Kenza eBookz
Cover art for HIYAAM  HAUSA NOVEL PAGE 8

Post

HIYAAM HAUSA NOVEL PAGE 8

..... yes, most of the time he and Haysaam are surprised by the way Ana looks at him, she remembers "Anything and everything" on his face. "Did you brush?" She said slowly. Then he stopped and looked at her, "No, what about you?" He didn't answer after a few seconds. She opened her eyes and winked at them, "I smelled your mouth." She said, staring at him with her big eyes, and he saw her smiling and blinking her eyes as if she was joking with him, "Uhm, get up and have breakfast." "Did you stop going to Lagos?" "No" he said shortly after sitting up. She was looking at him before she said "Will you marry me?" He heard what she said, so he said, "What are you going to eat before you take the medicine?" She lowered her head and did not say anything, it was not long before the doctor came in, he put two fingers and lifted her chin and he saw something he did not expect, she was crying silently and tears were pouring from her eyes and slowly falling down her face. "Nanaah.... "Jerry" answered. "What? Is it the body? I don't want to cry for nothing." "I don't like Innti's husband, I don't want to see him, Yaa Sam, go to me and sit on your back and listen." Seeing that she was serious, he

Standalone post6,459 words

*H I Y A A M*

Page 8: Tajmahar Palace

Bright pens Yota/001

"No one be like you" Nazeefah Sabo Nashe

Ganin ta zuba masa idanunta masu tasiri a jikinsa da zuciya ya sake ɗan ranƙwafawa ya share mata zufar fuskarta yaja hancinta kaɗan ya ce "Na ɗaga ki ne ki yi breakfast?" Sai ta girgiza masa kai kaɗan tana lumshe idanunta ƙirjinta na ɗagawa sama-sama da sauri ta buɗe ta ce "Yaa Sam ciwo nake ji"

Da damuwa ya ce "A ina?"

"Nan" ta nuna masa mararta.

"Sosai take mini ciwo, ina jin ciwo Yaa Sam" Ya yi jim cike da tausayi yana jin duk wani pain da Ana take ji a zuciyarsa kamar tare suke raba damuwa da raɗaɗin, duk farincikin da yake ciki muddin ya yi arba da fuskarta ya hangi damuwa zai ji bashi da saurin wani farinciki. "Sorry jerryna" ya faɗa a tausashe da laushin muryar nan tasa me cike da nutsuwa da kamala, ganin yadda take ta zufa ya saka ya ɗan miƙa bakinsa kaɗan ya hura mata iska yana me share mata zufar ita kuma sai bin fuskarsa take yi da kallo tsinin hancinsa tafi kalla fiye da komai, da yawan lokaci shi da kan shi Haysaam yana mamakin irin kallon da Ana take binsa dashi, ta haddace ”Anything and everything” da yake fuskar tashi. "Ka yi brush?" Ta ce a hankali.

Sai ya tsaya ba tare daya kalle ta ba "No, ya akai?"

Ya bata amsa after a few seconds. Taja ido ta lumshe su

"Na ji warin bakinka ne"

Ta ce tana kakkafe shi da manyan idanunta sai kuma yaga tana murmushi da lumshe idanunta alamar wasa take masa "Uhm, tashi ki yi breakfast"

"Ka fasa tafiya Lagos ɗin?"

"No" ya ce a gajarce bayan ya ɗagota zaune.

Tana ta kallon shi kafin ta ce

"Zaka dani?"

Ya ji me ta ce, sai ya share ya ce "Me za ki ci kafin ki sha maganin?" Ta yi ƙasa da kanta bata ce komai ba, baya ya yi kaɗan ganin tuni lokacin shigowar likita ya yi ma, yatsu biyu ya saka ya ɗago haɓarta abin da bai zata ba ya gani, kuka take yi kuka mara sauti sai hawaye ne suke zuba daga cikin idanunta suna sauka a fuskarta a hankali.

"Nanaah....

"Jerry" taƙi amsawa.

"Menene? Jikin ne ? Ban son kukan banzan nan"

"Bana son mijin Innti, bana son ganinsa Yaa Sam ka tafi dani na zauna a wajanka ka ji" Ganin da gaske take yi sai ya saka yatsu biyu yana goge mata fuska, sosai su Ana suke cikin talauci, wannan shi ne karo na farko kuma daya taɓa ɗora hannunsa a jikinta laushin da taushin fuskar Ana ya ɓaci, kodayake bai ci ya yi mamaki ba, sabulun wankanta, man shafawarta, turaran fesawa duka Haysaam ne ya ɗauke responsibilities ɗinsu.

"Shikenan, fara cin abincin"

"Fitsari nake ji" ta ce tana kumbura fuska.

"Ok. Na kai ki toilet ɗin kenan?" Sai ta yi saurin juyowa ta dube shi, ya ɗaga mata gira. "To kai ni" ta ce tana bubbuɗe idanunta yana miƙewa da tattara hannun Jallabiyarsa kafin ya yi aune ta miƙe ta shige toilet ɗin tana sakin ƴar ƙara "Auchhii"

*** Tsit cikin dajin ya ɗauka babu ƙarar komai sai ta tsuntsaye da suke kuka a saman bishiyoyi. Daji ne me duhun gaske da hatsari wanda yake da wahalar fahimta kai tsaye. Daga gefe guda kuka ne yake tashi daga muryoyi daban-daban, kai tsaye muryoyin sun nuna alamar gajiyawa da wahala da gazawa da gangar jikinsu ya yi.

A hankali ya fito daga cikin rumfar da suka kafa ta ƙawa da hutawa, cikin nutsuwa da gadara yake taka ƙafafuwansa da suke cikin wani kyakkyawan takalmi baƙi a ƙasan wajan. Kallo ɗaya za ka yi wa fuskarsa ka fahimci bai haɗa hanya da imani a zuciya ba, fari ne irin farin nan mara shiga ido, sumarsa har baya baƙa suɗik da ita, sick pack ɗinsa a bayyane yake yana ɗan motsawa ƙirjinsa yake fara rawa. Ash ɗin riga ce a jikinsa armless wacce ta saka rabin ƙirjinsa bayyana.

Daga gefen wuyansa rubutu akai da zane na baƙi inda aka rubuta Triplets-T, iya wannan ne ya bayyana sauran riga ta rufe su. Yana fitowa sauran yaran suka mimmiƙe tsaye daga sabgogin da suke yi. Ɗaya daga cikinsu ne ya kalli wanda ya fito ya ce.

"Ya kamata mu bar wajan nan soon fa"

Sannu a hankali ya juya ya kalli wanda ya yi maganar ya ce

"Kana bani umarni ne?" Sai ya girgiza kai. Ya ce "Akwai matsala ne Oga Hunter shi ya sa"

Wanda aka kira da Hunter ya saka hannu wajan zare glasses ɗin idanunsa ya jim for a while kafin ya numfasa ya ce "Zaman nan ɗin akwai nishaɗi na ganin korayen tsirre, takura ɗaya ce babu sararawa, dole mu yi haƙuri tunda muna under control na T.T.T ne, sai an cika aikinsa za mu tafi"

Jago ya fesar da numfashi can ya ce "Triplets-T, sa baka da dariya sai hamma, uban mazaje maganin mara kunya. Hunter yanzu ya ake ciki ne?" Sai ya ɗaga kafaɗa alamar rashin sani. Ya cigaba da takawa har zuwa inda tarin jama'ar suke, yawancinsu Fulani ne, manoma da makiyaya sai ɗaiɗaiki. A gaban wata dattijuwar mata ya zauna yana kallon ta wacce ta gama fita daga hayyacinta bata iya buɗe idanunta sama-sama haka numfashinta yake fita. Ya zaro chigger daga alijuhunsa ya saka leta ya kunna yana fesar da hayaƙin a fuskar matar. Ya muzar kaɗan. "Dattijuwa to ya? Are You in or out?" Ya zuƙi tabar ya fesar kafin ya ce

"Kina da rayuwar ƴanci a gaba idan kikai mana yadda muka so, bama buƙatar ko kwabo don ba mu yi kama da ɓarayin jama'a ba. Abu ɗaya mukai requesting, ki fita daga cikin Addinin Musulunci, kina fita daga Muslunci za ki samu rayuwa me kyau da tsaf a tattare damu"

Tana daga ƙwancen ƙirjinta na ɗagawa ta tofa masa yawon cikin bakinta wanda da ƙyar ta tattaro shi, laɓɓanta ya tsage yana zubar da jini ta ce "Allahu ahad, Allah ɗaya ne, kuma shine ya turo mana da Addinin Musulunci ta hannun Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, mabiya addinin Islama sune akan daidai muna kan daidai" ya miƙa hannunsa zuwa kan fuskarsa ya lakato yawon bakinta data tofa masa. Ya murmusa kaɗan ya ce. "While.........

Sai ya juya zuwa bayansa ya ce "Jago, wai ta ce ba zata fita daga addinin musulunci ba, me ya kamata a yi?" Wanda aka kira da Jago yana tattare belt ɗin wandonsa bayan ya fito daga wani lungu da wata yarinya wacece ya ci mutuncinta ya barta a wajan ya saki dariya. "Hunter wannan hukuncin yana hannunka ai, me girma Triplets-T ya bar komai a wajanka har zuwa sanda zai shigo ciki"

Hunter ya kalli matar ya ce "Hajju kin ji fa? Try your best kina da last chance na kasancewarki a raye, fita daga Muslunci ko rayuwa me kyau"

"Allah ɗaya ne, bashi da abokin tarayya, bai haifa ba, kuma ba'a haife shi ba, shine ya samar da Addinin Annabi Isah ɗan Maryama, kuma a bayan Addinin Yesu, ya kawo mana Addinin Musulunci, Addinin ƙarshe, Annabin ƙarshe, zamanin ƙarshe. Na shirya mutuwa akan addinina, ban san dalilinku na san raba mu da addininmu ba, ko ma mene idan addu'ar Ubangiji Ya hana ku cimma burinku, Allah Ya wulaƙantaku, Allah Ya ɗaukaka Muslunci da Musulmai" ta faɗa da wata murya me cike da alfahari jikinta na ƙara samun ƙwarin gwiwa tana jin babu wani mutum daya isa ya rabata da Addininta.

Hunter ya yi baya kaɗan, a hankali ya ɗora hannunsa a daidai gaban wandonsa ya janyo shi kaɗan, har ana iya ganin ƴar kwantattun sumar mararsa ya shiga rawa da juyi kaɗan, idan ya ɗan tura gaba sai ya yi baya. Yana rera wata waƙar Square. Jago dake gefe ya shiga murmushi yana rungume hannunsa.

Sannu a hankali ya daina rawar ya kalli Jago ya ce "Wa'azi take mana fa Jago, zaka jure ji ne ko yaya?" Jago ya ce

"So boring gaskiya"

Nan da nan Hunter ya haɗe fuska kamar bashi ya gama waƙa ba, a wannan lokacin duk wanda ya kalli fuskarsa sai ya girgiza ya ji gabansa ya faɗi ya ji kuma kamar ya saki fitsari a wando. Ya durƙusa gaban matar, ya zuba mata fararan manyan idanunsa kafin ya zaro wata kaifaffar wuƙa a ƙugunsa me kama da zarto, ganin hakan ya saka mutanen da suke ɗaure suka fasa gigitaccen ihu, suna rungume na kusa dasu, ƙafa ɗaya Hunter ya saka ya danne kan matar ya saita wuyanta daidai maƙogaranta ya shiga yanka wuyanta, zillo take jini na feshi ta wuyanta, bata gushe ba tana ambaton Allah da kalmar shahada tare da yin kaffa tare da shure-shure har rai ya yi halinsa.

Yau sun kashe mutane wajan goma akan ƙin fita daga Musulunci, da yawansu kuma waɗanda aka kashe Fulani su gaba da baya. Jago ya ce

"Ga wata fara kyakkyawa can, ko za'a kiwatawa Triplets-T ne ita?"

Hunter ya juya ya kalli yarinyar wacce ta ƙurawa gawar mahafiyarta idanu sai ya girgiza kai ya ce "No need, ba layinsa bane, ya dai bada umarnin duk matan da suke wajan ko ba'a kashe su ba, a tabbatar sun san namijin a gun nan so idan kana ra'ayinta go ahead" Jago ya ce

"Kai baka da ra'ayi ne ?" Hunter ya tattare girarsa biyu ya ɗage zuwa sama kafin ya ce "Tawa tana can duk runtsi zam koma gare ta, Ayshatuna matar Hunter yaron T.T.T. na hannun damar Triplets-T" yana faɗin hakan ya koma cikin rumfar daya fito.

*** TAJMAHAR PALACE.

Shirun da masarautar ta ɗauka na yau na musamman nan, ba sai an yi shela an faɗawa mutum wani abu na musamman yana faruwa ba, duba da yanayinsu manyan jami'an masarautar da suke tsaye tun daga gate na farko har zuwa na huɗu. Masarautar Tajmahar ba kawai masarauta ce ba, duniya ce gudu ta musamman, masarautar da take da iko da zartarwa, masarauta ta zamani da kayan ƙawa. Ginin golden ne da ita me haske da ɗaukan idanu tun daga sama an rubuta TAJMAHAR PALACE. Doka ce aka saka tun satin daya shige, an rufe shiga da fitar mutane, idan kana cikin Tajmahar kar ka fara yunƙurin fita, idan kana waje kar ka yi tunanin shigowa ciki, wannan umarni ba iya na jama'ar garin bane, hatta hadimai, bayi, barori, da ƴan majalisa na fada umarnin ya hau kan su, ba iya su ba, hatta jinin Tajmahar wannan ƙararrawar umarnin ta hau kan shi. Tor Tiv ne kawai me yin yadda yasu a daidai wannan lokacin.

Sannu a hankali ya fito daga ɓangarensa, yana taka ƙafafuwansa kamar baya son taka su, duk inda ya ɗora ƙafarsa ɗaya sai ya ɗan jira, da yawan lokaci wannan izzar da gadara bata biya damunsa ba, sai ya sako ƙafarsa zuwa Tajmahar, jinin Tajmahar ya ƙara sanar dashi waye shi, matsayinsa da abin da yake jira. Farar fatarsa me ɗaukan ido sai sheƙi take yi ta dalilin wuyan da yake sakkowa daga gashin wuyansa yana sauka a fatar wuyansa tare da sakkowa jikinsa. Garden za shi, har ta gilma ya ɗan ja ya tsaya, ya ɗauki lokaci yana kallon waje guda kafin ya juya zuwa inda ya ganta zaune ɗaure da sarƙa a jikinta.

Jikinta duk ya farfashe jini na zuba a jikinta, gashin kan nan nata a diddige, wannan shine karo na uku yana ganinta, dukkan bayin Tajmahar ai ba'a nan suke ba, me ya sa aka fito da wannan waje ne? Miƙewa ta yi a hankali ta fara tafiya duk inda ta taga jini take bari shaida. Har zai shige sai ya dubi wani badakare, cikin sauri badakaren ya yi ƙasa da kan shi sai kuma ya ce "Umarninka biyayya ne Madaki"

Wanda aka kira da Madakin ya juya ya cigaba da tafiya yana jin bugun zuciyarsa na ƙaruwa. Tun kafin ya kai waje ake yin ƙasa da kai tare da rusunawa har ƙasa, a haka ya shige hadaɗɗan garden ɗin yana shiga ya ƙarasa kan wata kujera wacce take a kwance ya bi kan kujerar ya kwanta idanunsa na kallon saman masarautar Tajmahar ɗin.

*** Duk da sanyin safiya ne wajejen 11:30 bai hana su jeruwa a majalisar da suke zama koyaushe suna sana'ar tasu ta karta ba. Su wajan biyar ne yanzu ma, Alhaji Baita, Daada, Ɗahe sai Garbati na ƙarshen kuma Sadisu. Tsofaffi ne masu iyalai da kuma shekaru sai dai sun lalata tsofan su wajan son abin duniya da kuma aikata saɓo. Daada ne rangwamen shekaru a cikin su. "Daada ko dai kana jin tsoro ne?" Garbati ya yi furucin yana daidaita zaman shi tare da kallon katin kartar dake hannun Daada. Yau ne suke yin cacar da Daada ya saka Iftihal a ciki, don haka wasai Daada yake jin zuciyarsa yana hasaso kan shi nan da mintina biyar ko goma ya zama mamallakin Naira biliyan Ashirin cif. Sai murza raguwar katin daya rage a hannunsa yake me alamar Square 2 sai ya jinjina kai

Ya ce "Garbati me kake ci na baka na zuba?"

Cikin sauri Garbati ya ce "Ɗoki da zumuɗi mana"

"Muje zuwa" Alhaji Baita ya furta yana cilla Square 1. Bayan ya saka ya dubi Daada ya ce. "Zagayenka ne abokina" ganin alamar nasara a tattare da Daada sai ya yi murmushin daɗi da farinciki

Ya ce "Nasara tawa ce"

"Ina maka fatan samun ta" In ji Alhji Baita ya yi masa raddi

Daada ya cilla Triangle 1 . Sai ya rasa juyinsa don haka ya yi hold on. A tunaninsa Alhaji Baita bashi da sauran katuna ya yi murmushin jin daɗi ya ce "Na rasa katina, na yi nasara" ya fara miƙewa tsaye da shirin ɗaukan jakar.

"Last card!" Alhaji Baita ya faɗa yana ajjiye katin hannunsa, Daada babu yadda zai yi yana ji yana gani Alhaji Baita ya saka katin kuma ya yi nasara. Zufa ta shiga yankowa Daada a kowanne ƙofa na gargasar jikinsa. Ba wai murnar kuɓutar da ƴarsa yake yi ba, baƙincikin rashin samun miliyan ashirin ɗin ita take ƙoƙarin ganin bayansa a yanzu. "Kuɗina ya dawo, kuma na ci yarinyarka a caca Daada, ba tare da kowa ya ji ya gani ba, ka shirya ƴarka ka kawo mini ita gidana a matsayin yarinyar da na ci a caca finally" ya faɗa da murna yana tattara kayan.

Daada ya kalli Alhaji Baita da jajayen idanunsa na makakku ya ce "Kutumar, kana nufin ka tafi da miliyan ashirin ɗin kuma na baka yarinyar da nake kallo matsayin jari? Ai da na baka Iftihal gwara na kama mata hayar shago a sabon gari ta dinga samar mini kuɗi, daman na jima da wannan burin" "Ka yi ƙarya, ka kuma kwana da yunwa Daada" Alhaji Baita ya miƙe tsaye yana kallon Garbati ya ce "Ɗakko mini yarjejeniyar nan Garba" cikin sauri ya fito da ita, Alhaji Baita ya amsa ya nunawa Daada.

Ya ce "Wasan WHOT wasa ne na haramci wanda idan jami'ai suka ji za su kama mu, kaina talaka kai zaka dauwama a wajansu bani da asara ni kam. Ina baka shawara bakinka a laikum ka je ka fito mini da ita"

"Na baka Iftihal a matsayin me?" Cikin isa da izza Alhaji Baita yana dariya ya ce

"A matsayin yarinyar da na ci a caca" Dadda ya haɗiye wani abu me ɗaci a maƙoshi yana ayyana yau har Innti ta shiga uku a wajansa. "Na ji, ina nufin aurenta za ka yi ko me? A matsayin me za'a kaita"

"Ko a matsayin mene baka da ruwa da tsaki, zan dinga hutawa ne a jikinta ba wani abu ba" Kallon Alhaji Baita kawai Daada ya yi kafin ya juya ya bar wajan. "Kar ka manta" Cewar Alhaji Baita "A daren nan za'a kawo ta bani da haƙurin jira na gama kaiwa geji"

WHOT wasa ne na katuna da ake yi domin nishaɗi ko gasa, inda mutane ke ƙoƙarin ƙare katunansu kafin sauran ƴan wasa, wasu na ce mata wasan karta wasu caca suke kiranta dashi a turance kuma ana kiranta da WHOT. Wasu na yi domin nishaɗi wasu kuma suna saka kadararsu na abin da suka mallaka a ciki. Idan ka yi nasara ka ciyo abin da ba ka yi tunani ba, idan ka yi rashin sa'a za'a cinye abin da ka saka. Kamar yadda Daada ya saka ɗiyar cikinsa a cacar kuma aka yi nasarar cinta. Hukuncinta a shari'a ya bambanta, Idan ana yin Whot da kuɗi (caca)Wannan yana shiga cikin abin da ake kira Maysir. A Musulunci, an haramta caca a fili haramun ce ta kowacce siga kamar yadda dalilai suka zo a cikin Alkur'ani mai girma, caca tana haddasa rikici da rigimar da zata iya yin wa'adin ran wani, tana hana ibada akan lokaci wasu basa yi, tana cin dukiyar mutane ba bisa ƙa'ida ba. Duk kuɗin da mutum ya samu a Whot ko ya mallaki wani abu, ba zai taɓa zama halak ba, waɗannan abubuwan sun zama haram a gare shi. Wasu kuma Malaman suka ce, Whot idan ana yi da sigar nishaɗi suka ce babu haramcin muddin bata hana mutum ibada ba, wasu kuma suka ce makruh ne (ba a so), saboda tana iya kai wa ga yin cacar yana iya ɓata lokaci.

Kamar zai tashi sama haka Daada ya nufi hanyar gidansa sai surfa bala'i yake kamar zai ciro bakinsa ya ajjiye a ƙasa. Bugo ƙofar da ya yi ya saka zuciyar Innti bugawa da ƙarfi, salati ta saki saboda tsabar yadda take tsoron ganinsa ko shigowarsa cikin gidan. Yana shigowa Iftihal na fitowa daga cikin ɗaki sanye da uniform zata tafi makaranta. Jikinta na rawa ta durƙusa ta ce "Ina...,"

Bata ƙarasa ba ya sakar mata wata uwar tsawa da faɗin "Gidan ubawa za ki da safiyar nan?" Kanta a ƙasa dukkan jikinta rawa da ɓari yake yi saboda tsananin tsoron daya gama ratsa mata zuciya bata taɓa jin tsoron wata halitta a duniya sama da halittar dake tsaye a gabanta ba, bata taɓa jin tsoron wani ba kamar yadda take tsoron mahaifinta Daada. Maganarsa faɗuwar gaba take haddasa mata, ko tari ya yi sai ta saka hannu ta dafe ƙirjinta domin ji take kamar zuciyarta ce zata faɗo ƙasa ta cikin ƙirjinta ba tare data shirya hakan ba.

"Ke don ƙaniyyarki munafurci kika koya irin na uwarki? Mugun abu take koya muku ashe?"

Ta girgiza kai a hankali ta ce

"A'a Daada...

"Makaranta zani muna exam ne" A hargitse ya ce "Dake da makarantar da uniform ɗin makarantar, da Malaman, da wacce ta saka ki makarantar Allah ya yi wadaranku tsinannu marasa amfani a duniya har ma da lahira, duk wani mugun abu kuma gama lashe shi a nonon uwarku"

Wani irin runtse idanu Innti ta yi idanunta sun yi jajur ta kasa motsi, idan cin mutuncin Daada ne ta saba amsar shi a koyaushe a gaban yaran nata. Babu ranar banza ita ta rasa yadda wannan ƙiyayyar ta samo asali da tushe. Kamar ba haka yake ba, kamar kuma haka ɗin yake tun fil'azal. Ta fuski numfashi da ƙyar ta tuna kamar ta tuna. Zata iya tuna dalilin faruwar komai.

"Bana son haihuwa Innti, bana son zuri'a Innti ban shirya mata ba, yara basa ɗaya daga cikin abin da yake birge duniyar Daada. Daga wannan cikin kar ki ƙara sakin jiki wajan ware ƙafa ki ɗauki ciki, shima wannan ɗin bana murna dashi, kuma ba zan ɗauki alhakin kulawa dashi ba na faɗa miki"

Wannan sune kalaman shi na farko, lokacin data samu cikin Babban yaya ne, tun bata san me zata haifa ba a lokacin cikin yana watanni bakwai ne dab da zuwa duniya yaso zubar dashi ma, haƙarsa bata cimma ruwa ba. Tunda aka wayi gari da labarin cikin komai ya sauya komai ya zama labari.

Zata iya tuna raddin data yi masa ma a lokacin. Kamar cewa ta yi "Daada ƴaƴa ai Rahma ne baka san me jin ƙan ka ba"

"Assalamu Alaikum"

Sallamar da aka yi ya katse ta daga tunanin abubuwan da suka shige, wata sabuwar faɗuwar gaban ce ta sake ruskarta. Uwar mijinta ce da kuma yayar mijin da ƙanwarsa.

"Ina yini Emama?"

Wani irin gatsine wacce aka kira da Emama ta yi ta dubi tukunyar da Innti ta dafa taliya ƴar murji jallof wacce ta ji ganyen albasa sai ta riƙe baki ta ce "Babu shakka ashe abin da nake ji na cewa kin shanye Daada gaskiya ne, ya tare a gindinki ke da yaranki har taliya kuke dafawa da wannan sanyin hantsin?" Innti ta kalli tukunyar tana mamakin shi Daada ne ya ce shi ya yi cefanen ko me? Sama da shekaru rabon da taga sisin kwabo nashi? Duk abin da yake dashi ko ya mallaka ya tafi a caca. Taliyar fa Haysaam ne ya kawo da saffafe ya ce su dafa a kai wa Shalale asibiti daga baya ma ya kira ya ce ya siya mata Rufaida da Shawarma. Shine za su azabtar da zuciyarta da wani baƙin cikin na dangin miji? Ita kam tana tunanin da ƙyar idan takaici da baƙin cikin namiji bai yi ajalinta ba.

Ƙoƙarin magana take yi Baba ta kalli babbar ƴarta me suna Hanna ta ce "ke jeki juyo mini taliyar nan a faranti gabaɗayanta kin ji"

"To Emama" Hanna ta faɗa cikin sauri.

"Wallahi Emama Daada ya zama mijin tace a gidansa, komai ya samu yana gidan wannan matar data zame mana bala'i. Haka jiya dana biya ta wajan abincin Bala yake bani labarin cin mutuncin da wannan me suffar Aljanu ta yi masa, Ana" Emama ta riƙe haɓa ta ce "Ba shakka iskancin yarinyar nan da rashin kunyarta haka ya bunƙasa?"

Daada dai ya yi shiru yaƙi cewa komai.

"Liya ki daina suffanta ƴata da Aljanu"

Kau! Daada ya ɗauke Innti da wani irin mari yana nuna ta da manuniyya ya ce "Ahir ɗinki. Ke kuma......" Ya juya kan Iftihal da take ta rusar kuka ya ce "Daga yau na haramta miki zuwa makaranta, kuma zuwa dare ki shirya akwai inda zamu dani dake"

"Ba mu yi haka dakai ba, duk abin da za ka yi don Allah na roƙe ka sbd Allah ka tsaya iya kaina. Kar ka rusa goben yarana na sadaukar da komai saboda su yi karatu"

"Wacce gobe? Har wata gobe suke dashi a nan? Ai indai cigaba ne a rayuwa sai dai su yi na me haƙar rijiya. Har abada yaranki ba za su taɓa zama wasu ba a rayuwa tunda suka fito daga cikinki"

Kuka Innti ta fashe dashi tana wani irin fidda numfashi da kiran sunan Allah, yadda take kuka haka ma Iftihal ke kuka ta rarrafa wajan Daada ta riƙe ƙafafuwansa ta ce "Muna da buruka a karatunmu Daada za ka ji daɗi ta dalilinmu, kar ka bari mafarkina na zama ƴar jarida ya rushe, kar ka bari mafarkin Ana na zama marubuciya ya zama tarihi mun rayu akan mafarkanmu da burinmu don Allah kar ka tarwatsa mana su" ƙafa ya saka ya shure ta ya nunata da yatsa ya ce. "Har wani mafakar kike dashi?"

Ya yi ƙwafa "Ni na riga na saka ki a caca kuma rashin sa'ar uwarki ta shafe ki wacce taja mini asara babu kuɗin kuma aka ciki"

Cak! Numfashin Iftifal ya tsaya a ƙirjinta dumm haka ta ji wani abu yana mata amo a kunne kallon Daada kawai take yi da kallo na rashin fahimta. "Ka.. saka..ni a caca Daada?" Ta yi maganar a rarrabe tana dafe ƙirjinta.

"La shakka kuma an ciki zuwa dare zan kai ki gidan Alhaji Baita, ban sani ba ko auranki zai yi ko kuma dai ajjiye ki zai yi kawai a gidan"

'Alhaji Baita?' ta maimaita sunan ba wannan tsohon bane me baki duk dauɗa wanda goro ya gama cinye masa haƙori har wata tsotsa ce take gani a bakin wannan Alhaji Baitan mai ciki kamar name shirin haihuwa shi ne za'a kaita gidansa a matsayin me?

"Na shiga uku Daada ka yi mini rai"

Ta fasa wani gigitaccen ihun daya saka Jadid dake kwance tun ɗazo saurin runtse idanunsa ya saka hannu ya dafe kai, fitowa yake son yi daga ɗaki abu ya ci tura saboda nauyin da jikinsa ya yi masa ga tashin zuciya da hakki da ƙyar yake iya buɗe idanunsa. A hankali hawayen da suka cika masa idanu suka silalo ta gefen idanunsa. "Allah ka ɗauki raina ko zan huta da ganin kuncin dake zuciyar Innti da ƴar'uwana"

"Ka aurar dani idan kana buƙatar hakan amma Daada don Allah kar ka kai ni gidan mutum nan mutuwa zan yi, kar ka saka ni a caca. Ka duban girman Allah ka tuna mu jininka ne, ƴaƴanka ne ka tuna mu amana ne a gare ka watarana Ubangiji zai tambaye ka. Ka ji tsoron haɗuwa da Ubangiji Daada wallahi muna son ka muna ƙaunarka kai mahafinmu koyaushe muna jiran sanda zaka dawo mana da soyayyar da muke maka" ya ɗauke kai zuwa gefe bai ce komai ba. Emama ce ta kalle shi bayan ta tattara wasu kayan miya data gani a wajan ta ce

"Zuwa na yi a siyar da rabin gidan nan a bawa Liya kuɗin zata tafi Saudia aikatau"

"Wanne gidan?"

Innti ta faɗa tana buɗe jajayen idanunta da ƙyar saboda faɗuwar gaba. Ta ɗora da faɗin

"Kar ku siyar da gidan nan don Allah, idan Babban yaya ya tashi aure a nan zai zauna bamu da komai ku tausaya mana don Allah"

Emama ta ce "Gidana ne sai an siyar shi Muradun ɗin aure aka ce za'a bashi? Wani ɗan iskan uba ne zai bawa wannan mara lakar ɗiyarsa? Da wacce sana'ar zai yi auren?"

"Emama, wannan gidan gidana ne bawai na Daada ba, ki tambayi Daada ki ji" tana faɗin hakan ta shiga ɗaki tana dafe saitin zuciyarta dake mata ciwo da raɗaɗi.

"Ohho dai. Ke kuma tashi aikatau na samo miki a wani gida, ko na kwana biyu ne ki yi kafin akai ki can gidan Baita ɗin, ba zan ɗauki wannan fitsarariyyar da zata iya ja mana bala'i a gidan jama'a ba" ta saka hannu ta fusgi Iftihal za su yi waje Daada ya ce

"Kin san Baita bashi da mutunci fa?"

"Ka bashi uzurin shirya yarinyar ake yi" Tana faɗin hakan ta fice daga gidan suka nufi titi napep ta shiga ta ce masa Maitaima Sule Baffas Estate kai tsaye.

Bayan fitar su zama Innti ta yi ta dinga kuka har sai da ta yi me isar ta tana kukan tana cewa. “Rabbanaa hab lanaa min azwaajinaa wa dhurriyyaatinaa qurrata a’yunin waj‘alnaa lilmuttaqeena imaamaa” (Surah Furqan: 74). Ta ɗora da faɗin.

“Allahumma ihdihi wa-shrah ṣadrahu lil-ḥaqqi, Allahumma habbib ilayhi al-īmāna wa zayyinhu fī qalbihi, wa karrih ilayhi al-kufra wal-fusūqa wal-‘iṣyāna, waj‘alhu minar-rāshidīn.” Ma’ana: “Ya Allah, Ka shiryar da shi, Ka buɗe ƙirjinsa ga gaskiya, Ka sanya ya so imani Ka yi masa kwalliya da shi a zuciyarsa, Ka tsanar da shi da kafirci, da fisqanci, da saba wa Allah. Ka sanya shi daga cikin masu samun shiriya.”

Wani irin numfashi take fitarwa me ɗauke da ciwo tattare da damuwar da ta yi shekaru a cikinta ba tare data buɗewa kowa cikinta ba. Idanunta na buɗewa da lumshe ta ce “Allahumma aslih lī zawjī, wa aslih līhi, waj‘alhu qurrata ‘ayni, waj‘alnī qurrata ‘aynih.” ta ɗan ja idanunta ta lumshe su.

Sama-sama ta ji kakarin amai tana fitowa taka Jadid ne ke kwara amai gabanta kuma ya faɗi ganin yadda fuskarsa ta kumbura sosai da ƙafafuwansa da hannayensa. Bayan ta wanke masa baki da fuska ta ce

"Ina maganinka?"

"Ya ƙare" ya ce da ƙyar.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"

Shimfiɗa ta yi masa ya kwanta ta dinga kallon shi tasan da ƙyar idan ba dialysis za'ayi wa Yaa Jadid ɗin ba.

"Babu komai, Allah duk abin da ka yi daidai kuma na amsa. Bari na ɗakko kuɗin adashin nan na jama'a siya maka magani kafin aje asibiti idan Allah ya hore mana" ko data miƙe ta nufi ɗaki tana zuwa inda take adana kuɗin jama'a na adashi taga babu komai kusan dubu ɗari biyu da hamsin an kwashe

*** BIYA.

Batty na rakuɓe a cikin bukkarta ta yi shiru tana kallon saman rufin wajan idanunta ya yi jajur saboda tsananin azabar da take jin tana yunƙuro mata, bata taɓa jin kanƙarar maita na mata yawo a ciki irin yau ɗin ba. A hankali ta juya ta kalli inda ta ajjiye kurwar Mado data kamo a jiya data fita maitar dare. Miƙewa ta yi a hankali ta isa wajan randar ruwan dake ɗakin, randar ta yi sanyi sosai ta miƙa hannu zuwa ƙasan randar ta buɗe wani ɗan ƙyalle idanunta ya sauka akan ƴar tsokar kurwar data kamo ta zubawa kurwar idanu tana jin kamar ta ci kamar kuma hakan ba dai-dai bane ba. Wasu hawaye ne suka shiga sakkowa daga cikin idanunta ta mayar da kurwar ta ajjiye. Wata baƙar leda ta ɗakko barkono ne ɗanye shar a ciki haka ta dinga damƙa tana kaiwa baki tana ci ga hawayen a zama na cika idanunta bayan ta gama ci abin da take ji ya ɗan lafa mata sai ya miƙe ta fito zuwa tsakar gidan turus ta yi ganin jama'a fal ta manta yaron Kulu ya rasu. Sadiatu ta ce "Batty kin fito ne?"

Ta jinjina kai alamar

"Eh"

"To jeki waje wajan yara muna amsar gaisuwa ne" nan ma ba ta yi magana ba kanta a ƙasa cike da nutsuwa ta fito sumar kan sai ɗaukan ƙyalli na dauɗa take yi a haka ta nufi waje cikin sa'a ta samu yara sa'aninta suna ta wasa tana zuwa ta shiga tsakiya aka fara wasa da ita. Kamar an ce ta ɗaga kai ta hango cikin Shatu fal wainar gero har da albasa bata gama narkewa ba.Caraf ta ce

"Sammin wainar geron kin ji"

Shatu ta fiddo ido ta ce

"Wa ɗin?"

"Ke, gashi nan kin ci wainar gero"

"Laaa ha'ilallah wallahi kin cinka waina na ci"

Gabaɗaya yaran suka zagaye Batty. "Ni me ma ce?"

"Rogo da gyaɗa" ta bawa Hawwa amsa.

Wani irin daɗi da murna ya kama yaran su basu taɓa sanin ana sanin me mutum ya ci ba sai yau. "Ni ki faɗa mini me na ce to"

Ramu ta yi tambayar a hankali tana kallon Batty cike da tsoro. Batty ta zubawa cikin Ramu idanu komai da komai dake cikin Ramu na kayan ciki tana gani, daman duk wani maye da kallo ɗaya yake kallon ka tsirara musamman idan babu dafa'i a jikinka. Madadin Batty taga abin da Ramu ta ci sai taga hanjin cikinta ya motse kuma ya yi kore. Ɗauke kai ta yi zuwa gefe guda ta ce

"Ai ba ki da lafiya, ga hanjinki nan ya ta mushe ya yi kore ki nemi magani idan ba haka ba za ki mutu wallahi ina faɗa miki"

Fashewa da kuka Ramu ta yi tana riƙe cikinta. "Na shi gangaɗi" ta faɗa gigice.

Su Shatu ne suka dinga bata haƙuri har ta yi shiru juyi kaɗan tana dafe da cikinta tana jin kamar hanjin nata ne zai fito ta cikinta.

Shatu ta ce "Kin zama ƙawarmu daga yau za ki dinga faɗa mana me muka ji kin ji ko?"

"To za ku dinga sam mini?"

"E, sosai ma. Ya sunanki?"

"Batty me gani har hanji"

Hawwa ta dafe ƙirjinta ta ce "Laa wallahi haka ne gashi nan ta hango hanjin Ramu"

Hira suka fara yi Batty ta shiga cewa "Ita fa ta kusa fara cin mutane tana shan wahala, ta taɓa shan man wani da babarta ta zuba mata man a cikin abinci akwai daɗi sosai. Kuma tana ganin jinin mutum da kayan cikinsa ita fa har mage tana iya zama" suka fashe da dariya suna jin abin kamar alamar.

Bayan sun gama hirar la'asar sakaliya ta koma gida tana ta zuba idanun a bata abinci amma shiru. Sai ma hira suke yi "Ai Kulu haƙuri ya zama dole, kinga samu kinga rashi amma hakan yin Allah ne. Yanzu fa mutuwar fuju'a ake yi babu ji babu gani ana ta zuba"

Lami dake ta wanki ta ce "Wallahi Sadiatu al'amarin har tsoro ya bani sosai"

Ita dai Batty jinsu kawai take ta san wannan mutuwar da ake yi rabinta mayu ne sanadi. Mutane za su ga ana ta rasuwa irin mutuwar abin mamaki nan, daga ciwon kai sai ace wane babu ko ciwon ciki, ko kuma mutum da lafiyarsa da komai sai aji ya yanke jiki ya faɗi shikenan sai tashin lahira. A cikin wannan watan ne na dab da babbar sallah Mayu suke sharafi a cikin watan ne suke yanka duk wanda suka ɗaure kurwarsa da niyyar shagalin babbar sallah. Don haka duk wanda yake fama da jinya ta Mayu a irin wannan watan Allah ne kaɗai me tsallakar dashi sai idan ya dage da addu'a da neman tsari da taimako.

Miƙewa ta yi ta sake shiga bukkarta, kurwar Mado ta ɗakko ta riƙe a hannunta sosai ta nufi hanyar rafi tana addu'ar Allah ya sa yau ma taga kyakkywan Kaɗo har mafarkinsa ta dinga yi tana isa ta haƙa rami a gefen rafin ta adana kurwar a ciki ta shiga wasa da ruwa can kuma ta fashe da kuka lokacin data tuna kisan gillar da akai wa Innarta

A can gidan Moddibo suna zaune a tsakar gida, suna ta amsar baƙin da suke zuwa duba Mado. Wani ihu suka ji Mado ya kwarara yana faɗin "Wayyo ga ruwana zai cinye ni ga kifi nan, ruwa ne zai tafi dani"

A razane suka shiga ɗakin suna masa sannu. Hanne ta ce "Moddibo anya ba iska bace ta kama Mado? Wanne irin ruwa zai tafi dashi ana zaune ƙalau Moddibo?"

Moddibo ya ɗan taɓa jikin Mado ya ce "Kuma jikin sanyi ƙalau. Bari zan kira me ruƙiyya in sha Allah sai a yi masa a gani"

"To da dai yafi" Hanne ta ce tana yin takumi.

***

Aikin yamma ne da ita yau bayan ta kammala shiryawa ta fito hannunta riƙe da jaka da damuwa ta bayyana sosai a tattare da ita. Engineer na zaune a parlour shi da matarsa Jiddah ta ɗan durƙusa ta ce "Barka da yammaci Abba" saboda da yawan lokaci tana bin bakinsu Mufeed wajan kiran Engineer da Abba. Itama ta yi imani da Allah bata da wani uba bayan Engineer ɗin nata.

"Baby an fito kenan?"

"E, Abba. Anty Jiddah sannu da aiki"

Jidda ta murmusa ta ce "Yawwa babyn mijina" murmushi kawai Ahlam ta yi.

Ya ɗan kalle ta sai kuma ya ce "Wannan baby hijab ɗin baya miki kaɗan ne a jiki Ahlam?" Ta dubi Hijab ɗin, abaya ce a jikinta me ɗan faɗi ruwan ƙasa sai ta ɗauki hijab ta saka madadin mayafin abayar. "Idan akwai kuskure a shigar zan je na sauya Abba"

"Matsayin naki ne ya sauya daga yadda kika sani. Ahlam na taɓa miki maganar fitar da mijin aure har na yi tunanin wannan yaron na wajan aikin ku ko son ki yake yi. Yama sunan nasa?" Kanta a ƙasa ta ce "Anees ne"

"Good, Anees"

Ya ɗan ɗaga filon kujera ya ciro kuɗi bandir bandir ya damƙa mata ɗaya ya ce "Wannan kuɗin na gani ina so ne naki dana amsa da safe. Ke da kan ki kika bani damar zaɓar miki mijin da nake ganin zai iya kulawa da nake. Nasan komai na zartar a rayuwarki ba za ki yi mini musu ba, ba za ki ce a'a ba. Daga ni har ke marayu ne, amma ke ba za'a taɓa miki kallon maraici ba, dukkan abin da zai zo ya tuna miki ke marainiyya ce bana son shi Ahlam ɗina. Na bada ke, na bada aurenki ga mijin daya kwanta mini kuma ina da yaƙinin ba zai cutar dake ba baby"

Sak Ahlam ta yi tana juya kuɗin a hannunta jikinta ya yi sanyi ba damuwarta waye mijin ba, saboda ba soyayya ce a ranta ba, cikar burinta shi ne gaba da komai a rayuwarta. Tambayoyin zuriyarta bai shige zai barta aiki ba? Ba zai tauye mata rayuwa wajan hanata zuwa aiki ba? Ya san cewa ita nakasasshiya ce? Waɗannan tambayoyin sune suke damunta a yanzu. "Baby " da ƙyar ta ce

"Abba ba zan tambaye ka waye ba, ba kuma zan bijire maka ba, na amshi abin da ka zaɓa mini na san ba zai taɓa cutar dani ba"

Sai ta ɗan yi shiru tana mai da murmushi.

"Ya san ina da nakasa Abba?"

"Ya san abin da ba ki sani ba don gane da rayuwarki ma Ahlam. Matsalolin suna bibiyarki wanda ni ban san su ba, ya ɗauki ɗamarar yaƙi da wannan matsalolin ne"

"Amshi nan....

Ya sake damƙa mata wasu kuɗin ya ce "Sadakinki an ɗaura aurenki a sanda suka kawo kuɗin baiko, ni ba zan iya wannan ba tsarina daban shi ya sa na buƙaci ɗauren auren daga baya a yi maganar tafiyarki"

Ji ta yi kamar Engineer ya saka igiyoyi ya sarƙafe rayuwarta da ita ne, komai ya tsaya mata. Yana nufin yanzu ita matar aure ce? Yana nufin igiya uku ke ɗaure da rayuwarta. An yi mata ɗaurin da sai hanata sakewa da zai kawo mata matsala a cikin burinta? Ta rufe ido ta buɗe yafi sau shurin masaƙi wajan tabbatar da abin mafarki ne amma da alama gaske ne. Wata faɗuwar gaba ta ruske ta, aikinta shine gaba da komai, ɗaukarta shine burinta. Ta yi aure bata cimma komai na rayuwa ba, Yussy ta samu sararin yi wa ƙaddararta dariya? Girgiza kai ta shiga yi wajan faɗin "Impossible....

"... menene impossible ɗin? Auren ko kuma mijin Ahlam Abdallah Kurmi?"

Sai ta ƙirƙiri murmushin ta ce "A'a Abba"

"Kina farinciki?"

"Sosai. Na gode sosai my 001 madakina"

"Nima na gode ƙwarai my happiness"

Wani abu ya caki zuciyar Jiddah ta yi saurin shaƙar iska ta fesar tana jifan Ahlam da wani irin kallo. Kishin yarinyar kamar ya kashe ta dannewa kawai take yi for more than a years yanzu ya fara cin ƙarfinta sosai.

"Tashi ki je a kiyaye kula wasu samarin tunda dai kina da naki zaɓin Baby Ubangiji ya yi miki albarka ya sa tafiyarmu ta yi nisa"

"Amin na tafi"

"Allah ya tsare Kakata" inji Jiddah.

Fita ta yi ɗauke da addu'ar fita daga gida a bakinta tana buɗe gate ɗin gidan ta fice sai taga mota daga can nesa kai tsaye ta yi gaba bata tsaya ba. Me motar ya sake kunnawa ya yi horn yasha gabanta, tsayawa ta yi tana ƙoƙarin yin masifa wanda ya buɗe motar ya saka gabanta faɗuwa ta yi saurin yin ƙasa da kanta jikinta duka ɓari yake yi. Ta cikin glasses ɗin idanunsa ya zuba mata ido yana daga kishingiɗen da yake a kujerar motar tasa....

Akwai chapters 9,10,11,12,13 duk a Arewapen. Ku shiga play store ko app store ko website ku yi searching ArewaPen ku yi register sai ku yi searching sunan Littafin HIYAAM.

Masu buƙata WhatsApp su yi magana ta WhatsApp.

08082101373 08164069385