
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 4
..." Omar said to Haisam, who was all focused on Ousmane's information. His eyes, which were slightly soft, raised a little. His hands are in his pocket. The results of the DNA test given by Dr. Na'eem to further confirm the relationship between Almaz and Ajani. He found the doctor, who has a good relationship with the security authorities of Ethiopia Baice didn't sign anything, he opened it and looked at the information. He was told that he would get it. All the documents were written on the top of the document.
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 04*
A nutse dukkaninsu suka zauna,ya kuma maida hankali ga oustaz Ousmane suka gaisa,sannan ya fara bibiyar yanayin karantarwar da ya dauki nauyin ya dinga yiwa ahmad da Muhammad(almaz da jinjiri).
A nutse yake sauraren bayanan Ousmane,yana gyada kai a hankali. Wato lamarin ubangiji girma gareshi,duk da sun datse dukkan rayuwa daga gun muhammad amma hakan bai sanya ya tashi a wata fandararriyar halitta ba. Yanayin yadda Ousmane ke masa bayani sai ya dinga duban fuskokinsu a hankali. Dukkaninsu suna da wata baiwa ta kaifin basira saurin fahimta da daukan abu,abinda ya yiwa haisam dadi kenan,ya kuma tabbatar masa komai zaizo musu da sauqi har fiye da yadda yake zato.
Kwanakin barinsa agadez ne kawai yakejin zasu haura,wasu kwanaki bakwai din yana zaton suna iya qaruwa,don yanason kafin yabar agadez ya kafa harsashi......ya kafa nakiyar da zata tarwatse da mammina dama dukkan wanda yake rab'e da ita.
"Dr Na'eem ya qaraso fa" Omar yace da haisam wanda dukka hankalinsa yake kan bayanan Ousmane. Idanunsa da sukayi wani irin laushi ya daga kadan.
"Ka qaraso dashi" Ya amsa yana maida dubansa ga oustaz Ousmane.
"Zanga baqo,kuna iya ci gaba,bayan nan zan gansu daya bayan daya"
"Mintuna goma ma suka rage mana lokacin tashi yayi......sai kuma karatun dare" Oustaz Ousmane ya fadi.
A nutse haisam din yake bin wata qofa da zata sadashi da wani parlor din na daban,ya sake zube hannuwansa a aljihun wandonsa yanajin yadda jikinsa yake amsawa. Results ne na DNA test da ya bayarwa Dr Na'eem din don qara rufe dukkan sauran hojjin da kuma sake tabbatar da nasabar almaz da sultane.....muhammad kuma da ajani.
A tsaye ya samu likitan,baqi kakkaura kuma giant ba'abzine sosai wanda yake da kyakkyawar alaqa da hukumomin sirri na tsaro na qasar Ethiopia. Hannu suka bawa juna kafin kowannensu ya nemi gurin zama,sannan Dr Na'eem din ya miqawa haisam wasu takardu.
Baice komai ba ya sanya hannu ya karba,ya bude ta farko yana duba bayanan. Bayanan dai da zuciyarsa keta gaya masa ne na za'a samu.....su dinne kuwa rubuce saman takardar. Dukkanin qwayoyin halittar muhammad na ajani ne......komai na gwajin yazo sak da sak da ajani dama duk wani yaro daya fito daga tsatsonsa.
Ta baya ya miqawa omar takardar,ya bude sakamakon ahmad almaz.
Wannan karon wani huci ya sauke,ya ajiye takardar a gefe yana daga risunannun idanunsa yana duban Dr Na'eem
"Na gode qwarai da qoqarinka na kawo gwajin haka da wurwuri,ina fata nan gaba idan wata buqatar ta sake tasowa zan samu goyon baya". Murmushi Dr Na'eem yayi yana duban haisam
"Aiki dakai wata babbar alfarma ce ga mutum........a shirye nake koda yaushe da amsa kiranka". Sai suka sake bawa juna hannu,Dr Na'eem ya miqe yana daukan briefcase dinsa.
Zagayowa omar yayi wani rudani yana bayyana saman fuskar sa,ya zauna sosai gaba haisam yana shafa sumarsa yana jin kwanyarsa na rikicewa.
"Ya akayi dukka zatonka da hasashenka suka zamo daidai?.....wacce irin matace wannan mara imani?,wannan aikin......koda namiji ne ya sarqa wannan qullin lallai ya cika baqin azzalumi.....waye yake raba uwa da 'ya'yanta idan ba Allah ba?......wanne irin zalunci ta yiwa wannan baiwar Allahn?"
"Ka dauka a banza Allah ya jarabceta itama ya hanata haihuwa?" Haisam ya furta da wani laushi yana qoqarin controlling kansa. Ya sani inde wannan fushin yaci gaba da masa jagora......tabbas zuciyarsa ba zata bashi goyon baya ya yiwa mammina yanayin kamun daya shirya zai mata ba.
*A K H N A N*
Karo na farko a rayuwarta data fara lura da irin girma da tsaruwar da dakin litattafan mahaifin nata ke dashi,duk kuwa da cewa tunda ta taso a gidan tasan da zaman gurin,amma ko sau daya bata taba mararin shiga don buqatar karatu ta qashin kanta irin wannan ba.
Yau sai gata kace kace cikin dakin karatun sultane din,da wai kuma buqatar yin karatu......karatun da a yanzun takejin ra'ayinta ya karkata sosai a kansa.
"Wanne littafi kike buqata ranki ya dade?" Mai hidimar kula da dakin karatun ya tambaya cikin girmamawa. Cikin izzar nan tata ta numfasa kadan. Me zata ce masa tana buqata?,littafin da zai nuna mata inda sheikh muhammad haisam ke kwaikwayon dabi'unsa?,ko kuma zatace masa tana sha'awar karanta halaye da dabi'u manzo saboda yawaitar jin abubuwa daga bakin haisam?,ko kuma dai dukka a ture wannan.....dabi'un wani d'a namiji takeson haskawa da kyau cikin kanta.....d'a namiji......malamin addini....wanda ya karya komai da komai nata......ya rushe duk wani tsari nata da komai?.
"Tarihin rayuwar manzon Allah.......rayuwarsa da mu'amalarsa da kowa" Tayi maganan kaman wadda ta zabi jera kalaman kafin ta furtasu.
"An gama" Ya fadi yana juyawa da dan hanzarinsa zuwa inda tarin litattafan ke ajiye jimgim amma a tsare kwaba bayan kwaba.
Zamanta ta gyara sosai tana harde hannuwanta a qirjinta. A nutse da kuma wannan blue eyes din nata takebin dakin gaba daya da kallo. A hankali sai taji yadda littattafai suka cika dakin da wani irin tsari abun yana burgeta. Ba zatace ga abinda akeji a karance karance ba,idan ka dauke karatun daya wuce na magazines da newspaper da zataga sauka da tashin hannuwan jari ba.
"Ga wadannan Allah ya taimakeki" Ya furta yana ajiye mata books din a gabanta.
"Sunyi?" Ya tambayeta yana fatan zabin nasa ya burgeta.
"Kana iya tafiya,ka shaidawa birra ta zama a kusa" Ta fadi tana aza kyawawan blue eyes dinta saman cover din littafin farko.
"Le prophéte de I'Islam,sa vie d'aprés les sources les plus anciennes" Sunan marubucin ta duba
"Martin lings" Saita sauke zuwa littafi na biyu.
"Muhammad viedu prophéte" Ta sake duba author din.
"Taariq ramadan" Ta sake zameshi qasa tana duba na uku.
"La Vie du prophéte muhammad na ibn kathir" Guda daya ta zame a ciki,ta ajiyeshi gefe sannan ta gyara zamanta sosai ta fara duba wallafar taariq ramadan.
A nutse takebin littafin da aka wallafashi da yarenta na faransa,cikin qasa da mintuna ashirin tarihin ya fara shiga jikinta sosai. Komai na cikin tarihin ya soma daukan hankalinta,a hankali ta soma jin wani girma da karramawa na musamman da kima na manzo yana shigarta.
Sam sam komai da takeji cikin tarihinsa da mu'amalarsa bata taba saninsu ba,bata taba sanin da akwaisu ba. To yaushe ma ta zauna tayi wani karatu daya shafi wannan bangaren ballantana taci karo dashi?.
Batasan lokaci yaja haka ba,saida taji sallamar birra tana neman iznin qarasowa inda take zaune.
Ajiyar zuciya ta saki,tana zare idanunta daga kan littafin da takejin ba zata iya tashi a wajen ba saita kammalashi duk da yawansa,ta dora kan birra.
Tsaye birran take dauke da tea tray daya bawa cups da kayan saman kai daman zama sosai a samansa,wani irin tea tray da koda tsautsayi yasa wani abu ya zube bazai zuba a qasa ba ko a jikin me amfani dashi ba,wani abu dake maqale daga qasansa ya tare wannan.
Idanu ta zuba mata ba tare da tace komai ba,yayin da birra din ke dubanta da girmamawa
"Allah yasa ban katsekk ba......na kawo miki wani abune,bansan ko zaki buqata ba" Kanta ta daga mata a hankali da sign din daya bawa birra daman fahimtar tana nufin ta qaraso ne. Saita tako a hankali tana ajiye tray din saman table din da akhnan ta ajiye hannuwanta akai.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Fidda butar shayi daya da cup tayi tana qoqarin zubawa akhnan shayin,saidai kuma muryoyin da suke jiyowa daga wajen library din ya dauki hankulansu gaba dayansu.
*MAMMINA* Dukkanin idanuwanta ta zubewa hadimim tana kallonsa,kallo iri daya amma mai dauke da tarin ma'anoni da mamaki zallarsa.
Wayeshi cikin hadimai?,batasan fuskarsa ba sam........abu mafi muni da firgitarwa ita GIWA ita GIWAR AGADEZ?......GIWAR SULTANE?......yau ita akewa iyaka da shiga wani sashe na masarautar agadez?. Cikin yaye yayen Mafarki ne?,ko kuma zahiri ne idani biyu take?.
Wanne irin lalacewa tayi da har wani wulaqantaccen hadimi zai tsaya gabanta?,zai tsaya gabanta yana gaya mata.....yana bata labarin wani qasqantaccen malami dake ci qarqashin ALFARMARSU ya hana kowa zuwa gurin da akhnan din ke zaune har sai ta tashi?,ya hana kusantar inda take?. Akhnan din data raineta a tsakanin hannuwanta irin rainon da taga dama?. Akhnan din da ita keda alhakin yankewa komai da kuma sarrafawa cikin rayuwarta?,akhnan din da sai wanda taso ta girmama zata girmama?,sai wanda taso ta mutunta zata mutunta?,sai wanda ta lamuncewa sannan zatayi mu'amala dashi?.
"A kiramin me wada" Ta fada da wani irin zafi da mamakin da har yanzu kanta ya gaza daukan itace yau a tokare a hanya,an hanata qarasawa zuwa ga akhnan.
"Ranki ya dade.....koda me wada yazo ba abinda zai iya canzawa" Ya fada a tausashe yana qoqarin bata girmanta gami da rusunar da kansa qasa.
"Wanene kai!.....nace waye kai don ubanka?,waye ya tsaya maka?" Tayi maganan da hargagin daya zama sanadin isar tarwatsin ga kunnuwan akhnan da birra dake cikin dakin karatun.
"Gaba salamun baya salamun....Allah ya huci ranki,kibi komai a hankali karki tarwatsin da zai janyo hankulan wadanda basusan ma me yake faruwa ba.......yaduwar labarin kamar raguwar darajarki ne a idanun kowa". Tafisu ta fada da murya qasa qasa.
Waiwayowa tayi tana zubewa tafisu wani irin kallo,yadda tafisun tayi mata magana saiya mata kama da wanda ke mata gatse......sao takejin kamar akwai wani sauti cikin muryar tafisu,to amma kuma can cikin kalamanta akwai GASKIYA,ba zataso kowa yasan wannan tozarcin ba sam sam,don haka ta maida dubanta ga hadimin,saidai kafin tace wani abu me wada ya qaraso.
"Yaushe ni giwa na zama wulaqantacciyar da ganin d'iyata ma saida izinin wani maras darajan malami?" Maganan ta yiwa me wada zurfi da yawa,to amma ya sani,a halin da ake ciki yanzun ko sultane bazai zame mata tsanin da zataga akhnan kai tsaye ba yarjewar haisam ba.
"Kiyi haquri Allah ya baki yawan rai......ba wata hanya ta tayar da maganar sheikh muhammad haisam a cikin gidan nan" Idanu ta zubawa me wada cikin madaukakin mamaki,yaushe abubuwa suka girmama haka ita zaituna tana zaune?,yaushe zamanin da bawa da hadimai dama baqi zasu iya jayayya da umarninta gami da tayar da hukuncinta?.
"Karkice zakici gaba da jayayya dasu,ba tsaranki bane giwa......abu daya ya rage,kin isa da gimbiya,kisa a shaida mata zaki shigo gurinta,koda basuso idan ta aminta da haka dole su baki dama".
"SU BAKI DAMA" maganar ta maimaitu cikin kanta ta kuma sanyata hadi wani abu me tauri cikin maqoshinta. Yau ita ke neman DAMA cikin masarautar?,damar da ita ke rarrabata ga wanda takeso?,ta kuma karbeta daga hannun duk wanda hakan yayi mata?.
"Ku shaida mata inason ganawa da ita" Tayi maganan tana jim alwashin cewa.......yadda ya soma da qoqarin maidata maqasqanciya bayan ya fara karbe ikon zartarwa da fada aji daga hannunta......lallai ba shakka saita sanya ya dandani radadin tozarci......saita sakashi yabar agadez a mafi qasqancin halitta......barin da bazai sake koda marmarin rubuta sunan yankin ba ballantana ya kalla ko yayi mararin shigarsa.
Bai musa ba,ya kuwa aika daya daga cikin masu tsaron gurin. Daidai lokacin da akhnan din ta maida labulen ta rufe... Labulen daya zama iyaka tsakaninta da gano fuskar mammina.
Haka kawai takejin ta fice fit daga rayuwarta,haka kawao takejin bata buqatar karbar hanyar rayuwa daga hannun kowa.....haka kawai takejin bata buqatar shawarwari masu dogon sharhi ko fashin baqi......haka kawai takejin ta jefata rami ta goga mata tabon da har ta tsufa bazai shafe daga rayuwarta ba. Saki....sakinma irin na wulaqanci......sakin aure cikin kwanaki uku kacal da daura auren?.
"Bana buqatar ganawa da kowa a yanzun......ina da abubuwa masu muhimmanci da nakeyi" Abinda ta fadawa birra kenan,ita kuma birra ta juya ta isar masa da saqon......shi kuma ya juya yana shaidawa zaituna bisa tarin qwarin zuciya da sauyin dabi'u da aka musu na FADIN GASKIYA YADDA TAKE daga rainon sheikh Muhammad haisam.
Tamkar gunki haka ta tsaya a gurin cak,idanunta suna qanqancewa zuwa ciki ciki,tana jin wani tarin qasqanci da tozarci yana baibayeta.
*Akhnasaim tales*🤍
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽