Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 16

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 16

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 16: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 16. WANNAN KENAN A ƁANGAREN SU A'AFIA, BARI MU…

3,372 words

WANNAN KENAN A ƁANGAREN SU A'AFIA, BARI MU LEƘA ƁANGAREN SU LION WATA KILA KAFIN MU DAWO SU AAFIA SUN ISA GIDA.

GIDAN LION💋

Yau dai Akila da Rimsha sun sha hira kamar ba gobe. Sai misalin karfe 2 da rabi Rimsha ta ce da Akila ta shiga ɗaki ta kwanta ta jira ta, bari ta kaiwa Lion abinci, to ta amsa mata da shi tare da miƙewa ta nufi cikin ɗakin.

Ita kuma ta nufi Kitchen dan ɗaukar abincin. Kamar kullum, wanke hannayenta ta fara yi kafin tazo ta ɗauki abincin, tana tafiya tana addu'ar Allah yasa ta kai lafiya ta kuma dawo lafiya.

A bakin kofar ta tsaya ta yo sallama, daga ciki Areef ya amsa sallamar tata tare da bata izinin shigowa, tattara dukkan natsuwar da Allah ya bata ta yi, ta kutsa cikin ɗakin tana kara yi mashi sallama.

Imran, Areef, kwance suke a saman gadon Lion suna hira, while shi kuma oga yana zaune saman sofa yana bincike a cikin laptop nasa.

In da ta saba ajiye mashi abincin ta nufa, a nutse ta ajiye mashi tare da ɗagowa ta gaida Areef da Imran, da fara'a suka amsa, dirowa kasa Imran ya yi yana faɗin bari ya je ya ɗauko mata abincinta daga gidan Akil, dan tun ɗazun AKil ya yi mashi massage akan Umaisha ta gama abinci ya zo ya ɗauka mata.

Cikin zolaya Areef ya ce zai bishi domin yau ya kalli bakin ƴan uwan Prof da bai sani ba, a zafafe Lion ya ɗago da dara daran blue eyes nasa, tare da wurga mashi wani mugun kallo, alamar baka da hankali ne zaka fita?. Dariya ya kwashe da shi, dama dan saboda Lion ɗin ya ɗago ya yi maganar, yasan ba ta yadda za'ayi ya fita da wannan ciwon nasa haka, amma kuma kafarsa na bala'in kaikayi, yana burin fita, har tausayawa kansa yake yi akan idan ya samu lafiya kalar yawon da zai yi, sai ya kewaye gabaɗaya States na Naija, zai je wajajen tarihi da saurasu, har ya gama tsara kalar yawon da zai yi, addu'ar samun lafiya kawai yanzu yake yi........( To fa lallai Areef ya shirya karewa kasarmu kallo)

Shi dai Imran bai ce komai ba, ya sa kai ya wuce abinsa, ita kuma Rimsha zama ta yi tana jiran Oga ya sauƙo ta zuba mashi abincin.

Sai da ya ɗauki almost 30 mins yana latsa laptop ɗin, ita kuma tana zaune shiru. A hankali cikin natsuwa ya ɗaura laptop ɗin saman hannun sofa tare da miƙewa ya sauƙo kasa, a in da ya saba zama ya zauna.

Ta kasar ido ta saci kallonsa, pajama ce launin fara tas a jikinsa, ya kulle gashin kan nan nasa a bayan wuyarsa, wannan fitinannen daddaɗar kamshin nasa dai kamar kullun take, ba canzawa.

Yana zama shima Areef ya sauƙo daga saman gadon, ya kariso in da suke yana Murmushi. Abincin ta fara zuba mashi kamar yadda ta saba.

"Our Queen zuba mini nima, amma tare zaki zuba mana dake". Cewar Areef, ya yi maganar yana zama kusa da ɗan uwan nasa, shima dai pajama ash color ce a jikinsa.

"Yaya Areef ni ai ban iya cin kalar abincinku ba". Ta yi maganar tana turawa Lion abincinsa da ta gama zuba mashi.

Kwaikwayon voice nata ya yi yana faɗin "To ai koya miki ci zanyi my Rimsha". Bata san time da dariya ya kubce mata ba, ba iya basajan wajen aiki kawai ya iya ba, ashe har da kwaikwayon murya ya iya, dan kuwa sak siririn voice ɗin nan nata ya yi, shi dai Lion tamkar babu shi a cikin ɗakin, abincinsa kawai yake ci cikin kwanciyar hankali.

"Dariyar me kike yi mini? Dan na kwaikwayi zazzakar muryar nan taki ko?". Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a. "Kinsan me my Rimsha?". A'a ta bashi amsa.

"Kina da murya mai shegen daɗi, idan kina magana bana son ki daina, just like uncle Musharraf voice naki yake, shima haka voice nasa yake da zaki, sai dai fa kina magana a sanyaye kamar Lion, ke da Lion sam baku son buɗe baki ku yi magana sosai, i don't know why, ko dai bakinku na yi maku zafi ne idan kuka ɗaga murya?". Yana magana yana satar kallon ɗan uwan nasa, wadda tamkar babu shi a cikin ɗakin.

Zuba mashi abincin ta yi ta tura mashi a gabansa tana faɗin "Yaya Areef nifa wlh kawai ban san ya akayi maganata take a haka ba".

Sai da ya bari ta gama zu ba masu abincin, ta turo masu, sannan ya kira Aseef video call dan su takurawa Lion, yau sai sun sanya shi ya canza magana, dole ya barta ta koma school, yarinya yar karama ace ba zata rinƙa zuwa school ba, cutar ta zaayi.

Ya danna video call ɗin yana faɗin "A'a akwai dalili dai, sai ku rinƙa magana kamar baku son yi?".

Bugu ɗaya Aseef ya katse kiran ya kirashi, hakan zai tabbar maka da cewa haɗa baki suka yi, sun shiryawa Lion kitimurmura, kuma da alama da wuya ya tsallake masu yau, dan sune rauninsa dama.

"Da gaske yaya Areef......" Bata kai karshen maganar ba zazzaƙar sexy voice nasa ya daki dodan kunnenta. "Get out". Sun cika mashi kunne da surutu, ba damar ya kori Areef, amma ita yana da damar korinta.

Cikin sauri ta miƙe ta nufi waje, tana jiyo voice ɗin Areef yana faɗin "After 30 mins ki zo ki kwashe kayan abincin". Okey ta amsa da shi tare da ficewa abinta.

Kada ku mance da Turanci suke magana.

Duk abin da ya faru, Aseef yana jinsu, dan Areef ya yi picking call ɗin. Jawo ɗan ƙaramin kyakkyawar table dake wajen ya yi tare da ɗaura wayar, ya jingina wayar da tissue pack, ta yadda Aseef zai ji daɗin ganinsu su biyun dukka da kyau.

"My bloods wlh kewarku zata iya yi mini illah fa, please ku dawo ko kuma ni na taho, saura mani Exam har guda huɗu fa, ni gaskiya almost 2 weeks suka rage ba zan iya jira ba, ya yi mini nisa".

Lion bai san time da Areef ya kira Aseef ɗin ba, jin zazzakar murya ɗan uwan nasa yasa shi ya ɗago blue eyes nasa daga kan abincin da yake ci zuwa kan wayar.

Zubawa Aseef ɗin idanu ya yi yana kallon yar ramar da ya yi, da alama dai yana yawan tunanin ƴan uwan nasa sosai, Allah sarki bawan Allah, tun da suka taso basu taɓa rabuwa su yi nisa har haka ba sai wannan karon, duk ya shiga damuwa sosai, dan ma Musharraf na rage mashi damuwar, amma duk da haka sai da damuwar ta fito ta hanyar sanya shi rama.

"Our pleasure muma muna kewar ka sosai, ban taɓa shiga damuwa sosai irin na wannan karon ba, seriously tamkar na rasa wani ɓangare na jikina haka nake ji, amma dai ka kammala Exam ɗin, 2 weeks ai kamar yau ne". Cewar Lion kenan, kuma tun da yake sai yau ya taɓa yin magana makamanciyar hakan, ya yi ne kuma dan ya kwantarwa da ɗan uwan nasa hankali ya samu ya natsu ya rubuta Exams nasa cikin kwanciyar hankali, sannan kuma har ga Allah yana kewar ɗan uwana nasa over, abin na damunsa a rai, dan dai kawai bai da yawan magana ne yasa ba zaka fahimci hakan ba.

Nisawa Areef ya yi kafin ya ce "Ni ba zan iya misilta kewarka da nake yi ba my blood, baki ba zai iya faɗa ba, a kullun ina ji tamkar na yi fiffige kawai na ganni a tare da kai". Turo baki ya yi zai fara yi masu shagwaɓa.

Har lokacin Lion bai ɗauke idanunsa daga kan wayar ba, ji yake tamkar ya sanya hannu ya fito da ɗan uwan nasa ta cikin wayar su rungumi juna. "Zaka fara yi mana shagwaɓar kenan ko?" Cewar Areef.

"Ni ba wani shagwaɓa da zan yi maku, yanzu dai Lion ina son kayi mini wata alfarma ne ka ji?". Shiru bai yi magana ba, sai dai ya ɗaga mashi gera ɗaya alamar ya ji.

Shiru shima Aseef ɗin ya yi ya rasa ta ina zai fara. "Aseef abin da nake so da kai shi ne, ka daina yawan tunaninmu da kake yi, bana son ganinka a ramen nan, idan kana son sanya ni cikin damuwa kuma shikenan". Cewar Lion ya yi maganar yana mai da spoon ɗin hannunsa ya ajiye a cikin plate ɗin abincin.

"To Shikenan Lion na yi alkawarin zai dai'na duk wata tunani, zan daure yanzu dai please my blood ina son ka bar Rimsha ta rinƙa zuwa school, ma'ana ta daina yi muku aikin safe, ya zamana iya na rana da dare ne kawai zata rinƙa yi muku, kaga yarinya ce, idan aka yi mata wasa da karatu a yanzu to za'a canzawa rayuwarta akalar shi ne, please ni zakayi wa ba kowa ba, idan ka yi hakan zan yi murna sosai wlh". Ya kai karshen maganar cikin sigar shagwaɓa.

Ɗaukar spoon ɗin da Lion ɗin ya ajiye Areef ya yi, ɗibar abincin ya yi tare da kawo wa ɗan uwan nasa a bakinsa, buɗe baki Lion ɗin ya yi ya karɓa yana mai dawo da kallonsa kan Areef ɗin, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, cigaba da bashi abincin a baki Areef ɗin ya yi tamkar wasu mata da miji.

Kuka Aseef ya fara yi musu a kan lallai shi gobe zai zo, ya za'ayi yanzu shi ba mai bashi abinci a baki, shi wlh ba zai yarda ba, ya gaji, yanzu ba mai bashi first spoon fa.

Girgiza kai Lion ya yi, Aseef sai Allah, yana bala'in kaunarsu fiye da tunanin mai tunani.

Shi kuma Areef ɗebo abincin ya yi tare da kawowa saitin wayar yana faɗin "Ɗan nema to maza buɗe bakinka na zuba maka, ba dai first spoon ba? To ga shi nan, har ma da last spoon zaka samu, ɗan babynmu, auntar TRIPLETS, sweetien daddy, pleasure Lion, shagwaɓati kuma damuwati na, ciwon kan Uncle T, ciwon cikin Uncle Herry, matsalar Jonh, addabawa rayuwar Jay, wadda mummy ta fi so, dukka kai kaɗai maza buɗe baki, yi sauri......" Bai kai karshen maganar ba ya yi shiru sakamakon damko gashin kansa da Lion ya yi, da ɗan karfi ya ja mashi gashin nasa.

"Wash Lion me nayi maka kuma? Ko mugunta zaka yi mini ne nima, kamar yadda kake yi wa sauran mutane". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Me pleasure na ya yi muku da zaka ce mashi ciwon kan Uncle T, ciwon cikin Uncle Herry, me yake yi masu da ya zama ciwon kansu? Me yasa zaka zage shi?". Cewar Lion.

"Kai fa Lion ka iya mugunta, kuma baka son gaskiya, ai ka sani, waye Aseef ya raina biyun Uncle T, ba dole ya rinƙa sanyawa uncle T ɗin ciwon kai ba, duk wata tsiyarsa idan ya ɗebo a kansu yake sauƙewa, mu kuma ya zo nan yana yi mana kuka da shagwaɓa." Cewar Areef, yana magana yana ciza laɓɓansa, saboda zafin riƙe mishi gashi da Lion ɗin ya yi.

Kara jan gashin nasa ya yi, har sai da ya yasar da spoon ɗin hannunsa ya damko hannun Lion ɗin da hannayensa dukka biyu yana faɗin "Wash wlh wasa nake yi Mishi, ai kowa yasan pleasure ka bawan Allah ne, mumini, shi da ko magana ma baya yi".......... Oh su Areef an ji wuya har ya sauya zance🤣

Runtse idanu Aseef ya yi, har cikin ransa yake jin wannan wash ɗin da Areef yake faɗa, ji yake yi tamkar shi ake jawa gashin ba Areef ba. "My Lion na yafe mishi, ka sake shi, gashin nasa fa zai iya cirewa, ni wlh na yafe mishi, gara ni ka ja nawa gashin ka sake mishi mashi". Yana magana idanunsa a datse, dan baya son ganin face ɗin ɗan uwan nasa cikin jin raɗaɗin zafin da yake ji.

Shiru Lion ya yi tamkar bai ji ba, shi kuwa Areef da ya ji azaba da gaske, bai san time da ya sake jiki ya kwanta a cinyar Lion ɗin ba, hakan kuma ta sanya dole Lion ɗin ya sake shi ba dan ya so ba, ba ta yadda zai yi ya cigaba da riƙe gashin yana kwance a jikinsa.

Duk da ya sake shi bai tashi daga cinyar tasa ba, sai ma gyara kwanciya da ya yi yana mai da numfashi, shi kuma Lion ruwa ya ɗauro ya fara sha.

After 2 mins "Tashi mini a kafata" Ya faɗa a sanyaye. Ƙin tashi ya yi, a kule ya ce "Wlh ba zan tashi ba, kazo ka cire mini fatar kai ne zaka wani ce na tashi, to naki tashi sai ka yi jinyata".

"My Areef please ka tashi kada ya sake ja maka gashi, idan ya sake zan yi kuka wlh". Cewar Aseef, ya yi maganar a shagwaɓe kamar zai yi kuka.

Ɗan zaro mashi dara daran blue eyes nasa Lion ya yi, har ɗan tsorata ya yi, saboda da ya zaro idanun nasa, har wani kyalli suka kara yi. Sake turo ɗan bakin nan ya yi "Haba mana Lion me nayi maka kuma da zaka tsorata Ni?". Kara zaro idanun nasa sosai ya yi, a sukwane Aseef ɗin ya datse nasa idanun kamar zai yi kuka.

Dama abin da Lion yake so kenan, yana son Aseef ɗin ya runtse idanu domin ya yi mashi kallon tsab, ya kalle shi da kyau, dan ya lura da canzawar ɗan uwan nasu.

Sosai yake kare mashi kallo, yasan idan idanunsa a buɗe, ba zai taɓa yarda su kare mashi kallo ba, sai ya zulle masu, wai kunyar ganin cikin idanunsu yake ji. Shi ma Areef juyo da kallonsa izuwa kan wayar ya yi ba tare da ya tashi daga kan cinyar ɗan uwan nasa ba.

Cikin Harshen larabci Areef ya ce "Serious fa Aseef ya canza sosai, ji wani irin kyakkyawar kyalli da face nasa take yi, kamar wadda ya shafa baby oil, har wani haske fa ya kara yi na musamman, amma fa kamar akwai zazzaɓi a jikinsa". Jinjina kai Lion ya yi alamar yah zancen Areef haka ne.

Jin suna magana da wani yare ne yasa shi waro idanunsa waje. Ɗaukar wayarsa Lion ya yi tare da rubutawa Tyrone massage akan ya duba jikin Aseef, idan zazzaɓi sosai ne ya gaya masu, kuma ko me zai faru ya tabbatar bai daka ta Aseef ɗin ba, ya tabbatar ya yi mishi allura, dan Aseef baya shiri da allura ko kaɗan, baya so, sun san halin kayansu.

"My Lion ya batun Sister? Dan Allah ina son ta je school, wlh idan ta koma school zan ji daɗin da ban taɓa ji ba". Ya yi maganar cikin marairacewar murya.

Ɗan zuro hannayensa shi ma Areef ya yi, sosai ya harɗe ɗan uwan nasa, while kansa har a lokacin yana a saman cikinyar ɗan uwan nasa, sosai ya riƙe shi yana faɗin "Same here, idan ka kyaleta tana zuwa school zan yi murna sosai".

A tare suka sake haɗa baki Areef da Aseef wajen cewa "Please mana Our Lion". Da mamaki yake binsu da kallo, sun tsaya tsayin daka a kan Rimsha tamkar suna da wata alaƙa da ita, anya ba wani abin suke shiryawa ba kuwa? Gaskiya yafara zarginsu.

Saka shi a gaba suka yi, sun ki barin shi ya ja wani dogon numfashi sosai, daga karshe dai dole ya amsa masu da to ya ji, wani irin miƙewa Areef ya yi tare da rungumo wayarsa wai ya rungumi Aseef, sai dariya suke yi kamar wasu zararru, Allah sarki suna Kaunar Rimsha over, musamman ma Aseef da idan baku mance ba, zuciyarsa yanzu sabuwa ce, duk abin da a ka bashi yasa a cikinta, to fa da gaske zai riƙeta hannu bibbiyu, dan bai san wasa, karya or yaudara ba, soyayya kawai ya sani, bugu da kari yana tare da Musharraf wadda ya kasance shi ne yake kalla a gabaɗaya Washington DC ya ji daɗi, yana bala'in kaunar Musharraf over, kun ga kuwa dole ya so Rimsha fiye da tunanin mai tunani.

Ba ƙaramin daɗin ganin su a cikin farinciki Lion ya yi ba, har cikin ransa ya ji cewa idan Rimsha ta shigo ɗakin nan zai ɗaga idanu yaga wai shin wace ce wannan da ƴan uwansa mafi soyuwa a garesa a duniyar nan suke shiga farincikin da bai taɓa ganinsu a ciki ba saboda ita, yau saboda ita suke irin wannan dariya da murna haka, tabbas bai taɓa ganinsu a irin wannan tsantsar farincikinba, suna dariya amma ba kamar na yau ba, ya ji yana son ganin wace ce ita ɗin, dan tun da suke da ita, take kawo mishi abinci, ko a ce take gidan, bai taɓa kallonta ba, bai san ya kamaninta yake ba, dama idan baku mance ba, shi yakan iya jimawa tare da mutun ba tare da ya ɗago ya kalli face nasa ba, to haka rayuwarsa take.

Sun ɗan ɗauki tsawon ƴan mintoci a haka kafin Areef ya maida wayar saman table ya ajiye tare da ɗan tsagaita dariyar.

Yana ajiye wayar ya juyo ya rungumi Lion ɗin tare da manna mashi kiss a kumatu, kuka Aseef ya sa masu akan lallai shi ma yana son ya yi kissing nasu, jan dogon hancin Areef Lion ya yi, kasa kasa cikin harshen larabci ya ce "Areef kana jawo mana jangwan gwan ko? Ba zaka bar shi ya natsu ya yi karatu ba ko? Yanzu idan ya ce ba zai zauna ya yi Exams ɗin da suka rage mashi kuma ba fa?". Kara mashi wani kiss ɗin Areef ɗin ya yi yana dariya kawai bai yi magana ba.

Shi ma Lion ɗin juyowa ya yi tare da sumbatar ɗan uwan nasa a goshi, ya miƙe ya bar wajen ya koma saman bed nasa, dan ba zai iya jure rigimar Aseef ba.

Dawo da kallonsa kan wayar shi kuma Areef ya yi tare da kashewa Aseef ido ɗaya, shi ma Aseef ɗin kashe mashi ido ɗaya ya yi, alama suke yi wa junansu akan sun yi nasara. "Aseef zan kiraka later, yanzu dai jeka yi abin da yake gabanka na practical da daddy". Bai jira amsar ɗan uwan nasa ba ya katse kiran tare da miƙewa ya nufi saman gadon shi ma.

Har ya kusa kai wa gadon, sai kuma ya juyo ya dawo, Apple wanda ba'a yanka ba gudarta ya ɗauka tare da nufar gadon.

Kusa da ɗan uwan nasa ya kwanta tare da kai Apple ɗin halinsa, a hankali ya datseta kaɗan, yana karewa ɗan uwan nasa kallo.

"Lion wlh Nigeria ta karɓeka sosai, ni dai ina son kasarnan over, kawai ku barni a nan, kuma kai ma ba zan so ka koma ba, dan serious soft skin naka ta kara kyau". Juyo da blue eyes nasa ya yi izuwa fuskar ɗan uwan nasa, gently ya fara magana. "Kai Areef ban san wani kalar hukunci zan yi maka ba, dan tabbas...." Bai kai karshen maganar ba ya tura mashi Apple dake hannunsa a ɗan bakin nasa, ya danne da karfe ta yadda dole ba dan ya so ba ya datsi Apple ɗin shima.

"Wlh Lion babu wani hukuncin da zaka yi mini, dole a kaina ka fara yi wa mutane afuwa, wai kai a tsarinka babu yafiya ne? To idan ma babu ni yanzu na sanya maka". Yana magana yana kara danna mashi Apple a baki.

Da ɗan karfi Lion ɗin ya ture shi tare da furzo mashi da Apple ɗin da ya datsa, dariya Areef ya kwashe da shi, ganin yadda ɗan uwan nasa ya kara tsuke wannan ɗan bakin nasa, alamar apple ɗin bata yi mashi daɗi ba, ya haɗe geran sama da kasa, fuska kamar wani hadari.

"Kai fa Areef wasa wasa mugu ne, yanzu da ka sanya ni amai fa?". Ya faɗa yana kara ɗaure fuska. "Ni ne kai, in dai a fagen mugunta ne, to ni Areef ni ne Saif". Yana magana yana ɗaga gera ɗaya.

A kule Lion ɗin ta kai hannu zai damƙoshi, da sauri ya faɗa jikinsa yana faɗin "Kafin ka riƙoni na kawo kaina". Hakan kuma ya yi daidai da shigowar Rimsha, dan ta zo ta tattare kayan abincin ta fitar.

Komawa Lion ya yi ya kwanta yana sauƙe ajiyar zuciya tare da kara jin tsantsar kaunar ƴan uwan nasa, sune farincikinsa, sune komai nasa a duniyar nan.

Readers Also Read