
Post
KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 15
.....the kind of sadness that Hunaif breathed, but then he smiled at her and said; "Thanks my love." He leaned closer to her, planted a kiss on her forehead, before turning to put down his car keys and phone and go into the bathroom. He was entering the bathroom and when he came back he saw where the bathroom looked like there was a fight inside, he turned around and looked angrily and said; "What's this Zainab, can't you keep your environment clean and organized for once? Just take a look at this bathroom." He said while pointing in the bathroom, he said; "Was there a war there? Or was there a market there?" Zee burst into tears, saying; "Oh God, I'm three years old, now I'm looking forward to the wedding? It's been a week since my husband started talking to me like he's going to beat you. Oh God, bring me back." She said, bursting into tears. Looking at her, Hunaif was disappointed, he pulled away and entered the bathroom. He had to go to the bathroom before taking a shower and came out, he went into the closet and got ready in his long pants and shirt and came out, took his car key and went out. "Your food is in the dining room." Looking at her back, he wondered what she meant b
KOMAI YA YI FARKO
Page 15
Ana tashi daga match da ake bugawa, Hunaif ya kama hanyar gida direct cike da ɗoki, yana jin wani farinciki yau zai ci girki made by the woman he loves dearly, amma wani gudu ba hanzari ba, yana shiga gidan ya fara bin sitting room ɗin that's so disorganized da kallo, Zee ta saukar da throw pillows ɗin ƙasa ta kwanta ta yi kallo, a kasan ta bar filon da remote na TV, a gefe guda kuma ga kwanon da ta ci abinci a kan centre table, TV kuwa na kunne volume a ƙure. Girgiza kai kawai Hunaif ya yi, ya shiga bedroom, Zee na zaune akan gado tana cin pringles, ta yi wanka ta sauya kaya zuwa simple short gown, kayan da ta tuɓe yau sun samu arzikin kaiwa laundry basket, amma kan gadon bai yi kamar wanda aka gyara shi ba, sannan ga cup da ta sha custard akan table, gaban mirror ma da ta gama shiryawa bayan ta fito wanka ba ta mayar da abubuwan wajen zamansu ba, she just left the place scattered and unkept. Murmushi ta sakar wa Hunaif tace; "Welcome back sweetheart." Duk da irin ɓacin rai da Hunaif ya shaƙa, amma sai ya daure ya yi mata murmushi yace; "Thanks my love." Ƙarasowa kusa da ita ya yi, ya manna mata kiss a goshi, kafin ya juya ya ajiye car keys ɗinshi da wayar shi ya shiga bathroom. Yana shiga bathroom ɗin sai da ya dawo da baya ganin inda banɗakin ya yi kamar an yi yaƙi a ciki, juyowa yayi ya kalleta cikin fushi yace; "What's this Zainab, can't you keep your environment clean and organized for once? Just take a look at this bathroom." Ya faɗa yana pointing cikin banɗakin, yace; "Yaƙi aka yi a ciki? Ko dai kasuwa aka ci a ciki?"
Kuka Zee ta fashe da shi, tana faɗin; "Ya Allah na shiga uku, yanzu nawa kallar auren kenan? Sati guda da tariya amma mijina ya fara yi min faɗa haka kamar zai dokeni, Ya Allah ka kawo min ɗauki." Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka.
Kallonta Hunaif ya yi cike da takaici, ya ja guntun tsaki ya shige banɗakin. Sai da ya kimtsa banɗakin kafin yayi wanka ya fito, closet ya shiga ya shirya cikin dogon wando da shirt ya fito, key ɗin motarsa ya ɗauka zai fita, Zee dake kwance ta juya mishi baya tace; "Abincinka na dining."
Kallon bayan nata ya yi da mamakin what she meant by abincinsa na dining, kenan shi bai da darajar da za ta yi serving dinsa abinci kenan, or could it be gaskiyar da ya faɗa mata ne take wannan fushin. Bai ce mata uffan ba ya fita daga ɗakin. Single foodflask ya gani a ajiye a tsakiyar dining table ɗin, duk da Zee ta riga da ta ɓata mishi rai amma wani ɓangare na zuciyarsa na nuna mishi rashin kyautawar shi idan bai ci abinda ta dafa ba, saboda shi ya saka ta. Ƙarasowa gaban dining table ɗin ya yi, ya ja kujera ɗaya ya zauna, a sukwane ya janyo foodflask ɗin, yana buɗe kulan warin ƙuna ya doke hancinsa, cike da baƙin ciki da takaici Hunaif ke kallon indomie dake cikin kulan da ya sha veggies da nama, abincin ya yi kyau a ido amma warin ƙuna yake. Fork da aka ɗora akan kulan ya ɗauka, ya ɗan goge, yayi ɗeba abincin kaɗan yayi Bismillah ya kai baki, ajiye fork ɗin ya yi da kyar ya iya haɗiye na bakinshi, ya tafi gaban fridge ya ɗauki bottle water, sai da ya kwankwaɗi fin rabin ruwan goran kafin ya ajiye, har ya juya zai tafi sai ya feeling urge ɗin ya tafi ya gan lafiyar kitchen ɗinsa, daga bakin ƙofa ya yi pause, zuciyarsa na ƙuna yana kallon kayyakin da Zee ta yi aiki da su ta tara a sink, ga kan cooker ɗin duk noodles da ya zuba a yayin serving, girgiza kai ya yi ya fita, ɗaki ya koma ya ɗauki car keys ɗinshi ya fita daga gidan.
Sai can dare misalin ƙarfe sha biyu kafin Hunaif ya dawo gida, kitchen ya fara leƙawa ya gan ko Zee ta gyara, amma yadda ya barshi haka ya tarar dashi, ajiye key ɗin motarsa ya yi, ya wanke kwanukan dake sink ɗin tas, ya goge kan cooker sannan ya share kitchen ɗin tsaf, kafin ya wuce daki. Gefen Zee da ya tarar ta riga da ta yi bacci ya kwanta, ya ja bargo ya lulluɓe kansa yana tunanin mafitar wannar matsalar da ta yi saurin kunno kai a aurenshi.
Washegari da sassafe Hunaif ya farka, ya yi dukkan gyare-gyaren gida kamar babu mace a gidan, kafin ya shiga ya yi wanka. Har ya gama shiri ya fita daga gidan Zee ba ta farka daga bacci ba, ko Sallar asuba ma yau taƙi tashi ta yi.
_________
A ɓangaren Humaira kuwa kwana biyu ta yi a gida ba ta zuwa makaranta tana kwance kawai a ɗaki, kafin ta ci abinci ma sai Umma A'i ta lallaɓata kafin ta ci da ƙyar, har ta kan yi mamakin kanta, ita da ba ta wasa da abinci ko kaɗan shine yau take ƙinsa. Yaya Kabir yazo gidan ya lallasheta sosai,vbayan ta faɗa mishi abinda ya faru, ya kuma sa ta dau mishi alƙawarin za ta kwantar da hankalinta, ta mayar da hankalinta akan karatunta.
Mallam Sadi ma a nasa ɓangaren yana matuƙar ƙoƙari wajen ganin ya ƙarfafata, kafin ya fita wajen aiki sai ya aika an kirata zuwa falonsa, ya ba ta words of encouragement sosai, sannan ya sa Umma A'i ta saka ido sosai akanta.
Su Laura da Hannatu ma ba a bar su a baya ba wajen ganin sun kwantar mata da hankali sun sata nishaɗi duk da ba su san ainahin abinda ke damunta ba.
Humaira na gaban mirror ɗin ɗakinsu tana ƙoƙarin parking gashinta da jiya su Hannatu suka tayata tsifa, Hannatu ta shigo tana kallon Humaira dake gaban mirror, tace; "Wai har yanzu ba ki gama shiryawa ba Humaira?"
Zumɓura baki Humaira tayi kamar za ta yi kuka, tace; "Na kasa kama kan."
Hannunta Hannatu ta kama, ta zaunar da ita a bakin gado ta karɓi ribbon ɗin a hannunta, ta tattara gashin Humaira dake cike ga kuma tsayi, ta parking mata shi, sai ta ɗauki mayafinta dake kan gadon ta miƙa mata, tace; "Saka mu tafi."
Kallon dogon rigar dake jikinta da ya ɗan kama jikinta ta yi, shape ɗinta ya fita sosai, sai tace; "Hannatu ba zan iya fita da wannan kayan da mayafi ba, bari dai na saka hijjabina kawai."
Harararta Hannatu ta yi, tace; "Wallahi ba za ki bi ni da hijjabi ba."
Murmushi Humaira tayi tace; "To bari na canza rigar to."
Dogon rigar material baƙi dake nan free ta saka, ta ɗora brown mayafin da Hannatu ta ba ta akai, tana juyowa Hannatu ta buɗe baki tace; "Wow! Look how pretty you are."
Rufe fuskarta Humaira ta yi da hannu tana murmushi. Hannatu tace; "Kin dai fi kyau idan kina farinciki, don haka ki daure ki cire damuwar komai a ranki, kin ji?" Kai Humaira ta gyaɗa mata, tace; "In Sha Allah, nagode sosai da kulawar ku, indeed you're my sisters from another mother.
Rungumarta Hannatu ta yi, tace; "Humaira you're such an innocent girl that everyone can't help but to love you."
Kama hannun Humairan ta yi suka fita daga ɗakin, suka sallame Umma A'i dake surfe a tsakar gida, kafin suka fita.
A daidai bakin gate ɗin Bayero University mai adaidaita ya yi parking, Hannatu ta ciro wayarta ta kira Laurat, tace; "Ku fito, mu na bakin gate."
Jira kaɗan suka yi, sai ga Laura da Aisha sun fito, adaidaitan suma suka shiga, Laurat ce ta faɗawa mai adaidaitan inda zai kai su.
A kanawa park suka sauka, Laurat ta biya mai adaidaita ta kama hannun humaira suka yi gaba, Hannatu da Aisha na bin su a baya zuwa cikin park ɗin. Zuwan su park ɗin idea ɗin Laurat ce, ita ta bukaci Abbansu ya ba su kuɗi su fita da HUMAIRA ta sha iska ko za ta manta damuwarta, Abba kuwa ya yi na'am da shawarar, ya bata kuɗi da ɗan dama. Ita da Aisha suna da lectures ɗin safe shiyasa suka fara zuwa makaranta.
Humaira ta yi kyau sosai cikin shigar da ta yi,dukda babu make-up a fuskarta, amma duk inda suka saka ƙafa a park ɗin nan sai an kalleta saboda yadda take fisgar hankalin mutane da kyaunta. At first she was feeling very uncomfortable da yadda mutane ke kallonta, amma daga baya sai ta sake jikinta, ta rinƙa yin ƴan wasanni abunta. Sosai ta having fun yau, she was genuinely happy yau, irin farincikin da ta daɗe ba ta tsinci kanta a ciki ba. Sai yamma lis kafin suka koma gida zuciyar kowa cike da farinciki.
___________
A lokacin da Hunaif ya dawo gida ya tarar da Zee akwance a falo, ga ledan cornflakes da ta sha da bowl ɗin a kan table, tana kallon TikTok videos a wayarta, wani irin zafi ya ji a zuciyarsa, amma sai ya daure ya kama hanyar ɗaki, Zee na ganin shi ta tashi daga kwancen da take, tana murmushi tace; "Masoyina ashe ka dawo." Danne zuciyarsa ya yi, ya mayar mata da murmushin, yace; "Na dawo masoyiya, but only to come and meet my wife with kayan da na fita na bar ta dashi, and a bowl thats already used akan table."
Langwaɓar da kai Zee ta yi, tace; "I'm just about to clean up ka shigo, bari ma na shiga wanka sharp-sharp saboda ina son ka fitar da ni yau na gan gari.
Tana faɗin haka ta ƙaraso kusa dashi ta yi kissing ɗinshi, kafin ta yi gaba zuwa ɗaki, girgiza kai Hunaif ya yi, ya bi ta a baya zuwa ɗakin. Yana zaune a bakin gado ta fito daga wanka daure da guntun towel da da kaɗan ya wuce mazaunanta, zuwa ta yi ta zauna kusa dashi ta ɗora kanta a kafaɗarshi, tace; "Tunanin me angon Zee yake yi bayan ga ta kusa dashi, Hunaif bai ce mata komai ba ya ɗaga kanta daga shoulder dinsa ya miƙe, a hankali ya taka zuwa gaban mirror, ya ɗauki man shafawarta ya dawo ya zauna kusa da ita, matsan man yayi a hannunsa ba tare da yace mata komai ba ya fara shafa mata, lumshe ido Zee ta yi tana jin daɗi a ranta ganin duk abinda ta yi wa Hunaif ba ya iya fushi da ita.
Bayan Hunaif ya gama shafa mata mai, ya tafi closet ya ciro mata doguwar riga ja, ajiye mata a gefenta yayi, yace; "Get dress." Yana kallonta ta zare towel ɗin jikinta, inner wears ta fara sawa kafin ta ɗora dogon rigar a kai, ta tafi gaban mirror ta feffesa turare.
"Can we?" Ta juyo tana tambayar Hunaif.
Wayoyinsa ya kwashe da car key ɗinsa ya yi gaba, da sauri Zee ta bi shi ta kamo hannunsa tace; "Ya zaka yi gaba ka bar ni? Ai kamata ya yi mu jera kamar ko wani ma'aurata ma su son junansu."
Murmushi Hunaif ya sakar mata, suka kuwa jera tare kamar yadda ta buƙata.
Baka jin ƙaran komai a cikin motar sai sautin karatun Alqur'ani na Abdul Rahman Sudais da Hunaif ya yi playing, wayar Hunaif ne ya ɗauki ƙara, a tare shi da Zee suka kai dubansu zuwa kan wayar, Sis Inti ne ya fito a kan wayar, taɓe baki zee ta yi ta mayar da dubanta zuwa kan titi, Hunaif kuma ya yi amfani da airpod dake kunnensa ya yi picking call ɗin. "Assalamualaikum Yaya ina wuni." Inti ta faɗa daga cikin wayar. "Lafiya ƙalau Inti, ya mutanen gida?"
"Lafiya ƙalau Yayana, ya haƙuri da ƙawata?"
Dan jim Hunaif ya yi don Inti ta taɓo masa inda ke masa ciwo, murmushi mai ciwo ya yi, yace; "Sai hamdala.
“Ka yi ta haƙuri Yaya, komai zai wuce.“
“In Sha Allah, thank you sis.“
Tana katse kiran ya kalle Zee dake kallon hanya, hanunta ya kama ya ɗan matsa, yace; "Why the sudden change of mood?“
Kamar wacce take jira kuwa, ta juyo a fusace, ta ƙwace hannunta daga nashi, tace; “A gabana ma sai ka yi waya da ƴanmatan ka? You can simply wait idan ka kaɗaice sai ka kira su, at least ka yi respecting ɗina.“ Dafa kansa Hunaif ya yi, ya kasa gane daga ina kuma wannan maganar ke fitowa. “Zee don Allah ki sama wa kanki sauƙi, Intisar cefa ba wata ba.“
“Intisar? Ita ɗin budurwarka ce? Alamu sun nuna daman tun ranar da na fara haɗuwa da kai, to meyasa ka zaɓeni?“
“Can you stop all these drama Zee, Inti ba budurwata bace please.“
“Kenan karuwarka ce, idan ba haka ba me zai sa ta kiraka by this time of the night.“
“Stop it Zee! I say stop it! Kina da hankali? Ko kin san me kike faɗa?“
“Na sani mana, ta yaya za ku yi min laifi kuma ka zo kana yi min faɗa, me zai sa a dakeni a kuma hana Ni kuka, wallahi baku isa ba.“
Nan fa Zee ta birkicewa Hunaif kamar lalatacciyar tsohon mota, tun yana lallashinta har ta fusata shi da munanan kalaman da take jifarsa da su. Daga ƙarshe dai gida suka koma ran kowa babu daɗi.