan sau uku ta k'irashi amma yak'i kulata, banza yayi da ita kaman baisan shi take k'ira da suna Jaan ba, sai spinning car key kawai yake yi yana tafiyarshi har ya kai stairs, shan gabanshi tayi ta rik'e dukka sides na stairs d'in kaman hannunta zai b'alle, tana kallonshi tace
"Jaan, da kai fa nake magana tun d'azu, why are you ignoring me all of a sudden?"
D'agowa yayi yana kallonta daga sama zuwa kasa, had'e rai yayi sosai, fuskan nan babu annuri kwata-kwata yace
"Ki matsar min a hanya na wuce, as you can see na gaji sosai and I need to go freshen up"
Sake k'ank'ame karfen stairs d'in tayi tana murgud'a bakinta "Not until ka fad'amin me yasa ka k'i kulani haka nan, nayi maka wani laifi ne?"
Wannan karon babu yabo babu fallasa fuskarshi ya dubeta, yace "Haka kawai naga dama fah y'an mata, ko bani da freedom ne kuma yanzu? Get out of my way please"
Narai-narai tayi da idanu, kafin kiftawar ido tuni hawaye sun fara wanke mata fuska, nan ta rushe mishi da kuka kuma tak'i matsa masa a hanya ya wuce, sai zuba hawayen keyi kaman an bud'e famfo, kawar da kanshi yayi gefe don ta bashi tausayi sosai, jin kukanta yake yi can kasan zuciyarshi amma he isn't ready to give up just yet, a hankali ya d'aura hannunshi a saman nata da nufin d'aukewa, daga shi har ita sai da suka feeling wani electrification, basarwa Khulayd yayi kamar bai ji ba ya d'auke hannun nata daga kan karfen stairs d'in, bata wani k'ok'arin hanashi ba saboda wani kasalan da ya sauk'ar mata, janye jiki tayi gefe guda, shi kuma yayi wucewarshi ko kallonta bai sake yi bah, sunkuyawa tayi a nan gurin ta rungume jikin stairs d'in tana kukanta sheshsheka, sai da tayi mai isanta tukun ta mik'e ta wuce d'akinta.
Yana shiga d'aki, gaban mirror ya nufa ya ajiye makullin motan dake hannunshi da waya, undressing kanshi yayi daga shi sai gajeren wando da singlet ya zauna bakin gado, ciwo kanshi keyi saboda hanyan sam babu dad'i, gargada yayi yawa kuma shi bai saba bin irin wannan hanyan bah, dafe kanshi yayi da dukka hannayenshi biyu ya lumshe ido, ita yake gani lokacin da ta rushe mishi da kuka, murmushi ne ya sub'uce mishi yana girgiza kai, a fili yace
"Crying crying precious, can't wait to have u all for myself" A nan inda yake zaune, idanunshi a lumshe ya fara imagination, wai gashi ga Sahr akan gado d'aya, a farkon daren aurensu, mik'ewa yayi da sauri kamar an mintsileshi ganin zai b'ata lokacinshi akan wani imagination, fad'awa toilet yayi ya sakar wa kanshi shower, still yayi a karkashin shiwer'n yaayin da ruwan ke sauk'a tun daga saman kanshi har tafin kafanshi, ya d'au lokaci a haka tukun ya tsala wanka sannan ya d'auro alwala, fitowa yayi d'aure da towel a k'ugunshi, yana towel drying suman kanshi da d'an k'aramin towel, gaban mirror ya nufa ya shafe kanshi da hair creams d'inshi sannan yayi combing, bai damu da ya shafa mai a jikinshi ba saboda yanayi na zafi da ake ciki, perfumes d'inshi kawai yayi spraying all over sai dad'ad'an kamshi ke tafi na turaruka daban-daban, wardrobe ya nufa ya ciro jallabiya mara nauyi ya zura sannan ya d'auko darduma a saman side drawer ya shimfid'a, ya tada kabbaran sallah. Asr da yayi missing saboda suna kan hanya ya fara gabatarwa, sannan ya mik'e ya gabatar da Magrib, ya d'auki tsawon lokaci zaune kan darduman kafin daga bisani ya mik'e, gaban mirror ya nufa ya d'au wayanshi ya fito. Hayaniyansu daya ji a dinning area ne ya tabbatar mishi cewa duk suna wurin, kai tsaye shima dinning area ya nufa ya gansu duk a zazzaune, kujeran dake kusa da na Mami ya ja ya zauna yana ta shan k'amshi, fuskarshi sam babu annuri, shafa gefen fuskarshi Mami tayi tace
"Yaya dai son naga duk baka walwala? Duk gajyan ne or is something bothering you?"
Murmushi yayi, kamar baison magana yace
"Babu komai fa aunt, kaina ke ciwo but nasha magani, I'll soon be okay."
Sahr ce tayi serving abinci yau, a hankali take bin plate na kowa tana zuba abinci, plate na Khulayd shine k'arshen wanda ta zuba abinci, tana zubawa tana kallonshi da tausayinshi fal zuciyarta tunda yace kanshi na ciwo, gaba d'aya hankalinta baya kan abunda take yi, batayi aune bah sai ji tayi serving spoon dake hannunta ya sub'uce ya fad'i kasa, da sauri taje kasa itama da nufin d'aukowa, ta kai hannunta kenan shima Khulayd ya kai nashi da nufin d'ago mata dashi, karaf ya rik'e hannunta instead of serving spoon d'in, kusan a tare suka d'ago suna kallon juna with so much love ne passion, sun dad'e a haka kuma yak'i sake mata hannu, hawaye ya gani suna zubowa daga idanunta suna gangarowa kan kumatunta, bai san lokacin da ya saki hannunta ba, sai ji tayi yana share mata hawayen shima kamar zaiyi k'walla, yana share hawayen wasu suna zubowa, d'ago hab'arta yayi yana kallonta, idonta da hawayen itama take kallonshi, tab'e baki yayi ya turoshi kamar yadda yara sukeyi idan suna son yin kuka, girgiza mata kai ya shiga yi alamar ta daina, a hankali yayi whispering mata
"Am sorry precious"
Murmushi neh ya sub'uce mata bata san lokacin bah, da kanta ta shiga share hawayen tana jan hanci tace
"Am sorry too Jaan"
"Ki share hawayenki, kinsan I hate to see your tears... Am always here for you okay?"
G'yad'a mishi kai ta shiga yi tana jin dad'i sosai, basuyi aune bah sai jin muryan Mami sukayi tana cewa
"Wai ni me kukeyi neh tun d'azu haka? Wani serving spoon d'in kuke k'erawa ne? don naga kamar d'ago wannan na baku matsala"
Da sauri Sahr ta d'auki serving spoon d'in ta mik'e, wani ta d'auko ta cigaba da zuba mishi abincin dashi.
Koda suka kammala dinner'n, Mami, Mr Abeed, Neenah da Nailah duk suka d'unguma zuwa parlor, Khulayd da Sahr kam suna nan zaune wai da sunan suna cin abinci, sai juya cokali kawai suke yi suna cakud'a abincin, kusan a tare suka ture plates d'insu, tura kujera Khulayd yayi zuwa baya ya mik'e da nufin komawa parlor shima, da sauri ta kamo hannunshi ya juyo yana kallonta, girgiza kanta take yi tace
"Kar ka tafi please Jaan, stay for my sake, ban gaji da kallonka ba"
Bai ce da ita komai bah, ya koma ya zauna kawai, tagumi tayi da both hannayenta tana kallonshi, tsawon mintuna biyu tayi tukun tace
"Jaan, ka dad'e baka ce kana sona bah, its been long, ka fad'a inji don Allah"
"Precious wallahi ak'waiki da son rigima, kin san fa koda ban fad'a bah you know I do, with the whole of my heart"
Mik'ewa tayi ta fara bubbuga kafafunta a kasa, tana
"Umm umm, nikam banason wayo, I just want to hear u say it, please Jaan"
Ta karashe maganan kamar zatayi kuka, ganin da gaske take fa kukan zatayi don ya santa sarai, akan k'ank'anin abu yanzu sai ta fashe mishi da kuka, bai san lokacin da yace
"Ina sonki precious, I love you irin sosai d'innan" bah
Kawai sai gani yayi ta fashe da dariya, har da y'ar tsallenta, kallonta kawai yake yi baki bud'e babu ko kiftawa, shi dai duk abunda tayi yana burgeshi, jin sonta yake yi yana ratsa jini da b'argonshi, a fili kuwa yace
"Drama Queen."
© *SEEMBY LUFF* 😘 ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff* ⚜ Page *72* ⚜
Ashe daya ce mata 'Drama queen' taji duk da cewa k'asa-k'asa ya fad'a, sake turo baki gaba tayi ta b'ata fuska kamar ba ita ke dariya yanzu bah, rungume hannu a k'irji tayi taje chan kusurwan dinning arean ta tsaya tana son fara kuka, kallonta yake yi duk wani movement d'inta da mamaki, shi dai baisan meye yayi mata yanzu na b'acin rai bah. Mik'ewa yayi daga kan kujeran tare da fusgar ta iska yana girgiza kai, a zuciyarshi kuwa cewa yake "What have I done wrong kuma yanzu?" A hankali yake tattaki har ya isa kusa da ita ya tsaya, k'wata-k'wata ratan dake tsakaninsu bai wuce inci biyu bah, rungume hannu a k'irji shima yayi kamar yadda yaga tayi, sun d'au kusan 2 minutes a haka kafin ya lang'wab'ar da kai, yace
"What now kuma baby doll?, yanzun nan fah kike fara'a kina dariya, me kuma ya faru kika dawo nan kika tsaya looking very upset? Menene y'ar matata?"
Juyawa tayi kamar zata shige bangon tana k'ok'arin k'irk'iro kuka, sakata yayi a tsakiya ya dafe bango da duk hannayenshi biyu, sauk'an numfashinshi a gadon bayanta neh yasata juyowa tana kallonshi da siraran hawaye a kowani gefen kumatunta, k'ura mata idanu yayi yanason ba sai ya sake maimaita tambayar da yayi mata bah, banza dashi tayi ta sadda kanta kasa, d'ago hab'arta yayi slowly yana kallon cikin idonta yace
"Kinsan Allah precious, in baki fad'amin meye ya sameki kika canza da wuri haka bah, am going to make sure na shanye lips nakin nan tas, kinga sai ya k'ara tsawo tunda dama hakan kike so, mutum sai shegen tura baki"
Zuciyarta ke skipping da sauri-sauri don kusancin dake tsakaninsu, juyowan da tayi a saitin fuskarshi take tsaye kuma yanzu numfashinshi a kan k'irjinta yake sauk'a, d'agowa tayi ta dubeshi taga babu alamar wasa a fuskarshi, tsab zai aikata abunda ya fad'a don tasan ba kunya neh dashi bah, dama kuma ta lura yana neman abunda zai sa ya tab'ata, sake shagwab'ewa tayi tace
"Toh ba kai bane ka cemin drama queen?"
Dariya ma abin ya bashi, da kyar ya iya gimtse dariyan don kada ta k'ara yin fushi
"Precious, Toh me don na k'iraki drama queen? Ain't you a drama queen? My drama queen, nifa ban fad'a da wata manufa bah, kawai komai naki kyau yake min precious, bana tab'a ganin aibun abunda kikeyi, I love just everything about you"
D'agowa ta sake yi a karo na biyu ta kalleshi, kashe mata ido yayi yana murmushi tare da d'aga mata gira, dariya ne ya sub'uce mata, a hankali ta kai mishi duka tace
"Nikam bari na wuce"
K'in barinta yayi ta wuce yana mata wani mayataccen kallo, sama zuwa k'asa, to and fro, a hankali taga ya fara kawo fuskanshi kusa da nata, runtse ido tayi kamar wacce za'a yanka ko k'wak'k'waran motsi bata yi, sai data bari ta fara jin sauk'an numfashinshi akan hancinta da idanunshi a lumshe, zillewa tayi ta k'arkashin hannunshi tana mishi dariya, d'agowa yayi da idanunshi da suka kad'a sukayi ja ya juyo yana kallonta, gwalo ta shiga mishi taga inda take tana ta faman dariya, cikin wani kasalallen murya yace
"Precious please"
Tausayi sosai ya bata, sai dai bata jin zata iya barinshi ya sumbaceta haka nan, girgiza mishi kai ta shiga yi tana
"Um um Jaan, Allah bazan barka bah, its only 2 months remaining, your kiss can wait" tana gama fad'in haka ta wuce cikin parlor abunta, dafe kanshi yayi ya kasa koda motsawa, still yayi a wurin har sai da ya gaji da tsayuwa don kanshi, a wahale shima ya dawo cikin parlor ya zauna, sai kallonta yake yi yana cizar leb'e, ita ko kamar bata san yana yi bah, wayanshi ya ciro daga aljihu yayi unlocking, wani short message yayi typing ya tura mata. K'aran shigowan sak'o ne yasa ta dubi wayanta, sunan data sanya mishi ta gani a rubuce, sai data dubeshi tukun ta bud'e sak'on tana karantawa
" _Only two months remaining kika ce koh? And that my kiss can wait ba? Hmm precious, I promise you sai na baki mamaki a wancan daren, you have my word_"
Sai da taji gabanta ya fad'i da kalamunshi, d'agowa ta sake yi ta kalleshi taga yana g'yad'a mata kai alamun da gaske yake, da sauri ta sadda kanta k'asa tana data sanin maganan da tayi.
_A month later_ ❤
Zauneh take a kan stool dake gaban mirror tana shafa cream, fitowanta daga wanka kenan take shafa man bayan tayi drying gashinta da hand dryer, mik'ewa tayi bayan ta gama shafan da nufin d'auko kaya a wardrobe, wayanta dake ajiye kan gado ya fara ruri, da sauri ta k'araso bakin gadon ta d'ago wayan tana kallon screen d'in, murmushi tayi kafin tayi picking ta kara a kunnenta, bai bari tace komai bama yace
"Ina jiranki a mota, ki fito zaki yimin rakiya"
"Jaan, ina kuma zamuje da tsakar ranan nan?"
"Inner wears d'inki zamu je in siyo, am taking you with me saboda bansan sizes naki bah"
Kunya sosai taji da yace inner wears, har rufe fuskarta tayi kamar yana gabanta, zama tayi a bakin gado tukun tace
"Umm umm Jaan, nikam bazani bah gaskiya, I can't go"
"Ki fad'amin sizes d'in toh tunda bazaki je bah, ko dai inzo in gwada da kaina neh precious na, kamar hakan zai fi ko?"
Babu shiri tace "Noooo, Allah Ya Khulayd ka bari, zan sending maka a waya" bata jira cewarshi ba ta katse wayan tana dariya, girgiza kanta ta shiga yi tana jinjina k'arfin halin Khulayd, sak'on ta tura mishi kafin daga bisani ta koma gaban mirror ta gama shafanta, zani da riga ta ciro a wardrobe ta saka, ko powder bata shafa bah ta d'aura kanta simple, tana saka d'ankunne landline na d'akin ya hau ruri, da kyar ma take tafiya da zanin kamar zata fad'i kasa ta k'arasa, d'agawa tayi ta k'ara a kunnenta taji muryan Mami tana cewa ta sameta a d'aki yanzu, tana ajiye wayan ta d'au d'ayan d'ankunnen da bata sakan bah ta fice zuwa d'akin Mami.
Da sallamarta ta bud'e d'akin ta shiga, zaune taga Mami a bakin gado tana duba wasu sets na diamond earrings, zuwa tayi ta zauna kasa sannan ta d'aura kanta a kafan Mami, babu yanda Mami ta iya dole ta bar abunda takeyi ta ajiye gefe guda, shafa kan Sahr d'in ta farayi tace "little princess ba zaki bar d'abi'arki na son jiki ba koh, kina gani fah ina aiki kika wani zo kika kwantar min a kafa" murmushi tayi ta d'ago tana kallon Mami tace "Mami toh meye? Wata d'aya fa ya rage min a gidannan, am gonna miss u all Allah Mami", Mami tace "Yawwa, that reminds me, zaki tafi Maiduguri in 3 days time, kin tuna kawata Hajiya Innah?"
Gyad'a kanta tayi tana tunanin me kuma zai kaita Maiduguri,
"Gyaran jikinki zakije yi don tayi insisting sai an kaiki,...."
Zata sake yin magana Khulayd ya turo k'ofan ya shigo, Sahr bata damu da ta d'aga kanta a kafan Mami bah, k'arasowa yayi ya zaunah a kasa shima, d'aura kafanta yayi shima a d'ayan b'angaren kafan Mami yana kallon precious d'inshi, yace
"Aunt, meye kike tattaunawa da surikarki kuma barni baku gayyaceni bah?"
D'aura hannunta tayi a saman kanshi shima, tana murmushi tace
"My dear son, wai fah ina koya mata yanda zata kularmin da son d'ina neh"
Ta kasan kafan Mami ya mik'owa Sahr hannu, taking hannunshi tayi suka rike juna gam, a lokaci guda suna exchanging love looks❤
"Really aunt?" Cewar Khulayd
"Sosai kuwa son, kasan ina sonka sosai"
Heart talking suka fara yi, Sahr tace
"Jaan, am going to miss u sosai Allah, zuciyata bugawa takeyi idan na tuna zan tafi in barka har tsawon kwana uku, my heart will not endure it gaskiya"
"Me kike nufi precious, ina zaki je kike wannan maganan?"
"Maiduguri, wai zani gyaran jiki" tayi saurin b'oye fuskanta a kafan Mami
"Then we are going together" ya bata amsa a takaice.
© *SEEMBY LUFF* 😘 [5/13, 1:52 PM] +234 706 824 7860: ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff* ⚜ Page *73* ⚜
"Kuje ina d'in tare son?" Suka tsinkayo muryan Mami tana tambaya, shi kanshi Khulayd d'in bai san maganarshi na karshen ya fito fili bah, sosa keya yayi yana dariya k'asa-k'asa yace "Aunt, nifa bance komai bah, I was just thinking maybe mu tafi Maidugurin tare neh coz I heard cewa hanyan garin babu kyau sam, kuma ai babu dad'i ta tafi ita kad'ai, she's still a baby fah" hararanshi Mami tayi sannan tasa hannu ta zunguri keyanshi tace "Shine don rashin kunya kake son rakata? Nifa na rasa meyasa ku y'ay'an zamani baku da kunya, toh shikenan sai in barka ka rakata gidan matan aure hakanan? Ina ce gyaran jikin don kai za'ayi? Toh naji, tunda she's still a baby sai a fasa auren har sai ta zama grown up yadda kake so" can k'asan mak'oshi yace "Ni dai a yadda take nake sonta, babu wani jiran da zanyi, wata d'ayan nan mah yai min nisa", bai yi aune bah yaji saukan duka a bayanshi, tsalle ya daka yana sosa bayan yana dariya, Mami tace "Zo ka fitar min a d'aki, mara kunyan banza", tana maganan tana nuna mishi k'ofa, babu yadda ya iya haka ya fice ba don yaso bah, kallon Sahr Mami tayi tace "Ke kuma ki rinka biye mishi yana mak'alk'ale miki kaman chewing gum kinji?", kunya sosai maganan ya baiwa Sahr, mik'ewa tayi ta bar d'akin da gudu tana rufe fuska, girgiza kai Mami tayi tace "Ku dai kuka sani, ni ayi ayi auren ma mu huta gaba d'aya", d'aukan d'ankunnayen tayi ta cigaba da dubasu. Ashe Khulayd bai koma d'aki bah, yana lab'e nan corridor yana jiran fitowanta, fitowa tayi da nufin komawa d'aki da murmushi d'auke a fuskanta, ji tayi an janyota an had'ata da bango, a tsorace ta dubeshi don batayi tsammanin yana nan bah, danneta yayi da iya karfinshi bata ko motsawa, yace "precious, its either mu tafi Maidugurin nan tare, ko kuma a fasa don bazan bari kiyi nesa dani ina gani bah, so its better u talk to aunt", b'ata fuska tayi sosai tana kallonshi tace "Wai nikam Ya Khulayd meye haka neh? U scared me sosai wallahi, wai ni sai ka rika tab'ani neh? Banason fa abunda kake yi sam", on a serious note take magana, still yayi yana kallonta da mamaki, yau precious ce take d'aga mishi murya?, basar da tunanin yayi don gudun kar ya biyewa zuciyarshi, "Precious, am sorry idan bakya son abunda nake miki, I know hakan ba dai-dai bane saidai bazan iya bah, idan na tab'aki at least ina samun ease a zuciyata, please understand me baby doll, please", da iya karfinta ta daddage ta turashi zata tafi, fisgota yayi ya sake manneta a jikin bangon yana wani shu'umin murmushi yace "not so fast baby doll, ai ban gama bah tukun" shiru yayi na d'an wani lokaci kafin yace "So nake in tabbatar da sizes na inners da kika turamin d'azu, ban yarda cewa sizes naki bane wad'ancan", d'agowa ta sake yi tana kallonshi, wannan karon ranta ya b'aci sosai, kasa cewa komai tayi kawai tana ta kallonshi kamar wata sok'uwa, d'aga mata gira yayi don ko a jikinshi b'acin ran da take yi, yasan kuma cewa da gaske ranta ya b'aci amma ya basar, a hankali yake tafiya da hannunshi a jikinta, yana zuwa chest d'inta ya tsaya kamar mai tunani, kai ya gyad'a kafin daga bisani ya je kan waist d'inta, baya taga ya koma ya rungume hannu a k'irji yana ta faman murmushi, "Its like fa sizes da kika turamin d'in dai-dai neh, ashe dai baby doll d'ina haka take?" Ya kare maganan yana kallonta kuma yana expecting ta bashi amsa, yanzu kam ta cika har wuya kamar zata fashe, wasu siraran hawaye neh suka zubo mata, bayan hannu tasa tana sharewa, a zuciye ta juya ta bar wurin, yadda tayi gaba d'aya ya bashi tsoro, bai san cewa ranta ya b'aci har haka bah, binta ya fara yi yana kiran sunanta tayi banza dashi, sai da ya had'a da gudu kafin ya isota, mik'a hannu yayi da nufin dafa kafad'arta, juyowa tayi tare da d'aga mishi hannu don tasan cewa dafatan zaiyi, "Don't touch me" ta fad'a mishi cikin b'acin rai ta cigaba da tafiyarta, still yayi a wurin yana kallonta har sai da ta b'ace da ganinshi. Tun daga wannan ranan bata sake bari ya sakata a idonshi bah, duk inda tasan zasu had'u toh bata zuwa wurin, Mami tayi tambayar duniya amma sai dai ta ce mata babu komai, Khulayd gaba d'aya hankalinshi ya tashi, duk k'ok'arinshi na ganin sai ya ganta ko ta halin k'ak'a abun yaci tura, zaune yake a d'akinshi ya rik'e kanshi dake ciwo tun safe, mik'ewa yayi kamar an mintsileshi ya fito ya nufi balconyn d'akinta, fitowanta kenan tana son zuwa d'akin Mami suka ci karo, duk su biyun tsayawa sukayi suna kallon junansu kamar su cinye, babu komai a k'wayoyin idanunsu banda kewar juna, sun d'au tsawon lokaci a haka kafin Sahr ta fara yin baya, kowani step datayi zuwa baya shi kuma Khulayd zaiyi zuwa gaba, tana kaiwa kofan d'akinta ta shige da sauri ta danna lock, jinginuwa tayi a jikin k'ofan zuciyanta na skipping da sauri-sauri, k'arasowa yayi bakin kofan ya murd'a yaji a rufe, a hankali shima ya jinginu da k'ofan yana bugawa, k'in bud'e mishi tayi tana jinshi kuma, d'aura kanshi yayi a jikin k'ofan yace "Precious, please ki bud'e k'ofan muyi magana, please", banza tayi dashi daga cikin d'akin itama ta d'aura kanta a jikin k'ofan, saitin inda Khulayd ya d'aura nashi, shiru tayi tana jinshi sai dai bata jin zatayi magana, "Precious am sorry for d other day, wallahi I didn't meant to hurt you, don Allah ki bud'e k'ofan nan" haka ya rinka pleading amma Sahr ta k'i bud'e mishi k'ofa kuma tak'i kulashi, sai da ya gaji don kanshi ya fusgar da iska mai zafi, a hankali yace "I love you precious" ya juya jiki babu k'wari ya bar wurin, d'aura hannunta tayi a kan k'ofan itama a hankali tace "I love you too Jaan", kamar yaji abunda ta fad'a ya juyo yana kallon kofan na d'an wani lokaci, murmushi yayi sannan ya juya ya cigaba da tafiyanshi.