
Post
FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 27
.....come? She didn't see any reason to do that, she just told her to go home without saying anything to her mouth. Then she raised her head, slowly she started telling her everything, from Pretty, to Lovie Dovie, to how Khalil goes out at night and doesn't sleep at home, to the pictures she saw with her friend. Maman listened to her without interrupting her, until Zahra finished, she was silent for a few seconds, then she said, "All men are like that Zahra" Zahra raised her head and looked at Jin what she said. Mom continued, "And you're not guilty, it's all your fault, Fatima." "Me?" Zahra asked in surprise, she didn't even say "Yes." Mom nodded. "Did someone tell you to touch your husband's phone?" Zahra was silent, looking somewhere else and then she said, "But Mom, when I stopped sleeping at home, I started touching the phone to see what it was." Mom said, "If you don't access his phone, you don't even know anything." Zahra was surprised, she thought that she would even feel sorry for her, or condemn what her son was doing, but it was the opposite. Mama continued to defend Khalil, "Khalil did not grow up in trouble, try to make him happy.....
*FARASHIN IZZAH*
Book 1 Chapter 27
Fitar Firdausi da wuya, aka ji ƙarar mota a compound, Farida ce ta leƙa ta window sannan ta juya da sauri ta haura sama
A hankali ta buga ƙofar ɗakin Zahra.
"Anty..."
Zahra ta ɗago kanta "Na'am?"
"Mama ce." Cewar Farida
Zahra ta haɗe gira "Wace Mama?"
"Maman Alhaji Khalil."
Nan take Zahra ta miƙe ta ce "Ina zuwa"
Toilet ta shiga ta wanke fuskarta da ruwan ɗumi, ta goge ta da towel sannan ta gyara scarf ɗinta kafin ta fito, hijab ta saka sannan sannan ta fita
A parlorn ƙasa ta same ta zaune, da alama daga gida take saboda babu alamar gajiya a jikinta
Zahra ta ƙarasa ta zauna "Ina kwana Mama."
"Lafiya lau" Ta amsa
Sannan ta ɗan yi murmushi.
"Na zo ne ina son na wuce office, nace Khalil ya kai min ke. Shine kuma nace bari na zo kawai da Kai na dan Ina da program da yanma"
Sai ta ɗan yi shiru. "Amma na ji kun samu matsala har shekaran jiya ya kwana a can gida?"
Zahra ta sunkuyar da kai, fingers ɗinta take wasa da su,
A da can zata iya ɓoye mata, amma yanzu? Bata ga dalilin yin hakan ba kawai gwara ta fada ko data koma gida karta ga bakinta
Sai ta ɗago kai, a hankali ta fara bata labarin komai, tun daga Pretty, har zuwa Lovie Dovie, har zuwa yadda Khalil yake fita da daddare baya kwana a gida, har zuwa hotunan da ta gani tare da kawarta
Maman ta saurare ta ba tare da ta katse ta ba, sai da Zahra ta gama, ta yi shiru na wasu dakiku, sannan tace,
"Ai duk maza haka suke Zahra"
Zahra ta ɗago kai ta kalleta Jin me tace
Mama ta ci gaba "Kuma ke ma kin yi laifi, gaba daya nan laifin ki ne Fatima"
"Ni?" Zahra ta tambaya cikin mamaki, bata ma sanda ta furta Ni din ba
"Eh." Mama ta gyada kai.
"Wani ya ce miki ki dinga taba wayar mijinki?"
Zahra tayi shiru tana kallon wani waje sai kuma ta ce
"Amma ai Mama sai daya daina kwana a gida shine na fara taba wayar dan ganin menene"
"Baki da wannan right ɗin" Mama ta katse ta
Zahra ta kasa magana.
Mama ta ɗora "Da baki shiga wayarsa ba ma da baki ga komai ba."
Wani irin mamaki ne ya rufe Zahra, ta zaci ko da kaɗan ne za ta ji tausayinta, ko ta yi Allah wadai da abin da ɗanta yake yi, sai dai akasin haka ne.
Mama ta ci gaba da kare Khalil "Khalil bai taso cikin kunci ba, ki yi ƙoƙari kina faranta masa rai sbd Namiji idan baya samun nutsuwa a gida ai zai fita waje ne"
Zahra ta haɗe hannayenta cikin juna tana kallon ikon Allah
Mama ta ɗora "Shi kaɗai gare ni Fatima, ba zan yarda wata mace ta saka shi gaba ba, Idan kina son zaman lafiya ki bi mijinki"
Daga haka ta miƙe tsaye
"Toh ni zan wuce" Ta faɗa, ba tare da ta jira amsa ba ta fice
Zahra ta bita da kallo har ta fita, sai kuma ta furta a hankali
"Sai dai idan wata matar ce zata bi sa..."
Ta girgiza kai "Amma ba Zahra ba"
Ta miƙe tsaye, kai tsaye sama ta haura, ta ƙarasa tattara sauran kayanta, da ta gama ta sauko ƙasa.
Farida ta fito da sauri "Anty bari na zuba miki abinci."
Zahra ta so cewa a'a, sai kuma ta taji kamar yunwa take ji, ta gyada kai
Farida ta zubo mata abinci, ta zauna a parlon tana ci a hankali ta ɗauki wayarta, ta kira Ya Umar
Yana shiga bai daɗe ba ya ɗaga "Hello Baby."
Ya faɗa da fara'a.
Zahra ta ɗan yi murmushi. "Yaya."
"Uhm Zahrah."
"Barka da aiki."
"Yauwa. Ya jikin?"
"Da sauƙi."
Sai ta ɗan yi shiru.
"Yaya ƙarfe nawa zaka koma gida?"
"Maybe wajen biyu" Ya amsa.
"Me ya faru?"
"A'a." Ta girgiza kai duk da baya ganinta.
"Nima ina zuwa ne, na fitson idan zan tafi kana gidan ne"
Ya Umar ya yi shiru na ɗan lokaci.
Sai yace "Toh can't wait to see you"
Daga haka suka yi sallama, a kashe wayar.
Sai ta buɗe Instagram. Tun da ta yanke hukunci rabuwa, tana son goge duk wani abu da ya haɗata da Khalil a page dinsa
Ta shiga profile ɗinsa, da niyyar fara goge hotunansu, selecting tayi ta goge su tass, ta fita zata shiga chats dinta da shi
Sai dai kafin ta yi wani abu... Wani post ya faɗo mata a timeline, da farko bata kula ba, sai kuma ta sake kallon hoton
Nan take gabanta ya faɗi, ta matso da wayar kusa da fuskarta
"What...?" Ta furta a hankali.
Sai taga notifications suna ta shigowa, ga uban tags Da sauri tayi switching to acc dinta, Tana shiga mutane suna ta tagging ɗinta
Da sauri ta shiga post ɗin, zaro Idanu tayi, ta miƙe tsaye ba tare da ta san tayi hakan ba
Cokalin da ke hannunta ya faɗi ƙasa, numfashinta ya fara canzawa, zufa ta fara keto mata
Comments suna ta shiga babu ƙaƙƙautawa, Likes suna ƙaruwa a seconds, shares suna ta karuwa
Ga uban maganar da mutane suke yi, sosai ta hada zufa, mutane suna ta mamaki, wasu suna ta tambaya, abu ne da ya isa hannun dubban mutane cikin ƙanƙanin lokaci.
Zahra ta dafe bakinta, ta kasa ko magana.
Domin abin da take gani a screen ɗin wayarta... bata taɓa tsammanin zai fito duniya ba
"Wai ya akayi...?"Ta furta a hankali.
"Ya akayi wannan ya fito?" Yatsunta na rawa ta shiga comment section.
Comments kuwa sai shigowa suke yi
"Saudat is evil wallahi." "How can you do this to your friend?" "This is betrayal" "Poor Zahra" "Na shiga page ɗin Zahra yanzu ma. Ashe friends ne tun secondary school" "Kai duniya" "Allah ya isa"
Wani ya saka screenshots na hotunan Saudat da Zahra da suke tare a Instagram, mutane suna ta ɗauka suna resharing post, suna nuna yadda suke fita tare,yadda Zahra take kiranta sister, yadda suke comment a posts ɗin juna, abin da ya ƙara dagula mutane kenan
Wasu na zagin Saudat, wasu na tausayin Zahra, wasu kuma na zagin Khalil
"Wife like Zahra kuma ka je ka bi kawarta?"
"Khalil should be ashamed of himself."
"This man is shameless."
"No wonder she looks unhappy these days."
"Men can be wicked."
Kowane refresh da Zahra take yi sai ta ga sabon zagi, sabon comment, sabon repost.
Zahra ta zauna a hankali kan kujera, wayar na hannunta, amma gaba ɗaya jikinta ya mutu
Abu ɗaya kawai yake yawo a ranta, waye ya fitar da wannan? Ta yaya ya samu?
Saboda hotunan da ta gani a wayar Khalil... ba kowa ne zai iya samunsu ba, sai wanda ya shiga wayarsa, wanda ya samu access ɗinsa
Can ta ji ƙarar buɗe gate, amma ko kallon kofar parlon bata yi ba, hankalinta gaba ɗaya yana kan screen ɗin wayarta
Har aka buɗe ƙofar parlorn, bata ɗago kai ba, har aka yi taku zuwa ciki
Sai kawai taji wata tsawar murya. "KEE!"
A firgice ta ɗago kai
Khalil ne, fuskarsa a hade kamar kunu Idanunsa sun yi ja, numfashinsa ma a bayyane yake saboda tsananin fushi
Tun daga ƙofar parlorn yake nuna ta da yatsa.
"ME KIKE SO KI MAYAR DA RAYUWATA NE?!"
Zahra ta zuba masa ido kawai, Khalil ya ƙaraso gabanta
"Dan uban ki baki ji Ina miki magana bane?" Ya faɗa cikin tsawa.
"Saboda baki samu abin da kike so ba sai kika je kika watsa ni a duniya ko?!"
Zahra ta ci gaba da kallonsa, kamar ma ba ita yake yi wa magana ba
Abin ne ya ƙara ɓata masa rai
"Kin yi hauka ne?!" Ya daka mata tsawa
"Dama plan dinki kenan ba? Ke da wannan ƙawar taki marar tarbiyyar!"
Nan ya fara zaginta itakam tama shiga shock ne
Khalil ya tsaya gabanta yana huci,
"Ke kika yi wannan ba!"Ya sake faɗa.
Zahra ta girgiza kai "Wallahi bani bane, ban san ya akayi waɗannan hotunan suka fita duniya ba"
Khalil ya yi wani irin dariyar takaici.
"Bayan na kama ki da wayana a hannunki? Har kina da bakin magana?"
"Khalil, gaskiya nake yi...." Kafin ta ƙarasa maganar.
Paa!
Mari ya sauka a fuskarta.
Zahra ta karkata gefe saboda zafin marin, wayar hannunta ta faɗi ƙasa
Farida dake kitchen ta firgita, da sauri ta leƙo.
Sai taga Khalil ya sake kai mata wani marin.
Paa!
A razane Farida ta juya da gudu ta koma ɗakinta ta kulle ƙofa, gabanta sai bugawa yake
Khalil ya gama fita hayyacinsa.
"Zaki sa duniya ta zage ni?!" Ya faɗa yana sake kai mata duka
"Zaki sa mutane su raina ni?!"
Zahra na ƙoƙarin ja baya, Tana kuka ta ce
"Khalil ka tsaya! Khalil wallahi ba ni bane! Lemme explain plss"
Amma ina, ko sauraren ta baya yi, ya sake fizgota, ya tura ta da karfi
Zahra ta juya da niyyar guduwa, sai kawai ta ji wani irin bugun a ƙafa, Khalil ya kwarfeta
Da ƙarfi ta faɗi ƙasa, kafin ta miƙe ma ya isa kanta, ita kuma sai faman ihuu take a zo a taimake ta
Mari ya fara sauke mata, baji ba gani Zahra ta fara kare kanta da hannayenta
"Khalil! Khalil dan Allah! Ka tausaya min, ka yarda da ni bani bane"
Amma gaba ɗaya baya jin ta, dukanta yake yi
Wani irin azaba ya ratsa mararta, wani sharp pain mai tsanani, nan take ta saki wata ƙara
"Wayyo Allah!" Ihun da ta yi ya cika gidan Baki daya
Ta riƙe mararta da hannu biyu, Fuskarta har murɗewa yayi saboda azaba
A dai-dai lokacin... aka turo ƙofar parlorn da ƙarfi
Bang!
Ya Umar ya shigo da gudu, Idanunsa sun yi ja saboda fushi.
Ko kallon Zahra bai yi ba, kai tsaye ya nufi Khalil
Kafin Khalil ya ankara.
Poom!
Ya Umar ya kai masa naushi a fuska.
Khalil ya ja baya sbd azaba, kafin ya gama recovering sai wani naushin, sai wani
Ya Umar ya kama rigarsa, ya sake kai masa fist.
"Mahaukaci kawai!" Ya daka masa tsawa.
"Fuck you, har ni zaka yi fada da?!" Khalil ya yi ƙoƙarin maida martani
Ya Umar ya sake kai masa wani naushi, har ya bige da kujera ya ce
"Zahra zaka taba???!"
Parlorn ya rikice, sai fasa abubuwa suke sun canza ma komai position
Zahra kuma ke kwance a ƙasa tana riƙe da mararta, Yayin da Ya Umar ke ci gaba da kai wa Khalil duka cikin fushi irin wanda bai taɓa yi ba
Domin abu ɗaya kawai yake gani a gabansa, kanwarsa, kanwarsa mai ciki, da aka daka
Farida ta fito daga ɗakinta da gudu, kukan Zahra da ta ji ne ya kasa barinta ta ci gaba da zama a ciki
"Anty Zahra!" Ta kira tana duban wajen.
Sai kuma ta tsaya cak, gabanta ya faɗi
Zahra na kwance a ƙasa, ko motsi bata yi, abin da ya fi firgita Farida kuwa... Jinin da ta gani
"Wayyo Allah!" Ta kwalla ihu.
A gigice ta ruga zuwa gareta, ta durƙusa
"Anty Zahra!" Ta jijjigata.
"Anty!"Amma babu amsa
Farida ta kalli Ya Umar, hawaye suka cika idanunta
"Yaya!" Ta yi ihu.
"Yaya dubi Anty Zahra!"
Ya Umar yana shirin sake kai wa Khalil naushi ya juya.
Farida ta kamo hannunsa, tana jan sa.
"Ka dubeta! Ka dubeta mana!"
Ya Umar ya bi inda take nunawa da ido.
Ganin Zahra kwance cikin jini kawai ya tsaya cak, kamar an dasa shi a wajen.
Duk fushin da yake ciki ya gushe lokaci guda.
"Ya Allah..." Ya furta a hankali Ya ƙarasa da sauri
Ya durƙusa a gefenta.
"Zahra." Ya kira.
"Baby." Ya sake kira.
Amma babu amsa.
Farida ta fashe da kuka.
"Mu kaita asibiti!" Ta faɗa cikin kuka.
"Dan Allah mu kaita asibiti!"
Nan take Ya Umar ya dawo cikin hayyacinsa.
Ya saka hannu ya ɗaga Zahra Jikinta babu wani ƙarfi, yayi kofar da ita Farida ta ci gaba da kuka tana binsa a baya
A lokacin ne Khalil ya miƙe daga ƙasa.
Fuskarsa duk ta kumbura saboda dukan da Ya Umar ya masa. Da alama zai sake kai wa Ya Umar hari
Tuni su kuma sun fita Farida na binsa tana kuka, suka fita compound.
Mai gadi ma ya fito cikin tashin hankali, yana tambayar meke faruwa
Amma babu wanda ya tsaya masa.
Kai tsaye suka nufi mota. Ya Umar ya buɗe ƙofar baya.
A hankali ya kwantar da Zahra.
Farida ta shiga kusa da ita.Tana riƙe hannunta tana kuka.
"Anty Zahra ki tashi."
"Dan Allah ki tashi."
"Ki yi magana."
Ya Umar ya shiga seat ɗin direba, hannunsa har rawa yake, ya tada motar.
Da ƙarfi ya fice daga compound ɗin.
A hanya kuwa...
Babu wanda yake magana, sai sautin kukan Farida.
Da kuma bugun zuciyar Ya Umar wanda yake jin kamar zai faso ƙirjinsa.
Karo na farko a rayuwarsa... Ya ji tsoro irin wannan Tsoron rasa mutum
Ya ci gaba da sharar gudu, kai tsaye zuwa asibiti
Da ƙyar Ya Umar ya iya parking motar saboda yadda hannayensa ke rawa
Tun kafin motar ya gama parking,ya buɗe ƙofar baya da sauri, Zahra na kwance babu wani motsi da take yi
Farida kuwa kuka kawai take yi.
"Dan Allah ku taimaka mana!" Ta fara faɗa tun kafin su shiga cikin asibitin
Da gudu Ya Umar ya ɗauki Zahra ya nufi emergency unit, Nurses da ke wajen suna ganinsu suka ƙaraso da trolley
"Meyafaru?" Ɗaya daga cikinsu ta tambaya
"Babu lokacin bayani, Kawai ku taimaka mata!" Ya Umar ya faɗa cikin tashin hankali
Da sauri suka kwantar da ita a trolley suka shiga da ita ciki.
Ya Umar da Farida suka bi bayansu, sai dai a bakin ƙofar emergency room aka tare su
"Please ku jira a waje." Nurse ɗin ta faɗa.
"Amma...."
"Please." Nurse din ta katse Ya Umar, daga haka ta shige ciki hadi da rufe kofar
Ya Umar ya tsaya yana kallon ƙofar, kamar idan ya ci gaba da kallonta zai ga abin da suke yi a ciki
Farida kuwa ta zauna kan kujera tana kuka har sannan, wasa wasa kusan awa kenan, Ya Umar kuma lokaci zuwa lokaci sai ya tashi ya zaga ya kuma dawo ya zauna, hankalinsa ya kasa kwanciya,
A ƙarshe wani doctor ya fito.
Da sauri Ya Umar ya ƙarasa wajensa.
"Doctor?"
Likitan ya kalle shi.
"Are you a family member?"
"Eh." Ya amsa ba tare da wata-wata ba.
Likitan ya gyada kai. "Mun fara bata first aid da emergency treatment."
Ya Umar ya haɗiye miyau. "Yaya take toh Dr?"
Likitan ya ɗan yi shiru. "Sai mun gama wasu checks tukuna, amma tana ƙarƙashin kulawa."
"Please ku kwantar da hankalinku."
Ya Umar ya gyada kai. Amma hankalinsa ya katsa kwanciya
Likitan ya koma ciki.
Ya Umar ya tsaya yana kallon ƙofar, sai a dafe kansa
Sai yanzu ma ya tuna da Abbah, dole ya sanar da shi
A hankali ya zaro wayarsa, ya shiga contacts
Yatsansa ya tsaya kan sunan Abbah, sai ya danna call
Abbah na daga wa yace
"Umar."
Muryar Abbah ta fito. "Lafiya dai?"
Ya Umar ya lumshe idanunsa Karo na farko muryarsa ta kasa fitowa yadda ya kamata.
"Abbah..." Ya kira a hankali.
Nan take Abbah ya gane akwai matsala
"Me ya faru?" Ya tambaya cikin damuwa.
Ya Umar ya haɗiye miyau.
"Abbah... Zahra tana asibiti."
Shiru Abbah yayi na wasu dakiku, sai kuma a dan rude yace
"Asibiti? Me ya same ta?"
Ya Umar ya dafe goshinsa Idanunsa suka cika da ƙwalla.
"An samu matsala ne..."
Ya faɗa cikin sanyin murya.
"Yanzu tana emergency."
Abbah ya miƙe tsaye daga inda yake zaune
"Umar." Ya kira
"Ka gaya min me ya faru da Zahra."
Ya Umar ya runtse idanunsa
"Bleeding take yi, shine aka kawota asibiti"
Few pages left, book 1 ya kusa karewa