
Post
SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 15
....every job has a bad attitude, and that's the nature of the job, you won't break the work law to impress you." Saddam pulled the neutral father and just frowned. Then after the afternoon they were listened to, and Laila was brought out, her face was covered in mosquito bites. The policeman calmly looked at Mama and said, "Hijaya, your girl is not listening to the truth. She went to touch the big people, and said that if they put their hands, they will be taken away." Frustrated, Mama said, "Laila, if you don't take care of your life, the next day you will kill us. God bless this newspaper. By God, may your life be long, there is no such red ear that I did not do to her, she was patient and left it to God, but she refused. Look at the greatness of God and be patient. She is a girl and she is your daughter, her father is a former policeman, she is your daughter." He looked at Laila and said, "Girl, you are young, live your life by focusing on everything that you have no power to fix, otherwise, you will suffer in vain." Laila bowed her head and refused to speak. she was crying and giving patience, son of God, they are asking for her bail" "Don't k.....
SARA DA SASSAƘA... YOTA 002 AYSHERCOOL
Page 15
Hankalin Maman Laila ya yi mummunan tashi, ganin a inda Laila take. A babbar headquarter yan sanda ta jiha aka kai ta. Shi ma sashen da aka kaita, aka gaya musu wanda case ɗin yake hannunsa baya nan sai dai su jira.
"Yanzu Saddam a gurin nan duk maza yarinyar nan ta kwana? Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Wai laifin me ma ta yi ne?"
Saddam da ransa yake a ɓace shi ma ya ce "Mama tare da ke fa muka zo gurin nan, nima ban san abin da ta yi ba, sai dai mu jira mu ji me za su ce"
Bala ya ce "Ki yi haƙuri Mama, da yardar Allah yau zamu tafi da ita."
Duk magiyar da Mama ta yi, aka hana su ganinta. Har azahar su na gurin a zaune, sai bayan azahar wanda case ɗin yake a hannunsa ya zo, shi ma da ya zo ya ce musu su na da meeting da IG dan haka su ci gaba da jira.
"Wallahi ban da mahaifina ma ɗan sanda ne a cikin aikin ya mutu, da sai na tarkata su na tsine musu wallahi yan wahala"
Bala ya ce "A'a Saddam kar ka yi abin da za su ƙara shanya mu, kuma kowane aiki akwai ɓata gari, wani abin kuma yanayin aiki ne a haka, ba za a karya dokar aiki domin a burge ka ba"
Saddam ya ja uban tsaki kawai yana sake turɓune fuska.
Sai bayan la'asar aka saurare su, aka fito da Laila, fuskarta duk cizon sauro.
Cikin nutsuwa ɗan sandan yake kallon Mama, ya ce "Hajiya yarinyarki ba ta ji gaskiya. Ta je ta taɓa manyan mutane, ta ce da saka hannunsu ake ƙwacen"
Cike da takaici Mama ta ce "Laila, idan ba ki kiyayi rayuwa ba, wataran sai kin janyo an kashe mu. Allah wadaran wannan harkar jaridar taki. Wallahi ranka ya daɗe, babu irin jan kunnen da ban yi mata ba, a kan ta yi haƙuri ta bar wa Allah ba, amma ta ƙi. Ku dubi girman Allah ku yi haƙuri. Marainiya ce kuma 'yarku ce, mahaifinta tsohon ɗan sanda ne yarku ce"
Ya kalli Laila ya ce "Yarinya, kina da ƙanan shekaru, ki mori rayuwarki ta hanya zuba ido ga duk abin da ba ki da ikon gyara shi, idan ba haka ba, wahala za ki sha a banza." Laila ta sunkuyar da kai ta ƙi magana.
Ya daddana waya ya kira wata lamba ya kara a kunnensa. Bayan sun gaisa ya ce "Honourable batun yarinyar nan ne, dan Allah a yi haƙuri, ga mahaifiyarta tana ta kuka tana bayar da haƙuri, dan Allah su na neman belinta"
"Kar ka kuskura, ba zai yiwu ba, ai sai na banbance mata aya da tsakuwa, ko da wasa aka sake cewa ta fito ta yi soki burutsu irin wannan ba za ta yi ba"
"Amma ga mahaifiyarta a gurin ba dan ita ba...
"Babu ruwana na gaya maka, sai na wulaƙanta yarinyar nan, za ta ga ƙarshen rashin hankali" Ɗan sandan ya kashe wayar. Mama ta riƙe haɓa, ta ce "Yanzu a kan wannan yar da ya haifa yake iƙirarin zai wulaƙanta? 'yar da ya haife ta? To Allah ya kyauta idan Allah bai wulaƙanta ta ba, babu wani wanda zai wulaƙantata"
"Shiyasa ake cewa, ku din ga ja wa yaranku kunne, ku din ga ba su tarbiyya su din ga iya bakinsu"
"Ku yi mata duk abin da za ku yi mata, kai ka ga alamar rashin tarbiyya a tattare da ita? Tsawon shekaru mahaifinmu na yi wa ƙasa hidima aikin ɗan sanda, ɗan abin da ya mutu ya bar mana, wasu sun yi kashe mu raba a tsakanin su, kuma a ce kar mu yi magana ƙasa za mu ci mu rayu? Idan hidimar wani ta tashi a cikinmu wani zai yi mana ne". Saddam ya ƙarasa maganar jikinsa yana rawa saboda baƙin ciki. "Kai, ka zo har gurin aikin nawa ka nemi ka gaya mana magana, yaran talakawa tarbiyyar ce da ku? Zan saka a rufe ka wallahi"
"Ba rufe ni za a yi ba kashe ni za a yi" Bala ne ya danƙi hannun Saddam suka yi waje, yana rarrashinsa.
"Saddam mutanen nan, wasu ba mutunci ne da su ba, babu Allah a ransu. Ka rabu da su, na san abin da zan yi, ko ba yau ba zuwa gobe in Allah ya kaimu, Laila za ta fito"
Haka ya rarrashi Mama ma, suka sai Abinci aka ba wa Laila suka koma gida, ya din ga basu ƙwarin gwiwa a kan yana da hanyar da zai fitar da ita.
Tun da suka koma gida, daga Saddam har Mama babu wanda yake walwala. Duk da Mama na ta faɗan halin Laila na azabar kafiya.
Shi kuwa Saddam daga baya bai ga laifin Laila ba, dan yarinya ce mai sauƙin kai mara hayaniya, amma akwai kafiya, kuma duk abin da ta wallafa ya san tana da cikakkiyar shaida da hujja a kan abin da ta yi.
Bala kuwa shi ma rubutun ya wallafa a shafinsa, da bayanin cewar an kama Laila, saboda maganar da ta yi da sunayen yan siyasar da kama, da cewar an haɗa kai da su ana ƙwacewa mutane filaye. Duk da wasu na jin haushinta, amma kasancewar ayyukan da take yi a shafinta ba siyasa bane kawai, ta kan faɗakar, koyarwar addini, girke-girke motivational speaking, idan baka ƙaru da ita ta wani fannin ba, za ka ƙaru ta wani, dan haka nan da nan mutane suka din ga reposting abin da ya faru.
****" A hankali ta motsa, ta yinƙura domin tashi zaune, amma ta koma yuuu saboda wani irin azababben jiri da ciwon kai da ya ɗebe ta. Ta buɗe idonta a hankali ta din ga gani dishi-dishi, ga kanta da yake yi mata wani irin azababben ciwo. Ta koma ta kwanata ta yi lamo, a hankali komai ya fara washewa. Ta kalli gurin ɗaki ne na Asibiti, da gadaje kusan biyar a ciki, sai dai itakaɗai ce a ɗakin. Ga hannunta ɗaya sanye da ruwa. Hayaniya ta din ga jiyowa sama-sama, ana wani irin yare ana haɗawa da broken English. Sai kuma ta ji ɗif an daina sai alamar takun takalma. Ƙofar ɗakin aka buɗe, maza ne suka shigo zabga-zabga, sanye da kaakin soja a jikinsu. Sai dai a wanda suka shigo ɗin duk ya kere su a tsayi. Wandon sojoji ne a jikinsa, sai riga armless shirt army green. Gefen wandonsa a soke da wata 'yar ƙaramar bindiga. Ya ɗan tara suma a kansa, sai dai yanayin askin gaban kan tafi cika, zagayen kuma kwantacciyar suma ce, gwari-gwari dai yanayin askin da ake kira da balatoli. An yi wani abu mai kama da arrow a gefen kan. Babban abin da ya sake jan hankalinta bai wuce sarƙar da take wuyansa ba, da ya zura ta a cikin rigarsa, amma saman chain ɗin ba za ta manta da shi ba, lokacin da ya zo tana Asibiti amma ya musa mata, ya ce ba shi ba ne. Gefensa wani matashin ne da za su iya yin tsawo ɗaya da shi, hatta askin kansu iri ɗaya ne, sai dai kowanne kamarsa daban. Sai dai ta tuna ranar da ta je sayen leda shagon Mamman da yamma ta gansu tare. Kenan duk tsawon wannan lokacin da take ganinsa, wani abin ne shi daban ba abin da take tunani ba? Ashe Yaya Ismail ya fita gaskiya. Tana nan kwance suka ƙarasa har gaban gadon take, sai dai tana kwance kamar an dasa ta, ta kasa komai. Suka ƙarasa suka kewaye gaban gadon take. Gani ta yi tamkar an canza shi, gaba ɗaya ya juye daga Mamman ɗin da ta sani, suka shaƙu, da suffarsa da kamaninsa sun koma wani abu na daban. Fuskarsa a tsuke tamkar bai san hanyar inda ake bi a yi dariya ba, babu alamar annuri, sai ɗan rarraba manyan idanunsa yake yi da suka ɗan kaɗa suka yi jawur, duk da idanunsa sun saba ba ta tsoro, amma sai ta ga gara lokacin da ta san shi a Mamman, babu alamar afuwa ko sassauci a cikin waɗannan idanuwan. Wannan gashin na fuskarsa ma babu shi, fuskarsa tas take sai ɗan yarfin gashin baki kaɗan. A hankali take buɗe idonta tana lumshewa. Ya riƙe ƙugunsa yana kallon drip ɗin da yake shiga jikinta ɗis-ɗis. "Kai Mega kamar haryanzu she's unconscious"
"Yeah" Ya faɗa a taƙaice, ya janyo side drower, ya ɗaukko file ya buɗe ya yi dube-dube, ya duba ya ɗauki ya biro, ya yi rubuce-rubuce a cikin file ɗin, ya mayar ya ajiye. Ya duba cikin kayan maganin da ke gurin, ya ɗauki wata allura, ya zuƙe ya fara zubawa a cikin drip ɗin. Miƙa ta yi tana yamutsa fuska, jin yadda shigar ruwan, tare da allurar ya burkita mata jiki gaba ɗaya, ta ji wani irin raɗaɗi, ƙoƙarin tashi ta yi saboda yadda allurar ta gigita ta. Ya saka hannayensa ya danne ta. A hankali jikinta ya saki, bacci ya ɗauke ta. Alfa ya ce "Mega, me ka ke yi mata haka kuma? Kar fa ta ƙarasa"
Mega ya ce "Shut up" Ya yi maganar yana ɗan zaro masa ido.
"An ƙi ɗin, ka san zuwa gobe in Allah ya kaimu Oga Musa za su zo, su ganta"
Ya kalli sauran sojojin da suka zo tare, ya yi musu alama da su fita. Bayan sun fita ya dubi inda Alina ke bacci ya ce "Ta na da magrine headache, tana cikin damuwa da kuma tsoro. Akwai buƙatar ta huta sosai ƙwaƙwalwarta ta samu nutsuwa. Sai ta zama stable ne za a iya samun bayanan da ake buƙata daga gare ta"
Ammar ya jinjina kai cike da gamsuwa.
"To yanzu what next?"
"Eh, zamu je gurin matar nan, ina son grabbing wasu abubuwan daga gare ta, ina buƙatar tattaunawa da ita"
Ammar ya yi shiru yana kallon Alina, ya kalli Mega ya ce "Omega, ka san tsabar soyayya kun fara kama da yarinyar nan?"
Tsaki Mega ya ja, ya saka ƙafarsa ɗaya, ya daki ta Ammar da ƙarfi tare da furta "You are not serious" Ammar ya biyo shi yana murmushi ya ce "Wallahi sai na rama"
*****
Laila na zaune a cikin cell, wani ɗan sanda ya buɗe ta ya ce ta fito. Ta tashi jiki a sanyaye ta fito. Ɗan sandan jiya ne ya saka aka kawo mata kayanta ya dube ta ya ce "Kin ci sa'a, an bayar da umarnin gaggawa a sake ki, idan kin ga dama ki je ki ci gaba da iskanci. Ku ba 'ya'yan kowa ba amma kun fi kowa rashin mutunci. Kuma a nan da awa arba'in da takwas, ki koma ki yi video ki ba wa Honourable da sauran mutanen da ki ka kama sunansu, haƙuri ko kuma abin da zai biyo baya ba zai yi miki daɗi ba" Ba ta ce komai ba, ta karɓi jakarta za wayoyinta, ta fito reception, ta waiwaya ta kalli ɗan sandan ta ce "Na gode sosai Sir, abin da ya faru da ni ya ƙara mini ƙwarin gwiwar gwagwarmaya, ka gaya wa Honourable zan yi video na ba shi haƙuri. Ba zan sake ba 'ya'yan talakawa mun bar wa masu duniya su ci gaba da cin jahannama a cikinsu"
"Laaa" Ɗan sandan ya faɗa bakinsa a sake.
"Sir yarinyar nan fa ba ta daku ba"
"A'a ki je ga ki ga su nan ai, a banza za su illata rayuwarki, babu abin da aka isa a yi kuma, sauka lafiya"
Ɗaya ɗan sandan ya ce "Ikon Allah, gaba ɗaya fuskarta ta salihai ce"
ISP Sagir ya ce "Ta munafukai dai, ni na yi mamaki, daga sama fa aka bayar da umarnin sakinta"
Suka ci gaba da tattaunawa, Laila kuma ta tsare abin hawa ta tafi gida.
*****
Ɓangaren su Rahama kuwa, dawowar Sadauki inda ake tsare da su, ya ɗan sama musu sassauci, ana ba su Abinci an daina dukansu. Tun da macijin nan ya sari Rahama, ba ta sake taka ƙafarta ba. Sai dai yau da ya dawo daga yawonsa, daga nesa da su kaɗan ya tsaya a kan babur, ya yi mata nuni da ta zo. Ta kalle shi ta kalli ƙafarta, ya sake yi mata alamar ta zo. A hankali ta yinƙura ta daddafa bishiya, ta miƙe ta tsaya ta ji ƙafafunta tamkar an ɗaura mata duwatsu. "Ta ko da Bismillah, da sunan Allah" Ya yi maganar yana zuba mata ido, ta fara takawa a hankali cikin tsoro, yana zaune a kan babur ɗin yana kallonta. Ji take yi tamkar ta faɗi, amma ta daure ta ci gaba da takawa har ta je inda yake ta tsaya, tare da sunkuyar da kanta. "Yayi kyau,koma ki je ki zauna" Ta sake juyawa ta koma, har za ta zauna cikin ɗaga murya ya kira sunanta "Rahama"
Ta waiwayo. "Waa ɗoo" (Zo nan)
Ta sake dawowa, sai cukuikuye jikinta take yi a cikin babbar rigarsa da ya bata.
"Ya jikin naki?"
"Da sauƙi"
"Alhamdillah, ba wata matsalar?" Ta jinjina kai.
Ya ce "Ba ki da baki ne?"
"Babu matsala" Ta yi maganar tana sunkuyar da kai.
"Allahumma yashfiki, je ki zauna Allah ya sauwaƙe. Je ki ki zauna"
Ta amsa da Amin, ta juya za ta tafi.
"Ke zo nan" Ta waiwaya ta sake tsayawa.
"Duk abubuwan alkhairin da na yi miki, babu ɗaya da za ki iya cewa kin gode?"
"Na gode"
"Wuce ba na so" Ya yi maganar yana kafe babur ɗin sa ya sauka daga kai. Ita dai ba ta sake cewa komai ba, ta koma gurin zamanta ta zauna.
*****
Arewapen
Zaune suke su biyar a cikin office ɗin, kowannensu sanye da kaakinsa na aiki. Sun baje wani map a kan table su na dubawa.
Ɗaya ya numfasa ya ce "Haryanzu mr. President, da al'ummar ƙasa, su na jiran ji daga gare mu, duk da pressure da aka saka mana, dole ne mu yi amfani da hikimomi da dabaru, dan kar rayuwar yaran ta salwanta"
Suka amsa da gaskiya ne.
"Commadore Edward, za mu jira, ku duba mana exact gurin da yaran suke, mu kuma za mu shirya duk abin da yakamata. Duk wani abu da zamu yi, za mu yi shi ne within 8days, mu fitar da kyakyawan result"
Commadore Edward ya ce "Babu case, komai zai tafi yadda aka tsara, akwai yiwuwar su canza guri, muddin suka farga mu na neman inda suke. Amma gano inda suke ɗin shi ne babban target, ba wani abu"
Suka kammala tattaunawa, suka yi musabaha da juna, sannan suka naɗe map ɗin suka bar office ɗin.
***** Laila ce ta yi sallama a gidansu, Da sauri Mama ta fito daga kitchen, cike da son tabattar da Lailan ce. Tana tozali da Laila kuma sai ta tsuke fuska. "Sun ga dama sun sako kin kenan?" Laila ta jinjina kai ba tare da ta yi magana ba.
"Yanzu kin ga sakamakon mai bijire wa maganar iyaye ko? Babu yadda ban yi da ke ki bar maganar nan ba, amma ki ka ƙi. Ke ba kowan kowa ba, ba ki da wani gata sai na Ubangiji, amma fitina ta yi miki yawa Laila. Ni dai lafiya na rabu da iyayena da mijina, balle na ce ko hakkinsu ne yake bibiyata ya sanya ba kya jin magana ko kaɗan.
Saddam da shigowarsa kenan, ya ce "Haba Mama dan Allah, daga dawowarta ki yi haƙuri ta huta ta ci abinci mana"
Mama ta juya kansa da faɗan "Ba zan bari ta huta ɗin ba, ni kwana biyu a jere hutawar na yi? Yanzu abin arziki ne a ce mace ta kwana a hannun 'yan sanda har kwana biyu, gurin 'yan sandan ma, sashen kula da manyan laifuk, ita ba kisan kai ba, ba fashi ba?"
Saddam ya yi wa Mama shiru, ya dubi Laila da take kuka, ya ce "Shigo ki zauna rabu da ita"
"Eh a rabu da ni mana, tun da ga mahaukaciya tana faɗa ko? Ku je ku yi abun da ku ka ga dama, babu mai kashe ni lokacina bai yi ba"
Saddam kuwa murya ƙasa-ƙasa ya ce "Ki yi haƙuri, ɓacin ran kin kwana biyu a gurin 'yan sanda ne ya sanya take yi miki faɗa, amma ki yi haƙuri. Ina fatan ba su yi miki komai ba dai ko?"
"Sun mare ni" Ta furta tana sake fashewa da kuka. Saddam ya yi shiru yana kallonta, wani abu ya tokare masa a ƙirji, idanunsa suka yi ja. Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Kar ki gaya mata an dake ki, ki yi haƙuri ni na fahimce ki, hakkinmu ne aka danne, shi ki ke fafutuka a kai, zan taya ki da yardar Allah ko ba za mu yi nasara ba, duk abin da ki ke nema, ki yi mini magana zan taimaka miki, amma ki daina kuka ki yi haƙuri" Ta jinjina kai tana share hawayen da yake gangarowa a kan fuskarta.
Ya miƙe tsaye ya ce "Bari na je gurin Umman su Bala, na karɓo miki ruwan zafi ki yi wanka, ki ƙyale Mama ta gama faɗanta ta huce" Jinjina masa kai kawai ta yi ya fice. *****
Sannu a hankali suke ratsa tsakanin ofisoshin, har suka ɓulla can wani ɓangare da babu wadatattun ma'aikata a gurin. "Alfa, tun da muka kawo mutumin nan fa, ba a sake bari mun gan shi ba"
Alfa ya ɗan sosa girarsa ya ce "I wonder, ina ta so na yi maganar amma dai na yi shiru, amma kamar na ji Oga Musa kan ya tafi yana cewa, za a canza masa guri, maybe ma a bar garin nan da shi gaba ɗaya"
Mega ya ja ya tsaya, ya ce "A bar nan garin da shu a kai shi ina?"
Alfa ya ɗage kafaɗa tare da faɗin"I don't know"
"Amma kana ganin ya dace a yi hakan, ba tare da mun ji komai ba, mussaman ni da na yi duk ƙoƙarin?"
"And someone is taking the credit of your work ba, so sad. Na tausaya maka Mega"
Abdallah ya ɗan yi shiru sannan ya numfasa ya ce "We shall see" Ya ƙarasa maganar ana buɗe musu wata ƙofa, da gurin yake ɗauke da duhu.
Mai tsaron gurin ya sara musu, sannan ya sake buɗe musu wata ƙofa, mai kama da ta fursinoni. Suka ajiye wayoyinsu a waje, da bindigoginsu, aka caje su. Mai cajesun ya damƙo wani abu a aljihun Alfa. Alfa ya zura hannu ya ɗaukko ƙaramin biro a jikinsa, aka karɓi biron aka ajiye, sannan suka shiga.
Tana zaune ta takure guri ɗaya, tamkar mai taɓin ƙwaƙwalwa, ta ɗago ta yi musu kallo ɗaya, ta mayar da kanta ƙasa ta sunkuyar.
Abdallah ya gyara zaman hular sojojin da ke kansa, ya ƙarasa gabanta ya durƙusa yana kallonta. Sai dai ta sunkuyar da kanta, ta ƙi ɗagowa su haɗa ido.
"Nadiya ko?" Ya furta yana tsare ta da idanunsa.
Ta ɗago a hankali ta dube shi ta ce "Au ba ka ma tabattar da sunan nawa ba?"
Mega ya girgiza kaiya ce "A'a, ina son sake samun tabbaci daga bakinki ne. Ina son zan yi miki wasu tambayoyi ne, da nake buƙatar ki bani haɗin kai, ki yi mini cikakken bayani"
Ta yi murmushi tare da maimaita faɗin "Tambayoyi? Ni za ka yi wa tambayoyi na baka amsa? Shikenan ina jinka faɗi"
"Suwaye iyayen Alina na haƙiƙa?"
Ta yi shiru tana ɗan kaɗa kanta, sannan ta ɗago fuskarta ɗauke da murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarsa ta ce "Kai da uban gayyar yake hannunku, yaya za ku zo ku na tambayata?, ai shi ya fi kyautuwa ku je tambaya? Shi ne yake da amsar tambayar ba ni ba"
Mega ya tsuke fuska, saboda yadda ya fara ƙuluwa da murmushin da take yi, ya ce "Ke nake tambaya yanzu"
"Ba ka da ikon tambayarsa, saboda an killace shi an hana ka ganinsa ko? Haryanzu fa ba ma a yarda da kai ba, na cewar ka kama Kacalla Sumale ba. Sannan ba ka da tabbacin yana ina a halin yanzu. Na san ka fara jin kanka kai wani jarumi ne, saboda ka kama shi, tabbas ka cancanci jinjina na ɗan lokaci, dan babu wanda ya taɓa gano gaskiya da ka gano a cikin duhu, sai dai gaskiyar ta suɓuce a hannunka, kuma ita ma ta yi duhu ta sake ɓacewa ganinka a cikin duhun. Wannan kuskuren da ka yi zai iya zama ajalinka, dan duk wanda ya gano shi, sai ya kawar da shi daga doron duniya, idan ba wanda ya yarjewa ya gano shi ba. Abu na gaba kuma muddin Kacalla na rayuwa a doron duniya, zai iya zubar da kowane irin jini, zai kashe kowane ne, domin Alina! Ka tafka babban kuskure mai muni da hatsari gare ka da rayuwarka" Gaba ɗaya suka yi shiru su na kallonta.
Ta jinjina kai ta ce "Ƙwarai, zai ci gaba da bibiyarka, zai yi farautarka babu dare babu rana, saboda ita. Kacalla Sumale ya shallake duk yadda ka ke tunani, yana da abin da baka tunani. Ni kaina a tsawon lokacin da na riƙe Alina da ina da hali, sai na ba ta guba na kashe ta, saboda tsananin kishin yadda yake ƙaunarta fiye da ransa. Sai dai ina kyautata zaton baƙin alhaki ne yake bibiyarsa, saboda iyayen Alina ne jini na farko da Isma'il ya fara zubarwa a Duniya da hannayensa!"
Tsit suka yi gaba ɗaya su na jin ta, tare da yin jarumtar ɓoye mamakinsu, mussaman ma Mega.
Alfa ya ce "Ke ban gane ba, iyayenta ne mutane na farko da ya fara kashewa, to ta yaya aka yi ya ɗauke ta ya riƙe ta? Suwaye iyayen nata? Sannan kema kuma wace ce? A ina sauran ahalinta suke?"
"Wannan tambayoyin duk shi ne zai ba ku amsar su. Abin da ba ka sani ba shi ne, Ismail ya san waye kai. Shi ne ya kashe Malam Ɗayyabu bayan da ya yi masa ƙarya. Bai yi maka komai bane ba, saboda gudun halin da Alina za ta iya shiga. Sannan ai ina aikinka a kansa ne kawai, tun da ka gama aiki a kansa babu buƙatar ka zurfafa a kan Alina babu ruwanka da ita. Ka sani ya gama tsara komai, a kan matakin da zai iya ɗauka a kanka, bai kai ga aiwatarwa ba, ka riga shi motsawa. Ina mai baka tabbacin zai fita, dan Kacalla Sumale ba mutum ɗaya ba ne ba, mutane da dama masu burin cimma muradai daban-daban a cikin mutum guda, kuma muddin ka na yawo a doron ƙasa ko shi ko na cikinsa za su hallaka ka, saboda ka gano abin da duk wanda ya gano mutuwa yake yi.
Har ya buɗe baki zai yi magana, ya jiyo muryar mai tsaron Nadiya ya ce "Oga Mega time fa ya yi, kar a zo a kama mu, daga ni har ku mu shiga matsala"
Mega bai iya cewa uffan ba, ya miƙe tsaye,, Alfa kansa bakinsa tambayoyi ne a ciki, gaba ɗaya maganganun Nadiya sun ɗaure musu kai, amma haka suka yi waje suka bar gurin.
Mega ya dafa kafaɗar Mai tsaron ya ce "Thank you Nelson"
"Welcome sir" Ya yi maganar cikin girmamawa yana yi wa Mega murmushi.
Yadda yake tafiya yana dukan ƙasa da ƙafafuwansa, tamkar ƙasar ce ta yi masa laifi. Ba tare da ya sani ba, haka yake ta wani irin huci, tamkar zai shiɗe saboda tashin hankali.
Sai da suka ƙarasa office ɗin su Mega, Ammar ya rufe ƙofa ya dubi Abdallah ya ce "Mega wata sabuwa in ji 'yan caca, ka yarda da maganganun matar nan kuwa?"
Ya jinjina kai ya ce "Biri ya yi kama da mutum, but was fooled Alfa, meyasa tun da muka kawo shi, bamu sake ganinsa ba ko jin inda yake ba, aka hana mu ganinsa mussaman ma ni da muka yi aikin tare da sauran jami'an?"
Alfa ya ce "Yes tambaya ce mai ma'ana, amma ni ban ji na yarda da ita ba, amma ni abin da ya bani mamaki, meyasa ya kashe iyayen yarinyar? Me kuma ya sanya ya ɗauke ta ya riƙe, yake yi mata irin wannan mugun so? Kai Mega akwai maganganu da dama a bakin matar nan da suke buƙatar fashin baƙi. Suwaye mutanen da suke cikin Kacalla Sumalen, suwa yake yi wa aiki?...
Ayshercool 08081012143
*ALHAMDILILLAH A NAN MUKA KAWO ƘARSHEN FREE PAGES, GA MAI SON CI GABAN LITTAFIN BOOK 1-3 ZAI BIYA 1K VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143. MUTANEN NIJAR KU TUNTUƁE NI, DAN JIN YADDA ZA KU SAI NAKU. WANDA ZA SU JIRA SAI NA KAMMALA SU SAYA ZA SU SAYE SHI A KAN 1500 NE. INA GODIYA SOSAI DA SOSAI DA KASANCEWARKU DA ALƘALAMINA TABBAS SARA DA SASSAƘA ZAI NISHAƊANTAR ZA FAƊAKAR, ZA KUMA BANKAƊO ABUBUWA DA DAMA WASU AN SAN DA SU WASU BA A SAN DA SU BA. AYSHERCOOL 08081012143
AMANA KAYAN MATAN Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto.
Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su..
Gumbar madara Gumbar mata Gumbar aya Gumbar chaku Gumbar dake saukar da ni'ima Gumabar taƙadari Gumbar riɗi Gumbar dabino Gumbar uku alkhairi Kazar amare Jijjiɓen saniya Tabaje Tsimi Rikita mai gida Jigidar tada sha'awa Ruwan boom ruwan daɗi kenan Ɗan matse Karya gado Maganin sanyi Zumar ƙarin ni'ima Zumar rage ƙiba Zumar ƙarin ƙiba Zumar riɗi Mai zamani Emergency powder Tarhama Kafi budurwa Sabon budurci Alfijir Gamzaki Garin dahuwar nama Sabaya Miskin ɗahara Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina.
*Jama'a Albishirinku, mun sake shirya tsaf domin kawo muku advance class, na koyar da sana'oi da muka yi firts batch, ga mu mun dawo domin kawo second batch, wanda zai kasance Advance class a kan na farko da muka gabatar* *Ki na son fara sana'a, kin rasa yadda za ki yi? Ko kuma jarinki ne kaɗan kin rasa wace sana'ar za ki yi? To wannan classes ɗin naku ne, ku garzayo ku yi rijista domin kar a yi tafiyar nan babu ku. Daga sana'oin da za a koyar sun haɗa da;* 1. Graphic design 2. Magungunan mata 3. Sabaya 4. Turaren wuta 5. Fara 6. Candies 7. Skin care products 8. Importation 9. Snacks 10. Yoghurt 11. Oil perfumes 12. Bead work 13. Hair cream/oil 14. Dabarun kiwon kaji 15. Huluna 16. Spice's 17. Dabarun sana'ar kayan kitchen 18. Noma a zamanance 19. Dabarun kasuwanci 20. Dabarun kiwon kifi 21. Garin ɗan wake
Dama ƙarin wasu, ga masu buƙatar sanin yadda tsarin yake kai tsaye su tuntuɓi wannan lambobin. 08081012143 08069611181 07037977211