Kenza eBookz
Cover art for FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 4

Post

FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 4

.....take the number and call. After they finished talking, he sent her their address. ***** Zahra stood up and said, "Let me take a bath." He smiled at her. Then she realized that this smile would not fade on his face... I saw her Ibrahim who came out. She lowered her eyes and went to the toilet, hearing the call to prayer. **** After she finished getting ready, the makeup artist gave her bridal makeup. He couldn't shut his mouth because of his happiness. He was holding her hand and she entered the car. He turned around and said, "My star." **** They arrived at a big organization... Northern Elite Business Consortium (NEBC) where the meeting will be held.

Standalone post2,055 words

*FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes

Young talented writers association (YOTA)

Book 1 Chapter 4

Da sauri yake hayewa sama saboda yadda lokaci yake tafiya. Ya nufi bakin ƙofar ɗakinta, a hankali ya murɗa sannan ya shiga.

Ya same duke a ƙasa tana shesheka. Ya ƙarasa wajenta ya duƙa, ya ɗagota jikinsa. Zata kwace kanta, ya riƙe ta gam.

Ya ce, "Haba Zahra, kin san bana son kukan ki fah"

Bata san sanda ta masa wani kallo ba.

Ya ce "Okay toh… ki daina Please"

Tayi shiru, still tana jinkinsa.

Ya shiga share mata hawayen fuskanta ya ce, "Na yi fushi ne saboda kin san zamu fita kuma kin sani kika fita… amma na sani bai kamata na ɗaga murya na haka sosai a kanki ba. I'm sorry."

Lokaci guda Zahra ta manta da wani ɓacin rai.

Yana riƙe da ita, suka zauna a bakin gado. Ya ciro wayansa yana kallonta ya ce "Wata mai makeup ɗin za'a miki booking? Ko kuma kawai tazo nan ta miki?"

Kai ta gyaɗa ta ce "Ka shiga IG."

Nan take ya shiga ya miƙa mata wayan. Ta yi searching wani account sannan ta miƙa masa

Ya ɗauki number ɗin ya kira. Bayan sun gama magana, ya tura mata address ɗinsu.

*****

Zahra ta miƙe ta ce, ''Bari nayi wanka."

Murmushi ya sakar mata.

Sai taji dama wannan murmushi ba zai yi fading a fuskarsa ba… sak Ibrahim ɗinta na da ya fito.

Ta sauke idonta sannan ta wuce toilet, jin an fara kiran sallah.

****

Bayan ta gama shiryawa, mai makeup ta mata bridal makeup

Ba kaɗan ba tayi kyau.

Ita kanta artist ɗin sai da tayi content da ita, musamman da ta gani ashe famous Zahra.xx ce

Zahra kuwa ta zama tamkar sabuwar amarya a wannan lokacin.

Khalil kam ya kasa rufe baki saboda murna. Shi ma ba ƙaramin kyau yayi ba.

Sai ya zama kamar yau ne ake bikin nasu.

****

Yana riƙe da hannunta suka fita zuwa compound.

Ya buɗe mata ƙofar gaban mota ta shiga, sannan ya zagaya ya shiga shima.

Ya juya yana kallonta ya ce, "Tauraruwata…"

Ta hararesa tana murmushi.

Ya ciro wayansa yayi musu hoto, sannan yayi posting da caption

'With my queen tonight My forever peace, my Tauraruwa #PowerCouple #RoyalVibes #MyZahra'

****

Suka isa wani babban organization... Northern Elite Business Consortium (NEBC) inda za'a gudanar da taron.

Ya yi parking.

Ta kai hannu zata buɗe ƙofa, ya ce, "No Gimbiya… ki bari na karasa aikina." Ta sakar masa murmushi.

Haka kawai take jin kanta cikin wani yanayi na farin ciki... kamar komai ya dawo daidai.

Ji tayi dama su dawwama a haka.

Ya sauka, ya zagaya side ɗinta, sannan ya buɗe mata mota.

A take idanu suka dawo kansu. Kowa sai kallo.

Ya kama hannunta ya saukar da ita a hankali, ta sauka.

Ya kai bakinsa gefen kunnanta yayi mata raɗa.

Ta yi dariya ta ce, "Ban so…

Ya ce, "It's okay, na daina Gimbiya"

A haka suka kama hanyar shiga cikin taron

Annual Northern Leadership & Investment Gala wani babban taro na manyan ‘yan kasuwa, shugabanni, da masu tasiri a Arewa.

***

Suna shiga cikin hall ɗin… ido ya dawo kan Zahra.

Kowa sai kallonta yake yi, wasu suna kallon kyawunta. Wasu kuma dama already sun santa a Social Media as Zahra.xx, kuma tun sanda aka aka yi bikin ta, ɗif ta sauke wuta ba'a sake jin motsinta ba a media, wasu suka fara yi wa juna magana a hankali.

Ibrahim kuwa...

zuciyarsa na cike da wani irin daɗi, Yes ita ce tasa.

Ita ce matarsa. Ita ce ke jawo hankalin kowa akansa, kuma yake tafiya viral a wannan watan

Amma... Duk lokacin da ya lura kallon ya yi yawa…

sai ya ɗan matse hannunta kaɗan, alamar kishi.

Suka samu wuri a gaba, inda aka tanadar wa manyan baƙi.

An fara gabatar da taron cikin tsari da nutsuwa.

MC ya hau stage ya fara da gabatarwa

"Ya ku maza da mata, baƙi masu daraja… a madadin Northern Elite Business Consortium, muna maraba da ku zuwa taron shekara-shekara na Northern Leadership & Investment Gala Night"

Akq ci gaba da gabatar da manyan baki, shugabanni, da 'yan kasuwa.

Ana kira suna… ana tafi ana dawowa… ana yin speeches…

Ana cikin tsakiyar taron amma har yanzu ido na kan Zahra.

Ibrahim ya jingina da kujera yana kallonta, yana murmushi.

Amma a zuciyarsa; yana jin wani abu guda biyu a lokaci ɗaya

'alfahari… da kuma kishi'

A tsakiyar taron… ana ta ɗaukar hotuna.

Flash na camera na walƙiya lokaci zuwa lokaci.

Wasu suna turo musu phones suna cewa, "Please, one picture…"

Wasu kuma daga nesa suke capturing ɗin su.

Zahra kuwa sai murmushi take yi natural, ba tare da wani Izzah ba

MC ya ɗan yi shiru kafin ya fara magana

"Yanzu kuma… za mu karrama ɗaya daga cikin manyan ‘yan kasuwa da suka yi fice a harkar sayar da manyan motoci a wannan yanki namu…"

Aka fara tafa hannu.

"Mutum ne da sunansa ya zama abin alfahari da kuma amana a harkar kasuwanci, musamman a fannin motoci masu tsada…"

Zuciyar Ibrahim ta ɗan buga.

"Babu shakka, ya bayar da gudunmawa sosai wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi…"

MC ya ɗan dakata sannan ya ce da ƙarfi:

"Mu marabci… Mr Ibrahim Khalil!"

Tafi ya kaure a hall ɗin, kowa ya juya yana kallonsu

Zahra ta juya ta kalleshi da murmushi

Ya ɗan gyara zama, sannan ya miƙe tsaye, ta miƙe tare da shi.

Yana riƙe da hannunta suka nufi stage

camera suka karkata kansu.

Flash… flash… flash… Kowa na ɗaukar su.

Wasu ma suna tashi tsaye don ganin su sosai

Suka isa stage, aka miƙa masa award.

Ya karɓa da murmushi. Zahra na tsaye a gefensa.. ta zama kamar haske a wajen.

Nan take aka fara musu hotuna.

Professional photographers na gaba

click… click… click… Sannan phones daga audience

recording… snapping…

Wasu tuni suka fara posting a social media:

"Who is she??" "Mr Khalil and his stunning wife" "Power couple spotted tonight"

Ana tagging account ɗinta kai tsaye. Notifications suka fara shiga a jere.

Zahra dai murmushi kawai take yi cikin nutsuwa

Amma a zuciyarta.. tana jin wani irin yanayi.

Bayan sun gama, suka sauka daga stage. Har yanzu ana binsu da camera.

Ibrahim ya riƙe hannunta sosai.. kamar baya son a raba shi da ita.

Suka koma suka zauna.

Ya ɗan matsa kusa da ita ya ce a hankali, "Kin ga yadda kike jawo hankali ko?"

Ta yi murmushi kaɗan bata ce komai ba

Aka ci gaba da taron har aka kai ƙarshe.

MC ya yi closing speech.

Ak yi addu'a.

Sannan aka sanar da ƙarshen taron.

Mutane suka fara fita, ana gaisawa, ana musabaha.

Ibrahim da Zahra suna tafiya tare, hannunsa riƙe da nata gam.

Duk inda suka wuce.. ana tsayawa a gaishe su.

"Congratulations, Mr Khalil" "Beautiful couple." "Masha Allah…"

Wasu suna kallon Zahra da sha'awa.

Wasu kuma suna kallon su da irin kallon da ke nuna hassada.

Ibrahim kuwa duk lokacin da wani ya tsaya kusa da ita sosai sai ya ƙara matso da ita jikinsa sosai.

A haka suka karasa jikin mota, ya buɗe mata motan, ta shiga.

Ya zagaya ya shiga shima, yana kallonta… yana murmushi, itama murmushin take masa, amma a cikin murmushin sa, akwai wani abu, wani abu da ba a fahimta kai tsaye

Ya tada motar daga haka suka bar wajen, wani babban restaurant ya tafi da ita, Zahra ba zata iya misilta farin cikin da take ciki ba, daga ranan aurensu sai wannan ranan a kalan farin cikin da take ji.

Sosai suke nuna wa juna soyayya da kulawa, ciyar da junan su suka yi, ba tare da sun damu wai akwai mutane ba, suna gama wa yana riƙe da ita haka suka fita daga restaurant ɗin suka wuce mota..

"So exhausted suka isa gida. Yayi parking sannan duk suka sauka, tana riƙe da award ɗinsa. Direct ɗakinsa suka wuce.

Ta faɗa kan gado ta ce, "What a stressful day… kasan yadda nake jin gajjiya a jikina kuwa?"

Ya ce, "Sorry, bari nayi wanka, nazo na miki massage."

Ta hararesa ta ce, "Ko ba massage ba…"

Yayi dariya, ya cire kayansa ya wuce toilet.

Wayansa ne ta gani ya kawo haske. Ta miƙe a hankali ta ƙarasa wajen. Ta kalli me kiran ‘dovie’, ta kurawa wayar ido har ya yanke.

Nan ta ga missed calls ɗin har wajen 8.

Tayi shiru tana kallon ƙofar toilet ɗin.

Tunanin kamar har da wayansa yake sa suke samun matsala… amma bata jin yau zata bar wani abu ya shiga tsakaninsu, musamman bayan ranar da ta sha wahala.

Sai kawai ta kashe wayar baki ɗaya, ta koma ta zauna a bakin gadon.

Can sai gashi ya fito.

Ta ƙarasa ta ciro masa rigan bacci a sif, ta kai masa kan gado, ita ma ta wuce toilet.

Da wuri ta fito, dan duk hankalinta yana kansa kar ya ɗauki wayansa.

Ya juya yana kallonta da mamaki, ganin har ta fito.

Ya ce, "Yau ke ce da gama wanka da wuri?"

Murmushi tayi ta ce, "Ai ba datti nayi ba… shiyasa."

Ya gyaɗa kai kawai. Itama ta gama saka kayanta.

Washegari…

Bayan ta gama breakfast tana kokarin fita da kulolin, sai Khalil ya shigo daga masallaci.

Ya tsaya a bakin ƙofar kitchen ɗin.

Ta juyo tana masa murmushi ta ce, "Ina kwana?"

Ya ce, "Lafiya… amma yau lafiya kika daura breakfast da wuri haka?"

Ta ce, "Ohh sorry, ban faɗa maka ba ko? Ai yau zan koma school. Baka ji ba, Abba ma sai da yayi magana.

Ya ce, "Really? Toh Allah bada sa'a"

Ta ce, "Ameen"

Tare suka yi breakfast, suka shirya.

** Suna sauka stairs suna hira da wasa mai ban sha'awa.

A haka suka wuce compound kowa ya nufi wajen motarsa.

As usual, haka ta shiga department ɗinsu, idanun mutane na kanta.

Bayan ta yi parking, sai da ta ɗauki few seconds kafin ta buɗe motar ta sauka.

Kaf department ɗin daga lecturers har students babu wanda motarsa ya kai na Zahra tsada da kyau.

Shiyasa kusan kowa yake mata fadanci. Ita kuma ta tsani hakan. Duk da tarin makiya da take da su

Ta buɗe back seat ta ɗauki jakkanta.

Ta fara tafiya kenan, sai ga class rep a bayanta ya ce, "Ahh, anty Amarya ce!"

Ta juya ta ce, "Class rep, ya gajjiya?"

Ya ce, "Ina kwana, fatan kin dawo lafiya?"

Tana murmushi ta ce, "Kalau, sannu da ƙoƙari" ya ce "Haba ai yiwa kai ne, Allah dai kawai ya kara rufa asiri" ta ce

"Ameen, naga an bada wani presentation topics na seminar"

Yayi murmushi ya ce "Ai tuni na gama miki Hajiya, kawai ban faɗa miki bane, amma ai kema kin san kinfi karfin haka" dariya tayi ta ce

"Toh Nagode kwarai"

Tana cikin tafiya, sai ga Asiya.

"Zahraaa!" ta kira da ƙarfi

Zahra ta juya tana murmushi ta ce "Kash Asiya ba zaki taɓa canzawa ba… kalli yadda kike ihu a mainan nasu"

Asiya ta ce, "Kyale ni nikam!, ashe zaki zo shine ko magana babu?"

Zahra ta ce "Abbah ne ma yayi magana, kuma dama yana raina, Shiyasa nace bari kawai na fara fito wa tunda shima ya koma aiki"

Ta karɓi jakar Zahra ta rataya.

Suka nufi lecture hall ɗinsu suna ɗan hira

Asiya ta ce, "Kee, jiya dai kun daga hankalin mutane a media. Kinga uban kyau da kuka yi, Ma Shaa Allah!"

Sai kuma ta ɗan dakata.

"Amma kuma ke ban ga kin yi posting ba. Ga Ya Khalil sai uban posting ɗinku yake yi da romantic caption"

Zahra ta ce, "Please Asiya, it's early ace mutum har ya fara uban surutu haka"

Asiya ta taɓe baki ta ce, "Ashe dai baki canza ba… chap toh Allah yasa Khalil ɗin ma irin ki ne, idan ba haka ba kun dinga samun matsala"

Zahra dai bata kuma kulata ba har suka isa cikin hall ɗin, haka colleagues ɗinta suka dinga zuwa suna gaishe ta, saboda uban souvenirs data bayar a kawo musu bayan bikin

Ga mamakinsu sai ga Saudat ta shigo, ko da wasa bata yarda tayi inda suke zaune ba, wani raw ma daban ta nufa, Zahra ta kalli Asiya ta ce

"Nikam Ko dai laifi nawa Saturday ne?"

Asiya ta ce "Kema da ɗaukan damuwa, dan Allah ki share ta, ko ba komai kin ɗaga Saudat har ta zama mutun"

#Farashin Izzah #Jiddatulkhayr writes #08110615256