
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 2
..... she will walk in the house with a stick. Anyone who comes will stop at the roads she will pass until she reaches where she intends to go. *_H A I S A M_* Tied with a towel around his waist, the length of the towel is almost below his knees.....the shortness of the towel made it not cover all the built body and the strong figure, full of heart and fullness of creation that God has given him. A situation that no one allows to see him like that.....even if they are Omar. His hair dripping with water alone is enough to tell you that he bathed, and the water flowed through his hair of the real Oromo tribe. From his steps to his facial expression, you will learn how much energy and happiness he has. It's the same..... because inside his head, he felt as if there were some small extensions since the first investigation was completed on the young man who gave him the same answer after asking him his name. "I HAVE NO NAME" It is the only name known to him as a complete human being for more than twenty years. "THE BLOOD IS AJAANI...... THE BLOOD IS SULTANESE MUHAMMAD HAMMUD" These two words do not show that there is a time or luck that will happen.....
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 02*
"An gama" Birra ta furta sannan ta miqe,saidai kuma tadan dakata kadan.
"Saidai morsa safiyya tabar saqo". Ido kawai akhnan ta lumshe kadan tana budesu sanda take qoqarin tura sumar kanta data cika mata kanta cikin siririn band.
"Tace inda zai yiwu,da kin daure kin qarasa karbar ragowar gyaran jikin na kwanakin da suka rage" Kaman ba zata amsa ba......da wannan kalar miskilancin daya zame mata halitta taci gaba da takawa,har takai qofar toilet din sannan ta bada amsa kafin ta shige.
"Zan shiga......bayan na kammala da library din". Haka kawai takejin nauyin a yau karon farko tace da morsa safiyya ba zata amsa tayinta ba......ba kuma zata amsa kiranta ba.
Sanda ta shige bandakin saida birra ta saki qaramin murmushi kadan sannan ta juya ta fice don sanar da fitarta daga sassan nata zuwa sashen da dakin karatu na me martaba yake don a gyara hanya. Doka ce.....kuma tsari ne nata ita kadai......bata tarayyan hanya da kowa a sanda zatayi tattaki cikin gida. Duk wani kai kawo zai dakata a hanyoyin da zata wuce din har sai takai inda tayi niyyar zuwa.
*_H A I S A M_*
D'aure da towel ya fito a qugunsa,towel din da duka duka tsahonsa iya qasan gwiwarsa ne da kadan.....qanqantar towel din ya sanya bai rufe duk wani ginannen jiki da surar qarfi me cike da zati da cikar halitta da Allah yayi masa baiwa da ita ba. Wani yanayi da ba wanda yake bari ya ganshi a haka.....koda kuwa su omar ne.
Sassalkar sumarsa dake d'igar ruwa kadai ta isa ta shaida maka wanka yayi,ya kuma kwarara ruwan daya ratsa cikin wannan sumar tasa ta anihin qabilar oromo da gasken gaske.
Tun daga takunsa zuwa yanayin fuskarsa zaka karanci qarancin kuzari da kuma walwala me tarin yawa dake tattare dashi. Haka yake.....don can cikin kansa yakejin kamar ana wasu qananun tsawawwaki tun daga sanda binciken farko ya kammala akan matashin da amsar daya bashi bayan ya tambayeshi sunansa.
"BANI DA SUNA" Shine kawai sunan daya sani nasa a matsayinsa na cikakken dan adam daya debi shekaru sama da ashirin yana rayuwa.
"JININ AJAANI NE......JININ SULTANE MUHAMMAD HAMMUD NE" Wadannan maganganu guda biyu bayajin akwai wani lokaci yanayi ko sa'a da zasu shafe daga cikin kanshi.
Ko a yanzun daya tsaya gaban qawataccen makeken madubin lafiyayyen master bedroom din nasa.......sai daya cusa yatsunsa dukka goma cikin jiqaqqiyar sumarsa. Yaja iska sosai cikin hunhunsa yana fesarwa bayan ya sauke hannuwansa a qasa.
Yayi cases kala kala na criminals iri iri......yaga tarin abubuwa da suka qara qarfafar imaninsa.......ya shiga cases masu hadarin gaske,ya kuma binciko sannan ya tabbatar da gaskiyar me gaskiya.......amma bai taba ganin zallar qwarewa gurin iya cutarwa.......daukan fansa akan wanda ba ma'abocin laifin ba.......da kuma tsananin bijirewa Allah irin na ZEENATUN ZAITUNA BA.
Manyan idanunsa masu wani irin kyau......irin kyan da ba abinda yake sauya sunansu na KYAWAWA ya lumshe yana sake cusa yatsunsa guda biyar cikin sumarsa gami da budesu fes saman kyakkyawar fuskar nan irin ta matasan oromo masu jini a jika.
Wani irin zafi yakeji daga can cikin zuciyarsa....zafin dake farawa tun daga saman fuskarsa har izuwa gangar jikinsa idan ya tuna AHMAD jini ga akhnan.......yayanta shaqiqinta da bata da kamarshi shi ZAITUNA taso aurawa a matsayin MIJINTA?.
"Ya salam" Ya fadi yana dunqule hannunsa a sanda zuciyarsa ke tambayarsa.
"Inda haka ya faru fa?,inda komai ya faru kaman yadda taso fa?,inda komai ya kasance kamar yadda ta tsara fa?". Wani irin rauni yaji qafafunsa sunyi da wani irin sanyi,kamar a yanzun abun ke shirin tabbata......wani irin rauni da babu kamarsa koda kuwa a runtsin aiki cikin kalolin ayyukansu masu tsananin hatsari da sarqaqiya,sai ya fara komawa da baya a hankali yanajin kamar nauyin dake cikin zuciyarsa shine yake qoqarin rinjayar gangar jikinsa gaba daya.
Yana shirin zama kiran wayarsa ya katse masa wannan hanzarin,ya sanya hannu ya dauki wayar yana duba sunan. Omar ne.......sai yanzu ya tuna ya barshi yana jiransa tsahon lokaci,don haka bai bata lokaci ba ya daga kiran yana fadi a taqaice
"dhiifama,dhufaa jira(afwa,gani nan zuwa)". Omar baice komai ba kamar yadda shima bai jira yaji abinda zaice din ba ya katse wayar,saidai kafin yayi wani yunquri green light ta bashi alama.
Green light ne na musamman daya qirqireshi ya kuma jonashi da duk inda yakeso yake kuma buqata cikin wasu sassa nata dama wasu sassanni na masarautar ba tare da sanin kowa ba. Cikin nutsuwa ya miqe,ya isa inda qaramar na'urar take,ya dauko wata qaramar system dinsa ya koma gefan mulmulallen gadon da yafi kama da qaramar duniya bawai gado ba ya zauna sosai sannan ya soma hada komai daidai da yadda yakeso.
Hannaunsa dafe da stool din daya dora system din yake kallon komai. Ta fito sosai ta cikin allon system din sanda take takawa a nutse birra na biye da ita. Wani irin taku da zaka dauka yauqi ne ko yanga bawai dabi'a na halittarta ba,takun da cikin kowanne yanayi yake iya nuna yadda qasaita kebin jininta. Idanunsa ya zare a hankali yana maidawa gefe inda wayarsa ke ajiye,siririyar ajiyar zuciya ta subuce masa. Wayar ya dauka ya bude da nufin aika saqo,wani abu yana kuncewa daga can qasan zuciyarsa,a yanzun daya sake ganinta sai yakejin rad'ad'in da yakeji a qirjinsa ya ninku......sai wani siririn abu me me kama da tausayi dake huda zuciyarsa a hankali,yanajin kamar ya rasa wani bangare na juriyar iya kallonta na tsahon lokaci,kamar yafi buqatar tsaronta a yanzu sama da kallon nata.
Bugu daya aka daga wayar,ya sakata a kunnensa. Idonsa ya lumshe ya kuma bude lokaci daya,yana jin yadda zuciyarsa har yanzu take ba dadi,cunkushe da wannan abun da yayi masa tsaye da har yanzu ya gaza fassara mene shi. Labbansa ya motsa yana amsa sallamar,wadannan kyawawan labban dake daukan hankali da burgewa.
"Ina zasu fita?".
"Dakin karatu obbo".
"Akwai cikakken tsaro?" Kaman haisam yana gabansa abdii ya gyada kai.
"Akwai obbo" Shuru ya gilma na sakanni kaman bazai amsa ba kafin yace.
"Zaituna ba......inaso a zareta daga cikin jerin sahun mutanen da suke da damar ganinta kai tsaye.....koda kuwa ta buqaci hakan"
"An gama obbo" Abdii ya fadi,amsawar ta abdii kuma ta kawo qarshen maganan tasu,ya maida wayar cikin nutsuwa ya ajiyeta.
Miqewa yayi yayi tattaki zuwa gaban mirror din,har yanzu yana jin kansa a cushe a kuma cunkushe da tarin abubuwa. A duk sanda zai tuna matasan guda biyu......a duk sanda zai tuna abubuwan da suka shude a wannin da suka gabata sai ya sakejin bacin ransa yana ninkuwa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Tsaf ya shirya cikin black trouser da dark olive green shirt. Kalolin da suka zauna da wani irin tsari da kuma dacewa a gangar jikinsa. Sun fidda tsahonsa dama murjewar murdadden jikinsa,kamar yadda suka haska farar fatarsa zuwa fuskarsa da a yau ya amsa cikakken sunansa na MISKILI ZAM.
Sassanyan turaren nasa dai shine abu na qarshe daya maida ya ajiye,sannan ya fara nufar qofa da 'yar sassarfa yana fita,kaman wanda ya tuna da mantuwar wani abu me muhimmanci da yayi.
Takunsa shi ya sanya Omar daga kansa daga tattaunawar kai tsaye da sukeyi da bobbo muhammad dawud ta hanyar kiran kai tsaye na ido da ido wato video call.
"Gashinan bobbo" Omar ya furta a nutse yana tashi ya zauna sosai saman kujerar.
Kai tsaye ya zabi daya daga cikin kujerun dake daura da omar,kuma tun kafin ya zauna ya miqa dogon hannunsa yana jawo fuskar system din zuwa saitin inda zai zauna din sannan ya koma ya zauna a dan gaggauce.
Abeer ya miqa wayoyinsa tare da sign na saka masa charge kafin ya dawo da hankalinsa kan allon system din. Kan bobbo muhammad dawud idanunsa suka sauka,wanda ya zubawa haisam din dukka idanunsa da irin kallon daya tabbatarwa da haisam din nazarinsa bobbo din yakeyi.
Janye idanunsa haisan yayi sanda bobbo Muhammad dawud ya saki qaramin murmushi,har yanzu idanunsa akan fuskar haisam din.
"Me yasa banga alamun farincikin nasara ba saman fuskar muhammadu ba?" Ya furta har qasan zuciyarsa yana mamakin daukewar walwala daga fuskar haisam.
Ba haka ya zata ba,bama shi kadai ba.....dukkan wanda yasan da aikin......dukkan wanda yasan da aikin yana hasashen farincikin nasarar haisam a ranar zai zama na dabanne.
Yatsunsa ya murxa kadan,baisan me zaice da bobbo da zai gane.....baisan da wanne yare zaiwa bobbo bayani ba,bashi kadai ba harda su omar. Abu daya ya sani wani qatoton abune yake a tsaye a wuyansa a yanzu haka idan ya tuna shirin mammina mafi muni,shirin halasta haram tsakanin muharraman da tafi kowa sanin girma da nisan haramcin dake tsakanin AHMED da KHADEEJA.
"Akwai sauran bayanai" Bobbo ya fadi kansa tsaye yana duban haisam. Sai a sannan haisam din ya dawo da dubansa ga fuskar bobbo din,ya gyara zamansa da yanayin zamannan dake cike da qasaita wanda ya zame masa jiki,ko a office ko a taro koma a inane,wanda yawancin lokuta baimasan yana yinsa ba.
"Akwai" Ya amsawa bobbo a nutse da muryar nan tasa da nutsuwa kewa ado koda yaushe.
"Ina saurare" Bobbo ya fada shima yana tattarawa haisam dukka nutsuwarsa.
"Asalin sunan ZEENATU ne.....zaituna sunan aminiyarta data salwantar da ita ne bayan ta tabbatar a duniya itace kadai ta rage halittar datasan kaf sirrikanta.....ta taho da jaririn ajaani xuwa niger.......ta kuma dauki jinin sultane muhammad hammud ta maidashi tantirin dan shaye shaye bayan ta bayar da kyautarsa ga magajiyar karuwai.....kyautar da an shiryata ne da nufin za'a waiwayeta bayan wasu shekaru saboda cika wasu munanan qudure qudure da muradi na hada haramtaccen aure tsakanin 'yan uwan da aure tsakaninsu ya haramta har gaban abada.......khadeeja diyar sultane......da ahmed babban d'an sultane daya kamata ace yana rayuwa a fada yanzu kaman sarki,.......wanda ya kamata ya karbi sunan MAGAJIN SULTANE a yanzu haka" Ya qarashe maganan yana jin wani d'aci yana ratsashi tun daga zuciyarsa har izuwa harshensa.
Shuru ya sake wanzuwa,girma bayanan da haisam yaci gaba da bashi yana ratsa bobbo. Girman rashin imani.....zallar zalunci da BAQAR SHUKAR zaituna yana ratsa zuciyar abbo din.
"Lokaci yayi muhammad.....a yanzu ka lalata komai,ka kuma bata dukkan wani shaida makama ko hujja tata,......ka saare dukkan wani qarfi da takejin tana dashi,na baka dama a kanta a yanzu" Bobbo muhammad dawud ya fada shima yana jin wani irin abu me nauyi yana sake sauka a zuciyarsa.
Wani kalar murmushi ne ya subucewa haisam din yana murza tafin hannunsa da yatsunsa,wani kalan murmushi da baida alaqa da jin dadi ko walwala ko kadan.
"Taci bulus kenan bobbo" Ya furta calmly,saidai wutar dake ruruwa me girma ce.
"Zunubin zama a qasar AGADEZ,cakuduwa da mutane masu aminci,da kuma ha'intarsu kadai....iya wannan zunubin yafi qarfin a kama zaituna cikin girma......dole ta rasa wannan GIRMAN data dade tana tattalinsa.......dole kuma ta zama mutum ta farko da zata fara tonawa kanta da kanta asiri........inaso a gaban idanunta AHMED ya zama magajin sultane....... Inaso akan idanunta abinda take jayayyar hukuncin Allah a kansa ya faru alhalin bata da yadda zatayi....."
"Sultane fa?" Bobbo ya fadi yana duban tsakiyar idanun haisam,yana kuma karantar zurfin bacin ransa.
"Za'a yi komai yana nan......saidai zai dan kwanta ya huta da kalar hutun da zai zame masa sassauqa.....hutun da zai hanashi ganin wasu daga cikin tashin hankulan da suka durfafoshi suka durfafo iyalinsa,suka koma durfafo masarautarsa......na shirya kawai bobbo.......idanu da kunnuwanka kawai nakeso ka kulle......a yanzu na shirya kowa yasan waye sheikh muhammad haisam ibraheem aba jifar......"
"Al_saamit?.......the silent one?" Bobbo ya fada da wani kwantaccen kuma sauqaqqan murmushi kan fuskarsa. Ya sani,tsokanarsa bobbo yake,wata tsokana cikin girmamawa wadda haisam ya riga ya saba da ita.
"Na kulle muhammad.......na damqa maka dukkan wata dama kuma dari bisa dari.....na zare hannuna na baka wuqa da dama......ka qarashe wasan da dukkan salon da kaso" Idanunsa haisam ya lumshe yana kuma budesu dukka lokaci daya.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽