
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 47
.....can you? What happened? What pain does he have if he is not allowed to visit? He took a small breath and said, I asked the nurse. She said it was simple, but she could not give detailed information. But she said he was getting a lot of attention. Easy? I repeated in ?ara. It's easy but no one is allowed to see it? Why do they hide everything from us? My heart was pounding, my body was cold, and my head began to spin quickly as if I was going to fall. I just grabbed the wall so I wouldn't fall there. Musa came closer and said softly. Stay with us. he said. It's like you feel tired. I shook my head a little, tears were gathering in my eyes. By God, Musa, if something happens to Khalil, I will not be able to bear it. I have been dreaming of him since yesterday. Today, you are not allowed to see him. How easy is this? He was silent, he didn't say anything. He just sat next to me and looked at me with pity. I'm going to school, I said out loud. Our presentation is today, and I am in charge. Musa stopped and looked at me as if he would not believe. But I stood up and washed my face with water, took my hijab, and left. When we got to school, my heart was empty. I sat in the clas
Da safe nayi kokarin tashi duk da jikina na a mace. Har yanzu kaina yana ciwo fiye da jiya. Na sha Paracetamol da safe, amma sai ciwon ke kara karfi kamar ana jujjuya kwano a cikin kwakwalwata. Na kasa cin abinci sosai, sai tea kadan da biskit. Komai a jikina kamar baya cikin hayyacinsa zuciyata na tashi, gabana na faduwa.
Amma yau presentation muke da shi, kuma ban yarda na sake karatu ba. Public Administration muke karantawa, kuma ina cikin group ?in da za su fara gabatarwa. Na ?auki takarduna, na zuba su a jaka, nayi addu a, nayi shiru na jima kafin na fita.
Kafin na fita ne kuma Musa yazo. Bai shigo da fara'a ba kamar yadda ya saba. Ya tsaya a bakin ?ofa kamar wanda aka daka.
Ina wuni, yace da sassautaccen murya.
Lafiya Musa? Ka ga Khalil din? Na tambaye shi cikin sauri, zuciyata na bugawa kamar an tada karfe.
Yayi shiru. Yana kokarin duba idona, sai ya kauda kai. Wallahi ba su barni na ganshi ba. Wani babban likita ne yace ba zamu iya ganin marasa lafiya yau ba.
Na ce, To lafiya kuwa? Me ya faru? Wane ciwo yake da shi da har ba a bari ana ziyara?
Yayi karamin numfashi yace, Na tambayi nurse. Tace kawai da sauki ne , amma bazata iya bada cikakken bayani ba. Sai dai ta ce yana samun kulawa sosai.
Da sauki? Na maimaita cikin ?ara. Da sauki amma ba a bar kowa ya ganshi? Me yasa suke boye mana komai?
Zuciyata tayi raurau, jiki na ya yi sanyi, kaina ya fara juyawa da sauri kamar zan fadi. Sai kawai na kama bango domin kada in sulale a wajen. Musa ya matso yana fa?in inyi a hankali.
Ki zauna mana. yace. Kamar kina jin jiri ne.
Na kada kai kadan, hawaye na taruwa a idona. Wallahi Musa idan wani abu ya faru da Khalil, bazan iya jurewa ba. Tun jiya nake mafarkinsa. Yau kuma sai ace ba a bar ka ka gan shi. Wane irin da sauki ne wannan?
Yayi shiru, bai ce komai ba. Sai kawai ya zauna kusa da ni yana kallona da tausayi.
Zan tafi makaranta, na fada da karfi. Presentation ?in mu yau ne, kuma ni ke da jagoranci.
Musa ya tsaya yana kallona kamar ba zai yarda ba. Amma na mike tsaye na wanke fuskata da ruwa, na ?auki hijab ?ina, na fice.
Da muka isa makaranta, zuciyata babu da?i. Na zauna a cikin ajin da presentation ?in zai gudana, ina jujjuya takardun da ban ma san me ke ciki ba. Idanuna sun rame, kaina kamar an dora masa dutse. Amma ina iya cewa duk da haka, na tafi da ?wazo da nutsuwa.
Lecture ?in ya shigo cikin aji, ya duba lissafin wa?anda ke da gabatarwa. Lokacin da ya kira sunan group ?inmu, zuciyata ta buga. Sai na mike da ?arfin hali, na fito gaban class. Na bu?e laptop ?ina, na ha?a projector, na fara magana.
Amma ina magana, sai na lura da wani abu da ya dame ni fiye da ciwon kai. Lecture ?in yana kallona kamar zai cinye ni da idanuwa. Kallon da bana so, kallon da ban da bu?ata, kallon da ya sa nayi kuskure na karanta Public Admiration maimakon Public Administration.
Sai na tsaya cak. Na gyara. Na yi murmushi na dole, amma zuciyata cike take da fargaba da jin kunya. Sauran daliban sai dariya suka fara yi kadan kadan. Na ji wata wuta kamar ina tafasa a ciki. Na ci gaba da magana, amma ganin irin kallon lecture ?in ya fara damuna sosai. Ko dai yana kokarin cutar da ni ne kamar yadda wasu malamai ke yi wa wasu dalibai? Kamar yana daukar hotona da idanuwa.
Sai na kasa jurewa. Na kalli shi a ido. Ya danyi murmushi.
Subhanallah... Wannan murmushin fa na mutumin da yake kallonki ba don aikin ilimi ba, sai don wata sha awa ko mugun nufi. Kamar na fa?i kalma guda a nan gaban aji Sir, please stop looking at me like that.
Amma na ?yale. Na ci gaba da gabatarwa. Na dage da karfin zuciya, na kare abinda nake da niyyar fada, na zauna. Na kalli kasa, na ji ciwon kai yana kara tsananta.
Bayan na fito daga makaranta, jikina ya ?ara tsananta. Zazzabi ya tashi sosai. Kaina yana ?ara ciwo, jiki na yayi rauni. Na ?ara shigowa cikin gida da ?yar, amma na ji muryar Mumy a palour tana fada kamar kullum.
Ina gaya miki Billy! Wallahi sai dai ki fitar min da tsayayye a Samarin naki. Idan ba haka ba, sai dai ki fitar da kanki daga gidan nan! Kina neman ki jawo min bala i! Mara tarbiyya kawai!
Na tsaya a ?ofar palour, zuciyata na bugawa. Sai Billy ta tashi ta bar palon ba tare da ta ce komai ba. Ni kuma na yi sallama, na shigo cikin gida a hankali.
Mumy ko kallona bata yi ba. Kamar bata ganni ba kamar ba sallama nake ba. Na wuce cikin ?akina. Na kwanta ina jin jiki na kamar ana hura masa wuta. Na rasa ina zan saka kaina. Dakyar nayi girkin dare ina Sallar isha i na kwanta kwana biyu ko adduar bana iyayi saboda zazzabin dare dake rufeni.
Washegari da wuri nake da lecture dan haka da wuri na fita, Ina gama lecture na ?arshe da rana, jikina kamar ba nawa ba. Kaina na sarawa sosai, idanuna na juyawa, ?afafuna na rawa. Komai yana tafiya da ?yar. Jikina yayi rauni fiye da yadda nake tsammani. Na dan tsaya gefe a bakin titi ina satar numfashi, sai na ga chemist a can nesa kadan. Na tattara ?arfin da ya rage min, na nufi wajen.
Yaya lafiya? Cewar mai chemist din bayan na shigo da wata irin kwana da take nuna ba lafiya nake ba.
Zazzabi ne, ciwon kai, da ciwon jiki. Na fada cikin sanyin murya.
Ta duba min wasu magunguna, ta duba farashinsu sannan ta ce, ?8,000 ne gaba daya.
Na tsaya da baki a bu?e. ?10,000 ne kacal ke hannuna kudin da nake ajiyewa don wani abu da nake so nayi na kaina, abu mai muhimmanci. Amma yanzu lafiya ta fi. Ba zan iya hakura da magani ba.
Na dube ta, na ce To ki bani. Na ciro kudi na ba ta, na karbi magungunan, na fita da wata irin karyewar zuciya.
Ina shiga gida da magunguna a jaka, jikina a mace, sai Mumy tace daga saman bene.
Ramlah ki shirya da sauri. Za mu gidan yan uwan Abba. An yi rasuwa.
Sai da gabana ya buga. Zuciyata ta fara faduwa. Na daina motsi tsawon dakika biyu. Mutuwa kuma? Ko dai... Khalil?
Na ?an taka kadan, na ce a hankali, Waye ya rasu?
Ta juyo tana daure fuska tace, Kakar su Abba ce. Wacce take zaune can kusa da su.
Na sauke ajiyar zuciya, Allah ya jikanta.
Nayi shiru, na shiga ?aki a hankali, na canza kaya. Hijab na dogo na saka, na fesa turare, Ina fitowa sai muka hadu da Bilkisu a waje Na nufi gaban mota kamar yadda na saba. Nayi niyyar bu?e ?ofa na zauna. Sai kawai na ji tsawa daga Bilkisu Ke gidan ubanki ne ke kadai? Ko motar ubanki ce? Wuce can, ki shiga baya! Na tsaya, na kalle ta cikin mamaki da haushi. Amma na tuna tafiya ce ta gaisuwa. Na kasa cewa komai. Na juya na bude ?ofar baya, na zauna. Har sai da hawaye suka taru a idona amma na danne su.
Mun isa gidan cikin natsuwa. An sa kujeru a farfajiya. Muka zauna. Ana ta shigowa da ficewa, ana kar?ar gaisuwa.
Ni kuma na zauna a gefen Mumy, cikin nutsuwa. Magungunan da na sha sun fara rage radadi, amma ba su kawar da gajiyata ba. Duk da haka, na zauna cikin ladabi da kamun kai. Na rufe bakina, na sunkuyar da kai. Amma a lokacin ne wasu suka fara gulma daga gefena. Wata dattijuwa daga cikin yan uwan Abba ta fara magana da wata a kunnenta, amma duk inajinsu.
To Ramlah ce dai kinganta kamar yar labarawa ko dayake balarabiyar ce tunda uwarta haka take. dayake tafara zuwa makaranta mai shigen tsada da kudi fa. Amma naga kamar ba ta damu da Khalil ba. Yaron har yanzu yana jinya, amma ki kalleta ko aji?inta ko adan yatsanta ahaka kamar ta Allah sai munafurci.
Wata tayi dariya ta ce, Ai ni nasan dai babu yanda za ayi su yi aure. Dama ita ce ta rikita Malam dinnan. Tace wai Khalil bai dace da ita ba. Dan taga tanada kyau.
Suka sa dariya. Wani daga cikinsu ya ce, To dan tanada kyau sai tafara raina mutane?.
Na sunkuyar da kai. Na ?ura ido cikin tabarma. Na ma rasa wane hawaye ne nake kokarin dannewa. Gaskiya ba su san ciwon zuciya na ba. Maganar su ta fi zafin maganin da na sha dazu.
Suna ci gaba da zance. Ai idan ba masu kudi ba wannan yarinyar bata auren dangi tabbijan bakuganta ba kamar ita tayi kanta?.
Na ci gaba dayin shiru. Ko kallonsu ban yi. Ban ma motsa ba. Na ce a raina, Na ha?ura. Zan yi shiru, zan barwa Allah.Ina zaune, Bilkisu tana gefe tana kallona da idon ?iyayya. Har da girgiza kai tana dan gunguni. Idan na duba, sai ta kau da kai kamar ba ni take kallo ba. Amma nasan zuciyarta kamar wuta take yanzu ni ce kowa ke magana akai haushina take ji. Bilkisu ta dade tana jin cewa rayuwata bata dace da jin da?i ba.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA TAKWAS
Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435
Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********