
Post
SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 14
.....the leg that was cut by the snake started to swell. He pulled out a pair of scissors and cut the place, he protected her with his eyes, and when she looked at his eyes that were white, she was afraid. He knelt down and placed his mouth on the exact spot. She felt as if he was pushing something in her body. She was crying so hard that her body was shaking, as if she was going to faint. He lifted up and opened the bottle that he had spilled the medicine in, and poured what was in his mouth. There is no beauty to be seen. He looked at her and said, "Be patient, if I drink, by God, the snake will bring its head, you will see the punishment I will give him. He spoke while wiping the sweat that had dried on her forehead. He took out the hiram that he was covering his face with, tore a part of the body, grabbed the upper leg where it had bitten and tied it. The way she was sitting. She was given a piece of cake in her hand, and she looked up at her friends who were in custody. "Their food is on the way, if you don't eat yours, the medicine you take can destroy you."
SARA DA SASSAƘA YOTA 002 AYSHERCOOL
Page 14
Cikin sauri Sabi'u ya saki Rahama ya tashi, saboda jin ƙarar babur a bayansu, ba tare da jin sautin tahowarsa ba.
Ya sauka daga kan babur ɗin, sauran 'yan bindigar suka nufo shi, su na yi masa barka da zuwa, ya miƙa musu bindigarsa suka karɓa. Ya ƙarasa inda Ramata ke yashe kamar abin banza, ya saka hannunsa ya ɗago ta zaune. Ya kalli leɓenta ya bushe, jikinta sanyi ƙalau. Sai motsa hannunta take yi, tana ƙoƙarin kare jikinta. Ya dubi ɗaya daga wanda suka zo tare, ya ce "Ba ni abin nan" Ya ƙaraso ya miƙa masa wata 'yar ƙaramar kwalba. Ya kwance ta ya ɗaga bakin Rahama ya zuba mata abin da yake cikin kwalbar. Mintuna kaɗan ya ɗaga ta zaune, aikuwa ta fara sheƙo amai babu ƙaƙƙautawa, ta galabaita sosai, sai da ya fuskanci ta gama sannan ya ja ta ya jinginar da ita a jikin bishiya. Sai haki take yi tana sauke numfashi. "Kina jikar makiyaya, ya aka yi ba ki sha maganin dafin maciji ba?" Ta yi shiru tana bin sa da kallo a galabaice. Ya kalli inda ƙafar da macijin ya sare ta, ya fara kumbura. Ya ciro wata aska ya tsaga gurin, ya tsare ta da idanunsa, da idan ta kalli idon nan nasa da ya sha farin kwalli sai tsoro ya kama ta. Ya durƙusa ya kafa bakinsa a dai-dai gurin. Ji ta yi tamkar yana fizgar wani abu a cikin jikinta. Wani irin wahalallen kuka ta din ga yi jikinta na karkarwa, tamkar za ta shiɗe. Ya ɗago ya buɗe kwalbar da ya bata magani a ciki, ya zuba abin da yake cikin bakinsa. Abun baƙi ƙirin babu kyawun gani. Ya dube ta ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah macijin zai kawo kansa, za ki ga hukuncin da zan yanke masa. Ya yi maganar yana goge mata gumin da ya tsatstsafo a goshinta. Ya ciro hiramin da yake rufe fuskarsa da shi, ya yagi wani sashi a jiki, ya kama ƙafar saman gurin da ya cije ta ya ɗaure.
Ya sa aka kawo masa ruwa, ya ba ta ta sha, ta rage tana daga zaune ta yi alwala, ta yi sallar asuba a haka a yadda take zaune.
Yana tsugune a gefenta, ta idar aka ba ta waina a cikin leda fal da ƙuli-ƙuli, ta riƙe wainar a hannunta, ta ɗaga kai tana kallon sauran 'yan uwanta da suke tsare tare, sannan ta kalli Sadauki.
"Nasu abincin yana hanya, idan ba ki ci naki ba, maganin da ki ka sha zai iya halaka ki"
Hannunta na rawa, ta gutsiri wainar, sai dai ta riƙe a hannunta, tana sinne kai ta kasa ci. Ya yi murmushi ya matsa gefe ya kawar da kansa daga kallonta, sannu a hankali ta fara kai wa bakinta tana ci, tamkar tana cin magani.
Sadauki ya ɗan waiwaya ya ce "Sabi'u zo ka karɓi kwalbar nan, ka ajiye mini zan yi aikinta na kama macijin nan" Ya yi maganar yana miƙa masa kwalbar da hannu ɗaya, hannunsa ɗaya kuma ya zura a cikin Aljihunsa. Sabi'u ya ƙaraso ya kawo hannu zai karɓi kwalbar. Sadauki ya janye kwalbar, Sabi'u ya sake ƙarasawa zai karɓa, amma Sadauki ya fito da ɗaya hannun nasa riƙe da bindiga ƙirar pistol ya harbe shi har lahira. A take da yawa daga cikin ɗaliban suka saka ihu cike da tsoro. Jikin Rahama kuma ya hau rawa ta kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi saboda jinin sai dai ya ɓata mata fuska. Idanunta da suka yo waje suka ƙara bayyanar da tashin hankalin da ta shiga. Sadauki ya ɗan tsura mata ido, ganin yadda numfashinta ke kai komo a ƙirjinta. Ya sake ciro hiraminsa ya kamo fuskarta, ya fara goge mata jinin yana faɗin "Yi haƙuri na tsorata ki ko? Ya aka yi jinin makiyaya ta kasance cikin matsorata ne? Mu fa ba matsarota bane ba a sammunda tsoro ba" Ya yi maganar yana ci gaba da goge mata fuskarta. Ya sakar mata murmushi ya ce "Kar ki yi mini mummunar fahimta fa, ni mutumin kirki ne" Ita kuwa ba ma ta gama iya tantance a wani yanayin take ciki ba, balle ta fahimci me yake faɗa. Sai da ya gama goge mata jinin sannan ya miƙe tsaye, ya murtuke fuska tamkar bai taɓa dariya ba ya ce "Wannan shi ne abin da zai biyo bayan duk wani wanda ya yi yinƙurin aikata halin ɗan taure a tsakanin yaran nan. Kai Gulafa, ku je ku binne shi, kai kuma je ku ƙarasa aikin da na saka ku ku yi mini, saboda zan din ga zagayowa ba tare da na sanar muku ba. Ya kalli sauran 'yan matan ya ce "Ku kuma ku kwantar da hankalinku, na gaya muku babu wanda za mu cutar" Ya saka hannunsa ya cire babbar rigar yadin da take jikinsa, ya durƙusa ya saka wa Rahama da har a lokacin jikinta bai daina rawa ba. Ba ta iya motsawa ba har ya gama saka mata, shi ma kuma bai sake ce mata komai ba. Ya nufi baburinsa ya hau, suka miƙa masa bindigarsa ya karɓa ya tafi.
*****
Laila ce a zaune, ta duƙufa a kan wayarta, hannunta ɗaya riƙe da biro da takarda tana rubuce-rubuce. Mama ta shigo ɗakin ta tsaya a kanta ta dube ta cike da takaici ta ce "Wai Laila uban me ki ke yi ne a kan wayar nan?"
Laila ta yi miƙa ta ce "Mama aiki nake yi"
"Aikin banza ba, awa ashirin da huɗu, kullum idonki a kan waya, ina jin wani likita na magana a radio, ya ce ba da jimawa ba idanun matasan yanzu duk zai mutu, saboda azabar kallon waya."
Laila ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Bincike nake yi ne, neman kuɗi nake yi da wayar nan Mama, dan Allah ki bani dubu ɗaya zan je wata unguwa ne"
Mama ta dube ta sheƙeƙe ta ce "Shegiyar wayar taki da ki ke wuni a kanta, ki ke neman kuɗin da ita, ba ta kawo miki dubu ɗayar da zaki yi yawon ba"
Laila ta yi murmushi ta ce "Hajiya Mama kenan, bari na yi wanka na je Cafe ɗin su Saddam, na san ko ya gama yi mini gori zai bani"
"Tsaya tukuna ma ina za ki je?"
Laila ta hau murmushi ta ce "Ba daɗewa zan yi ba, zuwa zan yi na dawo"
"Tambayarki na yi, ina za ki je?"
Laila ta ci gaba da murmushi ta ce "Mamansy, kin san ba zan je inda zan ɗaukko miki magana ba"
"To wallahi idan ba ki gaya mini ba, ba za ki fita ba"
Ta ɗan sunkuyar da kanta, jiki a sanyaye ta ce "Mama zan koma batun filinmu ne, ina ci gaba da bibiya, idan ba za su yi mana adalci ba, akwai yiwuwar na wallafa rubutu a kan lamarin"
Mama ta nemi guri ta zauna ta dube ta ta ce "Laila, na san an cutar da ku. Wannan filin shi ne abin da muka tsira da shi da wannan gidan, tun da an yi ƙarfa-ƙarfa a kan filin nan ki yi haƙuri kawai. Tun da mun tsira da gidan nan shikenan. Kin ga ɗan uwanki da na ba shi baki ya haƙura, to kema ki bar wa Allah kawai"
Laila ta sunkuyar da kanta, sannan ta ɗago kanta idonta duk hawaye ta ce "Mama shikaɗai fa muka tsira da shi, kina gani hakkin babanmu abokansa suka ci abin da suka ga dama, suka bamu wanda suka ga dama. Kuma filin da aka saya mana tsawon lokaci, mu na saka ran mu na da kadara mai tsada a ajiye, rana tsaka gwamnati ta ƙwace an bamu diyyar da bata kai rabin kuɗin kadararmu ba. Kuma an saya mana wani filin shi ma wasu su mallake su ce nasu ne, mu zuba ido"
"Laila ya za mu yi tun da sun fi ƙarfinmu? Da aka ƙwace filayen mun daina rayuwa ne? Muka rasa mahaifinku ma balle wani fili, mu bar wa Allah kawai. Albarkar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da Alqur'ani filaye idan mu na raye sai dai ku bawa wani kyautar su ma, mu bar wa Allah kawai" Ba haka Laila ta so ba, amma gudun ɗaga wa Mama hankali, ya sanya ta jinjina kai ta nuna mata cewar komai ya wuce.
*****
Ɓangaren Alina, abubuwa sun ƙara rikice mata, yadda ta kai ba ta iya sarrafa kanta sosai. Hankalin Nadiya ya tashi sosai, dan Alina ta kwanta rashin lafiya, saboda damuwa wannan ciwon kan ya tayar mata. Ga shi a duk lokacin da ta yi yinƙurin gaya wa Nadiya abin da ya faru, sai ta ji ba za ta iya ba, gani take yi kowa sai ya zarge ta da laifin faruwar komai dalilinta, dan babu irin kashedi da jan kunnen da Yaya bai yi mata ba a kan Mamman. Tun safe Alina ke kallon Nadiya daga kwance, tana harhaɗa musu kayansu a bagco. Ta dubi Alina cikin kulawa ta ce "Sannu ƙanwar Yaya"
Alina ta jinjina kai ta ce "Anty ina zamu ne, na ga kina haɗa kaya?"
"Tafiya zamu yi" Ta bata amsa.
"Ina za mu je?"
"Garin nan zamu bari"
Cikin rashin fahimta Alina ta ce "Mu je ina? Idan yayan ya dawo kuma fa?"
Nadiya ta ce "Alina kin fiye tambaya, ki zuba ido za ki gani, ci gaba da zamanmu a nan ba shi da wani amfani, Yaya kuma duk inda muka shiga, in dai ya dawo zai neme mu"
Alina ta sake cewa "Ta yaya zai san ina muka tafi, ko kin san inda yake ne?"
"Alina, ki kwanta ki yi shiru ki samu bacci, wannan ciwon kan ya sake ki, idan abin ya ci tura kin san sai mun je Asibiti abin da ba kya so" Alina ta jinjina mata kai kawai ta lumshe idanunta, sai dai ƙasan zuciyarta tana ci gaba da mamakin ina za su bar garin nan su tafi, su da ba su da kowa.
***** Tun da sadauki ya tafi, Rahama a cikin fargaba take, idan ta kalli babbar rigar da ya saka mata, ga shi ya suturta nata jikinta da take ta ɓoyewa, amma a mugun tsorace take. Ga rigar sai ƙamshin turare take yi. Da ta tuna yadda ya harbe Sabi'u sai ta razana kamar hankalinta zai gushe. Sai dai ɓangaren ƙafarta da maciji ya sare ta, a hankali ta saki ta daina yi mata wannan mugun zugin da take yi mata. Daga nesa kaɗan suka din ga jin ƙwale-ƙwale, sai dai ba su san me ake yi ba. Ko a tsakaninsu ɗaliban, ba a bari su yi hira a tsakaninsu saboda gudun kar su ƙulla wani abu a tsakaninsu.
A hankali Rahama ta takure jikinta, saboda wani irin azababben sanyi da yake ratsa ta, bacci ɓarawo ya fara ɗibarta. Sannu a hankali take ratsawa cikin ƙauyen Yelwa, kai tsaye ta tunkari rigarsu, ta shiga cikin gidansu, ta tarar da Baffa a zaune yana addu'a. Ta ƙarasa da gudu ta je gabansa ta zauna tana yi masa magana, sai dai ta ga alamun baya ganinta. Sadauki ta ga ya shigo gidan nasu, tare da su Saleh a bayansa, da wasu daga matasan garin nasu, riƙe da miyagun makamai. Kafin ta farga kawai Sadauki ya harbe Baffa, jininsa ya watso a fuskarta kamar yadda ya yi wa Sabi'u. Wani irin ihu Rahama ta yi tana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"', Wayyo Allahna Baffa"
Sadauki ne ya riƙe ta da hannayensa biyu, ya mayar da ita ya zaunar da ita. Ƙara rikicewa ta yi cikin tashin hankali ta fashe da matsanancin kuka tana girgiza masa kai "Dan Allah kar ka kashe shi, kar ka kashe Baffana dan Allah bai yi maka komai ba"
"Shhh. Ai kin baro mafarkin, kalli ba gaskiya ba ne" Ya yi maganar cikin sigar rarrashi, yana haske fuskarta da fitila.
Ya sake girgiza mata kai, yana yi mata nuni da ta kwantar da hankalinta.
Ta kalli gurin duhu ya yi sosai, alamar dare ya tsala, ga wuta an kunna a tsakanin su. Sai da ya tabattar da ta ɗan nustu, sannan ya saki hannunta, ya janyo wata ledar Viva, ya buɗe ya haska mata cikin ledar da fitila. Maciji ne a ciki baƙi ƙirin da shi, yana buɗe shi ya fasa kai, aikuwa ta zabura ta ja da baya.
Ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Shi ne ya sare ki, na yi amfani da dafinsa na nemo miki shi, ya ki ke son a kashe shi?" Ta girgiza masa kai.
"Sai fa an kashe shi, ya ki ke so a yi masa?" Ta takure jikinta tana kallon ledar cikin tsoro.
Kawai ya saka hannu ya damƙo kan macijin, ya jefa shi cikin wutar da take ci a gurin. Za ta yi ihu ya saka mata kan bindiga a ƙafarta, da sauri ta saka hannu ta toshe bakinta, ta ƙarfin tsiya ta haɗiye ihun. Zuciyarta ta karye ganin yadda macijin yake ta wutsul-wutsul a cikin wuta yana miƙewa yana neman hanyar guduwa, yana fitar da wani sauti mai ban tausayi. Ya waiwaya ya kalli wutar, sannan ya kalli yadda take kallon wutar hawaye na zuba daga idanunta, ya ciro kwalbar da ya zuƙe dafin macijin daga jikinta ya jefa a cikin wutar. Su na haɗa ido, ta sunkuyar da kai, tana jinjina girman rashin imani, da Allah ya dasa a cikin zuciyar Sadauki.
Ya miƙe ya tattaka ya je ya ɗaukko wani abu, ya zo kanta ya tsaya ya buɗe shi,ƙaton bargo ne mai kaurin gaske ya lulluɓa mata a jikinta. Ya miƙe ya yi gaba abin sa.
*****
YELWA
Baffa ya yi iya yin sa, gurin yin tawakalli, da miƙa lamuransa ga Allah, da ƙoƙarin danne zuciyarsa a kan abin da ya faru. Sai dai a ƙarƙashin zuciyar tasa wuta ke ci, da take ƙona shi shikaɗai ba tare da kowa ya sani ba. Cikin ƙarfin hali, yana zaune a ƙofar gida da radionsa da saurarenta ya zame masa jiki. Can ya hango Bukar na nufo inda yake tare da Hanne, hakan ya sanya shi tsayawa cike da tsoro da fatan ba wani laifin ya aikata ba. Cikin girmamawa Hanne da Bukar suka gaishe shi, ya amsa yana kallonsu da jiran jin abin da yake tafe da su.
"Baba shin da gaske ne labarin da muka samu, na cewa an sace su Ramata a makaranta?"
Baffa ya numfasa cikin ƙarfin hali ya ce "Haka ne Hannatu, sai dai ku taya mu da addu'a"
Bukar ya ce "Amma Baffa, Babu wani labari a kan inda aka kai su, ko labarin ƙoƙarin nemo su?"
Duk da Baba idan ya kalli su Bukar, yana fama masa mikin da ke zuciyarsa, na abin da ahalinsu, suka yi wa zuriyarsa, sai dai ya danne, duba da yadda suka zo yi masa jajen abin da ya faru da 'ya ɗaya da ta rage masa.
Ya ce "To, ko ma ana ƙoƙarin nemo sun, ka ga ni ina nan a cikin ƙauye, babu lallai na san halin da ake ciki. Amma na bayar da lambata ina tuntuɓar malamansu".
Jiki a sanyaye Bukar ya ce "Baffa ka yi haƙuri, in sha Allah Ramata za ta kuɓuta cikin aminci da yardar Allah"
Baffa ya ce "To, Allah ya sa"
Hanne ma cikin sanyin jiki ta ce "Za mu ci gaba da addu'a, da yardar Allah Rahama za ta kuɓuta cikin aminci"
Baffa ya ce "Ina fatan hakan, kuma yakamata ku koma haka kar a zargi wani abu, ko mu yi laifi daga ni har ku"
Suka yi wa Baffa sallama suka tashi suka tafi.
****
Kwana biyu Mama tana saka wa Laila ido, tare da sake rarrashinta, a kan batun filayensu da aka ƙwace, dan tana yawan mita a kan lamarin.
Ranar Talata da yamma, Mama ta fito daga ɗakinta, tana yi wa Saddam mitar, Laila tun safe ta fita amma haryanzu ba ta dawo ba.
Ya ce "To ki kira lambar wayarta mana"
"Na kira bata shiga, Ubangiji Allah ya shirya mini wannan yarinya, ni duk godiyata ga Allah da ya zamana ba wani abin ashshan take aikatawa ba, amma 'ya mace dole sai da saka ido ai"
Saddam ya ce "Mhmm, In dai Laila ce, tana can neman abin wallafawa a shafukanta ne, za ta dawo na san, iyaka idan ta dawo ki zane ta wallahi"
"Ba zan dake ta ɗin ba, ziga zigi" Mama ta yi maganar tana hararsa.
Ya ce "Daga bayar da shawara? Allah ya baki haƙuri ai kun fi kusa"
Sai dai abu kamar wasa, har magariba babu Laila babu dalilinta, wanda hakan ne ya ƙara ɗaga wa Mama hankali, ba ita ba har da Saddam, babu shiri ya fita yawon neman ta. Ga shi ita ba ƙawaye ne da ita ba, babbar ƙawarta Murja su na gama makarantar Sakandire aka yi mata aure, maƙwabciyarsu ce, da aka yi mata aure sai ta ci gaba da abotar da Bala, wanda yake Yayan Murja, wanda shi ne ya sanya mata sha'awar harkar sarrafa waya da kuma aikin jarida.
Laila ce rufe a cikin cell, sai rarraba ido take yi, ta kalli yadda duhun magariba ya fara yi. Ta jijjiga ƙarfe cell ɗin ta ce "Yallaɓai ka yi wa Allah da ma'aikinsa ku sake ni na tafi, babata dattijuwa ce ba ta da cikakkiyar lafiya, hankalinta yana nan a tashe na sani. Wannan kamun da ku ka yi mini kun take mini hakkina fa"
Babu wanda ya kula ta, daga cikin office wani ɗan sanda ne a zaune, sanye da uniform ya ɗaga wayarsa ya daddana ya saka a kunnensa. "Allah ya taimaki honourable"
"Yauwwa ya aikin?"
"Alhamdillah, game da yarinyar nan ne, haryanzu ba ka ce komai ba"
Honourable ya ce "Eh ina sane, ku ajiye mini ita sai na waiwaye ta. Ba dai ba ta da kunya da mutunci ba, za ta gane ba ta da wayo ku ajiye ta sai na waiwaye ta."
Ɗan sandan ya ce "Na fahimce ka sir, amma ka san yarinyar nan mutane sun fara gane ta a shafukan sada zumunta, idan abu ya bayyana ka saka an tsare ta, kar abu ya zama surtu"
"Ba na san aikinka ba ne?"
"Sorry sir"
"Ka ajiye ta sai na waiwaye ta, zan saka maka kuɗin mai"
Gidan su Laila kuwa kwanan tsaye Mama ta yi, saboda rashin Laila a gida. Tuni Saddam da Bala suka kai ɓatan Laila gurin jami'an tsaro.
Da sassafe Bala ya zo musu da labarin tana gurin 'yan sanda, dan haka Saddam ya zo su je.
Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Yanzu Laila ce ta kwana a hannun 'yan sanda me ta aikata har haka?. Ba zan iya zama a gida ba, mu je tare kawai"
Saddam ya dubi Mama ya ce "Dan Allah ki yi haƙuri ki zauna a gida, wallahi ko mun je babu abin da za ki yi, ki bari mu je mu gano tukuna"
"In kwana yarinyar ba ta gida, ta kwana a hannun 'yan sanda ka ce mini ba zan bi ku ba"
Bala ya ce "Saddam ina ga ka bari kawai mu je tare, hankalinta sai ya fi kwanciya"
Ba dan Saddam ya so ba, ya ƙyale Mama ta yafo mayafinta suka tafi.
*****
Alina na ta son sake tambayar Nadiya, inda za su tafi idan sun bar garin, amma ta fasa ganin yadda Nadiya ta nuna mata ba ta son tambayoyin. Sai da Nadiya ta dangana da kai Alina Asibiti, aka bata magunguna da allurai, suka taho gida. Da kyar Alina ta yi sallar isha'i ta kwanta, saboda baccin da take ji, a sakamakon magungunan da ta sha.
Baccinta ya yi nisa, ta din ga jin motsi da ɓuruntu a cikin gidan, a hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idonta. Gani ta yi an haske ta da wata irin fitila mai matuƙar haske, sai ta kasa tantance mafarki ne ko gaskiya.
Muryar Nadiya ta ji tana faɗin "Kar ku taɓa yarinyar nan, wallahi ba za ku iya ganin bayan Ismail ba. Babu ruwanku da ita. Ba dai shi ka ke son ka kama ba, ka kama shi, amma kamun da ka yi masa shi ne kuskure mafi girma da za ka aikata a rayuwarka".
"Shut up, da harbina za ki yi kenan?"
"Dole na kare kaina, abin da baka sani ba, tuntuni Isma'il ya san wane ne kai. Kar ka yi abu da ka, baka san abubuwa da yawa ba, zaka aikata mummunan kuskure"
A hankali Alina ta buɗe idanunta, ta yinƙura, ta miƙe tsaye a razane da ƙarfinta, tana son ganin suwaye suke wannan jayayyar da Nadiya, ammaba ta kai ga hakan ba, ta ji an shaƙa mata wani hankici ta baya, take ta ji ɗiff ta daina gane komai. Duhu ya ƙara mamaye ganinta.
1k ne a telegram. Ayshercool 08081012143
*Jama'a Albishirinku, mun sake shirya tsaf domin kawo muku advance class, na koyar da sana'oi da muka yi firts batch, ga mu mun dawo domin kawo second batch, wanda zai kasance Advance class a kan na farko da muka gabatar* *Ki na son fara sana'a, kin rasa yadda za ki yi? Ko kuma jarinki ne kaɗan kin rasa wace sana'ar za ki yi? To wannan classes ɗin naku ne, ku garzayo ku yi rijista domin kar a yi tafiyar nan babu ku. Daga sana'oin da za a koyar sun haɗa da;* 1. Graphic design 2. Magungunan mata 3. Sabaya 4. Turaren wuta 5. Fara 6. Candies 7. Skin care products 8. Importation 9. Snacks 10. Yoghurt 11. Oil perfumes 12. Bead work 13. Hair cream/oil 14. Dabarun kiwon kaji 15. Huluna 16. Spice's 17. Dabarun sana'ar kayan kitchen 18. Noma a zamanance 19. Dabarun kasuwanci
Dama ƙarin wasu, ga masu buƙatar sanin yadda tsarin yake kai tsaye su tuntuɓi wannan lambobin. 08081012143 08069611181 07037977211