Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 6
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 6: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 6. Shafa kanta ya yi cikin sigar rarrashi ya fara…
3,362 words
Shafa kanta ya yi cikin sigar rarrashi ya fara magana "Rimsha bappa Hosain ya yi kuskure, ba laifin Saif bane, laifin bappa Hosain ne, tayaya zai yi irin wannan furuci a gare su? Bari na fahimtar da ke wani abu, ki sani tsawon Wannan lokaci da baku tare da bappa yana tare ne da su ne fa, yana gidansu na Washington DC, ya zauna da su, wlh tun kafin su zo nan idan muka yi magana da Areef, ba zai yi magana biyu bai kira mani sunan Musharraf ba, yana matukar son daddynki, haka zalika shima Aseef, wannan son da suke yi wa daddynki yasa Saif ya fara kaunarsa, ki sani wlh ko tsuntsuwa bata isa ta sauƙa a gidansu Saif ba, basu son baki ko kaɗan, amma Allah shi kaɗai yasan dalilin da ya sanya ya sa masu kaunar daddynki a ransu da har suka sanya shima Saif ya fara son shi, sun kula da bappa sosai, sun kyautata mashi, yasan halinsu mai kyau da mara kyau, meyasa zai zo ya yi irin wannan furuci akan su na cewa yasan turawa basu da hankali, basu da hankali suka kula da shi haka? Ai ko dan saboda Aseef da Areef tun da bai san Saif ma yana kaunarsa ba, ko dan Areef bai kamata ya yi wannan magana ba, kuma na ƙara gaya maki Saif yana kaunar bappa saboda yadda ya rinƙa sanya Aseef farincikin, mawuyacin abune ki iya gane idan Saif yana son wani abu, amma su Areef sun gane yana kaunar Bappa, to kinga bappa ya yi kuskure, yes ke ƴarsa ce, yana da kyau ya nuna irin haka a kanki, amma baga mutane irinsu Areef ba, yakamata ya tausasa kalaman shi ne a kan su, ni da ban zauna da su a cikin gidansu na Usa ba ma, nasan cewa wallahil azim su ba manema mata bane, ke su dukka da kike ganinsun nan basu da lokacin mace, harta Areef da kike gani mai sauƙin kannan, yanzu da zaki kawo mashi maganar aure in a serious matter, dariya zai yi ya mai daki baki san me kike yi ba, babu zancen aure ko neman mata a ransu, saboda suna ganin ɓata lokaci ne, kawai ni na yarda wani iko ne na Ubangiji da yasa suke kaunarki, daga Areef har Aseef, Allah ne kawai ya sanya masu kaunarki, to su ba mazinata bane ,basu neman mata, amma bappa ya zo ya masu magana a gatse haka, wai turawa mazinata ne, basu ɗauki zina a bakin komai ba, kinga kuwa dole Saif ya ɓata rai, wlh ina mai tabbatar maki Saif ya yi maku hukunci mai sauƙin daga ke har bappa, kuma ya yi hakan ne saboda ni, dan ni ya sassauta maku hukuncin, to dan haka ki godewa Allah ma da hakan, sannan magana ta karshe ina son ki sani Saif ba mugu kamar yadda kike tunani bane, kawai haka yanayinsa yake, kuma bappa ya ɓata mashi rai ne, dama sai anyi laifi yake yin hukunci, baya hukunta wanda bai yi laifi ba, ina da tabbacin idan ya sauƙo zuciyarsa ta yi sanyi, shi da kansa ba zai so kina mace ƴar musulma kuma kina shiga ɗakin su Mark ba, ba zai so hakan ba, kuma zaki gani, zai dakatar da ke daga yin hakan, ni nasan waye shi fiye da yadda kike zato, amma dai kafin ya sauƙo ya waiwayeki ɗin shi ne aiki, zaki sha wuya kam, da ya sauƙo kuma shikenan zai dakatar dake daga yi wa su Mark aikin, sai dai fa rabaki da bappa kam ya riga da ya yi, an wuce wajen, shi ma aikin abin da yasa na sanya a raina zai dakatar dake, saboda shi musulmi ne, yasan haramcin hakan a addini, ke dai ki yi addu'a kawai, amma ki daina ganin laifin Saif". Ya kai karshen maganar tare da shafa kanta ya gangaro da hannunsa izuwa saman face nata ya goge mata hawaye.
Suna cikin haka Areef ya lallaɓo ya iso wajen ya same su, jikin nasa Alhamdulilah, ya sami kulawa daga wajen ɗan uwan nasa sosai, cikin ƙanƙanin lokaci ya sami sauƙin ciwon nasa.
A ɗayar kujerar dake fuskantarsu ya zauna yana tambayar Imran me ya yi wa Sarauniyar Triplets ɗin su, ya yi maganar yana zarewa Imran ɗin idanu.
Imran bai san time da dariya ta subce mashi ba, ji yadda Areef ya zare mashi waƴan nan dara daran idanun nasa, ai sai ya sa mutun ya gudu, ita ma dai Rimsha ya bata dariya kuma ya bata tsoro, domin kuwa, idan baku mance ba, akwaisu da dara daran idanu kamar ball, zarosu da ya yi kuwa, ai kunga za su kara girma.
Ganin ta yi dariya ne yasa shi ma ya saki cool murmushi. "Our Queen dariya yana yi maki kyau sosai over". Ya faɗa cikin sanyin murya. Kasa ta kara yi da kanta tana wasa da yatsun hannunta.
Kai ash eyes nasa ya yi saman hannun nata, wani irin tausayinta ya ji lokacin da ya kalli hannun nata, har lokacin sunanan wasu iri da su, sun ɗanyi wani baki bakin ciwo, alamar wajen yana son warkewa.
Sorry ya yi mata tare da gaya mata kalamai da za su sanyaya mata zuciyarta, ya kuma yi mata alkawarin ba zai sake bari ayi mata makamancin haka ba, komai wuya komai daɗi zai yi kokari wajen ganin ya cika alkawarin da ya ɗaukarwa Uncle Hosain ɗinsa na kula da ita.
Amma fa da ni da ku munsan sone ya jawo hakan, ita da Imran ne ba su sani ba, ba wani alkawari, kawai sonta yake yi yana dannewa saboda Saif take so, kuma a zahirin gaskiya shi ya fi su Saif sanin menene so, domin kuwa shi ya fi su yawan shige shige, Saif bai san menene so ba, dan kunsan baya shaga irin wannan layin, shima dai Aseef yanzu ba za'a yanke mashi hukunci ba, domin yanzu a sabon mutun yake, yanzu yake tantance daidai da ba daidai ba, Imran da yake wani gaya wa Rimsha su basu son mata, to ga dai Areef ya kamu da soyayya, sanin basu son mata or aure, sanin baya ya yi masu, sai dai auren ne har yanzu bamu sani ba, shin suna da niyar yi ko yaya, ko kuma muce Areef yana da niyar yi, domin shi kaɗai ne ya san me soyayya ma a cikinsu.
Kalamansa yasa dukkansu daga ita har Imran ɗin sun ji daɗi, sosai Imran ya yi mashi godiya, girgiza kai ya yi alamar baya son godiya, daga haka suka shiga hira, ta saki jiki sosai, ta mance komai ta biye masu sai hira suke yi, sun ɗauketa kamar wata babbar mace saboda hankalinta da natsuwarta, shiyasa basu damuwa suke sanyara a tsakiyarsu suna hira, ba zata rainasu ba, haka zalika tana da kamala sosai.
Suna tsaka da hira Aseef ya kira Areef a waya, wani daɗi na daban Areef ya ji ganin kiran Aseef ɗin, domin kuwa yana zargin Aseef ɗin, yana ji a jikinsa akwai wani abin da yake damun ɗan uwan nasa, ya yi mashi tambayar duniyar nan yaki gaya mashi, sai dai ya ce mashi Exam ne yasa ya shiga damuwa, baya son ya faɗa ne, kuma duk wata hanya da Aseef zai bi dan ya ɓoye damuwarsa ne ko menene Allahu aalam, to fa sai da ya bi wannan hanya, idan ba su da suka yi mashi muguwar farin sani ba, ba zaka taɓa cewa akwai abin da yake damun shi ba dan ya ɓoye.
Ɗaukar kiran Areef ya yi yana mai sakarwa ɗan uwan nasa cool murmushi, zaune yake saman irin waƴan nan manyan baloon na gym ɗin nan, ba bu riga a jikinsa, sai dai wata shegiyar ƴar short da bata gama sauƙa zuwa cinyarsa ba, ga shi wandon ta matse shi sosai, ta roba ce, irin dai wannan ɗan short da mafiya yawan masu motsa jiki suke sanyawa, to shi, waƴan nan santala santalan cinyoyin nasa a waje, ga gashin kansa sai kara tsawo yake yi, sai kara komawa sak kamanin su daddy yake yi abinsa, ya kara wani sihirtaccen kyau da sheƙi irin na addinin musulunci.
Satar kallon Rimsha Areef ya yi domin kuwa yau da ta ga Aseef a irin wannan shiga, da ta yi suma sau bakwai, ranar ma ba riga kawai ta gan shi, amma sai da ta razana, ina ga kuma yau mai kankanta da har zanen komai nasa ana gani, ai sai suma idan suka yi ido biyu.
Dawo da kallonsa ya yi a kan wayar. "Aseef kana buƙatar aure fa". kasa kasa cikin zolaya ya yi maganar.
Kin haɗa ido da shi Aseef ya yi, kuma Areef ya lura da rashin son haɗa ido da su da Aseef ɗin yake yi, dan baya son suna mashi kallon kurillah. "My Areef ina kewar kane fa yasa na kira ka". Sake maimaita maganar ɗazun Areef ya yi "Aseef kana buƙatar aure fa".
Sai lokacin ya ɗago kai suka kalli juna "To ai sai ku yi mani auren ko?". Jinjina kai Areef ya yi yana faɗin "Ai ko baka faɗa ba, zan sama maka mata a Nigeria in taho maka da ita".
Ɗaure fuska sosai ya yi yana faɗin "Ni bana son matan Nigeria, ni ka bar wannan shirmen ya jikinka?". "Am good now, hope kaima everything yana tafiya yadda kake so?". Girgiza kai ya yi alamar a'a ba komai yake tafiya yadda yake so ba.
"To me matsalar?". Shiru ya yi, tamkar shi da kansa bai san me matsalarsa ba, abin mamaki take bawa Areef, wai yau Aseef ne da jin kunyarsu, sai wani kau da fuska yake yi, anya lafiyarsa kuwa? Abin al'ajabi kunya a cikin jinin William jacop, suda kwata kwata ma basu san menene ita ɗin ba, kunya Hausa fulani suka santa, ba turawa ba, abin ya ɗaurewa Areef kai, da yake basu san kunya ba, shi ne suke ganin kamar wani abin Aseef yake ɓoye masu, a zahirin gaskiya kuma kunyarsu yake ji yasa yake kasa haɗa ido da su, shi kansa ya rasa me yake damunsa da yasa baya iya haɗa ido da su ɗin. TO FA BABBAR MAGANA, ME YASA ASEEF KE JIN KUNYA KENAN?.
"Aseef ashe akwai wani abin da zaka iya hidden mana ka da musani? Ashe akwai abin da bai kamata mu sani ba a dangane da kai?".
Cikin sauri ya ɗago kai jin yadda Areef ya yi maganar, hakan ta nuna In a serious matter Areef yake. "No Areef i can't hidden anything for you, trust me ba wani abin da yake damu na, just kawai dai..... " Sai kuma ya yi shiru.
"Anywhere just kawai ka riƙe maganarka no need ma ka gaya Mani, yanzu dai ya school?". "Kai Areef sarkin fushi, to ni nace ba zan gaya maka bane?" Ya yi maganar a shagwaɓe. Da mamaki Areef yake kallonsa, wato idan ya tashi tsiyarsa har yanzu bai manta yadda ake shagwaɓa ba kenan.
"Areef ba fa wani abu bane yake damuna, just kawai kullun idan na kwanta barci ne, sai na yi mafarkin wata ta yi kissed nawa, kuma ba iya kiss kawai ba, just like husband and wife dai".
Wani irin ɗan iskan dariya Areef ya kwashe da shi, wato just like husband and wife, eyye su Aseef husband, bawan Allah shi ne abin dake damunsa, kuma ya kasa gaya masu, Allah Mai iko a gabaɗaya family'n William jacop shi ne kaɗai ya samu albarkar kunya, ya rasa ta ya zai yi ya rabu da wannan ɗan iskar mafarkin.
Areef kuwa tsabar mugunta dariya har da riƙe ciki, zuba mashi ido Aseef ya yi yana kallonsa, suma su Rimsha, da mamaki suke bin shi da kallo, dan a gaskiya ba su ji me Aseef ya ce ba, da yake kasa kasa ya yi maganar, kuma na gaya maku kunya yake ji, hakan tasa ma ya yi maganar kasa kasa dan kar wani ya ji.
Saboda tsabar iskanci irin na Areef sai ya ce "No Aseef explain it dallah dallah for me, like how husband and wife?". Yana magana yana guntse dariya.
Ɗan turo baki ya yi "Kai my blood, Like husband and wife mana, i knew you knew yadda husband and wife suke yi, tun da ka wuceni a karatu, ni fa yanzu nake karanta"
"No ni dai I didn't know anything, kawai just explain it for me". Shiru ya ɗan yi kafin ya sunkuyar da kansa kasa, wani irin kunya ce take kara rufe shi, bawan Allah ya ciri tuta, ko ba komai ya zama zakara a cikinsu, tun da har ya yi nasarar samu al'kunya.
"She is sleeping on my chest, and she is socking my penis sometimes, and also she is kissing my lips, yesternight she wanted to sock my nipples, amma Allah yasa na hanata, ni bana son this kind of dreams, suna bani haushi, please my blood help me".
(Jama'a an sanu wata tana son lalata mana Aseef ɗin mu a cikin mafarki🤔 kunji shegiya,🤣🤣 to ya kamata mu tashi tsaye🤣)
Shi kam Areef kamar zai mutu saboda dariya, duk waƴan nan abubuwa sai yanzu Aseef yake saninsu, bai ma san menene aure ba sai da Musharraf ya fara koya mashi irinsu FIQHU da sauran littatafan addini, shi ne ya san ma'anar husband and wife, a gaskiya ciwon Aseef dai bata yi mashi adalci ba wlh, yana da 30 years a duniya amma babu abin da ya sani, sai yanzu da Allah ya ƙaddara yana da rabon jin daɗin rayuwa, shi ne ya sami lafiya har ya fara sanin abubuwa, kai amma abin sam bata yi daɗi ba, sai dai kuma ya yi nasarar samun kunya a lamuransa, duk mutumin da bashi da kunya, wlh da sauransa a addinance, addini bata tafiya sai da al'kunya, sai dai fatanmu Allah yasa su ma Areef da Saif su sami wannan kunya ko da kaɗan ce.
"My Areef pls stop laughing at me mana, that's why fa naki gaya maka what's going on, shiyasa na yi hidden na abuna ni kaɗai, amma yanzu kazo kayi forcing ɗina na gaya maka, shi ne kake ta yi mani dariya ko?".
Tsagaita dariyar ya yi. "Do you know what Aseef?". Girgiza kai ya yi alamar a'a. "Good, duk abin da ta yi maka a cikin DREAM ɗin just kawai kaima ka yi mata reply, kayi accepting nata, idan ka tashi barci zaka ji you are normal". Ya kai karshen maganar tare da sake kwashewa da dariya.
Shiru Aseef ya yi yana kallon sanka sanka walaƙanci da Areef yake yi mashi. Ganin ya yi shiru ne yasa ya ce "Sorry my blood zan gaya maka solution, ka dage ka yi mata fyaɗe da karfi a mafarkin, idan ta ji wuya ba zata sake dawowa ba".
Nan ma shiru ya yi bai sake magana ba, dan shi maganar ma kunya take bashi sosai wlh. Shi kuwa Areef sake dariyarsa ya yi, domin kuwa yau Aseef ya kawo mashi sabuwar lamari.
After 2mins. "Am so sorry my Aseef" ya faɗa yana daidaita natsuwarsa. "Areef don't worry, ni ban damu ba, tun da kayi dariya, kayi farinciki to bani da wata damuwa, burina dama na ganku kuna farinciki!!".
Jinjina kai Areef ya yi, har cikin ransa yana mai jin tsantsan kaunar ɗan uwan nasa, shawara ya fara bashi akan ya rinƙa kwana da alwala, sannan ya rinƙa addu'ar barci sosai, In Sha Allah zai rabu da waƴan nan mafarkai mafarkan na banza, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, daga nan Areef ɗin ya kara tambayarsa akan idan ya tashi barci yana yin wankar tsarki ne ko baya yi, wani irin kunya ce ta sake rufe shi, cike da kulawa ya ce yana yi domin Musharraf ya koya mashi, ya gaya mashi cewa idan mutum ya zubar da spam sai ya yi wankar tsarki, kuma ya mashi bayani sosai a kan yadda ita kanta spam ɗin take da sauransu, daga nan kuma ya koya mashi wankar tsarki, to ta hakan ne ma yasan aure da sauransu.
Sosai Areef ya ji daɗi, ya kuma kara jin Kaunar Musharraf sosai da sosai, domin ya bada gudun mawa ba kaɗan ba a rayuwar Aseef, wadda da ba dan shi ba, da abin zai yi masu yawa, domin komai daga farko a ka sake koyawa Aseef, amma cikin hukuncin Allah yanzu komai na tafiya daidai yadda ake so da taimakon Musharraf, kuma hakan ma yasa Lion yake Kaunar Musharraf ɗin, domin duk wani dirama da suke yi da Aseef yana ganinsu ta cikin laptop nasa, ta camerar dake gidan nasu, wadda ya haɗa da laptop ɗin nasa, yasan komai, kuma kunsan family'n William jacop suma basu manta Alkhari ko mai kankantarta.
Suna tsaka da hira Lion ya yi wa Imran massage akan Rimsha ta kawo mashi abincin rana, karfe 2:30 ta yi.
Wani irin faɗuwar gaba ta ji lokacin da ta ji saƙon Saif ɗin, jikinta har ya fara kerma, dama tana son ta tambayi Imran ɗin wai me Saif ya ci da safe ne, tun da ta zubar mashi da abinci, amma sai Areef ya zo ya shashantar da maganar.
Jiki ba kwari ta miƙe ta nufi cikin gida, tun da ta fito garden ɗin, sai binta da wani mayen kallo, da wasu mayun idanunsa gateman yake yi, tamkar zai cinyeta ɗanye.
A kitchen ta isko Mark, kamar dai kullun ya ji shigowarta, amma bai ɗago ya kalleta ba, kun dai san halinsa. Wucewa ta yi ta wanke hannayenta, bata ce mashi ko sannu ba, domin ko ta ce mashi ma, baya amsawa, shiyasa kawai ta daina yi mashi magana, sallama ma a cikin zuciya take yi abinta,
Cikin natsuwa ta zo ta ɗauki tray ɗin abincin, sai a lokacin ta fara jin wani azababben yunwa na nukurkusan cikinta, sai da ta nufi kaiwa Saif abinci, sannan ta tuna ashe ko abincin safe bata ci ba, kuma ba komai ne yasa ta tuna hakan ba fa ce bala'in tsoro.
Addu'a take yi sosai tana tafiya. Gabanta kara tsananta faɗuwa ya yi lokacin da ta kai bakin kofar ɗakinsa.
Tsayuwa ta yi tare da daidai ta natsuwarta sosai, ta yi sallama cikin sanyin murya, kamar dai kullum, a cikin zuciya ya amsa sallama, hakan ma saboda yasan mahimmancin sallamar ce yasa yake amsawa, duk wani cikakken musulmi mumini mai bin Allah da Annabi, to fa ya zama mashi dole ne wajibi amsa sallama domin cika addininsa.
Jin shiru ne yasa ta yi kamar yadda ta saba, wato ta kutsa kai cikin ɗakin.
Tana isa tsakiyar ɗakin karaf idanunta suka sauƙa akansa, wani irin mahaukaciyar razana ta yi wadda ta sanyata sakin tray ɗin abincin ya faɗi kasa.
A karo na biyu ta yi mashi kaca kaca da ɗaki, gabaɗaya komai ya watse, wasu kayan abincin har kan gado, ga shi babban abin haushin komai na ɗakin white color ne, harta bed sheet, kuma ta lalata komai, gabaɗaya bed sheet ɗin ya ɓaci. Ba komai bane kuma ya sanyata wannan irin Mahaukaciyar razana fa ce ganin ainahin surar jikinsa da ta yi, yana tsaye ne a gaban mirror, daga shi sai towel a kugunsa, da alama wanka ya fito, iya ta bayansa ta gani yasa ta razana haka, ina ga kuma sun yi ido huɗu ba riga a jikinsa? Ina ga ta gan shi ta gaba babu riga? Ko da yake dole ta razana, domin kuwa ya kai matakin da dole mai zuciya a kusa ya razana da ganin ainahin kyakkywar surar jikinsa, yana da wata sihirtaccen kyau ne na fitan Allah, ga shi ya yi gym sosai, damatsan hannun nan nasa ba'a magana, ga uban faɗin kirji, sannan ga bala'in kwarjini.
Turus ta tsaya ta kasa sake ɗaga ido ta kalle shi, haka zalika ta kasa gaba ta kasa baya, sai dukan uku uku zuciyarta ke yi mata, ji take yi ranta na barazanar fita daga gareta, wani irin wahalallen yawu ta haɗiye, wasu zufar wahale suka fara karyo mata a gefe da gefen kunnenta, tsoron kai kallonta a kan ɓarnar da ta yi ma take ji, a wannan karonfa ko kerma jikinta ya kasa yi, yadda zai tabbatar maka tashin hankalin dake sanya kerman jikima, ashe karamin tashin hankali ne, idan tashin hankali ya yi tashin hankali to jikinma kasa motsawa take yi, bare kuma ma har ta yi kerma.