Sakon so complete Novel - Chapter 29
Sakon so complete Novel Chapter 29: Sakon so complete Novel Chapter 29. rry..... " juvawa Abee vavi vace "bring the phone to me" yarufo kofan, ahankali…
2,408 words
rry..... " juvawa Abee vavi vace "bring the phone to me" yarufo kofan, ahankali tadauki wayan gabanta nawani kalan fadi tasaka slippers bude kofa tayi tafito tana bin kujerun falon da kallo ganin bata ganshi ba, hanyar stairs tayi gani tayi falo duh alamun an kashe wutan falo ma hakan yasa tasan yana dakinshi faduwa gabanta yayi hakan yasa kaman wacce kwai yafashewa aciki tai wajen kofan knocking tayi shiru akayi sosai zuciyanta kawai ke bugawa anya dudda daga Mama har Farida sunce tadaina tsoron Abee zata iya kuwa, komi nashi scares her, shakkanshi take kaman ba gobe, ahankali tabude kofan tareda wata yar karaman sallama dakin duhu wani dim side light ne kunne Abee na zaune kan gado ya jingina da bango yarufe kafafunshi da bargo hannunshi rike dawani novel dakeda tottle guda biyu na larabci da turenci yana dubawa, ajiyan zuciya Lujain tasauke mai kara batare data shigo dakin ba daganan bakin kofa tamikamai wayan ace "wayan nakawo ma" Abee yakai kusan 2min vav shiru kaman badashi takeba 2min yay shiru kaman badashi takeba kafin anatse batare daya kalleta ba yace "bring it here" gyadamai kai tayi tashigo dakin kafafunta har rawa suke kaman this is her first time anan dakinshi dakin ga sanyi kaman fridge ahankali take tafiya kaman wacce keda gyambo, komawa kofan yayi yarufe kaman dama jira kofan yake tashigo dawani kalan sauri afirgice tajuya takalli kotan, rawa bakinta yafara sosai hakan yasa tadan tsaya nesa dashi tamikamai wayan tana waigawa tana kallon kofan, batare da Abee yakalleta ba yace "hau gado ki kwanta" Dawani irin sauri takalleshi tana zaro idanunta gain ko E3 kallonta bayayi saima karatun dayake abinshi vasa dasauri tashare hawaven dasuka zubomata kasa hawa gadon tayi ta tsaya anan wajen dagowa Abee yayi suka hada idanu wani mugun kallo yamata batasan lokacin daya wuce da sauri hartana neman faduwa tahau gadon ba, jiye wayan tayi kusadashi sannan takoma chan karshen gadon tarufa da bargo tafashe da kuka sosai mara sauti ita batason kwana kusadashi wIh tsoronshi takeji idan yasake mata irin abinda yamata ranan fa, tun tana kuka zuciyanta na bugawa harta hakura da kukan wani bacci mai dadi yay awon gaba da ita tasauke ajiyan zuciya ahankali, juyowa Abee yayi yakalleta kafin ahankali varufe novel din dake hannunshi yaja drawer ya maida aciki, wayan yadauka daga inda ta ijiye yabude yana kallon game din datai downloading kafin ya girgixakai ace "children and silly stuff" jiye wayan yayi kan drawer sannan ahankali yasa hannunshi yakashe side lamp din dakin yay duhu addu'a yayi yashafa kafin ahankali yawani matsa kusada ita hannayenshi vadaura saman cikinta vadaura fuskanshi kan side na face nata ahankali yashiga juyoda ita.Duk WACCE TAKARANTA MINI LITTAFI BATA BIYABA BAN YAFEMATA BA DAGA DUNIYA HAR LAHIRA Ahankali tajuyo freely tai facing nashi kaman ira take daman wani kalan shigewa jikinshi tayi cikin bacci tana sauke ijiyan zuciya, ajyan zuciya shima Abee yasauke kaman daman abinda yake jira kenan kankameta yay so tight yana feeling yanda take kamshin turare mai dadi, tunda yaje Dubai bai iya yayi bacci lafiyayye ba yarinyar nan kaman tamai magani juve juye kawai zaitayi agado feeling her absent so terribly, lumshe idanu yayi yana feeling duk wani abinda Allah yamata ajiki na diya mace ajikinshi but yay alkawari bazai mata komiba at least not tonight he wants her to be free with him and gets emotionally attached to him, he was so horny amman haka ya daure baiwani dauki lokaci ba bacci yay awon gaba dashi, kiran sallan asuba yatadashi daga bacci wuraren 4:15, ahankali yabude ido yamika hannu yana kunna side lamp yanda shida Lujain suka rungume juna zaka dauka za'a rabasu ne, ahankali yajaye jikinshi cikin bacci ta turobaki alamun bataso ya tashi girgiza kai yayi yana kallon bakinta yasauka daga gadon yana gyara mata bargon sannan yawuce bayi wanka yayi yafito daure da towel shiryawa yayi cikin wata fadan Jallabiya mai kyau yasa hula akanshi karasawa wajen gadon yayi for the first time dukowa yayi yakai hannunshi yashafa kumatunta masu bala'in taushe cikin bacci ta yunkura zata juya kamota yayi sai kawai yadagata hakan yasa tashiga bude idanunta daukanta yayi tsam dasauri takarasa bude idanunta bayi yabude yasata ciki dasauri tasauke kanta kasa tana shafa wuyanta kana gani kasan baccin bai isheta ba, dan E3 murmushi yayi yajawo kofa yawuce yafita daga dakin yasauka kasa yafita masallaci. .. |36 Alwala tayo tafito daga bayin dakinta tawuce salla tayi saida tagama tai azkar sannan ta tashi kaman yanda Mama i takoya mata duk dakin data kwana koda yaushe ta gyara kafin tai wanka, fita tayi takoma dakin Abee gyara gadon tayi tsaf kaman ba'a kwana akai ba ta jera pillows din ta gyara bargon, fitowa tayi tasauka kasa tadauko burner dakinshi takoma takunna turaren wuta sannan tawuce takoma dakinta wanka tashiga tayi hartadau wani dry towel zata daura kaman wacce ta tuna abu tafasa wani Riga tasaka na dogon rigan atampa yellow sannan tasauka kasa kitchen tashiga ita tarasa a mezatayi tea tadafamai kaman vanda Mama takoya mata tazuba a flask takawo nan kan dinning komawa kitchen din tayi ta tsaya tana tunani bude kofan kitchen din akayi dasauri tajuyo ganin Abee yasa tasauke kanta kasa ahankali tace "good .... morning" batare daya amsa gaisuwan ba yace "what are you doing in the kitchen"? Murya chan kasa tace "I want to cook for you" shiru yayi yana kallonta har cikin ranshi yaji dadin maganan, saikuma chan yace "banson jagwalgwalon yara" dan turobaki tayi batare data kalleshi ba tace "ni ba yarinya bane" dan zaro idanu Abee yayi yabi bakin datai magana dashi da kallo vanda take turowa ahankali yace "ke menene" lankwashe mai kai tayi ashagwabe tace "ni babba ce sosai" murya chan kasa adan zafafe yace "zonan" dasauri tadan kalleshi hada idanu sukayi, makemai kafada tayi tareda bubbuga katanta akasa kaman wata yarinyar da aka yaye tace "ni tsoron ka nakeji" Abee jiyayi kaman zai kwarkwance sabida kalan shawaban datamai harda buga kafafu akafa dawani kalan sauri yajuya yafita daga kitchen din yana bubbuga zucianshi zama yayi a dinning dasauri yadauki cup yana tsayaya tea dasauri yakai baki azuciyanshi yace "this girl is trying to run me mad" shayin yashiga sha saikuma ahankali yadan dago kanshi yakalli Kofar kitchen din tsaye yaganta tana lekenshi tana kallonshi takofa tana murmushi, hade fuska Abee yayi yace "zonan" turobaki tayi tafito ahankali batare daya karasa zuwa wajenshi ba, Abee yace "why are you smiling?" Yatsunta tashiga wasa dashi taki magana, ahankali Abee yakalli tea dayakesha saikuma yace "sabida inashan tea Yar yarinya" juyamai idanu tayi, dan murmushi Abee yavi vace "jeki shirya Kihada kayanki zamu koma gidan Hajiya" dasauri takalleshi wani kalan dadi taji dasauri tai stairs tashiga hawa dagudu bin ass nata yay da kallo babu yanda zaiyine yasa zai koma da ita kar Hajiva ko kannenshi su daukeshi kaman karamin mutum. Tass tahada kavanta da sababbin akwatinan da Abee yasayo mata na kaya dakuma wanda yadauko mata daga gida, shiryawa tayi cikin wani black dubai abaya mai bala'in tsada dava sayomata ta daura veil din kan saman kanta tafito daga dakin tai wani kalan kyau daidai shima Abee vafito yana sanye da fararen manyan kaya yay kyau binta yayi da kallo dasauri tasauke kanta kasa strictly yace "ina hilab" dan tabe fuska tavi kafin tamai pointing akwati, jawo kofa yayi sannan yazo wajen ya tsugunna yace "wanne daga ciki"? Nunamai karamin daya taho mata dashi daga gida yayi hakan yasa ya kwantar da akwatin yabude wani milk Hijab yaciro har kasa mai kyau, maida akwatin yayi yarufe yadaga sama sannan shima yatashi yakalleta kanta akasa har gabanta yazo ya tsaya dab da ita hannu tanikamai batare data kalleshi ba zata amshi hijabin gamamakinta warware hijabin yayi ahankali yasamata, gently yadago fuskanta yana gyaramata wuyan hijabin yana kallon eyelashes nata sabida yanda taki dago idanunta takalleshi, komawa yayi baya bayan yagama samata yadaga akwati biyu yaja trolley dasauri tazo itama zata ja daya wani mugun kallo yamata yasa ahankali tacire hannun takoma baya wucewa da biyun yayi yasauka kasa baiwani dade ba yadawo yakwashe sauran nata duka ukun yawuce dasu sannan yakara dawowa daga bakin stairs yakalleta yanda take zauna yace "let's go" tasowa tayi ahankali tafara tahowa tsayawa yayi yana kallonta hakan yasa tasauke kanta kasa saida tazo inda yake sannan suka cigaba da sauka ahankali har falo kashe komi vavi all abinci dana yariga yabama sojas masu gadin gidan sannan suka wuce Duk wacce takaranta mini littafi batare data biyaba ban YAFEMATA BA DUNIYA DA LAHIRADUK WACCE TAKARANTA MINI LITTAFI BATA BIYABA BAN YAFEBA DUNIYA DA AKHIRA Bini bini yana tuki yana kallonta sabida vanda taketa kallon hanya kana gani kasan tadade bataga hanya ba sai murmushi take agwaluma tagani ahanya kaman zata mike tsaye tana kallon abin ahankali Abee dake lurada ita yace "you want that?" Dasauri tajuyo takalleshi tambayan yabalain mata dadi, gyadamai kai tayi ahankali tana sauke kanta kasa, gangarawa gefen hanya Abee yay yay parking sannan yakashe motan yafito yatafi wajen mai agwaluman almost rabin tray din agwaluman Abee yasaya har baki tabude cikeda mamaki tana kallo daga mota kudi yaciro yabama mai agwaluman yajuya vataho side nata yabude kofan da sauri tasauke kanta kasa still tana murmushi yatsanshi yakai ahankali yadaura kan dimple nata dasauri tadago kwayar idanunta takalleshi suka hada ido ledan yamikamata batare daya zare hannunshi dagakan dimple dinba sauke idanunta tavi takarbi ledan dasauri still murmushi take ahankali tace "Thank you Uncle" sounding so excited tashiga bude ledan tadauko daya dasauri zatakai baki yatsanshi Abee vacire dagakan dimple nata ya karbe agwaluman yanamata wani mugun kallo kaman zatai kuka takallai saikuma tasauke kanta kasa ahankali, hannu Abee yamika yadauki bottle water dake motanshi yajuya ya wanke mata agwaluman sannan yabata karba tayi takalleshi wani cute smile tasakinmai dayasa Abee yaji kaman zuciyanshi na swelling dasauri yadauke kai, hannu yasa cikin ledan yadauko guda 2 yasake wankematae sannan yadauke ledan dagakan jikinta ya ijiye akasa yabata wankankun guda biyu dasauri tasa hannunta takarbe hannunta da nashi suka had dukansu shocking sukaji hakan yasa da sauri Abee yazare naahi tareda maida kofan yarufe yazaga yashiga bangaren direba sannan yatada motan yaja motan vana kallon yanda takeshan agwaluman da gefen idanunshi suka wuce. ..Il 33 Ba karamin gaidashi masu gadin estate nashi sukayiba koba komi sunaan baya gari dan basa ganinshi babu mai dan basu kudi, kyauta Abee yamusu suka shige suna shiga estate din tundaga nesa tahango Mandawari tsaye kofar gidanshi da waya a kunnenshi yawani kalan rame, for the first ever time in her life dauke kanta tavi daga kallonshi Back SAKON SO 1 waiting for network. tacigaba da shantagavaluman dake hannunta har karkashin ranta targa tayafe Mandawari Abee yariga ya aureta, ya maidata matarshi toyaya zatayi, Mandawari na saurayi bazai auri bazawara ba saisa tai zero dinshi azuciyanta, tsaf Abee ke lurada ita wuceshi sukayi yawani bi motan da kallo dudda motan is tinted but hakanan Mandawari yaji ajikinshi Lujain naciki dan he just felt her, budemusu gate akayi Abee yashiga cikin gidansu uban motocin dayagani yasa yasan kowa na nan harda abokanenshi kashe motan yay dasauri Lujain tasa hannu zata bude kofan vace "Ke" dasauri E3 takallai hartadan firgita, ahankali yace "idan mun shiga if you want to remove your hijab go to your room kiyi hakan and stay there kinajina" gyadamai kai tayi ahankali, kaman karya barta taje yakeji daurewa yayi yace "sauka" bude motan tayi tasauko shima Abee yasauko daidai gateman na zuwa cikeda girmamawa yace "Alhaji sannu da zuwa, Hajiya ina yini" yay maganan yana gaida Lujain data ware idanu tana kallonshi, alamu Abee yamata data wuce sannan yabama gateman hannu suka gaisa yawuto shima vana kallon yanda Lujain ke tafiya, her steps are so tempting duk tafiya sai jikinta ya girgiza is as it Hijab ma baya boyeta vanda yakeso hannu tasa zata bude kofan falon yadaura hannunshi akan nata da sauri takalleshi, hannunsu na tare ahaka yabude kofan falon Lujain da sauri ta sunnar da kanta kasa sabida kunya kafin ahankali tashiga falon, tasowa Anty Binta tayi cikeda murna tace "Oyoyoooo Lulun Gwaggo" batai wata wata ba tawani kalan rungume Lujain ta gefensu Abee daya haderai yabi yashigo cikin falon batare daya kalli fuskan abokanshi ba Kausar ta taho da gudu ta rungumeshi. ..Il 33 10:20 AM "Oyoyo Abee naaaa" dan murmushi yayi vacirota daga jikinshi kafin ahankali yaja hancinta yakalli Hajiya dasauri yadauke kanshi dan wani kalan kunya yaji yanaji anatse yace "ina kwana Hajiya" murmushi Hajiya tayi tace "andawo lpy" zama yayi kan one sitter shi as usual yaran dakin duka sukazo wajenshi rungumesu yayi daidai mai gadi na shigowa da abubuwan boot, Ibro da Hamza da Abdallah dayau baiie makaranta ba sabida ance babanshi zai dawo duk suka gaidashi. "Sannu da zuwa Abee" gyadama Abdallah kai yayi yana kallonshi kaman mai nazarin wani abu yace "have you been sleeping well"? Dasauri Kausar data zauna kusada kafan Abee akasa tace "Abee wh bayayi karatu yake tdb sabida exams dasukeyi" kallonshi Abee yayi dan sosakai Abdallah yay ahankali yace "Abee zan dinga bacci daga yanzu I promise" gyadamai kai Abee yayi, Sajida da Zainab da Maman Aneesarh da duk suke nan suka gaidashi gyadamusu kai kawai yayi, Hajiya dai kallon Anty Binta tayi dahar lokacin take rungume da Lujain data boye fuskanta ajikin Anty Binta ta kankameta har zucivanta tai kewan Anty Binta tace "wai Binta angayamiki ke kadai kikai kewan Lujain ne" dan dariya Anty Binta tayi ahankali tace "Haiva nida Lujain munada special connection tai kewana tana ganina tafara kuka kuma" dadan sauri Abee yakalli wajen karaf a idanun abokanenshi da ita Hajiya kanta, cikeda lallashi Anty Binta tadagota hawayen tashare mata tace "bagani nan ba muje ki gaida Hajiya sai mutane dakin" kanta akasa taki kallon kowa sukai waien Hajiya Kausar ta dauke kai, zaunar da ita Anty Binta tayi akan kujeran da Hajiya ke zaune dasauri Lujain tasauko dan tanajin nauyin Hajiya sosai, sosai take bove fuskanta ahankali tace "ina kwana Hajiya" tunda chan Hajiya bawai ta tsani Lujain bane amman yanzu datariga tasan darolday/a aminta da ita jitayi takarason yarinyar ainun ahankali takai hannunta tace "yaki zonan" dan dukowa Hajiya tayi cikeda hikima irin na manya tabama Lujain light hug kafin tadago takamo fuskanta gently ta sunbaceta a goshi tace "sannu da zuwa Lujain ya hanya" ahankali tace "lafiya lau" dan juyowa tayi takalli duka yan dakin sunnar da kanta kasa tayi tabove fuskanta da Hijabi ahankali tace "Ina Kwanan ku" amsata kowa yayi banda Kausar. Masu fitarwa akwai hisabi