Kenza eBookz

Sahr khulaiyd complete - Chapter 9

Sahr khulaiyd complete - Chapter 9

Sahr khulaiyd complete Chapter 9: Sahr khulaiyd complete Chapter 9. Without knowing inda kalamanshi suka dosa Neenah tayi wani dariya tace "Da kyau Barr,…

4,496 words

Without knowing inda kalamanshi suka dosa Neenah tayi wani dariya tace "Da kyau Barr, da kyau. Ni dakai munsan waye zaisha wahala idan asiri ya tonu, Mr Omair zayyi sparing d'ina coz am his favorite Mukhtar girl kuma ni 'yar kanwarshi ceh amma kai fah??? He's gonna treat u like a dog don kai ba komai baneh so don't dare mess with Neenah" Tana kaiwa nan tayi hanging up tare da dafe kanta tana tunanin meyasa Barr Zayyad zai juyaa mata baya a wannan lokacin.

Wiiiip! Taga inuwan mutum ya wuce a gabanta ta mike da sauri a tsorace tana waige-waige, wiiip! Ya sake wucewa ta bayanta ta sake juyawa da sauri har tana zufa

"Wayene?, show yourself and stop scaring me"

Taji wani strange and scary voice Wanda har walls na gidan ya amsa yana cewa

"Meyasa kika raba Sahr da Khulayd???"

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

#TeamsahrKhulayd

© *SEEMBY LUFF*😘

[12/9, 10:10 PM] ‪+234 806 939 3966‬: ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

*SAHR-KHULAYD*

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

By *Seemby luff*😘

*PAGE 43*

"Why"

Ta sake tsintar muryan yana tambayanta, tuni ta fara zufa jikinta ya fara rawa tana da dube-dube tana waro idonta waje kamar tab'ab'b'iya

"Www... Waye kai kuma ina ruwanka da abunda nayi, ka nuna kanka kabar tsoratar dani"

Neenah ta fad'a duk da a mugun tsorace take sosai, ji takeyi kamar ta saki fitsari a wajen.

"Ohhh miss Mukhtar!" Muryan yayi exclaiming tukunna ya cigaba

"Kinyi babban kuskuren raba Sahr da Khulayd da kikayi, sai kin fad'a da bakinki abunda kika aikata, I promise u this" cewar muryan sounding very scary this time.

Iya tsurewa Neenah ta tsure lokaci guda ta koma kamar zautacciya, tana nan tsaye ta sake ganin inuwan mutum ya wuce wiiip!, ta kurma wani ihu daya karad'e ilahirin gidan ta zube kasa tare da dafe kanta, cikin rawar murya tace

"Please ka nuna min kanka ko kai waye neh"

Dariya sosai muryan yayi kafin yace

"Look up"

Neenah tayi saurin d'aga kanta tana dubi zuwa all direction taga fuskan Khulayd a dukka kusurwan parlor'n, a tsorace kuma da mugun mamaki tace

"Mr Omair!, kkk...kai neh?, ain't you supposed to be at d hospital on your sick bed??"

Zata sake yin maganan taga fuskan Khulayd yana matsowa kusa da ita, ta sake fasa kara ta zare d'ankwalin kanta ta wurgar sannan ta fice daga parlor'n da gudu..

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

*Sahr*

Can karshen gado ta takure kanta ta cusa kanta cikin fadafunta tana ta aikin kuka wanda ya zame mata jiki yanzu, gabad'aya ta lalale ta zama kamar ba Sahr bah, fuskarta ya dawo paled harda 'yar rama kamar wacce tayi ciwo, sallah kawai ke d'agata don ko abinci bata ci, yadda aka kawo mata haka za'a fitar. Da sallama Barr Zayyad ya tura kofan ya shigo saidai bayyi mamakin ganinta a haka dayayi bah saboda idan da sabo ya saba ganinta a haka duk sa'in daya shigo d'akin. Wurin gadon ya nufa ya zaunah d'an nesa da ita kad'an yana kallonta har saida yakai minti 3 tukunna yace

"'Yan mata, its high time ki barni in aiwatar da kudiri nah akanki and I promise to set you free... Zamanki anan baida wani amfani a wajena just lemme do it once" ya kare maganar da damuwa kwance a fuskarsa.

A hankali ta d'ago kanta tana kallonshi da jajayen idonta tace

"Wa iyazubillah, shin ko isharan da ka gani jiya bai isheka hankali bah? I tot kai mai ilimi neh ashe kai babban jahili neh, y do u keep insisting akan abunda kasan bazai tab'a faruwa bah?"

"Uhum, maganganunki basa b'atamin rai ko kad'an coz I know koda ta karfi saina cika burinah before I set u free, ki bani had'in kai kawai and before d blink of an eye komai zai wakana" cewar Barr

A harzuqe Sahr ta mik'e duk jikinta na b'ari ta nuna Barr da yatsa tana kuka sosai tace

"How could u be so heartless, a tunani nah kayi karatu neh don ka kare wa mutane hakkinsu amma sai gashi kaine maison ketare musu iyaka, don't you understand? Kasan meye soyayya kuwa... Koda yake no one will fall for a monster like you bare kasan halin da zuciya take shiga a lokacinda ta fad'a soyyaya, ni da Ya Khulayd are destined for each other, I live for him and shall die for him idan ta kama"

Cikin zafin nama Barr ya fisgota ya kifa mata tagwayen mari da suka sa ta fita hayyacinta ya matseta a jikinshi ya shiga b'alle buttons d'in rigarshi da d'ayan hannunshi, Sahr na ganin haka ta gantsara mishi cizo har saida yayi 'yar kara,

"Arrrrghh"

da sauri ya saketa ya rike wurin cizon. Sahr ta sauka daga gadon da nufin gudu Barr ya damko gashinta ta baya ya janyota ta zube a kasa tare da buga kanta da karfen gadon tayi saurin dafewa

Gadan-gadan Barr yayo kan Sahr tasa hannunta karkashin gadon ta lalub'o kwalban coke ta sambad'a mishi akai ya tafi luuu zuwa kasa a sume.

Sahr tana ganin haka ta mik'e tayi waje, tun ranan da aka kawota gidan sai yau ta fita, duk kofar da ta gani sai ta bud'e ta shiga, kusan 8 doors ta shiga kafin finally ta tsinci kanta a haraban gidan amma me?

Kafin ta karisa zuwa gate d'in taji muryan Barr Zayyad yana fad'in

"Karku barta ta fita"

A tsorace ta juya sukayi ido hud'u da Barr Zayyad tsaye ya dafe kanshi dake gudun jini, a sanyaye Sahr ta durkushe a wurin ta d'aura hannunta aka tana kuka...

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

*Neenah*

Da gudu ta nufi gate d'insu tana gudun tana juyowa, Malam Habu dake zauneh kusa da gate d'in da 'yar radio'nsa yaga Neenah tayo gurin yasa ya mike a rikice yana tare kofar fitan

"Hajiya Lafia kuwa kike gudu kamar an biyoki" Malam Habu ya tambaya a rikice

Nishi sosai Neenah takeyi

"Hhh..hhh..hhh, malam Habu ya khul...Ya Khulayd neh yake bina ka bani hanya in wuce pls" cewar Neenah

Malam Habu yace

"Amma hajia babu wanda ya shigo gidannan yau don tun d'azun nake zauneh anan ko d'aki ban shiga bah, hajia ko kinyi gamo neh? Oga Khulayd fa yana kwance a asibiti" ya fad'a da mamaki

Neenah dafe kanta dake barazanar tsagewa yayinda bugun zuciyarta ya tsananta, a hankali ta furta

"What's happening??"

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

#TeamsahrKhulayd❤

© *SEEMBY LUFF*😘 [12/9, 10:11 PM] ‪+234 806 939 3966‬: ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜

*Seemby Luff*😘

*I want to use this medium to thank all of you for giving me the support, encouragement and strength to do this, I couldn't have done this without all of you... Shutout to you all, Seemby luff loves you a whole lot much*❤❤❤

*M-Jay*, you are someone closed to my heart❤ *Sad-Nas* thanks for being there for me always❤ *Miss Xoxo* u are the best❤ *Aysha Ummi* thanks for everything babes, I'll remember u for ages😍

*I love you all sosai da sosai*❤❤

*SAHR-KHULAYD* *THE STORY CONTINUES*

*PAGE 44*

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Neenah tace

"What's happening to me, meyasa nakejin muryan Mr Omair while he's at d hospital on his sick bed"

"What you did is hunting u Neenah, dama kin d'auka zaki gama duk muguntarki kuma ki tafi haka, just like that Neenah? No, u must pay for every single evil deed you planted, you must pay" ta tsinkayo muryan Khulayd yana fad'a.

Iyakar rikicewa Neenah ta rikice, gabad'aya she's not in her right senses, duk hawaye ya jika mata fuska a yayinda zuciyarta ta cika da tsoro da fargaba, tasan cewa komai dad'ewa gaskiya zatayi halinta and that the truth will come out in front of everyone, saidai har yanzu bata saduda bah, tayi murmushin yak'e tace

"Wallahi Mr Omair bazan tab'a bari ka rusa min dagiya ta bah, this war is very far from coming to an end, wallahi I will not back out until my dreams comes true, until I fulfil my wish of making you mine, sai na cika burina na zama matarka Mr Omair, matarka" Ta goge hawayen fuskarta tana murmushin da bai kai zuciyarta bah ta karaso parlor'n duk da tsoron da takeji ta haura stairs don zuwa d'akinta...

*At the hospital*

A hankali Khulayd ya lumshe idanunshi, maganganun Nailah suna mishi yawo a kwakwalwarshi, a hankali yace

"Thank you Nailah, thank you for d encouragement words, now I must get up, I must fight for what belongs to me, I will never let someone who doesn't deserve her to have her, da na sakankance kuma na bari tayi nisa dani har na tsawon kwanaki but not anymore, INA sonki baby doll, irin sonda zan iya yin komai akanki, I know if I go out there to look for you, my life will be at stake but my life doesn't matter anymore, I only have one wish now and dat is to see you once again, to be with you once again, to hold u tight in my arms once again, to kiss your lips once again, to feel your heart beat once again" hawaye masu zafi suka shiga zarya akan fuskarshi, ji yakeyi rayuwarshi yazo karshe idan har bai samo sahr bah, a hankali ya sake furta

"Ya Allah, give me the strength, ka bayyana min sanyin idaniyata, Ya Allah ga bawanka mai tsananin bukatar taimakonka, ina tawassuli da sunayenka kyawawa kuma tsarkaka ka sadani da farin cikin rayuwata nan bada dad'ewa bah. Ya Allah ina rokonka ka karemin Sahr a duk inda take kuma kayi mata tsari ga dukkan mugun nufi"

Mami na zauneh kasan darduma ta rafka uban tagumi tana ta aikin kallon Khulayd wanda tausayinshi ya cika mata zuciya da duk gab'ob'in jikinta ta hangoshi yana shafa addu'ar daya gama yanzu

Mami ta lumshe ido ta sake bud'esu disbelievingly da tsananin mamaki taga fa da gaske Khulayd ya d'aga hannayenshi kuma ya shafa a fuskarshi but how could he? Mutumin da tun zuwansu asibiti baya ko iya motsa yatsarshi guda d'aya, how is that possible?"

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

*Barrister Zayyad*

Tun 15 minutes back ya shigo flat d'in da Sahr ke ciki amma ya kasa shiga bedroom d'in, a nan parlor ya tsaya gabad'aya al'amarin Sahr yana k'ulle mishi kai, duk irin kokarin da yayi wajen ganin ta tsorata kuma zuciyarta ta karaya yaci tura, ta kasa barinshi ya kusanceta duk da yana kwad'ayin yin hakan, duk lokacin da ya ganta sai ya hadiye miyau. Ya zube nan kan couch dake a parlor'n yana fusgar da iska mai zafi, gabad'aya he isn't thinking straight, ya mik'a hannunshi ya d'auko landline dake ajiye saman table ya danna wasu digits sannan ya fara magana a wahale

"Inason inga duk wani security dake gidannan a gabana, and please come along with 4 bottles of alcoholic wine with some glass cups" karaf yayi hanging up sannan ya mik'e kan couch d'in tare da lumshe ido.

In no time suka fara shigowa parlor'n, gard'a gard'a dasu kuma majiya karfi, kana ganin fuskarsu zakasan babu imani a cikin zuciyarsu kuma babu alamun tausayi a idanun su. Gabad'aya suka zauna akan sofa fuskar nan tasu babu annuri, lastly wani ya shigo da tray mai d'auke da wine da kuma cups dai dai adadin su, ya dire kan center table dake ajiye a tskiyan parlor'n ya koma ya zaunah.

Barr Zayyad da kanshi ya mik'e zuwa gaban table d'in ya d'auki kwalban wine d'aya yayi popping da iya karfin shi sannan ya bud'e tayi wata kara 'puup', a take wine din ya fara zubewa in foam. Barr Zayyad yayi murmushi ya dauki cup ya fara tsiyayo wine d'in yana mika musu one after d other haka har duk kwalaben 4 suka k'are sannan ya umurcesu su mik'e tare da fad'in

"Let's propose a toast"

Duk suka d'aga cups d'insu sama, barr zayyad ya d'aura

"To my success, to my being intimate with Sahr Mukhtar today.... Cheers"

*20 minutes later*

Duk sun zube kamar kayan wanki a parlor'n, daga Barr Zayyad har boys d'inshi basa iya koda motsa hannunsu sabida buguwa, they were drunken to a bastard level, sai munshari kawai kakeji yana tashi a parlor'n.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

*SAHR* Tun data tashi yau bataji motsin Barr Zayyad bah kuma ta d'auka tunda bai shigo da safe ba zai shigo da azahar, but yanzu har karfe hud'u ta gota bai shigo bah.. Hakan bawai ta damu dashi baneh sai dai a koda yaushe tana fargaban dame zai zo mata.

Munsharin dake tashiwa a parlor'n ya tsananta har ya iso kunnen Sahr dake bedroom, shiru tayi na tsawon mintuna biyar tana sauraron ta inda sautin munsharin yake tashi.

A hankali ta isa gefen gado inda take sallah ta d'auko hijabita ta sanya don fitowarta daga band'aki kenan, ta sanya takalminta flat marar kara. Sadaf sadaf ta karaso bakin kofar ta bud'e a hankali tana matse bakinta, tsoro takeji kada kofar tayi k'ara har ta kutsa kai cikin parlor'n tamayar da kofan ta sake rufowa a hankali.

Tana juyowa ta gansu a zube a parlor'n kowa da style d'in kwanciyarshi, duk bakinsu a bud'e sun d'ad'd'aga hancinsu sama suna kwasar bacci. Batayi wani dogon nazari ko tunani bah domin a 'yan mintunan data tsaya kallonsu zuciyarta ta bata shawaran gudu kawai

"Baki da lokacin tunani yanzu, just run as fast as you can because this is the only opportunity for u to be free... Run Sahr, run". Shawaran da zuciyarta ta bata kenan.

A hankali ta fara tafiya kmar wata munafuka tana tsallaka su d'aya bayan d'aya, kusan mutum tara ta tsallaka duk da a mugun tsoroce take, the 10th person da zata wuce Barr Zayyad neh, yana kwance akan couch d'in hannunshi d'aya a kasa d'aya a sama, haka mah kafafunshi... Saida zuciyar Sahr ta buga da taga Barr Zayyad, nan take wani tsoro ya sake baibayeta, gabad'aya dai taji bazata iya gudu bah don a tunaninta baza tayi nisa bama zai kamota kuma ya dawo da ita cikin gidannan da tayiwa laqabi da ' *kurkuku* ', duk sai taji ta karaya ta juya da nufin komawa, sai ta tsinkayo muryan Khulayd yana cewa

"You can do it baby doll, you can do it".

A nan take zuciyarta ta bushe, taji karfin gwiwa yazo mata, ta rufe idanunta tana tafiya a hankali amma me?

Ji tayi Barr Zayyad ya cafkota ta bata,ta juyo a razane ta ganshi yana mata wani shu'umin murmushi, cikin muryan bacci da buguwa yace

"Bazaki tab'a gujemin bah, never sweetheart"... 😜😜😜😜😜😜😜😛 (Wollah wasa nake muku, nasan yanzu wasu har sun fara jin haushi nah, wata harda tsaki, wata kuma har cewa tayi bazata kara karanta littafin bah, wata kuma wurgar da wayar tayi.. Toh dai ki d'auko wayarki ki ji asalin abunda ya faru.. *sorry for the joke*😎)

A hankali Sahr take tafiya kuma she's being extra careful this time, burin ta kawai ta wuce couch da Barr Zayyad ke kwance akai taje bakin kofah. Barr Zayyad cikin bacci ya rike hijabin Sahr ya sake gyara kwanciyarshi.

Ta sake taking a step forward amma sai taji kamar an riketa ta baya, ji tayi kamar ta saki fitsari a wurin don tsoro

"Allahumma ajirnee fi musibati, wakhlifhu khairan minnee" abunda ta iya furtawa kenan

Juyowa tayi tana wurga mishi kallon tsana, all her life bata tab'a Sanin ma'anar tsana bah sai akan barr Zayyad, she hates him with all her life, cikin ddabara ta samu ta janye hijabinta daga rikon da yayi mata, bata bari ta b'ata lokaci ba ta isa bakin kofa tayi ficewarta bata ko tsaya ta rufe kofan bah.

Babu kowa a haraban gidan, haka ya bata daman zuwa bakin gate da gudu, da iya karfin da Allah ya bata ta banke kofan gate d'in ta fita, sai ga Sahr a waje.

Huh! Finally

© *SEEMBY LUFF*😘 [12/9, 10:11 PM] ‪+234 806 939 3966‬: ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜

*SEEMBY LUFF*😘

*PAGE 45*

*This page is for you HAUWA SALEH ADAMU, you are indeed a sister from another mother, girl I love you to the moon and back... Stay blessed always sweery* 💜💜💜

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Gudu kawai takeyi bata san inda zataje bah, duk wani corner data gani sai ta bi duk da batasan inda zai kaita bah.

Kusan mintuna 10 tayi tana gudu bata ko tsaya bah, ga yunwa yana matukar damunta a yayinda bakinta ya bushe saboda kishirwa. Ta gaji tilis ta zube karkashin wani bishiya tana maida numfashi, gabad'aya karfinta ya kare bata tunanin zata iya gudun kuma, addu'arta kawai Allah ya turo wanda zai taimaketa tunda ta lura ta shigo wata unguwa.. Tana nan zauneh karkashin bishiyar aka turo kofar wani gate, wani saurayi da bazai girme mata sosai bah ya fito da motah ya ajiye nan kusa da itah sanan ya koma ciki yana kokarin kulle gate d'in duk a idon Sahr .

Bayan 2 minutes wannan saurayin ya fito, ya karaso wurin motan yana kokarin sa key yayi unlocking motan ya lura da Sahr dake zauneh ta k'ura mishi idanu, da har ya bud'e motan zai shiga yayi tafiyarsa sai kuma ya fasa, ya mayar da kofar motan ya rufe sannan ya nufota.

Har ya karaso inda take bata sani bah, a nutse cikin kamala da sanyin murya yace

"Salamou Alaikoum, baiwar Allah me kikeyi anan neh tun d'azun kike zauneh ke kad'ai, lafiya kuwa?"

Shiru Sahr tayi bata ce komai bah, bata ma san yana yi bah, a karo na biyu ya sake cewa

"Baiwar Allah lafiya ina magana kinyi shiru?" Ya fad'a neh tare da bubbuga hannayenshi

'Firgigit' ta dawo daga duniyar tunanin ta takeyi, a razaneh ta kalleshi shi d'in ma ita yake kallo. Kafin tayi magana hawaye ya fara wanke mata fuska, a cikin muryan kuka tace

"Don Allah bawan Allah ka taimakeni, am thirsty I need water, ruwa please"

Gabad'aya Sahr ta bashi tausayi yadda yaga bakinta duk a bushe, kuma duk da bai santa bah she don't seem alright, she must have went through something terrible.

Cikin tausayawa wannan saurayin yace "Sunana Sameer kuma wannan gidan mu neh, if you can trust me zaki iya bina ciki wurin umma, daga nan sai kisha ruwa kici abinci don na lura harda yunwa kikeji ba kishirwa kawai bah, ki yarda dani bazan cutar dake bah". Ya fad'a don ya lura tana d'ari d'ari dashi.

Da kyar Sahr ta iya d'ago idonta tana kare mishi kallo har yanzu tana hak'i, haka kawai ta gamsu Sameer bazai cutar da ita bah, a hankali tace

"Nah... Nah gode"

Sannan ta rik'e bishiyar domin ta mik'e, duk tanajin jikinta babu k'wari kuma jiri yana d'ibanta, bata gama mik'ewa bah ta tafi luuuu, ta fad'i kasa sumammiya.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'uun" kawai Sameer yake furtawa, hankalinshi yakai k'ololuwa wurin tashi, kardai ace wani mugun abu ya samu yarinyar nan. A rikice ya d'agata yayi wajen mota da ita, jikinshi har rawa yakeyi yayi unlocking motan sannan ya b'ude back seat ya sakata a ciki ya rufe, da 'yar gudunshi ya dawo gaba ya shiga yayi starting motan without any idea'n asibitin da zai kaita, da sauri yayi reversing motan sannan yabar wurin in a very high speed.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

*KHULAYD, 03:45PM*

Da sauri Mami ta mik'e jiki na b'ari ta karasa wurin gadon cikin tsananin farin ciki, tsayawa kawai tayi tana kallonshi tama rasa me zata ce mishi sai tayi bursting into tears, out of happiness tace

"Son am I dreaming ko abunda na gani da gaske neh, don Allah Son kar kace mafarki nakeyi, don Allah", tana fad'an maganan tana kuka at same time tana murmushi.

With tears rolling down his cheek Khulayd ya mika hannunshi ya riko hannun Mami, don ya tabbatar mata da cewa ba mafarkin takeyi bah, yace

"Aunt you are not dreaming, da gaskene am moving, am feeling inside of me that I can seat up Aunt, Allah ne ya amshi addu'ata ya dawomin da kuzari nah don inje chan waje in nemo soyayyar rayuwata, kuma zuwa yanzu na gama yarda cewa *Sahr-Khulayd* are destined for each other, zuwa yanzun na tabbatar da cewa Allah neh ya had'a soyayyar mu kuma babu mai rabamu" Kamar wasa mami taga Khulayd ya tashi ya zaunah yana kallonta, yana murmushi shima.

Da gudu Mami ta fita tana fad'in

"Lemme inform the doctor" bata tsaya taji me zai fad'a bah

On seeing that, Khulayd ya sauke kafafunshi ya mik'e kamar zai fad'i, ya fisge abun drip da aka d'aura mishi sannan yasa slippers dake ajiye kasan gadon, baiyi wani tunani bah ya fice don zuciyarshi ta gama yarda da maganganun Nailah da shawaranta. Tafiya yakeyi da sauri sauri a cikin asibitin bai masan inda take shiga bah, burinshi kawai ya isa bakin gate ya hau ko adaidaita sahu neh yaje gida ya d'auko mota... Ya d'auki tsawon mintuna kafin ya isa gate din yana kokarin fita.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

*SAHR-KHULAYD*

Sameer yayi droving cikin asibitin da wani uban gudu, he's not even seeing clearly, fatanshi Sahr ta samu immediate medical attention, saura kad'an ya k'ade Khulayd dake kokarin fita zuwa waje

"Baka gani neh malam, can't you drive carefully? Wannan asibiti neh not your father's house" Khulayd ya fad'a cikin fushi.

A fusace Sameer yayi packing motan a nan bakin gate d'in ba tare da ya damu da next car dake bayanshi yana ta faman horn bah, kuma ba tare da ya rufe marfin motan bah ya karasa gaban Khulayd wanda ya tsaya yana kallonshi a kufule, cikin b'acin rai Sameer yace

"Hey Mr whatever, ka iya bakinka, karka kuskura ka zagar min iyaye or else...."

Khulayd bai bar Sameer ya karasa zancenshi bah yace

"Or else what huh? Me zakayi min,who do you even think you are to talk to me this way, zan iya inyi maganinka kafin kyaftawan ido"

Sameer zayyi magana Khulayd ya tari numfashin shi

"Am not done talking to you yet, bari in gaya maka abunda baka sani bah, no one messes with me coz am *KHULAYD ABEED OMAIR* " ya fad'a da karfi

Karaf a kunnen Sahr dake kwance a mota lifeless, sunan Khulayd ya daki dodon kunnenta duk da a sume take, hakan ya tilasta mata farfad'owa. Da sauri ta bud'e idonta tanaji kamar karya kunnenta ya jiyo mata, ta tattara dukkan karfin ta tashi ta banke kofar motan har tana tuntub'e

Kamar a mafarki taga Khulayd a tsaye yana ta faman fad'a da Sameer, da karfi tace

*Ya Khulayd*

Ko a mafarki Khulayd bazai taba manta voice d'innan bah

*Baby doll* ya fad'a shima da karfi yana waige waige.

#TEAMSAHRKHULAYD💯

Drop your comments via my inbox @ 08060522342, my Facebook page @ Seemby luff novels or follow me on instagram @ Seemby_luff

© *SEEMBY LUFF*😘 [12/9, 10:11 PM] ‪+234 806 939 3966‬: ⚜ *SAHR-KHULAYD* ⚜

*SEEMBY LUFF*😘

*Page 46*

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

*Baby doll* Khulayd ya fad'a da karfi yana waige-waige kaman wuyanshi zai tsinke. Cak idonshi ya tsaya kan Sahr dake tsaye hawaye yana zarya akan fuskarta, har zuwa yanzun ta kasa gaskata abunda idanunta suka nuna mata, tafi yarda cewa gizo ne kawai Khulayd yake mata as usual.

Shima Khulayd d'in hakan take a b'angarenshi, a hankali ya fara tafiya kamar mutum mutumi ya karaso gaban Sahr wacce take tsaye still a wurin, ya d'ago hannunshi cikin alamun rashin yarda ya d'aura akan lallausar fatar fuskarta, cikin sanyin murya yace

"Baby doll, is this you? Are u really standing in front of me?"

Sahr ta lumshe idanunta da suka kumbura don kuka, itama ta d'ago hannunta ta d'aura akan hannunshi dake kan fuskarta tana gyad'a mishi kanta

"Ya Khulayd ni ce, Baby doll d'inka ce, Sahr d'inka ceh... Ya Khulayd anya ba gizo kake yimin bah, I can't believe am seeing u today after so many days, please tell me you are real" ta fashe da matsanancin kuka.

Murmushin farin ciki Khulayd yakeyi saidai ya kasa furta koda kalma d'aya neh, seeing her made him totally speechless, a hankali ya sake d'ago d'ayan hannun nashi ya d'aura a d'ayan gefen fuskarta yana kallon cikin idonta

"Am real baby doll, its me"

Farin ciki mara misaltuwa ya lullube zuciyar Sahr, bata taba tsammanin zata sa Khulayd a idonta nan kusa bah, hakan yasa ta tafi luu ta fad'a jikinshi sumammiya.

Tashin hankalin da babu irinshi Khulayd ya shiga, yama rasa ya zayyi da ita. Bazai tab'a iya juran ganin Sahr acikin tashin hankali ko rashin lafiya bah,a razaneh ya d'ago fuskarta yana girgizawa

"A'ah baby doll, don't do this to me please, karkisa zuciyata ta buga, don Allah ki tashi bazan iya jurar ganinki a cikin halin nan bah, u can't do this to me. Remember we just met now after so many days, I want to tell you the story of what happened when you are not around, I want to tell you how much I love and missed you again, baby doll karki min haka, kece rayuwata bazan tab'a iya rayuwa a duniyar da babu ke bah, please get up"

Kamar an mintsileshi ya mik'e ya sureta sai cikin asibitin, yana

"Please don't leave me, don't give up on life coz am here for you, you are the reason of my existence"

Baiko kula Sameer dake tsaye a wurin yana kallonsu bah, duk su biyun sun sakashi a rud'ani, gabad'aya sun k'ulle mishi kai, babu yadda ya iya yabi bayansu da mota.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Da sauri Mami ta shiga office na likitan, after 2minutes ta fito likitan na biye da ita, happily ta tura kofan d'akin amma sai idonta ya saukan kan empty bed dake d'akin, zuciyarta ta tsinke amma idan tayi la'akari da abunda ya fad'a mata d'azun cewa 'he can seat up', sai ta d'auka he went to the toilet all by himself. Xuciyarta bata daina tsikewa bah ta karasa wurin toilet ta kwankwasa amma shiru, a tsorace tace "Son, are you there?" Amma har yanzun shiru, ta murd'a handle d'in ta tura kofan tana leka all directions amma babu shi babu alamarshi. Mami tayi matukar tsorata jikinta yayi sanyi ta juyo tana kallon doctor'n, kwalla ya ciko mata idanu, a hankali ta tafi kasa tayi zaman dirshan a nan bakin toilet d'in ta d'aura hannu akanta tace

Doctor Son baya nan, where could he have gone to in this condition?" Tayi shiru kamar tana nazari ta d'aura

"Kardai ace ya tafi neman little princess neh, why is he very strong headed bayan na fad'a mishi not to try something like that, na fad'a mishi yayi hakuri Allah zai bayyana ko don karfin addu'o'in my but he couldn't listen" Tayi bursting into tears tace "This children want to kill me,......" Zata sake magana Khulayd yayi banging kofar d'akin ya shigo rike da Sahr wacce take neman taimakon gaggawa, turus kawai Mami tayi tana kallon karfin ikon ubangiji.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Khulayd bai kalli kowa a d'akin bah ya nufi gadon da yakamata shi yake kwance akai ya kwantar da Mami's little princess, sai daya juya da niyyan zuwa kiran likita ya lura da likitan dake tsaye, both shi da mami sun zuba musu idanu kamar TV suna kallo, a rikice yace

"Doctor please save my life, she needs emergency medical treatment, ka duba min ita please.... Do everything in your power to make sure she stays alive, I don't want to loose her please"

Dr Khaleel yayi murmushi ya dafa kafad'ar Khulayd yace

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull