
Post
KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 13
.....ro, then she threw her lip balm in the bag, Hannatu opened her eyes a bit, lowered them and put them on Humaira, got up and sat down and said; "Not until you're ready to go out?" Humaira smiled at her and said; "Yes, I have lectures at eight o'clock." "Really, is Aisha lying still?" "Maybe she doesn't have lectures now, since we are not in the same department." Humaira said that she is trying to keep a secret from Aisha, it is because of GST for them in the morning which all level one is taking. Hannah touched her lips and said; "You don't know who Aisha is." Before Humaira said anything, Aisha, who had been lying down with her two eyes for a long time, corrected her voice letting them know she's hearing them. Hannatu touched her mouth, she went back to bed, Humaira smiled, took her handbag and hung it, and left the room. Umma A'i had to go to their rooms and greet them before leaving the house to go to school. It is a 20-minute journey from Mallam Sadi's house to BUK, so Humaira is doing her trekking, the day she is very tired and she has to come back in the morning. ___________ On their part, Hunaif and Zee are making love without playing, for two days, Hunaif knows for sure
KOMAI YA YI FARKO
PAGE 13
Bayan kwana biyu da zuwan Humaira gidan Mallam Sadi ta fara tafiya makaranta. Yau tana da lectures ɗin ƙarfe takwas na safe, hakan ya saka da ta idar da sallar asuba ba ta daɗe a darduma yadda ta saba ba, wayarta ta ɗauka ta kunna tocin wayar ta fita tsakar gidan, gefe guda ta ajiye wayarta yadda zai iya haske gidan da kyau, tsintsiya ta ɗauka ta share kitchen ɗin gidan ta hura wuta, tukunya lamba biyar ta ɗora akan wutar ta cika shi da ruwa, sai ta fita ta fara share tsakar gidan kafin ruwan ya yi zafi, ƙarar shara da take yi ne ya saka Umma Rabi da ita ke da girki leƙowa, tana ganin Humaira ce ta taɓe baki ta koma ɗaki. Tsaf Humaira ta share gidan, ta tattara kwanukan wanke-wanke ta wanke tsaf, kafin ta juye ruwan wanka ta shiga wanka.
Kafin ƙarfe bakwai ta gama komai ta shirya cikin blue doguwar rigar material da hijabi baƙi wadda ya ƙara fito da kyau da kuma hasken fatarta, ɗaya daga cikin handbags da Ya Kabir ya siyo mata ta ɗauka ta jera takardarta da biro, sai ta jefa lip balm ɗinta a jakan, Hannatu ta ɗan yi miƙa ta buɗe idonta, sauke su ta yi akan Humaira, tashi ta yi ta zauna tace; "Kar dai har kin yi shirin fita?" Murmushi Humaira tayi mata, tace; "Eh ina da lectures ɗin ƙarfe takwas."
"Lallai kam, shine Aisha ke kwance har yanzu?"
"Ƙilla ita ba ta da lectures yanzu, tunda ba department ɗaya muke ba." Humaira ta faɗa tana ƙoƙarin rufa wa Aisha asiri, don GST ne gare su da safen wanda dukka level one ke taking.
Hannatu ta taɓe baki, tace; "Ba ki san waye Aisha ba kenan." Kafin Humaira ta ce wani abu, Aisha da ta daɗe idonta biyu kawai kwanciya take, ta yi gyaran murya letting them know she's hearing them. Taɓe baki Hannatu ta yi, ta koma ta kwanta, murmushi Humaira ta yi, ta ɗauki handbag ɗinta ta rataya, ta fita daga ɗakin. Sai da ta bi ɗakunan su Umma A'i ta gaishe su kafin ta fita daga gidan zuwa makaranta. Tafiyar mintina ashirin ne daga gidan Mallam Sadi zuwa BUK, hakan ya sa Humaira ke trekking abinta, ranar da ta gaji sosai kuma sai ta dawo a adaidaita.
___________
A ɓangaren su Hunaif da Zee kuwa soyayya suke yi babu wasa, kwana biyu Hunaif ya san tabbas mai mata da mara mata ba ɗaya ba, a duk lokacin da ya dawo daga aiki zai zo ne ya tarar da kyakyawan tarba daga matarshi, matsalan da yake samu daga gareta shine rashin son gyara waje da kuma rashin ɗaukan karatu da wuri, tun aurensu har yau suna waje ɗaya a karatu, abun ma looks like ba ta da interest a koyon karatun ma, wannan abun na damunshi, amma yana ƙoƙarin ganin ya gyarata saboda ya san nobody's life is perfect.
Ya dawo daga stadium kenan, ya fara bin gidan da kallo, tun daga sitting room har bedroom har bathroom ɗin looks so scattered and unkept, kallon Zee da ta yi ɗaiɗaya akan gado tana sharar baccinta hankali kwance ta ƙure AC, girgiza kai kawai ya yi, ya luluɓeta da bargo ya fita farko. Arranging falon ya yi, ya share ko ina tsaf, ya dawo ɗakin ya gyara kafin ya shiga bathroom ya wanke tsada, sannan ya yi wanka ya ɗora da alaula.
Bayan ya idar da sallah ya miƙe ya ƙarasa bakin gado, a hankali ya fara shafa fuakar Zee dake bacci, buɗe idonta ta fara yi a hankali har ta buɗe su tar akan fuskarsa, murmushi ya sakar mata, murmushin ta mayar masa, ta miƙe tace; "Abun ƙaunata yaushe ka dawo?"
"Ban daɗe da dawowa ba, tashi ki yi sallah muje mu siya abinci." Hunaif ya faɗa yana shafar girarta.
Yana daga zaune yana kallonta har ta yi sallarta sharp-sharp ta sallame, ta shirya cikin expensive Turkish gown ta yi rolling kanta da mayafi, tace; "Mu je." Hunaif ya kalleta, yace; "Wifey please ki rinƙa natsuwa idan kina sallah, da mahaliccinki fa kike ganawa, to mai amfanin gaggawa?" Zumɓura baki Zee ta yi, tace; "Ka yi haƙuri masoyina, zan gyara In Sha Allah."
Hunaif ya ja hancinta yace; "Yauwwa wifey, Allah ya yi miki albarka, ya bamu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba."
"Aameen my love."
Babban eatery su Hunaif suka tafi suka yi dinner, sannan suka dawo gida.
Washegari Hunaif ne ya tashi ya gyara gidan tsaf, yayi wanka, har ya fita Zee ba ta farka ba, ya yi mata uzuri don kwakwata daren jiya bai barta ta huta ba, breakfast ya ajiye mata a table dake ɗakin ya ajiye mata short note ya fita.
Tun safe da Hunaif ya fita bai dawo gida ba sai bayan La'asar, a gajiye lis ya dawo gidan saboda yau ɗin zirga-zirga ya yi sosai, Company ɗinsa na shoe making dake garin ya tafi, saida ya zaga dukka departments dake kamfanin ya duba ayyukan da suke yi.
Yana shiga gidan ya gan ko ina tsaf yadda ya fita ya bar shi, table dake ɗakin ya ƙurawa ido, kwanukan da ya ajiyewa Zee breakfast da safe ya gani, ta ci abincin ta bar kwanukan a wajen, kan gadon da ta tashi ma bata gyara ba, ga kayan da ta tuɓe a kan gadon, ƙarar ruwan da yake ji a banɗakin ne ya tabbatar masa da wanka take yi, tattara kayanta dake gadon ya yi, ya tafi ya zuba a washing machine dake passage tsakanin falo da ɗaki, ya dawo ya kwanta akan gado, in no time bacci ya ɗauke shi, fita kawai Zee ta yi daga wanka ta gan shi kwance yana sharar bacci.
Shiryawa ta yi cikin ƙananun kaya, ta feffeshe jikinta da turare, a hankali ta lallaɓa ta shige jinkinsa ta kwantar da kanta a kirjinsa, cikin bacci Hunaif ya rungumeta, a hakan itama bacci ya ɗauketa.
___________
Satin Humaira biyu a gidan Mallam Sadi, amma tun bayan kira ɗaya da Alhaji Sani ya yi mata bai sake kiranta ba, tun Humaira tana jiran kiransa har ta gan ya dace ta kira shi tunda shi ɗin is a very caring person ta sani. Tana idar da sallah a massallacin dake department ɗinsu, ta Ciro wayarta daga handbag ɗinta, lambar Alhaji Sani ta yi dialling amma har ya gama ringing ba a ɗauka ba, ba ta haƙura ba ta sake kira, sai da ta yi mishi four missed call bai ɗaga ba, a hankali ta tashi ta koma lecture hall, lectures ɗin four too six ta yi, bayan lecturer ɗin ya gama lectures ya fita, tana zaune har yan ajin suka gama fita, wayarta ta ciro daga jakarta ta duba ta gan ko Alhaji Sani ya kira, da ba ta gan kiranshi ba sai ita ta kira, ringing ɗaya biyu sai aka rejecting kiran, sai gashi an biyo bayan kiran, Humaira kamar za ta yi kuka tace; "Haba kwana nawa rabon da mu yi waya, ko dai ba ka da lafiya ne?"
"Lafiyata ƙalau Humaira, ya karatun?"
"Alhamdulillah, amma me yasa ka daina kira?"
Ɗan jim Alhaji Sani yayi, can sai yace; "Humaira meyasa kika ɓoye min ainahin wacece ke?"
Sounding confused Humaira tace; "Kamar yaya?"
Nan Alhaji Sani ya faɗa mata abubuwan da ya ji game da ita a anguwarsu, kuma yace ya fi yarda da wanda suka ce daman can ita ɗin tana bin maza, idan ba haka ba me zai sa ta ɓoye masa gaskiya.
Kuka Humaira ta fashe dashi, ita take ganin jarabawa, kuka kawai take yi ta rasa me za ta ma faɗawa Alhaji Sani.
"Humaira Ni kam na hakura dake, duk abinda na taɓa baki na bar miki saboda tsakani da Allah na yi miki, idan kuma akwai abinda kika taɓa yi mini na yafe miki, ina roƙon nima ki yafe mini idan da akwai abinda na taɓa yi miki, Allah ya haɗa kowa da rabon shi ya kuma shiryar da mu baki ɗaya."
Cikin kuka Humaira tace; "Don Allah kar ka katse, wallahi Ni ba karuwa nace, ban taɓa sanin namiji ba sai da tsautsayi ta afka min, fyaɗe aka yi min, to me lefina?"
"Tabbas ba ki da laifi idan da gaske fyaɗen aka yi miki, amma Ni kam na yafe daman ba sona kike ba." Alhaji Sani na faɗan haka ya katse kiran, ya kuma blocking layinta.
Life kanta Humaira ta yi akan table ta fashe da kuka, ta kai kusan mintina ashirin a ajin tana kuka, kafin ta mike da kyar tana ganin hajjijiya ta fita daga ajin, adaidaita ta tare zuwa gida. A lokacin da ta shiga gidan Umma Rabi na kason abincin dare, sauran mutanen gidan kuma na shirin shiga sallar maghrib da ake kira a loudspeakern masallaci, gasihe ta yi idonta na ƙasa, ta shige ɗaki, kwanciya ta yi akan gado ta cigaba da kukanta daga inda ta tsaya, tana kwance a wajen har dukka ƴan matan suka shigo suka yi sallah, bayan sun iddar Laurat taje ta dauko musu abincinsu, dambu ne aka baza musu shi kan tray, ta ajiye a tsakiyar ɗakin, ta je ta taɓa Humaira ta ce; "Tashi mu ci abinci." Humaira ta ja hanci tace; "Na ƙoshi." Laurat da ta ji muryarta wani iri, tace; "Kuka? Lafiya kike kuka?" Da dabara Humaira ta goge idanunta, tace; "A'a ba kuka nake ba." Laurat ta zubawa kumburarun idanunta kallo, tace; "Gashi alamu sun nuna zahiran kuka kike yi, Allah dai ya sa ba wani abun aka yi miki ba." Hannatu ta tashi tazo kusa da su, itama ta kalli idanun Humaira da suka yi ja suka kumbura, tace; "Subhanallah! Wani abu ya faru a gidane?" Girgiza kai Humaira ta yi, tace; "Babu komai, gajiya ne fa kawai." Amma sai hawayenta suka betraying ɗinta, suka fara gangarowa kamar an kunna famfo. Hannatu ta zauna a gefenta ta kwantar da kanta a ƙafarta, ta fara shafa kanta a hankali tana lallashinta har kukan ya tsaya, sai tace; "Ki yi hakuri Humaira, komai ya yi zafi maganinsa Allah, maybe abinda ke damunki ba wanda za ki iya faɗa bane, amma da wannan kukan da kina ambatar Allah sai ki fi jin sauki a ranki."
Kai Humaira ta gyaɗa mata tana mayar da nunfashi, lumshe idonta ta yi, tayi luf kamar mai bacci, Hannatu ta ja pillow ta ɗora mata kanta kafin ta tashi ta tafi suka fara cin abinci.
Cikin dare Aisha na jin Humaira tana shesheƙan kuka, sai ta rasa me ke damunta da har za ta hana kanta bacci ta tsaya wani kuka, tocin wayarta ta kunna, ta haska Humairan, tace; "Wai lafiyarki kuwa?"
Humaira ta yi shiru amma ba ta kulata ba, can sai Aisha ta tashi ta dauko jakarta, paracetamol ta ciro daga jakar ta ajiye a gaban Humaira tace; "Ki sha ki yi bacci ya fi miki da wannan kukan, ko menene ya faru ya riga da ya faru, kukanki ba zai canza komai ba."
Hannu Humaira ta saka ta ɗauki paracetamol ɗin, ballan biyu ta yi ta zuba a bakinta, tauna maganin ta yi ta haɗiye, Aisha dake kallonta ta taɓe baki ta kwanta.
Tunda Humaira ta sha paracetamol ɗin kamar wacce ta sha ƙwayar bacci, bacci mai nauyi ne ya ɗauke ta, Da Aisha ta ji shiru, sai ta ɗan haska Humairan ta gan bacci take yi, kashe hasken wayarta ta yi, tace; "Allah ya kyauta."
YA KUKE GANIN ZAMAN HUNAIF DA ZEE ZAI KASANCE?
SHIN ABINDA ALHAJI SANI YA YI WA HUMAIRA YA KYAUTA?
ANYA HUMAIRA ZA TA YARDA TA ƘARA BA WA SO DAMA KUMA?
"WHAT DO YOU GUYS THINK ABOUT AISHA?"
SHARE AND COMMENT PLS 🙏
JIKARGARBA ✍️ 07048694211.