Kenza eBookz
Cover art for SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 13

Post

SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 13

.....Amar told her the truth of what happened, but like the one who was kept secret, she couldn't tell her anything. That's how she went to Islam, she was walking and dragging her feet and her body calmly. She heard his voice "Girls" as if she ignored it and left and stopped. He ended by saying "Alhamdillah, you've gone back to school? That's the right thing to do to stay at home. Worry will continue to make you sad." She raised her eyes and stared at him, swallowing something bitter, her eyes filled with tears. "Alright, what else?" She was silent and allowed the tears to flow from her eyes. He calmly said, "Listen, girls, be patient, be patient and continue praying that God will return in good health and safety." "When? When will you bring it back to me?" He stared at her. "Tell me when you will bring him back? I saw you, I saw everything, but I couldn't tell anyone. I kept looking at you to see if you would bring him back, but you refused. I know you and Yaya don't get along, but what you did was harsh" "What do you mean?" "I saw you, I saw you, in front of my eyes, you tied him up with others and took him away. That night I came back from the night school. I walked around and s

Standalone post3,868 words

More pages available at Arewapen.

SARA DA SASSAƘA... AYSHERCOOL YOTA/002 BRIGHT PENS

13 Murmushi ya yi ganin yadda alamun mamaki suka bayyana a fuskarta baki ɗaya, a lokaci ɗaya.

*****

Fuskar Ummi ɗauke da matsananciyar damuwa take kallon Ruƙayya, tana kwance a gadon Asibiti sai dai ba ta magana. Sai dai Likitoci sun tabattar wa su Ummi cewar, tsoro ne kawai da razani suke damunta. Haka suka karɓo ta suka tafi da ita, da niyyar su canza mata Asibiti, zuwa na kusa da su can cikin gari. Babu yadda Ammar bai yi ba, ya samu release ya je gida, ya ji halin da ake ciki game da Ruƙayya amma aka hana shi, sai dai su yi waya ya ji ya jikinta, saboda su na daji ma a lokacin.

*****

Nadiya ta takura wa Alina a kan lallai sai ta koma makaranta, dan idan Yaya ya dawo, ya tarara ta jingine zuwa makaranta, sai ya yi mata faɗa.

Ko da ta shirya ta je makarantar ma, jikinta duk a sanyaye yake, malamai da ɗalibai su na ta yi mata jajen ɓatan yayanta. Hafsa ta yi ta rarrashinta tana bata haƙuri, ji ta yi kamar ta gaya mata haƙiƙanin abin da ya faru, amma tamkar wadda aka asirce ta kasa furta mata komai.

Haka ta je Islamiyya ma, tana tafe tana jan ƙafarta jikinta a sanyaye. Ta jiyo muryarsa "'yan mata" Kamar ta yi banza ta tafi sai kuma ta tsaya cak. Ya ƙaraso yana faɗin "Alhamdillah, kin koma makaranta kenan? Ai hakan ne ya dace zama a gidan damuwa zai ci gaba da saka ki"

Ta ɗago idanunta ta zuba masa, tare da haɗiye wani abu mai ɗaci, idanunta ya cika da hawaye.

"Lafiya mene ne kuma?" Ta yi shiru tana bawa hawayen idanunta damar zubowa.

Jiki a sanyaye ya ce "Ki na ji 'yan mata, ki yi haƙuri, ki yi haƙuri ki ci gaba da addu'a in sha Allah zai dawo cikin ƙoshin lafiya da aminci"

"Yaushe? Zuwa yaushe zaka dawo mini da shi?"

Ya yi saroro yana kallonta. "Ka gaya mini yaushe za ka dawo da shi? Na ganka fa, na ga komai, amma na kasa gayawa kowa, ina ta kallonka in ga ko za ka dawo da shi, amma ka ƙi. Na san kai da Yaya ba kwa jituwa amma abin da ka yi ya yi tsauri"

"Me ki ke nufi?"

"Na ganka, na gani, a kan idona ka ɗaure shi kai da wasu ku ka tafi da shi Da daddare ranar na dawo daga makarantar dare. Ta can baya na zagayo ina tsaye a bakin lungun can, na ganka. Dan Allah Mamman dan darajar iyayenka ka dawo mini da yayana dan Allah" Ya waiwaya layin ya ga babu kowa, ya sassauta murya ya ce "Ni fa ban gane me ki ke nufi ba"

"Ka sani wallahi ka sani, kai ka ɗaure Yaya da igiya ku ka tafi da shi" Ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba ni ba ne ba, dan ranar da ki ke magana bana garin nan, na je gurin Inna"

"Kai fa ma'abocin karanta Alqur'ani ne, bai kamata ka yi ƙarya ba, dan Allah dan Annabi ka dawo mini da shi"

"Amm ina ga ki je gida kawai, wataƙila damuwa ce ta yi miki yawa ki kr irin wannan tunanin, amma gaskiya ba ni ki ka gani ba." Ya wuce ta ya bar ta a tsaye a gurin.

Sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta ƙarasa gida, ko da ta je gidan ta tarar Nadiya ta fita, dan haka ta samu cikakkiyar damar yin kuka.

*****

"Haƙiƙa mu na yabawa yadda mr. President yake ta ƙoƙarin ganin yaran nan sun kuɓuta, mun san ayyuka sun yi maka yawa, kuma duk wani abu da ka ke yi, domin al'immarka ka ke yin su. Amma Allah wadai da fadarka ta yi da sace ɗalibai, ta bakin mai magana da yawunka ta yi kaɗan. Ko ba ka je da kanka ba, ka rarrashi al'ummarka mussaman iyayen waɗanda aka sace ɗin nan, za su ji daɗi, komai ƙanƙantar abin da zaka gaya musu kuwa za su ji daɗi domin kai uba ne ga kowa. Please ka ce wani abu ko babu yawa, za mu ji daɗi"

A hankali ya ja ajiyar zuciya, bayan kammala kallon videon da ta wallafa, gaba ɗaya ƙasar ta ruɗe, ko ta ina bring back our girls ake posting. Ji ya yi ya samu ƙwarin gwiwa da kalamanta, ko da maganarsa ba za ta yi tasiri ba, akwai buƙatar ya yi magana da bakinsa, ba a ji iya ta bakin mai magana da yawunsa ba.

Halilu ne ya shigo ofishin, hannunsa riƙe da takardu. Cikin matuƙar girmamawa, suka gaisa. Bayan an yi masa iznin zama, ya dubi Kankiya ya ce "Mr. President, tafiyarka taron kasashe masu arzikin man fetur fa jibi ne, ina yi maka tuni duk da na ga ka yi busy da yawa."

"Na soke tafiyar"

Da sauri Halilu ya dube shi ya ce "Mr. President ka soke kuma?"

"Eh, hankalina na kan batun yaran nan, ba zan iya komai ba"

"Haka ne, amma akwai buƙatar ko wakilci a naɗa ka tura"

"Babu buƙata, mutanen nan hawan ƙawara suke yi mana kawai, wannan shekarar ba zamu halarci taron ba, hanyoyi da yarjejeniyoyin da za su durƙusar da mu, su azurta kansu kawai suke yi"

"Amma Your excellency, ƙin halartar zaman, ya saɓa da yarjejeniyar da tsohuwar gwamnati ta saka hannu, kafin karɓar bashin biliyoyin da aka yi a shekarun baya, za su iya hukunta mu, ta hanyar janye mana wani tallafin, ko kuma sanya mana takunkumin da zai durƙusar da tattalin arzikinmu ma baki ɗaya"

Ya ɗan yi shiru yana matsa yatunsa, ya dubi Halilu ya ce "Ina buƙatar zama da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa. Ina buƙatar bincikar yadda aka gudanar da wannan maƙudan kuɗaɗen, da ainihin kwafin yarjejeniyar basussukan da aka karɓa. Dan yanzu haka ma, ƙasar ba za ta tafi ba sai an ciyo wani bashin, kuɗaɗen da suke asusun ƙasar nan, ko jihohi goma ba zai riƙe ba"

Halilu ya risuna ya ce "In sha Allah, za a yi yadda ka ce, amma mr. President ka sake nazari a kan batun taron nan" Kai kawai ya jinjina. Bayan fitar Halilu ya sake ɗaukko wayarsa yana dubawa. Comments ne na rashin kyautawa, da cin zarafi aka cika Laila da shi. Cin mutumci har da iyayenta, cin mutunci mai matuƙar muni ga ita da iyayenta, ban da ƙazafi da kushe mata halitta a ƙoƙarinta na bawa gwamnatinsa kariya.

A hankali ya dafe goshinsa yana ɗan murzawa a hankali. Yana tunanin meya kamata ya yi.

*****

YELWA Duk da dakiya da juriya irin ta Baffan Rahama, sai da ya yi wata irin muguwar rama, dan ko lokacin da aka kashe masa ɗa, bai shiga mummunan tashin hankali kamar yanzu ba. Ko Abinci baya iya ci, baya iya bacci, 'yar kasuwar da yake ɗan zuwa ma ya daina saboda matsananciyar damuwa da kuma tashin hankali. Tashin hankali da damuwa da yake ciki, bai hana jama'ar garin zunɗensa ba, har da masu yi masa dariya da Allah ya ƙara.

Hanne na zaune a ɗakinta, tana saƙar mafici, Bukar ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi. Ta ɗaga kai ta bi shi da kallo tana mamakin me ya faru.

"Hanne, kin san me yake faruwa kuwa?"

Ta girgiza kai tana tsare shi da ido, tana jiran ƙarin bayani.

"Su Ramata aka sace s makarantar boko"

"Kamar ya ya aka sace su? Ta ya za a sace mutum? Ko dai ba ka ji dai-dai ba ne?"

Bukar ya tsuke fuska ya ce "Zan yi miki ƙarya ne? Da gaske nake an sace su Ramata a makaranta, ba a ma san inda suke ba"

Hanne ta dafe ƙirji tana nanata "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan wane irin abu ne? Allah sarki Baban Ramata, anya akwai wanda Allah ya taɓa jarabta a garin nan kamar sa? Amma ni ta yaya za a ce an sace mutum"

Cikin damuwa Bukar ya ce "To nima dai haka na ji"

"Gaskiya zan je gidan nasu, zan sake tambayar Baffan"

"A'a babu ruwana, kin san a ƙarƙashin takunkumi ki ke, kuma a gan ki a gidansu Ramata?"

Hanne da idanunta suka cika da hawaye ta ce "Wallahi ko za su kashe ni sai na je, har Duniya ta naɗe Ramata da ahalinsu su na bin mu gagarumin bashi, ba zan iya jurewa ba sai na je"

*****

Sosai ɗaya daga cikin masu tsaron su Rahama, yake ƙoƙarin kai musu farmaki. Da ƙoƙarin fito da zalamarsa a fili a kansu. Duk dare haka ake ɗaure musu ƙafafuwa, domin kar ma a samu mai yinƙurin guduwa. Idanun Rahama biyu, tana rarraba su a cikin duhu, ta ji wani abu mai sanyi, yana bin ƙafarta. Ta ɗan motsa ƙafarta a hankali, ta ji abin ya daina bin ta. Wata irin ƙara ta saki, bayan jin wani irin raɗaɗi ya ratsa ƙwaurinta zuwa cikin ƙwaƙwalwarta ta gigice. Cikin hanzari masu tsaronsu, suka yo kanta su na haskata da fitila, su na yi mata tsawa. Tuni gumi ya wanke ta, sai dai kafin su yi magana suka hangi wani irin ƙaton baƙin maciji ya bar gurin. Su ka haska ƙafar Rahama, ga shaidar gurin da ya cije ta, jikinta sai wata irin tsuma yake yi. Da yawa daga cikin ɗaliban, har da wanda suka fara bacci, duk su ka zubo mata ido, su na yi mata sannu. Ya yin da tsoro ya shige su, kar ya kuma cizon wani. "Dare ne yanzu babu abin da za mu iya yi, zuwa da safe a sanar da sadauki" cewar ɗaya daga cikinsu.

Babu wanda ya damu ya ba ta wani taimakon gaggawa, kawai suka koma mazauninsu, suka bar ta. Rahama kuwa ji take yi tamkar ranta ne zai bar gangar jikinta, saboda azaba da raɗaɗin da yake ratsa ta. Duk yadda ta so gwada jarumta sai ta kasa, ta fara kuka mai sauti, mai nuna tsantsar azaba da galabaita.

"Ke ki rufe mana baki, ko mu ƙarasa ki" Ya yi mata tsawa. Sai dai ba ma ta fahimtar abin da yake faɗa, wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, jikinta ya din ga karkarwa. Gaba ɗaya hankalin ɗaliban ya tashi wasu suka fara kuka. Dukansu suka fara yi, da kan bindigogi su na taka su da ƙafa, tare da yi musu barazanar harbi, hakan ya tilasta musu jan bakinsu su yi shiru. Jin Rahama ba ta da niyyar yin shiru, ya sanya ɗayan sanya bakin bindiga ya buga mata a kanta, hakan ya sanya ta sulalewa a gurin.

***** Ta na daga kwance a kan gadon Asibiti, duk ta rame ta yi zuru-zuru, cikin damuwa Ummi ta riƙo hannunta ta numfasa ta ce "Ruƙayya, haryanzu jikin naki? Yakamata a sallame mu zuwa gida"

"Tsoro nake ji ne" Ta yi maganar cikin rauni, tana fashewa da kuka.

"You are safe dear, gida zamu koma babu wanda zai biyo ki gida ya cutar da ke, in sha Allah. Ki nutsu ki kwantar da hankalinki ki yi ta addu'a.

"Ummi an tafi da Rahama fa. Kuma harbi suka harbe securitynmu" Ta yi maganar tsoro na bayyana a muryarta.

Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah za ta dawo cikin aminci." Ta yi maganar tana shafa kanta da sigar rarrashi.

*****

Safiyar Lahadi yana zaune a cikin ɗakinsa, yana daddana wayarsa, ya ji alamar motsi a bakin ƙofa, ya ɗan yi shiru yaga alamar motsi a gurin. "Waye a nan?" Ya yi maganar yana kallon ƙofar, tare da zura hannunsa ƙarƙashin pillownsa. Ɗaga labulen ta yi ta shiga, ya yi saroro yana kallonta. "Lafiya kuwa? Me ki ka zo yi ɗakina da sassafiyar nan Alina, sai kin saka a zarge mu?" Ya yi maganar yana ƙarewa kumburarriyar fuskarta ido. Allah ya wadata Alina da manyan idanuwa, sai dai sun rine sun yi jawur kamar an zuba mata kala.

Gani ya yi ta durƙusa a kan ƙafafuwanta, ta haɗa hannayenta biyu, hawaye na rige-rigen zubowa daga idanunta ta ja numfashi da kyar ta ce "Dan girman Allah, dan son da ka ke yi wa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, ka taimaka ka gaya mini ina ka kai mini Yaya? Ka san ba mu da kowa sai Allah sai shi, ban san yadda zan rayu babu shi ba, shi ne komai nawa. Dan Allah ka gaya mini inda yake, na kasa gaya wa kowa abin da ya faru, dan Allah dan Annabi ka dawo mana da shi, ka yi haƙuri dan ma wani laifin ya yi maka ka yafe masa dan Allah"

"Alina" Ya kira sunanta yana tsare ta da ido. Ta ɗaga kanta tana kallonsa.

"Sau nawa zan gaya miki cewar ni ba ni bane ba ki yarda? In ɗauki yayanki na kai shi ina?"

"Wallahi kai ne, na ganka da idanuna, kai ne ba wani ba. Dan Allah Mamman ka taimake ni ka dawo da shi. Ba wanda zan gaya wa na ga abin da ya faru, dan Allah ka taimaka. A duniya bayan Allah da ma'aiki ba ni da kowa sai Yayana ka duba rayuwata da maraicina dan Allah"

Wani irin motsi ya din ga ji a ƙasan zuciyarsa, ƙwaƙwalwarsa ta shiga kai komo, lissafi na neman ƙwace masa, kawai ya tashi ya nufi hanyar fita ya ce "Zo ki tafi, zan fita"

Jiki a sanyaye ta taso, ta sake nufarsa, amma ya murtuke fuska ya ce "Ki fita ki bani guri" Ta girgiza masa kai tana haɗa hannayenta tana kuka, ya kawar da kansa daga kallonta yana nuna mata hanyar fita. Wani irin tsoro ya mamaye ta, ta fita tana jan ƙafarta a hankali tana kuka mai sauti.

*****

Yanayin fuskar Laila ne ɗauke da damuwa, da alama ta sha kuka ne sosai da sosai. Cikin yanayinta na nutsuwa ta fara da sallama, kamar yadda ta saba a dukkanin videos ɗin ta.

"Na ga alamar posting ɗina na ƙarshe a kan mr. President, bai yi wa da yawan mutane daɗi ba. Na ci zagi da ni da iyayena, da masu ce mini karuwa, da masu cewa kuɗi ake ba ni, nake kare gwamanti. Ni babu wanda ya bani kuɗi na kare gwamanati, hasali ma ba a san da zamana ba. Son da nake yi wa shugaban ƙasa ya faro ne, silar sunansa ɗaya mahaifina marigayi DSP Faruk Kankiya. Wanda ya rasa rayuwarsa shekarun baya, bayan artabunsa da 'yan fashi, wanda wani case ne daban. Tun Mr. President yana riƙe muƙami a matakin jiha nake son sa, Saboda son da nake yi wa mahaifina aka kashe shi, kuma 'yan fashin da ya kama aka sake su. Har Mr. President ya zama shugaban ƙasa, ina bibiyar lamarin siyasar sa, ina son shi, yana burge ni, kuma halayensa sun yi kama da mahaifina a wasu ɓangarorin. Ba zan iya daina son sa da ba shi goyon baya ba, son zuciya ɗabi'ar zuciya ce, ba zan iya kushe shi dan na faranta muku ba. A ƙarshe ina baku haƙurin, duk wanda baya son abin da nake yi ya yi haƙuri, ya daina following ɗina, roƙona ɗaya ku daina zagin Abbana dan baya raye. Mr. President kuma har abada bana fatan ko shi ko muƙarabbansa, wani ya maganta mini sisinsa ba na buƙata. Shugaba ne da nake wa kallon Uba, zan yi masa addu'a Allah ya yi riƙo da hannayensa kuma zan ci gaba da goyon bayansa ɗari bisa ɗari".

Mama na wanke-wanke a tsakar gida, ta ji ana ta ƙwala sallama a ƙofar gida.

"Waye?" Ta yi maganar tana kallon hanyar soro.

"Bala ne"

"Shigo" Ta amsa tana ɗauraye plate ɗin hannunta.

Ya shigo yana sake sallama ta amsa masa tana faɗin "Dama kai ne ka maƙale a waje ka na kwaɗa sallama?"

"Wallahi kuwa, mutuniyar fa?"

"Ta je karɓo caji"

Ya zauna a kan tabarmar da ke shimfiɗe, ya ce "Bari na jira ta"

Su na cikin hira, Laila ta dawo, tana ganinsa ta yi murmushi ta ce "Balansy"

Ya ɗan tsuke fuska ya ce "Dalla zauna, mai abin haushi" Ta tsuke fuska ta ce "Me na yi?"

"Videon da ki ka wallafa ɗazu mana, uban wa ya aike ki? Ina ruwanki da wasu masu Comment da zagi, ko dai ki rama zagin ko ki ƙyale su"

Ta sake ɓata fuska ta ce "Ni ba zan zama 'yar balaja'u na din ga zage-zage ba"

Bala ya ce "Ina ruwanki da wani balaja'au in dai za ki samu kuɗaɗenki? Next week akwai yiwuwar dollar ta ƙara tashi, sai ki cire kuɗinki"

Ta yi murmushi ta ce "Kai ka ce ina cikin alkhairi, nawa zan samu?"

"Kusan dubu ɗari da hamsin a ƙiyasi, sai dai yadda ta kaya. Ke ba wannan ba, na ji wai-wai, shugaban ƙasa zai zo garin nan, jajen abin da ya faru na ɓatan matan nan, idan hakan ta tabatta dole ki halarci gurin nan, duk yadda za mu yi, ko hoto ki yi da shi"

Ta waro ido ta ce "Dan Allah? Ni ba sai na yi hoto da shi ba, ko ganinsa kawai na yi"

Mama da ke kitchen ta ce "Bala me ka ke ƙulla mata, ba dai wata tsiyar za ka saka ta kuma aikatawa ba ko? Kun yi ƙulle-ƙullen da sai da ta rasa aikinta, yanzu kana kitsa mata wani abin, ni dai kar ku janyo abin da za a zo har gida a same mu, mu shiga uku ina lallaɓa rayuwata"

Bala ya ce "Hajiya Mama ba za ki gane ba, idan Allah ya ɗaga likkafar Laila, sai kin manta duk wata wahala fa, za ki sarara"

Sadam ya fito daga ɗakinsa, fuskarsa duk alamun bacci ya ce "Maƙaryaci, wace likkafa kullum cikin wahala ku ke, ba kwa samun ko sisi, sai ma kuka da baƙin ciki da take kwasa"

Bala ya ce "To ina ruwanka? Duk ranar da Allah ya sanya ta fashe mana, muka sha kwana zaka sha mamaki. Mu na nan zamu fara wallafa ayyukanmu a jaridarmu mai zaman kanta ta online".

Saddam ya yi tsaki ya ce "Jaridar bugaggu ba"

Bala ya ce "Laila, kar gwiwar ki ta yi sanyi, za mu ba su mamaki da yardar Allah"

Ta yi murmushi ta ce "Ba zan gajiya ba, ba kuma zan sare ba in sha Allah"

***** Can a daji kuwa, Rahama tana yashe a ƙasa, su maharan ba su bari an taɓa ta ba, kuma ba su taɓa ta ba. Ɗaya ne daga cikinsu ya saka ƙafarsa yana taka tata. A hankali ta motsa, ta buɗe idanunta da suka yi mat nauyi, sai dai ta ji kanta kamar ba nata ba. Ga shi ba ta gani sosai sai dishi-dishi. Ya yin da ƙafar da maciji ya sare ta, take jin ta tamkar ba a jikinta take yi ba. Ga jikinta sanyi ƙalau. Ganin ta motsa ya sanya ya durƙusa a kanta yana kallonta. Ta kalle shi da kyar, amma ta kasa motsi. Ya yi wani irin murmushi yana lashe laɓɓansa, ya miƙa hannunsa jikinta yana faɗin "Ashe dai da sauranki ba ki yi mushe ba?" Ya yi maganar yana neman ɗage mata riga a gaban mutane. Tafasar da zuciyarta ke yi, ya bata wani irin ƙwarin gwiwa da niyyar ta hankaɗe shi, amma tana ɗaga hannunta ya koma ya faɗi.

"A'a Halliru, kar ka yi wa yarinyar nan wani abu, kar Sadauki ya zo ya yi mana hauka"

"Shhh" Ya yi maganar yana kallon Salisu, da fuskarsa ke bayyanar da tsoro.

"Ba zai yiwu a bawa kura ajiyar nama a hana ta ɗanɗanawa ba" Ya yi maganar yana ɗago Rahama, yana kallonta cikin murmushi. "Kai ba fa zai yiwu ba, idan na gama sai mu ƙarasa ta, mu ce saran macijin ne ya kashe ta kawai" Ya yi maganar idanunsa na yin ja, jikinsa na rawa, saboda sosai yake ƙarewa jikinta kallo, mussaman da kullum cikin takurewa take.

Ayshercool 08081012143

Mun kusa Kammala free pages. 1k ne a telegram via 0069685771 Aisha Adam stanbic Sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira sai an kammala 1500 za su biya.

AMANA KAYAN MATAN Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto.

Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su..

Gumbar madara Gumbar mata Gumbar aya Gumbar chaku Gumbar dake saukar da ni'ima Gumabar taƙadari Gumbar riɗi Gumbar dabino Gumbar uku alkhairi Kazar amare Jijjiɓen saniya Tabaje Tsimi Rikita mai gida Jigidar tada sha'awa Ruwan boom ruwan daɗi kenan Ɗan matse Karya gado Maganin sanyi Zumar ƙarin ni'ima Zumar rage ƙiba Zumar ƙarin ƙiba Zumar riɗi Mai zamani Emergency powder Tarhama Kafi budurwa Sabon budurci Alfijir Gamzaki Garin dahuwar nama Sabaya Miskin ɗahara Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina.

*ALBISHIR ALBISHIR ALBISHIR*

*Jama'a Albishirinku, mun sake shirya tsaf domin kawo muku advance class, na koyar da sana'oi da muka yi firts batch, ga mu mun dawo domin kawo second batch, wanda zai kasance Advance class a kan na farko da muka gabatar* *Ki na son fara sana'a, kin rasa yadda za ki yi? Ko kuma jarinki ne kaɗan kin rasa wace sana'ar za ki yi? To wannan classes ɗin naku ne, ku garzayo ku yi rijista domin kar a yi tafiyar nan babu ku. Daga sana'oin da za a koyar sun haɗa da;* 1. Graphic design 2. Magungunan mata 3. Sabaya 4. Turaren wuta 5. Fara 6. Candies 7. Skin care products 8. Importation 9. Snacks 10. Yoghurt 11. Oil perfumes 12. Bead work 13. Hair cream/oil 14. Dabarun kiwon kaji 15. Huluna 16. Spice's 17. Dabarun sana'ar kayan kitchen 18. Noma a zamanance 19. Dabarun kasuwanci

Dama ƙarin wasu, ga masu buƙatar sanin yadda tsarin yake kai tsaye su tuntuɓi wannan lambobin.

08081012143 07037977211 08069611181