Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 43

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 43

..... she won't give me a night's sleep. I insisted on cooking, until the smell filled the house. Despite being tired from today's lecture, and physically tired, my heart is full of peace. I feel a kind of happiness with the new phone, with kindness from brother Usman, and seeing that life is changing little by little. At night, Abba came back with a big ledger. I came right to join you, and he handed it to me. Here is your system. I know that one has been destroyed for a long time but this one is gone. . I looked at him in amazement. I still wonder how Abba is trying to make him happy despite the harshness he showed me in the past. I am grateful, my heart is full of love for my parents. I gave him my old system and he went to sell it. It was bought for about 200,000 Naira. I opened my Opay slowly, I sent a message to Musa to go and deposit the money into my new account. No one knows. This is a secret between me and Moses. In the morning, while I was mopping, I saw Abba's phone on his chair. I went to take it to him, and my eyes fell on the name that came out "Maman Khalil." My heart beat. I quickly wrote down the number and saved it in my new phone. After getting ready for school,

Standalone post1,275 words

Yau da na dawo daga makaranta, sai naga Abba yana jirana a falo, yana murmushi a hankali. Na kalle shi cikin mamaki da farin ciki, kafin ya ce min Ga wayarki nan, Ramlah. Samsung ce sabuwa. Yaya Usman ne yace na ba ki. Bani da abin cewa a lokacin sai murmushi da hawaye da suka cika idona. Wannan ?aramar kyauta da aka yi min ta ?aga ni fiye da yadda nake zato. Nace Abba nagode sosai. Allah ya saka da alheri. Na kar?i wayar hannu na kama kiran Yaya Usman, har layi an sakamun aciki raina na tsalle da murna. Ya ?aga cikin natsuwa kamar yadda ya saba. Ramlah, wannan kankanin abu ne. Ki kula da kanki, ki dage da karatu, ki bar damuwa. Yaya Usman yana sona sosai. Yafi kowa a gidanmu tausaya min da fahimtar halina. Yayi min wa'azi, kamar kullum, akan hakuri da karatu. Na amsa da zuciyata gaba ?aya. Ina son hakan, ina godiya da kasancewarsa cikin rayuwata.

Bayan na gama waya, na cire kayan makaranta na, na sa hijabi na shiga kitchen kai tsaye. Na san idan na bari Momy ta rigani, tabbas abincin dare ba zata bani ba. Sai na dage nayi girki, har kamshi ya cika gidan.

Duk da gajiya da lecture na yau, da gajiya ta jiki, zuciyata tana cike da kwanciyar hankali. Wani irin farin ciki nake ji da sabon waya, da kirki daga yaya Usman, da kuma ganin cewa rayuwa tana sauyawa kadan-kadan.

Da daddare, Abba ya dawo da wani babban leda. Na zo daidai zai shiga ?aki, ya mi?a min shi Ga system dinki. Nasan waccan ta dade da lallacewa amma ai wannan tafi. .

Na kalle shi cike da mamaki. Har yanzu ina mamakin yadda Abba ke kokarin ganin yasani farinciki duk da irin tsaurin da ya nuna min a baya. Na kar?a da godiya, zuciyata cike da ?aunar iyayena. Na bawa musa tsohuwar system dina yaje ya siyarmun, Kimanin Naira 200,000 aka siye ta.

Na bude Opay dina a hankali, na aika da sakon Musa yaje ya saka kudin cikin asusun sabon account ?ina. Babu wanda ya sani. Wannan sirri ne nawa da Musa.

Da asuba, ina cikin mopping, sai naga wayar Abba a saman kujerarsa. Na ?auka don in kai masa, sai kuma ido na ya sauka kan sunan da ya fito "Maman Khalil." Zuciyata ta buga. Da sauri na rubuta number din, na ajiye a sabuwar wayata. Bayan nayi shirin makaranta, zuciyata ba ta da natsuwa. Daga bisani, sai na tara ?arfin hali na kira Maman Khalil. Tayi shiru na ?an da?i?u kafin ta amsa. Hello? Na ce da murya mai sanyi Mama, Ramlah ce. Yaya Khalil? Tayi shiru na ?an lokaci, kafin tace cikin ?an murmush Yamai jiki ne? Kawai sai tace Kalou yake. Ta katse wayar nan take.

Bayan ta katse wayar da waccan ?an gajeren amsa Kalou yake , zuciyata ta fa?i ?asa. Kamar ana jefa dutse a cikin ruwan zuciyata. Katsewar nan ta cije ni sosai. Ban fahimta ba ko katina ne ya kare? Ko kuma network ne? Na kasa yarda haka kawai aka datse waya.

Na sake kira.

Bayan sa?on farko na ringing, wani murya ta ?aga . Muryar Umman Khalil.

Ramlatu! Kin kamu da hauka ne?! Me kika sake kiran layin nan?! Wannan rayuwar kice? Ko ta mahaifinki ce? Ku barmin ?ana! Wallahi bana kaunarku, bana kaunar jin sunanki, bana kaunar ganin lambar da ke kirana

Kaina ya da?e a kasa, wayar na kunne amma zuciyata na ?an?amewa kamar zata tsaya. Ba wai masifa kawai take ba ta caccaka min kalmomi masu zafi da ban ta?a tsammani ba.

Ina ro?on Allah ya wulakanta ku kamar yadda kuka wulakanta ?ana! Ki guji inda yake! Wallahi karki kuskura ki ?ara neman shi ko kallon inda yake!

Ban iya magana ba. Har motsi a le?ena na rasa. Kalmarta ta ratsa raina kamar wuta, tana ?ona duk wata fahimta da nake da ita. Har ta katse wayar, har yanzu idona a bu?e yake, wayar a hannu, zuciyata cike da ?unci, kunya da wata irin azaba da ba a iya fasalta ta.

Na lumshe ido, hawaye suka fara gangarowa. Kamar ruwa ne a cikin ido, amma wuta ne a zuciya. Kalmar "bana kaunarki" ta yi karfi fiye da duka. Na rasa ko na kalle kaina a madubi, ko kuma na share kwalla, ko in kwanta in huta komai ya tsaya. Abin da ya fi zafi, ba wai masifar ba ce amincewa ce da gaskiyar da ta fi komai ciwo Ban da matsayi a zuciyar su.

Ina zaune a gefen gado, ?afafuna na kankame su a jikina, wayata na kwance a gefe. Kalmar Allah ya wulakanta ku... tana yawo a cikin kunnena. Wannan ba magana bace da ake yi da halin ?an adam. Wannan addu a ce da zuciya mai cike da ?iyayya ta fitar Na dafe zuciyata da hannayena biyu. Na bu?e baki a hankali nace Ni Ramlah me nayi haka?

Na rasa wanda zan gayawa. Ban san inda zan ajiye wannan zafin ba. Ban san yadda zan maida wannan bakincikin ba. Malam Idi? Momy? Yaya Usman? Ba wanda zai fahimta. Zuciyata ce kawai ta san yanda zafin kalmomin nan suka huda ni.

"Kamar ni, ni ce bakin ciki, ni ce sharri." ********

Washegari na tashi da wuri, saboda lecture dina zai fara da asuba kusan. Na shirya cikin hanzari, hijab ?ina mai laushi a kai, wayata a jaka, da na ?an fesa turaren da ke tuna min da Yaya usman dan shine yabani.

Rayuwar jami a ba wasa bace. A kullum ina da sabon abu da nake fuskanta ko dai sabon malam, sabon salo, ko kuma matsin lissafi da nake ?o?arin fahimta. Wasu lokutan bana iya cin abinci, wasu lokuta kuma nakan ci da ?yar amma bana ?in zuwa makaranta. Wani lokaci ma ina jin kamar makarantar ce ke ?arfafa zuciyata.

Yau lecture ?in mu zai kai har zuwa ?arfe shida na yamma. Ajinmu yau ya cika kamar kullum, wasu sun shigo da kwalliya kamar na dinner, wasu kuma suna janye jakar su kamar yan kasuwa. A makaranta babu wanda ke tambayarka damuwarka Na zauna kusa da Maryam. Tana ta sharhi akan group assignment da aka basu a previous class, amma hankalina ya kai ga malam ?in da ke shigowa cikin ajin. Ya fara da cewa Duk wanda ba zai iya jure kalubale ba, ba zai iya gina kansa ba. Na lumshe ido. Kamar ya karanta raina. Wani lokaci nakan ji kamar malamai ba kawai koyar da darasi suke ba suna karanta mana rayuwa ne a cikin kwana-kwana. Mun ci gaba da lectures har zuwa lokacin la asar. Sai da rana ta fara dushewa sannan muka gama. Na ji jikina ya gaji sosai.

Da na dawo gida, na tarar mun yi baki wasu daga cikin yan uwan Abba ne sun zo. Nayi sallama da ladabi, na gaishe su duka, kowanne da murmushi da tambaya Ke ce Ramlah? Hmmm, gashi kin girma. Na murmusa da ?an kunya, na amsa Eh, nice. Barka da zuwa.

Bayan dan zaman gaisuwa, na shiga ?aki na yi wanka. Ruwa mai sanyi ya bugi jikina ya kwantar da ragowar gajiya da na dawo da ita daga makaranta. Na canza kaya riga mai laushi da dogon wando, na ?an shafa man fuska mai ?amshi.

Na fito kitchen.

Na san idan na barwa Momy girki yau, babu komai da zan ci.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ARBA'IN DA HUDU

Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435

Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********