Sahr khulaiyd complete - Chapter 6
Sahr khulaiyd complete Chapter 6: Sahr khulaiyd complete Chapter 6. "Ya Khulayd" ta fad'a happily but still in tears, Khulayd ya tako a hankali ya zaunah…
4,415 words
"Ya Khulayd" ta fad'a happily but still in tears, Khulayd ya tako a hankali ya zaunah bakin gadon, zamanshi keda wuya Sahr ta fad'a jikinshi tayi hugging d'inshi. Da kyar Khulayd ya iya breaking hug d'in da tayi mishi ya d'ago fuskarta yana kallo "Meya saki kuka kuma baby doll, ko ciwon cikin neh ya dawo?"
Tayi saurin maida kanta jikinshi tana girgizawa, "ba kai baneh ka tafi ka barni" ta fad'a a shagwabe tana sake rik'eshi, hugging d'inta back Khulayd yayi yace "Kiyi hakuri I had a lot to do at the office shiyasa na tafi, amma ai gani na dawo yanzu". Sahr tayi shiru a jikinshi duk su biyun suna sauraran heart beats na junansu.
Khulayd yayi ajiyar zuciya, a zuciyarshi yace "I missed you" Abun mamaki yaji tace "I missed you too" a zuciyarta. Neenah kam bushewa tayi a wurin kamar statue, gabad'aya Khulayd ya mugun bata mamaki, tayi murmushin yak'e a zuciyarta tace " *Sahr-Khulayd* "
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*DAILY AS'AAL*❓
⚜ *20••••* cikin sahabban Rasulullah(S.A.W) waye ya sak'i mata kuma annabi ya aurah?
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 29*
Zuciyar Neenah gabad'aya ya jagule bataso ta gaskata abunda zuciyarta ke gayamata, a sanyaye ta mik'e zata fita har ta kai bakin k'ofa ta sake waiwayensu but babu wanda yayi breaking hug d'in tsakanin Sahr da Khulayd.
A fusace ta murd'a kofan ta fita tare da banging musu kamar zata b'alle kofan, gabad'aya idanunta sun rufe don takaici ta k'asa ganin Nailah dake k'okarin shiga d'akin Sahr d'in itama don dubata, sai kawai taji ta bank'e mutum
Angrily Nailah ta shiga kallon Neenah kamar taga worst enemy d'inta kafin tace, "Wai Adda Neenah bakiya ganin gabanki neh saiki wani bank'e mutum... Na lura tunda kika san cewa I also had a crush akan ya Khulayd kikayi developing hatred min koh?, toh lemme warn u for d last time ki fita harkata haba!" Tayi exclaiming
Neenah da jikinta yake a sanyaye tayi murmushin yak'e tace, "take it easy baby sister, idan k'ika tambayeni did I lost my mind mah amsan zai zama capital YES because I did lost my mind, ke kuma idan har da gaskeh kina son Mr Omair kamar yadda kike ikirarin kina yi toh am sure you'll go mad if you see what I saw, barin ji haushinki bah yanzu just go in and find out for yourself" tana gama fad'an haka ta rab'e ta gefen Nailah hadi da cewa "Excuse me" tayi tafiyarta.
'Yar karamar tsaki Nailah taja sannan a hankali ta murd'a k'ofan tana tunanin meye Neenah ta gani ya d'aga mata hankali haka, tana tura kofan tayi arba da Sahr kwance comfortably tana bacci shima ya rik'eta very tight har yana gyangyad'i. Dumm! Taji zuciyarta yayi beating coz she couldn't believe what she's seeing right in front of her, saida tayi da gaske kafin ta iya controlling kanta ta karasa cikin d'akin
"U'um" tayi gyaran murya wanda yasa Khulayd bud'e idonshi da sauri shi kanshi baisan sanda ya fara gyangyad'in bah. Yayi feeling a little bit guilty, a hankali ya raba Sahr da jikinshi ya kwantar da ita sannan ya mik'e without even lookin up at Nailah zai wuce
Nailah da k'arfin da Allah ya bata ta juyo da Khulayd, bai ankara bah yaji ta had'a musu baki ta shiga kissing d'inshi as if zata cinye bakin. Da k'arfi Khulayd ya turata har tana neman fad'uwa ya sake kifa mata mari har saida ta fad'i a kasa ta buga kanta da bedside drawer, without saying a word ya fita ya barta dafe da kuncinta. Duk da Marin da Khulayd yayi mata baisa ta saduda bah ta bishi a baya.
A balcony ta ga bayanshi yana tafiya tayi saurin k'iran sunanshi da k'arfi "YA KHULAYD", cak Khulayd ya tsaya ba tare da ya juyo bah itakuma Nailah tayi tattaki tazo ta tsaya a bayanshi
In tears ta fara magana "Ya Khulayd why?, meya ka tsaneni har haka?, me na tab'a yi maka a rayuwa that I deserve this hatred?, a kullum inaso in nuna maka cewa ni masoyiyarka ce kuma nafi kowa cancantar soyayyarka but ka kasa fahimtata, yanzu am giving you myself, jikina amma haryanzu baka damu bah duba da cewa ni mace ceh why?" Ta kare maganar tana kuka
"Kinsan me?" Cewar Khulayd but bai bari ta amsashi bah ya cigaba "I kinda hate if if its d woman that do the courting"
Cikin muryan kuka tace "and y did u shunned my kiss?"
Saida Khulayd yayi dariya kafin yace "sabida bana tsammanin kin iya brushing mah, and I'll advice that you see a dental surgeon coz your mouth smells like trash" yana kaiwa nan ya tafi ya barta tsaye da mugun mamaki kwance kan teary fuskarta.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_*Khulayd*_
Bayan ya shiga d'aki yayi wurgi da jakar laptop d'inshi saman gado yayi undressing kanshi ya fad'a toilet don taking shower, a zuciyarshi yana kyamar halin Nailah da har zata iya uselessing kanta a gaban namiji, how could she stood so low?, shikam yaga 'yan mata dayawa masu irin haka in d outside world but bai tab'a tsammanin matan arewa zasu iya bah, da tunanin nan ya gama wanka.
Jallabiya kawai ya zura ya fad'a kan gado yana kallon ceiling, a hankali ya lumshe idonshi yana feeling wani emptiness da loneliness
"Why do I feel empty when she's not in my arms?, why do I miss her idan bata tare dani?, meyasa nakeson ganin fuskarta kowani second daya wuce?" Ya tashi ya zaunah tare da crossing hands d'inshi zuwa shoulder'nshi
" _Dude, you are in love, ka daina wahalar da kanka a tunanin banza, you two are destined for each other shiyasa kake feeling incomplete idan bata kusa da kai.. Ka aureta kawai ka huta man_ " ya tsinkayo muryan 2nd Khulayd.
Bai damu da bud'e idonshi bah sanin cewa ko ya bud'e bazaiga mai voice d'in bah, a hankali ya furta "I love you baby doll kuma lokaci yayi da zaki Sani, I can't deny it anymore, you are a part of me and am incomplete without you"
Nan mah voice d'in yace " _Bravo alaik, shine abunda ya kamata kayi coz Khulayds are not cowards_ "
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_Nailah_
Gabad'aya b'arin fuskarta ya turning red tsabar marin da Khulayd ya kifa mata, babu abunda yafi k'ona mata rai kamar furucinshi na karshe
" _I advice dat you see a dental surgeon coz you mouth smells like trash_ "
Tayi murmushin yak'e tace "Khulayd you re mine kuma babu wanda ya isa ya hanani mallakan ka, not even yourself kuma this trash mouth of mine koh, ...................."
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*DAILY AS'AAL*❓
20-Zaid Ibn Harith (R.A) shine ya saki Zainab Bint Jahsh(R.A) kuma manzon Allah (S.A.W)ya aureta don cika umarnin Allah (S.W.T) Duba cikin suratul Ahzaab don karin bayani.
❣❣❣❣❣❣❣❣❣
*21••••* cikin matayen Rasulullah(S.A.W), wacece tafi karb'o hadisai❓
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 30*
A hankali Sahr ke farkawa daga long sleep da tayi, all her life kuma da wayonta bata tab'a samun a very peaceful sleep kamar irin na yau bah and its because ta yishi a jikin Khulayd. Jinta takeyi extremely happy idan tayi recalling moments da sukayi sharing some hours ago, sallah'n magrib da aka kira neh yasa ta mik'ewa daga kan gadonta ta fad'a bathroom, saida ta fara yin wanka kafin ta d'auro alwala ta fito bayan tayi 'yan shafe-shafenta ta saka simple dogon riga sannan ta shimfid'a darduma don yin sallah. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ A sanyaye Nailah ta turo k'ofar d'akin Neenah ta hangota zauneh toward her bed end ta dafe kanta, Nailah ta karisa shigowa d'akin ta zaunah d'an nesa da Neenah kad'an. Jin alamar mutum a gefenta yasa ta d'ago kanta a hankali idanunta suka sauka kan Nailah, take yanayin fuskarta ya chanza ta had'e rai tana harararta "What now huh Nailah?, kinzo ki sake adding min ciwon kai akan wanda already nakeda shi koh?... Toh please get out coz I don't have time for that" ta fad'a tare da sake dafe kanta.
Cike da damuwa da rashin nuna b'acin ran kalamun Neenah duk da ya d'anyi hurting d'inta Nailah tace, "Adda Neenah am not here to exchange words with u, nazo neh in tambayeki one simple question kuma ina fatan samun amsa" rashin kulata da Neenah tayi yasa ta cigaba "Me kikayi observing tsakanin Ya Khulayd ko kuma in che Mr Omair kamar yadda kike k'iranshi da kid sister Sahr, ain't they acting strange?" Da sauri Neenah ta d'ago kanta tana kallon Nailah "Ina observing d'insu tun first day da Khulayd yazo gidannan, kece dai da brain d'inki bai functioning kika k'asa ganin haka, and now that you've start to observe them acting strange saiki nemi hanyar da zaki tsirar da soyayyarki and don't dare ask me of any help because am not stupid to help you, karki manta we are competing to win his heart". Gabad'aya Nailah ta gama karaya da al'amarin, ita dai tasan tanason Khulayd but what if Sahr yakeso?, she loves Sahr enough that she can sacrifice all that she have for her, a sanyaye ta sake mik'ewa ta fita daga d'akin Neenah tana saka da warwara, "Saina tabbatar da zargina tukunna zanyi taking measure" abunda ta fad'a a zuciyarta kenan. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Washegari 7:00am Khulayd ya fito don tafia office, sai da ya sauk'o downstairs yaga wayam babu Sahr a inda take zama ta jirashi. He couldn't take any step forward kuma ya sake juyawa ya nufi balcony d'in d'akinta. Tashiwanta daga bacci kenan don tun jiya tayi deciding bazata office yau bah, sanye take cikin baby pink sleeping dress mai d'auke da hoton mickey mouse a hankali tayi juyi daga kan gadon ta koma baki ta zaunah tana 'yar mik'a, kafeta da idanu Khulayd yayi don about a minute kenan da shigowanshi d'akin ya hard'e hannaye a k'irji yana kallonta yana tsaye nan bakin kofan. A hankali ya saki wani lafiyayyen smile saboda tun jiya idanunshi suke kewar ganinta, "baby doll har kin tashi?" Ya fad'a ba tare da yabar bakin kofar bah, da sauri Sahr ta juyo don ita bata masan akwai mutum a wurin bah, with lot of surprise ta tsaya kallonshi kafin tayi saurin sadda kanta k'asa "Gud morning Ya Khulayd" ta fad'a ciki-ciki, yad'an kwaikwayi muryanta da salon maganarta ya amsa gaisuwan ya k'ara da fad'in "Y are u not dressed up for office?, kinsan banason late coming" A sanyaye tace "Ya Khulayd wallahi bazin iya zuwa bah, har yanzu cikina na ciwo fah.." Khulayd yace "oh I almost forgot, ashe fa baby doll tana period" ai Sahr tanajin haka ta tashi ta shige toilet da gudu tana jin kunya. Khulayd yayi dariya yana girgiza kanshi, "at least I've seen your morning smile" ya fad'a tare da k'ullo mata kofan a hankali sannan ya k'ara da cewa "am gonna miss u at the office".
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
The answer to question 20 is A'ishat Bint Abu-Bakr (R.A)
Barakallahu feekum wa jazakumullahu bil jannah ajma'een 💚💙💜💚💙💜💚💙💜
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 31*
Gabad'aya sai Khulayd yaji babu dad'i, ji yakeyi kamar a part of him is missing don kawai Sahr bazata bishi office bah duk da cewa they only went to the office together sau 3 tunda ta zama miss OGC but he's feeling like they always go together, nan take kishin Sahr as miss OGC ya k'amashi ace the girl he's in love with kuma future wife d'inshi za'a rik'a lik'a hotunanta jikin every item na OGC sannan kowani tsami gaye ya ganta? "Bazai yiwu bah" cewar Khulayd as he is walking towards the car, duk wannan tunanin ya yishi neh kafin yabar gidan. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Koda yaje office bayan ya gama settling kanshi ya kunna laptop d'inshi ya shiga duba ayyukan da ya kamata ya yisu tun jiya, shigowar wani email neh yayi interrupting d'inshi daga aikin da yakeyi, daya duba yaga secretary d'inshi ceh tayi emailing d'inshi " _sir, I kept some documents on your table, they need to be signed before 9:00am_" tsaki Khulayd yaja kafin ya ture laptop d'in gefe ya jawo files d'in gabanshi, a hankali ya cire pen daga aljihun suit d'inshi ya bud'e first file d'in yayi signing without reading its content, jawo second file d'in yayi har ya d'aura pen d'in kan inda zayyi signing da sauri kamar an mintsileshi ya d'ago kai yana kallon sofa'n da Sahr ke zama idan sunzo office ya ganta zauneh ta sa hankalinta gabad'ai a kanshi tana jefa mishi wani smile mai kayatarwa.
Khulayd baisan lokacinda yayi dropping pen d'in hannunshi bah ya mik'e da mamaki yana cigaba da kallonta har ya iso gurin sofa'n, a hankali ta mika mishi hannunta tana lumshe ido alamar "take my hands" d'innan, har jikin Khulayd na rawa yayi stretching out hannunsa da nufin tab'aata yaji wayam yana tab'a Iska, da sauri yaja da baya still ya kallonta, take wani sanyi da iska ya mamaye office d'in har peppers dake kan table d'inshi suna flying, a cikin iskan ya tsinkayo voice d'inta ta whispering mishi " _I love youuu_ ", cak iskan ya tsaya. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Murmushi yayi can k'asa k'asa yace " I love you more" ya koma kujeranshi ya zaunah, sai da ya gama signing files d'in gaba'daya ya d'auki landline mai amfani da simcard ya shiga dialing digits na d'akin Sahr, a hankali ya koma ya jingina da kujeran tare da lumshe idanu. Sahr ta kwance ita k'ad'ai a d'aki taji landline dake saman kanta yayi kara, da kamar bazata d'auka bah sai kuma ta d'aga ta k'ara a kunnenta "Salamou Alaikoum" ta fad'a cikin slimy voice d'inta. Saida Khulayd yayi wani nauyayyen ajiyan zuciya lokaci d'aya yaji ya samu peace of mind, a kasalance ya amsa sallamarta kafin yace, "baby doll kina Lafia" a shagwab'e tace " _um um bani da lafia Ya Khulayd_ " "OMG! Haryanzu ciwon cikin neh?" Ya tambaya cike da damuwa, " _ba ciwon ciki bah Ya Khulayd, am missing you around, ka dawo gida manah_ " cewar Sahr, a hankali ya fara lallab'ata ganin kamar so take tayi masa kuka, "baby doll kinsan bazin iya barin office yanzu bah but I promise you lokacin tashi nayi I'll not waste even a minute, and get prepared coz am gonna tell you something of extreme importance today" haka ya rinka bata baki har ta hakura, daga karshe yace "take care of yourself for me, I lo...." Da sauri yayi hanging up gudun kar taji heart secret nashi yana ta blushing alone in the office. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_*kuyi hak'uri for rashin posting da banyi bah 2days ago, I was busy at my friends wedding ceremony neh dats y*_❤❣❤❣
*DAILY AS'AAL*❓
⚜ *22••••* Idan ana Aadhan(kiran sallah), yana da kyau musulmi ya fad'i duk abunda Mu'adhdhin(mai kiran sallah) ya fad'a, saidai gurin 'Hayya alas-salah' da 'Hayya alal falah', me ake cewa a dai-dai wannan gab'ar❓
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 32*
_6:00pm_ ya tashi daga office as usual ya tattara stuffs d'inshi ya fito, ko minti d'aya bai k'ara bah as he promised ya samu driver na jiranshi a mota ya shiga suka tafi. On their way back home Khulayd ya hango wani d'an karamin wurin sayar da cards da flowers yayiwa driver umarnin su k'arasa wajen, bayan driver'n yayi parking Khulayd ya fito cikin takunshi na kasaita, fuskarshi d'auke da murmushi mai kyau wanda ya k'ara mishi annuri ya nufi cikin wurin, a hankali ya shiga zagayawa yana duba flower'n da ya dace da baby doll d'insa daga k'arshe ya hango wani an k'ulleshi cikin glass da light yana haskawa, a hankali ya taka ya matsa kusa da glass d'in dake ajiye chan corner'n shop d'in ya bud'e carefully ya cire, yellow and green color neh sai ya matukar burgeshi, da ya matsar kusa da hancinshi yaji wani fragrance mai dad'i ya fitowa within d flower hakan ma ba karamin burgeshi yayi bah, ya nufi inda ake biya ya biya cash d'in ya dawo mota sannan driver yayi starting car d'in suka tafi. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ On reaching home stairs ya nufa ya wuce d'akinshi direct, bayan yayi undressing kanshi yayi freshen up ya fito ya saka light kayan shan iska. Sai after isha' prayer ya k'irata, bayan ta d'aga bai bari tace komai bah yace "Meet me at the garden" ya katse wayan, a nutse ya d'auki flower'n with a smiling face ya nufi other balcony door dazaiyi leading d'inshi zuwa garden d'in, wurin ya matukar burgeshi kuma ya chanza coz tun zuwanshi bai samu time d'in zuwa bah, wani couch ya zaunah akai fresh air'n garden d'in yana ratsa every outermost part of his body. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Sahr ta fito daga d'akinta cikin takunta mai yauk'i wanda yafi kama da wahainiya, a nutse itama tabi hanyar da Khulayd yabi ta b'ulla a garden d'in, kasancewar couch d'in da Khulayd ke zaune akai yana facing kofar yasa tayi saurin sadda kanta k'asa saboda irin k'warjinin da yayi mata lokaci guda shyness yayi overtaking d'inta. Kanta a k'asa har ta karisa ta zaunah same couch da yake zaune akai but a bit far from him, a hankali Khulayd ya matso kusa da ita yana kallonta, yayi murmushi ganin she seemed uncomfortable with him around. "Baby doll" ya kira sunanta in a very cool voice, Sahr bata d'ago kai bah tace "uhum" ya rik'o hannunta tare da saka mata flower'n a hannunta ya mayar da hannunshi ya hard'e a kirjinshi yana son ganin how her reaction will be. Sosai ta ware idonta tana kallon hannunta happiness ya lullub'e ilahirin zuciyarta, "is this for me Ya Khulayd?" Ta tambaya eagerly, Khulayd yayi murmushi kafin yace "yes baby doll, don't u like it?" Tayi saurin nodding kanta " I don't like it Ya Khulayd, but I love it" ta fad'a still kanta a kasa.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
"Sahr" ya sake kiran sunanta in d second place sadai this time bata amsashi bah, ya kai hannunshi karkashin chin d'inta ya d'ago fuskarta tayi saurin rufe idonta, "open your eyes and look into my eyes" yayi demanding, a hankali ta fara bud'e idon har ta gama bud'esu gabad'aya sai cikin idanunshi da babu komai sai zallar soyayya, passionately suka shiga kallon cikin idanun juna for some minute sannan Sahr ta sake kulle idanun da sauri, Khulayd yace " *I love you* " whole hearted, sai ganin Sahr yayi ta mike da gudu tabar gurin, a sanyaye shima ya mik'e yabar garden d'in zuwa d'aki with so much stocked on his mind.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Banging kofan d'akinta tayi without closing it ta fad'a kan gadonta tana maida numfashi tana dafe k'irji, shiru tayi daga kwancen da takeyi kalamun Khulayd na karshe yana mata yawo a kanta, she don't really know what to feel now that Khulayd has finally revealed to her his heart secret. " _don't give that a second thought Sahr, kiyi accepting soyayyarshi before its too late_ " Sahr ta tsinkayo voice d'in d'ayar Sahr da bata gani, kamar an mintsileta ta d'auki landline d'inta itama tayi dialling number'in d'akin Khulayd.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Yana kwance kan tangamemen gadonshi yana tunani, tsoronshi d'aya kar Sahr ta ki accepting d'inshi yaji wayar na k'ara, a sanyaye ya d'aga thinking that Mami ce ke kira, tsinkayo muryan Sahr yayi tana fad'in " nima ina sonka, I love you... I love you too Ya Khulayd". ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*DAILY AS'AAL*❓
22- answer is 'La haula wala quwwata illa billah' Bravo Alaikoum all😘😍
⚜ *23••••* cikin wani surah Ayat-al- Qursiyyu yake, kuma shi aya na nawaneh a cikin suran❓ ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 33*
Khulayd kamar an sakar mishi ice block yakeji a cikin zuciyarshi, wani farin ciki marar misaltuwa ya tsinci kanshi a ciki, yanzu yana da tabbacin ruling zuciyar Sahr ya fad'a kan gado tare da lumshe creamy eyes d'inshi yana smiling.
*Sahr* hugging landline d'in tayi gabad'aya tana murmushinta mai kyau but still can't believe Khulayd ya furta yana sonta she feels like the happiest woman on earth, bata tab'a tsammanin wannan ranar zata zo bah. A hankali Neenah ta turo kofar d'akin Sahr don suyi magana one on one da ita, surprisingly ta ga Sahr rungume da landline tana ta blushing ita kad'ai, har abun yaso bawa Neenah dariya tadai lallab'a ta karasa cikin d'akin Wanda Sahr bata masan da zuwanta bah sai ji tayi an dafa kafad'arta. A tsorace ta juyo har zata fasa ihu taga Neenah ce, saida tayi taking very deep breathe kafin tace, "Allah Adda Neenah you scared me, I was about to scream coz banyi noticing shigowanki bah ai" Neenah tad'anyi murmushin yak'e tace "Ai dama you won't notice me tunda gashi you re hugging a landline and blushing kamar wacce tayi gamon katar" A kunyace Sahr tayi dropping landline d'in a saman gadonta sannan ta zaunah wanda hakan yasa Neenah zama as well, sai dai ta fasa yiwa Sahr question d'in da tazo yi mata coz she's eager to hear what is making her baby sister to blush again and again.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ _8:30pm_ suka hallara a dining area for dinner, yau kam Mami ce tayi serving 'ya'yanta dukka sannan daga karshe tayi serving kanta ta koma ta zaunah, babu wanda yayi wa d'an uwanshi magana sai ma kowa yayi rinsing hannunshi suka fara cin abincinsu a nutse. Sahr gabad'aya ta kasa samun nutsuwa taci abincinta don wani nauyi da kunyan Khulayd da takeji, ji takeyi bazata iya cin abinci with him around bah. Hannu biyu Khulayd yayi a plate nashi ya d'ago kai yana kallon baby doll d'insa yaga sai wasa da abincin takeyi bata iya tayi koda loma d'aya bah, cire hannu Khulayd yayi acikin abincin harda yin tagumi da left hand d'inshi yana kallonta, jikinta neh ya bata ana kallonta ta d'ago brown eyes d'inta sai cikin nashi, da sauri ta sadda kanta k'asa ta juyar da fuskarta gefe ta fara heart talking "Ya Khulayd please ka daina kallona haka, you re making me feel uncomfortable with that look fah" Murmushi Khulayd yayi shima ya mata responding a zuciyarshi "Why won't I stare at you baby doll tunda gashi kinsa abinci a gaba kina wasa dashi, kici manah"
"Ya Khulayd bazin iya cin abincin bah idan kana kallona haka Allah" cewar Sahr Khulayd yace " please eat baby doll, banason zama da yunwan nan, kici koda kad'an neh kinji" Ta marairaice fuska but still heart talking sukeyi, " not until you say you love me, I want to hear it one again" Khulayd yayi murmushi yace " you'll hear it not once but again and again, look up at me and read my lips", a hankali Sahr ta d'ago kanta ta kalleshi " I LOVE YOU" ya fad'a a fili amma voice d'inshi bai fito bah yayinda Sahr kuma take reading lips d'inshi, unfortunately Neenah kuma tana lura dasu kuma itama tayi reading lips d'in Khulayd, dummm! Zuciyarta ta buga, nan take taji tayi loosing appetite d'inta, ture plate d'inta tayi ta mik'e tabar wurin, a zuciyarta tace " barin tab'a bari haka ya faru bah so long as ina numfashi"
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari, normal time da Khulayd ya saba zuwa office ya tafi ko breakfast baiyi bah don akwai urgent meeting da zaiyi attending tare da boards. Sai kusan 10:00am akayi dismissing meeting d'in after lots of discussion wanda duk akan cigaban OGC neh, Khulayd ya dawo office d'inshi so stressed out, bai ida zama bah Head of sales department ta shigo hannunta rik'e da wasu files bayan ta zauna sukayi exchanging gaisuwa ta fara da " Sir, wani matter neh yayi arising which I believe if you look into it, it'll be of great importance to the whole of OGC" ganin Khulayd baiyi magana bah yasa ta shiga bud'e file d'in hannunta ta tura mishi sannan tacigaba "Mr Omair, Shaheed corporation neh suke so su sayar da huge share acikin company'nsu and I think OGC is the right company to own that share coz it'll boost our productions and supplies" ta nuna file d'in da 'yar yatsarta "wannan shine proposal d'insu and the amount at which they want to sell the share, please do look into it sire before other companies do"
Ajiyar zuciya Khulayd yayi sannan a gajiye ya jawo files d'in zai duba Neenah ta shigo office d'in fuskarta a tamk'e. Zama tayi kan d'ayan kujeran dake kallon na HSD tayi crossing legs d'inta tana wurga wa Mss Jiddah Adam(Head of Sales Department) mugun kallo wanda yake nufin 'get out of my sight', a sanyaye Mss Jiddah ta mik'e zata fita, Khulayd yace "bakomai zan duba and I'll inform u when am done"
Mss Jiddah tace "okay sir" sannan ta fice.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Neenah ta kalli Khulayd tace "Mr Omair am lost and I don't understand anything. Last week Miss Sahr Mukhtar tayi signing contract damu as Miss OGC, sau 2 kawai tazo office, what is happening and why isn't she coming at this point that we need her d most?"
"Because she quit being Miss OGC" Khulayd ya bata amsa a takaice.
Zaro ido waje Neenah tayi tana kallonshi da mugun mamaki, "then we have to sue her tunda contact tayi signing and the contract is not yet complete, besides she just got started" Murmushi Khulayd yayi kafin yace "not in such situation Miss Muktar, I asked her to quit and the reason is something personal. Tunda kinji yanzu, you know what do" Take zuciyar Neenah ya fara beating fast, har gumi ta fara da jin furucin Khulayd but before she could say something, wani ya shigo office d'in hannunsa rike da briefcase yana sanye cikin suit, daka ganshi kaga barrister. Barr. Zayyad kenan, personal lawyer'n OGC tun lokacin da mahaifin Khulayd yake a matsayin CEO. Mik'ewa Khulayd yayi sukayi hand shake da Barr. Zayyad sannan ya nuna mishi seat ya zaunah. Khulayd neh ya fara da cewa "Barr its still about what we've discussed over the phone yesternight, ya kake ganin za'ayi?" Barr Zayyad yace "well, its simple. Kawai zatayi signing papers dana zo dasu daga court like she signed the contract at first, kaima zakayi signing as well nikuma as the witness so that no charges will be filed against her, shikenan". Khulayd baice komai bah ya kira secretary d'inshi yace ta gayawa driver yaje ya kawo Sahr. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Sai kusan 12:00pm Sahr ta shigo office d'in tayi kyau abinta. Suna had'a ido da Khulayd suka sakarwa juna murmushi Khulayd ya tashi akan kujeranshi ya nuna mata "have a seat future Mrs Omair", dariya ma ya bata a yayinda suka matukar d'aure wa Neenah kai.