Kenza eBookz
Cover art for FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 26

Post

FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 26

...... She closed her eyes and looked at the pictures, then she opened them quickly, she closed her head. Some kind of pain was increasing in her, so she leaned against the wall and cried slowly, even though she was playing, she never thought that there would be a day when she would be sad or cry in her life. She started her application as usual, cleaned the parlor, fixed the dining room, and then went to the kitchen. There they started knocking on the gate of the house, at first the knocking was done gently, then it started forcefully. Farida raised her head, "Wow, who came so early in the morning?" She said removing her apron. She went out with the intention of going to open the door, but before she arrived, the guard quickly came out of the toilet and opened the gate. It was Firdausi who came in as fast as she could. "It's okay." She answered without stopping, and said "Where is Anty Zahra?" Farida was a little surprised. "She is pregnant for us." "Did she come down?" Firdausi asked again, "No." Farida answered, "She hasn't come down since morning." Firdausi felt her face fall again. "Okay." She could only say. Then she went faster. Straight up, she didn't even knock, she went u

Standalone post2,548 words

*FARASHIN IZZAH*

Book 1 Chapter 26

Firdausi ta fito daga gida ko kallon gabanta bata yi

Tun daga lokacin da Zahra ta katse wayar, zuciyarta ta kasa samun nutsuwa

A bakin titi ta tsaya tana jiran abin hawa.

Motoci na wucewa, napep na wucewa, amma ko ɗaya yaki tsayawa

Lokaci zuwa lokaci tana sake danna number Zahra.

Wayar tana ringing, amma ba a ɗagawa

Hakan ya ƙara dagula mata lissafi.

"Ya Allah ka sa lafiya..." Ta faɗa a hankali

Da ƙyar dai wani napep ya tsaya, wata tsohuwa ce kawai a ciki, ta shiga haɗi da faɗa masa inda zai kaita

Tun daga nan ma wayar Zahra take ta kira, yana shiga amma kuma bata dauka

Firdausi ta rasa irin tunanin da zata yi.

A rayuwarta bata taɓa jin muryar Zahra kamar yadda ta ji ta yau ba.

A ɓangaren Zahra kuwa...

Bayan ta kashe wayar, ta zauna bakin gado tana kuka.

Kukan da ta yi har ta gaji, har hawayen ma kamar sun fara ƙafewa

Wayarta na gefe, amma bata da ƙarfin sake ɗaukarta

Hotunan da ta gani ne kawai ke yawo a fuskanta

Saudat... Kawarta Saudat... da Khalil.

Tana rintse idanunta sai ta kalli hotunan, sai ta bude su da sauri, ta dafe kanta

Wani irin ciwon maran kuma yana karuwa mata, a haka ta jingina da bango tana kuka a hankali, ko da wasa bata taɓa ɗauka akwai ranan da zata shiga kunci ko tayi kuka a rayuwarta ba

Farida ta fito daga ɗakinta tana tunanin aikin da aka saka ta anya zata iya?

Ta fara aikace-aikacenta kamar yadda ta saba, ta share parlorn, ta gyara dining, daga nan ta nufi kitchen.

Can aka fara bugun gate din gidan, da farko bugun a hankali ake yi, sai kuma aka fara da karfi

Farida ta ɗago kai "Wayyo wa ya zo haka da sassafe?" Ta faɗa tana cire apron ɗinta.

Ta fita da niyyar zuwa buɗewa, sai dai kafin ta isa, mai gadi ya fito da sauri daga toilet ya buɗe gate ɗin

Firdausi ce ta shigo da saurin ta Kamar ma zata faɗi saboda hanzari

Farida ta ƙarasa gareta "Ina kwana Anty Firdausi."

"Lafiya lau." Ta amsa ba tare data tsaya ba, kuma ta ce

"Ina Anty Zahra?"

Farida ta ɗan yi mamaki. "Tana ciki mana."

"Ta sauko?" Firdausi ta Kara tambaya

"A'a" Farida ta amsa "Tun da safe bata sauko ba."

Firdausi ta ji gabanta ya sake faɗuwa. "Okay." Kawai ta iya faɗa.

Daga nan ta kara sauri Kai tsaye ta nufi sama, ko knocking bata yi ba, ta tura ƙofar ɗakin ta tsaya kallonta

Zahra na zaune kan gado. Idanunta sun kumbura sosai, fuskarta tayi jaa

Da alama ma tun daga lokacin da suka yi waya bata daina kuka ba.

Zahra na ganin Firdausi... sai ta miƙe da sauri, ta ƙarasa gareta, ta rungume ta gam.

Nan take kuma ta sake fashewa da wani kukan. Kuka mai taba zuciya

Firdausi ta ruɗe "Zahra!"

Ta riƙe ta "Me ya faru?"

Zahra ta kasa cewa komai sai kukan da take yi ta cigaba

"Wallahi kina bani tsoro, gaba na sai faduwa yake" Firdausi ta ƙara faɗa

"Talk to me mana. Me ya faru?"

Da ƙyar ta samu ta zaunar da ita bakin gado. Ita ma ta zauna kusa da ita

Har yanzu Zahra kuka kawai take yi. Firdausi ta kamo hannunta.

"Zahra, ki kalle ni."

A hankali Zahra ta ɗago.

"Menene?"

Sai Zahra ta miƙa hannu, ta ɗauki wayarta, Gallery ta shiga, ba tare da ta ce komai ba ta miƙa mata wayar

Firdausi ta karɓa cikin rashin fahimta. Ta fara kallon hoton farko

A take ta zaro idanuntan kamar zasu fito fili

"Wai me...? Me nake gan..?"

Tayi sliding wani, nan take ta miƙe tsaye

Wayar ma kusan faɗuwa tayi daga hannunta

"What?!!!!" Ta faɗa da ƙarfi

Sai ta sake kallon hoton, sannan a jefar da wayar kan gadon saboda tsananin mamaki

"Saudat?!" Ta faɗa

"Saudat?!"

Zahra ta rufe fuskarta da tafin hannunta, sabon kuka ya sake ƙwace mata

Firdausi ta dafe kanta.

"Wannan yarinyar mahaukaciya ce wallahi." Ta faɗa cikin fushi.

"Saudat kuma?" Ta sake ɗaukar wayar

Ta sake kallon hotunan. Kowanne ya fi ɗan'uwansa ɗaga hankali.

"Wallahi sai tayi nadamar abin da ta aikata, idan har ni kawace ta gari, Duk halarcin da kika mata?" Ta faɗa a fusace

"Na rantse sai tayi nadama."

Zahra bata ce komai ba. Kanta kawai ta sunkuyar.

Firdausi ta sauke numfashi, ta zauna kusa da ita, ta janyo ta jikinta.

"Shhh..." Ta fara bubbuga bayanta a hankali

"Karki yi kuka Zahra, nasan abun da ciwo musamman yarda kika yarda da ita, Duk da ba sa'arki bace amma haka ko kyamanta bakya yi kika jawo ta jiki, yanzu please kiyi hakuri ki daina kuka musan abun yi"

Amma Zahra ƙara fashewa da kuka take yi, Firdausi ta lumshe idanunta

Ita kanta ta ji zafin abin, domin ba wata ba ce, ba yarinya daga waje ba ce balle ace bata san zahra ba, ace kawar Zahra.

Kawarta? Wacca tasan sirrinta Wacce suke hira tare. Wacce Zahra ta amince da ita.

Ta ƙara rungume Zahra.

"Ki yi haƙuri." Ta faɗa a hankali.

"Wallahi komai zai wuce."

"Ki kwantar da hankalinki saboda cikin da ke jikinki Zahra"

"Ki bar ni da Saudat." Ta ƙara faɗa cikin fushi. "Sai ta gane kuskuren da tayi."

A haka ta ci gaba da lallashin Zahra.

Tana bubbuga bayanta.

Firdausi ta daɗe tana lallashin Zahra kafin kukan nata ya ɗan lafa

Sai dai ko bayan ta yi shiru, idanunta basu daina zubar da hawaye lokaci zuwa lokaci ba

Firdausi na kallonta kawai tana jin tausayinta.

A hankali ta miƙe tsaye "Ina zuwa" Ta faɗa

Zahra bata ce komai ba, kawai ta zauna a bakin gado tana kallon wani waje

Firdausi ta sauko ƙasa, ai tsaye kitchen ta nufa.

Farida ta samu tana gyara wajen breakfast, da alama ta gama komai

Tana ganin Firdausi ta yi murmushi "Kin ga Anty Zahra?"

Kai Firdausi ta gyada. "Na ganta."

Farida ta lura da yanayin fuskarta "Lafiya dai?"

Firdausi ta yi murmushin dole "Eh lafiya."

Sai ta kalli abincin da aka shirya "Ta karya ne?"

Farida ta girgiza kai "A'a, Kuma wallahi rabonta da cin shekaran tun jiya."

Firdausi ta sauke ajiyar zuciya, ta san halin Zahra Idan damuwa ta yi yawa, bata ma tuna da abinci

"Toh" Kawai ta faɗa.

Daga nan ta juya ta sake komawa sama.

Tana shiga ɗakin ta tarar da Zahra a yadda ta barta.

Har yanzu tana zaune, kai a sunkuye

Firdausi ta ƙarasa kusa da ita. "Zahra." Ta kira a hankali

Zahra ta ɗaga kai tana kallonta

"Mu je ki karya"

Kai tsaye ta girgiza kai "Ba na jin yunwa."

Firdausi ta ɗan haɗe gira "Ba tambayarki ko kina jin yunwa nayi ba, cewa nayi mu je ki karya"

Shiru tayi ba tare data ce komai ba

"Zahra kina da ciki." Cewar firdausi

Har yanzu Zahra ta girgiza kai "Wallahi ba zan iya ci ne"

Firdausi ta zauna kusa da ita "Ko kaɗan ne mana Babyn Abbah"

"A'a"

"Zahra."

"A'a Firdausi."

Ta katse ta.

"Please."

Firdausi ta daɗe tana lallashinta, tana bata baki, tana tunasar da ita halin da take ciki

Amma Zahra ta firrrr taki

Daga ƙarshe Firdausi ta miƙe, ta girgiza kai

"Matsalata da ke taurin kai " Ta faɗa

Sai ta juya ta fita, a sake komawa kitchen.

Farida tana can tana gyara kayan amfani.

"Ta sauko?" Farida ta tambaya.

Firdausi ta yi tsaki. "Ta ƙi"

"Wayyo." Farida ta faɗa cikin damuwa

Firdausi ta buɗe warmers ɗin, ta zaɓi abincin da ta ga zai fi sauƙin ci

Ta ɗebo kaɗan, ta haɗa da cup na tea, ta kuma ɗauki ruwa.

Farida tana kallonta "Ko zata ci kuwa?"

Firdausi ta ɗan yi murmushi "Ko da ba zata ci ba sai na sa ta ci"

Ta ɗauki tray ɗin, ta nufi sama

Da ta shiga ɗakin, Zahra na nan zaune

Firdausi ta ajiye tray ɗin a center table, sannan ta ja kujera ta zauna gabanta

"Yanzu." Ta faɗa tana ɗaukar spoon

"Ko da ni zan baki a baki ne, sai kin ci"

Zahra ta kalleta.

A karo na farko tun safen nan wani ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskarta

Firdausi ta nuna spoon ɗin.

"Exactly." Ta faɗa.

"Ki yi murmushi yanzu, amma idan na fara baki a baki kar ki ce ban gargaɗe ki ba tass zaki cinye"

Duk da ciwon da ke zuciyarta, Zahra ta sake ɗan murmushi.

Firdausi kuwa ta ji daɗin ganin hakan, kuma aim dinta taci abincin dan zai taimaka mata da kuma jaririn da ke cikinta.

Bayan Zahra ta gama cin abincin da ƙyar, Firdausi ta karɓi plate ɗin ta ajiye gefe.

Na wasu daƙiƙu babu wacce ta ce komai.

Zahra na zaune tana kallon hannayenta.

Firdausi kuma tana kallonta cikin tausayawa.

Daga ƙarshe Zahra ta miƙa hannunta ta kama na Firdausi.

Wata irin nutsuwa ce ta bayyana a fuskarta.

"Firdausi..." Ta kira a hankali.

"Na'am."

"Yau zan koma gida."

Firdausi ta kalleta. "Gida?"

Kai Zahra ta gyada. "Eh!Gidanmu." Ta gyara.

"Na gama zaman gidan nan ne "

Shiru ya ratsa ɗakin.

Firdausi ta sauke ajiyar zuciya, gaskiya ne, abin ya yi yawa, fiye da yadda zata ci gaba da cewa Zahra ta yi haƙuri, musamman bayan abin da ta gani da idanunta yau

"Kin tabbatar you're okay with it?" Ta tambaya

"Eh." Zahra ta amsa ba tare da wata shakka ba "Na tabbatar."

Sai ta ƙara da cewa, "Kuma na san Ya Umar zai tsaya min wajen komai."

Ta haɗiye miyau. "Har wajen ya karɓo min takardar sakina idan ma shi yaki bani"

Firdausi ta daɗe tana kallonta, sai daga ƙarshe ta gyada kai.

"Toh." Ta faɗa a hankali

"Idan wannan ne abin da kika yanke, Allah ya sa alkhairi, ya kuma baki Wanda ya fi shi wanda zai rike ki da gaskiya"

Zahra bata ce komai ba, kawai ta gyada kai

Firdausi ta miƙe tsaye, kai tsaye wardrobe ɗin Zahra ta nufa, ta buɗe shi

Ta fara ciro takardunta masu muhimmanci, credentials, documents, takardun filaye

Duk ta tattara ta saka a cikin wani babban backpack.

Daga nan ta buɗe drawer, ta fito da gold ɗinta, sarkoki, 'Yan kunne, Zobuna, a saka su a wani pouch sannan ta zuba su a cikin jakar.

Bata tsaya nan ba, ta ciro mata inner wears, Sleeping wears, Abayas, da wasu kaya masu muhimmanci da zata iya buƙata na wasu kwanaki

Duk ta ci gaba da zubawa a cikin jakar.

Zahra dai tana zaune tana kallonta, kamar wacce jikinta ya mutu

Bayan Firdausi ta gama shirya komai, ta rufe jakar

Sai ta juya tana kallon Zahra.

"Is there anything else you will need?"

Zahra ta ɗan yi shiru, sai ta girgiza kai "No."

"Kin tabbatar?"

"Eh."

Firdausi ta gyada kai, rufe backpack din tayi.

Zahra ta ɗauki wayarta, ta shiga contacts

Yatsanta ya tsaya kan sunan Ya Umar ❤️, da alama zata kira shi, sai kuma ta tsaya

Ta daɗe tana kallon sunan, daga ƙarshe ta kashe screen ɗin wayar.

"A'a." Ta faɗa a hankali.

Firdausi ta kalleta. "Me ya faru?"

Zahra ta girgiza kai.

"Ba zan kira Ya Umar yanzu ba"

"Why?"

"Zan masa bayanin komai idan na isa"

Ta sauke numfashi "Sannan..." Ta ɗan yi shiru

"Na fi son na koma gida ya dawo daga aiki"

Firdausi ta kama hannunta.

"Toh." Ta faɗa cikin tausasawa

"Yanzu ki shirya, anjima sai mu tafi gidan"

A karo na farko tun safen nan, Zahra ta ji wani abu kamar sauƙi ya ratsa zuciyarta, ba saboda ciwon ya ragu ba

Sai saboda ta yanke hukuncin da taji shine mafi alkhairi gareta Zahra ta miƙe a hankali ta nufi toilet, tana rufe kofar toilet din, Firdausi ta ɗauki wayarta tare da ta Zahra

Tayi Unlocking wayar Zahra na, yatsunta suka yi wasu abubuwa cikin sauri

Can sai ta kashe screen ɗin ta ajiye wayar a gefen gado, wani irin murmushi ne ya bayyana a fuskarta

Murmushin da da wuya mutum ya iya fassara ma'anarsa

Sai ga Zahra ta fito daga toilet ɗin, Firdausi ta miƙe da sauri

Ta ɗauki tray ɗin da suka ci abinci

"Barin mayar da wannan kitchen" Ta faɗa

Kai kawai Zahra ta gyada, Firdausi ta fito da tray ɗin, anan parlon sama ta ci karo da Khalil

Daga gani yanzu ya gama shiryawa ne, yana ganinta kuwa fuskarsa ta sauya

"Keeee!" Ya faɗa yana nuna ta.

"Me kike yi anan?"

Firdausi ta tsaya, amma bata ce komai ba

Khalil ya ci gaba "Ina tambayarki ba? Wani munafurcin ne ya kawo ki nan?"

Har yanzu shiru ta masa

"Da safe shine har za ki zo gidan mutane." Ya yi tsaki.

"Idan ba gulma ba me ya kawo ki nan?"

Firdausi ta haɗe fuska, amma ko kallonsa bata yi ba.

Ta wuce ta ajiye tray ɗin kan center table na parlon

Khalil ya bi bayanta yana magana

"Baki da aiki sai shiga tsakanin mata da mazajensu."

"Ki fita ki bar min gida, ko ki sha mamaki na"

Firdausi ta juya ta nufi ɗakin Zahra. Khalil na biye da ita yana ta magana.

Da ta shiga ɗakin,suna hada ido da Zahra tayi saurin mata alama, alamar kar ta ce komai, kar ta tanka masa, balle ya gane zata koma gida,

Zahra ta fahimta, ta gyada kai kawai, ta koma kan gado ta zauna daddanna wayanta shi kuma yana tsaye bakin kofar yana ta maganganu

Firdausi ta ɗauki hijab ɗinta, sannan ta juya tana kallon Khalil

A karo na farko ta yi magana.

"Well..." Ta gyara jakarta a kafaɗarta

"Zan bar maka gidan." Ta ɗan tsaya.

Sai ta ƙara da,

"Amma ka sani akwai lokacin da za ka neme ni wallahi, lokacin ne nikuma zan baka amsar maganganunka"

Khalil ya yi wani irin murmushin raini, ko amsa mata bai yi ba

Firdausi ta girgiza kai, ta wuce ta gefensa, ta fita daga ɗakin.

Ta sauko ƙasa, daga haka ta tafi

Wata matashiyar budurwa ce kwance kan gado bayan ta gama cin abinci. Wayarta kawai take dannawa tana yawo a Instagram ba tare da wani takamaiman abu a ranta ba.

Can wani post ya faɗo mata, da farko ta wuce, sai uma ta dawo baya, ta sake kallon hoton

Ta matso wayar kusa da fuskarta.

"What??!!!..." Ta furta a hankali

Ta sake duba sunan account ɗin, ta sake kallon hoton, nan take ta miƙe zaune

"Wayyo Allah!" Ta yi ihu da ƙarfi

A take ƙannenta biyu suka shigo ɗakin da gudu

"Lafiya?" "Me ya faru?"

Ba tare da ta iya magana ba ta miƙa musu wayar, suka karɓa.

Da farko ba su gane ba, sai ɗaya daga cikinsu ta zaro ido

"Haba!" Ta faɗa.

"Wai da gaske ne wannan?"

Dayar kuma ta karɓi wayar "Subhanallah..." Ta furta

"Kinga comments!"

Da sauri suka shiga comment section.

Tun a lokacin comments ɗin sun fara taruwa

"No wonder..."

"I feel sorry for the wife."

"Wallahi idan wannan gaskiya ne akwai matsala."

"Men are wicked."

"This is heartbreaking."

"Someone said they were happily married."

"Kai duniya..."

Budurwar ta ci gaba da scrolling, kowane second comments suna ƙaruwa ne haka shares ma suna ƙaruwa

Mutane na tagging juna, wasu suna mamaki, wasu suna zagi, wasu kuma suna neman ƙarin bayani nr

A hankali post ɗin ya fara bazuwa, daga Instagram zuwa WhatsApp, daga WhatsApp zuwa Facebook

Mutane sai screenshot suke suna forwarding, suna magana a kai

Kuma cikin ƙanƙanin lokaci... Post ɗin ya fara yawa

#08110615256 #Jiddatulkhayr writes