Kenza eBookz
Cover art for KOMAI YA YI FARKO  HAUSA NOVEL 14

Post

KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 14

.....do, then he said; "Cook for me today with your own hands," Humaira said silently as if she didn't want him to cook, but then she said; "It's over dear Zee." Hunaif smiled and licked her nose before he left and took his car keys and left. As he was going out, Zee went back to bed and went to bed, tossing and turning and complaining that it had been a week until he asked her to go into the kitchen, she took out her phone and called Intisar. "Hello bride with time." Zee made a white face and said; "Say it and say it again." "But if you went away and didn't call me until today, you will be happy for your husband." Zee laughed and said; "But you're a bitch Intisar, now that's not all, could you imagine that a week after I arrived, your cousin said I cooked for him." "Huh? Even if you're happy, you'll start reaping the rewards soon." Zee did it together and said; "What about the reward? All the teasing he does in bed is not enough, so I cooked for him as my bride. It's just that he didn't have the mood to buy us food for six months, so I apologized to him." Intisar was surprised and said; "Now, Zee, all the love you claim you have for Ya Hunaif, is it because he asked you to cook fo

Standalone post1,894 words

KOMAI YA YI FARKO

PAGE 14

Satin Zee ɗaya da zuwa Brazil, amma duk Hunaif ya gaji da halinta na rashin gyara, tsaftar da gidansa ke dashi kafin zuwanta ya neme shi ya rasa, sannan har yanzu babu abinda ya canza daga yadda take sallah babu lura da kuma ilimin yinsa, yana ƙoƙari sosai wajen yi mata gyara, amma sam ba ta ɗaukar gyaran. Hunaif is a very neat and arranged person shiyasa ya damu sosai da inda Zee ke scarter masa gida, ya yi mata magana har ya gaji. Yana rufe botir ɗin gaban rigasa ya kalle Humaira dake kwance tana kallonsa ɗauke da murmushi a fuskarta, kashe mata ido ɗaya yayi yace; "Wannan kallo haka wifey" "Ba dole in kalla wannan kyautar wuce daga da Allah ya yi min ba." Zee ta faɗa tana miƙewa, takowa ta yi zuwa gabanshi ta fara rufe mishi button ɗin. Light kiss Hunaif ya yi mata a bakinta, yace; "Nagode Wifey."

Langwaɓar da kai Zee ta yi, tace; "Don Allah kar ka daɗe a waje yau."

"Me za ki ajiye min? sai na dawo da wuri"

"Me kake so mijina?"

Dan tunanin seconds Hunaif ya yi, sai yace; "Ki yi min girki yau da hannunki"

Shiru Humaira ta yi kamar ba ta so yace girki ba, amma sai ta daure tace; "An gama masoyin Zee." Murmushi Hunaif ya yi, ya lakuce hancinta kafin ya saketa ya ɗauki car keys dinsa ya fita.

Yana fita Zee ta koma gado ta kwanta tana ta zumɓure-zumɓure da gunaguni wai ace satinta ɗaya da zuwa har zai ce ta shiga kitchen, wayarta ta janyo ta kira Intisar. "Hello amarya mai lokaci."

Zee ta yi wani fari da ido tace; "Ki faɗa ki sake faɗi."

"Amma ace tunda kika tafi ki kasa kirana sai yau, ke gaki miji daɗi."

Zee ta yi wani dariya tace; "Amma fa ke ƴar iska ce Intisar, yanzu duk ba wannan ba, could you imagine wai daga zuwana sati ɗaya tak ɗan uwanki wai na yi mishi girki."

"Haba? Ai ko kin ji daɗi, tun wuri za ki fara kwasar lada."

Haɗe rai Zee ta yi, tace; "Lada fa? Duk tumurmusheni da yake yi a gado bai isa ba sai na yi masa wani girki ina amaryata, dama dai bashi da halin siya mana abincine har na tsawon six months haka sai na yi mishi uzuri."

Sake baki Intisar ta yi da mamaki, sai tace; "Yanzu Zee duk son da kike ikirarin kina yi wa Ya Hunaif ashe don ya ce ki yi mishi girki zai zama laifi, Tunda kin san ya fi ƙarfin siyan abinci for six months to ya kamata ki san ƙilla gwadaki yake yi."

"Kuma fa hakane ƙawata, possibly gwada Ni yake, idan hakane kuwa zan dafa masa ko da indomie ne kar ya gan rashin kirkina."

"Indomie fa kika ce? Wai lafiyarki kuwa Zainab, girkinki na farko a gidan miji da zaki zuba dukkan iyawarki ki yi girki iya girki amma kice wai wani noodles, haba ZEE! Ki rinƙa yin abu saboda Allah mana."

"Ya isa haka Intisar!" Zee ta katseta a fusace, "Ai na manta ke ɗin dangin miji ce, da babu abinda zai saka ni yin hirar nan dake." Ta katse kiran ba tare da ta ba wa Inti daman sake faɗin wani abu ba. Inti ta rinƙa bin wayar hannunta da kallo baki a buɗe, she just can't believe wai ZEE ce ta hanging up call on her, ta san wasu halayyar Zee sai ita, amma ba ta san rashin hankalin Zee ya kai haka ba, nuna kanta da yatsa Inti ta yi, murya cike da mamaki tace; "wato Ni ɗin ce dangin miji?" Murmushi ta yi tace; "Lallai Zee za ki gan halin dangin miji kuwa." Wayarta ta ɗauka ta dannawa Hunaif kira, Hunaif na stadium ya gan kiran Inti, murmushi yayi ya picking call ɗin; "Ba mu tare na barta a gida, ina stadium." Hunaif ya faɗa kai tsaye bayan ya saka wayar a kunne.

"Babu wa?" Inti ta tambaya.

"Zee mana, don na san saboda kawarki kika kira, idan ba haka ba yaushe kika taɓa kirana."

Murmushi Intisar tayi, tace; "Na yi mamaki ma da ka gane ni."

"Ai Ni ɗin mai kirkine ba irinki ba."

"Na yarda, kuma In Sha Allah yanzu kam zan fara kira sai na baka mamaki."

"Allah ya sa Intin Mami."

Murmushi inti tayi tace; "Ya ƙawata take? Hope you're taking good care of her and she's doing same?"

"We're all doing great, alhamdulillah."

Murmushi Intisar ta yi tace; "Yaya ka ƙara haƙuri da ita please, I know how Zee can be."

Numfashi Hunaif ya sauke, yace; "It's fine Inti, thanks for your concern."

Ɗan tattaunawa suka ɗan yi kafin suka hangup, Intisar ta jujjuya wayar hannunta tana sakar murmushi, tace; "Da Ni kike zancen Zee, tun bayan aurenkin nan you're claiming to be stupid amma zan nuna miki nawa kalan wasar, Allah sarki ɗanuwana baka yi sa'ar mata ba." Ta zauna a bakin gado, tagumi ta buga tana tunanin me ya kamata ta yi wa Zee to make her come back to her senses.

________________

Washegari Humaira ta tashi trying hard to be strong, ta yi wa kanta alƙawarin ba zata sake saka damuwar fyaɗen nan a ranta ba, she believed it's her destiny, and she accepts it a yanda yazo mata, duk wanda yake doubting ɗinta kuma shi ya sani, wanda suke gulma da ƙaryayyaki akanta kuma is left for them, za su gani a ƙwaryar su.

Ta farka ne da ciwon kai mai tsanani, a daddafe ta iya tashi ta ɗora ruwan wanka, bayan ta yi wanka ta koma ta kwanta akan gado tana jin sanyi sosai, bargon Aisha ta ja ta lulluɓe jikinta har kai.

Aisha na shiga ɗakin daga ɗakin Ummanta ta gan Humaira lulluɓe da bargonta, tsayuwa ta yi a kanta tana kallonta, juya baya ta yi ta fice daga ɗakin.

Su Laurat suna fere dankalin da za a yi kari dashi Aisha ta fito, tace; "Baƙuwar ku bata da lafiya."

Ɗago kai Laurat ta yi ta kalle Aisha, tace; "Baƙuwar mu?"

Aisha ba ta ƙara cewa komai ba ta yi wucewarta zuwa ɗakin Ummanta. Laurat ta miƙe ta shige ɗakin, daga bakin ƙofa ta tsaya ta kalle Humaira dake kwance, takowa ta yi zuwa gaban gadon, yaye bargon tayi daga kanta, A hankali Humaira ta buɗe jajayen idanunta dake kumbure ta zuba su wa Laurat hawaye na bin gefen idanunta, Laurat ta zauna a gefen gadon ta riƙe hannunta da yayi zafi kamar wuta, tace; "Subhanallah, jikinki zafi kamar wuta, me ke damunki." Share hawayenta Humaira ta yi da bayan hannu, "Laurat ba zan iya ce miki ga abinda ke damuna ba, but I know ina jin zafi tun daga cikin jikina har zuwa waje, Laurat, I have a feeling ni ɗin ba zan yi tsawon rai ba, ku yafe mini idan akwai laifin da na taɓa yi muku a ƴar zama da muka yi daku, please." Humaira ta faɗa cikin murya mai tsananin rauni.

Da gudu Laurat ta fita daga ɗakin jin irin maganar da Humaira ke yi, ɗakin Ummansu ta shiga da gudu, Umma dake kwance tana sauraron labarai ta juyo da sauri jin yadda aka shigo mata a guje, miƙewa ta yi tana kallon Laurat, tace; "Lafiyar ki kuwa?"

Laurat ta girgiza kai, a rikice tace; "Umma babu wallahi, Humaira ce babu lafiya tun jiya da daddare, to yanzu kuma wasu kalan maganganu take yi kamar wacce za ta mutu."

Miƙewa Umma A'i ta yi hankali tashe ta fita daga dakin zuwa ɗakinsu, Hannatu na zaune a gefenta tana yi mata sannu suka shigo. Taɓa goshinta Umma A'i ta yi, da sauri ta cire hannunta, tana kallon Hannatu tace; "Ku taimaka mata ta shirya, yanzu zan kira babanku a kaita asibiti. Hannatu ta buɗe akwatin Humaira da kayanta kenan well arranged a ciki, dogon hijjab ta ciro mata saboda already tana sanye da simple gown a jikinta, taimaka mata ta yi ta tashi ta saka mata hijjabin. Hannatu na riƙe da ita suka fita tsakar gidan, Umma A'i tace su yi gaba bari ita ta sanar da Umma Rabi abinda ake ciki. Koda Umma A'i ta sanar da Umma Rabi cewa za su kai Humaira asibiti ba ta ji daɗi ba, taɓe baki tayi tace "A dawo lafiya." Girgiza kai kawai Umma A'i ta yi, ta fita ta bi bayan su Laurat da har sun riga da sun tare adaidaita sun zaunar da Humairan a ciki, Umman suke jira, Umma na shiga me adaidaita ya ja su.

Primary health care dake ƙasan unguwar su kaɗan suka kaita, bayan sun yanka kati suka nema waje suka zauna suna jiran layi ya kai kansu. Humaira ta kwantar da kanta a kafaɗar Umma A'i tana fitar da numfashi mai ɗumi. Suna zaune a wajen Malam Sadi ya zo ya same su, ciki ya shiga ya yi magana, sai aka dawo da file ɗin Humairan sama, sunanta aka kira next, Umma na riƙe da ita suka shiga office ɗin likita Abba na biye da su a baya.

Bayan doctor ya examining ɗinta, sai ya ɗaga ido ya kalle Mallam Sadi yace; "Malam ya aka yi haka?" Kallonta Abba ya yi confused yace; "Me aka yi?"

Likita ya gyara zamansa yace; "Ya aka yi kuka bari jinin ƙaramar yarinya ya haura sosai haka, sannan ta zauna da yunwa har haka?"

"Subhanallah hawan jini da ka ce likita, wallahi babu abinda ake mata." Malam Sadi ya kalle Humaira dake zaune shiru, yace; "Humaira ko dai wani abu ake miki a gidan idan ba na nan?"

Girgiza kai Humaira ta yi, tace; "Babu komai Abba, daman tun a gida ina da hawan jini."

"Damuwa ya yi miki yawa, me ke damunki?" Likitan ya tambaya yana tsare Humaira da ido.

Murmushn takaici Humaira ta yi, tace"My problem is better left unsaid." Shiru ta ɗan yi, sai tace; "Please doctor don't insist on knowing what my problem is, just prescribe medication for me, zan yi kokari wajen ganin na rage damuwa, though I'm trying, zuciya da ƙwaƙwalwata suke betraying ɗina."

Kallonta likitan ya yi da tausayawa, yace; "Zan ba ki magunguna, amma don Allah ki cigaba da ƙoƙari wajen ganin kin rage damuwa, sannan no matter irin damuwar da za ki shiga ki ɗaure ki rinƙa cin abinci, kar ki tsaya da yunwa."

Kai Humaira ta gyaɗa mishi, tace; "In Sha Allah."

Ko da suka koma gida Umma Rabi ko leƙowa ba ta yi ba, balle ta yi musu sannu, Malam Sadi kuwa da ya tabbatar da Humaira ta ci abinci ta haɗiye magungunanta kafin ya fita daga ɗakin zuwa ɗakinsa.

Yana shiga ɗakinsa ya dannawa Abban Humaira kira. Abban Humaira na wajen sana'ar sa ya gan kiran Malam Sadi, picking ya yi suka gaisa, kafin Malam Sadi ya yi wa Abba bayanin abinda ke faruwa. Abba jin yadda Malam Sadi ya shiga damuwa a tunaninsa a gidansa ne ake yiwa Humairan wani abu, ga kuma yarda da aminttaka dake tsakaninsu tun yarinta hakan ya sa Abba ya faɗawa Malam Sadi abinda ke damun Humaira, sannan yace zai tura Kabir gobe, yazo ya ji me ya tunar da ita raɗaɗin da ta gama yaƙi dashi, har ya kuma jefata cikin wannan yanayi da suke farincikin ta fita daga ciki.

ANYA KAWANTAKA ZAI ƊORE TSAKANIN INTISAR DA ZEE KUWA 🤔

ALLAH SARKI HUMAIRA, TANA BA NI TAUSAYI SOSAi😭

#Jikargarba✍️ 0748694211