Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 43
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 43: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 43. Sai wani lumshe idanu yake yi ya kariso cikin…
3,343 words
Sai wani lumshe idanu yake yi ya kariso cikin ɗaki, da sauri ta miƙe tare da nufo shi tana yi mishi sannu da dawowa cikin harshen turanci, da yauwa ya amsa mata tare da rungumota, ta sha kwalliya da wata danƙareriyar doguwar riga mai bala'in kyau da tsada, bata yi wani make up sosai ba, dan ba wani son make up ɗin take yi ba, iya ka powder ta murza da kwalli, ta ɗaura gyalen rigar a kanta kafin ta sanya hijabi, dukkansu bayin Allah sun shiga sabuwar rayuwa, da alama ma sun mance da rayuwar da suka yi a baya, idan kuma basu mance ba, to akwai wani abu a kasa, amma lokaci ne zai nuna mana komai, dan abin da mamaki yadda Abba bai yi mamakin sauyawarta ba, duk da eh yasan haka take a baya, amma basu nuna wata alamu da zata nuna cewa sun san sun yi rayuwa cikin kazanta da wahala ba, ko da yake dama idan dodannin ma suka zo suka zanesu, mantar da su komai suke yi, koma dai me lokaci zai nuna mana menene yake faruwa? Menene gaskiyar lamari?.
Sannu da zuwa ta yi mishi, shi kuma cike da nuna so da kulawa ya tambayeta ina su Imran, AKil, AKila, basu dawo bane?, Da mamaki cikin harshen turanci ta ce "Su Imran ban san in da suke ba, Akila kuma ta tafi school, amma ka kira mini Imran ɗin a waya, ya zo maza, ko ina suka shige Oho". Sai da ta yi maganar ya tuna Akil ya gaya mishi zai koma Madina sati mai zuwa, ya sha'afa da zancen baki ɗaya sai da ta yi maganarsu yanzu.
To ya amsa mata da shi tare da ciro waya ya kira number Imran ɗin, bugu ɗaya ya ɗaga, cikin girmamawa ya gaishe da Abban nasa, da fara'a sosai a kan fuskarsa ya amsa tare da ce mishi "Ina kake ne Imran?" "Abba ina gidan Saif ne lafiya?" Nisawa ya yi kafin ya ce "Tom ka zo Ammie ku na buƙatar ganinka yanzu". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Abba jelly ce bata da lafiya, babu ta yadda za'ayi na tafi na barta". "Me ya sameta?" Ya faɗa yana ɗan zaro idanu, ita ma Ammien zaro idanu waje ta yi tana kallonsa tana jiran ta ji me ya faru.
Ƴan kame kame ya fara yi musu, daga nan Abban ya fahimci menene matsalar, dan haka sai ya ce zuwa yamma idan ta sami lafiya ya taho da ita, da mamaki ya ce "Abba Ammie ba zai zama matsala da ita ba?" "E babu komai ka taho da ita". Okey ya amsa da shi, katse kiran Abban ya yi tare da juyowa yana kallonta yadda ta tsare shi da ido tana jiran ta ji menene yake faru, Ammie ba karya kyakkyawa ce idan baku manta ba, gata fara tas mai ɗan ƙaramin jiki, idan ka ganta, ba zaka bata bata shekarun nan nata ba, ba zata taɓa cewa ita ta haifi Imran, Akil ba, amma za'a iya cewa ita ta haifi AKila, nan ma ba kowa ne zai yarda ba, dan ba karya ta mori jiki mai kyau.
"Me yake faruwa Abban Imran?". Still dai cikin harshen turanci ta yi maganar, to fa akwai ayar tambaya a nan, kenan bata jin hausa ne ko kuma yaya ne? Ko dai dama ba su yin magana da hausa ne before ta fara ciwo? To Allah masani mu dai je zuwa, koma menene munanan zamu ji komai daga biri har wutsiya.
"Ɗan ki fa ya angwance ne, idan an sami baby sai ki shirya zama kaka". Ya faɗa yana mai sakinta ya nufi toilet, da sauri ta sake shan gabansa tana faɗin "Ban gane ya angwance ba? Yaushe ya yi aure kuma?". Ɗan shafa kan ta ya yi cikin zoyala ya ce "Au a bayanan da na yi miki jiya ban gaya miki sun yi aure ba ko?". Da sauri ta gyaɗa mishi ka alamar e "To da Imran da Akil duk sun yi aure". "Kai, kai, kai a lallai tom waye suka aura ban sani ba?" Kai tsaye ya gaya mata su waye ne matan nasu, fuskarta ɗauke da fara'a ta ce "Tom ka kirasu duk su kawo mini matan nasu nan yau ɗin nan ba sai gobe ba, su kawo mini surukaina mu zauna". Jinjina mata kai ya yi babu ko ɗigon alamar mamaki a face nasa, da alama dai jiya sun yi zama da ita ne, tun da kunji ya ce a bayanan da ya yi mata bai gaya mata su Imran sun yi aure bako? Hakan na nufin jiya ya mata bayanin wasu abubuwa shiyasa baya mamaki.
Toilet ya shiga ita kuma ta wuce ta fitar mishi da kayan sakawa tare da zama saman gefen bed tana jiransa ya fito.
A ɓangaren gidan Lion kuwa.
Da misalin karfe 4 na yamma, suna zaune a garden suna hira, Aseef, Areef, Rimsha, dukkansu fuskokinsu ɗauke da murmushin, da gani kasan suna jin daɗin kasancewa a tare, sun nutsa cikin hiran da suke yi ne Areef ya ce da Rimsha "Our Queen jeki ki ɗauki abincin Lion ki kai mishi ɗakinsa kin ji?". Zaro wannan fararen dara daran sleeping eyes ɗin nata ta yi, ba ita kaɗai ba har da Aseef, shi ma ya sha ruwan mamaki har sai da ya zaro idanu waje.
"Yaya Areef abincin yaya Saif kuma?" Ta yi maganar tamkar zata sa kuka, shafa kan ta ya yi cike da kulawa ya ce "E sister abincin shi, kada ki damu ba zai hanaki zuwa school ba, na rana da dare kawai zaki rinƙa kai mishi, da safe Mark zai kai ki school, yau Aseef yana barci, ni kuma ba zan iya tuki bane yasa Mark ya je ya ɗauko ki, shi kuma Prof matarsa bata da lafiya, shi ne nace ya zauna kusa da ita, to daga yanzu Mark ne zai rinƙa kai ki school, tashi ki je ki kai mishi abincin da wuri, tun ɗazun kinga ya yi mini massage". Tom ta amsa mishi da shi tare da miƙewa jiki ba kwari ta nufi cikin gidan, kamar dai kullum kananan kaya ne a jikinta, wando jeans baki da t-shirt maroon, ta ɗaura wani ɗan ƙaramin gyale baki na doguwar rigarta a kanta.
Bayan tafiyarta Aseef ya dubi Areef ya ce "Areef what is going on ne? Me yasa zata kaiwa Lion abinci?". Wayarsa ya ɗauko ya fara latsawa yana faɗin "Bincike mana, bincike a kan face ɗin nan nata Lion ɗin yake yi, ai dama na gaya maka zai buƙa ce ta a kusa da shi, sai dai ba zai ce mata ga abin da yake yi bane, kuma ka bita yanzu ka gani, ka san me nake tunani?" .
Girgiza kai ya yi alamar a'a "Idan ta je ɗakin, zai rinƙa yawan ganin face nata dan aikinsa, da aikin babanta, ina mishi mummunar addu'a da ya faɗa tarko, wlh duk wadda ya kalli sister sai ya ji yana sonta, shi ma kuma zai sota In Sha Allah, mu zuba ido mu gani, ina tunanin ma ni kam nan ba da jimawa ba hakan zata faru, dan zaka kalla zai ɗan saki jiki da ita, sannan kuma zai so ta rinƙa zama kusa da shi, abin da yasa kuma zai so zamantaa kusa da shi, kasan halinsa, yafi karfin ya nemi alfarma or ya tambayi wani mutun wani abu, to akwai tambayoyin da ya kamata ya yi mata, amma ba zai yi ba saboda idan ya yi hakan kamar ya nemi alfarma a wajenta ne, zai yi amfani ne da zaman da take yi kusa da shi ya binciko amsoshin tambayoyinsa da kansa".
Shiru Aseef dai ya ɗan yi kafin ya ce "Ni ma fa ina son in sami special time, lokacin da yake cikin farinciki na gaya mishi batun aure na, ya je ya nema mini aure heartbeat". A sukawane ya juyo da ash eyes nasa zuwa kan Aseef ɗin, cikin sauri ya ce "Amma Aseef yau ka sha wine (giya) ko?" "Wine kuma?" Ya faɗa yana zaro idanu.
"E mana wine, yo idan ba wadda ya sha wine ba, waye zai ce Lion ya je ya nema mishi aure, hmmm wlh na rantse ba zan yi kaffara ba, idan kayi ganganci yi mishi magana ma ba zai kula kaba, idan kuma ka matsa ya kula ka ya je, to fa ka sani da kai da Heartbeat har abada, dan kuwa izza da isa zai je ya nunawa iyayenta, ko ma ya ce a ɗauko mishi iyayen nata a kawo su har nan, idan hakan ta faru kuma Heartbeat ɗin taka zata dai'na sonka, dan su a nan kasar basu yarda a raina iyayensu, suna bin umarnin iyayensu sosai, ba zata taɓa yarda tana ji tana gani Lion ya sanya a ɗauko iyayenta kamar wasu yaransa a kawo su gidan nan ba, kuma ta yarda ta cigaba da zama da kai ba, na dai gaya maka, gwara ka canza hanya dan Lion kam ba zai je neman alfarman a baka aure ba, yanzu fa na gama gaya maka, wasu tambayoyi yake son yi wa Rimsha, amma saboda yafi karfin neman wani abu wajen wani, shi ne gara ta rinƙa zama kusa da shi tana kai mishi abinci daga motsinta da yanayinta har ya fahinci abubuwan da yake so, na buɗe laptop nasa jiya, na rasa a ina ya samo hotunan kusan gabaɗaya family'n uncle Hossain, har da mahaifin Prof naga hotonsa a can, ina ga fa babban al'amari ne kuma babban case ne ba kaɗan ba, dan daga bayanan da naga ya samu akwai rikici ba kaɗan ba, Rimsha ita kaɗai ce wadda take da kusanci da uncle Hosain, kaga ko Prof bai da kusanci da shi sosai, shiyasa Lion ya zaɓeta, ba dan haka ba Prof ma ya wadatar, amma Prof bai san Komai game da uncle ba, kuma ba sai na sake gaya maka ba, Kasan Lion ba zai tambayi uncle Hossain wani abu dan gane da binciken ba, ita dai Rimsha ta hannunta zai sami biyan bukatarsa, mu dai namu idanu kawai". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa yana mai jin tausayin Aseef ɗin, dan kuwa yasan Lion ba zai je neman auren nan ba, idan kuma suka matsa, to sai dai yasa a tattaro mishi iyayen yarinya a kawo mishi, su zo nan su karɓi sadakin ƴarsu, su kuma bada auren a nan a ɗaura iya su kawai, babbar magana lallai akwai kallo.
Areef na tafi Aseef ɗin ya ciro wayarsa ya fara kiran daddyn Rimsha, bugu ɗaya ya katse ya kira shi, yana ɗauka ya saka mishi kukan shagwaɓa, daga ɗayan ɓangaren yana daga zaune saman sofa a part ɗin Aseef ɗin na Washington DC sanye da kayan barci masu kyau da tsada ya fara magana a nitse "Haba mana ɗan auta, waye ya taɓa mana kai kuma da kake kuka?".
Shagwaɓe fuska ya yi "Uncle ni wlh kawai ka zo Nigeria mu je neman auren heartbeat, ba zan taɓa yarda ba, Lion ba zai neman mini aurenta ba, kuma ni aure nake son yi da wuri, dan haka kawai kazo Nigeria gobe sai mu je wajen Abbanta".
"To shikenan yanzu dai a dai'na yi mini kuka, ba dai auren AKila ba ce? To ka kwantar da hankalinka, Akila taka ce, ba sai nazo Nigeria ba, ni kaina ina da damar aura maka ita, amma sai na gayawa baban nata duk da nake da daman, yanzu dai duk ranar da ka shirya zuwa ganin Abban nata, idan ka je ka kirani a waya ka haɗa mu, zan yi magana da shi, dolema ai a baka Heartbeat ɗin ka, idan ba haka ba mu hana kowa kwanciyar hankali, mu takurawa kowa". Ya kai karshen maganar cikin zolaya.
Cool murmushi ya saki yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya, sai yanzu ya ji daɗi a ransa, shiyasa yake bala'in kaunar uncle Hosain ɗin nan, duk yadda zai bi ya faranta mishi rai ya sani, yana kula da shi ba ɗan kaɗan ba, yana son farincikinsa sosai tamkar kaninsa na jini. "To shikenan Uncle zanje wajen Abban nata gobe In Sha Allah". Okey daddyn Rimsha ya amsa mishi da shi, daga nan suka shiga hirar duniya abinsu da kuma kewar juna, yana yi yana karawa Aseef ɗin karatu, Aseef da daddyn Rimsha sai Allah, suna matikar kaunar junansu ba kaɗan ba.
A ɓangaren Rimsha kuwa, Kitchen ta nufa, hannunta ta wanke kafin ta ɗauki abincin, ga mamakinta yau da ta cewa Mark sannu ya ce mata Okey, tambayar kanta ta yi to ko dan ta jima bata shigo Kitchen ɗin bane yasa ya amsa mata yau kuma? Oho mishi mutun kamar wani aljani, daga shi har ogan nasa baka taɓa gane musu, kamar waƴan da ake pappasu, yau ka gansu fari, gobe kuma baki, sai ma ka rasa gane ina ne alkiblarsu dan bakin hali. Duk wannan masifa fa a cikin zuciyarta take yin shi, Mark na kona mata rai da abin da yake yi matan nan, dan iskanci yau ka gan shi fari, gobe kuma baki, ji take kamar ta yi ta tsitsinkawa ɗan banza mari har sai wannan farar ɓul ɓul ɗin kumatun nasa sun yi jawur kamar tumatiri ruɓaɓɓe ko zata ji daɗi. Shi dai ko kallon in da take ma bai yi ba, kawai yau en amsawar ne suka zo shiyasa ya ce mata okey ba tare da ya kalli in da take ba.
Wucewa ta yi zuwa bedroom ɗin Lion, a bakin kofa ta tsaya ta yi sallama, can kasa kasa da ta kasa kunne ta ji ya amsa kamar baya son buɗe baki ya yi magana, kutsa kai ciki ta yi tana mai jin kirjinta na dukan uku uku, a in da ta saba ajiye mishi, nan ta nufa ta ajiye tare da zama, ta wutsiyar idanunsa ya kalleta.
Yau dai da zamanta a wajen bai fi minti biyar ba sai ga shi ya miƙe ya nufota, gefenta ya zauna a in da ya saba zama kenan, cike da kasada da tsoro ta ce mishi "Good evening". Bai amsa ba amma dai ya gyaɗa mata kai, da yake tana duƙe ba kallonsa take yi ba, sai bata san ya yi hakan ba, abinci ta fara zuba mishi, kamar dai yadda ta saba, bayan ta kammala ta tura mishi a gabansa, spoon ya ɗauka ya fara ci.
Shiru ta zauna tana ɗan satar kallon kyawawan fararen kafafunsa da ya lanƙwashesu dan yin zaman cin abinci ta sunnah, wato kamar yadda annabi yake yi kenan. Can kasa kasa kamar a mafarki zazzakar muryarsa ya daki dodan kunnenta a kan ta miƙo mishi wayarsa da laptop nasa, okey ta amsa tare da miƙewa a nitse.
Tana miƙewa ya ɗago dara daran blue eyes nasa ya bita da kallo, ɗauko laptop ɗin ta yi tare da wayar, har lokacin bai kawar da kallonsa a kanta ba, zubawa face nata idanu ya yi yana son yaga action ɗin da zata ɗauka lokacin da zata kalli home screen na laptop ɗin.
aura kaɗan ta saki laptop ɗin ya faɗi kasa ya tarwatse lokacin da idanunta suka sauƙa a kan screen ɗin, ta sha ruwan mamaki sosai ganin wata kyakkyawar farar baturiya mai kama da daddynta sak babu maraba, ba dan ta ganta da gashi ba ma, da sai ta ce wannan daddynta ne, sun yi kama sosai over, tsayuwa ta yi tana kallon matar ta manta ma da shi ya aiketa, ta mance ma da a ɗakinsa take, ga shi dai matar ba babbar mace bace bare tace ko yar daddynta ne ko wani abu, a yadda take ganin matar ba zata wuci 28 years ba, da alama ma budurwa ce, tariyo fuskar ƴan uwan daddynta da ta sani gabaɗaya ta fara yi a cikin ƙwaƙwalwarta, duk wadda ta tuno sai taga baya kama da wannan mata sosai sai daddynta, ba dan wannan mata ta fi Jehan shekaru ba, da sai ta ce Jehan ce, dan kuwa babu maraba. Ganin wannan ta shiga duniyar tunani ba zata kawo mishi laptop ɗin bane yasa ya yi mata gyaran murya tare da ɗauke kallonsa daga kanta.
A hanzarce ta ɗago tana kallonsa, jikinta duk ya mutu, da sauri ta kariso wajen nasa tare da zama kafin ta miƙa mishi laptop ɗin, hannu yasa zai karɓa hannunsu ya goge na juna, cikin sauri ta sake mishi dan wani irin shock da ta ji, shi kuwa ko a jikinsa ya karɓa ya ajiye a gefensa wajen da ya saba ajiyewa, kasa kasa ya ce ta bashi ruwa, a hanzarce ta zuba ta miƙa mishi, still ya zo karɓa hannayensu ya sake haɗuwa, cikin sauri ta sakar mishi cup ɗin, shi kuma bai kai ga riƙewa da kyau ba, ruwan gabaɗaya ya zube mishi a saman cinyarsa, gently ya ɗago da idanunsa ya sauƙe a kan face nata dan yaga wai me matsalar yarinyar nan ne? Dan hannunsu ya taɓe na juna take haukace mishi haka.
Daidai lokacin da ya ɗago idanu, ita ma ta ɗago nata dan ta kalli wani irin action ne a kan face nasa da ta zubar mishi da ruwan, yau a karo na biyu suka kalli juna ido cikin ido, da sauri ta yi kasa da kallonta, shiru ya ɗan yi kafin ya ce da ita ta miƙo mishi hannunta bari ya gani, a razane ta ɗago kanta, nan take idanunta suka cika da kwallah, addu'a take yi Allah yasa ba wani hukunci zai yi wa hannun nata ba dan ta zuba mishi ruwa a jiki, shi kam tambayar kansa yake yi wai me matsalar yarinyar nan ne? Daga ya ce ta bashi hannu har ta fara kwallah, daga hannunta ya taɓe nasa ta zubar mishi da ruwa a jiki, ba dan akwai abin da yake son sani a tattare da ita ba ai da ya bata hukunci mai tsanani, yariya kamar ba lafiya take ba.
Jikinta har ya fara kerma ta miƙo mishi hannun nata tare da runtse idanu, nan take hawayen da suka cika mata idanu suka gangaro saman kuncinta, kallon second biyar ya yi wa hannun nata kafin ya kai nashi hannun ya kama natan, waro dara daran sleeping eyes nata waje ta yi, jujjuya hannun nata ya yi kamar mai neman wani abu, ga yatsun nata zara zara da su sak irin na Areef, ya ɗan yi mamaki ganin irin ƴatsun Areef a tattare da nata, amma bai wani damu ba, dan ba yadda Allah baya halittar bawa, shi dai ya riƙe hannunta ne dan ya ga wai me matsalar ta dan hannun nata ya ɗan taɓa nashi har take yi mishi ɓarna, baya son hukunta ta, dan haka baya son ta yi mishi ɓarna ta ɓata mishi rai, baya son abin da zai dakatar da shi daga binciken da yake yi, shiyasa zai kawar da duk wani abin da zai ja ta yi mishi wani ɓarnan da ba daidai ba har ya hukunta ta.
Almost second 30 yana riƙe da hannun nata yana jujjuyawa kafin daga bisani ya saketa tare da maido da kallonsa zuwa saman face nata, da sauri ta yi kasa da idanunta, "Dama ganganci yasa kike yi mini ba daidai ba?" Shi ne abin da ya faɗa, girgiza mishi kai ta yi har lokacin tana hawaye, "To me matsalarki dan hannunki ya taɓa nawa zaki zuba mini ruwa a jiki?". "Babu komai". Ta bashi amsa, shiru ya yi daga nan bai sake magana ba, sai ma miƙewa da ya yi ya nufi dressing room nasa dan ya canza kaya, bin shi da kallo ta yi tana mamakin wai shin yau wace iriyar sa'a ne taci a rayuwarta da har ta yi mishi laifi bai hukunta ta ba, ita da ko bata yi laifi ba in dai ta biyo hanyar da aka yi mishi laifi a wajen to sai ya hukunta ta, anya yau lafiya yake kuwa? To ko dai mala'ikun rahma da imani sun rokawa zuciyarsa samun imani da rahmar ne? Ta tambayi kanta, bata san akwai abin da yake nema a tattare da ita bane yasa bai yi hakan ba, yo idan ba dan haka ba ai da wani zance ake yi yanzu.