Sahr khulaiyd complete - Chapter 7
Sahr khulaiyd complete Chapter 7: Sahr khulaiyd complete Chapter 7. Kamar yadda Barr ya fad'a haka sukayi sai dai tunda barrister Zayyad yayi setting eyes…
4,478 words
Kamar yadda Barr ya fad'a haka sukayi sai dai tunda barrister Zayyad yayi setting eyes d'inshi akan Sahr ya kasa d'aukewa, both Neenah da Khulayd sun lura da hakan Wanda yasa wani tukuk'in kishi ya turnuke zuciyan Khulayd. "Baby doll jeki jirani a mota" cewar Khulayd coz he can't stand barrister Zayyad looking at her, tana fita duk suka mik'e tsaye, Khulayd ya mik'awa Barr Zayyad hannu suka sake yin musabaha sannan ya nufi k'ofa. A tare Neenah da barrister suka jera zuwa waje "She's beautiful huh barrister?" Neenah ta tambaya ba tareda ta kalleshi bah, kai ya fara nodding kamar wani sok'o "Zan taimake ka ka sameta idan har kaima zaka taimakeni Barr Zayyad" Da sauri ya kalleta yace "really zaki taimaka min?" Neenah ta gyad'a mishi kanta tace "She's my blood sister so there's no big deal" ta karashe maganar tana kashe mishi ido, nan sukayi exchanging contacts. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*DAILY AS'AAL*❓
22- surah Al-Baqarah, verse 225.
⚜ *23••••* wani kalmomi neh Rasulullah(S.A.W) yace "suna da sauk'i akan harshe amma suna da nauyi akan mizani❓
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 34*
As a barrister har Zayyad ya ganeh manufar Neenah coz yaga yadda take kallon Khulayd kamar zata cinye, duk motsinshi idonta na akanshi, dariya yayi yace "I'll wait for your call Mrs Mukhtar" sannan ya wuce. Neenah tayi wani shu'umin murmushi tace "Let's see how this love story will end" sannan ta koma office don cigaba da ayyukanta. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Sai da Khulayd ya tabbata Barr Zayyad ya tafi sannan a hankali ya k'arasa jikin motan, Sahr na zauneh shiru taji Khulayd ya bud'e back seat inda take zauneh shima ya shiga, tayi saurin sauke kanta k'asa bataso ta kalleshi. Sparkling smile yayi yana kallonta sannan in a cool voice yace "Baby doll you look takeaway, kinyi kyau sosai" A hankali ta d'ago idanunta tana kallon kyakkyawan fuskarshi sai ta samu kanta da kasa daina kallonshi "Ya Khulayd ai ban kaika kyau bah you know that, you re always looking handsome and I think am the luckiest woman to have a soulmate like you"
"Um" cewar Khulayd yana nodding kanshi, "ashe dai babynah d'in tana da baki haka?" Ya kare maganar yana mata kallon kurilla. Sahr tayi saurin sa fuskarta cikin palms d'inta cike da jin kunya, lips d'inta da suka kasa b'uya duk da ta rufe fuskarta Khulayd ya sauke idanunshi akai, a hankali ya lashe lower lips d'inshi idanunshi a kanta "I want to kiss those cute lips" ya fad'a cike da tsokana D'auke hannunta tayi daga kan fuskar ta rufe bakinta da sauri ta runtse idanunta "Allah Ya Khulayd babu kyau fah, haramun neh abunda kakeson yi please don't do it banaso"
Khulayd yayi saurin fad'in "calm down babe, am just kidding bari driver ya mayar dake gida kada Mami tace an rike little princess d'inta"
A shagwab'e Sahr tace "but Ya I'll mishh you" har idanunta ya ciko da kwalla,ya k'wailwayi voice d'inta yace "I'll missh u too Mami's princess" da kyar Khulayd ya lallab'ata ta yarda ya koma office ita kuma aka kaita gidah.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Karfe shida(6) daidai Neenah ta tashi a aiki, tayi shutting down desktop d'inta tayi clearing table d'inta sannan ta tattara stuffs d'inta ta fito. A cikin OGC tayi hanging out har sai da ta tabbata Khulayd ya tafi tukunna ta fice itama.
Wani Eatery dake d'an kusa da OGC Neenah tayi parking car d'inta, kamar wata munafuka ta fara waige-waige kafin daga bisani ta zura hannunta cikin handbag d'inta (channel product) ta ciro wayarta k'irar iPhone 7 ta shiga contacts tare da dialling digits d'in Barr Zayyad. Ringing 2 Barr yayi picking, Neenah bata nemar mishi aminci bah bare ta bari shi ya nemar mata tace, "Barr ka sameni a Golden Eatery yanzun" tayi hanging up without him respond.
Kusan 15 gud minutes Barr Zayyad yayi kafin ya isa inda Neenah take jiranshi. Kusan a tare suka fito daga cars d'insu bayan sunyi locking suka jera kamar couples zuwa cikin eatery'n, drink kawai sukayi ordering after going through the menu, babu wanda ya yiwa wani magana har sai da waitress ta kawo musu order'nsu.
Neenah ta d'ago kai tana nazarin Barr for some seconds kafin tace "Barr Zayyad by coming here ya nuna cewa ka amince zakayi aiki dani, but I have a condition guiding this assignment" ta kare maganar tare da sipping " _pure heavens grape_ " drink d'inta.
Barr Zayyad yace "I don't think condition d'inki zai tsoratani Mrs Mukhtar, so long as zan samu kid sister'nki "
Tafawa Neenah tayi tace "bravo Barr, inason courage d'inka... The condition is simple, there's no backing out idan an fara assignment d'in and be very extra careful coz idan har Mr Omair ya ganomu, you and I both know what is going to happen" Barr Zayyad yace "idan har ya ganeni den am not a barrister, so condition accepted"
Confidently Neenah tace " plans 3 muke dashi, plan A,B&C which yanzu zan baka first plan da zamu aiwatar which is PLAN A.... Kidnapping d'inta zakayi and I don't care how you'll do it, in ganta kawai a hannu"
Barr Zayyad yace "kindai san bazamu tambayi ransom bako, coz zai iya basu clue akan mu, if that's what you re thinking toh its better mu chanza plan"
Neenah tad'anyi frowning sannan ta sake smiling tace, "Barr wannan plan d'in will benefit me a lot" ta sake wani shu'umin murmushi tace "and as for you, zaka samu something much more than ransom" ta kashe mishi ido #wink Da sauri Barr ya lashe leb'b'ansa both cikin yanayin gamsuwa da jawabinta. "Zan tsara komai for d kidnap, just expect ma call" cewar Neenah
Barr yace "okay I'll await your call" sannan kowa ya kama gabansa.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*DAILY AS'AAL*❓
24- Subhanallahi wa bi hamdih, Subhanallahil Azeem sune kalmomi biyu masu sauki akan harshe amma masu nauyi akan mizani. ❣❣❣❣❣❣❣❣❣
⚜ *25•••••* A cikin 'ya'yan Rasulullah(S.A.W), wacece Sayyidina Ali(R.A) ya fara aura?
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
#TeamSahrKhulayd.
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 35*
Sai kusan 8pm Neenah ta isa gidah, a parlor ta tarar da Mami zauneh tana kallon TV, a sanyaye ta k'arasa cikin parlor'n sanin cewa dole Mami tayi mata sababi, tazo dai-dai gaban Mami ta d'an duka tace "Good day momma" tana ta faman b'oye fuskarta like a guilty person.
Wani mugun kallo Mami ta jefeta da wanda yasa hanjin cikinta kad'awa, "Neenah duk cikinku ku ukun nan ke kike bani matsala, you re very strong headed tun bayan rasuwan papanku kikeso kifi karfinah.... How many times will I have to tell you cewa ban yarda koda magrib ya sameki a waje bah? Kika sake maimaita haka wallahi I'll make u quit that so called job of yours... Now get out of my sight" Mami ta fad'a a fusace. Sum sum Neenah ta mik'e tana tura baki, "sorry Mami" ta fad'a cikin muryan tausayi ta nufi stairs zuwa d'akinta.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Bayan Neenah tayi wanka ta d'an huta ta nufi d'akin Sahr ta sameta zauneh tana kallon Indian series d'inta. Murmushi Neenah tayi ta k'arasa cikin d'akin ta zaunah kan sofa'n da Sahr ke zaune akai tana fad'in "Hey kid sister, kallo kikeyi?" Amma gabad'aya hankalinta baya jikinta, she was carried away by what she's watching har saida Neenah ta d'an bubbugata tukunna ta juyo a firgice ta kallete. "Adda Neenah y do u always scare me, wallahi naji tsoro sosai can't u even say salaam?" Sahr ta fad'a tana tura baki.
Neenah tayi mata hararan wasa tace "must I take permission before I see my kid sis, ai a ganinah zan iya shigowa duk lokacinda nakeso koh?" Cewar Neenah
"Last time I checked, this room is mine alone" Sahr ta fad'a itama tana d'an hararan Neenah. Neenah ta had'iye fushinta duk da abunda Sahr ta fad'a ya mugun b'ata mata rai tace "Okay am sorry kanwata, kinga d'azun har na siya miki ice cream sai kuma na manta a office, to tell u what saida nazo gate na tuna" da sauri Sahr tayi pausing film d'in da take kallon ta dubi Neenah da fuskar tausayi tace "Haba Adda Neenah, ni wallahi da baki fad'amin bah gashi yanzu duk kin samin kwad'ayin ice-cream d'in kuma ba bani zakiyi ba fah" ta k'are maganar kamar zatayi kuka.
Duk ta baiwa Neenah tausayi, ta jawota jikinta tana petting d'inta tace "Kid sis me zai hana kibi Mr Omair office gobe, kinga daga chan sai ki fad'a masa kina son shan ice cream, and I guess if he's very busy zai had'aki da driver sai kuje ice cream shop d'in kinga you'll have as much flavour as u want" Da sauri Sahr ta tashi daga jikin Neenah tana dariya tace "yeeee! Gaskiya Adda Neenah shawarar nan tayi, dama I've been wanting to go with him to d office don banaso yayi nisa dani I want to always see him" Neenah a zuciyarta tace "daga gobe you'll see him no more" sannan tayi munafukin dariya "Just go and inform him idan yak'i kiyi mishi kuka". A haka Neenah tayi convincing Sahr ta yarda da maganarta.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
_Washegari..._ Khulayd ya sauko downstairs to have his breakfast kamar kullum but to his greatest surprise yaga Sahr all dressed up tana zauneh kan sofa'n data saba zama ta jirashi idan zasu office. Tana ganinshi tayi saurin sadda kanta k'asa tace "Ya Khulayd ina kwana" Khulayd ya kalleta yana murmushi, yace "Morning sunshine, how was your night?"
Itadai Sahr shiru tayi batace komai bah, Khulayd ya wuce dinning kawai bai sake ce mata komai bah coz he's in a hurry. Tana nan zauneh ya gama breakfast d'inshi ya mik'e sai yaga itama ta mik'e ta karaso gabanshi ta shagwab'e fuska "Please Ya Khulayd ka tafi dani, just want to feel your presence" ta kare maganar kamar zatayi kukah.
Mamaki ma ta baiwa Khulayd wanda hakan yasashi hard'e hannunshi a k'irji yana kallonta kawai speechless, ganin bashida niyyan magana yasa ta langwab'ar da kanta tayi sliming voice d'inta "Please kaaji" Bata jira abunda zaice bah kawai ta zare jakar laptop dake rataye a kafad'arsa ta rataya a tata tayi ficewarta zuwa mota. Khulayd ya girgiza kansa kawai yace "I just love everything that is about u" sannan yabi bayanta.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Suna isa cikin office d'in Sahr ta ajiye mishi jakar laptop d'in kan table sannan ta zagaya ta zauna kan kujeran Khulayd tana murmushi tace "Yau nice Mr Omair, so have a seat" tana nuna mishi inda zai zaunah. Khulayd ya zaunah kawai yayi tagumi yana kallonta don duk abunda takeyi yana burgeshi sosai, da taga kallon yayi yawa ta tura baki "C'mon Ya Khulayd ka daina kallona haka, you'll make me quit d act fah" ta fad'a tana kokarin mikewa Khulayd yayi saurin rike hannunta "You know definitely cewa idan kin biyoni office barin iya aiki bah, what else will I do other than to stare at you Umm hun" Sahr ta fara kokarin fusge hannunta daga rikon da yayi mata but she couldn't, kamar zatayi kuka tace "Please ka sakeni Ya banaso" A hankali ya furta "I love you" kafin ya saketa ta koma kan sofa tana b'oye fuskarta.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Kusan *5:00pm* Neenah ta shigo office d'in Mr Omair, tun kafin ta ce wani abu Sahr tace "Yawwa Adda Neenah ganinki ya tunamin da ice-cream d'ina" Tayi saurin tashi ta isa gaban table d'in Khulayd "Ya zansha ice-cream" ta fad'a tana kallonshi in the eye Khulayd yayi ajiyar zuciya "hhuuuh" sannan yace "Sunshine saidai ki tafi da driver zuwa ice-cream shop d'in, kinga I still have a lot do do".
Sahr tad'an marairaice fuska "Okay" ta fad'a kawai ready to cry
"C'mon baby doll cheer up, kinsan bariñ bari driver ya kaiki bah idan banda abun yi.. Sorry kinji" cewar Khulayd. Sahr tayi nodding kanta tana murmushi tace Its okay"
Shima murmushi yayi tare da mika mata kudi sannan yace "I love u and take care of yourself for me okay" nan ma gyad'a mishi kai tayi. Khulayd ya wuce gaba yana cewa "Lemme see u off" itama Sahr ta bishi a baya suka bar Neenah tsaye kamar gunki a wurin.
Suna fita Neenah tayi wani dariyan mugunta tace "Guess today is d last day you both will see each other" takare maganar tana dialling contact d'in Barr Zayyad. Bugu biyu ya d'aga, bata bari yace komai bah tace "Get ready for the kidnap, yanzu zasu fito" tayi hanging up tare da sakeyin wani murmushi tace "Khulayd Abeed Omair, yanzu kai nawa neh"
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Like my facebook page @ Seemby Luff Novels, thank u❣ #TeamSahrKhulayd.
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 36* _*This chapter is dedicated to u Murjanat Alkali, tanks for the love, support and encouragements.. It means a lot••••*_❤
Har mota Khulayd yayi mata rakiya, da kanshi ya bud'e mata owners corner ta shiga, har tasa hannu zata mayar da kofan ta rufe thinking that sallaman da sukayi a cikin office d'inshi was enough, Khulayd yayi saurin rike hannunta yana girgiza mata kai "Har kin gaji da ganina neh sunshine?" Ya fad'a tare da jinginuwa jikin kofan motan yana kallonta. Tayi saurin b'oye fuskanta tana girgiza mishi kai kawai shiko bai sake cewa komai bah, he kept looking at her as if it were the first day they met kusan 10 minute ya d'auka yana kallonta.
Sahr ta tura bakinta gaba ta d'ago da kanta ta kalleshi sannan tace "Ka fara ko hubby, sai kayi ta kallona kamar something bad is going to happen to me" Khulayd yayi ajiyar zuciya yace "That's what am feeling sunshine, I feel like we re not going to see each other again... Ko dai zaki fasa zuwa neh and wait for me sai mu tafi tare" Tayi saurin mak'e kafad'arta kamar zatayi kukah tace "Um um nidai ka bari muje, ai zamu had'u a gidah koh Yayanah?"
"Okay if you said so" sannan yad'an matsa kusa da ita yace "Come here" ya jawota tare da pecking goshinta, da sauri yabar gurin zuwa office yayinda driver ya ja motan zuwa ice cream shop...
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Sahr tayi shiru a mota tana tunanin maganganun Khulayd, itama she have a bad feeling a cikin zuciyarta tadai yi addu'a sannan ta kawar da zancen. Dai-dai gaban shop d'in driver yayi parking sannan a hankali Sahr ta fito daga mota ta nufi cikin shop d'in, driver'n kuma sai yad'an fita zuwa bakin titi don biyan nashi bukatan leaving the car unlocked....
Kusan 20 minute Sahr tayi acikin shop d'in kana ta fito ta tarar da driver baya nan, ba tare da ta nuna damuwa ta jingina da motan tana 'yan kalle-kallenta. Chan ta hangoshi yana zuwa da gudu-gudu har ya karaso, yad'an duka a gabanta yace "Kiyi hakuri hajiya, nad'an sayi wani abun neh a bakin titi". Ita dai Sahr batace komai bah tayi shigewarta mota, shima driver'n yayi saurin zagayawa ya shiga yayi reversing suka bar gurin.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Dai dai corner da zai kaisu gida sukaji wani murya mai firgitarwa daga cikin motan yace "Kai driver tsayar da motan nan"
Ba Sahr ba har driver'n saida 'yan hanjinshi suka kad'a, da sauri yayi brake sannan ya d'aga hannunshi sama yana juyowa a hankali idanunshi sukayi karo da wani mummunan fuska, gashi bak'i kirin daka ganshi kaga mugu mara imani, Sahr kam tunda taji voice d'inshi ta kusa sumewa don ta mugun tsorata..
"Get down" suka kuma jin muryan mutumin, Sahr ta tuni jikinta ya fara rawa ta fashe da kuka. Da sauri driver'n ya sauko ya bud'ewa Sahr kofa, ikon Allah ne kawai ya fitar da ita ganin yanda kafafunta suke shivering, ji takeyi kafan bazai d'auketa ba, tana fitowa ta durkushe a wurin tana kuka. Mutumin ya fito daga motar ya finciko Sahr saboda already guys d'inshi sun iso ya shiga janta zai kai motarsu. Karfi sosai yazo wa driver'n yayi saurin zuwa k'asa ya damke kafafun mutumin wanda ya hanashi taking even a step forward
"Don Allah kuyi hakuri ku barta, ku tafi dani amaimakon ta amma don Allah kubarta ta tafi" cewar driver yana pleading. Wani dariya mutumin yayi wanda ya sake sa Sahr ji kamar zata mutu, ga azaban zafin da kanta keyi mata saboda rik'on da yayi mata, "Tsami gaye dakai kace mu tafi dakai? What will we gain from an ordinary driver huh?.. Zaka sakeni neh ko sai mun illata kah" mutumin ya fad'a.
Gagam driver'n ya sake damke kafan har saida mutumin yaji kafar na masa zogi "Guys, take care of him" mutumin ya basu order, gabad'ayansu sukayi kan driver'n amma da kyar suka kwace kafan ogansun sannan suka fara naushinshi from everywhere. Mutumin ya shiga jan Sahr zuwa mota tana kuka tana bashi hakuri "Please Plea let me gooo, don Allah karku tafi dani kubarni in tafi gidah, I beg of you don't get me separated from my Mami and sisters... Karku d'aukeni kubarni inje inga Ya Khulayd, ku bari in ganshi even for d last time please"
Ganin zata dameshi da surutu ta tara mishi Jama'a yasa ya bata wani powerful slap har saida bakinta ya fara bleeding, take kanta ya fara juyawa tana ganin abu tara-tara har suka isa gurin mota, mutumin nan mercilessly ya shiga turata cikin motan tana fisge-fisge har karfinta ya kare.
Da ihu cikin dashashshiiyar muryarta wanda yasha kuka tace "YA KHULAYD I LOVE YOU" ta sake fashewa da kuka, dai-dai lokacinda mutumin yayi nasaran cusata cikin motan, a hankali Sahr tayi whispering "I'll hold on to our love, I believe in it and I will come back for u Ya Khulayd.. I love you".
Dai-dai nan guys d'in suka karaso wurin mota suka shiga after beating the hell out of the driver, suka ja motarsu suka tafi leaving him helpless a yashe a kasa, baya ko iya motsa yatsar hannunshi don yasha sambad'a da suburbud'a... LOL
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*DAILY AS'AAL*❓
⚜ *26••••* meyasa ake k'Iran sayyidinaa Uthman da suna Zun-Nurain ❓
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
#TeamSahrKhulayd
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ By *Seemby luff*😘 *PAGE 37*
Da kyar driver'n ya lallab'a ya ja jikinshi zuwa bakin gate na gidan ya shiga bugawa da sauran karfin daya rage mishi. Gateman d'in na zauneh da 'yar radio'nshi yana sauraran labarai yaji kamar ana bugun kofan, tsaki yaja ya cigaba da jin radio'nshi don baya sa ran wani zai zo gidan in this time, saida yaji an tsananta bugu yasa ya mik'e badon yaso bah ya isa bakin gate d'in ya bud'e karamin kofa.
"Subhanallah!" Ya fad'a lokacinda yaga driver'n kwance a kasa, da alama ya gama exhausting k'arfinshi gabad'aya a bugun kofan sai numfashi yake fitarwa da sauri da sauri. A kid'ime gateman d'in yaje k'asa ya tallaboshi ya shiga tambayarsa "Sani miye ya sameka haka, ina ka baro motar kuma waye yayi maka wannan d'anyen aikin?" All those questions ya tambayeshi thinking that he'll get an answer Sani driver bai iya ko bud'e bakinshi yayi magana sai nuni yake yiwa gateman d'in da cikin gidan, da kyar ya iya cewa "Ka kaini ciki Malam Habu, ka kaini ciki" Nan Malam Habu ya fara kiciniyar d'agashi ya shiga dashi compound d'in
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Bayan khulayd ya dawo gidah ya nufi room d'insa ya sake kimtsawa tukunna ya nufi garden looking very happy as he'll see his sunshine da tunaninta ya hanashi tab'uka komai a office, all he wants is to see her pretty face, a hankali ya jingina da kujera ya d'auki landline ya shiga kiran digits d'in d'akinta as always but wajen sau 5 ya kira ba'a d'aga bah, ba tare da ya nuna damuwa bah ya mik'e ya koma ciki, kai tsaye d'akinta ya nufa ya murd'a a hankali ya shiga ya tarar da d'akin neat as always amma bata ciki, hakan yasa ya zauna bakin gado coz he's thinking maybe wanka takeyi but ya d'auki tsawon 30 minute baiji saukan ruwa bah, last inda tunaninshi yaje shina tana d'akin Mami, a sanyaye ya mik'e ya fice daga d'akin zuwa na Mami. Da sallamansa ya shiga ya sameta zauneh towards her bed end tayi tagumi, jin an tab'a kofa yasa Mami saurin juyowa ta ganshi , bata bari yace komai bah ta mik'e ta karaso gabanshi tare da sauke ajiyan zuciya tace "Hamdan lillah! Son miye ya ajiyeku tun d'azun baku dawo gidah bah, wallahi i was so worried thinking maybe something bad happened to u both, huuh" ta sake yin ajiyar zuciya.
Cike da rashin fahimta khulayd ya kalli Mami yace "Aunt i didn't get you, kina nufin my baby doll isn't home yet?" Ya tambayeta cike da damuwa, take zufa ya fara keto mishi from everywhere yana jin heart d'inshi yana zogi. Hankalin Mami yayi mugun tashi ta d'ago da idanunta da suka sauya color zuwa red tace "Me kake nufi neh son, you mean ba tare kuke bah all along, I thought you both went to d office together" Khulayd da ya gama birkice ya kasa fad'awa Mami komai saida ta d'an jijjigashi tana hawaye tace "Talk to me son, where is my little princess?, didn't you two went out together?" Khulayd ya sa hannunshi cikin gashinshi yana hargitsawa "Yyyy...yes Aunt mun fita tare but tun 4:00pm tacemin zata sha ice cream sai na had'ata da Sani suje ice cream shop d'in coz I was kinda busy... Yanzu d'inma I came to check on her ne don naje d'akinta she isn't around." Ya kare maganar yana dafe kanshi dake barazanar fashewa don ciwo. "Inna lillahi Wa inna ilaihi raji'unn" kawai Mami ta iya furtawa tayi zaman dirshan a kasa, cikin zafin nama Khulayd ya juya zai fice daga d'akin amma kafafunshi sun gaza d'aukarsa, ji yayi bazai iya koda taku d'aya bah ya zube kasan d'akin Mami feeling like his heart is gonna burst, ya dafe kanshi dake sarawa, da kyar ya iya gathering courage ya mik'e ya fitah zuwa downstairs, Mami tayi saurin mik'ewa tabi bayanshi.
Duk hankulansu ya tsananin tashi ganin cewa Sahr bata dawo gidah ba har yanzu, Barin ma Khulayd daya samu labarin wani bambarakwai, all he thought was ta jima da dawowa gidah "What could have happened to her" Khulayd ya tambayi zuciyarshi yayinda zuciyar tashi take tunano mishi how his life will be meaningless without her " _she is your life and you can't live without her_ "
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Saukowarsu yayi dai-dai da shigowan Malam Habu rik'e da Sani suka karaso cikin parlor'n. Mami ce tayi karfin halin saukowa duk da cewa tayi mugun tsorata kuma ta karaya sanin cewa tare dashi Sahr ta fitah zuwa ice cream shop and now ya dawo cikin mummunar yanayi and without Sahr "me ya faru dakai haka Sani? Ina ita Sahr d'in take? Please ka bani amsa mai kyau domin zuciyata tana gab da fashewa, I can't stand you telling me something bad about my baby doll" Mami ta fad'a tana dafe zuciyarta. Khulayd was just standing back and folding his hands, shi kad'ai yasan abunda yake ji within him.
Da kyar Sani ya iya bud'e baki yace "Sun saceta hajiya sun gudu da ita" yana magana yana cizar lower lip d'inshi, basu ankara bah suka ganshi ya fad'o gabansu dafe da kirjinshi and lifeless.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
*_Thank you all for your condolences and prayers, I recieved lots of your text messages, calls and mails and I want to say Allah yabar zumunci da kaunah, I really appreciate it and it means a lot.. Love y'all*_ 💗💚💙❤
#TeamSahrKhulayd
© *SEEMBY LUFF*😘
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ by *Seemby luff*😘 *PAGE 38*
*This page is for you MUNAY ('yar Gashuwa), FAXYFASHION & SAD-NAS(Umm Shuraym)... Luv u guys buhu-buhu*❤❤❤
"Inna lillahi wa inna ilaihi raj'uun" kawai Mami take maimaitawa tabi Khulayd dake kwance lifeless a tsakiyan parlor'n k'asa, gabad'aya kanta ya kwance lissafinta ya birkice sannan gefe guda tana tunanin meyasa Khulayd fad'uwa, hannu takai kan wuyanshi tsabar rikicewa taji breathe d'inshi ya tsaya chak. Ihu ta fasa Wanda ya tilastawa Neenah da Nailah dake d'aki fitowa suka sauko downstairs suma kusan a tare, da mamaki suka tsaya kallon poor Khulayd who seemed not in the world of the living.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
"Malam Habu please d'auko motan nan da sauri mu kaishi asibiti" Mami ta fad'a a rud'e, tama manta cewa Sani is the driver not Malam Habu. "Hajiya ai ni ban ko iya tuka mota bah" cewar Malam Habu yana jinjina lamarin
"OMG!" Mami ta fad'a a fusace tana kallon girls d'inta da suka tsaya guri d'aya sun kasa motsawa "What's wrong with the both of you huh?, my friends will one of you go upstairs and bring the car key, kun wani tsaya kuna kallona ko kunaso inyi da kaina neh wawaye kawai" Mami ta karisa maganar tare da juyawa gurin Khulayd ta d'ago kanshi ta d'aura akan laps d'inta tana blowing mishi iska da bakinta. Kusan a tare Neenah da nainah suka juya da nufin zuwa d'auko car key d'in har suna karo da juna daga karshe Nailah ta wuce sama don d'aukowa yayinda Nailah ta sake juyowa direction da Mami da Khulayd suke, tayi folding hands d'inta a kirji tana wondering what happened to the arrogant Mr Omair, badai don yaji news na kidnapping Sahr da akayi bah coz da alama Sani ya sanar dashi knowing he was the one that drove her to the ice cream shop.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Da sauri Nailah ta sauko da key d'in a hannunta, Mami ta kalli Malam Habu tace "Pls taimaka ka kaishi mota saika dawo ka d'auki Sanin duk mukaisu hospital" Malam habu ya mike ya ciccib'i Khulayd yayi hanyar waje dashi yayinda Nailah ta rufa musu baya don tayi unlocking musu motan.
"And you miss" Mami ta fad'a tana kallon Neenah, "jeki kawo car key d'inki kiyi driving Sani zuwa hospital kuma kizomin da mayafi nah" Neenah ta waro idanunta waje tace "Mami inyi driving Sani fah kikace?, u re asking me to drive an ordinary person who is supposed to be driving me?" Ta fad'a tana nuna kanta full of surprise with Mami's words. Wani mugun kallo Mami ta wurgeta dashi kafin tace "Miss, will you get lost and do what I asked of you to ko sai na b'ata miki rai. What do u think of yourself Neenah?" Sum sum sum Neenah ta wuce tana kunkuni tana tura baki har ta haura sama ta dawo rike da car key d'inta, Mami ta mik'e suka fice zuwa asibiti bayan Malam Habu ya dawo yayi assisting Sani zuwa mota.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ *SAHR*
A mota sai zillewa takeyi tana kokarin kwace kanta daga rikon da sukayi mata "Let me gooo, ku sakeni in tafi don Allah, I need to see my hubb, am feeling something bad happened to him don Allah ku kyaleni inje wurin hubby nah please" ta fad'a tana shedding hot tears of love, all her life she never thought of loving someone this deep. Wanda ke zauneh ta left side d'inta yayi stretching out hannunshi ya wanke mata fuska da marin dayasa kanta fara ciwo at that spot.
*KHULAYD*