Kenza eBookz

Sahr khulaiyd complete - Chapter 20

Sahr khulaiyd complete - Chapter 20

Sahr khulaiyd complete Chapter 20: Sahr khulaiyd complete Chapter 20. Kan gado suka zube dukkansu kowa a gajiye, maida zance suka fara suna kallon hotunan…

2,887 words

Kan gado suka zube dukkansu kowa a gajiye, maida zance suka fara suna kallon hotunan da sukayi ta d'auka a wurin, shiru Sahr tayi tana kallonsu kawai tana ta murmushi, gajiya tayi sosai and she feel very exhausted, so takeyi ta tashi ta watsa ruwa amma gajiyan ya hanata koda motsawa, ita dama bata saba zuwa irin wad'annan wuraren bah amma kawayenta sukayi insisting sai anyi, ca sukayi ai ko auren bazawara ceh za'ayi d'an event bare kuma ita budurwa sabuwa fil, lumshe ido tayi ta yi shiru tana ji kamar duka akayi mata, wayanta dake cikin channel purse d'inta taji ya fara k'ara, a wahale ta mik'a hannunta ta janyo purse d'in ta bud'e, cirowa tayi tana duba gaban screen d'in da idanunta da suka k'ank'ance don gajiya, a hankali takai wayan kan kunnenta tana murmushi, cikin wani kasalallen murya tace "Assalamu alaik, Jaan", a b'angaren Khulayd sai da ya sauk'e wani nauyayyen ajiyan zuciya tukun yace "Precious, can you come to my room please, ina son magana dake" zatayi magana ya katse wayan don yasan yanzu sai tace tana jin kunyan y'an biki ba zata iya zuwa bah, y'ar tsaki taja tana k'okarin tashi zauneh, Fa'iza ce ta juyo tana kallonta tace "Ya dai precious da tsaki, what's wrong?" Ta tambaya tana jiran amsa, turo baki Sahr tayi kamar zata yi kuka tace "Ba Jaan baneh, wai in sameshi a d'akinshi alhalin yana ganin y'an biki sun cika gida, if someone sees me going to his room ai sai suce mara kunya ce ni, and kuma bai san na gaji baneh?", dariya Fa'iza tayi ta taso ta zaunah tace "Toh matar Jaan, duk abubuwan nan dai will end tomorrow, and I see nothing wrong in him calling you, maybe wani abun zaki yi mishi, u know dai koda ba aurenki zayyi bah ai shi yayanki neh, don't be rude, kije kawai", sake tura baki Sahr tayi tace "Toh sai ni neh sis, kefa baki san halin mutumin nan bah atoh...." Zata sake yin magana Fa'iza ta d'aura mata gyale a kanta tace "Your husband is calling, start going joor", badon taso ba ta yafa gyalen ta mik'e tana tafiya kamar bata son yi, bud'e k'ofan tayi a hankali tana lek'awa ko da akwai wanda zai ganta, babu wanda ta gani don yawanci suna downstairs, a guje ta fita daga d'akin zuwa balconyn d'akinshi, babu kowa a wurin as she expected don kusan babu abunda zai kawo y'an biki wurin, tsayawa tayi ta gyara zaman scarf d'inta da rigan jikinta sannan ta k'arasa zuwa doorstep d'inshi, k'wank'wasawa ta fara yi a hankali taji yace "Come in", tura kofan tayi slowly ta shiga, daga nan bakin k'ofan ta tsaya kawai tana kallonshi bayan ta maida k'ofan ta rufe,zaune yake a tsakiyan gado sanye da jallabiya da laptop a gabanshi, d'agowa yayi yana kallonta na d'an wani lokaci tukun yace "Ki k'araso mana precious, just want to have a word with you" k'in kulashi tayi kuma ta k'i k'arasowan, murmushi yayi sannan a hankali ya ture laptop d'in gefe, sauk'owa yayi daga kan gadon yayi tattaki zuwa gabanta, kallon skin d'inta ya shiga yi da yanda gown d'in yayi fitting d'inta, duk da cewa gyalen ya tare mishi bai gani sosai amma har yanzu its a little bit transparent, saka hannu yayi ya yaye gyalen ya wurgar a k'asa, da sauri ta had'e rai ta sadda kanta k'asa, kallonta yake yi with so much passion, babu komai a idanunshi sai zallar sonta da kuma son kasancewa tare da ita, hannu yasa ya zagaye k'wank'wasonta dashi ya janyota so very closed to him har saida fuskansu ya had'e, da sauri ta kawar da kanta gefe tana mai jin haushin abunda yake yi, a zuciyarta tace "Why is he always like this?" Mamaki taji lokacin da taji yace "Its your love that is driving me crazy baby doll", sunsunarta ya fara yi yana lumshe idanu yana shak'an dad'ad'an kamshi dake fitowa daga jikinta, gaba d'aya ya manta a wani hali suke ciki, baka jin k'aran komai sai numfashinshi dake fita da sauri-sauri, a wahale tace "Ya Khulayd don Allah ka daina, please", bai ma san tana yi bah sai kara matseta yayi a jikinshi, ganin abun na neman taking sani diversion, bata san lokacin da ta mai wani ihu bah, "I SAID STOP!" ta fad'a da karfin gaske wanda ya tilasta mishi saketa da sauri yayi baya yana kallonta, babu wasa a kan fuskarta tace "Ya Khulayd, sau nawa nake fad'a maka bana son haka? Why do you keep on doing it? Its just a matter of some hours and I shall be yours, can't you wait?" Har zai yi magana wayarshi dake gaban mirror ya fara ringing, ignoring yayi har ya yanke sannan ya juyo gareta da niyyan mata magana, ringing wayan ya sake farawa a karo na biyu, tsoki yaja ya nufi gaban mirror'n yana duba screen d'in, new number ya gani wanda hakan yasa shi picking a fusace yace "I hate to pick calls from new numbers, wayene?" Daga d'ayan b'angaren aka ce "Hey man, chill mana, me yake saka fushi haka?", fad'ad'a fara'a Khulayd yayi yace "Sameer, is that you?", dariya Sameer yayi yace "It isn't just me man, ina airport yanzu shiyasa na k'iraka kazo ka d'auken", waro ido Khulayd yayi disbelievingly yace "Da gaske kake man?", tsaki Sameer yayi yace "Da wasa neh, dallah zo ka d'auken Malam, na gaji da zama nan ni kad'ai" yana kaiwa nan ya katse wayan, car key kawai Khulayd ya d'auka ya fice, yama manta tana wurin, girgiza kai tayi bayan fitanshi tayi tafiyanta d'aki itama. Tana shiga d'aki, duk suka juyo suna kallonta suna dariya, k'arasowa tayi ta zauna kan sofa tana kallonsu, gajiya tayi da dariyan da suke mata tace "Ha'a, wai nikam meye naga kuna ta yimin dariya, me ya faru neh", Fa'iza ce tace "A'a ba dole muyi dariya ba, nan kika yi wani narai-narai da idanu kamar zakiyi kuka don ya k'iraki, sai gashi kinje kin jima, kodai kukan kika masa neh miss cry cry?" Mik'ewa tayi ta musu tsoki, toilet ta wuce abunta bata ce dasu komai bah. _At the airport_ Speedy Khulayd ya shiga airport d'in kamar zai tashi sama, ko gyara parking nashi bai yi mai kyau bah ya fito daga motan, arrivals ya nufa yana ta faman juye-juyen inda zai hango Sameer, chan ya hangoshi tsaye shi kad'ai ya juya bayanshi, k'arasawa yayi ya tsaya a bayanshi na d'an wani lokaci tukun ya dafa kafad'ashi, a nutse Sameer ya juyo yana son ganin ko waye, hugging d'in Khulayd yayi happily kamar wani karamin yaro, shima Khulayd d'in rik'eshi yayi ya kasa b'oye farin cikin shi, "Welcome man, so good to see you" cewar Khulayd yana bubbuga bayan Sameer a hankali, breaking hug d'in Sameer yayi yace "God to see you too man, you loom good fah, meye sirrin?" Bugu Khulayd ya kai mai a k'irji yace "Wannan amsan a mota zan baka shi coz I don't think a nan zamuyi ta zama har in gama baka amsoshin tambayoyinka, I know man, you have lots of questions to ask", duk sukayi dariya suka wuce mota, wani security na binsu da trolley a baya. Shiru sukayi a motan kamar basa nan, ganin shirun yayi yawa yasa Sameer fad'in "Man, I still can't believe aure zaka yi, mamaki abun yake bani", murmushi Khulayd yayi yana kallon hanya yace "Meye abun mamaki kuma, I've decide to settle", d'an bugunshi Sameer yayi yace "Are you sure you want to do this? Kar fa kazo kana zaluntar yarinyar mutaneh, coz nasan kai mayen mata neh kuma ita kad'ai ba zata iya satisfying d'inka bah", juyowa Khulayd yayi ya kalleshi sannan ya sake maida hankalinshi kan driving yace "Man, am not the Khulayd you used to know, wancan mayen matan is long gone, am a changed person now, that girl have changed me completely, tayi transforming d'ina zuwa sabon mutum", dariya sosai Sameer ya fashe da, har da rike cikinshi yana nuna Khulayd yace "Kai d'inne wai mace zata canza ka, don't forget cewa ka maida mata kamar toothpick, u pick and throw it whenever you wish to, shine kake cewa mace ta canzaka? Abun da kamar wuya Man", ajiyan zuciya Khulayd yayi lokacin da suke shiga layin gidah, a bakin gate yayi parking ba tare da yayi horn bah ya juyo yana fuskantar Sameer, yace "Man, bazaka ganeh bane, I so much love this girl with the whole of my heart, I feel her love running through my veins, through my blood and flesh, idan ban ganta ba I feel my heart doesn't beat, but the moment I set eyes on her sai inji zuciyata ta fara bugawa, bazaka gane bah Sameer, that girl is all what I want in life yanzu haka, ji nakeyi kamar gobe bazai zo bah, my heart beat only because that girl is in it" ya karasa maganan tare da kwantar da kanshi akan steering ya lumshe ido, da mamaki sosai Sameer ke kallonshi, bai tab'a tsammanin zai ji irin maganganun nan a bakin Khulayd bah, dafashi yayi yace "Man, you re so damn in love, ina maka fatan alkhairi but nikam I don't believe in love, mata ai ababen more rayuwa neh, ba sai ka auresu bah", d'agowa Khulayd yayi yace "Man, not if you meet the right person, sai kaji numfashinka ya d'auke duk randa ka gamu da wacce kake so, I promise u this", ajiyan zuciya Sameer yayi ya kwantar da kanshi a jikin seat bai ce komai bah, horn Khulayd yayi maigadi ya wangale gate suka shiga ciki. D'akin Khulayd suka nufa kai tsaye bayan sun bi ta balcony'n baya inda ba zasu had'u da mata bah, suna shiga Sameer ya fad'a toilet, unlocking wayanshi Khulayd yayi ya k'ira babynshi suna hiran soyayyansu, kusan 30min Sameer yayi a toilet ya fito d'aure da towel a k'ugunshi, fridge ya nufa ya bud'e yana dube-dube bai ga abunda yake nema bah, d'agowa yayi ya jira har sai da Khulayd ya sauk'e wayan yace "Man, ya banga giya a fridge bah, ko akwai inda kake b'oyewa neh?" Ko kallonshi Khulayd bai yiba yace "Bana sha", surprisingly Sameer ya sake kallonshi yace "Ban gane bah", "I don't take alcohol anymore, shine abunda nake nufi" cewar Khulayd, mayar da marfin fridge d'in Sameer yayi ya rufe,k'arasawa yayi ya zauna kusa da Khulayd a bakin gado yace "But why?", "Sahr" kawai Khulayd ya fad'a, Sameer "Toh naji, bani tabs in had'iye coz na gaji, wanna feel on top", "Wannan ma bana sha" ya bashi amsa a takaice, rai a b'ace Sameer yace "Shi kuma meyasa?", "Sahr" Khulayd ya sake fad'a baya ko kallonshi, a fusace Sameer ya mik'e ya fara bambami "Dallah me haka, Sahr, Sahr, Sahr, meyasa ne wai ina tambayanka abu kana kiramin sunan wata yarinya?", had'e rai shima Khulayd yayi ya mik'e yana kallon Sameer in the eye yace "Hey, she's not just wata yarinya man, she's my life" yana kaiwa nan ya ajiye wayanshi ya shige toilet, zama Sameer yayi ya dafa kanshi don yaga cewa da gaske Khulayd yake, haka suka kwana basa yiwa juna magana, akan gado Sameer ya kwana, Khulayd kuma kan three seated sofa. _Friday_ 12pm Khulayd da Sameer suka kammala shurinsu cikin wani white shadda da babban riga wanda yaji aiki dark blue, hulansu ma dark blue d'inkin Bama dake jihar Borno sai sheki yake yi, pure diamond wrist watch suka saka na Rolex, sunyi kyau sosai tun ba ma Khulayd bah, ji yake yi lokacin bai tafiya sam, wayanshi ya d'auko yayi dialling number d'inta, bugu uku Fa'iza tai picking tace "Hello Jaan", jin ba muryanta bane yasa ya murmusa yace "Miss Fa'iza, where's my wife", dariya ta k'yalk'yale dashi tace "Wife to be dai koh", shima sai da ya d'ara sannan yace "Whatever, ina take?" "Jaa, precious fah bata da lafiya, jiya haka muka kwana bamu runtsa bah" cewar Fa'iza, "Shine baku fad'amin bah? Ya take yanzxu? Ko a kaita hospital neh?" Ya tambaya a rud'e, da sauri tace "Mami tace babu need a kaita asibiti, inaga as a result of gajiyan da tayi jiya neh, amma yanzu ta samu bacci and we hope she'll be okay when she wakes up", ajiyan zuciya yayi yace "I'll come and see her yanzu", bai jira yaji abunda zata ce ba yayi hanging up, mik'ewa yayi ya fito daga d'akinshi, ya kama hanyan nata d'akin without minding kallonshi da ake yi. Mami na zauneh a gefenta akan gadon, Nailah da Fa'iza tare da sauran y'an matan duk a tsatstsaye, turo k'ofan yayi da sallamarshi ya shigo, duk suka juyo suna kallonshi tare da amsa sallamarshi, duk y'an matan sai da numfashinsu ya kusa d'aukewa don tsabar yadda Khulayd yayi kyau, baki bud'e suke kallonshi kamar su cinye, k'arasowa yayi kusa da Mami ya zaunah yana tambayar ya take?, cikin baccinta ta shak'i unique k'amshinshi mai tafiya da imaninta, idanunta a rufe tace "Jaan", da sauri Khulayd ya rik'o hannunta cikin nashi yana kallon palled fuskarta yace "Am here precious, am here", murmushi tayi ta damke hannunshi sosai tace "Yau aurenmu koh?" Bama Khulayd ba sai da kowa yayi murmushi da mamaki ganin idanunta a rufe amma tana magana, shafa hannun yayi yace "Yes precious, yau rananmu neh dats y I need u to fight and be strong okay?" Gyad'a masa kai ta shiga yi tana murmushinta mai kyau, chan tace "Miss Khulayd Abeed Omair, I love you so much Jaan", Mik'ewa Mami tayi ta fita don kunya, haka ma Nailah da sauran y'an matan suka yi waje, Fa'iza kad'ai ce ta zaunah don tasan tabbas Khulayd zai tafi yanxu and she can't be left alone, "I love you too wify" ya fad'a tare da pecking hannunta, tasowa yayi yana kallon agogon hannunshi yaga lokaci ya ja, a gurguje ya kalli Fa'iza yace "Please take care of her" daga haka ya fice. Tarar da Sameer yayi ya cika ya kusan fashewa, dariya yayi ya tsaya gaban mirror yana gyara zaman hulanshi yace "Am sorry man, naje duba matata neh, yanzu ka tashi mu tafi" yana gama fad'in haka ya wuce abinshi don yasan yanzu Sameer zai fara masa bambami. Jumma'ah suka wuce aka idar da sallah sannan suka dawo k'ofar gida, jama'a sun cika mak'il, manyan mutane da attajirai, y'an kasuwa da sarakai. K'arfe 2:30pm dandazon jama'a suka shaida d'aurin auren Khulayd Abeed Omair da Sahr Mukhtar a bisa sadaki dubu d'ari, akayi fatiha, Khulayd ji yayi kamar an yayyafa masa ruwan sani a zuciyarshi, he feels like a new man, farin ciki kam ba'a magana, sai gaisawa da mutane yake ana mishi congrats, sai da mutane suka d'an raguwa yaje wuri Papanshi, rungumeshi yayi yana "Thank yo Dad, for everything", murmushi Mr Abeed yayi yana bubbuga bayanshi a hankali yace "Congratulations son, wish u a happy married life". Bayan sun d'an matsa neh ya kira wayanta, lokacin idanunta biyu but still a kwance take ta d'aga, bai bari tace komai bah yace "Precious you are now mine, from head to toe ke tawa ceh, am the happiest man on the planet earth today, nagode Allah daya bani keh Precious, Alhamdulillah", ji tayi ta nemi rashin lafiyan ta rasa, sosai take murmushi tace "Mijinah" a hankali tana rufe fuska, jin kalman yayi kamar wani sabon kalma, "Yes with,am coming to kiss you now" dif ya katse wayan yana dariya, bugunshi Sameer yayi yace "Kabi da y'ar mutaneh a hankali please, na sanka ba sauk'i kuma naga yarinyar k'arama ceh", hararanshi Khulayd yayi yace "Ba zaka koyamin yanda zan bi da matata bah, ya wuce ya barshi yana tsaye a wurin, girgiza kai Sameer yayi sannan ya bishi a baya. A cikin gidah sai gud'a ake mai duk inda ya ratsa, sam shi ba ta kansu yake bah, stairs ya hau direct to her room, tana d'aure da towel zata shiga wanka ya bud'e k'ofan ya shiga, ita da Fa'iza neh kawai a d'akin don haka ya tunkareta, Fa'iza na ganin haka ta kannewa Sahr ido tayi waje, ita koh sai kakkare jikinta takeyi, ganin ya kusa isota yasa ta juya ta shige toilet da sauri, zata rufe taga ya rik'e da hannunshi, iya k'arfinta take turawa amma ko motsawa baya yi, ganin k'arfinta ya kare yasa ta sake kofan kawai, shiga yayi ya mayar da k'ofan ya rufe har da key, fisgota yayi ya mannata da jikin bango a k'arkashin shower, saka hannu yayi ya kunna shower'n nan da nan ruwan ya fara jik'asu, d'ago hab'arta yayi yana kallon cikin idanunta, da sauri ta lumshe ido zuciyanta na bugawa, murmushi yayi ya d'aura lips d'inshi akan nata ya fara kissing passionately, kusan 30min ya d'auka yana abu d'aya sannan ya sake mata baki, forehead dinta yayi pecking sannan a hankali yace "I love you precious", saketa yayi yana murmushi sannan ya bud'e toilet d'in ya fita, a hankali ta bud'e idanunta itama tana murmushin, shafa lips d'inta tayi tace "Nima ina sonka sosai mijinah", daga haka ta fara wankanta, sai blushing takeyi ita kad'ai, lokac-lokaci kuma sai ta shafa lips d'inta duk da zogin da suke yi.

#TeamSahrKhulayd

© *SEEMBY LUFF* 😘 *SAHR-KHULAYD* Written by *Seemby luff* 😘 Page *76*

*THIS IS FOR U, SAHR-KHULAYD FANS GROUP 2* ❤ Am so happy and overwhelmed with this reunion, thanks a lot for your love and supports.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull