
Post
SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 1
.....r will tear, pull and stop. He weakly looked at the boy and said, "Be patient, since I have taken you to the road, men, hurry up and leave this town, don't let the morning catch up with you, just listen to what they say with your ears. If God decides that we will meet in the future, we will meet again. He grabbed the boy's clothes, then put his hand in his pocket, took out money and handed it to him. Since he started talking, the boy was following his eyes and looking through the light of the lightning. His body calmly said, "Go to Samale, don't let them find you." Without uttering a word, the boy turned and started walking. "I will come back, I will definitely come back, tomorrow, the day after tomorrow, or privilege? I don't know, but I know I'll be back." He said while swallowing a pain in his throat. *** The city was quiet, nothing was going on, except for the sound of security vehicles, the streets were empty as a result of the curfew imposed, because...
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
P1
15 ga watan Ogusta, hadari ya yi ganganko a sararin samaniya, babu abin da ake iya gani face hasken walƙiyyar da hadarin yake ta yi babu ƙaƙƙautawa. Haka zalika babu abin da kunnuwa ke iya ji, banda sautin rugugin cidar hadarin nan. Riƙe yake da hannun matashin yaron da hannu ɗaya, hannunsa ɗaya kuma riƙe da kaya, su na ta sauri, suna ratsa tsakanin zangarniyar hatsi, da ta yi tsawo, kasancewar tsakiyar damuna ne, amfanin gona ya fito ya yi kyau. Da kyar yaron yake cira ƙafafuwansa, duk da saurin da mutumin da ya riƙa masa hannu yake yi. Zuciyarsa ɗauke da wani nauyi da yake barazana ga numfashinsa, haka yake bin mutumin, yana jin kansa tamkar ba shi ba. Sannu a hankali yayyafi ya fara sauka kaɗan-kaɗan, a daidai lokacin da walƙiyya ta haska wata ragargajajjiyar hanya mai tarin kwazazzabai da da ramuka suka fito. Mutumin ya kalli yaron, zuciyarsa na wani irin raɗaɗi, tamkar mai ci da wuta, raɗaɗin da yake tasowa daga zuciyarsa har maƙogwaronsa yake ji, tamkar zai tsage,ya ja ya tsaya. A raunane ya dubi yaron ya ce "Ka yi haƙuri, tun da na fito da kai hanya, maza ka yi sauri ka bar garin nan, kar ka bari gari ya waye su cim maka, ka dai ji abin da suka faɗa da kunnenka. Idan Allah ya ƙaddara saduwarmu a gaba, sai mu sake haɗuwa. Ya damƙawa yaron ƙullin kayansa, sannan ya zura hannunsa a cikin aljihunsa, ya ciro kuɗi ya damƙa masa. "Ga wannan, maza ka ci gaba da tafiya, idan ka samu guri ka laɓe kar ruwa ya dake ka" Tun da ya fara maganar, yaron yake bin idanunsa da kallo ta cikin hasken walƙiyar da ake yi. Jikinsa a sanyaye ya ce "Ka tafi sumale, kar su same ka" Ba tare da ya furta uffan ba, yaron ya juya ya fara takawa, bai fi taku biyar ya yi ba, ya tsaya ya waiwaya, ya ga mutumin ya kama hanyar komawa cikin ƙauyen. Ya tsaya ya zuba masa ido, a dai-dai lokacin da ruwa mai ƙarfin gaske ya ɓalle, ya fara zuba a jikinsa. "Zan dawo, tabbas zan dawo, gobe, jibi, ko kuma gata? Ban sani ba, amma dai na san zan dawo" Ya furta yana haɗiye wani raɗaɗi da yake yi masa ɗaci a maƙogwaronsa.
***
Gari ya yi tsit, babu abin da ke tashi, sai sautin kai komon ababen hawan jami'an tsaro, tituna babu kowa sakamakon dokar ta ɓaci da aka sanya, saboda gudun tashin tarzoma a daidai lokacin da ake shirin sanar da sakamakon ƙarshe na zaɓen shugaban ƙasa. Galibi mutane na cikin gida, da radio wasu da waya wasu talabijin, wasu da na'urar buga lissafa, su na lissafin yawan ƙuri'un da wanda suke so suka samu, su na dakon faɗin sakamakon, daga hukumar zaɓe mai zaman kanta.
** Dattijo ne ɗan shekaru sittin da takwas, wanda hutu da jin daɗi ya ɓoye tsufan nasa, ya koma tamkar ɗan shekaru hamsin. Yana tsaye ya zubawa hotuna uku da suke jikin katafaren ɗakin ido. Hoton shugaban ƙasa, da gwamna sai kuma sarkin garin. Bayansa kuma wasu manyan dattijan ne sa'aninsa, a zazzaune sun yi shiru, su na dakon abin da zai ce. Ya juyo a hankali, ya ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya, ya ɗan yi gyaran murya sannan ya ce "Haƙiƙa ya ƙetare iyakokin da muka gindaya masa, ba tare da duba mu muka ɗora shi a kan mulki ba. Motar kawai muka ba shi, amma sitiyari yana hannunmu. Dan haka zamu murza sitiyarin da fasinjojin zuwa inda muke so. Idan ya so a mutu har liman in dai lissafin siyasarmu ya fita shikenan"
"Wannan gaskiya ne" suka amsa cikin girmamawa.
"Za mu ƙirƙiri abin da zai hana shi mulkin nan cikin kwanciyar hankali, zamu ɗora daga inda muka tsaya a wancan karon, zamu haɗe koko giya, zamu saka masa pressure da hankalinsa zai koma kan kawo daidaito, a dai-dai lokacin da zamu saka a matsa masa lamba"
Ɗaya daga cikin mutanen ya ce "Amma ta yaya kenan ranka ya daɗe?"
Mutumin ya ƙara murtuke fuska ya ce "Amfani da tsaro mu sanya tsoro!!!"
***
MAFARI...
Masu iya magana na cewa tushiya masomar dawa, kuma duk wanda ya bar gida gida ya bar shi. Kowace halitta na alfahari da tushiyar da ta samar da ita, sai da tamu tushiyar, ta ginu a kan wata mummunar aƙida da muka buɗi ido, muka ga iyaye da kakaninmu a kanta, ba tare da sanin yadda aka yi ta fara ba, sai jin wai wai a cikin labarai da su kan bamu. Har gaban abada majigin abin da ya faru, ba zai taɓa barin allon zuciyata ba, hakazalika zuciya ba zata gushe ba, tana raɗaɗi da sanya idanu zubar hawaye, a sanadiyar gadon bashin gabar da iyaye da kakaninmu zuwa kanmu, babu abin da muke yi bayan lissafa asararta.
Ƙauyenmu na can wani yanki a can cikin ƙauyukan wata jiha a arewacin ƙasarmu. Inda ƙabilu uku zuwa huɗu ne muke rayuwa a guri ɗaya. Kowane ƙabila a cikinmu, akwai nau'in sana'ar da suka ƙware a kai. Sai dai wannan zama da muke guri ɗaya, bai zame mana Alkhairi ba, domin ƙabila ɗaya daga cikin ƙabilu uku, sun fi mu yawa, da ƙarfi dan haka sun mayar da mu tamkar bayinsu. Sauran ƙabilun nan ta ƙarfin tsiya suka bar tsakiyar garin Yelwa, su ka bar garin baki ɗaya, zuwa nesa kaɗan su ka kafa nasu garuruwan, aka bar ƙabilu biyu a cikin garin.
Bari na gajarce muku dogon labari zuwa gajere, domin hana shi gundurarku, labarin da nake son baku, ya fara ne daga wani lokaci.
Damuna uwar albarka, in ji masu iya magana, kasancewar ta lokaci da al'umma ke amfana da tarin alkhairan da take tattare da ita. Yanayin garin ya canza da sassanyar iska mai samar da nutsuwa. Korayen bishiyu masu kyawun kallo ga idaniya, kuma abinci ga dabbobin tudu da na Daji. Tumbatsar tekuna, da samun wadataccen ruwa, ga mutane da dabbobi, ga uwa uba na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar, wato noma da ake a wannan yanayi, domin samar da abinci. Zukatan makiyaya tare da manoma, yana cika da farin ciki, a dai-dai lokacin da damuna ta kankama.
Cak na tsaya na ɗaga kaina, ina kallon yadda garin ya yi duhu, hadari yake ta rugugi, wanda idan har ya zubar da ruwa, zai zama ruwan farko da ya zuba a wannan damunar. Duk da son yanayin na damuna da nake yi, ƙasan zuciyata a cike yake da zullumi da tashin hankali. Domin daga lokacin da damunar ta kankama ya kan zama tamkar zagoyawar jijjiga tsohuwar gaba, da mummunan tashin hankalin da yake tsakanin ragowar ƙabilu biyun da ke rayuwa a ƙauyen Yelwa. Adadin yadda garin yake ƙara duhu, haka tashin hankali da mummunar fargaba, ke ƙara mamaye lungu da saƙo na zuciyata. Ina kallon yadda mahaifina ke kaiwa yana komowa a tskar gida, yana magana da Innarmu, sai dai a muryarsa nake iya karanto damuwa da rashin nutsuwa.
"Kai abin nan da mamaki fa, ina Iro ya shiga a wannan tsohon daren, ga gari na damina fisabilillahi, ai ko yawon zai je, ya bar wa gobe. Kwata-kwata yaushe ya dawo ma, da zai yi nisa haka? Ke Mairo, ba ni tagiyata na zagaya ko Allah zai sanya na gan shi" Ya yi maganar cikin damuwa. Innarmu ta amsa masa da to, ta ba shi hularsa ya karɓa ya fita. Ban san dalili ba, na ji jikina ya yi sanyi, na ji tamkar ƙafafuwana ba za su iya ɗauka na ba. Haka nan zuciyata ta din ga bugawa, da wata irin matsananciyar fargaba da ban san ta mece ce ba.
Daki-daki nake tuna abin da ya faru. Kwanaki biyu kenan, da dawowar Iro daga kiwo da ya tafi, ya shafe watanni huɗu, ba ya garin da dabbobinmu.
Na dawo daga rafi, ina tafe ina ta karanta wasiƙar Jaki a zuciyata, da tunanin ta inda zan samu nasarar abin da nake kwana nake tashi da shi a cikin zuciyata. A dai-dai lokacin na hangi kyakyawan murmushi a kan kyakyawar fuskarsa. Ban yi ƙasa a gwiwa ba, na mayar masa da martanin murmushin na ce " Wannan kwalliyar da ka sha haka? Ina aka nufa?"
Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Kin aike ni ne?"
Na girgiza na ce "Ai gani na yi bamu gama ganin ka ba, amma har za ka fita. Ko zance za ka je?" Na ƙarasa maganar ina yin ƙasa da muryata.
Daƙuwa ya yi mini ya ce "Wuce ki shiga gida, idan na dawo akwai tarin labaran da zan baki. Kuma ki kula da karsanar nan dan Allah, alamu sun nuna, ta kusa haihuwa"
Na jinjina kai na ce "Sai ka dawo. Ina jiran ka zo ka bani labarin, dan ka san duk inda labari yake ina gurin, kuma bana raina saurarensa, komai ƙanƙantarsa. Dan akwai darasi a cikin kowane labari.
Tun daga wannan fitar, har wannan lokacin, kusan ƙarfe sha ɗaya da rabi na dare, bai dawo ba.
Sallamar Baffa ta katse mini tunanin da nake yi, sai dai gabana ya yanke ya faɗi, ganin Baffa shikaɗai ba tare da Iro ba.
Tun kafin Baffa ya furta komai, bugun zuciyata ya ƙaru, abin da ya furta kuwa ya kusa katse mini numfashi.
"Na je duk inda nake tunanin zan gan shi, ban same shi ba"
Inna ta ɗora hannu a ka ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ina yaron nan ya shiga haka? Iro bai taɓa irin wannan ba"
Ni dai tamkar an shuka ni, domin gani nake su da suka haife shi ma, ba su kai ni tashin hankali da fargaba ba.
A hankali kunnuwana su ka fara jiyo mini hayaniya sama-sama, na kalli su Baffa ko sun ji, amma na ga babu alamar suna jin hayaniyar.
Sai daga Baya Baffa ya ɗan yi shiru ya ce "Kamar hayaniya nake ji fa"
Da sauri na ce "Nima haka"
Jin hayaniyar na ƙara kusantowa, ya sanya Baffa yin waje da sauri, ba mu jira komai ba daga ni har Inna, mu ka rufa masa baya, hannunmu ɗauke da cocilan.
Dandazon mutane mu ka gani, ɗauke da cocilan a hannayensu, da sanduna su na ta hayaniya.
Kafin mu ƙarasa tuni Baffa, ya ƙarasa ya kutsa cikin dandazon mutanen.
Tsananin azalzalar son sanin abin da yake faruwa ya ingiza ni, na taka da gudu, ba tare da tunanin komai ba, nima na kutsa domin ganin abin da yake faruwa.
Sai dai kafin idanuna su gane mini komai, sautin salatin Baffa ya karaɗe kunnuwana, fiye da hayaniyar mutanen, wanda ya yi daidai da ganin Ironmu a kwance, cikin jini jikinsa futu-futu da taɓo, sai zubar da jini yake yi.
Durƙusawa na yi jikina na karkarwa, tamkar ana kaɗa mini mazari.
Baffaa ya rirriƙe Iro, ya fashe da kuka yana tambayar "Me ya yi muku? Me Iro ya yi muku daga dawowarsa Sale?"
Ba tare da Sale, ya duba adadin furfurar kan Baffa ba, ya haske shi da fitila ya ce "Au tambaya ma ka ke yi? Hukunci ne da muka zartar a kan wanda yake tunanin karansa ya kai tsaikon da zai iya taɓa ahalinmu. Kai ku ja shi a ƙasa, ku ɗaure shi a jikin bishiyar nan, ya zama izina, ga duk wani wanda ya gaza ɓoye ƙwalamarsa a kan 'yan matan manoma"
Ras gabana ya yi mummunar faɗuwa, me Saleh yake nufi? Me yake Irona ya aikata da har ya cancanci wannan tozarcin?
Na yi kukan kura, na damƙe jikin Iro, da ba ni da tabbacin akwai rai a gangar jikinsa, ina kuka, na gaza furta komai.
Saleh ya haska ni da fitilar hannunsa nima, ya saka hannunsa ya fizge ni daga jikin Iro, ya yi jifa da ni gefe ɗaya, ya hankaɗe Baffa, ya ja Iro a ƙasa, sauran matasan suka rufa masa baya, wasu na dukan Iro da ƙafa, wasu na kwaɗa masa sandunan hannunsu.
Maƙwabtanmu suka fito, su na yi wa Saleh magiya, a kan ya yi haƙuri, a yi magana a sansanta, a ji me Iron ya yi musu, amma ya ce duk wanda ya kuma yi masa magana, sai ya haɗa da shi.
Na tashi na kuma nufar su, ina gursheƙen kuka, amma babu wanda ya saurari kuwwa da magiyarmu a cikin matasan nan. Aka rirriƙe ni, saboda kada Saleh ya cutar da ni. Mu na kallo su ka ɗaure Iro a jikin bishiyar darjebiya.
Cikin isa da bayar da umarni Saleh ya ce "Ku je gidan su, ku kwanto mini dabbobin da suke garken gidansu, zai zamana tamkar diyyar abin da ya aikata mana. Kuma wallahi duk wanda ya kwance shi daga jikin bishiyar nan, sai na yi masa abin da ya yi mana. Ba wannan ba ma, ina mai sanar da ku da jaddada muku, wannan hukuncin shi ne zai biyo bayan duk wanda ya aikata irin laifin da Iro ya aikata. Mun kama shi da yinƙurin haikewa ɗaya daga cikin yaranmu a bayan gari, dan haka wannan sai ya zama izina ga duk mai yinƙurin aikata laifi makamancin wannan. Suman zaune na yi, da jin maganganun da suka fito daga bakin Saleh. Ko rantsuwa na yi ba na tunanin kaffara za ta hau kaina, ƙarya yake yi wa Ironmu. Innarmu tuni ta sume dama, mu na ji mu na gani aka kaɗo dabbobinmu, aka shiga cikin gidanmu aka burkice komai, suka tafi suka bar Iro ɗaure a jikin bishiyar nan.
Na yi kuka, na yi gunji, na yi yinƙurin zuwa inda ɗan uwana yake, amma aka tare ni aka hana ni, saboda gudun abin da ka iya biyo bayan zuwa gurin nasa.
aka kece da ruwan sama, ma ƙarfin gaske, haka mu ka yi kwanan baƙin ciki da takaici, zukatanmu da na kusa da mu cike da baƙin ciki da ɓacin ran, da baki ba zai iya bayyana nauyin da zukata ke ɗauke da shi ba.
Da Asubar fari, muka fito, babu alamar rai a jikin Iro.
Har rana ta fito ta take, babu wanda ya iya zuwa inda Iro yake, saboda tsoron abin da ka iya faruwa. Kamar yadda tun tasowarmu, haka muka tarar da iyayenmu na rayuwa a cikin wannan tsoron, da ya yi wa rayuwar su dabaibayi, ake yi musu cin kashi yadda aka ga dama, mu ma kuma su ka haife mu, muka tashi a haka.
Sai da rana ta take, sannan Saleh ya taho da tawagar sa, ɗauke da wasu miyagun sanduna.
Su ka kwance Iro, yadda ya faɗo timm, ya ƙara tabbatar mana da babu rai a jikin Iro.
"Ka biyo mu bayan gari, ka binne wannan najastaciyyar gawar ɗan naka, dan ba za a sallaci mazainaci a cikin garinmu ba, ka je ka haƙa rami ka binne shi, a can bayan gari shikaɗai, dan wannan ƙazamar gawa ce, ba ta cancanci sutura ba".
Duk da ƙulli gami da ƙudurin da yake cikin zuciyata tun bayan da na tasa, na fara mallakar hankalina kaina, a yau na ajiye alwashina a gefe, na fito gaban mutane na sanya gwiwoyina a ƙasa, cikin magiya da hawaye a gaban Saleh, muryata na rawa na ce "Ka duba girman zatin Allah, ka yi haƙuri a yi masa sutura a binne shi kamar yadda addini ya tanada, ko wani laifin ya aikata, musulmi ne shi, dan Allah"
Ya zura mini ido na wani lokaci, daga bisani ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya, mai cike da rashin ɗigon imani ya ce "Jikar makiyaya, har kin karaya? Har kin manta alwashin da ki ka yi a kaina? Yau ke ce a gabana ki ke neman alfarma? Na so a ce zan iya yi miki wannan alfarmar, ko dan duƙa mini da ki ka yi, sai dai kash ɗan uwanki fasiƙi ne, kuma da ya tashi bai gwada halin nasa a kan kowa ba, sai a kan ahalinmu, dan haka wannan shi ne abin da ahalinku ya cancanta"
Ina kuka su ka tasa Baffa shikaɗai ƙwal, suka ja gawar Iro a ƙasa suka nausa cikin daji.
Duk dandazon mutanen da suke gurin, babu mutum ɗaya da zai iya faɗa a ji, balle ya tsawatarwa Saleh.
'Yan uwan mahaifina, su ka haɗa kai su ka tafi gidan su Saleh, wanda mahaifinsa ne, jagoran garin namu baki ɗaya, amma suka dawo gwiwa a saɓule, saboda yadda ya goyi bayan abin da ɗan sa ya yi. Tare da Jaddada cewar, an kama Iro da yinƙurin aikata wannan mummunan laifi, ba ƙazafi aka yi masa ba.
Duk da ba yau aka saba danne mu, da yi mana mulkin kama karya a ƙauyenmu ba, amma wannan karon an bar mana wani mummunan miki da zai dauwwama a cikin zukata har gaban abada. A iya sanina da ɗan uwana, mutum ne mai taka tsantsan da gudun duniya, kullum hankalinsa yana kan, yadda zai kiyaye mu, ya kiyaye mutuncinmu mussaman ni da Akuyata ta yi kuka a garin, kuma nake takun saƙa da Saleh. Kullum cikin nasiha yake yi mini, da ja mini kunne, a kan na yi haƙuri da abin da Allah ya hukunta mana, na rayu cikin salama da aminci. Baba ya yi niyyar haɗa Iro, shi da 'yar Baffanmu Mariya aure, amma ya nuna shi ba ya buƙatar aure a wannan lokacin, kasancewar Babanmu mutum ne mai son 'ya'yansa, sai ya ƙyale Iro bai sake yi masa maganar ba.
Sai dai na damu matuƙa da son sanin, wace yarinyar ce wannan, da har ake cewa ya yi yinƙurin ketawa haddi? Mutumin da ya shafe watanni huɗu ba ya gari, yaushe ya dawo da har ya yi yinƙurin haikewa wata? "Wace yarinyar ce a garin nan? Dole na nemo wace ce, sai ta ɗanɗana abin da Iro ya ɗanɗana, kuma ko a mutu ko a yi rai, jinin ɗan uwana Iro ba zai tafi a banza ba. Amma wace ce wannan yarinyar?" Na sake tambayar kaina.
Ghost writer 12/7/....
A hankali ta ja guntun tsaki, ganin a inda labarin ya tsaya, ta kai ta komo a cikin group ɗin, amma babu ci gaba.
**
Dandazon 'yan makarantar islamiyya ne suke ta fitowa daga cikin makarantar, wasu sun tsatstsaya su na ƙoƙarin tsallaka titi da ababen hawa ke ta kaiwa su na komowa. Matashiyar yarinya ce, aƙalla za ta yi shekaru sha huɗu zuwa sha biyar, hannunta riƙe da jakar islamiyyarta, tare da wasu yaran, su na ta surutu, suka tsallaka titi, suka gota wani matashi a tsaye su ka wuce. Sosai suke dariya cike da nishaɗi, suna hirarrakinsu. Ta waiwaya ta hango shi a bayansu yana tafiya. Ba ta damu ba, suka ci-gaba da hira da ƙawayenta. Suna tafe duk wadda aka zo kan kwanar gidansu, sai su yi sallama ta tafi, har ya rage saura su biyu. Suka ƙarasa wata mararraba, ta dubi ɗayar Ta ce "To sai kuma Allah ya kaimu gobe, ki riƙe dai-dai inda ki ka tsaya mini, za ki ƙarasa bani labarin, ni idan Yaya ya kama ni da karatun littafi ina ga kashe ni zai yi, amma duk yadda za a yi ki karanto ki zo ki bani labari"
Ɗayar ta yi dariya ta ce "Nima a ɓoye nake yi, sai kowa ya yi bacci, nake haska fitila ƙasa-ƙasa, ki gaida gida da matar Yaya"
"Za ta ji in sha Allah, ki gaida su baby" Tana ƙoƙarin shiga wani layi, ta waiwaya baya suka sake yin ido huɗu da matashin nan. Dogo ne launin fatarsa ba za ka kira shi baƙi ba, kuma kai tsaye ba za ka ce fari bane. Fuskarsa na ɗauke da yanayi na samartaka, yana da ɗan jiki, sai dai fuskarsa a cike da ƙasumba, ya sanya wata uwar babbar riga duk ta yamutse babu guga, yana da manyan idanuwa sai dai ba farare bane, sun sirka sun yi ja, haka kurum ta ji tsoro na neman ya shige ta. Da sauri ta shiga layin nasu, amma da ta yi nisa ta waiwaya sai ta sake ganinsa. Ba shiri ta fara sauri tamkar za ta tashi sama. Ta sake waiwayawa cikin tsoro, sai ta ga ba taga gan shi ba. Ta yi ajiyar zuciya, ganin layin babu kowa, ya sanya ta kyalla da gudu ta ƙarasa gida.
"Assalamu alaikum" Ta yi sallama daidai lokacin da ta faɗo tsakar gidan.
Matashiyar mata ce a tsaye, tana kwashe shanya ta ce "Yaya? Ke da wa?"
Ta ɗan waro ido "Wani mutum na gani, tun daga ƙofar islamiyyarmu yana bina"Ta yi maganar fuskarta na bayyanar da tsoro.
Matar ta yi turus tana nazarin maganganunta. "Yake binki saboda me?"
Ta ce "Ina na sani, daga baya dai da na shigo layin nan, ya daina bina, dan da na waiwaya ban gan shi ba"
Ta yi murmushi ta ce "Alina kenan, ƙila ma hanya ce kawai ta biyo da shi, ki ka sani ma, ko saurayi ki ka yi, gani yayi yana so ya biyo ki? Amma ki ke ta guje-guje kamar ba budurwa ba"
Ta waro ido tana ƙiftawa ta ce "Kai rufa mini asiri, kar Yayanmu ya ji wannan maganar ma, wai a ce na zo da saurayi ai sai ya kusa kashe ni, rufa mini asiri. Amma an rage abinci?"
Matar ta tsuke fuska ta ce "To acici, ai kya fara zuwa ki cire kayan ki nutsu tukuna"
Alina ta nufi ɗakin tana murmushi ta ce "Kin san ina da tsutsar ciki ne, da na ci take cinyewa"
"Ke ce tsutsar ai" Ta yi dariya tana shiga ɗaki.
**
Tana tsugunne a cikin turken awakin da ke tsakiyar ƙaton tsakar gidan. Ta share turken tsaf, ta din ga kama dabbobin tana ɗaurewa ɗaya bayan ɗaya. Ta gama ta zuzzuba musu abinci da abin sha.
"Sannu da aiki Ramatu" ta ɗago ta kalli farin dattijon, da yake zaune a kan tabarmar kaba, gefensa da radio yana saurare.
"Baffa dan Allah ka din ga gaya mini sunan zamani, tun da ka je mini visiting, ka faɗi Ramatun nan, ake tsokanata"
Ya yi dariya ya ce "To Ramata"
"Kash ana jika dai kunamar bebe Baffa, ka ce Rahma"
"Na ƙi" ya yi maganar yana dariya. Ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi a kan tabarmar.
"Idan kin huta, zan baki magani ki kai wa Talatu, an ce yaronta yana masassara"
Ramata ta rausayar da kai "To Baffa" ta yi maganar tana ɗan sunkuyar da kai.
"Ramata, na san abin da ki ke tunani, babu ruwanki da su, da kin kai ki dawo, kar ma ki tsaya ki ji me za su faɗa"
Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Baffa, amma dama...
"Dama me?"
Ta ɗan daidaita nutsuwarta ta ce "Baffa zan samu ci gaba da karatun kuwa?"
Ya ɗan yi shiru, sannan ya dube ta "Ramata, zan yi alfahari na ga kin yi karatu mai zurfi, wataƙila albarkacinki, mu samu ci gaba da mafita a garin nan, amma kina kallo a haka ma, su na nema su kafirta mu, saboda makarantar da ki ka yi. Ki yi haƙuri a manemanki, ki samu wani ku daidaita ko ba yanzu ba, idan da rabo sai ki ga kin ci gaba a gaba. Amma ba na so baki ya yi mini yawa a kanki. Duk da na san ko a yanzu mun ciri tuta kaf rigar garin nan, babu wadda ta samu ilimin da ki ka samu, na shiga kundin tarihi ginis rikol suke cewa a radio ko me?"
Ramata ta tuntsire da dariya ta ce "Baffa guinnes world record ake cewa. Kar ka damu ko kai ba ka shiga ba, ni zan shiga, zan rubuta littafi mafi tsawo a duniya, ko kuma wani abu mai ban mamaki dai, da sai duniya ta tafawa Ramatanka"
Baffa ya yi dariya ya ce "Ko a yanzu dole na tafa miki ai. Ai ni tun da aka nuno mini ke a salalula, kin ci gasar lissafi, sannan na ji sunanki da nawa a radiyo, na ce haihuwa mai rana, dalilin ramatuna ga sunana a radiyo"
Wata mata ce ta fito, daga ɗaya daga cikin jerin bukkokin da suke harabar gidan, tana jan guntun tsaki, da surutai ƙasa-ƙasa. Ta harari inda su Ramata ke zaune suna hira.
Ramata kuwa hankali kwance suka ci gaba da hira da Baffanta. "Yanzu ka ga Baffa, da karatun boko ka yi, tsaf za ka zama farfesa, kana da saurin gane abubuwa da riƙe su"
Suka yi dariya baki ɗaya.
*** Su na zaune da daddare su na cin abincin dare.
"Alina" ya kira sunanta
"Na'am Yaya"
"Tunanin me ki ke yi ne?"
Ta ce "Ba komai, abinci nake ci"
Yaya ya ce "Faɗi gaskiya dai"
Matar Yaya ta yi murmushi ta ce "Alina na faɗa"
Ta ɗago ta ce "Me?"
"Abin da ki ke tunani mana"
Alina ta yi dariya ta ce "Ai babu abin da nake tunani"
"A'a fa, Yaya saurayi ta yi shi ne...
Da sauri Alina ta ce "Innalillahi, wallahi yaya ba haka aka yi ba, haba Anty idan ya zane ni fa?"ta ƙarasa maganar a shagwaɓe, kamar za ta yi kuka.
Ta kwashe da dariya ta ce "Yaya ka san ba zan yi mata ƙarya ba ko? Siriki ta samo maka"
Cikin tsoro ta ce "Wallahi ni ba saurayina ba ne ba, kin gan shi kuwa, ƙazami da shi fuskarsa duk gashi" Ta yi maganar duk a ruɗe, da ƙoƙarin kare kanta, kar yayan ya ɗauka da gaske ne. Ganin ta ruɗe shi ma ya ce "A'a mutuniyar gaya mini gaskiya, idan aure ki ke so ai ba wani abu, ki turo shi mu gaisa mana"
Kawai ta hau kuka "Ni wallahi ba saurayina ba ne, ba aure nake so ba"
Gaba ɗaya suka hau yi mata dariya, ya ce "Ni dai kin san bana son kwana-kwana, abin da ki ke so shi nake so. Masoyiyya ina ga zan ba ki kuɗi a fara sayayya"
"A'a da wasa nake yi, haba Alina daga wasa sai kuka, ba mai yi miki aure yanzu, sai mun gama jin ɗumin juna ko ƙanwar yaya?"
Ta yi maganar tana janyo Alina jikinta.
Ya yi dariya ya ce "Wai kukan take da gaske?"
"Wallahi kuka take yi"
Ya miƙe yana faɗin "Babu ruwana, ai kun fi kusa, Kano da jigawa in ji kanawa, ke ki ka haɗa zancen"
Da kyar ta rarrashe ta ta daina kukan.
**
Uniform ɗin makarantarta sun sha karin guga, tana tafe tana ta ƙara karkaɗe ƙura daga jikin uniform ɗin, idan ta karkaɗe uniform, sai ga koma karkaɗe jaka, ta koma kan goge takalmi. Ta ɗaga kai zata shiga lungun da zai ƙarasa sadar da ita da titi, kawai ta gan shi a tsaye cak yana kallonta, da manyan idanunsa tamkar za su faɗo, yau ma da wannan Koriyar babbar rigar a jikinsa, wadda take duk a yamutse. Gabanta ya yi wata irin faɗuwa ta tsaya cak.
1k ne littafin nan a telegram via 0069685771 Aisha Adam stanbic Sai shaidar biya ta 08081012143