
Post
FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 28
..... they were shouting from the parking space and Firdausi finished quickly "O Umar?" She called worriedly "How is she?" Umar shook his head. "They haven't come out yet." Asia shook her head. "God willing, she will get better" She said, "When I called her, she didn't pick up, that's why I got worried." Firdausi said, "If she didn't pick up, we called Farida." Farida who was sitting on the side wiped her eyes, a new cry came to her again. Asia sat next to Mami, she held her hand "God will make her well, God willing Mami" She said in a calm voice, Mummy just nodded, tears filled her eyes. Then some doctors came out of the emergency room, so they all stood up and looked at the ophthalmologist. The doctor removed his mask and said, "The patient has internal injuries." Their faces fell at the same time. "We have bleeding inside" He continued "Alhamdulillah we have controlled the bleeding now, but she is still under control." Mummy clutched her chest. "Oh God" She said Abbah moved forward "Doctor, can we see her?" The doctor shook his head "Not yet, she needs complete rest, once we confirm everything is.....
*FARASHIN IZZAH*
Book 1 Chapter 28
Chapter 28
Abbah da Mummy suna isa asibitin suka tarar da Ya Umar zaune a wajen emergency unit, kansa sunkuye cikin hannayensa.
Farida kuma tana gefe idanunta sun kumbura saboda kuka.
Da sauri Mami ta ƙarasa.
“Ina take?” Ta tambaya cikin rawar murya
Ya Umar ya miƙe tsaye “Tana ciki Mummy.”
Abbah ya kalli ƙofar emergency room “Me likita ya ce?”
Ya Umar ya girgiza kai “Har yanzu suna tare da ita.”
Mummy ta dafe ƙirji, Tana hoping ba abun da zuciyarta take raya mata bane
Ta zauna a kujera, tasbihi kawai take yi a hankali
Abbah kuwa ya ci gaba da tsaye. Lokaci zuwa lokaci yana kallon ƙofar, lokaci zuwa lokaci kuma yana kallon Ya Umar
Yana son tambayar abin da ya faru, amma yanayin da suke ciki bai bashi damar hakan ba
Duk hankalinsu yana kan Zahra, saboda haka babu wanda yasan abun da ke yawo a internet.
Can bayan wani lokaci suna zaune, suka ji ance
“Ya Allah…” Dukkaninsu suka ɗago kai
Firdausi ce tare da Asiya, dukkansu numfashinsu a ɗauke, da alama sauri suka yi tun daga parking space
Firdausi ta ƙarasa da sauri
“Ya Umar?” Ta kira cikin damuwa
“Yaya take?”
Ya Umar ya girgiza kai. “Har yanzu ba su fito ba.”
Asiya ta dafe kai.
“In shaa Allah zata samu sauki” Ta furta
“Ina ta kiranta bata dagawa shine hankalina ya tashi” Firdausi ta ce
“Da ba ta ɗagawa ba ne muka kira Farida.”
Farida da ke zaune gefe ta goge idanunta, sabon kuka ya sake taho mata
Asiya ta zauna kusa da Mami, ta kamo hannunta
“Allah zai bata Lafiya In shaa Allah Mami” Ta faɗa cikin sanyin murya
Mummy ta gyada kai kawai, hawaye na cika idanunta
Wani irin yanayi ne ya mamaye wajen
Kowa ya rasa abin cewa sai addu’a da fatan alheri.
Can sai ka wasu likitoco sun fito daga emergency room din, hakan yasa Duk suka mike
Dukkansu suka zuba wa likitan ido
Likitan ya cire face mask ɗinsa, sannan ya ce,
“Patient ɗin tana da internal injuries ne”
Gabansu ya faɗi lokaci guda.
“Mun samu bleeding a ciki” Ya ci gaba
“Alhamdulillah mun shawo kan bleeding ɗin yanzu, amma har yanzu tana ƙarƙashin kulawa.”
Mummy ta dafe ƙirji.
“Ya Allah” Ta furta
Abbah ya matsa gaba “Doctor, za mu iya ganinta?”
Likitan ya girgiza kai “Not yet, tana bukatar complete rest, da zarar mun tabbatar komai ya daidaita, za mu sanar da ku”
Dole suka amince.
Likitan ya koma ciki, suka ci gaba da tsayuwa a wajen
A karo na farko tsoro ya bayyana sosai a fuskar Abbah ya ce
“Umar wai meya same ta ne? Bangane bleeding a ciki ba? As in how internal injuries” sai kuma ya juya ya bi bayan dayan likitan daya tafi
Mami kam bata san sanda ta fara hawaye ba
Ya Umar ya juya ya kalli ƙofar emergency room, a ransa kuwa…
Abu ɗaya kawai yake maimaitawa… Khalil zai yi bayanin abin da ya aikata
Bayan kwana biyu a asibiti… Alhamdulillah, jikin Zahra ya fara ɗan samun sauƙi, ba kamar ranar farko ba da ko idanuwanta da ƙyar suke buɗewa
Yanzu tana iya magana kaɗan-kaɗan, tana iya shan ruwa, tana iya gane mutanen da ke kusa da ita
Sai dai har yanzu rauni ya yi mata yawa, Internal injuries ɗin da ta samu sun sa likitoci suka ci gaba da sanya ta a ƙarƙashin kulawa sosai
Abin da ya fi ɗaga hankalin kowa kuwa shi ne… cikin da take ɗauke da shi bai tsira ba, last last sai daya zube, hakan yasa dole sai da aka yi mata wankin ciki
Tun da likita ya gaya musu hakan, Mami ta yi kuka sosai, Munmy ma ta nuna damuwarta ainun , Abbah ma ya yi shiru na tsawon lokaci
Amma Ya Umar bai nuna wata damuwa kan zubewar cikin ba, hasali ma a ransa yana jin wani irin sauƙi
Daya kalli Zahra dake kwance kan gadon asibiti, sai ya ce a ransa,
“Ko cikin bai zube ba shima mai iyasa likita ya zubar ne”
Domin duk lokacin da ya tuna cewa ko bayan rabuwarsu wannan cikin ne zai ci gaba da hada Zahra da Khalil… sai ya ji haushinsa yana ƙaruwa.
Washe gari da yamma bayan likita ya tabbatar musu cewa Zahra ta fara samun sauƙi sosai.
Ya Umar ya fito daga ɗakin da take kwance. A corridor ya tarar da Farida zaune.
Tun ranar farko yarinyar take kai-komo tsakanin gida da asibiti
Da ganinsa ta miƙe tsaye “Yaya.”
Ta gaishe shi.
Ya amsa sannan ya tsaya yana kallonta na wasu daƙiƙu.
Sai ya ce “Farida.”
Ta ɗago kai “Na gode.”
Mamaki ta yi, ta ce “Da mene Yaya?”
Ya Umar ya yi murmushi karon farko cikin kwanakin nan
“Dan kirana da kika yi akan lokaci”
Farida ta yi shiru
Ya ci gaba “Da ba don ke ba…”
Sai ya girgiza kai “Ban san me zai faru ba.”
Nan take idanun Farida suka cika da ƙwalla
“Ai na tsorata ne sosai Yaya.” Ta faɗa a hankali.
Ya Umar ya gyada kai. “Na sani. Sai kuma information da kike bani na komai a gidan, Nagode sosai”
Farida ta sunkuyar da kai.
Tun ranar da zai kawosu gidan ya saya wa Farida waya da sim, yace Duk abun da yake faruwa a gidan tana Kira tana sanar da shi, ko kuma ya Kira, kasan komai ya Umar ya sani dake faruwa a gidan, ko ta Kira ta ce ga Zahra ba ta cikin yanayi mai kyau.
Ko idan ta ƙi cin abinci, ko idan ta yi kuka, ko idan ta kwana babu walwala, ko idan Ibrahim bai kwana a gidan ba
Ya Umar ya san komai saboda Farida
Shine ranan da irdausi ta zo gidan da sassafe, Farida ta kira shi ta gaya masa Zahra ba ta cikin yanayi mai kyau sam, ta ce har Firdausi ta zo tun safen saboda damuwa.
Tun daga lokacin ne kuma gabansa ya faɗi, ya gama abin da yake yi cikin gaggawa ya kamo hanyar ko sanda zahra ta kirasa ma yana areansu, shiyasa ma ya isa gidan da sauri.
Ya Umar ya lumshe idanuwansa. Kawai tunanin mintuna kaɗan da ya yi, yaji kamar yaje ya kashe Ibrahim
Ya buɗe idanunsa ya kalli Farida. “Nagode sosai Farida, akwai tukuicin ki, Bari mu koma gida”
Farida ta yi saurin girgiza kai.
“A’a Yaya, Anty Zahra ai kamar yayata ce”
Maganar ta ta sa Ya Umar ya yi murmushi
Bayan kusan mako guda da suka yi a asibiti, likitoci suka tabbatar cewa Zahra ta samu sauƙi sosai duk da akwai abu da ba’a rasa ba, a ranan kuma aka sallama su
Abin da ya fi ɗaga hankalin su Mami shi ne babu ko mutum ɗaya daga gidan Khalil da ya zo balle su Kira suji ya take, ba wani yunƙurin sanin halin da take ciki.
Ba su dan abun dake going ba shiyasa dukkansu suka kwallace su arai
Bayan sun dawo gida kuwa… Kowa ya dage wajen kula da Zahra.
Mami ba ta bari wani ya yi mata komai, abinci, magani, komai da kanta take wa ‘yarta, Wanda Mummy taji haushi gani take ita ya kamata ta kula da Zhara ba Mami ba
Ya Umar ma duk lokacin da ya dawo daga aiki sai ya fara tambayar Zahra kafin komai.
Yau ma hakan ne Da yamma suna zaune a babban parlorn.
Zahra na kan kujera, a gabanta akwai bowl ɗin kaza da Mami ta matsa mata sai ta ci, Ya Umar yana opposite dinta yana bata labarin wani korean movie sanin Zahra na son su
Abbah na gefe yana karanta wasu takardu.
Mami kuma tana zaune kusa da Zahra.
A lokacin suka ji ƙarar mota ta shigo harabar gidan tayi parking, ba da daɗewa ba mai gadi ya shigo da sallama ya gaisu, yana kallon Ya Umar ya ce
“Yaya Umar, wasu ne suka zo suna nemanka.”
Ya Umar ya ɗago kai. “Su waye suka ce maka?”
“Suka cewa lawyers ne.” Ya amsa
Ya Umar ya gyada kai “Toh, gani fitowa”
Ya miƙe ya fita
Abbah ya bi shi da kallo Sai dai bai ce komai ba, haka ma Mami, Zahra kam gabanta ne ya fadi ya fara sake sake a ranta
Kusan rabin awa ya ɗauka a waje, can sai gashi ya dawo parlorn.
Abbah ya ajiye takardunsa yana kallonsa ya ce
“Su waye?” Ya tambaya.
Ya Umar ya zauna a hankali. “Barristers ne.”
Abbah ya gyada kai “Suna son me toh?”
Ya Umar ya yi shiru na wasu dakiku, sai ya saci kallon Zahra suka hada ido yayi saurin dauke kansa
Sannan ya ce, “Ai ni na kira su.”
Nan take Mummy ta ɗago kai tana kallonsa
Abbah ma ya haɗe gira ya ce
“Ka kira su? Can’t you explain?”
Ya Umar ya gyada kai
“Eh” Sai ya ɗaga kansa ya kalli Abbah, sannan ya kalli Mami
Daga nan idanunsa suka sauka kan Zahra, wacce take zaune shiru jikinta duk yayi sanyi, bowl ɗin da ke gabanta ma ta daina cin abin cikin
A hankali Ya Umar ya ce,
“Ina son su karbawa Zahra dakartan saki ne”
Parlorn ya yi tsit, kowa ya tsaya da abin da yake yi, Zahra ta sauke kanta kasa Tana wasa da fingers dinta
Abbah ya kalli Ya Umar. “Kana nufin me?”
Ya Umar ya ja numfashi. A hankali ya fara ba su labarin abin da ya faru, tun daga ranar da ya same su a parlorn, yadda Khalil ya ke kai wa Zahra duka ta ko ina, yadda yake fita ya barta ya kwana a waje, da kuma yadda likitoci suka tabbatar da abin da ya jawo internal injuries tare da zubewar ciki, bai ɓoye komai ba
Nan take Abbah ya miƙe tsaye, sai da kujerar da yake kai ta ja da baya
“What?!” Ya faɗa da ƙarfi
“My baby?!” Fuskarsa ta sauya gaba ɗaya Idanunsa suka yi ja lokaci guda
Ya Umar ya gyada kai a hankali
“Kabar wannan a hannuna, sai naga uban da zai tsaya masa a kaff kasar nan” Ya fada cikin ɓacin rai
Sai kuma ya sauke numfashi ya kalli Zahra, wacce kanta ke sunkuye
“Nagode Umar” Abbah ya faɗa cikin rawar murya
“Allah Ya albarkace ka, dan ka tabbatar min ko bana raye kai me tsaya wa ne akan gidan nan”
Ya Umar ya ce “Ameen Abbah”
Mami ta kasa cewa komai, tun lokacin da Ya Umar ya fara magana hawaye suka fara bin kuncinta
Ta rufe bakinta, saboda kukan da ke neman ƙwace mata, ta kalli Zahra, her only Baby.
Ƴar da ta ɗauka ta shiga gidan aure domin samun farin ciki, ashe tana rayuwa cikin irin wannan azaba.
Mami ta kasa jurewa, ta miƙe daga inda take, ta ƙarasa kusa da Zahra, ta zauna gefenta, sannan ta rungume ta
Mami na shafa kanta, hawaye na zuba daga idanunta
Abbah na kai-komo a tsakaninsu, da tunanin irin matakin da zai dauka
Daga ƙarshe Mami ta sauke ajiyar zuciya, har sannan tana rungume da zahra. Muryarta na rawa tace,
“Abin da nake gudu kenan, My Dear.” Ta kalli Abbah, idanunta cike da hawaye
“Amma kai da Umar…” Ta girgiza kai a hankali.
“Duk abin da Zahra take so shi ne abin da ku ma kuke so.”
Abbah ya yi shiru. Ya Umar ma bai ce komai ba.
Mami ta ci gaba.
“Na yi iya ƙoƙarina wajen nuna muku tsoron da nake ji akan wannan yaron, amma Ina…”
“Amma saboda kuna son farin cikin Zahra, kuka bi abin da take so.”
Ta sake goge hawayen da suka zubo mata.
“Yau ga maganata ta fito fili.”
Da jin waɗannan kalamai… Zahra ta fashe da kuka
Ta miƙe daga jikin Mami, ta durƙusa
“Mami…” Ta kira cikin kuka.
Mami ta kalleta. Zahra ta kama hannunta.
“Ki yafe min Mami” Kuka ya sake ƙwace mata.
“Mami ki yafe min, naki sauraren ki, naki karɓi shawararki ba, Mami na sani baki son wannan auren…. Amma na nace. Na zaɓi abin da nake so
Hawayenta na bin kuncinta Ta sunkuyar da kanta.
“Mami na yi kuskure Ki yi haƙuri. Dan Allah ki yafe min.”
Parlorn ya sake yin shiru, Kowa na kallon Zahra cike da tausayi
Mami kuwa ta kalleta na wasu daƙiƙu
Sai kuma ta miƙa hannu ta kamo haɓarta, ta ɗago fuskarta sama.
“A’a.” Ta faɗa cikin sanyin murya.
“A’a Zahra. Ba haka bane”
Ta share mata hawayen da ke kan kumatunta.
“Sau nawa zan gaya miki? Ni uwa ce.”
Ta ɗan yi murmushi duk da hawayen idanunta.
“Uwa kuma ba ta riƙe ɗanta a rai.”
Zahra ta sake fashewa da kuka.
Mami ta kamo hannunta. “Ban taɓa riƙe ki a raina ba. Ko da na yi magana a lokacin Ko da ban yarda da zaɓinki ba. Ban taɓa daina son ki ba.” Ban taɓa daina yi miki addu’a ba.”
Ta ɗora hannunta kan Zahra.
“Wallahi kullum cikin addu’ata kike Kullum ina roƙon Allah Ya ba ki alheri. Ya ba ki farin ciki. Ya kare ki daga duk wani sharri.”
Muryarta na rawa “Ko a lokacin da kika zaɓi abin da ba na so, ba yanda zanyi, sbd ke ɗiyata ce.”
Nan take Zahra ta mike ta rungume Mami Tana cigaba da kuka sosai
Mami ma ta rungume ta back, tana shafa bayanta a hankali
Abbah ya juya gefe yana goge idanunsa, shi kansa hawaye sun cika masa ido
Ya Umar kuwa ya sauke ajiyar zuciya A karo na farko cikin kwanakin nan… Ya ji kamar wani babban nauyi ya fara sauka daga zuciyar Zahra
Ko ba komai ta dawo cikin gidan da ake sonta. Cikin mutanen da ba za su taɓa juya mata baya ba
Abbah ya kalli Zahra na wasu daƙiƙu, zuciyarsa cike da tausayin ƴarsa.
A hankali ya miƙe daga inda yake zaune ya karasa wajen su
“Zo nan” Ya faɗa cikin sanyin murya
Ya ɗagota daga jikin Mami sannan ya rungume ta gam a ƙirjinsa. Nan take Zahra ta sake fashewa da kuka
Abbah ya rufe idanunsa na ɗan lokaci yana bubbuga bayanta a hankali.
“Zahra…” Ya kira sunanta cike da taushi
“You’ll be blessed.”
Ya ɗan ja baya kaɗan yana kallon fuskarta “Kar ki sa komai a ranki.”
“Muna son ki.”
“Kuma za mu bi miki haƙƙinki.”
Ya ɗaga hannunsa ya share mata hawayen da suka cika kumatunta.
“Sannan zan ci gaba da ɗaukar responsibilities ɗinki.”
Wani murmushi ya yi mata. “As a pleasure to me.”
Sabbin hawaye suka sake cika idanun Zahra, ta kasa cewa komai sai kallon mahaifinta take yi
Abbah ya sake rungumeta na ɗan lokaci kafin ya sake ta.
buɗe ƙofar parlorn akayi, Mummy ce ta shigo tare da Batoul
Sai dai Abbah ko kallonsu bai yi ba, ya san idan sun samu labari yanzu, cikin mintuna kaɗan familyn gaba ɗaya zasu sani
Ya juya wajen Ya Umar.
“Umar.”Ya kira
“Na’am Abbah.” Ya amsa yana ɗago kai.
Abbah ya miƙe tsaye “Tashi mu tafi.”
Ya Umar ya ce “Yanzu?”
“Eh.” Abbah ya amsa kai tsaye.
“Make sure ka kira barristers ɗinnan.” Muryarsa ta canza zuwa ta mutum mai yanke hukunci.
“Ina son na gansu yanzu.”
Ya Umar ya kalli Zahra na ɗan lokaci sannan ya gyada kai.
“Okay Abbah.”
Ya miƙe tsaye yana ɗaukar wayarsa. Yayin da Mami ke kallonsu
Ta san daga yanayin Abbah ba maganar sasanci zai yi ba, ba maganar haƙuri zai yi ba kuma
Ya Umar ya fara bin Abbah zuwa waje
#Jiddatulkhayr writes #08110615256