Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 50

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 50

..... She knew what she needed in the evening, light food, even if she was late she didn't miss her lunch, so she didn't hesitate to ask her what to eat, she started serving her. It is a healthy professor who is very attentive to the fact that she is very fond of their food. It has a very secret in it, she poured Oromian black tea for her, it was royal black tea because of the high price of the herbs that are used to steal it, you don't get it in everyone's house, as it is rare to find it even though they are the ones who grow it, she gave her a spoon and fork, and then they all gathered and left her parlor because they didn't like to eat among people. From the first gate where their cars stopped, all the doors of the house started to be opened with a kind of respect and dignity. His cars are different.....in Ethiopia and neighboring countries, in a short time the servants in the house all surrounded him in a warm welcome, and he greeted everyone with respect and knowing the honor and value that God has given to human beings, before everyone left him, he turned and started walking into the house quietly. Any setting room or parlor that will pass in the utmost respect for the servan

Standalone post2,086 words

πŸ’Ž *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*πŸ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 50*

"Allah ya qara daukaka darajarki.....an kammala" Ta fada da girmamawa. Tadan juya ta kalli alitash,sai kawai suka burgeta.

"Na gode......"

"Amhara tace ko zaki fara cin wani abu?" Alitash ta fada da kulawa. Kai ta gyada a hankali,ba shakka zata iya bawa hadimai da bayin agadez maki casa'in ta cikashewa wadannan zuwa dari bisa dari. Ta fahimci zataje din,saita miqe suna mara mata baya zuwa parlor din da tafi zama cin abinci.

Falon yana cikin falukanta da tafiso a 'yan kwanakinta cikin gidan. Komai ya kasance da tsarin gargajiyar dake nuna al'adar oromia. Wasu abubuwan nasu suna burgeta,amma yadda ba wanda yace mata komai,ba wanda ya taba mata bayani,itama bata damu ta daga kanta ta tambaya ba.

Kafin ta qaraso sun saita mata takalman da zata sanya ta cire wadanda ta fito dasu a qafarta kamar yadda suka saba,ta zare wadancan ta saka wadanda suka batan,ta fara takawa a nutse tana nufar traditional royal dining table din.

Ta san abinda tafi buqata a yammacin,abinci mara nauyi,koda ta makara bataci abincin rana ba,don haka bata takurata da tambayarta me zataci ba,ta soma serving dinta.

Wani lafiyayyen farfesu ne me romo sosai data lura akhnan din tana matuqar so cikin irin abinciccikansu. Yana tattare da wani sirri sosai a cikinsa,ta zuba mata oromian black tea daya kasance royal black tea ne saboda tsadar ganyayyakin da ake dafashi dasu,ba gidan kowa kake samunsa ba,kamar yadda ba kasafai ake samunsa ba duk da sune suke nomashi,ta saka mata spoon da fork,sannan dukkaninsu suka tattara suka bar mata parlor din saboda sun karanci bata fiyason cin abinci cikin mutane ba.

Tun daga gate din farko da motocinsu suka tsaya aka soma bude dukkanin qofofin gidan da wani iri salo na karramawa da girma. Motocinsa daban suke.....cikin fadin Ethiopia dama qasashen dake maqwabtaka dasu,cikin qanqanin lokaci hadiman dake gidan gaba daya suka zagayeshi cikin marabta ta girma,ya kuma gaisa da kowa cikin mutuntawa da sanin daraja da kimar da Allah ya yiwa dan adam,kafin kowa ya qyaleshi,ya juya ya soma takawa zuwa cikin gidan a nutse.

Duk wani setting room ko parlor da zai wuce cikin matuqar girmakawa hadiman dake gurin suke zubewa su gaidashi,sannan kuna su zare jikinsu su fita don sun tabbatar yau yazo ganin gimbiya ne. Baya da dabi'ar son a zube a gaidashi,amma duk yadda yayi dasu sun gaza dainawa. Sunajin ba zasu iya daina gaidashi ta hakan ba,girma da kimarsa da mutuntakar dake tsakaninsu tafi qarfin su iya gaidashi daga tsaye.

Kai tsaye ya zarce zuwa parlor din,ya tabbatar tana can,don yana da analysis na motsinta cikin gidan,yana da rahoto kan duk wani abu da tafiso.

Wata irin qofa ce da bata bada alama ko sauti ko daya yayin budeta,wannan ya sanya hankali kwance ya janye qofar gefe,ya kuma saka qafarsa a parlor din idanunsa suna dauko masa hotonta a matsayin abu na farko da suka fara gani cikin falon din.

Tana zaune saman kujerun,ta dafe gwiwar hannunta dukka biyun da table din. A hankali take juya tea din idanunta cikin cup din,kallo daya zaka mata kasan akwai wani d'an qaramin tunani dake mata kai kawo cikin ranta. Yadda tadan karkatar da kanta ya sanya jelar sumarta da aka fake a tsakiyar kanta ya dawo kafadar hagunta yake reto a hankali daga bayanta zuwa gefan fuskarta.

Ta gama juyawa,ta ajiye spoon din a gefe,ta daga mug din ta soma kurba a hankali. Labbanta yabi da kallo,labbanta da hucin ruwan dumin ya sake sanyawa suka sake canza kala.....a idanunsa sunyi looking very soft,abinda ya soma tayar masa da tsumin data dasa masa a dukka gangar jikinsa tun a wancan ranar.

Idanunsa ya zame a hankali zuwa santala santalan qafafunta,yayi sama da dubansa har zuwa qugunta daya fito sosai ya bayyana bajajjun mazaunanta da suka dace da shafaffen cikinta. Yadda ta zauna saman kujerar ba'a daidai ba ya sake fidda shape dinta sosai,ya kuma sake fidda fadi da tudun mazaunanta,don ta karkace bangaren damanta ne sosai,sai hakan ya zamana kakar da gayya ta turosu daga daya side din.

A hankali yaci gaba da bin sassan jikin nata da kallo,har zuwa sanda ya kawo kan mutanen nasa. Wannan gurin da kallo daya tak ya masa yaji kaman qafafunsa ba zasu iya daukarsa ba......sai kawai ya zube hannuwansa cikin aljihun trouser dinsa ya jingina kafadarsa da jikin qofar,yayi crossing qafafunsa kawai yana ci gaba da narke idanunsa a kansu kamar an bashi aikin kallonta,ko kuma wanda ya shiga gasar iya kallo ta duniya.

"Ya salam.....ya salam sallim sallim" Ya furta yana jin yadda ake jona masa wani wiring na shocking cikin jikinsa gaba daya.

A cikin jikinta ta soma jin she's not comfortable ba kaman dazu ba,amma sanin cewa ita kadai ce cikin gidan ya sanyata jawo plate din farfesun,ta sanya spoon din,amma ta gaza kaiwa bakinta sai juyawa take a hankali. Ta kusa minti daya kafin takai na farko bakinta,yabi dan qaramin bakinnnata da kallo,yana tuna yanayin daya shiga wancan lokacin daya hade bakunansu guri daya......yana tuna abinda ya dinga ji da yadda kowacce wuta ta jikinsa ta dauke masa.

Tana zare spoon din daga bakinta idanunta suna sauka a kansa. Wani bugawa zuciyarta tayi da kyau,bugawar data haddasa mata qwarewa ta ajiye spoon din ta fara tari.

Da sauri ya zare hannunsa daga aljihun wandon ya fara takowa sa sassarfa. Kai tsaye ya isa gaban table din,ya dauki gorar ruwan data kasance ruwan kamfanin masarautar ne,ya bude ya tsiyaya mata a cup a gaggauce ya miqa mata. Ta miqa hannunta tana yin tarin a hankali,ga zatonta zai sakar mata cup dinne,amma sai taji ya hada harda hannunta ya riqe gam ya isar da cup din bakinta,sai data fara sha sannan ya zare hannunsa a hankali ya koma da baya a nutse ya zauna saman kujerar dake opposite din tata yana kallonta. Komai nata da jan aji,komai nata akwai isa a ciki,ko yadda takeshan ruwan kawai zakasan akwai ginshira cikin lamarinta.

Cire cup din tayi daga bakinta,sannan ta soma ajiyeshi a nutse tana sauke numfashi. Idanunta ta daga ta aza a kansa. Still kallonta yake kaman Allah ya aikoshi,fuskarta ta hade sosai tana jin bugun zuciyarta har yanzu bai daidaita ba. Batason wannan kallon......yana sanyata ta daburce gaba daya.....batason wannan kallon saboda yana karanta mata kai tsaye abinda yake cikin zuciyarta. Bataso ta nuna masa rauninta ko wani abu makamancin haka,don haka ba zata tashi ta bar masa gurin ba,hakanan batasan me zatace dashi ba tunda sai yau ya tuna da ita?,don haka ta sake jawo plate din ta maida spoon din da zummar ci gaba daci,amma kallonsa a kanta yayi yawan data kasa hakan,sai kawai ta zabi ci gaba da juya spoon din.

Ya fahimceta duk da batace komai ba,baijin zai iya hana kansa ci gaba da kallonta.....bayajin kuma zai cuci kansa ya janye idanunsa daga kanta,halal ce.....halal dinsa ce.....wannan kallon da yake mata na halal ne......wannan kallon da Allah zai bashi lada ne.....wannan kallon da Allah zai saka ya sake yarda dashi ne,don bai kalli d'iyar kowa ba......bai kalli halalin kowa ba sai nashi.

Spoon daya ya zaro shima cikin wani hadadden abu na silver dake gefe wanda aka adana spoons din a cikinsa. Kai tsaye ya zura cikin bata kwanon,ya kuma yi bismillah ya debo ya fara kaiwa cikinsa.

Yunwa yakeji.....yunwar da bata tashi ba sai a yanzu da yaga abincin gabanta. Yana lissafe kwanaki daya daya har kwana biyar bai zauna yaci abincin kirki ba,uwa uba kuma ga mura da yakejin alamu tana son kamashi. Duk wannan tunanin duk wannan zaman duk wannan cin naman da yake bai dauke idonsa a kanta ko na second daya ba.

Tako ta ina......ta kowanne bangare ya takurata. Kallonsa wani irin dafi yake sauke mata a jikinta wanda ba zata iya jura ba,duk iya yadda take zaton tana da zarrar da zata iya basar masa saita dinga jin kamar idanunsa suna yaye mata kowacce sutura dake jikinta,suturar da wata irin nadamar sakata tazo ta mamayeta,don daidai da bugawar da zuciyarta takeyi ta tabbatar yana iya gani ta d'amammen qirjinta.

Batayi qarya ba.....idanunsa suna kai.....idanunsa suna ankare da wajen yana irga adadin bugun zuciyarta daya tabbatar adadin ya zarta yadda ya kamata ya kasance. Can qasan ransa ya saki murmushin da bai nuna a saman fuskarsa ba. Ya sani fushi take,fushin da ya tabbatar koda ya gaya mata dalilin yinsa ba yarda zatayi ba.

Idanunta ta maida kan plate din da tun naman farko bata sake kai komai bakinta ba,amma yana dab da cinye naman gaba daya.

"To zaman me nake?" Ta tambayi kanta,sai kawai ta ture kujerarta baya da zummar miqewa,saidai kuma kawai taji tattausan tafin hannunsa saman bayan hannunta.

Wani irin abu ya tsarga mata yarrrr a jikinta,tana jin wata kewa me nauyi na wannan tattausan tafin hannun tana ratsata,amma a zahiri saita hade rai ta daga blue eyes dinta ta watsa masa.

"Zaifi kyau ki zauna mu sasanta a nan your royal highness" Ya fada softly yana sake kasheta da wadannan abubuwan dake cikin narkakkun idanunta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Idanma saqo ya aike mata da gaske ya isa har tsakiyar zuciyarta,taji kaman an ragewa qafafunta qwari,to amma ba zata taba yarda ba.

"Me ya faru?,me zamu sasanta?,ba abinda kayimin,kawai zamanka a nan ne banaso,ka tafi" Sune kalaman da takeson gaya masa,amma kamar daukewar ruwa suka dauke daga bakinta,sukaqi bata hadin kai ballantana ta furtasu. Abu daya tayi shine zame hannunta,ta kuma juya ta soma sauka daga gurin,abinda ya bashi full access na ganin komai da komai,da yadda suke juyawa da wani irin yanayi daya fusgi hankalinsa,ya kuma sanya naman tsaiwa saman bakinsa,kafin ya tattara qarfinsa ya hadiyeshi da qyar. Sai kawai ya daina jin duk wani taste na naman,wannan dadin da ya masa ya dauke daga kan harshensa gaba daya,sai ya miqe a nutse yana ture tasa kujerar baya,ya soma takawa da kuzari da burin cinmata sanda take shiga parlour din da daga shi sai bedroom dinta.

Tsaiwa tayi tana zare takalman qafarta don musanyasu da bedroom slippers,ta saka qafa daya,tana zura qafa dayar kawai taji an mata wata kyakkyawar runguma daga baya,rungumar data tabbatar duk iya qarfin halinta bata isa ta qwace ba,rungumar data sanyata taji tana narkewa cikin jikinsa gaba daya,shu'umin turarensa yana gaya mata MUHAMMAD HAISAM NE.

*NA BIYAKU BASHINKU NA JIYA DAI KO?*

*_Assalamu alaikum warahmatullah_*

*_Na gode sosai,na gode da jumurinku,duk da na dauka zamu fahimci juna ni daku sama da haka,shi yasa na yita dagewa ina baku pages sama da yadda nake bayarwa,ashe da saura_*

*_Ko nawa kake samu a komai ma.....dan adam ne kai akwai gajiya,kana buqatar hutu,ballantana rubutu da yake cinye awanni mafi rinjaye na rayuwarka_*

*_kin taba biki na tabbatar,kinsan yadda hidimarsa take,yaushe kika samu kanki sanda kuka fara naki bikin?,yaushe kika gama nutsuwa duka kika koma daidai?_*

*_wannan rubutun da kuke ganin muna muku shi,wallahil azeem ko baci ranki yayi a rana bakya iya rubutun,koda kin takura kanki kinyi kowa pages din zasu zowa me karantawa ba armashi,koda yara ne suke gida baka samun nutsuwar yinsa,har sai basa kusa dake,walwala kike buqata,nutsuwa kike buqata ta gaske kafin yin kowanne page_*

*_wannan ya sanya sau tari da zaku gane haka don marubuci yayi ALLAH YA ISA ga wanda ke fidda masa pages ba zaku zargeshi ba_*

*_shi kadai yasan takura da quncin da yake fuskanta kafin ya hada kowanne page,a haka me sata ya fitar yake zaton ZAICI BULUS A GABAN ALLAH?_*

*_Ina amfani da wannan damar na shaida ma masu fidda mana pages ta kowacce hanya cewa,zanta gayawa Allah inde ban taba satar miki komai ba....ban taba cutar miki da komai ba......to Allah ubangijin al'arshi yayi min sakayya Allah ya isana duk wadda ta fitarmin da pages ta kowacce fuska kuwa,Allah ya sakamin_*

*_Yadda muka killace haqqinmu kayanmu,kuka watsawa duniya UBANGIJI KA BANKADE SIRRINTA DA TAKE ALKINTAWA A IDANUN DUNIYA,ALLAH KARKA SUTURTATA HAR ABADA_*

*_Na gode da jumurin bina da kuke,kuma in sha Allah next time labarinmu zai zamana pages saba'in tamanin kamar yadda aka saba book a baya ayi a qarqareshi_*

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

*HUGUMANKU CE*✍🏽