
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 49
..... because of the fever in my body. Until my body was cold, they brought me back to the room. The nurse patted Mumy Mumy's shoulder, take care of her now, don't you hear all her screams because God has gone out and there is no one in the ward. Mumy nodded. Then they went out and left us. I was lying in the room, I could not move, but my two eyes. I am not sleeping. Mumy woke up and I fell asleep. Then she let out a breath. She turned around and lay down on the chair, and I heard her start talking. She was trying to go back to sleep. I didn't move, but my heart felt everything. In the morning, I was lying down and could not speak. My body is weak, my breathing is slow, like that of a weak person. However, my heart is still unable to say that Khalil is dead. A nurse came in and checked me. She said, Alhamdulillah, you are getting better. But the body is still not very strong. Then continue to observe her. After a while, Abba brought in some of the family members. They stood by the bed, some said God help you, Ramlah. Some pat me on the shoulder, some look at me with pity. But no one.....
Cikin dare na farka da tsananin kuka. Na farka kamar wacce aka tasar da ita daga mafarki mai zafi. Na dinga jijjiga jikina, ina girgiza kai, hawaye suna zuba a idona sosai. Sai na fara magana da karfi Khalil! Khalil! Don Allah kar ka bar ni! Ka dawo mana! Ka ce min zaka warke Na tashi daga gadon da nake kwance, da ?yar na ?aga jikina. Jiki a mace, amma zuciyata kamar wuta ake hura mata. Na dinga kokarin fita daga dakin asibiti da ?arfi, kiran sunan Khalil kamar zan same shi a wani sashi. KHALIL! KHALIL!! Na dinga kiran sa cikin murya mai cike da ra?a?i.
Mumy tana zaune a gefen kujera. Tayi kamar tana bacci, amma na tabbata tana jin kiran da nake yi. Ta motsa, amma ta yi shiru.
Nayi ward din da ?afa na ina rawar jiki. Ihu na ya firgita ma aikatan asibitin. Nurse biyu da wani likita suka fito a guje. Daya ya ce, Rikota! Har yanzu tana cikin shock, zata iya cutar da kanta!
Suka ri?e ni da ?arfi, suna kwantar da ni da tausayi. Na dinga fizge-fizge, har suka ?auko allura suka yi min maganin saboda zazzabin dake jikinai. Har sai da jikina ya yi sanyi, suka dawo da ni dakin.
Nurse ta ?an tafa kafadar Mumy Mumy, ki kula da ita hajiya yanzu duk ihun nan nata bakiji ba saboda Allah data fita babu kowa a ward dinfa?.
Mumy ta jinjina kai. Sai suka fita suka bar mu. Ina kwance a dakin, ban iya motsawa, amma idona biyu. Ba bacci nake ba.
Mumy ta ?auka nayi bacci ne. Sai ta sauke numfashi. Ta juyo ta kwanta a kujera, sai na ji ta fara magana Ni baiwartace da zan tsaya ina gadinta ji wata nurse da maganar banza ai data fita tabi duniya yafi mana, haka kurum Ta gyara kwanciya. Tana kokarin komawa bacci.
Ni dai ban motsa ba, amma zuciyata ta ji komai.
Da safe, ina kwance ban iya magana. Jikina ya yi rauni, numfashi na yana fitowa a hankali, kamar na wanda ba ya da karfi.
Sai dai har yanzu zuciyata ta kasa yadda cewa Khalil ya mutu.
Wata nurse ta shigo ta duba ni. Tace, Alhamdulillah, kina samun sauki. Amma har yanzu jiki ba ya da karfi sosai. Sai a ci gaba da lura da ita.
Bayan lokaci kadan, su Abba suka shigo da wasu daga cikin yan uwa. Sun tsaya a bakin gadon, wasu na cewa Allah ya taimake ki, Ramlah. Wasu na shafa kafada, wasu na kallona da tausayi. Amma babu wanda ya san yanda nake ji.
Ban ce komai ba. Ina jin kamar wata hasara ce ta cika zuciyata har tana hana ni magana. Sai dai hawaye ne kawai suke kwaranya daga idona, koda ba na kuka da murya.
Sai ga Yaya Mujittapha, dan uwan Khalil na jini, wanda yayi karatun addini sosai, yana da nutsuwa da mutunci. Yana zuwa ya tsaya a gefen gadon. Ya kama hannuna a hankali.
Shima idanunsa cike da hawaye. Bai ce komai ba na wani lokaci. Sai ya daure, ya ce Ramlah Khalil ya gaya min wani abu kafin ya rasu. Yace idan wani abu ya faru da shi, ki sani cewa ba ki da laifi. Ki yi masa addua. Kada ki zubar da hawayen da bai cancanta ba. Ki ci gaba da rayuwarki. Ki gina kanki. Kiyi masa addu a.
Na fashe da kuka. Na saki hannunsa, na dafe kaina Khalil! Khalil!! Me yasa ka tafi? Kaina! Kaina!! Na hau ihu, na zame da ?arfi, jikina ya fara rawa. Ya Mujittapha ya firgita, ya ce Nurse! Nurse! ya fita da gudu ya kira su Abba da Nurse.
Nurse ta shigo a guje, Abba ya biyo bayanta da wasu daga gidan. Suka kama ni. Na shiga fizge-fizge, sai dai a ?arshe suka danne ni, suka sake yi min allura. Jikina ya lafa. Idona ya lumshe. Numfashi ya koma a hankali.
Yayin da ake zaman makokin Khalil a gida, ni kuma a nan asibiti nake kwance. Ina kwance cikin rauni da zafin zazzabi. Cikin damuwa da rashin kuzari. Cikin raunukan da ba likita zai gane ba, sai zuciya mai fahimtar zafin rasa masoyi. Cikin wani salo mai ban tsoro, na kasance wacce ba ta da ?arfi a jiki da zuciya. Ranar da aka tafi da shi, ni ban je ba. Ban gan shi ba. Ban ga jana'izarsa ba. Amma na ji kamar raina yana tare da gawarsa.
Yau da asuba, zazzabi ya taso min sosai. Na tashi da kyar na yi sallar asuba, jikina duk yana rawa. Na ?ora hannu a ?irjina, ina jin bugun zuciyata da ?arfi. Baya ga zafin rashin lafiya, bayanin jana izar da akayi min jiya yana ci gaba da dawowa a zuciyata kamar fim.
Nurse ta shigo da allura a hannu, tana murmushi kadan kamar tana tausayina. Ta duba zafin jikina ta ce Zazzabin ki yana da yawa. Amma da sannu zaki warke. Ki ?arfafa zuciya. Na kada kai kawai. Na kasa magana. Idona sun kumbura da kuka da rashin bacci. Daga nan ta fita Kusan mintuna talatin da nurse ta fita, sai na ji ana bude ?ofar dakin. Sai ga Maman Khalil da wasu yan uwanta mata biyu. Suka shigo ba tare da sallama ba, ba tare da murmushi ko rahama ba. Kamar masu aikin bibiya suka shigo.
Na juyo na kallesu. Cikin ciwo, na ?an daga kai kawai. Ina son na ce da su Sannu da zuwa, amma babu muryar da zata fito.
Sai Maman Khalil ta tsaya a gabana, ta dubeni da idon da ya cika da tsana, sai ta ce da karfi: Ke ba kya jin tsoron Allah ne? Da kika kashe min ?a! Kin tsaya kika hana shi kwanciyar hankali har Allah ya kar?i amanarsa!
Na bu?e baki da mamaki. Kamar mafarki nake. Na sauke idona kasa, hawaye suka zubo daga idanuna. Wata daga cikin su ta ce Allah zai saka mana! Rayuwa ba zata bar ki lafiya ba. Zaki ?an?ani kunci.yanzu kuma sai ki ?an?ani sakamako.
Na kara juyar da idona gefe. Na ma rasa inda zan kalle su. Wani abu a zuciyata yana ce min Toh ni fa ban yi komai ba
Amma ban iya kare kaina ba. Babu karfi, babu lafiyar jiki, kuma babu wanda zai tsaya min.
Suka ci gaba da maganganun su . Sun yi tsawon lokaci suna zagina, suna fadin abubuwan da suka firgita zuciyata. Wasu daga cikinsu suna cewa Ai ita ce ta jawo wa ?anmu cutar da ta kashe shi. Ta raina mu, yanzu zata ga abinda rayuwa ke nufi.: Zan tabbatar ba zata cigaba da karatu ba... Daga karshe, suka juya suka fita. Ba su tsaya ko don su dubi yanayina na ciwo ba. Ba su yi addu a ba.
Ban san inda Mumy take ba a lokacin. Amma ina zaton tana waje, ko tana waya da wani, ko kuma tana fakewa ne kamar ba ta sani. Duk da kuwa ta ce zan kula da Ramlah. Kuma duk da cewa asibitin ya cika da jama a nurses da marasa lafiya na ji kamar ni daya ce a duniya. Duk da irin zafin jiki da nake ji, zafin zuciya da cin mutunci ne ya fi komai zafi. Na runtse ido da karfi, ina jin yadda hawaye ke kwaranya. Ban iya hana kaina ba. Ban iya daurewa ba. Na fashe da kuka. Sai na ce a raina Me na yi wa mutane haka? Na rasa masoyi na rasa lafiya yanzu kuma cin mutunci? Kamar na fasa ihu. Kamar na bu?e ?irjina in nuna musu raunin da nake ji. Amma babu wanda zai gani. Babu wanda zai ji. Sai Allah.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH
SHAFI NA HAMSIN
Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435
Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********