Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 17
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 17: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 17. Shi kuma Areef matsowa ya yi daidai bakin…
3,288 words
Shi kuma Areef matsowa ya yi daidai bakin gadon, cikin zolaya ya ce "Sister wai ya naga sai kara kyau kike yi ne? Me sirrin ne? Ko da yake ba ke kaɗai ba, ga Lion ma har wani fresh ya kara yi, Kasarku akwai shegen daɗi, da Lion mace ce sai na ce ciki gare shi yasa ya yi wannan kyau ɗin". Yana magana yana guntse dariya, ita ma maganar dariya ya bata, wai da Lion mace ce sai ya ce ciki gare shi irin wannan kyau da ya kara.
Tana tsoron yin magana Oga ya koreta irin ta ɗazun, sai ta yi shiru kawai, sai murmushi take yi ta tattare kayan ta fita waje.
Tana fita kamar wani walkiya haka Areef ya tashi a guje, abin da ya sanya ya yi hakan kuma, wani wawan damƙa Lion ya kai mashi a wuya, shi ne ya zulle, dama kuma yasan sai Lion ya shaƙe shi haɗa shi da mace da ya yi, da gangan ya yi maganar dama, dan kawai ya tanka.
Abin da ya sanya shi kuma Lion ɗin bai kula shi a gaban Rimsha ba, dan baya son kowa ma yasan yana wasa da ƴan uwansa har haka, kun dai san baya son raini, komai shi ne a sama yake so.
"Come here Areef". Ya faɗa yana ɗaure fuska. "Wlh i can't, ni zaka yi wa mugunta, ai suɓutar baki ce, mistake ne". Kara ɗaure fuska sosai ya yi "I said come here ko?".
Kashe mashi ash eyes nasa ɗaya ya yi tare da ɗaga gera guda yana faɗin "Haba my sweetheart na fa ce maka mistake ne, haba mana son ɗin daddy, ka manta sunan ko? To ban mance ba, yanzu dai serious yau zan haɗa maka Salmon da kai na tun da Aseef baya nan, shikenan ka hakura?".
Kawar da kai ya yi gefe guda, har ga Allah ba zai iya yi wa TRIPLETS nasa komai ba, amma ba dan haka ba, wlh da wani ne ya danganta shi da mace, idan bai kashe shi ba kaɗan ne zai rage mashi, dama ko da Areef ɗin ya zo, bai wuce ya ja mashi gashin kansa da karfi kamar yadda ya saba ba, bayan hakan kuma ba wani abin da zai iya yi masu.
Shi kuma Areef sarkin daɗin baki, ko ɗaura pot a wuta bai iya ba, amma yana faɗin wai zai haɗa mishi Salmon, ya faɗa ne dan ya sanya ɗan uwan nasa farinciki, yasan shi ne best abincin da ya fiso tun suna yara, kasan cewar Aseef baya son kifi ne yasa ya daina cin Salmon ɗin gabaɗaya, amma ba wai dan baya so ba, har gobe ita ce best food nasa.
Komawa Lion ya yi ya kwanta yana sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, lallaɓowa shi ma ya yi ya dawo saman gadon ya kwanta yana faɗin "My blood akwai in da Rimsha zata rakani gobe, please kada ka ce ba zan je ko'ina ba". Idanunsa a Lumshe ya ce ba in da Areef ɗin zai je, ba zai fita ba har sai ya sami sauƙi, marairace murya ya yi tamkar zai yi kuka, ya dage a kan lallai ya sami sauƙi, kin kula shi Lion ya yi, har ya gaji da magana ya kwanta shiru kamar mai tunanin wani abin.
A ɓangaren Rimsha kuwa, tana mai da kayan abinicn kitchen ta nufi bedroom nata, yadda ta bar Akila kwance a saman gado, haka ta dawo ta sameta, kwanciya ita ma ta yi suka cigaba da zuba hira, Akila na kara mata lecture a kan soyayya.
Suna tsaka da hira misalin karfe 4:30 bayan sun yi sallar la'asar, masoyin ɓoye ya kira Akila, cikin sauri ta ɗauki kiran, tare da manna wayar a kunnenta.........
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
E13-14
Suna tsaka da hira misalin karfe 4:30 bayan sun yi sallar la'asar, masoyin ɓoye ya kira Akila, cikin sauri ta ɗauki kiran, tare da manna wayar a kunnenta.
"Heartbeat yau fa tun da safe da muka yi magana ba mu sake yi ba, ina ka shiga ne?" Kamar dai kullun kun san a shagwaɓe ta yi Maganar.
Daga ɗayan ɓangaren ya amsa mata shi ma a shagwaɓe. "Am so so sorry my heartbeat, nasan na yi laifi, to amma ba Rimsha ta ɗebe maki kewa ba? Ai Rimsha ta fanshi laifi na ko?". Turo baki ta yi tamkar tana a gaban shi. "Yanzu Heartbeat ita kuma Rimsha a ina ka santa? Yaushe kuma kasan mun haɗu da ita?". "Kai heartbeat to ai ita Rimsha kanwarmu ce, yanzu dai bar zancen Rimsha yakika wuni? Ya fama da kewa na?". Shiru ta yi a cikin zuciyarta tana maimaita kalmar ita Rimsha kanwarsu ce? Me hakan yake nufi kuma?.
Jin tayi shiru ne yasan ta faɗa duniyar tunani, idan ya canka daidai kuma, tunani take yi a kan maganar da ya ce na Rimsha kanwarsu ce, dan haka sai ya katse mata tunani da cewa "Heartbeat kamar yadda kika ji na faɗa Rimsha kanwar mu ce, yas kanwar mu ce kamar yadda kike kema kanwa a gare ni, abin da yasa nace Rimsha kanwar mu ce kuma, ba komai bane face dan saboda na fita shekaru, kuma kema kin fita shekaru, kin ga kuwa ai kanwarmu ce ni da ke ko? Wai kin manta duk abin da kike so nima zan so shi ne? To idan kin manta na tuna miki, a cikin zuciyata na ji cewa kina Kaunar Rimsha sosai, shiyasa na kirata da kanwarmu kai tsaye".
Murmushi ta sakar mashi kafin ta ce "Wai ka saya mini goribar da nace ne?". Kai tsaye ya ce mata "Prof bai kawo ba tukun nan". Da yake bata san waye suke cewa Prof ɗin ba, sai ta ce "Tom shikenan ka ce mishi ya haɗo mini da aduwa". Maimaita sunan aduwar ya yi kafin ya amsa mata da okey.
Ita dai Rimsha kamar Tv haka ta mai da su, sai kallon ikon Allah take yi, ji yadda Akila take wani tsuke fuska tana zuba shagwaɓa tamkar wata baby, lallai ma, abin mamaki ma ya bawa Baiwar Allah nan Rimsha.
Ita kuwa Akila da alama ta mance da Rimsha a cikin ɗakin, kamar yadda suka saba da sahibin nata, ta zage sai zuba hira da shagwaɓar ta take yi har sai lokacin sallar mangariba suka yi sallama, ɗagowa da zata yi already Rimsha ta yi barci a gefenta, bata san time da ta saki cool murmushi ba.
A hankali ta tashi Rimsha ɗin akan su je su yi sallar mangariba ba, da kyar ta iya tashi dan barcin yana a idanunta sosai.
Bayan sun yi sallah ne suka koma suka zauna a saman gadon suka cigaba da zuba hirarsu kamar yadda suka saba.
Wayar Rimsha dake ɗaure saman bedside drawer ne ya fara kara alamar shegowar kira, kasan cewar Akila ta fi kusa da wayar sai ta ɗauko ta miƙa mata. Anaya ce mai kirar tata, cike da farinciki da zumuɗi ta ɗauki kiran.
"Hello Anaya? Ykk?" Da fara'a ita ma Anaya ta ce "Lafiya lou Rimsha yasu Yaya Imran naki?" "Suna nan lafiya lou ina su yaya Feroz da mummy, daddy, Uncle Shitu da Zaira?" "Suna nan lafiya Uncle Shitu gobe da asuba zai je Maiduguri ya duba su Gwaggo Aisha, tun da suka koma Maiduguri basu sake dawowa ba, ina kewarsu wlh, gobe daddy ne zai kai mu school dan ya zo yau, da uncle Shitu ya gaya mashi zai je duba su Gwaggo Aisha, shi ne ya zo dan ya kula da mu kafin uncle Shitu ya dawo nan da kwana biyu". Ta kai karshen maganar tana ɗan dariya.
Nasan baku gane suwa ye Anaya take Magana a kai ba, Gwaggo Aisha dai ba kowa bace fa ce Gwaggon Jehan, sai mummyn su Rimsha, na san zaku yi mamakin ya aka yi suka haɗu da Uncle Shitu da kuma daddy Anaya, to ku saurara, ya akayi suka haɗu da daddy Anaya zai zo maku a gaba, shi kuma uncle Shitu dama kun san already yana tare da daddy Anaya kafin su mummy su zo, wai shin menene yake tsakanin Uncle Shitu da su mummyn Rimsha? Uncle Shitu yaya ne ga mummy'n Rimsha, ɗan bappanta ne, sai dai shi Mahaifin mummy Rimsha ya yi wayo ne a Niger ba'a Nigeria ba, tun yana saurayi ya tafi Niger kasuwanci, daga nan bai sake dawowa Nigeria ba har sai da ya auri mahaifiyar mummyn Rimsha wadda ta kasance ƴar Niger ɗin ce, bayan auren nasu ne ya ɗaukota zuwa Maiduguri Nigeria dan taga ƴan uwansa, lokacin da ya zo kuma ya samu yayan sa Mahaifin uncle Shitu ya samu karuwar yaro wato uncle Shitu, a lokacin har ya yi wayo, dan zai shekaru 10 haka, da suka zo komawa Niger ya so komawa da uncle Shitu, amma yayan nasa yaki, ba dan yaso ba ya koma ba tare da uncle Shitu ɗin ba, tun daga lokacin kuma bai sake zuwa Nigeria ba har sai da suka haifi Mummyn Rimsha tana da shekara biyar a duniya suka zo Nigeria, a lokacin uncle Shitu yana da 15 to 16 years, da suka tashi koma a wannan karon, sun tafi da uncle Shitu ɗin, dan ya je ya ga in da suke ya yi masu hutu ya dawo, ba ƙaramin jin daɗin zaman Niger uncle Shitu ya yi ba, ba dan yaso ba ya dawo NIGERIA, tun daga nan kuma ba su sake jin ya su mummyn Rimsha suke ba, har bayan shakaru 7, lokacin mummyn Rimsha tana da shakaru 12 zuwa 13 a duniya, shi kuma uncle Shitu 22 to 23 years yake da shi kenan, a lokacin ya shirya yaje Niger ɗin bisa umarnin Mahaifinsa akan ya je ya dubo mashi ɗan uwansa ya yake, a lokacin yana 100 level karatu a Ahmadu Bello University, hutu yake zuwa Maiduguri, da yazo hutun ne ya je Niger duba bappan nasa, a nan ya sami mummunar labari na ce wa, bappansa Allah ya yi mashi rasuwa shekara ɗaya da ta wuce, ya sha kuka ba kaɗan ba, ya so su dawo tare da mummyn Rimsha da mahaifiyarta, amma iyayenta wato kakannin mummyn Rimsha sun ki yarda, haka ya hakura ya dawo ya sanar da gida abin da ya faru, sun sha kuka sosai kuma sun ji haushin mahaifiyar mummyn Rimsha da ta kasa turo ɗan aika ko ta nemi waya ta gaya masu rasuwar ɗan uwan nasu, sun ji ba daɗi ainun, hakan yasa suka yi fushi suka ce ba zasu karɓo mummyn Rimsha ɗin ba, sun yi fushi da mahaifiyarta, kun san Shuwa Arab su ma sun iya fushi ba kaɗan ba, daga nan kuma basu sake bibiyar ya Mummy Rimsha take ba, sun watsar da su, basu sake sanin ya suke ba sai yanzu da ta kai kanta da kanta ga dangin mahaifin nata, to shi ne suka sake sanyata a idanunsu..... KUNJI ALAƘAR DAKE TSAKANIN UNCLE SHITU DA MUMMY RIMSHA, YA AKAYI MUMMY RIMSHA TA AURI DADDY RIMSHA? YA AKAYI TA ZO NIGERIA? INA MAHAIFIYARTA? MEYASA BATA TAƁA ZANCEN MAHAIFIYAR TATA BA? MEYASA BATA KOMA NIGER BA BAYAN ƁATAR DADDY RIMSHA? DUK AMSA ZAI ZO MAKU DAGA BAKIN DADDY RIMSHA DA UNCLE SHITU, YANZU DAI NA FAYYACE MAKU ALAƘAR TA DA UNCLE SHITU NE A TAKAICE DAN KU GANE ME MATSAYINSA A WAJEN SU RIMSHA, DAN HAKA MU KOMA KAN LABARIN MU.
STORY💋
"Allah sarki Anaya ni dai ina son ganin Gwaggo Aisha nan naki, wlh ko dan takura mini da zancensu da kike yi ma dole naso ganinsu" . Ta yi maganar tana mai dafe kirjinta, ta rasa dalilin da yasa duk lokacin da Anaya take bata labarin ƴan uwanta sai ta rinƙa jin gabanta yana faɗuwa, kirjinta na bugawa da sauri sauri, wani lokaci har sai ta dafe kirji nata take samun sauƙi.
A ɓangaren ita ma Anaya duk lokacin data kalli Rimsha sai gabanta ya faɗi, da yake dukka dai yara ne sai ba wanda ya kawo komai a ransa, kuma sosai Anaya tana ganin muguwar Kamannin dake tsakanin Rimsha da kuma Gwaggo Maryam wadda ta kasace mummy Rimsha ɗin kenan, amma bata taɓa gayawa Rimsha ba, sau da dama tana zucci zuccin gaya mata tana yi mata kama da Gwaggon ta Maryam matar uncle ɗinta, sai dai idan sun haɗu sai hiran school ko hirar wani abin, Anaya ta na mancewa da zancen kullum.
"Rimsha In Sha Allah zaki kalli su Gwaggo Aisha, kin san me? ". A'a ta bata amsa. "Idan su Gwaggo Aisha suka sake zuwa zan ce daddy ya kawo ni gidanku mu ɗauko ki, kizo ku gaisa, jiya ma munyi waya da Gwaggo Aisha ta ce mini zasu zo azumi, kuma kinga azumi ya kusa, tun da an kusa babban zaɓe, to suna zuwa zan gaya miki, wlh suna da kirki kuma suna son mu sosai, musamman ma ni, gwaggon A'isha ta fi sona fiye da kowa, dan nayi kama da ita, naso su zauna damu a gidan nan, amma suka ce a'a, daddy ma ba yadda bai yi ba, sunki yarda suka ce sun fi son Maiduguri, shi ne kawai daddy ya barsu a can yana saya musu duk wani abin da suke so ya tura musu can, amma zan gaya miki gaskiyar meyasa basu son zama damu, wlh mummymu ce bata son su, tana zaginsu, shi ne suka ce zasu koma Maiduguri, kuma gwaggo A'isha ta ce kada na gayawa daddy mummy ta zagesu, da nace sai na gaya, amma sai na fasa dan kar gwaggo A'isha ta ji na daɗi". Anaya sarki magana, faɗi ba'a tambaye ki ba, sai mamaki Akila take yi na irin shegen surutun nan na Anaya, duk ta gama tune asirin gidan nasu kamar wadda aka tambaya, ta zube komai a faranti abinta.
Ita dai Rimsha da yake ba mai cika son surutu bane, tun tana amsawa Anaya har ta dawo binta da to, a'a, da kuma e, wani lokaci ma girgiza kai kawai take yi tamkar Anaya ɗin na a gabanta. Sai dariya kasa kasa Akila take yi, dan ta tula Rimsha ta gaji da surutun Anaya, ita kuma Anaya tamkar yanzu ma ta fara, babu niyar dakatawa a lamuranta.
Sai da aka kira sallar issha, cikin sauri Rimsha ta sallameta tana sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya tare da godiya ga Allah ta tsira daga takurar Anaya, ita kuwa Anaya cewa ta yi idan ta yi Sallah zata sake kiran ta, da okey kawai Rimsha ta bita da shi, ba dai idan ta kira ɗin sai ta ɗauka ne zata ji surutun ba? To wlh ba zata ɗauka ba, ta faɗa a ranta tana turo ɗan bakin, da haka ta nufi toilet dan yin alwala.
Bayan ta fito Akila ta shiga ita ma. A tare suka yi sallar mangariba suka zauna har lokacin issha ya yi, bayan sun yi issha ne Rimsha ta miƙe dan ta kaiwa Lion abinci, ita kuma Akila ta haye saman gado tare da jawo wayarta dan ta yi hira da masoyinta a WhatsApp, tun da yanzu ya bata damar tana iya yi mishi massage a WhatsApp, amma ko a WhatsApp ɗin numbersa a rufe take.
Kamar kullum, Kitchen ta nufa dan ɗaukar abincin, bayan ta wanke hannayenta ta ɗauka a nutse, ba tare da ta ce da Mark ko sannu ba, shi ma ko sannu bai ce mata ba, kamar kullu ko kallon in da take bai yi ba.
Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga ɗakin, yanzu ta daina tsayuwar jiran sai an amsa mata sallamar ta, tana zuwa zata yi sallama ta faɗa.
Babu kowa a ɗakin, da alama sun fita, a in da ta saba ajiye abincin, a nan taje ta ajiye tare da zama tana tunanin ina kuma suka shiga.
Bata gama rufe tunanin nata ba ya shigo cikin ɗakin yana mai yin sallama kasa kasa, da mamaki ta amsa sallamar kasa kasa ita ma, kenan dama idan zai shigo ɗakin nasa yana yin sallama? Ta tambayi kanta tana ɗan satar kallon shi, yes idan zai shiga ɗakin nasa yana yin sallama, duk da yasan babu kowa a ciki, amma yana yin Sallama saboda sunnah ce ta annabi yin hakan, idan kayi sallama mala'ikun rahma zasu amsa maka idan ba mutane, yanzu ma bai san da ita a cikin ɗakin ba, ya dai yi sallamarsa ne kamar yadda ya saba.
Ta kasar ido ya kalli inuwarta, hakan ya tabbatar mashi da mutun a cikin ɗakin, kwata kwata ya manta da ya ce zai kalleta idan ta shigo, zai kalli wacece su Areef suke so haka?, Allah sarki sabo tirken wawa, ya saba da ɗabi'arsa na rashin ɗaga idanu ya kalli abu, da wuya ya dai'na.
Da yake yana jin yunwa, sai ya wuce wajen da ya saba zama ya zauna, yana zama gabaɗaya wutar gidan ta ɗauke diff tamkar dama wutar nepa ce, mamaki ne ya kama shi, ta ya akayi engine nan ya mutu? Tun da yazo Naija da aka ɗauke nepa sau ɗaya aka yi wajen 3 hours ba'a dawo da shi ba, daga nan ya yi watsi da nepa ya saho wani tampatsetsen engine wuta, mai matukar gudu da bada wuta mai karfi, baya shiri da zafi, Shiyasa ba zai iya zama babu wuta ba.
Wani irin mugun tsoro ne ya dira mata a ranta ganin duhu ya mayaye ko'ina na cikin ɗakin, kun santa da tsoron bala'i, shi kuma jingina kansa da jikin sofar dake kusa da shi ya yi tare da waro idabunsa sosai yana kallon gabansa, ma'ana yana kallon in da yake fuskanta.
Shiru shiru wutar bata dawo ba, shi kuma bai kunna wutar wayarsa ba, yana jin ta yadda take wani jan numfashin tsoro a hankali hankali, alamar ta tsorata over.
Almost 10 mins shiru babu wuta babu labarinsa, sai raba idanu take yi, shi kuma har jikinsa ta fara haɗa zufa, ya tsani zafi fiye da tunanin mai tunani, Sojoji goma sha huɗu da su Mark a gidan amma wuta ta ɗauke har tsawon minti goma basu duba me matsalar ba?.
Guntun tsaki ya ja tare da ɗago kan nasa da nufin ya miƙe ya nufi wajen, kwatsam sai ga hasken wutar ta dawo, wani mahaukaciyar ihu ta kurma tare da sulalewa kasa sumammiya.
Da mamaki ya kalleta kwance a kasar, ko me ya sumar da ita Oho, yarinya tamkar mai aljanu, tamkar kanta biyu, da yake tana kwance ne sai bai samu damar ganin face nata ba, kuma irin kwanciyar da ta yi, ta ɗaura hannunta ɗaya a saman kumatunta, dan lokacin da take kurma ihun sai da ta dafe kumatun nata da hannayenta dukka biyu, ba komai ne kuma ya sanyata ihu da suma ba fa ce ganin cikin kwanyar idanunsa da ta yi, tana fuskantarsa, ga shi da yake a duhune idanun nasa a buɗe suke sosai, kuma shima yadda ya yunkura zai tashi ita yake fuskanta, hakan yasa ta kalli tsakiyar kwayar idanun nasa, ba ƙaramin razanata suka yi ba, saboda hasken wutar yasa kwayar idanun sun kara kyalli.
Komawa ya yi ya zauna, har ya kai hannu zai ɗauki ruwa ya zazzage mata a kai, nan take zuciyarsa ta tunano mashi da irin farincikin da TRIPLETS nasa suka shiga ɗazun a ta dalilinta, har ga Allah yaji daɗin da bai taɓa ji ba na ganinsu a wannan farincikin, tuna hakan yasa ya fasa zazzaga mata ruwan sanyi, dan kada ta cutu sosai, idan ya zazzaga mata wannan ruwa mai uban sanyi, to fa a haukace zata tashi, idan ba'a yi Sa'a bama, tana iya hayewa kansa, dan fita zata yi a hayyacinta.
A na haka sai ga Areef ya shigo ɗakin shima yanzu ya idar da sallah, daman sun rabu da Lion ne, shi ya wuce bedroom nasa dan yin Sallah a can, Imran, Lion kuma suka wuce masallaci.
Wajensu ya nufo dansu ci abinci, yanzu kusan gabaɗaya ya tare a ɗakin ɗan uwan nasa.