Sahr khulaiyd complete - Chapter 19
Sahr khulaiyd complete Chapter 19: Sahr khulaiyd complete Chapter 19. K'arfe 3:00pm dai-dai Sahr ta kammala shirinta cikin Arabian gown mai d'an karen…
2,725 words
K'arfe 3:00pm dai-dai Sahr ta kammala shirinta cikin Arabian gown mai d'an karen kyau, rolling tayi da scarf din kayan ta d'auki hand bag d'inta ta mak'aleshi a hannunta, flat shoe ta saka na kamfanin Gucci don ita dama ba gwanar sa heel bace, k'arasowa tayi inda ta ajiye trolley d'inta ta jashi zuwa waje, sannan tayi locking d'akinta. Downstairs ta nufa sanin kowa na jiranta a can, a hankali take sauk'owanta har ta ida sauk'owan ta k'araso cikin parlorn, a kusa da Mami taje ta zauna tana kallonsu kamar tayi kuka, sanin halinta yasa Mami tace "Kinga princess karki ma fara yimin kuka a nan, mutum sai shegen kukan tsiya kamar wacce zataje inda za'a yankata? Ni dai abunda zan fad'a miki shine kiyi behaving, duk da nasan halinki princess but zama da mutum sai hakuri, its just a matter of some weeks zaki dawo gida, just take care of yourself kinji?" Ta kare maganar tare da d'ago hab'an Sahr d'in tana kallonta, hawayen da ya mak'ale mata ne ya fara zubowa, fad'awa tayi jikin Mami tana kukanta a hankali tace, " I'll miss you Mum" a hankali Mami ke bubbuga bayanta don itama sai datayi hawayen, k'arasowa Nailah tayi ta zauna kan hannun kujeran, d'ago Sahr tayi ta dawo da ita kan cinyarta tana bata baki, itama Neenah ta dawo kusa dasu duk suka rungumeta suna bata hak'uri. Kamar an biyoshi ya sauk'o downstairs d'in da mak'ullin mota a hannunshi, Mami tace "Ya dai son? Ya naga ka sauk'o kamar wanda aka biyo?", "Babu komai fah aunt, just want to take her to d airport don jirgin nata ma ya kusa tashi" ya k'are maganar yana duba agogon dake d'aure a wrist d'inshi, jan trolleyn yayi ya fice abunshi, sai da suka gama koke-kokensu tukun suka rakota inda Khulayd ke jiranta a mota, Mami da kanta ta bud'e mata kofa, sai da ta sake hugging d'inta tukun ta shiga motan, daga haka mai gadi ya wangale gate suka fice.
Babu wanda yayi wa junanshi magana a motan, da gudu sosai Khulayd ke driving, daka ganshi kasan baya tattare da nutsuwa, ganin speed d'in yayi yawa yasa Sahr saurin d'aura hannunta akan nashi dake kan steering, wani brake yaje a lokaci guda ya tsayar da motan, juyowa yayi yana kallonta yaga tana girgiza mishi kai alamun kar yayi gudu, cikin wani cool voice tace "Jaan please, ka tafi a hankali" Bai ce da ita komai bah yayi starting motan, wannan karon a hankali yake tuk'in kamar yadda ta buk'ata har suka isa airport, da kanshi ya fitar da trolley suka jera tare har wurin departure, sai da aka gama duba ticket d'inta da komai kafin ya sake mata trolleyn, bai bita bah, ita d'aya ta wuce abunda yana tsaye yana kallonta, sai da tayi nisa ta juyo tana waving mishi a hankali tana share hawaye, juyawa yayi ya bar wurin don baison ganin hawayenta, har sai da jirginsu ya tashi tukun ya bar airport d'in da dumbin kewarta, itama shirtu tayi kan seat d'inta ta lumshe ido tana ganinshi a tsaye lokacin da take waving mishi, she'll miss him a lot, haka jirginsu ya d'aga zuwa Borno, Maiduguri.
© *SEEMBY LUFF* 😘 [5/13, 1:52 PM] +234 706 824 7860: ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜ Written by *Seemby luff* ⚜ Page *74* ⚜
Komawa yayi cikin mota ya zauna, a hankali ya d'aura kanshi akan steering tare da lumshe idanu, kusan minti 20 ya d'auka zaune a cikin motan yana jin kewarta sosai, jikinshi duk a mace yayi starting motan ya bar airport d'in. Karfe 05:40pm Sahr ta sauk'a a Maiduguri international airport dake jihar Maiduguri, a hankali take sauk'owa daga matakalan tana kare fuskarta daga zafin rana, kamar batason tafiyan ta k'arasa sauk'owa, bin ko ina takeyi da kallo kasancewar bata tab'a zuwa Maiduguri bah, inda taga an rubuta 'ARRIVALS' da manyan bak'i ta nufa, kusan itace ma kawai aka zo d'auka don yawancin wad'anda suka zo tare sun san gari, tana kallon kowa yana d'aukan trolleynshi yana tafiya, juye-juye ta shiga yi tana son ganin wanda zai zo d'aukanta, wani board ta gani rik'e a hannun wani matashi ya d'aga d'auke da sunanta a kai, murmushi tayi bayan itama ta d'auki trollerynta ta k'arasa wajen, a gefen wannan matashin wata farar mace ce k'yak'k'yawa, bata cika tsayi bah haka kuma tana da y'ar kibanta, sanye take cikin lufaya red nd black mai k'yawun gaske, muirmushi itama tayi yayinda hak'orin gold d'inta ya bayyana, ganin kamannin Mami a fuskar Sahr yasa ta tabbatar cewa ita d'in ce. A nutse Sahr ta k'araso kusa dasu, kafin tayi magana Hajiya Innah ta rungumeta tana "Lale marhaban da y'ata" fad'ad'a murmushi Sahr tayi tace "You must be Aunt Innah", breaking hug d'in Hajiya Innah tayi tana kallon Sahr "Of course I am my child, sannu da zuwa kinji" "Nagode" kawai Sahr ta fad'a, da kanta Hajiya Innah taja trolleyn Sahr har suka k'arasa wurin mota, driver ya saka kayan a boot, Sahr da Auntynta suka shige gidan baya, suka wuce gidah. A mota sosai Sahr ta bud'e idanunta tana kallon garin duk da she's damn sleepy, har sai da ta gaji don kanta ta koma ta jinginu da jikin kujeran, lumshe idanu tayi tana tuna rabuwansu da yayanta har suka isa gida. Suna isa gidah, direct guest room Hajiya Innah ta wuce da ita, " Wannan shine d'aikinki throughout your stay, I hope you like it?" Gyad'a kai Sahr ta shiga yi tana kallon d'akin, wani mini bed ne na mutum d'aya daga gefen dama, sai side drawers biyu a kowane b'angaren gad'on, d'aya d'auke da bedside lamp a kai, wardrobe yana ajiye a left hand side na d'akin, sai mirror dake ajiye a center, sai kuma sofa three seated, bathroom, fan, air conditioner komai available, "I like it aunt, nagode" cewar Sahr, d'an had'e rai Hajiya Innah tayi tace "We only say thank you to strangers, not family.. Besides, ni mahaifiyarki ce kinji?" Gyad'a mata kai Sahr tayi itama tana murmushi, dafa kafad'anta Hajiya Innah tayi tace "Yanzu bari na barki kiyi wanka ki d'an huta, then sai ki sauk'o parlor at your own convenient time kici abinci koh?" "Nagode" Sahr ta sake cewa, nan take taga fuskar Hajiyan ya chanza, sagr tayi narai narai da idanu kamar wacce zata yi kuka, hannunta ta d'ago ta rik'e kunnunwanta duk guda biyu tace "Kiyi hakuri aunt, am used to saying thanks neh amma insha Allah zan kula nan gaba", shafa gefen fuskarta Hajiya Innah tayi tace "it's okay, bari in barki" tana kaiwa nan ta juya ta fice tare da ja mata kofan. Fad'awa kan gado Sahr tayi tana jin kad'aici, she missed everyone back at home musamman Mami da Khulayd, lumshe idanu tayi ta d'aura hannunta a k'irjinta tana jin yanda zuciyanta ke skipping, mirginawa tayi ta ciro wayanta daga cikin handbag d'inta tayi unlocking, hotonshi ne mak'ale a screen d'inta, kallonshi ta shiga yi tana ta faman blushing ita kad'ai, gallery d'inta ta shiga tana kallon hotunanshi, more than 100 pictures of him take da wanda tayi snapping d'inshi da sanenshi da wad'anda bai sani bah, tayi kusan 10mins tana ganin hotonshi daga k'arshe tayi zooming d'aya daga ciki ta manne bakinta a kai, a hankali tace "Jaan, I know am already yours, amma nan da kwanaki kad'an zan zama taka har abada" mik'ewa tayi ta undressing kanta, daga ita sai vest da under wear ta k'arasa wajen trolleynta ta bud'e ta ciro towel, daga k'ofan toilet d'in ta saka bathroom slippers ta shige. Ta dad'e a toilet kafin ta fito, duk da air conditioner dake d'akin bai hanata jin zafi bah don haka tayi deciding ba zata shafa mai bah, simple kayan shan iska ta sanya da hijabi, sannan ta shimfid'a darduma ta tada kabbaran sallah, sai da ta tabbata ta biya wanda tayi missing tukun tayi sallar magrib d'inta, bayan ta idar nan kan sallayan bacci ya d'auketa. A hankali taji ana bubbugata, kad'an-kad'an take bud'e idanunta har ta gama bud'esu gaba d'aya, y'ar mik'a tayi ta kalli wacce ke tashintan, wata budurwa ta gani wacce take sa'arta ce, murmushi tayi mata itama ta mayar, mik'a mata hannu yarinyar tayi suka gaisa, "Am Fa'eezah" cewar yarinyar, "And am Sahr" Sahr ta bata amsa a takaice, "Mum ce tace inzo in dubaki, wai tace bazaki sauk'o kici abinci bah?", neman agogo Sahr ta shiga yi a d'akin amma bata gani bah, juyowa tayi ta kalli Fa'iza tace "Har lokacin dinner yayi? How long nayi baccin nan?" Itama Fa'izan kallonta takeyi tace "Dunno, amma da alama kin d'an jima coz yanzu fa 10pm" waro ido Sahr tayi kamar zasu zube k'asa ta mik'e da sauri ta fad'a bathroom, komawa Fa'iza tayi ta zauna kan sofa tana jiranta, jim kad'an ta fito da alwalanta ta k'araso kan darduman ta tada sallah. Laziminta ta d'anyi bayan ta idar, mik'ewa tayi ta nad'e sallayan sannan ta dubi Fa'iza tace "Muje koh?" Daga haka suka fita zuwa downstairs. Sai da Sahr tayi kwana biyu tana hutawa tukun aka fara gyara mata jiki, tun ba'ayi nisa bah ta fara wani shek'i da haske tamkar wata, ko kad'an ba'a barinta ta fita bare har ta hau kan rana, babu abunda take yi a gidan kasancewar ak'wai House helps dayawa, cikin lokaci k'ak'ani tayi y'ar kibanta, gaba d'aya ta canza komai yayi dai-dai, sosai suka shak'u da Fa'iza, kullum suna cikin hira kamar wad'anda suka jima da sabawa, idan basa d'akin Fa'iza to tabbas suna d'akin Sahr, sunan Khulayd kam ya gaji da kuka a kunnen Fa'iza, har k'osawa tayi su tafi don taje ta ganshi duk da cewa ta ganshi a hoto. Washegari Fa'iza ta koma gidan sistern mamarta, har da kuka sai da sukayi lokacin rabuwa, da k'yar Hajiya Innah ta rarrashi Sahr tukun ta hak'ura, tun daga ranan ta daina koda zaman parlor, kullum ta d'akinta lonely and bored, Hajiya tayi fad'a har ta gaji ta k'yaleta. _A week later_ Sad'af-sad'af Fa'iza ta shigo d'akin Sahr, kwance ta hangota can k'arshen gado tayi lamo a k'wance, tsalle ta daka ta fad'a kan Sahr tana "Oyoyo precious d'in Ya Khulayd", jin muryanta yasa Sahr juyowa ta kurma wani uban ihu ta rungumota tana "welcome back babes, nayi kewarki sosai Allah" breaking hug Fa'iza tayi tana mata dariya tace "Ai naji, Mum ta fad'amin har kuka kikayi dana tafi, kuma tace kin ma daina sauk'a downstairs, u re always alone in thee room, duk missing d'ina ne haka precious, ko dai Ya Khulayd kike missing? Oya fad'a min", turo baki Sahr tayi kamar wata k'aramar yarinya as usual da niyyan kuka, har idanunta sun kawo kwalla tace "Toh ba ke bace kika tafi kika barni when u know I have no one to talk to" tana gama fad'in haka wani siririn hawaye ya gangaro gefen fuskarta, da sauri Fa'iza ta shiga share mata hawayen ta sake rungumota tana bubbuga bayanta slowly, da mamaki tace "Kai precious! Wallahi u never seize to amaze me, yanzu meye na hawaye kuma bayan gani na dawo?", tureta Sahr tayi tana nunata da y'ar yatsa tace "Hey, daina kirana precious d'innan don bai ma da dad'i a bakinki sam, Ya Khulayd yafi kowa iya kira don haka only he have the right to call me that" tsakaninta da Allah take maganan, rik'e kunne Fa'iza tayi tana dariya tace "Okay Miss Khulayd Abeed Omair, as u wish" duk suka zube da dariya, sai a sannan Fa'iza ta kalli Sahr da kyau, baki bud'e ta kamo hannunta tana gani, jim kad'an ta d'ago tana kallonta tace "Oh Ya Allah! Karfa gyaran jikin nan ya maidaki ki zama something else, kin ganki kuwa sis, wallahi am sure Ya Khulayd baze iya resisting naki bah, gaki ga shi kam sai Allah kad'ai zai ceceki wallahi, dubeki fah kin zama wata ajebo, tab Ya Khulayd zai....." Bata kare maganan ba Sahr ta jefeta da pillow tana "Zo ki fitar min a d'aki, bana son tsokanar tsiya, dama ko mun kwana biyu bamuyi fad'a bah", direwa daga gadon Fa'iza tayi ta gudu bakin k'ofa tana dariya tace "Ai gaskiya na fad'a, he can't takes his eyes off u idan ya ganki" da sauri ta fice ta bar d'akin, haka nan kawai Sahr taji fad'uwan gaba saboda kalamun Fa'iza. Sai da Sahr tayi sati uku da kwanaki uku cif a Maiduguri, ranan alhamis da k'arfe 2:00pm dai-dai jirginsu ya d'aga ita da Fa'iza da Hajiya Innah. A can gida shirye-shirye ake ba kama hannun yaro, gida ya cika makil da y'an uwa da abokan arziki, Mami da Nailah sam baka gane kansu, shirin tarb'an amarya sukeyi yayin da kawayenta suka had'a bridal shower, kusan kowa ya shirya, amarya kawai ake jira a wuce wajen event. Kamar jirgin yayi timing, 4pm suka sauk'a a airport, Khulayd da kanshi yazo d'aukan amaryanshi don bakin kishi, gani yake mutane zasu kalle mishi ita a irin kyawun da tayin nan, tun daga nesa ya hangota cikin Arabian outfit d'in da ya zama fav d'inta, ta sauya kama zuwa wata shuwa Arab haka, wani miyau ya had'ye yana jin wani yanayi da bai tab'a jin irinshi bah, har suka k'araso wurinshi bai sani bah, ita kawai yake kallo kamar zai cinye, hannu tayi clasping a kusa da kunnenshi hakan yasa ya dawo daga duniyan tunanin da ya shiga, niyyan hugging d'inta yayi amma ganin Hajiya Innah yasa ya kama kanshi, "Wow! Ya Allah!" Yayi exclaiming yana kallonta sama zuwa kasa, a hankali yace "My precious, u look extremely beautiful, nagode wa Allah daya bani ke precious" , rufe fuskanta tayi da hannayenta tana mai jin nauyin maganganunshi a gaban Hajiya Innah, daga haka suka shiga mota suka wuce. A motan ma sam hankalinshi baya kan tuk'i, juyowa yake rikayi yana kallonta, ita ko kamar batasan yana yi bah, wani kunyanshi ta tsiri ji haka nan bata iya kallonshi, kallonsu Fa'iza takeyi da sha'awa how they look perfect with each other, a zuciyanta tace "Masha Allah, what a perfect match" ganin fa Khulayd na neman zubar dasu a motan yasa Fa'iza tace "Jaan, da dai ka daina kallon precious ka kaimu gidah tukunna, kaga sai kayi ta kallonta har ka cinyeta, please ka kula da hanya", dariya sosai maganarta ya bawa Khulayd, haka nan yaji yarinyan ta kwanta mishi, sosa keyanshi yayi ya kalli Fa'iza ta mirror kawai ya basar bai ce komai bah, still kuma bai daina kallonta bah, kasa daurewa yayi saida ya rik'o hannunta, don dole ya cike guraben hannunta da nashi yana matsawa, jin muryan Hajiya Innah sukayi tana "Kunji min mara kunya, sake min hannun d'iyata dan Allah, kai gaka mara hakuri koh?" Da sauri ya saki hannunta ya maida hankali kan hanya kaman zaiyi kuka, juyowa Sahr tayi ta kalli Fa'iza tana gimtse dariyarta, a hankali Fa'iza tayi whispering mata "I told you".
Suna kaiwa gidah, motan bai ida tsayawa bah Sahr ta bud'e k'ofa ta fita, da gudu ta shiga parlor tana ihun kiran sunan Mami, Mami batayi aune bah tajita a jikinta, happily itama tayi hugging y'arta sosai, ganinta sai da kowa ya tofa albarkacin bakinshi, barin ma Neenah da Nailah. Babu b'ata lokaci aka shiga shirya amarya, wani Mint green gown ta saka wanda d'inkin ba'a cewa komai, earring da necklace duk mint green da wani ubansu heeled takalmi, babu wani scarf da aka d'aura mata, cikin friends d'inta Mami Arab tayi mata gyaran gashi da makeover, kai! Masha Allah kowa ke cewa sannan aka rataya mata 'Bride to be', kawayenta all dressed in complete peach sunyi kyau, nan na hango kaf d'in y'an Seemby luff fans club, da Seemby luff novels world 1 and 2 duk sun zuba anko, Miss Xoxo, Halyma Kurba, Cutie, Fa'iza bunu, Shaby baby, Haulat Saleh, Hawwa Tanko, Meenart, Aisha Ummi da jama'a dayawa duk suna fad'an shiga mota wai don kada a tafi a barsu😭🤣🤪😅🙈, Toh dai enough cars Khulayd yayi providing don kowa ya tafi. Event yayi kyau masha Allah, ina ganin su T-baby suna spinning waist kamar zai karye don rawa, sai yamma lis aka dawo gidah.
© *SEEMBY LUFF*😘 *SAHR-KHULAYD* Written by *Seemby luff* 😘 Page *75*
*DEDICATED TO ALL PARTICIPANTS OF SEEMBY LUFF NOVELS WORLD 1&2, AND SEEMBY LUFF FANS CLUB, I so much love you guys irin sosai d'innan, you are the real source of my strength and courage, stay blessed always, Jumu'at Mubarak* ❤❤❤
_Noble, Nabila Yusuf Dalha_ ina gaisuwa🧡🧡🧡