Sahr khulaiyd complete - Chapter 4
Sahr khulaiyd complete Chapter 4: Sahr khulaiyd complete Chapter 4. "Come back here you little brat, am not done talking to you yet so don't dare walk out…
4,455 words
"Come back here you little brat, am not done talking to you yet so don't dare walk out on me.... Ki saurareni da kyau 'yan mata, Mr Omair is mine and mine alone, zan iya yin komai akanshi don haka don't stand in my way, so get that stocked in your freaking mind" ta fad'a tana nuna kan Nailah sannan ta wuce
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*DAILY AS'AAL*❓
⚜ *10••••* A ina aka birne Annabi [S.A.W] bayan mutuwarsa❓
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 20*
_Washegari_
Da sassafe Khulayd yayi shirin fita office chikin traditional outfit, manyan kaya ya saka wanda ya bala'in fitting d'insa, ya d'auki jakar laptop d'insa ya fita. Saida ya biya d'akin Mami ya gaidata tukunna yace zai wuce office
"Son bazaka tsaya kayi breakfast bah, nifa banason zama da yunwan nan" yayi murmushi yace, "Aunt its just that I have a lot to do at the office, shiyasa zan fita this early saboda mun fata search for miss OGC, unfortunately tun Monday zuwa yau banga wacce ta dace da zama model bah, but I pray today would be the last day and I pray mu sameta"
"Toh Allah ya taimaka son, off you go"
Ya d'anyi bending tare da pecking nata on the cheek sannan ya fita
Bayan tafiyanshi neh Mami ta wuce d'akin Neenah, kwance ta sameta kan gado tana ta faman baccinta, Mami ta bubbugata "wai Neenah yau bazaki je office bah, its getting late already"
Cikin bacci Neenah tace, "kai Mami yaushe ma garin ya waye?, lemme sleep a little manah"
"Ehen keep sleeping while your boss is already at d office" a firgice Neenah ta tashi zauneh tana kallon Mami "Mami kina nufin Ya Khulayd ya tafi?"
"Ki tsaya tambayata kinji karki tashi ki shirya" ta fitar mata daga d'aki.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_*KHULAYD*_
Zauneh yake kan office chair dake cikin karamin conference room na company'n, ga files masu yawa a gabanshi, bayanshi kuma wani board neh da aka rubuta *SEARCH FOR MISS OGC* da manyan baki, file d'in kuma na d'auke da passports each da kuma credentials na 'yan mata masu neman zama model na Omair Group of Companies, sai dai ya kasa yin komai kasancewar Neenah is absent kuma under department d'inta neh miss OGC takeh
A hankali ya dafe kansa ranshi ya matukar b'aci da rashin zuwanta, kuma he was hoping zasu samu model d'insu yau basai yakai wani week bah kasancewar yau Friday
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_*An hour later*_
Neenah ta shigo conference room d'in kanta a kasa knowing irin halin Mr Omair da abunda zai iya yi mata
To her greatest surprise kuma bayan ta gaisheshi ya amsa bai kuma ce mata komai bah "Can we start?" Ya fad'a yana bud'e first file dake gabanshi
One by one ake kiran 'yan matan amma har suka kare Khulayd baiga wacce ta dace da position d'in bah. Neenah ta mike ta tattara files d'in da stuffs d'inta ta fice leaving him all alone a conference d'in .
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_Da yamma_
Bayan Khulayd ya dawo gidah a parlor ya zauna all worried, Sahr ta sauko sanye cikin dogon rigan English wear wanda yad'an matseta kad'an
Tunda take saukowa ya kafeta da idanu yana kare mata kallo, she's a bit slim kuma tanada flat tummy, batada wani tsayi and she's young, har ta sake dawowa bai daina kallonta bah, sai da ta b'ace da ganinsa yayi taking very deep breathe "Just perfect for miss OGC" ya fad'a putting his mind at ease.
_later that evening_
Khulayd ya shigo d'akin Mami ya sameta tana duba news paper ' _Daily Trust_ , ya zaunah kan stool na dressing mirror'nta yana facing d'inta
A hankali ta sauke paper'n tare da cire medicated glass dake idonta tana kallonshi "Lafia Son, naga kaman you want to share something with me"
"Yes Aunt, wani abu nakeson fad'a miki and please don't say no to my request, you are my very last hope kinji?"
Gyad'a mishi kai tayi, "make your request and I'll grant it to u if its within my authority"
"Aunt pls inaso Sahr ta fara aiki a karkashina, inaso ta zama miss OGC" ya kare maganar eager to hear Mami's response
Shiru tayi for about 5mins kafin tace, "bazance a'a bah son, besides you have the right over her as a brother, kawai ni fatana ka kulamin da little princess d'ita saboda she's still young and batasan me duniya ke ciki bah, make her your baby princess too and take good care of her will you?"
"Na yarda Aunt, just say yes please, she's the perfect model for my company"
"YES" ta fad'a tana dariya, yayi hugging d'inta very tight and not willing to let go off her, da kyar ta iya breaking hug d'in.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*DAILY AS'AAL*❓
Bravo Alaikoum all habibties, you all got the answer right
A d'akin Nanah A'isha[R.A] dake madinatul munawwar aka birne Annabi[S.A.W]
Jazakumullahu bi ahsanil jaza'a ajma'een❣
⚜ *11••••* A cikin sahabban Annabi [S.A.W] Wayene shi Annabin ya girmar har yake amfani da sunan shi [S.A.W] a matsayin mahaifi?
⚜ *12••••* cikin sahabban Annabi[S.A.W] waye aka kira sunanshi acikin Qur'ani kai tsaye❓
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
© *SEEMBY LUFF*😘 ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 21*
_SATURDAY MORNING_
Dukka girls d'in Mami suka nufi gym dake gidansu don yin weekend exercise kamar yadda suka saba every blessed weekend, banda Sahr dake kwance d'aki tana ta faman bacci kamar mai sleeping sickness
7:00am Khulayd ya dawo daga jogging sanye cikin dogon wando da shirt mara hannu, ya nufi d'akinshi direct ya canza towel dake rataye a wuyanshi ya fita zuwa gym d'in shima
Tun a bakin kofa ya hango Neenah da Nailah suna ta faman exercising suna hararan junah because of the incident that happened yesterday
Neenah tace, "ki daina kallona haka fah Nailah, I won't take it if you disrespect me"
"Saiki rike girmanki ai Adda Neenah if u truly want me to respect you" ta kare maganar tana hararanta basu ma kula da love d'insu dake tsaye a bakin kofah bah
'Yar karamar tsaki yaja ya juya yabar gurin coz baison koda ganinsu neh
A balcony'n gym d'in suka had'u da Sahr daketa faman sauri taje saboda tayi latti. Tana ganinshi tayi saurin sadda kanta kasa remembering what she did to him the last time they met "Ina kwana Ya Khulayd" ta fad'a muryanta har yana sark'ewa
Bai damu da amsa gaisuwanta bah yace, "ki sameni a d'akina, I want to talk to you" ya juya yana tafiya. Cikin b'arin jiki ta fara binshi a baya zuciyanta na bugun tara-tara
Jim mutum a bayanshi yasa ya juyo yana kallonta surprisingly, "bazakiyi exercise d'in baneh, nifah bance sai yanzu bah, maybe after you are done exercising"
Ta girgiza kanta, "um um Ya Khulayd, na fasa exercise d'inne, kuma dama Adda Neenah ke sani zuwa gym if not ni bason zuwa nake bah
Ya d'aga kafad'anshi, "as you wish" ya wuce tana binshi a baya to his room
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_*SAHR-KHULAYD*_
Zamanshi yayi a bakin gado yayinda ta zaunah kan doguwar sofa dake d'akin kanta a kasa tana wasa da fingers d'inta.
"How old are you" ya tambayeta yana kallonta
"Am 18" ta fad'a tare da d'ago idonta tana kallonshi, karap idonsu ya faad'a cikin na juna suka tsaya like this for some minutes. Ita ta fara d'auke idonta da sauri da barin kallonshi
Amma shi he couldn't take his eyes off her saboda he finds pleasure looking at her, sai da ya gama kallonta iya son ranshi tukunna yace "Am offering you a job at OGC, Mami ta fad'a miki?"
Da sauri ta gyad'a kanta alamar a'a
A tsawace yace, "talk to me the way I do bawai ki tsaya kina using body parts d'inki bah, guess u re not deaf or dump so open you mouth god damn it"
Jikinta neh ya fara b'ari don ta tsorata da tsawan da yayi mata, "a.....a'a bamuyi magana bah"
"Okay zan offering d'inki aiki as model and miss OGC coz naga kinada view mai kyau, u are a model type so ki had'o min credentials d'inki, zaki fara zuwa office Monday am I clear?"
"Ye.....yes" "Zaki iya tafiya" tana mikewa wayarshi ya fara ringing, kamar Wanda bazai d'aga bah sai kuma ya d'aga yana sauraren mai magana
"Okay I'll be there in a jiffy" ya fad'a tare da hanging up na wayan da sauri ya fad'a toilet don yayi taking bath
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_Some minutes later_
Ya fito cikin shirinshi na kananan k'aya, ya d'auki car key d'inshi ya fito
Benz d'inshi ya fitar daga parking space, maigadi ya bud'e mishi gate ya fita. Wayanshi dake ajiye kan d'ayan seat ne ya fara ringing, without minding d road ya juya yana kokarin leka sunan mai kiran bai kula da katuwar mota dake zuwa direction d'inshi bah
Sai ji yayi sunyi karo, ohhh it has happened, Mr Omair just had an accident
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
A hankali yake bud'e idanunshi har ya waresu completely yana kallon inda yake da mugun mamaki, he was like " _who saved me?_"
Har mutaneh sun fara taruwa suna mamakin yanda accident d'in ya faru kamar magic/sorcery kowa yana tofa albarkacin mouth d'inshi.
Juyowan da zaiyi ya ganta tsaye a tsakiyar titin tana murmushi as always Da mugun mamaki yace "little sis" unbelievingly
Heart talk ta fara mishi which he hears her
" _Am not your little sister, but she did asked me to save you, you can see me as her_" tayi disappering
Wayanshi ya cire ya kira Mami ya sanar da ita abunda ya faru, sannan ya kira driver yazo yayi picking d'inshi
Mami na tsaye da 'yan matanta dukkansu da mugun damuwa a fuskarsu Khulayd ya shigo parlor'n
Suna ganinshi suka yi kanshi suna tambayarshi abunda ya faru. Ko takansu bai biba ya wuce wurin Sahr tare da hugging d'inta very very tight
"Thanks so much for saving my life little sis"
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*DAILY AS'AAL*❓
Kamar yanda amsoshinku suka nuna, Zaid Ibn Harith[R.A] ne sahabbin da Annabi [S.A.W] ya girmar bayan ya zabi Annabin samada iyayenshi har ake kiranshi da Zaid Ibn Muhammad Sannan kuma shineh sahabbin da aka kira sunanshi kai tsaye cikin Qur'ani (Falamma qadaa Zaidun minha.... Ila aakhiri aayah) cikin suratul AHZAAB, aya ta 37
✔Bravo Alaikoum all❤❣
⚜ *13••••*Shekarun Annabi(S.A.W)nawa neh ya rasu❓
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 22*
"Me kakeyi haka ya Khulayd they are looking at us fah, ka sakeni don Allah" tayi whispering only to his hearing
"Little sis this the only thing I can do to show my appreciation, kin ceci rayuwata kuma nagode"
Da kyar ta iya breaking hug d'inta ya mata saboda irin riketa datayi kamar zai sakata jikinshi har da kyar take breathing Kowa a parlour'n ya tsaya kallonsu da mugun mamaki, bama kamar Neenah dakejin kamar ache itace Mr Omair yayi hugging haka, da zata zama d most happiest woman on d planet earth
Sai a lokacin Khulayd yaji kunyan abunda yayi, yad'an sosa keyanshi ganin yanda Mami ta kafesa da idanu tana mishi tambaya da ido, "what's the meaning of this?"
Yayi gyaran murya, "errrm Mami I was just thanking her for saving my life"
Kallon rashin fahimta tayi mishi tace, "ka samu dukka a duhu har ita Sahr d'in I guess, a while ago ka kirani telling me you had an accident, yanzu kuma ka dawo looking all well sannan you re thanking her for saving your life?... Can you please tell me what's happening here huh?"
Ganin zai b'ata lokacinshi wajen explaining mata abunda ke faruwa yasa yayi ignoring maganan, "Its nothing Aunt, kawai there's a lot in my head neh" ya juya ya haura sama abunshi ya barsu kowa yana sak'e-sak'e acikin ranshi.
Neenah da Nailah suka kalli juna totally speechless suna hararan juna, da haka ta kowa ya wuce d'akinshi with many on the mind, banda Sahr wacce warm hug d'in Mr Omair ya tsaya mata a rai.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*KHULAYD*
Shiganshi d'aki ya fad'a kan gado gabad'aya kanshi ya jagule he isn't thinking straight at all, sam yaki believing abunda yake gani right in front of his wai Sahr ce dream girl d'inshi
"Noo this is not true, it can't be her, hakan na nufin itace ke zuwar min a mafarki?, itace ke stopping d'ina when ever I intend to do something bad, nooo bazai tab'a zama gaskia bah" Ya mike ya nufi fridge d'inshi ya ciro giya ya dawo ya zaunah ya b'alle marfin bottle d'in, d'agawa yayi zuwa bakinshi da nufin kwank'wad'a
" *Don't*" muryan da bazai tab'a mantawa dashi ko a mafarki bah yaji
" _meyasa kayi tunanin cewa giya zai kau da tunani nah acikin ranka, drinking is never a solution coz even if you are damn drunk I'll still be in your head... Abunda baka sani bah shine Sahr is me and I'm her but she doesn't know about me, she's your destiny and your wife, you both belong to each other saboda idan babu *SAHR* babu *KHULAYD* .... Your love story is already written and will never be erased_"
"Noo maganarki karyace, tayaya zan fad'a mata ina sonta?"
A part of his heart yace, "you mustn't do that, you can never tell her you love her, karka manta u re Mr Omair, the one with ego, the handsome one and the rich... The one who steps on everyone kuma kai 'yan mata ke bi suna rok'on soyayyanka karka manta haka"
Yayi nodding kanshi like a lizard, "of course am Mr Omair and I must never say to her hearing cewa ina sonta, never!"
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_Washegari...._
Khulayd yayi taking morning shower bayan ya dawo daga gym ya shirya white polo shirt da white ¾ trouser. Kasancewar yau sunday yasa yayi deciding joining su Mami a dining suyi breakfast, ya sauko ya samesu all seated and ready to eat "Morning Aunt" ya fad'a lokacinda yake kok'arin zama kan kujera
"Morning son, yanzu nakeson fad'awa Sahr takai maka naka upstair" yad'an harari Sahr kafin yace, "No need Aunt, zanci tare daku ai yau kam"
Duk girls d'in suka gaidashi ya amsa yana yamutse fuska, barin ma Sahr daya amsata kamar baison maganah. Tsayawa tayi tana kallonshi baki wangalau kamar bashi ya hugging d'inta warmly jiya bah, mutum sai shegen canzawa kaman wahainiya.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Neenah ce tayi serving kowa kafin tayi serving kanta ta koma ta zaunah
Few minutes later bakajin muryan kowa sai k'aaran spoon suna had'uwa da plates. A nutse Khulayd ke cin abincinshi sanin table manners wanda hakan ya baiwa Sahr sha'awa sosai
Purposely tayi dropping spoon d'inta tayi tagumi tana kallonshi cike da sha'awa, babu wanda ya lura da hakan kowa ya maida hankalinshi kan cin abincin da yakeyi.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_Sahr-Khulayd_
Khulayd jin kamar ana kallonshi yasa ya d'ago creamy eyes d'inshi sai cikin nata,idanunsu ya gauraye cikin na juna, ya harareta saboda ba yadda zai mata magana, hakan ya sashi yin heart talking
"Y are u starring at me kamar wata mayya, ko baki tab'a ganin saurayi as handsome as I am baneh" to his geatest surprise yaji tayi responding
"I must confess Ya Khulayd, you re very handsome but hakan bazai sa in kalleka as u are insinuating bah"
"Dat's because I caught u red handed yasa kike fad'an haka, I'll appreciate it idan zaki daina kallona kiyi concentrating kan abincinki"
Tayi 'yar murmushi wanda yasashi murmushin, duk Neenah na lura dasu tana ta saka da warwarewa, hakan yasa tasha al'washin gano duk abunda ke faruwa tsakaninsu.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*DAILY AS'AAL*❓
Y'all right, Rasulullah[S.A.W] died at d age of 63 ✔bravo alaikoum❤❣
⚜ *14••••* cikin matan Annabi[S.A.W] wacece ta yafewa Nanah A'isha[R.A] kwananta❓
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 23*
_Monday...._
Tun 6:00am Mami ta sa Sahr a gaba ta shirya cikin Arabian outfit, tayi rolling scarf dinta mai kyau wanda ya fito da kyauwun fuskarta, light makeup tayi applying which made her look like a sparkling star
Sai 6:30am Khulayd ya fito yayi shirinsa cikin blue-black suit da blue shirt sannan ya d'aura tie same color as the suit, yayi mugun kyau sosai ya sauko parlor rike da jakar laptop d'inshi as usual, a gurguje yayi having breakfast saboda yau za'ayi introducing model a OGC. Tana nan zauneh kan sofa tana jiranshi don tasan definitely tare zasu tafi.
Neenah ta sauko itama sanye cikin wani matsatstsen gown na English wear taci heavy makeup, tahau wani ubansu takalmi heel tana rike da handbag d'inta 'FS', wurin Sahr dake zauneh ta nufa tana murmushi "Kid sis tashi muje kada muyi latti, kinsan Mr Omair hates late coming"
Khulayd na kallonsu har lokacin yana sipping coffee baice dasu komai bah saida ya bari suka isa bakin kofan parlor'n yace, "And where do you think you are taking her to Neenah?"
Cak suka tsaya both babu wacce ta sake taking a step forward, suka juya suna kallonshi, Neenah ce tayi karfin halin cewa "Mr Omair I tot office zataje shine nace mu tafi tare, saboda ranan kacemin bakason driving da mutum a gefenka"
"Ranan kikace ai but not today, and beside ranan kece banaso ki zaunah gefena hope you get me now.... Zaki iya tafiya and make sure you ain't late"
Jiki babu lak'a Neenah ta fita tana mamakin halin Khulayd, meyasa baya sonta har haka? What has she ever done to him?, "this hatred will surely turn to love so soon" ta fad'a a zuciyarta.
Saida ya gama k'urbe coffee'n tas tukunna ya mik'e ya d'auki jakar laptop d'inshi yayi gaba. Daidai bak'in kofa inda Sahr ke tsaye yazo wucewa, a hankali ya rak'ub'e ta gefenta ya wuce without saying a word to her. Sai da ta bari ya wuce tukunna itama tabi bayanshi, lokacin har driver ya fitar da mota
Sahr ta zagaya zuwa d'ayan b'angaren zata bud'e kofan, ta d'aura hannunta shima ya d'aura nashi, wani electrification suka ji both tun daga tafin kafansu zuwa tsakiyar Kansu,a hankali Sahr ta d'ago brown eyes d'inta ta zubasu cikin nashi suka shiga kallon idon junah
Ita ta fara sauke idonta ta d'aurasu kan hannunshi Wanda yake fari tas, ga zara-zaran gashi da suka kwanta luf akai. Saida ya kalleta to his own satisfaction kafin yace, "Ki daina kallar min jiki 'yan mata, nasan zakice I have a nice body tunda u've once saw me naked... Anyways thanks"
Da mugun mamaki ta tsaya kallonshi, wato shi ya sata a gaba saida ya k'are mata kallon yanzu kuma ga abinda yake cewa?, "lallai Ya Khulayd d'innan mugun d'an rainin hankali neh" ta fad'a in her heart. A hankali ta zare hannunta daga jikin motan tad'an yi baya kad'an, yayi murmushi kafin ya bud'e ya shiga, saida ta zagaya d'ayan side d'in ta shiga.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_7:15am_ Suka isa office d'in, Sahr sai bin building d'in takeyi da ido don ya amsa sunan gini mai kyau kam. Office 'dinshi suka nufa kai tsaye yayi mata izinin zama. Sai bayan ya gama abunda zaiyi tukun ya d'ago kai yana kallonta, karaf idonsu ya had'u saboda tunda suka shigo taketa aikin kallonshi Clapping hands d'inshi yayi daidan idonta tayi blinking a firgice "Just admit bazaki iya daina kallona bah, zan iya miki uzurin haka but unfortunately barin iya barinki bah so stop it will you"
A kunyace ta sauke kanta tana wasa da yatsunta, ya girgiza kanshi kawai yana duba wasu files "Nasan you know what model means ryt?" Ya tambaya
Da sauri ta gyad'a kanta "ye....yes sir na sani"
"Good, from now on kece model d'inmu kuma miss OGC, meaning every item da muke producing hotonki neh zai zama akai, just like a celebrity you'll be provided with just everything, make sure you give OGC your best"
Tunda ya fara magana ta kafesa da idanu tana kallon yadda lips d'inshi ke moving a yayinda yake furta kowace kalma one after d other neatly, ta d'an lank'wasa kanta kad'an tana kallonshi with a smiling face.
"Do you understand?" Ya fad'a lokacinda yazo karshen maganarshi, but hankalinta gabad'aya baya kanshi. Da mamaki yake kallonta yanda take kallonshi bata ko kyaftawa
Mikewa yayi daga kujeranshi ya karaso har gabanta, gab da fuskarta ya matso da nashi har tana iya jin saukar numfashin sa akan fuskarta, ratan da yake tsakanin lips dinsu kuwa bai kai inchi d'aya bah
Tanajin saukar numfashinshi kan fuskarta tayi firgigit a tsorace da sauri ta mike daga zaunen da takeyi "What's the meaning of this ya Khulayd, me kake kokarin yi ne haka?"
"Karki mayar dani mai karamin kwakwalwa manah little miss OGC, you were busy looking at my lips while ina miki magana, dama na baki domin maybe you'll never have it bayan wannan, so kiss me" A tsorace ta sake taking one step backward jikinta na rawa sosai, "Ya bbbbb...bafa haka baneh, kawai ina....."
"Oh don't give me dat excuse little sis, that's what you want kuma ina baki dama neh, just kiss me ki cire maitanki a kainah, karki damu da cewar am your boss, am all yours for now, you can kiss me for as long as u want"
Takaici da tsoro neh suka kamata ta fara yin baya, every stepping backward da tayi shima sai yayi stepping forward har suka k'ure bangon office d'in ya shiga sunsunarta yanda yaga dama,ya sake kawo lips d'inshi kusa da nata tayi saurin kawar da fuskarta
"I said kiss me" ya fad'a a tsawace har sai da ta kusan sakin fitsari a tsaye "You asked for it kuma wallahi baki isa kiyi shunning kiss d'ina bah so do it"
Gagam ta runtse idanunta ta juyo da fuskarta all willing to do as he said because she had no choice, saura kad'an lips d'insu yayi collabo Neenah ta turo kofar office d'in
Da sauri Khulayd yayi baya ita kuma ta sauke nauyayyen ajiyan zuciya tana godewa Allah daya kwaceta a hannunshi
With lots of surprise Neenah ta tsaya kallonsu totally speechless tanason gano wani abu a idanunsu both
"Excuse me, I want to use the toilet" Sahr ta fad'a sannan ta fice jikinta yana rawa sosai.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*DAILY AS'AAL*❓
Hakaneh, Saudat Bint Zam'ah[R.A] itace ta yafewa Nanah A'isha (R.A) kwananta
⚜ *15••••* A cikin matayen Rasulullah [S.A.W] wacece yake yawan ambaton ta da yabonta duk da bata raye❓
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 24*
Khulayd ya juya zuwa kujeranshi feeling a bit guilty, Neenah ta matso gaban table d'in ta tsaya tana kallonshi tukunna tace "Mr Omair meke faruwa neh?"
"A ina kenan? Ko kinga wani abu ya faru neh kike tambaya?"
Ta zaunah kan d'aya daga cikin kujerun without him giving her permission to sit, "Nazo na ganka da little sis a tsaitsaye, kuma fuskanku both were looking worried, ko zan iya jin meye faru?"
"What" ya fad'a a tsawace "I can't remember hiring you as a lawyer and waye ya fad'a miki kin kai matsayin wacce zata tambayeni such a stupid and silly question miss? What's your problem really?" Ya fad'a yana kallonta sama zuwa kasa
"Mr Omair don't get me wrong, kawai naga kamar I have the right over you both tunda ita sister tace and you are my brother also"
"Didn't I warn u chewa kar ki nuna we are somehow related anan?, bakida damn right kiyi meddling acikin personal life d'ina hope zakisa wannan cikin karamin k'wak'walwarki, wannan office neh so pls let's discuss business"
Ba haka Neenah taso bah, taso ace zai bata koda wani clue ne dazai tabbatar da zargin da takeyi amma ba yadda ta iya, dole ta kawar da zancen ta kawo office issue
"Boards sunyi arriving d'azu and all department heads suna jira ayi presenting musu model, the meeting is already scheduled 10:00am a 3rd floor conference room, kai kawai ake jirah Mr Omair" ta kare maganar tana kumbure-kumbure. Khulayd zaiyi magana Sahr ta shigo office d'in kanta a kasa, da ganinta zaka san har yanzu a tsorace take da abunda ya faru d'azu
Khulayd bai ko kalli inda take bah se faman tattara files dake gabanshi yakeyi, ya mike tare da cire suit d'inshi a jikin hanger ya saka, yana gyara zaman tie d'inshi yacewa Neenah "Zaki iya tafiya, we are after you"
Bataso hakan bah amma tana tsoro zai iya disappointing d'inta a gaban Sahr, ta juya rai a b'ace ta fitar musu daga office d'in. Sai a lokacin ya kalli inda Sahr ke zauneh "Yanzun zanje inyi presenting d'inki gaban boards so don't do anything stupid and ruin my plans, kina jinah?"
Tayi saurin gyad'a kanta, "eh naji" ta fad'a a takaice
"Follow me" ya fad'a lokacinda yake kokarin zuwa bakin kofa, a hanzarce ta mike tana gyara fuskanta da zaman scarf d'inta ta isa wurinshi.
Hanunshi yasa tare da zagaye 'yar karamar k'ugunta ya janyota ta fad'a k'irjinsa, tayi saurin runtse ido tare da zagaye hannunta a wuyanshi gudun karta sha k'asa. Mr Omair ya k'urawa cute small lips d'inta ido yana sak'e-sak'e a cikin mind d'inshi, ita kam ta gama sadakarwa yau Ya Khulayd zai shanye mata bakinta kamar yadda take gani a movie.
Chan yakai bak'inshi kusa da kunnenta "About that kiss, we are not done yet" ya mata whispering yana dariyan mugunta kafin ya saketa ya fita, tayi nauyayyen ajiyar zuciya kafin ta bishi a baya.
Elevator suka nufa, bayan sun shiga Khulayd yayi pressing wasu digits wanda in no time sai gasu a 3rd floor'n company'n
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_*3rd floor conference room*_
Security man dake tsaye bakin k'ofan conference room d'in yana ganin Mr Omair yayi saurin bud'e k'ofan tare fad'in "welcome sir".
Kai kawai Khulayd yayi nodding ya wuce ciki, little princess na biye dashi a baya har inda zasu zaunah, itakam sai feeling uncomfortable takeyi saboda taga all eyes on her kuma bata tab'a zama gaban mutane dayawa haka bah, har wani rawa jikinta yakeyi "Ya Allah plea help me out" abunda take maimaitawa a zuciyanta kenan taji wani strange voice same as khulayds yana fad'a mata " _feel at ease sweetheart, you can do this *AM HERE FOR YOU*_ "
A hankali taji duk tsoro da fargaban da takeyi ya gushe, sai ma kamar an bata courage da confidence. Ta d'ago kanta a hankali tana kallonshi, sai taga attention d'inshi baya ma kanta "Waye yamin magana toh?" Ta fad'a tana wondering
Khulayd ya bud'e first file dake ajiye gabanshi kafin ya mik'e zuwa stage ya tsaya gaban mike, ya maida kallonshi kan d'and'azon mutanen dake conference room d'in ya fara speech kamar haka: "As y'all already know, many have happened here at OGC which includes my immerging as the new CEO and impeaching of the model/miss OGC Miss Safreen Ishaq, we've spent almost 2 weeks in search of who'll become the new miss OGC.... Today I'll present to you the model OGC will forever be proud of. Ladies and Gentlemen, I give u Sahr Muktar the new model and miss OGC"