Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 1

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 1

.....I went in and pulled on my hijab, I started cooking like someone who has been used to this life since birth. "Ramlah, wash the dressing, and then take the tomatoes. When you're done, grind the spices, but grind half of them, you know your father doesn't eat very spicy." These words of hers are more than ten times daily, as well as the way she tries to show that she cares, while I know better than anyone that I have a different position in her heart. I didn't finish leaving the town when I heard Abba's greeting, that is my father. She quickly came out of the kitchen laughing, "Well, Alhaji, welcome! Come here early, we are about to finish the meal." "Hello, Abba." I looked at him while he was studying and I heard him say, "God bless Ramlatu." I think the community is responding. I turned away from the spear and struck, and continued my work. "Wai Ramlah, won't you hurry?!" Her voice filled the entire house. "By the way, if you can't work like I have to, I don't know why you are upset! The day I don't have a soul, you will prove that I am a privilege for you!" My head is bowed, my body is shaking. I feel that her words cut my heart, but I could not say anything to her. When I he

Standalone post1,888 words

?ADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ?AYA

Tsaye nake a farfajiyar gidan mu, littafi a hannuna, ina kokarin kammala wani assignment kamar yadda na saba. Har na fara jin bacci yana mamaye ni, sai naji murya daga cikin kicin.

"Wai Ramlah! Aikin naki ne har yanzu ba zaki zo ki karasa mana abincin ba? Kinsan Baba Zuwaira batanan fa!"

Cikin ?acin rai na lumshe idona, na rufe littafina ina turo baki waje. "Mumy wallahi nagaji da kama mata aiki. Ki samo wata yar aikin mana." Na fada cikin raina, abace.

Tana jiyo shigowata sai kawai tayi dariya, tana fadin, "Allah ya shiryamin ke yanzu Ramlah. Zo kishige, abbanku zai shigo yanzu. Kuma kin san kamain yayanki su dawo su damemu da tambayoyi. Ina abincin?"

Na kame kaina. Na san dai wannan itace rayuwata. Amma yau ita ce kishiyar mahaifiyata da na koma ?ar?ashinta... Kuma komai take so, to dole ne in bi.

A wannan lokacin ban san cewa wannan karamin gajiya da kuka nake yi yau, shine mafari na babban juyin rayuwa da zai sauya duk wata mafarkina ba.

A dakin girki na shige ina jan hijab dina, na tashi girki kamar wacce ta saba da wannan rayuwar tun daga haihuwa.

"Ramlah ki wanke kayan kubewa nan, sannan ki ni?a tumatir din. Idan kika gama ki daka garin yaji, amma ki tsame rabin, kin san Abban ku baya cin mai yaji sosai,"

Wannan kalaman nata sun fi sau goma a kullum, haka kuma yadda take kokarin nuna kamar kulawa take yi, alhali dai ni na fi kowa sanin cewa ina da matsayi na daban a zuciyarta.

Ban gama daka garin ba sai naji sallamar Abba, wato mahaifina. Da sauri ta fito daga kicin tana dariya, "To Alhaji, sannu da zuwa! Yauwa gwara ka iso da wuri, dama muna shirin kammala abinci." "Sannu da zauwa abba." Kallona yayi yana dan nazari sai naji yace " Allah yayi Albarka Ramlatu."

Ina jin umma tana amsawa. Na juya daga mashin na daka yajin, na cigaba da aikina.

"Wai Ramlah, ba zaki yi sauri ba?!" Muryarta ta cika gidan gaba ?aya. "Ni wallahi idan nasakaki aiki kamar ina miki dole, narasa dalilin da yasa ki ke ta bata rai! Ranar da babu raina zaki tabbatar gata nake miki!"

Kaina na sunkuyar, jikina yana rawa. Ina jin har kalmarta ta sare zuciyata, amma ban iya ce mata komai ba.

Sai jin muryar Abba nayi, ya shigo cikin ?akin girki da sauri kamar wanda ya jima da sauraron rikici. "Me kuma ke faruwa ne?! Wai Ramlatu har yanzu kina ta nuna rashin jin da?i akan ayyukan gidan? Nasan tayi hakan ne dan Abba yaji!"

Yana ?aga murya sosai, fuskar sa cike da ?acin rai.

"Aikuwa sai na ?auki mataki. Yarinya shekara goma sha biyar idan ba ta iya girki ba, me zatayi? Duk irin yadda Zainab ke sangarta ki, amma ke kullum sai kin nuna mata kamar ba diyarta kike ba. Wallahi banason haka Ramlatu, zamusa kafar wando ?aya dake."

Cikin rawar murya da kuka nace, "Abba kayi hakuri... Mumy kema kiyi hakuri... bari na karasa."

Abba yana tsaye yana cigaba da yi min fa?a, kamar zan zubar masa da mutunci a ido. Kowane kalma nashi kamar ?aya ce a kunnena, zuciyata kuwa kamar ana mur?ushe ta da hannu.

Cikin gaggawa Mumy ta katse shi, tana cewa da ?arfi "Haba Abban Ramlah! Ka daina yi mata fa?a haka. Wallahi Ramlah diyata ce kuma ba ta ta?a nuna min bambanci ba. Yarinyace fa! Waye bai yi kuskure a ?uruciya ba?"

Tana karasawa da hawaye a idonta, sai ta juya gareni. "Allah ya shirya min ke Ramlah... Allah ya sa ki yi albarka. Amma meye na kuka ke kuma?"

Na saki hawayena a hankali, ban iya ce mata komai ba. Kalmar "diyata ce" kawai ke yawo a kunne na kamar mafarki, kamar ?arya.

Sai Abba ya ja wani mugun tsaki ya ce, "Dama ai ke kike sangarta. To ku cigaba. Kuyi dai tayi. Ku kawo min abinci kawai, ni zan sake fita."

A gaggauce na kammala duk aikace-aikacen gidan na jera abinci a dining kamar yadda aka saba, na share ?asa, na yi wanke-wanke. Jikina duk ya gaji. Test ce dani gobe a makaranta, amma karatu ya zama abu na ?arshe a raina yau.

Ina kwance a ?akina, lokacin ya kusa ?arfe goma na dare. Na jingina da gado, ina shirin rufe idona sai na ji ?ofar ?akin ta ?an bu?e.

Mumy ce. Ta shigo da fara'a a fuska tana cewa

"Ramlah, ba zaki je kici abinci ba? Yanzu Ramlah, damuwa kike son saka min ne? Ba kya so na ji da?i kuwa?"

Ta karaso kusa da ni tana bubbuga cinyata cikin tausayi. "Haba diyata, ai aikin ya ?are. Gobe Babah zai dawo, kuma kinsan yadda nake son komai ya kasance lafiya. Taso yar albarka, mu ci abinci."

Cikin shiru na dago idona, zuciyata na yi min yawo. Idan ta nuna ?auna irin wannan, sai in manta cewa ita ce take kallona kamar ba kowa ba da safe. Sai in ce "ko da gaske take?" ko kuma "haka kawai take so in ji da?i yanzu ne?"

Kafin in ce komai, sai na ji muryar Abba daga tsakar gida "Takawo min ruwa! Ina jin kishirwa."

Na fito falon gidanmu cikin gajiya, na zuba abinci akan tebur. Ina cikin aikin naji muryar Abba da Mumy daga ?aki suna hira akan dawowar Yaya Billy. Ita ce babbar yayata kuma ni ce auta a gidanmu. Mu hu?u ne yaran gidan:

Yaya Abbas shine babba. Yana da shekara talatin da biyar (35). Shi yana da aure da yara biyu, yana zaune lafiya da iyalinsa.

Sai Yaya Usman, wanda bai da?e da yin aure ba. Shekararsa talatin (30). Shi kuma yana sona sosai, har nakan ji kamar ciki ?aya muka fito dashi saboda yadda yake kula da ni.

Sai Yaya Billy, wacce suke magana kanta yanzu. Ita tana da shekara ashirin (20). Tana karatu ne a Abuja a gidan abokin mahaifina, wanda ake kira As'ad. Wannan As'ad babban mutum ne kuma ?an gidan Sarki ne, saboda haka kowa yana girmama shi sosai.

Ni kuma ni ce ?aramar gidan. Ni ka?ai mahaifiyata ta haifa, kuma ta rasu tun ina shekara biyu da haihuwa. Na taso a hannun Mumy, wacce take rike ni tamkar ita ce ta haifeni. Duk da cewa tana sakani aiki sosai wani lokacin har da fada, amma gaskiya tana sona kamar yar da ta haifa.

Sai dai Yaya Billy akwai matsala da ita. Tana sona, amma tana da girman kai sosai, kuma tana da rashin ha?uri. Wani lokaci idan na yi mata wani abu sai ta nuna fushinta. Gaskiya tana bani haushi sosai, amma ba zan iya fa?a mata ba saboda girma da take min.

Mahaifinmu kuma mutum ne mai tsauri da ?a'idoji. Shi baya son wasa a cikin gidan, saboda haka kowa yana bin dokokinsa. Wannan ne yasa muka tashi cikin nutsuwa da hankali.

A haka rayuwata take tafiya, amma duk wahalar da nake sha, ina godewa Allah domin ban rasa gata ba.

Ina zaune a gefen kujera har yanzu, gajiya ta lullube ni amma ban da niyyar kwanciya ba. Sai na ji Mumy ta ce da fara'a, "Ramlah, tashi ki je ki kwanta mana."

Abba yana kallona daga gefe ya kar?a, "Haka ne, tashi ki huta."

Sai na zaro ido kadan nace, "Abba, ai banason kwanciya yanzu saboda ban da?e da cin abinci ba."

Mumy ta dariya tace, "Sannu uwar mata! Idan kina magana sai a rantse babbar mace ce. Abban Ramlah, ka daina bamu dariya fa. Kada muyi tumbi ko auta."

Sai muka fashe da dariya gaba ?aya. Cikin shagwa?a nace, "Mumyta, Allah ya ?ara miki lafiya. Abba, good night." Na mike na shige ?aki da murmushi.

Ina shirin rufe ?ofa sai na jiyo Abba yana cewa da Mumy "To ai dole tayi iyayi, rainon Zainab ce fa... uwar magana."

Mumy ta daga hijab dinta tana bin shi da dariya, "Au! Sharri zaka min kenan, Abban Ramlah? To bari in biyo ka zuwa sama!"

Washegari tun da na idar da sallar asuba, na kama aikin gida kamar yadda na saba. Daman doya da kwai nayi niyya a yi, don haka na fara da gyara gidan, sannan na dafa tea cikin sauri. Na diba nawa na kai dining, sannan na dafa koko saboda nasan Abba ya fi son koko fiye da shayi.

Kuna ganina kamar ?arama, ko? Abba kullum yana cewa shekaruna ba su fi goma sha biyar ba, amma ni yanzu Allah ya kai ni 16 years. Kuma gaskiya, duk aikin gidan nan babu wanda ban iya ba - daga girki, tsafta, har ma da kula da kowa.

A haka ma ina SS2 yanzu a makaranta. Mumy kuwa, gimbiya ce ta gaske. Wayayyiyar mace ce wadda idan kana tare da ita, sai ka rinka dariya da mamaki. Wayo da iya magana? Ai daga gareta na koya. Ni da Anty Billy, wallahi ba za a iya kayar damu da magana ba.

Da na ga karfe 7 na kusa, sai na kunna turaren wuta a gidan domin kamshi. Na huce da wanka, na fito na shirya cikin uniform dina.

Ni ba fara bace sosai ba, amma fatar jikina na da haske. Ina da kyau irin wanda ba sai a ?yale ba. Ina da hanci mai kyau, idanuwa da kyau, ga baki ?arami, mashaa Allah. Jikina kuwa? Ai ko bra bana sawa. Tunda Yaya Billy ta fara siyamun kayayyakin da masu tsada ke amfani da su, jikina ya canza - ya yi kyau, ya yi laushi, ya kara "fresh".

Na shirya lunch box dina, na ha?a komai, sai na haura sama inda na tarar da Abba yana lazumi kamar kullum. Mumy kuwa, ai bata tashi da wuri - sai 9.

Na gaishe shi, ya amsa da fara'a. Ya bani 500, sannan ya dubeni da murmushi yace:

"Ramlah, ki rike mutuncinki. Ki yi karatu sosai. Ki zamo mace mai daraja."

Ina fita harabar gidanmu da jakata a hannu, sai na tarar da Malam Idi, direban gidanmu, yana gyara motar. Na gaishe shi cikin fara'a:

"Ina kwana Malam Idi."

Yace, "Lafiya lau Ramlah. Ya gida?"

"Alhamdulillah," nace, "don Allah ka wuce da ni gidan Babah kafin makaranta."

Yace, "Ba damuwa," sai muka tafi cikin sau?i.

Cikin kankanin lokaci muka isa. Da na sauka, sai na hanzarta shiga gidan. Babah, matar da ke aiki a gidanmu da daddare, tana zaune akan tabarma. Na gaisheta cikin nutsuwa:

"Babah, lafiya kuwa? Me yasa baki dawo aiki ba ne?"

Sai ta dubeni da hankali tace, "Ai Mumy ce tace na huta, tunda ga Ramlah a gida zata rinka taimakawa."

Na yi shiru. Ban ce komai ba.

"Mumy ce tace haka?" Sai na sake tambaya a raina. Na tuna yadda jiya da dare ta ce min "ki je ki kwanta, kin gaji," amma yau ga Babah a gida tana hutu ni kuma zan rika ?aukar nauyin komai.

Babah tayi murmushi, irin nasu na manya, ta ce: "Eh to hakanne, ai yanzu kin girma."

Na danyi murmushi shima, amma zuciyata cike take da tambayoyi da ban da amsarsu.

"Me Mumy take nufi da haka? Me yasa komai sai ni?"

Ban jima ba, sai muka yi sallama. Na koma mota muka wuce makaranta. A cikin motar nayi shiru. Zuciyata cike da kokonto. Ban gane kan Mumy ba, wallahi.

Wasu lokuta tana nuna ?auna kamar uwa, wasu lokuta kuma kamar ba ta so na huta ko na numfasa.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH