Kenza eBookz

Sahr khulaiyd complete - Chapter 21

Sahr khulaiyd complete - Chapter 21

Sahr khulaiyd complete Chapter 21: Sahr khulaiyd complete Chapter 21. Ta d'auki lokaci sosai a bathroom d'innan kafin ta bud'e ta fito da murmushi d'auke…

4,486 words

Ta d'auki lokaci sosai a bathroom d'innan kafin ta bud'e ta fito da murmushi d'auke akan fuskarta, rik'e take da towel tana towel drying fuskarta tana y'ar wakanta, zaune taga Fa'iza kan sofa ta rungume hannu a k'irji tana kallonta, d'aga mata hannu tayi alamar meye tayi ta k'arasa bakin mirror ta zauna kan stool tana fuskantar ta, tasowa Fa'izan tayi daga kan Sofan ta dawo kusa da ita a gaban mirror'n tace "Sis, naga fa sai blushing kike tayi tun da Ya Khulayd ya fita daga d'akin nan, tell me meye ya baki haka that makes u keep blushing alone, na tabbata akwai wani abu. Fari da idanu Sahr tayi kafin ta d'ago tana kallonta tace "Well, zan iya cewa babu ruwanki a ciki sis, this is between a husband and his wife" ta k'arashe maganan tare da d'aukan comb ta fara combing gashinta, bud'e baki Fa'iza tayi tana kallonta da mamaki sosai, dafata tayi tana lek'o fuskarta da kyau tace " Like seriously, kece kike fad'in haka sis? Wai ma tsaya, yaushe akayi auren neh har kike cewa wai its between a husband and his wife? Ba dai auren da akayi an hour ago baneh?" Ajiye comb d'in Sahr tayi ta sake d'agowa tana kallonta tace " even if it was a second ago, ai dai shi mijinah neh koh? And everything we do is our secret", ta d'ago comb d'inta ta cigaba da abunda take yi, " Are you kidding me sis?" Cewar Fa'iza, gyad'a mata kai Sahr ta shiga yi tace " Umhum... Kinga ni ki tayani zab'an kayan da zan saka, idona rawa yake yi Allah kuma I want to look the most beautiful bride ever", murgud'a mata baki Fa'iza tayi tace " Ki dai k'ira mijinki ya zab'ar miki, kinga zai fi zab'ar miki wanda zai karb'eki", turo baki Sahr tayi kamar zatayi kuka tace " Ohh sis, please ki bar maganan nan, kinsan kina da taste when it comes to choosing outfit" ta mik'e ta rungumeta tana " Kiyi hakuri maganan dana fad'a miki d'azu, kinsan cewa wasa nakeyi koh? Zo in fad'a miki abunda ya min" ta k'are maganar tana yi mata gwalo, don tasan tabbas Fa'iza ba zata bari ta fad'a mata abunda Khulayd yai mata bah, tureta Fa'iza tayi tana hararanta tace "Dallah yimin shiru, ban ma so naji komai, barin cire miki kayan" ta juya zuwa wurin ak'watunan dake jere kusa da closet, nan ta ciro mata wani dank'areren swiss lace mai kyawun gaske, jewelries, takalmi, gyale da purse duk matching colors ta dawo ta zubesu kan gado, kallon Sahr dake shafa a gaban mirror tayi tace " Ba na k'ira Mami Arab tazo tayi miki makeover", daga haka ta fita zuwa downstairs. Jim kad'an ta dawo tare da Mami Arab, makeup kit ta d'auko sannan ta dawo ta ije gaban mirror, nan ta fara yi mata, ba'a d'au lokaci bah suka kammala saboda light and simple makeup suka yi, amma tayi bala'in kyau sosai da sosai, babu abunda suka barta tayi da kanta, komai suka yi mata suka shiryata tsab, su da kansu sai da suka ce Masha Allaah. Bi tayi ta gaisa da duk wanda yazo bikin, lis ta gaji ta dawo d'aki tana maida numfashi, da yamma kusan kowa ya watse, d'aid'aiku neh suka rage daga wad'anda suka zo daga nesa, normal ma gidan ya dawo saboda baki duk suna guest side, wani small family dinner suka had'a don nuna farin cikinsu, yanda suka saba yin dinner haka babu abunda ya canza, sai mummy'n Khulayd, Hajiya Innah da Fa'iza suka k'aru, kowa ya hallara a dinning area banda Sahr kuma it seems ita suke jira. A d'aki suke ita da Fa'iza suna ta duba kayan da zata saka, gajiya sukayi daga k'arshe suka yi deciding ta sanya wani milk colored gown, ta d'aura kanta da coffee tie tayi kyau sosai, tare da Fa'iza suka sauk'o daga stairs din zuwa dinning area, gaishe da Mr Abeed tayi da farko sannan ta wuce wurin Mummy'n Khulayd, har k'asa ta sunkuya cike da kunya tana gaidata, d'agota Mummy'n Khulayd tayi ta d'aurata a cinyarta, d'ago hab'arta tayi tana kallon k'yak'k'yawan fuskarta, saka hannu Sahr tayi ta rufe fuskarta, murmushi Mummy'n tayi tace " How are you my child?", k'asa-k'asa Sahr ta amsa da " Am fyn", kallonsu Mami tayi tana murmushi tace " Oh Ya Allah, wannan k'atuwar yarinyar zaki d'aura a kafafunki don neman magana? Kalen anjima kad'an ki ce wa Yaya k'afarki na ciwo koh?", d'auke kai Mummy'n Khulayd tayi tace " Oho dai, yau am very happy son yayi aure, kuma ikon Allah ya auro min wannan y'ar tawa mai kyau da tarbiyya, am indeed the happiest mother on earth today" ta k'are maganar tana shafa gefen fuskan Sahr, da sauri ta k'wantar da kanta a kafad'ar Mummy'n tana dariya. Foot step na Khulayd suka ji yana making call, yana approaching dinning area'n, tsayawa yayi ya kammala wayan tukunna ya k'araso, kan Mummy da Sahr idanunshi ya sauk'a da shigowanshi, d'an ware ido yayi yace " Mummy dama nan kika zo kika b'oyemin wify na koh, have looked for her ko ina upstairs ban ganta bah, ashe tana nan", spoon Mummy ta d'auka ta wugeshi da har sai da yayi y'ar k'ara " Argggh", Sahr dake zaune a cinyar Mummy bata san sanda tace "Issshhh" bah, basar da ita Mummy tayi ta kalli Khulayd tana nunashi da y'ar yatsa tace " Ka fitar min a ido in rufe fah kai d'innan, wai sau nawa zan ke fad'a maka ka koyi jin kunya neh kam? Kai Khulayd, learn some manners fah" kamar zai yi kuka ya rik'e wurin data jefeshin yana sosawa, yace " Haba Mum, ba gaskiya na fad'a bane? Isn't she my wife? Sai kuma ba zan k'irata in sakata aiki bah?" Ya k'are maganan yana had'e ranshi, baki bud'e Mummy ta kalleshi tace " Iyyeh, lallai ma yaron nan, du du yaushe akayi auren neh har zaka fara gajiyarmin da y'a, y'ar aikinka ceh ita?" Ta tambaya, zai yi magana Mami ta riga shi tace " A'ah sis in-law, gaskiya ya fad'a she's his wife and he have the right ya sakata aiki, it doesn't matter yaushe aka d'aura auren", k'arasawa yayi kusa da Mami ya ja kujera ya jera da ita, zama yayi ya k'wantar da kanshi a kafad'arta kaman baby yace " Yawwa sweet aunt, kin ji abunda Mum take cewa bah? Murmushi tayi tana bubbuga bayanshi tace " Kada ka kulasu son, suna nuna maka bambanci neh kawai unknown to them cewa ni ma Mummy'nka ceh, so ka sharesu muyi maganar mu, ka riga ka siyan muku ticket d'inneh?" D'ago kanshi daga kafad'arta yayi yana gyad'a kai yace " Eh aunt, nayi booking 4 seats a flight na gobe, so we are good to go", sai a sannan Mr Abeed yayi magana " What flight are you talking about? Waye zai yi tafiya kuma ban sani bah?", ajiyan zuciya Mami tayi tace " Tafiya zasu yi manah, ko ba muyi maganar da kai jiya baneh Ya?", girgiza kanshi yayi yace " Of course munyi, but that's not what we've agreed upon, n......." Katseshi Mami tayi tace " Yaya please kar muyi arguing akan maganan nan, son ya sameni yace lallai zai tafi da matarshi Abuja, ni kuma gaskiya na goyi bayanshi, bai kamata a k'i bashi matarshi saboda wasu dalilai da bah k'warara bah", " Baki gane baneh sis, kiga fa yanda yake yi mata ihu at times, Allah kad'ai yasan meye zai mata idan sun tafi, besides she's still a baby ai, su d'an zauna dai tukun" cewar Mr Abeed, itama Mummy tace " Am with you on this, ba zai yiwu ya tafi da ita haka nan bah, wannan shegen rigiman nashi ba zata iya d'auka bafa, rigimamme ne to the highest order", takaici neh ya turnuk'e zuciyan Mami har sai da ya bayyana a fuskarta, cikin fushi tace " Har zuwa wani lokaci za'a cigaba haka? Mutum da matarshi amma kuna nuna mishi iyakarshi? Toh idan ita baby ce me yasa akayi auren in the first place? I know my son very well, he loves her so much don haka zai kula da ita, ni dai wallahi zai tafi da matarshi gobe neh", Mr Abeed zai yi magana Mami tayi saurin cewa " Yaya please, an riga an wuce wurin fah", haka ba don yaso bah ya yarda, tattab'ata Khulayd yayi ta juya ta dubeshi, murmushi ya sake mata sannan k'asa-k'asa yace " Thank you aunt, I love you", murmushin itama ta sakar mishi tana gyad'a mishi kai tace " And I you son", daga Nailah ta mik'e zata fara serving dinner, tsayar da ita Mummy'n Khulayd tayi tace " Kiyi zamanki Nailah dear, bari daughter in-law tayi serving d'in mu", dariya kowa yayi banda Sahr da ta mik'e a kunyace ta fara zuba abincin. Bayan dinner Sahr ta wuce d'aki abinta, ko cin abincin bata yi na k'irki bah don she's uncomfortable, gaba d'aya kunyan Mummy da Papa take yi, kwanciya tayi a saman gado tana kallon ceiling, ta kai tsawon lokaci a haka, daga bisani ta mik'e ta nufi closet d'inta, y'ar riga ta ciro da three quarter wando, cire kayan jikinta tayi ta sake fad'awa bathroom a gurguje, watsa ruwan kawai tayi ta fito ta sanya kaya, bata ida zama bah Mami da Nailah da Neenah suka shigo, gani tayi kawai sun jajjawo akwatunan suna packing kaya, shiru tayi ta koma kan sofa tana kallonsu, jim kad'an idanunta suka fara kawo kwallah, babu wanda ya kula da ita, sai packing suke yi, tagumi ta buga a hankali tace " Yanzu Mamina da gaske tafiya zanyi in barki gobe?" K'in kulata Mami tayi duk da ta jita, tasowa tayi daga kan sofan taje da gudu ta rungumeta, still Mami tayi ta k'i juyowa don itama idonta ya kawo kwallan, kuka sosai Sahr ta fashe da abun tausayi, watsar da kayan Nailah tayi ta rungumesu itama tana hawaye, haka Neenah ta k'araso a wheelchair d'inta ta rik'esu, sosai suke kuka babu mai rarrashin wani, daure zuciyanta Mami tayi tasa bayan hannu ta share hawayenta ta juyo, d'ago hab'arta tayi tana kallon cikin idanunta tace " Little princess meye na kukah? Ai wannan shine auren so you have to go along with your husband, shine hanyar samun aljannarki babynah", kwantowa Sahr ta sake yi a kafad'an Mami Mami, a shagwab'e tace " Um um Mami, Allah babu inda zanje, am staying here with all of you", shafo fuskarta Nailah tayi tace " Kiyi hak'uri kid sis, ba zai yiwu ki zauna damu bayan kina da miji bah, ai Ya Khulayd ba zai hanaki zuwa ki ganmu a duk lokacin da kike so bah", rungume Nailah tayi tace " Addah Nailah, Allah na fasa auren, zan zauna da ku", buge mata baki Mami tayi tace " Kin ci gidanku, lemme not hear this coming out of your mouth ever again", haka suka gama had'a kayan da koke-kokensu. Washegari, morning flight zasu bi don Sameer ya tasa Khulayd a gaba suka shirya da wuri, a b'angaren Sahr kuma, tun da'azu Fa'iza ta sata shiri amma ta k'i, sai kuka take yi tana ta cewa ita ba zata ko ina bah, da abun yafi k'arfin Fa'iza ta k'ira Mami a landline ta fad'a mata, ba'a jima bah Mamin ta shigo rai a b'ace, Sahr na zaune bakin gado tana ta rusar kukah, k'rasowa Mamin tayi wurinta tace " Wai nikam yaushe kika zamo mai kunnen k'ashi ne princess? Tun jiya aka bar zancen nan amma ki rinka yiwa mutane kukah? Toh wai da kin d'auka idan anyi auren zama ake yi a gidah? Ai kuwa da bazan baro gidanmu in zaunah da mahaifinku bah, gashi even after his death ina zaune a nan. In ba so kike ranki ya b'aci bah ki tashi maza kiyi wanka, lokacin tafiyaku ya kusa and your husband is already waiting for you", yi Sahr tayi kamar bata ji me Mami take cewa bah,cikin tsananin fushi da tsawa Mami tace " Ki tashi nace", a tsorace ta mik'e jiki na rawa ta shiga bathroom da gudu, kafin ta fito Fa'iza ta cire mata kayan da zata saka, jiki a mace take yin komai har ta kammala shirinta, already an fita da trolleys nasu zuwa motan, tsayawa tayi na tsawon lokaci tana bin d'akinta da kallo haka nan, a hankali tasa bayan hannunta ta share sabbin hawayen da suka gangaro mata, ta fita da gudu, sai da Fa'iza ce tai locking kofan sannan ta samesu a downstairs. A sanyaye ta k'araso cikin parlor'n tana kallonsu d'aya bayan d'aya, kusa da Hajiya Innah ta tafi ta zaunah, sunkuyar da kanta tayi saboda bata so ta kallesu, babu wanda yace komai a parlor'n na wanj lokaci, Mami ceh ta kawar da shirun tace " Princess", a hankali Sahr ta d'ago kai ta kalleta ta sake sauk'ewa, hakan ya bawa Mami damar cigaba, " I don't have much to tell you, but inaso kisan cewa zaman aure ba wasa baneh, duk yadda kike tunaninshi ya wuce haka, abunda zan fad'a miki shine ki yiwa mijinki biyayya, ki tabbatar kin kula da hak'k'okinshi daya rataya a wuyanki, ki zama mai bin umarninsa, banda kazanta duk da na san cewa ke d'in mai biyayyace kuma mai tsafta" haka Mami ta rinka mata nasiha mai ratsa jiki, da gudu Sahr ta tashi daga inda take zaune taje ta fad'a jikin Mami tana kuka, ita kanta Mamin ta kasa daurewa itama ta soma kukan, babu wanda bai yi k'wallah a parlor'n bah sai Khulayd da Sameer, d'agota Mami tayi ta kallo fuskarta tace " Go and make me proud princess, kije ki tabbatar min da cewa ban sha wahalan tarbiyyanki a banza bah", sake rungumeta Sahr tayi tana " Insha Allah Mami I'll make u proud, I love you so very much", " And I love you more my child, Allah yayi muku albarka", haka Sahr tabi yayyenta tana rungumarsu, har Mummy da Hajiya Innah kafin daga bisani suka fita haraban gidan, k'in zuwa Mami tayi ta tsaya abunda a parlor'n tana hawaye, Khulayd ne ya fita dga k'arshe, har ya kai bakin k'ofa Mami tace " Son", juyowa yayi yana kallonta daga nesan, a hankali Mami tace " Take care of her please", gyad'a mata kai yayi yace " Sure, I will aunt" daga haka ya fice.

Har suka isa airport bata yiwa kowa magana bah, rusar kukanta kawai take yi tun muryanta na fita har ya tafi ta dawo yin sheshsheka, duk efforts nasu na ganin sun rarrasheta tak'i dainaawa, har suka shiga jirgi bata ce da kowa komai bah, data gaji da kukan ma ta kwantar da kanta a seat ta lumshe idanu har bacci ya d'auketa. Basu jima bah suka isa Abuja, direct gidansu suka wuce bayan driver yazo ya d'aukesu, katamfaren gidah ne mai kyawun gaske, babu abunda babu a cikin gidan, ga enough d'akuna da manyan parlor har uku, nuna musu d'aki Khulayd yayi sannan ya kai Sameer guest room, dawowa yayi ya fad'a bathroom don freshening up, a b'angaren Sahr da Fa'iza ma wankan sukayi sannan suka idar da sallah, nan kasan darduman Sahr ta mik'e don gajiya, haka Khulayd, Sameer da Fa'iza suka hau tidying na gidan don k'ura, share nan, goge can har saida suka gyara gidan tsaf har kusan 5pm,sosai suka gaji kowa ya koma d'akinshi ya sake watsa ruwa, bayan sun kammala Khulayd da Sameer suka fita don nema musu abunda zasu ci. Sai da Fa'iza ta kammala komanta ta dawo d'akin Sahr, kwance take a inda take tana ta sharar baccinta, girgixa kai tayi tana murmushi taje kasa ta d'an bubbugata, a hankali ta ware idanunta tana kallon Fa'izan, nuna mata lokaci da Fa'izan tayi ne yasa ta tashi babu shiri ta fad'a bathroom, alwala ta d'auro ta fito ta fara nafila, ganin haka yasa Fa'iza mik'ewa ta fita, bayan ta kammala nafila ta tada iqaman sallan Magrib, nan dai tayi ta zama tana laziminta har aka k'ira Isha'i. Sai 8pm suka dawo gidah, side nashi Sameer ya tafi da takeaway d'inshi, shi kuma Khulayd ya hayo stairs, a k'ofar d'akin Fa'iza ya tsaya ya k'wamk'wasa, bayan ta bud'e ya mik'a mata nata takeaway d'in sannan ya wuce d'akin Sahr. Zaune ya ganta bakin gado ta had'a kai da gwiwa shiru abinta, girgiza kai yayi ya ajiye ledan hannunshi kan table dake ajiye a gefe, wurga car key d'inshi yayi kan gado ya sake shiga toilet yayi wanka, fitowa yayi as usual dai-dai tana d'ago kanta ta ganshi, da sauri ta sake maida kanta tsakanin kafafunta tana runtse ido, bai ce komai bah ya nufi closet nata, a side d'in daya d'an saka kayanshi ya ciro vest da singlet ya sanya, dawowa yayi kusa da ita ya zaunah, d'aura hannunshi yayi kan kafarta ta d'ago a firgice kamar zata fasa k'ara, da sauri ya toshe bakinta yace " Its alright precious, ni neh fah", kawar da kanta tayi gefe ya sake juyowa da fuskarta, " Have you prayed?" Ya tambayeta, gyad'a mishi kai kawai tayi, yace " Let's eat then" ya fad'a tare da janyo table d'in kusa, turo baki tayi ta soma girgiza mishi kai, " Ni ba zan ci bah" haka tayi ta zuba mishi shagwab'a yana biye mata, daga k'arshe dai ya samu taci spoon biyu, shima bai wani ci sosai bah ya ture table d'in, kallonta yayi yanda duk ta zama wata iri yace " Tashi kiyi wanda" can kasan mak'oshi tace " nayi", " Je kiyi alwala toh", babu musu ta mik'e zuwa bathroom tayi alwala ta fito, mik'ewa yayi yaje ya ciro jallabiya ita kuma ya ciro mata hijabi, nan yayi leading d'insu sallah, bayan sun idar ya kama goshinta yai mata addu'a, few questions regarding religion ya tambayeta duk ta bashi amsa, cike da jin dad'i yace " Je ki cire kayan jikinki, kisa sleeping dress", k'asa-k'asa tace " Ni da na jikina zan kwanta" b''ata rai yayi yace " Oh, stop being stubborn, ki tashi ki canza nace" a sanyaye ta mik'e ta ciro nighty da take sawa a gidah ta shiga bathroom ta canza, fitowa tayi ta nufi bakin gado abunta ta zaunah, tashi yayi ya koma kusa da ita, kissing wuyanta ya fara yana tura kanshi cikin jikinta, da kyar ya lalubo bakinta ya saka a nashi, wani salon romance ya shiga yi mata, sai rawa jikinta keyi, ga tsoro da fargaba sun cika mata zuciya, sosai Khulayd yai nisa a abunda yake yi sai numfashi yake, mutsu mutsu ta fara tana so ya kyaleta amma ina! Da iya k'arfinta ta daddage ta tureshi ya fad'a kan gado, mik'ewa tayi tana gyara kayanta kamar zatai kukah, d'agowa yayi yana kallonta da idanunshi da suka sauya zuwa ja, " What was that precious?" Ya tambaya da kyar, murgud'a mai baki tayi tace ". Bana so neh", cikin rashin fahimta yace " Ba kya son me?", a kufule tace " Abunda kake yi, ni ka kyaleni" tasowa yayi yazo gabanta, rik'eta yayi yace " Precious why? Kafin muyi aure idan na tab'aki kice haramun, yanzu kuma na tab'aki kice baki so? Do u have any idea as to how long I've been waiting for today? Please kada ki hanani tab'aki precious, I find pleasure touching you,please kinji", kai kanshi yayi zai kwantar a jikinta ta fasa mishi k'asa, cikin raising voice tace " Don't touch me, nace banaso", ihunta bai tab'a b'ata mishi rai ba kamar yau, komawa bakin gado yayi ya d'au jallabiyanshi yana sakawa, sai a sannan tayi realising bata mishi dai-dai bah, kusa dashi ta dawo lokacin ya gama saka jallabiya, cikin tattausan murya tace " Jaan, am s....." Dakatar da ita yayi ta hanyan d'aga mata hanu yace " Just hold it there precious", d'aukan wayarshi yayi ya fice daga dakin ya ruf'e k'ofan da karfin tsiya har sai da ta tsorata.

© *SEEMBY LUFF* 😘 [6/23, 10:18 PM] ‪+234 703 699 3170‬: *SAHR-KHULAYD* Written by *Seemby luff* 😘 Page *77*

*Taqabbalallahu minna wa minkum ajma'een, may Allah (S.W.T) accept the fast and prayers we've offered.*

Tsorata sosai tayi da jin yadda ya rufe kofan, a hankali ta koma baya ta zaunah bakin gado tana dafe kanta, lumshe ido tayi shiru tana baiwa kanta laifi, sosai ta san abunda tayi ba dai-dai baneh sam, tsoron da take ji neh ya hatana barinshi ya aikata koma meye yake da niyya, ganin zaman da take yi bazai taimaketa bah ta mik'e jiki babu kwari ta fita daga d'akin, d'akin Fa'eeza ta nufa ta murd'a a hankali, kwance ta hangota tsakiyar gado tana ta faman danna waya, har ta k'arasa kusa da gadon ta zaunah Fa'eeza bata ji bah, jin an dafata yasa ta yasar da wayan dake hannunta tana neman yin ihu, bugu Sahr ta kai mata tana "Dallah chan matsoraciya, ni ceh toh" tsaki Fa'eeza tayi ta tashi zauneh tana harararta, tace "Wallahi u scared me sis, meye haka ko sallama babu kika shigo min d'aki? Ba dole inji tsoro bah" numfashi taja tukunna ta cigaba "Me ya kawoki d'akina by this hour of d nyt? Ain't u supposed to be with your husband now?" Ta tambaya tana jiran response. Shiru Sahr tayi bata tanka bah, dake kanta ta sake yi saboda zuciyanta ya sake tsinkewa jin furucin Fa'eeza, matsowa Fa'eezan tayi daf da ita ta rik'eta, a hankali ta sa hannunta a kasan hab'arta ta juyo da fuskarta tace "Y re u silent all of a sudden? Na tambayeki and you know I demand for an answer, ain't you supposed to be with your husband now?" Hawaye ta gani suna sauka a fuskar Sahr, da mamaki tace "Hey, me ya faru kuma? Fad'a kuka yi?" Girgiza mata kai Sahr tayi tana cigaba da hawayenta, sosai hankalin Fa'eeza ya tashi ganin yadda take ta sheshshekar kuka, girgizata ta sake yi tace " pls sis kiyi min magana, meye ya faru?" Da kyar Sahr ta iya tsayar da kukanta ta juya da kyau tana fuskantar Fa'eeza, d'ago idanu tayi ta zubasu cikin nata tace "Si... sis, I sent him away" cikin rashin fahimta Fa'eeza ta sake dafa kafad'arta tace " Ban gane bah sis, whom did u sent away?" Sai da Sahr ta matse wasu kwallan daga idanunta kafin tace " Sis, wallahi na hanashi, na hanashi tab'ani and now he's hurt, I know he's hurt saboda abunda nayi ba dai-dai baneh, wallahi Fs' eeza I didn't meant to hurt him, banaso in b'ata ran Jaan dai-dai da k'wayan zarra, gashi yanzu na sa ranshi ya b'aci" kuka ta fashe da sosai kamar ranta zai fita tace " I so much hate myself for what I did to Jaan" tana gama fad'in haka ta kwanta a kafar Fa'eeza ta cigaba da aikin kukanta. Ciza leb'e Fa'eeza tayi tana jinjina lamarin, ta sani sosai cewa Khulayd has been longing for this day, tana iya hango hakan a k'wayar idonshi kuma baya tab'a iya b'oyewa, hannu tasa tana bubbuga bayan Sahr a hankali tace " Amma sis me yasa kikayi haka? You knw very well cewa Ya Khulayd bazai tab'a yin abunda bakya so bah, da kin bishi a hankali watakila shi da kanshi zai kyaleki, buh d way u sounded kamar kinyi mishi da fad'a, wanda hakan sam bai dace bah, kinfi kowa sanin cewa baya tab'a iya controlling kanshi when it comes to you, ya kamata kiyi mishi uzuri ko dan dad'ewan da yayi da hakan a ranshi, zaki iya sanyashi a cikin wani hali sanadin abunda kika aikata, besides me a ciki don mijinki ya tab'aki? Is it forbidden? Ain't u guys married? Sis why nah?" Tashi Sahr tayi daga kwancen da take yi ta kallo Fa'eeza tace "Sis, wallahi tsoro nake ji, ina tsoro sis" "Shhhh!" Cewar Fa'eeza, "Banson jin komai yanzu, you'll cheer up now, then go nd apologize to your husband kinji?" D'agowa Sahr ta sake yi tana kallon Fa'eeza, gyad'a mata kai Fa'eezan tayi tace "You'll do just what I said" ta shiga share mata hawayen fuskarta, sannan ta umarceta da ta shiga bathroom ta wanke fuskarta, haka ko tayi, bayan ta fito har powder sai da Fa'eeza ta shafa mata, sannan ta sake spraying mata perfumes tukun ta tura, har ta isa bakin kofa Fa'eeza ta k'irata, a hankali ta juyo ta kalleta, murmushi tayi mata sannan tace " Make sure ya sauk'o" murmushin itama Sahr tayi, sannan ta gyad'a mata kai ta fice.

Direct d'akinshi ta nufa, sai da ta tsaya a bakin k'ofan ta ja dogon numfashi tukunna, gyara zaman rigan jikinta tayi kafin ta murd'a kofan da kutsa ciki d'auke da sallamarta, wutan d'akin a kunne sannan kuma bata ganshi a cikin d'akin bah, wurin bathroom taje ko zata ji k'aran ruwa a ciki amma shiru, hakan ya tabbatar mata cewa he isn't in d room, jiki babu laka ta dawo ta fice daga d'akin da nufin komawa d'akinta, a downstairs taji k'aran TV, a hankali ta lek'a ta hangoshi kwance kan three seated sofa, bata ma san ko bacci yake yi ko idonshi biyu bah, shawaran zuwa ta sameshi tayi don haka ta kama hanyan sauka kasa, a hankali take tafiya har ta k'arasa sauk'a ta isa kusa da sofan, sunkuyawa tayi ta kai bakinta kusa da kunnenshi, " Jaan" ta fad'a cikin wani slimmy voice wanda ita kanta bata san tana dashi bah, shiru yayi bai kulata bah, haka ma kuma bai d'ago ya kalleta bah, bata damu bah don tasan she's at fault, dawowa tayi gabanshi ta inda zai ganta da kyau da murmushi d'auke akan fuskarta ta sake cewa " Jaan" karo na biyu, har yanzu idanunshi a lumshe kamar yadda yake, sosai yaji voice d'inta ya daki kololuwar zuciyarshi, ji yayi kamar ya rungumota ko yaji sassaucin abunda yake ji amma pride da ego sun hanashi kulata, duk da haka he's eager ya sake jin voice d'inta coz it sounds so so romantic, gyara zamanta ta a kasan ta sake yi, a hankali ta janyo hannunshi ta saka cikin nata ta matse gam, kurawa fuskarshi ido tayi tana murmushinta mai kyau kaman yana ganinta, a hankali tace " Jaan, I know am wrong, nasan abunda nayi ba dai-dai bane and I regret it, I could have known better that ba zaka tab'a cutar dani bah, I know you re thirsty of me and u need me to quench that thirst sai nayi disappointing naka, am so sorry Jaan, wallahi I didn't meant to hurt you, I'll never hurt u intentionally because I love you more than my own life, please forgive me Jaan, please" ta kare maganan kamar zata yi kuka, shiru ne ya ziyarci parlor'n na d'an wani lokaci, yayin da duk su biyun suke sake-sake cikin ransu, yana cikin tunaninshi yaji tace "Please kayi min magana Jaan, please... If it's me u want, wallahi gani nan, you can do whatever u wish to do with me, am all yours tonight and forever."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull