
Post
FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 9
..... in this problem, I have nowhere to go, I'm sure I'm closer to Zahra than you." The doctor raised his head and looked at them and said, "If you are not ready to speak calmly, don't leave. I have work to do." This made Ibrahim take care of Firdausi again. The doctor straightened up and said, "The patient went into shock, that's what caused the bleeding you saw." But Alhamdulillah, we managed to stop the bleeding." They all stared at him and listened. He continued, “But there is something you should know. She is pregnant, and the womb is very weak now. She did not want to go through any stress or violence from now on. Also, avoid anything that will disturb her, because the stomach can leak if not taken care of." Then Ibrahim raised his head quickly looking at him and said, "Is Dama pregnant?" The doctor said, “Yes. The pregnancy is about twenty-six days in her body." Firdausi closed her eyes and hoped for this Ibrahim, what happened made him change. She went out and left him in the office. Mom called. "Mom, I'm sorry, you called, I didn't even pay attention." Mom said, "Today you are not going to go back to school and stay, where are you?" She said, "Mama yes...
*FARASHIN IZZAH* Jiddatulkhayr writes
Young talented writers association (YOTA)
Book 1 Chapter 9
Wayan hannun Firdausi ne ya fara ringing, ta ɗaga kai ta kalli Ibrahim ta ce
“Sai ka kira iyayenta ka faɗa musu inda muke yanzu, dan Mahaifiyarta ce ke kira. Ni kuma ban san me zan faɗa mata ba idan na ɗauka.”
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce, “Kawai ki kashe wayarki.”
Da mamaki ta juyo tana kallonsa. Zama yayi ya dafe kansa, sai kuma ya ciro wayarsa wanda tun ɗazu yake jin vibrating ɗinta a aljihun wandonsa. Unlocking yayi ya ga mai kiran, wani tsaki yaja sannan ya kashe wayar gaba ɗaya.
Wani likita ne ya fito daga cikin ɗakin, da sauri Ibrahim ya miƙe yana kallonsa.
“Ku ne kuka kawo ta?” likitan ya tambaya.
Da sauri Ibrahim ya ce, “Yes, mu ne.”
Likitan ya ce, “Follow me.”
Duk suka bi bayansa. Suna shiga office ɗin, Ibrahim ya ɗaga kai yana kallon Firdausi ya ce, “Zaki iya bamu waje? Wannan kamar privacy ɗinmu ne.”
Wani kallo ta masa sannan ta ce
“Sannu ko! ka san kai ne silar shigarta cikin wannan matsalar, ni kuma babu inda zan tafi, dan ina da tabbacin na fi ka kusanci da Zahra.”
Likitan ya ɗaga kai yana kallonsu ya ce “Idan baku shirya magana cikin nutsuwa ba ku fita, ina da aikin yi.”
Hakan yasa Ibrahim ya ɗauke kai ba tare da ya sake kula Firdausi ba.
Likitan ya gyara zamansa sannan ya ce, “Patient ɗin ta shiga cikin shock sosai, hakan ne ya jawo bleeding ɗin da kuka gani. Amma Alhamdulillah, mun samu nasarar tsaida zubar jinin.”
Duk suka zuba masa ido suna sauraro.
Ya ci gaba da cewa, “Amma akwai wani abu da ya kamata ku sani. Tana da ciki, kuma cikin yana da rauni sosai a yanzu. Ba’a so ta shiga wani stress ko tashin hankali daga yanzu. Haka kuma ku guji duk wani abu da zai dagula mata rai, saboda cikin zai iya zubewa idan ba a kula ba.”
Nan Ibrahim ya ɗaga kai da sauri yana kallonsa ya ce, “Dama tana da ciki ne?”
Likitan ya ce, “Eh. Cikin yana da kimanin days ashirin da shida a jikinta.”
Firdausi ta rufe idanunta tana fatan Ibrahim ɗin nan, abin da ya faru ya sa ya canza.
Fita tayi ta barsa a office ɗin.
Kiran Mama tayi.
“Mama sorry, kin kira ban kula ba ma.”
Mama ta ce, “Yau kuma shiru baki ce min zaki koma makaranta da zama ba, kina ina ne?”
Ta ce, “Mama ina kan Zahra ne a asibiti. Mun taso ne daga makaranta, shine ta yi ɓari.”
Mama ta ce, “Allah sarki, Allah ya bata lafiya toh. Sai da safe.”
Daga haka ta kashe kiran.
Dialing number ɗin Mami tayi. Mami na ɗagawa ta ce, “Firdausi ina ta kiran ki shiru? Na kira su Asiya sun ce basu tare da Zahra, amma na kira ki. Maman ki ma tace baki dawo gida ba. Lafiya kuwa? Kuma ina kuke?”
A hankali Firdausi ta ce, “Mami, Zahra ce ba lafiya, muna asibiti ne.”
A rude Mami ta ce, “SubhanAllah! Firdausi meke damun Zahra na? Faɗa min wani asibiti kuke yanzu?”
Firdausi ta ce, “Mami please, calm down. Kar ki daga hankalinki. In Shaa Allah Zahra zata samu sauƙi. Bari na turo miki sunan asibitin yanzu.”
“In Shaa Allah,” Mami ta ce.
Daga haka ta kashe kiran ta tura mata sunan asibitin. Zama tayi ta lumshe idanunta.
Da sauri Mami ta sauka ƙasa, kana ganinta zaka san a birkice take. A daidai ƙofar shiga parlour, Mami ta haɗu da Ya Umar.
Ya ce, “Mami lafiya?”
Ta ce, “Ina Abbanku?”
Ya ce, “Yana ciki.”
Shiga tayi, kamar zai bar wajen sai kuma ya ji hankalinsa ya kasa kwanciya, hakan yasa ya bi Mami a baya.
Mami na kallon Abbah ta ce, “Abban yara, ashe Zahra ba lafiya? Tana asibiti yanzu haka.”
Abbah ya miƙe da sauri ya ce, “Wa ya gaya miki?”
Ta ce, “Yanzu nayi waya da kawarta Firdausi, ita ta faɗa min. Dama hankalina bai kwanta ba tun da nasan anan take, kuma naga bata dawo ba.”
Ya Umar ya ce, “Wani asibiti take? Bari na tafi.”
Abbah ya ce, “A’a, mu tafi dukkanmu kawai.”
Daga haka Mami ta wuce domin ɗauko hijab ɗinta.
A cikin compound ɗin asibitin, Ya Umar yayi parking motarsa. Duk suka sauka, sai ga Firdausi ta fito sakamakon kiran da Ya Umar yayi mata.
Ta ƙarasa wajensu ta durƙusa ta ce, “Abbah sannu da zuwa, ina wuni.”
Ya ce, “Lafiya lau Firdausi.”
Ta gaishe da Mami sannan ta koma kan Ya Umar. Daga haka suka juya zuwa ciki.
Duk da ba’a bari a shiga ba, haka aka buɗe ƙofar ɗakin suka shiga.
Ibrahim ya sauke kansa ƙasa da ganin su. Wani kallo mai wuyar fassaruwa Ya Umar ya masa, kuma ya ƙi ɗauke idanunsa daga kansa, dan yana ƙoƙarin karantar yanayinsa ne.
Ibrahim ya ɗan duƙa ya gaishe da Abbah sannan ya gaishe da Mami, daga haka ya fita daga ɗakin.
Wani banzan kallo Ya Umar ya bishi da shi.
Ƙarasa kan Zahra dake kwance suka yi. Sun daɗe suna kallonta babu mai cewa uffan, sannan suka koma suka zauna.
Mami ta ce, “Firdausi, me ya same ta ne?”
Firdausi ta sauke kanta ƙasa, ta rasa ta ina zata fara bayani. A hankali ta soma cewa,
“Mun fito daga evening lectures ne. Duk mun gaji, muka fito tare da Zahra saboda zata sauke ni a gida, tunda yanzu tace min tana gida ne. Shine muka biya zamu sayi abu, daga saukarta ke da wuya sai ta yanke jiki ta faɗi. Nan take kuma ta fara bleeding.”
Mami ta ce, “Cikin jikinta ya zube ne?”
Kai ta girgiza ta ce, “A’a bai zube ba, amma likitocin sun bada ka’idojin da za’a bi. Ba’a son a ɗaga mata hankali, haka kuma ba’a son stress yana samunta.”
Mami tayi shiru.
Abbah ya miƙe ya ce, “Toh amma me ya kawo yanke jikin nata? Ina likitan da ya duba ta? I need to see him, dan bana son wani abu ya samu baby na.”
Duk maganar lokaci guda yayi ta, meanwhile yana fita daga ɗakin.
Mami ta miƙe ta bishi. Suma suka fita daga ɗakin.
Can sai ga su Mami sun dawo.
Ya Umar na kallonsu ya ce, “Mami bari na kai ku gida, idan yaso ni na zauna anan, kuma kinga ga kawarta.”
Abbah ya ce, “A’a, ba zan iya barin nan ba.”
Mami ta ce, “Kar ka damu, kaje ka huta son.”
Ya san halinsu, tun da suka fara faɗin hakan ya san ba lalle bane su yarda su tafi.
Yana kallon Firdausi ya ce, “Toh bari na maida ke gida.”
Ba dan taso ba, amma tasan suna buƙatar zama kusa da ‘yarsu yasa kawai ta ce, “Tohm.”
Sallama tayi wa su Mami. Abbah yayi ta sa mata albarka tare da godiya.
Fita tayi yana binta a baya.
Bayan sun shiga mota ya tada motar. Ya ɗan kalleta sannan ya maida hankalinsa kan tuƙi ya ce,
“Mun gode ko.”
Ta ce, “Haba, ai duk abin da zan ma Zahra wallahi yi ma kai ne, dan Zahra tafi yar uwa a wajena.”
Bai ce mata komai ba har ya kaita ƙofar gidansu.
Parking yayi a ƙofar gidan. Ta kai hannu zata buɗe ƙofar kawai sai yayi locking.
Ta ɗaga kai tana kallonsa.
Bata rai yayi yana kallon wani waje ya ce, “Faɗa min gaskiyar abin da ya faru da Zahra.”
Ta ce, “Ya Umar ai abin da na faɗa ɗazu shine gaskiya.”
Wani tsawa ya daka mata har sai da ta firgita ya ce, “Zaki faɗa min ne ko yaya?”
Ba shiri balle tayi tunani, nan take ta faɗa masa abin da ya faru har ya jawo Zahra ta fara bleeding.
Wani murmushi yayi yana kallon waje.
Ta ce, “Zan iya sauka?”
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce, “Sauka.”
Ta ce, “Tohm ai baka buɗe ƙofar ba.”
Ya ce, “Zan buɗe, amma sai kin faɗa min me Zahra take ɓoyewa.”
Ta ce, “Dan Allah kar ka sa na faɗi abin da Zahra zata ji haushi na, Ya Umar. Is better ka tambaye ta.”
Kawai sai taji ya kunna motar suka fara tafiya.
Ta juyo a razane tana kallonsa ta ce, “Ina zaka kai ni?”
Ya ce, “Baki shirya faɗin gaskiyar bane ko?”
Ta ce, “Allah zan faɗa.”
Yayi parking gefen wani gida ya ce, “Ina sauraren ki.”
A hankali ta ce, “Kawai iya abin da na sani shine, Ya Ibrahim ya canzawa Zahra. Kuma duk wata soyayyarsa yanzu bata samun ta kamar da. Toh abin gaskiya yana damunta. In fact, har ta fara complain cewa soyayyarsa ta ragu a zuciyarta yanzu.”
Ta sauke numfashi sannan ta ci gaba da cewa,
“Ni kuma gani nake kamar yana using ɗinta ne. Dan idan ka kalli posts ɗinsa, kamar wanda suke zaune lafiya kalau babu matsala. Ranar gala night na promotion ɗinsa ma, babu wanda zai yarda suna samun matsala.”
Juya kan motar yayi ya koma ƙofar gidansu.
Yayi unlocking motar ya ce, “Sauka. Mun gode.”
Ta ce, “Sai da safe, nagode.”
Daga haka ta shiga cikin gidansu.
Washegari da safe, bayan Abbah ya tafi masallaci, Mami na zaune tana lazumi taji motsin Zahra. Da sauri ta miƙe tana kallonta.
Zahra ta buɗe idanunta haɗi da dafe ƙirjinta saboda nawi daya mats.
Mami ta ƙarasa kanta da sauri ta ce, “Meke damunki Zahra?”
Kai ta girgiza wa Mami.
Mami ta ce, “Sannu ko?”
Ta ce da raunanniyar murya, “Mami… nan ina ne?”
Mami ta ce, “Ki huta Zahra, ki daina wannan surutun kar ciwon kai ya kamaki.”
Ta girgiza mata kai ta ce, “A’a Mami, ina ne nan?”
Mami tana shafa kanta ta ce, “Asibiti ne Zahra.”
Ta ce, “Ina Firdausi toh?”
Mami ta ce, “Jiya da dare yayanki ya mayar da ita gida.”
Tayi shiru kamar mai nazari.
Hakan yasa Mami ta ce, “Kar ki damu, babu abin da ya samu cikin ki. Ki kwantar da hankalinki kinji ko?”
Kallon Mami take da rashin fahimta ta ce, “Mami ban gane ba?”
Buɗe ƙofar aka yi. Wata nurse ce ta shigo. Bayan ta gaishe da Mami ta ƙarasa kan Zahra. Bayan ta gama mata allurai ta bata wasu magani sannan ta juya ta fita.
Mami zata yi magana sai ga su Abbah sun shigo.
Ganin ta farka yasa ya ƙarasa wajenta ya rungume ta ya ce, “Sannu Baby.”
Ta naɗe hannayenta a wuyansa ta ce da murya mai rauni, “Abbah…”
Ya ce, “Don’t cry kinji ko?”
Kai ta gyaɗa masa.
Ya Umar kuwa kallon tausayi yake mata kawai.
Abbah ya sake ta ya ce, “Sannu Baby.”
Ta gyaɗa masa kai tana murmushi kaɗan.
Ya miƙe ya ce, “Kin san yau zan je ganin likitana a Dubai, ina son na tafi gida dan shiryawa. Ga su Mamin ki anan kinji.”
Kai ta gyaɗa masa ta ce, “Allah ya baka lafiya Abbah, ya kuma dawo da kai lafiya.”
Ya ce, “Ameen.”
Ta sauke idanunta ƙasa.
Ya Umar ya ce, “Me kike so kiyi breakfast da shi?”
Tayi shiru kamar mai nazari sai kuma ta ce, “Alale.”
Bai kai ga rufe baki ba sai ga wayarsa ta fara ringing. Ya ɗaga ya kai kunne ya ce,
“Da sauƙi Firdausi, gashi ma ta farka.”
Can ɗayan ɓangaren Firdausi ta ce “Me zata ci?”
Ya ce, “Ki barshi kar ki bama kanki wahala.”
Sai kuma ya ɗan murmusa ya ce, “Toh.”
Da alama Firdausi bata yarda ba, dan sai ya sake cewa,
“Nasan kina son kiyi mata, amma ki huta.”
Ganin suruntun Firdausi har ciwon kai ya fara saka masa yasa ya ce “Alale.”
Daga haka ya kashe wayar ya saka a aljihunsa.
Sallama aka yi haɗi da turo ƙofar ɗakin.
Duk suka juya.
Ibrahim ne ya shigo.
Nan take Zahra ta ɗauke kanta gefe.
Mami ta miƙe tana kallon Ya Umar ta ce, “Ka maida ni gida, ina son na mata breakfast da kaina.”
Ibrahim ya duƙa ya gaishe da su Mami.
Abbah ya ce, “Haa’an, kamar jiya naganka sai kuma daga baya ban sake ganinka ba.”
Yana sosa kai ya ce, “Eh Abbah, ai ganin ku ne yasa na tafi.”
Nan suka gaisa.
Ya Umar kuwa wani irin kallo yake binsa da shi.
Mami da Abbah suka juya suka fita. Ya Umar ma yayi kamar zai bisu.
Da Zahra ta ɗaga kai ta ga daga ita sai Ibrahim ne a ɗakin, nan take ta ce,
“Ka fita, bana son ganin ka.”
Zai yi magana ta ce,
“Wallahi zan maka ihu idan ka ce ba zaka fita ba. Bana ƙaunar ganin ka nace.”
Ya Umar ne ya dawo cikin ɗakin, dama reaction ɗinta yake son gani.
Tana kallonsa ta ce, “Yauwa Ya Umar, dan Allah ka zauna anan kar ka tafi.”
Ya ce, “Ba tafiya zan yi ba.”
Zama yayi ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kaɗawa haɗi da fara danna wayarsa.
#08110615256 #Jiddatulkhayr