
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 42
.....the presentation, we were divided into first class groups. I and two other girls that we have met since registration went to the Use of English class. We sat together in the second row, where the teacher came in with a laptop in his hand and a projector in a bag. He started looking at everyone one by one. I know most of you think this is just English. But trust me, this course will test how you reason, how you write, and how you present yourself as a scholar. While he was talking, I looked in my book and said to myself, I hope I can, I will make sure this opportunity does not pass me by. The time of day is near. After the first lectures, I went out to the cafeteria. It is a spacious place, decorated with red and white chairs and tables. I bought meat pie and lemonade, and found a place to sit. There a young man greeted me, politely and with a soft voice. His name is Fahad. We started talking slowly, without any restrictions. It's a start, it's quiet. From our conversation, I understand that he is a student at the Faculty of Law, and he is in his second year. Don't worry, he said, it's the first day. You will get used to it. That's how I started. I smiled. This little word he
Bayan mun gama rajista, aka umarce mu da mu wuce zuwa ?akin karatu na farko domin gabatar da zaman gabatarwa orientation. Hanyar zuwa ?akin karatu tana zagaye da manyan bishiyoyi masu launin kore, kuma ginin ya ke?e da gilashi mai she?i. Na tsaya na kalli surar jami ar gaba ?aya, zuciyata na ta bugawa da sauri ba saboda tsoro ba, sai dai sabon abu da nake fuskanta.
A cikin ?akin, mun zauna a tsari. Wurin ya ?auki ?alibai da dama, kowanne yana cikin natsuwa, wasu suna daukar hoto, wasu kuma suna faman rubuce-rubuce. Wata babbar malama ce ta shigo cikin tsari da kwarjini, ta fara yi mana jawabi.
Ku kasance da gaskiya, ku bi dokoki, ku mutunta kanku da malamanku. Wannan ba irin makarantar secondary bace. Anan ne zaku fara gina kanku da gina makomarku. Na zuba mata ido, kamar kowane kalmarta na shigar min kai tsaye cikin zuciya. Na fara fahimtar cewa jami a ba kawai wurin karatu bace wurin canjin tunani ne. Wurin da ake kai mutum daga irin yadda yake zuwa wani matakin dabam.
Bayan zaman gabatarwar, aka raba mu zuwa rukunan ajin farko. Ni da wasu 'yan mata guda biyu da muka saba dasu tun daga wajen rajista muka ha?u a ajin Use of English . Mun zauna tare a layi na biyu, inda malam din ya shigo da laptop a hannunsa da projector a cikin jaka. Ya fara duba kowa da ido ?aya bayan ?aya.
I know most of you think this is just English. But trust me, this course will test how you reason, how you write, and how you present yourself as a scholar.
Yayin da yake magana, na duba cikin littafi na, na ce a raina Ina fatan zan iya, zan tabbatar wannan dama ba ta wuce ni ba.
Lokacin rana ya kusa. Bayan lectures na farko, na fita zuwa cafeteria. Wuri ne mai fa?i, an kawata shi da kujeru da tebura masu launin ja da fari. Na sayi meat pie da ruwan lemo, na samu wuri na zauna. A can wani saurayi ya gaishe ni, cikin ladabi da murya mai laushi. Sunansa Fahad.
Mun fara hira a hankali, ba tare da wata takura ba. Yana da fara a, yana da nutsuwa. Daga hirar mu na gane cewa shi ?alibi ne a Faculty of Law, kuma yana shekararsa ta biyu. Don t worry, in ji shi, Ranar farko ce ke nan. Za ki saba. Ai nima haka na fara. Na murmusa. Wannan karamin kalma da ya fada ta saka min ?warin gwiwa. Bayan mun gama cin abinci a cafeteria, na lura cewa rana ta fara ja. Fahad ya kalli agogon hannunsa. Ya kamata ki je ki ?auki ID card ?inki kafin su rufe ofis. Na yi masa godiya, na mi?e daga kujerar, na ?auki jakata, sannan muka rabu. Ina tafiya zuwa ofishin ?aukar ID, zuciyata na karanta dukan abubuwan da suka faru tun daga safe rajista, orientation, ajin farko, da kuma wannan sabon abokin da na samu a cafeteria.
A ofishin, ?alibai sun yi layi. Kowa na jiran a ?auke masa hoto, ya kar?i kati da zai zama shaidarsa a cikin jami a. Lokacin da aka kira sunana, na tashi na tsaya gaban kyamara. Wani mai daukar hoto ne ya ce Kalli kai tsaye, ki murmusa kadan. Na yi kamar yadda ya ce. A cikin wannan ?an murmushin, akwai fata, akwai mafarki, akwai wata sabuwar ni da nake ?o?arin ginawa. Bayan na kar?i katin, na fito daga ofishin cikin natsuwa. Rana ta fara sauka, iska mai sanyi na busowa daga gefen bishiyoyi masu tsawo da suka kewaye makarantar. Na tsaya gefe ?aya, na jingina da wata katanga, na duba katin ID dina sunana, hotona, da tambarin jami a sun bayyana da kyau. Na saki ajiyar zuciya. Wannan kadan ne, amma yana nufin "na fara".
Bayan ?arfe biyu aka sanar da mu cewa babu lecture har sai gobe. Kamar yadda yawancin ?alibai suka ji da?i da wannan dama, suka watse cikin nisha?i, ni kuma nayi shiru. Na zauna cikin kaina, zuciyata na harbawa da sauri. Kawai sai naji inason naje naga Khalil.
Tun lokacin da na tura Musa ya tambaye min shi, ya ce min yana lafiya kalou. Wannan kalmar ta sauka a zuciyata tamkar ruwa mai sanyi. Sai dai ba ta isa ta kashe wutar da ke ci min zuciya ba wutar rashin ?arewar tambayoyi da ?aunar da na kasa musawa har yanzu.
Amma tsoro ya mamaye ni. Ina jin tsoro. Tsoron raina da nawa, da kuma tsoron abin da kalmar Abba ke nufi a raina. Tun wancan ranar da Abba ya gano cewa na sake kusantar Khalil, sai ya ce da karfi Allah ya isa! Wallahi ba zan yafe ba idan kika sake zuwa wajen wannan yaron! Wannan kalmar ba ta bar zuciyata ba. Duk lokacin da nake jin inason na sake ganinsa, wannan kalma ce ke tsaya min a wuya kamar dutse. Ina so na yafe kaina, amma na san Abba bai yafe min ba. Kuma idan Abba bai yafe ba... shin Allah zai yafe?
A raina na tambayi kaina "Shin soyayya har ila yau zata sa ni bijirewa fushin uba?" Kallon Abba lokacin da yake fa?in kalmarsa yana cike da ?acin rai da zafi yana yawo a idanunsa, har yanzu yana hango min a ido. Na tuna yanda nake kuka a wancan dare, na ro?i gafararsa, amma sai ya ?auke kai. Na san babu inda zan sa kaina idan na karya alkawarina.
Na lumshe ido. Na dafe zuciyata. Wannan ba lokaci bane na jin da?in soyayya. Wannan lokaci ne na ?aukar matsayi matsayi tsakanin soyayya da biyayya. Na zabi biyayya. Kawai na hakura.
Na cire niyyar zuwa. Ban kuma kiran Musa ba. Ban tambaya ko Khalil yana ina ba. Na zauna a ?ar?ashin bishiyar da ke gaban hostel, zuciyata cike da murya guda
Allah ya isa... ba zan yafe ba.
Lokacin da Malam Idi ya zo daukaya, na shiga motar da gajiya amma da natsuwa. A wannan safiya, na fito daga gida da zuciya mai cike da rudani, amma yanzu, zan koma da zuciyar da ke cike da ?aramin haske hasken da ke nuni da cewa abubuwa za su yi kyau, da lokaci. Na jingina a kujerar baya, na lumshe ido, ina sauraron sautin motar da ke gudu a kan titi. A raina, wata murya ta ce
Kiyi hakuri da kanki. Ki ba kanki lokaci. Rayuwa tana da lokaci, da jarabawa, da lada.
Da na koma gida da yamma, gajiya ta saukar min sosai kamar jaka da aka jefa. Jikina duk ya dau nauyi, kaina ma ya daina ?aukar tunani. Na zube a kujera a falo ina sauke ajiyar zuciya. Cikin kankanin lokaci na mike da nauyi na shige ?aki, nayi wanka da ruwa mai sanyi wanda ya dan kwantar da zafin gajiya a jikina. Na shirya cikin kayan gida masu sau?i sannan na fito ina neman inda kayan Islamiyya suke.
Momy, Islamiyya fa? Na tambaya.
Tace cikin sakin fuska mara kulawa Abbanki ne ya ce ki je.
Na gyada kai, ba don na gamsu ba, sai don bana da ?arfi a halin da nake ciki. Na le?a cikin kicin babu abinci. Ko ?amshin miya babu. Sai kwanon cornflakes da ya tsaya min idanuwa. Na ha?a shi da madara, na zauna a hankali na sha kamar wanda ba shi da gata.
Bayan haka na koma ?aki na kwanta. Na lumshe ido amma kwakwalwata na ci gaba da tunani. Washegari lectures uku ke jirana kuma har yamma zan shafe a makaranta. A raina nace, "Ramlah, sai ki dage. Wannan ba lokacin kasala bane."
Na tashi da asuba da ?an nauyi a jikina amma zuciyata cike take da ?aramin ?arfin guiwa. Bayan sallah na shirya cikin kayan makaranta, na saka hijabi, na ?auki jakata, sannan na fita. Malam Idi ya iso da mota kamar kullum, na shiga a hankali ba tare da nayi magana ba. Hanya ba ta da hayaniya, sai zuciyata dake ta tattauna da ni.
Ni fa ?aliba ce a Business Administration, kuma yau GST 102, BUS 101 da BUS 103 ne a jadawali na.
Lecture Na Farko GST 102 Communication Skills. Muka fara da GST. Aji ya cika da ?alibai. Wasu na ?aukar hoto, wasu kuma na gyara litattafai. Na zauna a baya kadan, ina mai shirin shan ilimi. Malamin ya shigo da fara a, ya bu?e lecture din da cewa Without communication, business cannot survive. Ya ?an sa dariya. Daga nan ya shiga bayani mai zurfi akan verbal da non-verbal communication, barriers, da feedback. Na rubuta sosai. Wasu lokuta nakan ji kamar lecture ?in na magana da raina ne kamar ina karanta rayuwata cikin lecture.
Lecture Na Biyu BUS 101 Principles of Management. Wannan lecture ya rikita min hankali ka?an. Malam ya shigo da kasala kamar wanda aka taso daga barci, amma sai ya fara magana da kwarjini A good manager doesn t control people. He guides them. Ya koya mana game da planning, organizing, leading da controlling, sannan ya ambaci Henry Fayol. Kamar ana fa?a min yadda zan tsara rayuwata daga yanzu.
Lecture Na Uku BUS 103 Business Mathematics. Ni da lissafi ba abokai bane sosai, amma na shiga da shirin cin karo da kalubale. Lecture din ya rikita mutane da dama, amma na dage. Profit and loss, percentage analysis, da basic statistics ne abin da muka koya. Na rike biro kamar bindiga. Na sha?e takarda kamar zanyi jayayya da ita.
A yau makaranta cike take da kuzari da nisha?i. Kowa yana harkar dake gabansa wasu na zuwa caf , wasu na ?aukar hoto a harabar makaranta. Na zauna kusa da sabuwar kawata Maryam, muna tattaunawa akan test ?in da malam ya ce zai kawo mako mai zuwa. Maryam tana da fara a. Kamar bata da damuwa. Na dinga kallonta ina tunanin "Shin ni ma zan iya zama haka wata rana?"
Yayin da rana ta fara dusashewa, na fito daga lecture na karshe ina jin gajiya.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA UKU
Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435
Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********