Triplets book 4 Complete - Chapter 82
Triplets book 4 Complete Chapter 82: Triplets book 4 Complete Chapter 82. Misalin karfe 1 aka daura auren Irfan da Pinky a kofar gidan Abbin, sannan suka…
3,343 words
Misalin karfe 1 aka daura auren Irfan da Pinky a kofar gidan Abbin, sannan suka je gidan Azharuddin Bature, a nan aka ɗaura auren Handsome da Zaira, daga nan suka wuce Kano wajen daddyn Jelly, nan suka sami Ayla da babynta kyakkyawan gaske, ita ma Maman Ayla tana gidan, dan dama daddyn Jelly ya mayar da ita wajen iyayenta ta nemi yafiyarsu, ta kuma yi sa'a albarkacin daddyn sun yafe mata, to shi ne ta cigaba da zama a gidan nasu, da Ayla ta haihu ne sai ta zo zama da ita.
A hanyarsu ta dawowa Abuja daga Kano ne Jehan ta kalli A'isha ta gidan Hjyr daɗi a kan hanya kamar mahaukaciya tana tafiya, sai tsince tsince take yi, Allah sarki ashe har Kano su Hjy daɗi suka zo suka jefar da ita, ƙwaƙwalwarta ya taɓu.
Sosai Jehan ɗin ta ji babu daɗi, sannan ta roki Areef da yasa a kaita asibiti a nema mata lafiya.
Hakan kuwa aka yi, yasa sojoji suka ɗauketa dan su kaita asibiti.
Akil da Umaisha dai suna Madina hankalinsu a kwance da ɗan babynsu gwanin ban sha'awa.
Sun je kauyensu Maryam, a nan suka tarar da babanta ya mutu bayan fama da ya yi da jinya na tsawon lokaci, cutar daji ce ta kashe shi, ɗan banza ko alhakinsu Maryam ɗin ma ai ba zai barshi ba, haka zalika ita ma yayarta Allah ya yi mata rasuwa shekara ɗaya da suka wuce, Maryam ta sha kuka sosai da sosai, sai rarrashinta Sir Safwan yake yi. Masu hali irin na Baban Maryam aya gareku! Tun lokacin bai kure maku ba ku tuba!!.
Ita kuma Adiva sun yi sa'a da suka je Maiduguri sun sami mamanta a can, dan haka uncle Shitu ya ɗauko matarsa suka dawo Abuja.
Gaskiya ba karya family fa sun yi ziyara sosai, sun leƙe yan uwa da abokan arziki sosai. A takaice dai wata guda suka yi a Nigeria kafin su tattara su koma ƙasarsu.
Lion ya cigaba da renon cikin Rimsha yana tarairayar kayarsa har sai da cikin ya bayyana kowa ya gani.
Sun sha ruwan mamakin ganin cikin nata, a lokacin cikin nata ya kai almost 7 month, abin da yasa kuma basu gane da wuri ba, kowa dai yasan Rimsha bata fita, ko nan da part ɗin gwaggo Lion baya barinta ta je, kullum zaman ɗaki kamar wata mai takaba, matar kowa daga cikin QUADRUPLE suna yawonsu a cikin gidan, amma ban da ita, sai tafi sati bata fito daga cikin bedroom ba, abin ku da mai ciki, daga barci sai wanka, cin abinci da sallah, to da yake kowa yasan halin Lion da bakar kishi, sai babu wanda ya damu kansa ko ya yi tunanin wani abin a kan rashin fitowar tata, kawai sai suka zuba masu ido, basu ankara ba sai ganin Rimshar suka yi da katon ciki kamar me.
Murna iya murna sun yi, Brr Naurat ta rinƙa yi wa Lion tsiya, abinku da Turawa ba kunya ke garesu ba, haka ta rinƙa yi mashi tsiya tana faɗa mashi cewa ashe abin da ya aikatawa ƴar mutane kenan yasa yake ɓoyeta a daki, sai dai ya ce mata ya yi ɗin ba kayarsa bace?.
Dukkansu ba mai alamar kunya a idanunsa ko kaɗan, waɗan nan family guda biyu suna sha'aninsu son ransu.
Rayuwar farinciki ya wuce baki ya faɗa suke yi, Anderson da His Excellence Lion ya turasu bakin gida, wani gidan kurkuku ne da yake a cikin teku, ba halin gudu daga wannan gida, dan a tsakiyar ruwa yake, ga bakar azabar da ake ganawa prisoners ɗin, abinci sau ɗaya ake basu a rana, kuma abincin ma rabin plat ne, ga uban duka da suke sha na safe daban na yamma daban, wannan gida shi ma Areef yasa aka jefa Hjyr daɗi da kuma Zinariya and Ƴar gwal bayan ya ruguje gidan nasu kenan.
Rungunar sojoji ya sa suka dira a Nigeria bisa umarnin shugaban kasa, yasa suka yi pata pata da gidan Hjyr daɗin, aka saki duk yaran da suke a ciki dan su koma gidajen iyayensu, sannan suka kwaso Hjyr daɗin ita da masu goya mata baya, aka zubasu a bakin gida, wannan bakin gida sai mutun ya gwammaci mutuwa da shiga gidan, dan ɗakunan dake a cikin gidan ma a tsaye bawa yake kwana, ba halin kwanciya, kafafu duk su kumbura, idan kunga bawa ya miƙe kafafu ya ɗan kwanta, to sai da safe idan sun fito tsakar gidan, kuma ba kullum ake fito da su tsakar gidan ba, a sati sau biyu suke fitowa, sauran kwanaki duk suna cikin ɗaki a tsaye kamar gumaka, suna ganin izayar rayuwa. To masu hali irin nasu aya gareku, mugu dai karshensa bata kyau!!.
Su kuma family yanzu komai zam zam, rayuwa mai tsabta tare da farinciki mai kawa suke yi har izuwa ranar haihuwar Rimsha, a lokacin kuma Maryam ta haifi yaro ɗaya, Adiva ta haifi yarinyarta mace, Aafia ta haifi ƴan biyu dukka mata, Ummin Dr Nawid tuni ta karɓe yaran wai ita zata renesu, Allah sarki tana son yara sosai, ga shi har yanzu Jellynta kuma Jellyn Yah Imran bata haihu ba.
Gida ya kara cika sosai da yara da jikoki, yanzu kowa dakon jiran yaran Lion yake yi.
Tun safe Rimshar take naƙuda har karfe 2 na rana, amma shiru bata haihuwa, da alama ba zata iya haihuwa da kanta ba, hakan yasa Lion ya ce ayi mata aiki a cire babyn kawai, dan hankalinsa ya kai makura wajen tashi, ya shiga damuwa na wuce misali, ya ji ba zai iya jurewa ba, dole kawai ayi mata aiki a cire yaran nan kada matarsa ta mutu.
Dan dole su Dr William suka karɓi maganar Lion ɗin a in da aka shirya tsab aka yi mata aiki, cikin ikon Allah aka ciro mata baby's nata Maza guda uku da mace ɗaya, duk cikin QUADRUPLE ita kaɗai ta haifa masu ɗiya mace, yarinyar tamkar Pinky, ma'ana kamar Lion ɗin, harta kalar idanunta, duk yaran babu wanda ya biyo Rimshar, dukkansu Lion ɗin suka ɗauko, harta kwayar idanuwansu blue eyes ne, sak irin nasa.
Gwaggo baki har kunne, dama burinta kenan, ga shi Lion ya samu ɗiya mace, abin ba'a magana, gwaggo kamar baki ba zai rufu ba, kowa idan ya zo ganin baby's macen yake ɗauka, sun fi son macen sama da sauran mazan, dan sun gaji da rike maza, yanzu sun samu canji, harta su Areef da suka zo ganin yaran macen suka ɗauka, kowa santin macen kawai yake yi, daddyn Rimsha ma macen ya ɗauka da ya zo.
Abin har sai da yasa gwaggo ta ce, kai lafiya kuwa? Kowa idan ya zo sai ya ɗauki macen yana santinta, dole ta rinƙa yi wa yarinyar nan addu'a, idan ba haka ba ai sai a samu matsala. Yarinyar ne ta ɗauko shegen shiga rai irin na mamanta, kowa sonta yake yi, gata jajir irin babanta, kunsan blue eyes kuma da shiga rai da ɗaukar idanu, musamman a wajen kananan yara, sai hakan tasa yarinyar ta kara shiga ran kowa.
Shi kansa Lion ɗin ana ciro yaran bayan an gyarasu macen ya ɗauka, ita ya fara yi wa huɗuba, yau dai bai ce baya son ganin yara ba, wani irin azababben so ma yake yi wa ƴaƴan nasa, sai dai yafi son macen nan, dan wlh ita ce ta fito sak shi sosai tamkar an tsaga kara, ga ɗan bakin nan nata kamar nasa aka cire aka sanya mata, sosai yake jin azababben kaunar yarinyar, hakan yasa da ranar suna ta zago sai ya sanyawa yarinyar sunan gwaggo, hjy gwaggo mulki ta karu......😂
Su kuma mazan ya yi wa daddyn Rimshar takwara, ɗaya kuma Dr William, ɗayan Dr Salman. Wlh baki ya yi kaɗan wajen zayyano maku irin farincikin da waɗan nan familyn suke ciki.
Daga kan waɗan nan QUADRUPLE da Rimsha ta haifa, Lion ya dakatar mata da haihuwa, ta hanyar tsari mai kyau, ya ce yaran sun ishe su, huɗu yake da buƙata, kuma ga shi ya yi sa'a ya samu mace da maza uku, kunga yana da kowani jinsi, dan haka sai ya ce su kam sun gama kenan, sun rufe kofa, shi ma Areef hakan ce, ya ce sun gama kenan, amma shi Aseef ya ce zasu kara ɗaya idan ta huta nan da shekara biyar haka, zasu gwada ko zasu sami mace, shi dai Sir Safwan bai ce komai ba, binsu da idanu kawai yake yi abinsa, dan shi bashi da zaɓi a kan yara.
After some years.
Sanye take da wando three cuter zuwa gwiwa da ƴar vest zuwa cibiyarta, ta kara kyau ta yi ƙiba sosai, tamkar ba ita ta haifo QUADRUPLE ba, ta yi haske komai yana nan cif cif. Hannunta na rike da wasu towels guda huɗu masu matuƙar kyau, launin white color.
Tafiya take yi komai na jikinta yana motsawa, kai tsaye wajen katafaren pool da yake cikin gidan ta nufa, ba White house ba, ainahin Daular Lion ɗin, nan suka zo hutu, wani lokaci Lion ɗin yana ɗaukosu su zo gidan su yi two weeks su ɗan huta ba tare da damuwar kowa ba kafin su koma white house.
A bakin pool ɗin ta tsaya tana faɗin. "Oya come out, kuzo ku je ku ci abinci".
Kyawawan QUADRUPLE nata ne a cikin pool ɗin tare da daddynsu, ya ɗaura takwarar gwaggo wadda suke kira da pretty a saman Lion chest nasa yana tara mata kyakkyawar dark black curly hairnta da yake jike da ruwa. Yaran nan tun suna ƴan wata shidda Lion yake shiga dasu cikin pool, sai ya ɗaura masu robar hana yaro lumewa a wuya, ya jefasu cikin ruwan suna yawo asama ya shiga shima su yi wanka a tare, har ya saba masu, ya koya masu, yanzu kullum suna ninƙaya a ciki abinsu, ita kam Rimsha ko a jikinta.
"Mummy we can't eat anything now, ki bari sai anjuma". Cewar ɗaya daga cikin mazan wanda suke kira da little, dan shi ne karami kuma shi ne takwaran Dr William.
"Noorish Allah kai ne kake koyawa yaran nan duk wani abin da suke yi, zaku fito ne ko sai na shigo na same ku?".
Ɗaya takwaran daddynta ɗin ne ya ce. "Mummy we're soldiers, bamu jin yunwa, daddy ya ce sai muna nuna jarumta zamu zama jarumai irinsa, so we can't eat anything".
Harara ta wurgawa Lion ɗin, ya tsareta da idanun yana kare mata kallo bai ce da ita ko uppan ba, shi wani azababben sha'awarta ma yake ji, ta wani kara kyau, komai yana nan cif cif ɓul ɓul kamar bata taɓa haihuwa ba, ga tula tulan nan nata kamar an hura balo balo, sun sha gyara a wajen gwaggo, duk sai ya ji kai ina yana hannu fa.
Ita kuma haushinsa ma take ji, duk ya bi ya yi wa yara huɗubar banza wai su zama jarumai, duk ya koya masu halayyarsa, harta macen ma wai sai ta tsaya tana wani cewa daddy ya ce zata zama jaruma idan ta yi kaza ko ta yi kaza.
Ganin sai harara take wurga mashi ne yasa ya kashe mata ido ɗaya tare da motsa laɓɓansa a hankali tamkar mai ciwon baki ya ce. "In zo ne ƴan mata?".
A kule ta ce. "Allah Noorish ba zan barka ba, wato kai bama kasan ina jin haushi ba ko?".
Sake kashe mata ido ɗaya ya yi tare da ɗaga mata gera guda.
A kule ta jefa mashi towels da suke hannunta wanda ta ɗauko zata gogewa yaran jiki, ta jefa mashi su a fuska tare da juyawa ta bar wajen tana huci.
Dariya Pretty ta yi har sai da dimple nata irin na mamanta suka lotsa, cikin wani ɗan siririn muryarta na yara mai shegen daɗi kamar na babanta ta ce. "Daddy mum want to be a hero ko?".
Nisawa ya yi kafin ya ce. "She's a hero since before, now let's go and eat food, kunga mum ɗin ku ta ɓata rai, kada ta yi fushi". Ya kai karshen maganar tare da zame towels ɗin daga saman face nasa, sannan ya ɗaga pretty ɗin sama ya fitar da ita daga cikin ruwan.
Da sauri su little suka riga shi fitowa, kamasu ya yi tare da ɗan goge masu jiki, sannan ya ce to su je.
Gaba suka yi ya rufa masu baya bayan ya ɗauki pretty cancak kenan, ita duk in da zai je to tana jikinsa, ɗaukarta yake yi.
A parlourn sama na part ɗin Lion ɗin suka iskon Rimshar, ta fitar masu da kayan da zasu saka. Ta zauna shiru suna hira da Malika, Malikar ta zo tayata murna ne, shi ne take tambayarta ina ta je tsawon shekaru biyar yanzu rabonta da ta leƙota, nan take gaya mata cewa tana nan tana kusa da su, kawai bayyana ne bata yi, amma tana tare da su, shi ne Rimshar ta ce to dan Allah yau kam ta gaya mata a ina ta sansu?.
Yau dai bata ki gaya mata ba, labari ta fara bata na zaman da suka yi a Dubai, da taimakon da daddynta ya yi wa iyayen Malikar a rashin sani, bai san cewa dattijawan da ya taimakawa a kan hanya aljanu bane, shi ne yasa dayawan lokuta ba kyau walaƙanta ɗan adam, musamman ma dattijo, dan baka san waye shi ba, ba kuma kasan a ina zaku sake haɗuwa ba, to su dai iyayen Malika suna yawan zama a suffar mutane ne, basu cika zama a suffar aljanu ba, hakan ya ba daddyn Rimshar nasarar taimaka masu, har gida ya saya masu kyauta, shi duk a tunaninsa bayin Allan ƴan adam talakawa ya taimakawa, dan ya gansu cikin kunci da talauci a gefen titi, a lokacin kuma suna a tare da mummyn Rimshar ne, lokacin Jehan tana karama Rimshar kuma tana ciki ba'a haifeta ba, ita kuma Malikar ta tafi yawonta abinta, to wannan taimako da ya yi masu ne yasa suma suke taimakawa iyalansa babu kakkautawa, dan duk wani aljani na kirki baya manta alkhairi, suna da tuni, sannan suna da rama alkhairi da alkhairi, sai shaiɗanun cikinsu ne basu da kirki sam sam, wannan shi ne a takaice tarihin tarayyar su Malika aljana da su Rimsha, babu wanda yasan da Malikar sai Rimshar, dan a lokacin ita ce a cikin cikin mum, kuma ba tare da Jehan suke tafiyar ba, Jehan tana wajen gwaggo a gida, so Rimshar kawai suka sani a lokacin, shiyasa ita suka fi tallafawa kuma suka bayyanawa ta sansu, fatan kun gane?.
STORY🔥
Kusa da ita Lion ɗin ya zauna ya hau tayata sanya masu kayan tare da shafa masu lotions nasu, gwanin ban sha'awa.
Su Aseef kuwa suna white house tare da yaransu, yanzu Aseef da Akila an rage shagwaɓa, amma ba wani sosai suka rage ba, sai dai kuma fa sun haifo irinsu, dan kuwa a cikin TRIPLETS nasa akwai mai shegen shagwaɓa irin baban nasa, da an taɓa shi kaɗan sai kuka. Dama aka ce gado ba karambani ba.
Bayan sun kammala shirya yaran a tare, sai suka nufi saman table, gwanin ban sha'awa suka ci abinci a tare, sai hira sama sama suke yi har suka kammala, sannan ne Lion ya ce su zo su ne wajen gudun motsa jiki.
Gaba yaran suka yi da gudu suna rige rige, rufa masu baya ya yi suka bar Rimshar tana aikin cin fruits salad da ta haɗa.
Gudu ya fara sanya yaran suna yi, rige rige yasa su su yi, ya ce duk wanda ya riga shi ne hero, kun san wajen motsa jikinsu already, waje ne mai matuƙar girman gaske.
Fara gudun suka yi babu kama hannun yaro, gwanin ban sha'awa, ƴan ɓul ɓul dasu kamanin daddyn nasu, sak kuwa kamar an tsaga kara, da ganinsu ba tambaya kasan cewa ƴaƴansa ne, yana ji da su ne fiye da yanda nake son kansa, ya dai ce daga kansu an rufe kofa a haihuwa, Rimsha ta huta baiwar Allah.
Yana tsaye yana kallonsu cike da kaunarsu har suka je suka juyo, pretty ta riga kowa isowa.
Tsalle ta fara yi tana faɗin. "I am a hero daddy...."
Bata gama rufe baki na boy takwaran Dr Salman ya tsinketa da mari a kumatu. Cikin huci da fushi ya ce. "Baki ji daddy ya ce maza sune a sama da mata ba, so mune hero's ba ke ba!".
Ihu ta sanya tare da dafe kuncinta.
Tsugunnawa a kusa da ita Lion ɗin ya yi yana faɗin. "Sorry my momma, kyale boy ba zamu je Russia da shi ba........".
Katse mashi maganarsa Rimsha dake tsaye a bayansu ta yi da cewa. "Gaya masu zaka yi mata sune a sama da maza ba maza ne hero's ba!!".
Tayi maganar tana murtuƙe fuska, irin Boss ɗin nan..........😂
Miƙewa tsaye ya yi yana faɗin. "No maza sune a sama da mata, kada ki ɓata mun tunanin yara".
Tsalle little ya yi yana faɗin. "Yes daddy mune a sama".
Harara ta wurgawa little ɗin kafin ta ce. "Mata ne a sama da maza, so gara ma ka ji in gaya maka......"
Lion bai bari ta karisa maganar tata ba ya ɗauketa cancak yana faɗin. "Boy little yanzu ku gaya mun wanene a sama? Kunga dai yadda na ɗauki mum ɗin taku kamar baby, to waye yafi wani karfi?".
Da sauri little ya ce. "You dad, kai ne hero a kan mummy".
A kule Rimsha ta buɗe baki zata yi magana, kamar yasan me zata ce ya yi maza ya rufe mata baki tare da nufar cikin gida da ita yana gayawa su Little su je wajen uncle Donal su yi wasa bari ya zo.
Okey suka amsa mashi da shi tare da wucewa wajen sojojin suna neman Donal, ita kuma pretty yarinya mai hakuri mai irin halin Areef, sai ta wuce bedroom nasu mai shegen kyau ta haye saman bed ta kwanta, hannunta na'a saman kumatunta in da boy ya mareta barci ya ɗauketa, baiwar Allah, tana da kyan zuciya tamkar uncle nata Areef, sai dai akwai ta da faɗa idan ka kureta.
Shi kuma Lion bai sauke Rimsha a ko'ina ba sai a saman katafaren bed nasu.
Yana sauketa ta yi saurin yunkurawa zata bar bed ɗin.
A hanzarce ya riƙota yana faɗin. "Haba mana rigimammiyata, yanzu me kuma nayi?".
"Maza sune suka fi mata jarunta ko? To ni raguwace ba zan iya sake ɗaukarka ba". Ta kai karshen maganar tare da sake yin yunkurin sauka daga saman bed ɗin.
Fisgota ya yi ta faɗa saman Lion chest nasa, juyawa da ita ya yi ya mata rumfa da faffaɗar kirjinsa, cikin sanyin murya ya ce. "Am so so sorry my Queen, mata sune a sama to, yanzu dai please a kula dani, tun ɗazun fa nake jin ina hannu, please mana gimbiyata".
Harara ta wurga mashi ba tare da ta ce komai ba, shi kuwa hakan ma ya yi mashi, tuni ya kara matseta a jikinsa ya fara aikin matse mata tula tula, dama a hannu yake.
"Noorish wai yanzu da gaske ba zaka taɓa yi mun murmushi ba a rayuwarmu? Ban fa taɓa ganin murmushinka ba".
"Ba ke kaɗai ba my Meesha, ni babu wanda ya taɓa ganin murmushina, dan bana yi kuma ban iya ba".
Yana magana yana matse mata tula tulan nata kamar zai fasa mata su.
Shigewa jikinsa da kyau da kyau ta yi tare da kai hannunta a saman Heronsa tana faɗin. "Bari na ji".
Wash ya furta da karfi tare da kara matse mata breast ɗin nata tamkar su ne suka taɓa mashi heron nasa, da zafa zafa ya fara kissing nata, tuni ya rabata da kayan jikinta suka hau aikin da suka saba..................... (Da alamun dai zasu samowa su pretty kanne ne😌 Irin wannan zafa haka?)
A can white house kuma, Areef ne sundume tsulundum cikin katafaren pool shi da Jehan, sun manne da juna kamar nace zan rabasu, a cikin pool ɗin ma basu hakura ba, sai sun yi kiss, ga kyawawan QUADRUPLE nasa suna wasa a wajen, suma jikinsu na sanye da kayan wanka, amma basu shiga cikin ruwan ba, suna ta aikin guje guje dai a wajen, kyawawa da su masu kama da daddynsu.