
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 48
..... my body. It was like a wind hit me from behind. Everything stopped. It's like life stopped moving. I lost my breath. I was looking at Alhaji Munzali, my mouth was open, my heart was pounding. I opened my mouth to say something but no voice came out. My eyes have lost sight. My eyes were wet, confused. I felt like I was going to explode. Khalil? I said slowly. I just had to shout loudly A yes! Khalil is not dead! Please tell me it's fake! Everyone turned my head. Before anyone could get up, I let out a loud scream. I grabbed my hijab and pulled it off, I knelt on the ground, and I fell on the ground like a tree had been cut down, I fainted. In front of everyone. People started screaming. One held my hand, the other looked into my eyes. She lost her mind! someone said. Quickly call a car, take him to the hospital! Alhaji Munzali quickly picked up the phone and called Abba. Bring a car! Ramlah said she couldn't move. How scared Billy, Mumy and some of the family members were. It seems that it was better than they expected. Mumy couldn't say anything, her eyes were fixed on me.. When I fell in the greeting house, I didn't know myself anymore. I fell to the ground like on
Muna zaune a gefe, nayi shiru kamar ba ni ba. Na dafe kaina saboda ciwo yana ?ara girma. Duk da magungunan da na sha da safe, kamar ba su aiki. Idanuna suna sauka da wahala, zuciyata kuma cike take da abubuwa da yawa. Har yanzu nake jin kalaman gulmar da suka yi a kusa da ni, suna yawo cikin kunne na kamar amsa.
Yaya za a ce gidan mutuwa ya koma gidan gulma? Gidan da za a tuna da mutuwa da addu a ya koma wurin cin zarafi da wulakanci?
Wannan tambaya ce kawai da zuciyata ke maimaitawa. Sai kuma naji muryar maza suna shigowa harabar gidan sunata gaida mutane suna gaisuwa..
Alhaji Munzali ne kawun su Abba, babban mutum a cikin yan uwan Abba. Idan ya shigo, kowa yana nutsuwa, domin mutum ne mai daraja. Amma yau kam, fuskar sa ta bayyana damuwa. Kamar wanda ya jima da kuka.
Yana shigowa, sai kawai ya kalli mutanen gidan. Kowa yayi shiru. Sai ya ce da murya mai rauni Khalil ya rasu. Allah yayi masa rasuwa yanzu.
Wani dumi ne ya zube min a kai. Wani sanyi mai ?ara daka zuciya ya ratsa gabadaya jikina. Kamar wata iska ta buga ni daga baya. Komai ya tsaya. Kamar rayuwa ta daina tafiya. Na rasa numfashi. Ina kallon Alhaji Munzali, baki na a bu?e, zuciyata na harbawa da ?arfi. Na bu?e baki ina so in ce wani abu amma babu muryar da zata fito. Idona ya raina gani. Idanuna sun jike, sun rikice. Na ji kamar zan fashe. Khalil? Na furta a hankali.
Sai kawai niyi wani ?ara da karfi A a! Khalil bai mutu ba! Don Allah kuce karya ne! Kowa ya juya kaina. Kafin wani ya iya tashi na saki ihu mai karfi.Na kamo hijabi na na fizge, na dur?usa kasa, sannan na fadi a kasa kamar an sare itace,Na suma. A gaban kowa.
Mutane suka fara kururuwa. Wata ta kama hannuna, wata ta duba idanuna. Ta fita hayyacinta! wani yace. Da sauri a kira mota, a kaita asibiti! Alhaji Munzali ya dakko waya da sauri ya kira Abba. Ku zo da mota! Ramlah ta fa?i bata motsi.
Yaya Billy da Mumy da wasu daga cikin dangin gidan suka tsorata. Kamar abin ya fi yadda suka zata. Mumy ta kasa cewa komai, idonta ya ?afe a kaina..
Lokacin da na fadi a gidan gaisuwa, ban kuma san kaina ba. Na fadi a kasa tamkar wadda aka cire rai. Kamar wani iska ya kwashe ni, ya tafi da zuciyata zuwa wani wuri nesa. Komai duhu. Komai shiru. Ina cikin wata irin ?asa da ba na iya kiran ta duniya ba.
Gaba daya jikina ya mutu. Na shiga doguwar suma. Likitoci suna ta kokarin dawo da ni hayyacina. A gaggauce aka kaini asibiti cikin mota, aka shigar da ni zuwa gaggawa (emergency ward). Na kwanta a gadon asibiti, hannaye na kwance, numfashina a hankali. Kamar numfashin wanda ke cikin mafarki, ba tare da mafarkin yana da dadi ba.
Likita ya dubi nurse yace, Ta shiga doguwar suma. Amma har yanzu zuciyarta na bugawa. Jikinta na da rauni sosai.
Bayan kusan awa biyu, na fara motsawa kadan. Na bu?e ido a hankali. Ina duba sama. Idona na yawo, amma zuciyata a cike take da wani irin zafi da na kasa fassarawa Sai na saki wani irin ihun da ya girgiza dakin
Khalil! Khalil! Don Allah kar ka barni! Ka dawo! Khalil! Na sanya kuka. Na fara jijjiga jikina kamar ina yaki da wani abu da ba a gani. Nurse ta rike ni da sauri, ta kira likita, ta kira family dina da ke bakin asibiti. Abba da Mumy suka shigo. Na dago kai na ina kuka, na ce, Yace min zai dawo. Me ya sa bai dawo ba? Don Allah ku gaya min ba gaskiya bane Na sake fa?i. Likita ya duba ni, ya ce da nurse Ta rasa jini. Blood pressure dinta ya sauka ?asa sosai. Sai an sanya mata jini cikin gaggawa. Nurse tace, To yanzu sai mu fara gwajin wanda ya dace da jinin nata. A gaggauce aka fara duba wanda jinin sa zai dace da nawa. Ina kwance a gado, ina cikin ciwo da rashin hayyacina, amma jiki na yana kokarin faduwa gaba daya. Wata nurse ta zo ta dubi Abba Dan Allah malam, akwai wani daga cikin yan uwa da za mu iya amfani da jinin sa? Idan babu, za mu je asubuti mu siya. Abba ya ce, Ku fara gwada jinina dana kanina . Aka fara da su. Sakamako ya fito bai dace ba. Aka gwada na wani daga cikin dangin abba suma bai dace ba. Har ana tunanin sai an je asibitin gwamnati don a samo jini cikin gaggawa.
Sai likita ya ce, Mu kira Dr Hari shima babban likitane Da aka duba nasa, sai aka ga jinin sa ne ya dace da na Ramlah.
Cikin sauri aka saka mata allurar kariya, aka cire masa jini, aka soma shiryawa don sanyamin.
Mumy na zaune kusa da gadon asibiti, tana ri?e da hannuna kamar tausayinta ya kai kololuwa. Ita ce ke girgiza kai tana cewa, Ya Allah ka tausaya wa Ramlah. Zan rasa komai idan na rasa ta.
A gaban mutane sai tana share hawaye, tana nuna kamar tafi kowa damuwa. Har mutane suna ce mata, Mumy ki kwantar da hankali. Allah zai bata lafiya. Sai ta ce, Ramlah rayuwata ce. Ko ban nuna ba, ina sonta fiye da rai na. Amma a cikin zuciyarta, ba haka take ji ba nasani. Abba ya ce da ita, Ki zauna anan da ita, ni zan je ayi jana izar Khalil.
Ta ce, To, Allah ya kar?e sa ya yafe masa ya gafarta masa. Ka je, zan tsaya da ita. Sai ta mayar da murmushin tausayi ga mutanen da ke kusa. Amma da aka fita, bayan mutane sun bar dakin, sai tace Yanzu ai rayuwar ki tafara lallacewa ramlah sai kin zamana baki da gata koda na sauro ne sai tasanya dariya. Allah ya ?auki abin da zai jawo min matsala.
Sai tayi wani siririn dariya.
Ina kwance Jini yana shigowa jikina a hankali. Amma har yanzu ina cikin doguwar suma. Nurse suna lura dani.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA TARA
Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435
Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********