
Post
FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 29
"Destiny has come and you have to accept it and continue living as you used to." Zahra smiled. She didn't have the strength to speak. At the moment, one of their workers brought in a bowl of fruit and placed it on the side table. Mami looked at her. "Don of God, let's fix Zahra's room, since she is now back home." Yana tsaye ne a bakin parlorn, bai jima ba Ibrahim ya fito Suka gaisa. Sai dattijon ya gyara tsayuwarsa "Kai ne Ibrahim?" "Eh." Ibrahim ya amsa Dattijon ya gyada kai. "Nine uban Saudat ne." Nan take Ibrahim ya ɗago kai. Dattijon ya ci gaba. "Na zo ne dan na shaida maka." Ibrahim ya yi shiru. "Ina neman magabatan ka dan zan aura maka Saudat" Fuskar Ibrahim ta canza ya koma na mamaki Dattijon ya ɗora "Ka gama cutarta, yanzu babu who will be interested in marrying her, so the way you start is the way you will end. I want to see you marry her." Ibrahim lowered his head, before he had a chance to speak. Then they heard footsteps. It was Mama who came out. From the door of the parlor she heard the end of the conversation. "Oh Sir." She said.....
*FARASHIN IZZAH*
Book 1 Chapter 29
Fitar Abbah da Ya Umar ke da wuya daga parlorn, Mami ta miƙe tsaye.
Tun kafin Mummy ta yi wata magana, ta gyara mayafinta.
"Zan haura sama." Ta faɗa a taƙaice
Mummy ta haɗe gira "Ni kam meke faruwa ne?" Ta tambaya cikin son jin abin da ke gudana
Mami ko kallonta bata yi ba.
"Babu komai" Kawai ta faɗa, daga haka ta juya ta nufi staircase.
Zahra ma ta miƙe a hankali
"Bari na sha maganina." Ta faɗa, sannan ta bi bayan Mami
Batoul ta kalli Mummy, Mummy ma ta kalleta sai dukansu suka yi dariya
"Wallahi akwai wani abu Mummy" Batoul ta faɗa
Mummy ta gyada kai "Ni ma haka na gani, amma idan tayi tsami zamu ji"
Da suka shiga ɗakin Mami. Mami ta zauna a gefen gado sannan ta kalli Zahra
"Zo nan."
Zahra ta ƙarasa kusa da ita. Mami ta kama hannunta
"Ki kwanta Zahra." Ta faɗa cikin taushi.
"Amma dan Allah ki cire duk wani damuwa daga ranki."
Zahra ta yi shiru tana kallonta.
Mami ta ci gaba. "Kar ki sa wa kanki hawan jini. Abin da ya faru ya riga ya faru, haka taki kaddarar ta zo sai ki karɓa ki ci gaba da rayuwa kamar yadda kika saba"
Murmushi Zahra ta yi Ba ta da ƙarfin magana sosai a halin yanzu
ɗaya daga cikin masu aikinsu ta shigo da bowl ɗin fruits, ta ajiye a kan side table
Mami ta kalleta "Dan Allah ku haɗu ku gyara ɗakin Zahra, tunda yanzu ta dawo gida"
"Toh Hajiya." Ta amsa, daga haka ta fita
Wani dattijo mai shekaru ne ya zo gidansu Ibrahim, baƙin cikinsa a bayyane yake
Mai gadi ya shigar da shi ciki bayan ya bayyana dalilinsa na zuwa
Yana tsaye ne a bakin parlorn, bai jima ba Ibrahim ya fito
Suka gaisa.
Sai dattijon ya gyara tsayuwarsa
"Kai ne Ibrahim?"
"Eh." Ibrahim ya amsa
Dattijon ya gyada kai. "Nine uban Saudat ne."
Nan take Ibrahim ya ɗago kai.
Dattijon ya ci gaba. "Na zo ne dan na shaida maka."
Ibrahim ya yi shiru. "Ina neman magabatan ka dan zan aura maka Saudat"
Fuskar Ibrahim ta canza ya koma na mamaki
Dattijon ya ɗora "Ka gama cutarta, yanzu babu wanda zai yi sha'awar aurenta don haka yadda kuka fara haka zaku karasa, manyan ka nake son gani dan aura maka ita"
Ibrahim ya sauke kansa ƙasa, kafin ya samu damar magana
Sai suka ji takun sawu, Mama ce ta fito, tun daga ƙofar parlorn ta ji ƙarshen maganar.
"Ai Malam." Ta faɗa tana ƙaraso wa
"Yana da mata, sannan bai daɗe da yin aure ba, taya zai auri wata yanzu?"
Dattijon ya juya ya kalleta.
"Ko mata uku yake da su." Ya faɗa cikin fushi
"Ko jiya ya aure su, sai ya aureta."
Mama ta haɗe hannu tana masa wani kallo ta ce "A bisa wani dalili?"
Dattijon ya kalleta "A dalilin abin da ya bata min ɗiyata."
Mama ta yi wata dariya mai cike da raini "Toh dama yarinya naka tana da tarbiya ne?"
Nan take fuskar dattijon ta canza
"Ke ki iya bakin ki" Ya faɗa da ƙarfi yana nuna ta da yatsa
Mama ta matso gaba "An ƙi har talaka da kai zaka zo kana mana ihu a gida?"
Dattijon ya kalleta sosai, sai ya gyada kai
"Haka kika ce ko?"
Mama ta ɗaga kafaɗa.
Dattijon yayi wani murmushi yace
"Ki jira" Ya faɗa cikin sanyin murya
"Za ki gani."
Daga haka ya juya ya fice.
Ibrahim ya daɗe tsaye a wajen kansa a sunkuye, ba shi da ƙarfin wata magana.
Daga ƙarshe kai tsaye BQ ya nufa.
Ba ya son jin wata magana daga kowa a wannan lokacin...
Abbah da Ya Umar suna fitowa daga wani chamber Barristers uku ne suka rakosu har bakin mota.
Suna godiya saboda ba kadan ba abbah ya jikasu da kudi
"Mun gode sosai sir" Ɗaya daga cikinsu ya faɗa
"Ai irin wannan case din muke so Sir, ya bashi da bakin magana daga shi har Wanda zasu tsaya masa"
Abbah ya yi murmushi "Ku tabbatar kun yi aikinku yadda ya kamata."
"In sha Allah sir." Suka amsa gaba ɗaya.
Abbah ya gyara agogon hannunsa.
Sannan ya ce, "Make sure ku kai masa yau."
Dukkansu suka gyada kai. "Ai dole ne sir, yau ɗin nan za a kai."
Abbah ya gyada kai cikin gamsuwa, daga haka suka yi sallama
Ya Umar ya shiga seat ɗin direba. Abbah ya shiga dayan site din, daga haka suka bar wajen
Firdausi ce ke sallama a bakin parlorn. Da alama yanzu ta iso.
Farida ta leƙo daga kitchen "Laaa Anty Firdausi!" Ta faɗa cikin fara'a.
"Shigo mana."
Firdausi ta yi dariya, sannan ta shiga
Bayan sun gaisa, Firdausi ta tambaya
"Ina Zahra?"
Farida ta nuna sama "Tana bangaren Mami."
Firdausi ta gyada kai. "Toh."
Daga haka ta juya ta nufi staircase Kai tsaye zuwa bangaren Mami.
Domin tun da ta ji an sallamo Zahra daga asibiti, zuciyarta ta kasa haƙuri har sai ta gan ta da idanunta
A parlorn Mami suka fara haɗuwa. Mami na zaune tana duba wasu takardu lokacin da Firdausi ta shigo
Da sauri ta durƙusa ta gaishe ta Mami ta amsa cikin fara'a.
"Firdausi, sannu da zuwa."
"Yauwa Mami." Ta amsa.
Mami ta nuna mata ƙofar ɗakin "Ki shiga ciki, tana can."
Firdausi ta gyada kai.
"Toh Mami."
Daga haka ta miƙe ta nufi ɗakin.
A hankali ta tura ƙofar.
Zahra na kwance kan gado tana duba wayarta. Da ta ji an shigo ta ɗago kai, Idanunsu suna haɗuwa Zahra ta dan bata rai
Nan take Firdausi ta lura akwai wani yanayi a fuskar Zahra, ba irin fara'ar da ta saba yi mata ba
Duk da haka ta ƙarasa cikin murmushi, ta rungume ta a hankali.
"Sorry my friend" Ta faɗa.
"Ya jikin naki?"
Zahra ta rungumeta back amma babu walwala.
"Da sauƙi" Ta faɗa a taƙaice. Sai kuma ta ɗan ja baya ta zauna, Idanunta na kan Firdausi
"Firdausi... "Ta kira.
"Na'am?" Firdausi ta amsa
Zahra ta yi shiru na ɗan lokaci kafin tace
"Meya sa za ki yi posting hotunan Ibrahim da Saudat?"
Firdausi ta haɗe gira "Ban gane ba."
Ta faɗa "Wane hoto kike nufi?"
Zahra ta ce, "Wanda yake trending mana"
Firdausi ta zuba mata ido.
Zahra ta ci gaba.
"No matter what, Saudat is still our friend. Why would you want to ruin her life that way?"
Firdausi ta zaro ido, sai kuma ta miƙe tsaye, ranta ya fara ɓaci
"Enough, Zahra." Ta faɗa.
"Nima ban san abin da kike magana a kai ba."
Ta nuna kanta. "Akan me yasa za ki dinga zargina haka?"
Sai ta girgiza kai cikin takaici. "Can't you see what she did to you? Kin manta wa Saudat take?"
Ta matsa kusa da gadon.
"Kin manta a department tana ta nuna miki yanzu tafi karfin ki, you're nothing?"
"Kin manta lokacin da take cewa, 'gida yayi kyau saura kwanciyar hankali' wasu Asiya da suka zo?"
Ta ɗaga hannayenta "How did she know baki cikin kwanciyar hankali?"
Zahra ta yi shiru.
Firdausi ta ci gaba.
"Saudat is a devil. Kuma har yanzu kina iya kareta?"
Ta yi wata dariya mai ciwo.
"It's okay! Choose Saudat over me, Zahra, ba yau kika fara ba"
Zahra kallonta kawai take yi
Firdausi kuwa zuciyarta ta cika da bacin rai
"A kan Saudat kin taɓa marin ni, Kin tuna? Amma duk da haka ina tare da ke saboda Allah kuma saboda son da nake miki."
Sai ta nuna Zahra da yatsa.
"Remember, ke kika ɗauki responsibilities ɗinta.m, ke kika taimaka mata, ke kika tsaya mata har ta zama mutum but what?! Yanzu kuma ta zama kishiyarki na waje"
Ta girgiza kai.
"Abin da ta shuka ne take girba zahra, she's reaping what she sowed"
Jikin Zahra ya yi sanyi, ta sunkuyar da kai, sai bayan wani lokaci ta ce a hankali,
"No matter what, Firdausi... ita ma mace ce ki tuna.. Na ji babu daɗi ne kawai. Saboda idan ni ce, ba zan so a fito da abin da nake yi a media ba."
Sai ta ɗago kai "But please, Firdausi... Ba ke ce kika fitar da su ba?"
Firdausi ta zaro ido. "How?" Ta faɗa.
"Bayan wayarki tana wajenki?" Sai ta girgiza kai.
"Kuma ai da saninsu suka ɗauki hotunan, ba kunya, ba tsoron Allah kuma har murmushi take abun ta, Toh idan sun fito duniya, ni ban ga laifin wanda ya fitar da su ba"
Zahra ta yi shiru maganar gaskiya har yanzu bata gama yarda da Firdausi ba. Amma kuma babu wata hujja da take da ita.
Suna cikin haka ne Farida ta shigo riƙe da tray mai ruwa da snacks, ta ajiye a gabansu.
"Ga ruwa." Ta faɗa cikin murmushi.
Daga haka ta fita.
Firdausi ta zauna ta ɗauki lemu, sai kuma ta canza zance.
"Wallahi lectures sun yi wuta yanzu."
Zahra ta ɗago kai.
Firdausi ta ci gaba da bata labarin yadda wani lecturer ya shiga ya ba su assignment kamar ba gobe, yadda ɗalibai suka fara gunaguni, tadda Asiya ta yi wata magana da ta sa gaba ɗayan class suka yi dariya.
A hankali a hankali zahra ta janyo Zhara da labari Wanda har ta sake.
A haka suka ci gaba da hira har Firdausi ta miƙe zata tafi.
"Toh bari na wuce kafin Mama ta fara nema na" Ta faɗa tana ɗaukar jakarta.
Zahra ta gyada kai.
"Okay." Sai kuma ta miƙe tana rakata.
Har bakin gate ta rakata.
Firdausi ta juya tana kallonta.
"Please ki daina tunani da yawa."
Zahra ta yi murmushi "In sha Allah."
Firdausi ta gyada kai sannan ta fice.
Zahra kuwa ta juya ta koma cikin gida.
Firdausi na fita daga gate ɗin kuwa ta hango motar Ya Umar tana shigowa layin, murmushi ya suɓuce mata, ta tsaya tana jiransa.
Da motar ta ƙaraso ya sauke glass dan ganinta da yayi, ta gaishe shi.
Ya amsa cikin fara'a.
Sai ya kalleta "Ina zaki?"
"Gida." Ta amsa.
Ya nuna mata seat ɗin gaba. "Shigo na kai ki."
Ba musu ta buɗe motar ta shiga Da farko dukansu suka yi shiru
Sai karar AC kaɗai ke tashi a cikin motar Can bayan sun ɗan yi nisa Ya Umar ya kalleta.
"Kin ga abin da ke faruwa a media kuwa?"
Murmushi ya bayyana a fuskar Firdausi. "Ai hakan ya fi, maganinsu kenan."
Ya Umar ya ɗan kalleta.
"I wonder ya akayi secret ɗinsu ya fito fili."
Ya ɗan yi murmushi "Da yake Zahra ba ta da hakkin su"
Firdausi ta ɗan gyara zamanta.
Sannan tace, "Ni na tura wa bloggers su yi posting."
Ya Umar ya juya ya kalleta da sauri.
Ita kuma ta ɗaga kafaɗa. "Saboda yadda zuciyata take kuna a lokacin ne"
Ta ci gaba. "Abin da Saudat ta yi wa Zahra ya yi muni, idan aka barta haka ta ci banza kenan, shi yasa na yi Wallahi zuciyata ma ta yi sanyi."
Ta ɗan yi shiru kafin ta ƙara da cewa,
"At least ba Zahra kaɗai bace zata shiga silent depression."
Ya Umar ya kasa hana murmushi bayyana a fuskarsa.
"Good job, Firdausi."
Nan take ta juya tana kallonsa. "Please kar ka gaya wa Zahra komai."
Ya ɗaga gira. "Why?"
Firdausi ta yi ajiyar zuciya. "Saboda dazu ma har fada ta fara dani wai ni na fitar da pictures ɗin."
Ta girgiza kai. "Na nuna mata I know nothing, kasan Zahra da pure and innocent mind gareta, shiyasa na gwada mata ba ni ba ce, dan idan ta san ni ce, zamu iya samun matsala."
Ya Umar ya gyada kai cikin fahimta. "Okay."
Firdausi ta sake kallon window. Sannan ta ce a hankali,
"Ranar da Zahra ta ga hotunan nan..."
Ta haɗiye wani abu da ya tsaya mata a maƙoshi.
"Allah na ji tsoro sosai, yadda take kuka, yadda ta koma, yadda gaba ɗaya ta canza."
Ta girgiza kai "Shi yasa na yi abin da na yi. Nima cikin baƙin rai ne"
Ya Umar ya ɗan yi shiru. Sai daga baya yace,
"It's okay. Hakan zai zama lesson a garesu, da kuma masu irin halinsu."
Firdausi ta gyada kai.
Daga nan babu wanda ya sake magana. Kowannensu na tunanin abubuwan da suka faru cikin kwanakin nan.
Har suka isa ƙofar gidansu.
Ya Umar ya tsaya.
Firdausi ta buɗe ƙofa
Ta juya tana murmushi
"Thank you for the ride."
"Anytime." Ya Umar ya amsa.
Ta sauka.
Sai da ya tabbatar ta shiga gida lafiya kafin ya ja motar ya tafi.
Yammacin ranar... Ibrahim yana zaune a parlorn, wayarsa a hannunsa amma ko abin da yake dubawa baya gani sosai
Tun bayan abubuwan da suka faru, rayuwarsa ta rikice fiye da yadda yake son ya yarda.
Mama ce ke zaune a gefe tana kallon wani programme a TV.
Sai aka ji ƙarar horn daga waje, ba wanda ya kula da farko.
Bayan wasu mintuna kaɗan kuwa mai gadi ya shigo parlorn.
"Yallabai, wasu mutane ne a waje suna neman ka."
Ibrahim ya ɗago kai "Su waye?"
"Ban sansu ba amma sunsa kaya kamar masu aikin banki"
Nan take Mama ta juya. "Polisawa ne?"
"Aa hajiya su ai na San su"
Ibrahim ya miƙe tsaye. "Toh bari na gani."
Ya fita zuwa harabar gidan Mutane biyu ne tsaye a wajen.
Da ya ƙarasa suka gaisa.
Daya daga cikinsu ya miƙa masa wasu envelope
"Mr. Ibrahim..."
Ya kira sunansa cikin hukuma. "An aiko mu, mu kawo maka wannan."
Ibrahim ya karɓa. Da ya ga tambarin kotu a saman takardar, zuciyarsa ta yi wani irin bugawa.
Ya buɗe. Ya fara karantawa.
Kuma yayin da idanunsa ke bin layukan rubutun... Fuskarsa ta fara sauyawa, a hankali, a hankali Har ta koma tamkar wadda aka cire wa lakka
Mama da ke tsaye daga nesa ta fara jin gabanta na faɗuwa.
Da mutanen suka tafi ne ta ƙaraso da sauri.
"Meye ne?" Ta tambaya.
Ibrahim bai amsa ba.
Kawai ya miƙa mata takardar.
Ta karɓa, ta fara karantawa.
Da ta gama...
"What??!" Ta faɗa da ƙarfi.
Idanunta ta zaro "Saki?!"
Ta ɗago tana kallon Ibrahim. "Wai Zahra ce ta kai ka kotu?"
Ibrahim ya juya gefe, bai ce komai ba.
Mama ta sake kallon takardar.
A wannan karon ta fahimci lamarin ba wasa ba ne, tunda had suna shirking daukar mataki
Ta matso kusa da Ibrahim.
"Karka kuskura ka yarda." Ta faɗa cikin tsanani bacin rai
Ibrahim ya ɗago kai.
Mama ta ci gaba. "Ka ce kana son matarka, karka yarda a raba ka da ita, ko nawa za a kashe, zamu biya, ko me za a yi, zamu yi"
Ta nuna takardar "Amma karka yarda."
Ibrahim ya yi shiru.
Mama ta ci gaba da magana cikin fushi.
"Mace idan ta huce zata dawo, yanzu zugan mutane ne, amma idan ka yarda yanzu, komai ya ƙare mana"
Ibrahim ya sauke idanunsa kan takardar da ke hannunta.
Wani irin nauyin ne ya sauka kirjinsa, da ko Mama na ta magana... Bai san me take fadi ba
Book 1 ya kusa karewa, just few pages left Zaku iya fara making payment dinku ta wannan acc no din , 500 ne kacal 7084571222, Hauwa Jibrin, OPay. Evidence of payment ta 08110615256, Nagode