Kenza eBookz
Cover art for HIYAAM  HAUSA NOVEL PAGE 5

Post

HIYAAM HAUSA NOVEL PAGE 5

.....in her hijab saying "She will run" The Elder was watching her do it, she slowly looked at the side of her hijab where he was holding her. She lowered her eyes, her chest felt heavy as if a stone had been placed on her chest, she felt a burning sensation mixed with spicy. She opened her mouth with difficulty and said "I think the value of gray hair is not my father's, take your hands off my body, Father" The elder said, "Will you deny me shame?" He said, "Are you a human being? I have never seen you in this neighborhood. Are these children the kind of brats who leave their parents' presence and follow a young man to their neighborhood?" The frustration that was too much in her heart felt as if she shot a gun because she felt a fire burning in her heart and she opened her mouth and said "Yes, it is her. Let me go" "Who is your father in this neighborhood?" She said "DAADA" The name came out in her secret voice that did not want to make noise and shout at all. "Father! This old man is your father? What do you mean by gambling?" Said a young man, when he spoke he was holding his head because of the great surprise of the other. This time, Ana cast her terrified eyes on the young ma

Standalone post6,551 words

*H I Y A A M*

Page 5: Six Worlds Around Me

Bright pens Yota/001

“I pray that Allah grants you Jannah together with your parents.” Nazeefah Sabo Nashe.

Page ɗin yau naku ne, Rabi'ahtu Achadu Fulani gal tare da Hiyaam book channel Allah Ya saka muku da alheri ya biya ku da Aljanna.

"Ko duka garin nan gatanki ne, wallahi sai kin zo kin tsallaka yaron nan ya tashi, mayyar banza mayyar wofi masu cinye kurwar mutane a duhu" wani irin kallon gefen hagu ta yi wa yayan yaron ta ce "Bani da gatan daya shige na Allah da kuma mutanen shidan da suke tare dani, maita kuma kai ne mayen bani ƴar gidan Innti ba"

Yadda take furucin a hankali ɗaya bayan ɗaya, da yadda idanunta sukai jajur wajan sauya launi amma taurin zuciya ya hanata zubar da hawaye zai tabbatar wa duk wanda yake wajan ranta ya kai maƙura wajan ɓaci. A nutse ta sake juya idanunta akan Yaa Sam, kafin ta mayar da ganinta kan yaron dake kwance har yanzu, sai ta yi baya kaɗan tana ƙoƙarin juyawa ta bar wajan. Caraf wani dattijo ya riƙe gefen hijabinta yana faɗin "Guduwa za ta yi"

Ana kallon Dattijon ta yi, sannu a hankali ta kalli gefen hijabin nata inda ya riƙe mata. Runtse idanunta ta yi, ƙirjinta yana yi mata wani irin nauyi kamar an saka mata dutse a ƙirjin, wani zafi-zafi take ji haɗe da yaji-yaji.

Ta buɗe baki da ƙyar ta ce

"Ina ganin darajar furfura ko bata mahaifina bace, ka cire hannunka a jikina Baba"

Dattijon ya ce "Rashin kunya za ki mini?" Ya ɗora da "Ke anya ke kuwa mutum ce? Ban taɓa ganinki a wannan unguwar ba, ko irin ƴan iskan yaran nan ne masu barin gaban iyaye zance su biyo saurayi har unguwarsu?"

Takaicin da ya yi mata yawa a zuciya tana jin kamar ta yi bindiga saboda yadda take jin wata wuta na rura kanta a cikin zuciyarta sai ta ka da bakinta ta ce "E, ita ce. Ka sake ni"

"Waye ubanki a unguwar nan?" Ta ce "DAADA"

Sunan ya fita ta cikin sirriyar muryarta mara son hayaniya da ihu ko kaɗan bata so.

"Kan uba! Wannan tantirin tsohon shine uban naki? Me caca da garta kike nufi?"

Cewar wani matashi, da ya yi maganar yana riƙe haɓa saboda tsananin mamakin daya cisa. A wannan karon Ana watsa firgitattun idanunta ta yi akan matashin, idanun da tunda take bai taɓa fita daga hayyacinsa irin yau ba, kanta wani irin ciwo yake mata yana juyawa tana jin kamar zai rabe mata biyu.

A tausashe ta ce "E, shine ubana"

"Babangida wai Daada me shan barasa yana yawo tsirara a kwararo idan dare da ya yi kake nufi? Me bin matan banza yana aikata aikin banza dasu, kamar yadda ya kasance ɗan banza? Wannan shine uban yarinyar nan?" Kai tsaye Babangida ya bashi amsa da

"Wallahi shine, ai Daada ɗaya ne unguwar nan" ya tuntsire da dariya ta mugunta.

Kallon tsana Dattijon yake bin Ana dashi kafin ya sake ta yana ɓata fuska kamar yaga kashi ya ce "Sannu ƴar nan, na tayaki baƙinciki da kuma takaicin samun mahaifi irin wannan, ashe yana da yarinya data girma har haka yake aikin banza da wofi a gari babu kunya babu tsoran Allah? Ashe yana da zuri'a mace yake bin manta banza? Yarinya kin yi kyawun ɗan maciji, kyawun da kike dashi ya tashi a banza ya kuma tafi a banza, babu uban arziƙi da zai yadda ɗansa ya aure ki domin baki kasance tsatson arziƙi ba" Babangida ne ya ce "Gaskiya kam baba"

"Abin ya muku yawa wai shege da hauka, ke maita, Ubanki Dattijon banza, ƙanin ubanki wanda Allah Ya tsinewa me shigar mata"

Sai a lokacin ne wasu azababbun hawaye masu masifar zafi da raɗaɗi suka kwace mata tare da bin kyakkyawar fuskarta suna sauka da gudu saman kumatunta, cikin sauri ta saka bayan hannunta ta goge su.

Ba'a taɓa bin Ana bashin magana. Saboda haka ta kalli Dattijon ta ce

"Na gode Allah da baka da gidan wuta balle na Aljanna, Ubangiji shike fitar da iri daga matacciyyar shuka, kuma shike raya wannan irin har ya zama ganye kore shar wanda kowa yake birge shi, na yarda ubana yana shan giya, yana caca, amma ƙazafin bin mata da kukai masa Allah shine zai mana sakayya daku, ban taɓa jin tsanar shi ba, soyayyar da nake masa ce ta saka kai tsaye nace muku shine ubana, babu wanda ya isa ya saka na sauya sunana daga nasa"

Za su yi magana Jaheed daya rufe shagon ya ƙarasu wajan, idanunsa zube akan shalelen Innti ya dube ta tsaf kafin ya ce

"Meya fito dake?"

"Au ɓoye ta kuke yi saboda mugun iri ce ko?" Jaheed ya kalli Babangida ya ce

"Sai dai ban fahimce ka ba"

Babangida ya ce "Borin kunya daman da hauka ake naɗe shi, yaron mutane ta kama"

"Kar ka sake ce mata Mayya!"

Furucin Yaa Sam ya fito a nutse a tausashe yana bubbuɗe grey eyes ɗinsa zuwa waje.

"Na faɗa a saka kaina gabas a yanka, wallahi ni dai kurwata kur nafi ƙarfinta"

Cikin zafin rai da raɗaɗin kalaman Babangida da yake jifan Ana dasu wanda kai tsaye suke sauka a zuciyarsa suna kartar naman dake sarrafata ya nuna shi yana tattare hannun rigarsa ya ce "Ka yi kuskuren jifanta da wannan kalmar wallahi sai na maka illa mutumin banza da wofi, yunwa duk ta cinye muku yara babu mamaki ma olser gare shi, shine za ku zo kuna ihun banza bara a kufai" ganin da gaske Yaa Sam naushin Babangida yake shirin yi ya saka Jaheed saurin matsawa gabansa yana faɗin

"Ka yi haƙuri ka rabu dashi Yaa Sam. Ana dai ba mayya bace kuma banda Innti ta hana mu faɗa da mutane wallahi yau da ya ɗauki kashinsa a hannu babu wanda ba ɗan iskan kan shi bane, da ita mayya ce da mune farkon waɗanda zata fara cinyewa I'm telling you this"

"Kuma da mayyar ce me zan yi da naman mummunan mutum irinsa jiki duk basir da sanyi ya yi masa illa" Jaheed ya ce

"Gaya masa dai tawan"

Yaa Sam ya juya ya kalli Jaheed sai ya mayar da idanunsa akan Babangida ya ce "kuma wannan maganar shari'a ce zata rabani da kai, tunda ko mugun abu kukai iya da tsinanne sa ido wa jama'ar unguwa"

Cikin shakku dattijon ya dubi Yaa Sam yana nuna shi da yatsa ya ce "Wannan ba ɗan gidan Malam Usmanu bane? Shi Usmanun ya barka kaka mu'amala da zuri'ar Daada?"

Ko inda dattijon yake Yaa Sam bai kalla ba. Jaheed da ya shiga mamaki da takaicin fitowar Ana ya dube ta a hankali ya ce

"Me ya fito da Shalelen Innti?"

Ta ji shi sarai amma ko motsi ta kasa yi balle ya yi tunanin zata ɗago ta kalle shi har ta bashi amsar da kunnuwansa suka mace wajan jiran jin abin da yake faruwa, shi dai a tunaninsa da iya lissafin ƙwaƙwalwarsa a shekarun nan ɗaiɗai har shekaru goma sha Bakwai, tun daga haihuwar tawayen Innti, Iftifal da Ana, tun daga rainonsu zuwa girma idan kaga Ana ta fito waje a cikin biyu ko uku akwai ɗaya, babban dalili zuwa makaranta, boko, Islamiyya sai ta dare, dalilin dake bayan neman ilimin shine kiran Yaa Sam idan ya dawo gari. Wannan sune.

Ƙawaye bata dasu, sau tari ta kan ce;

"Duniyoyi shida ne ke zagaye da rayuwata, ina jin sanyi daga kowacce kusurwa Innti"

Zata ja numfashi a hankali ta sauke manyan idanunta na sauyawa zuwa yanayi na ruwa, ruwan dake ƙara musu nagarta da kuma sahihin kyau, wanda yake sake fitar da kalarsu na “sexcy eyes” bata fiye kallon mutane da wannan suffar idanun ba.

Babban mutum kawai take iya kalla dasu kai tsaye ta ji ta yi na'am da kallon har ranta.

Da wannan nauyin zuciyar take riƙe hannun Innti da Iftihal musamman a ƙasan bishiyar dake ƙara musu ƙaunar juna saboda sanyinta. "Innti ni kaɗai nake jin idan na rasa ku kamar Ana ba zata iya rayuwa ba? Ina jin kamar nima wa'adina zai zo ɗaya da naku ne, zan jure komai, zan haƙura da komai, zan fahimce komai, zan yarda da komai, a cikin komai ɗin nan banda ku...,"

Ta lumshe idanunta ta ɗora da,

"A cikin komai ɗin nan ban da rashinku a duniyata, kune ƙawayena, aminaina na cikin zuciyata, farinciki da walwalar Ana"

A irin wannan lokacin Iftihal ke damƙe hannun Ana ƙam hawaye na sauka a saman fuskarta ta ce "Ita kanta mutuwa na san za ta yi mana halarci mahaɗita, zata ɗauke mu ne tare, dani dake da Inntinmu, yadda muka zo duniya a rana ɗaya, a kusan daƙiƙa ɗaya, a mahaifa ɗaya, daga cikin nagartacciyar uwa ɗaya, ina roƙan Allah ya amshi rayukanmu su yi wa'adi ɗaya tare da uwar data kawo mu duniya" Ita kanta Innti wannnan ranar ta rabuwa kashe ta take yi tun kafin mutuwarta, tana rayuwa da mutuwa da tunanin rabuwa dasu watarana dole. Idan ta tuna su yarana sai ta ji ta mutu, idan ta tuna su mata ne sai ta sake yin wata mutuwar, idan ta tuna dangin mahafinsu sake macewa take yi, babban dalilin dake sawa ta ji ta zama matacciyya shine; halin mahafinsu Daada.

Bayan macewar tana farfaɗo wa da ƙarfin zuciya da shauƙin tuna cewa akwai, wani jigo a rayuwarsu bayan ita. Akwai garkuwarsu. Suna da Babban yaya a tare dasu tabbas..... Ta yi nisa cikin tunaninta

Jaheed ya sake maimaita mata tambayar

"Mene ya fito dake Ana?"

Bata iya bashi amsa ba, saboda yadda ƙirjinta ke ɗagawa tana jin wani zafi da raɗaɗi kiranta da mayya, kalmar da bata san ma'anarta ba, bata kuma san me take nufi ba. Tambayar duniya Jaheed ya yi mata ganin kamar zata haɗiye zuciya ya saka Yaa Sam ya yi gyaran murya ya ce

"Ka barta"

"Shikenan, amma....,"

Bai ƙarasa faɗa ba, su kaga yaron ya miƙe a guje yana ihu ya yi lungun gidansu yana faɗin

"Cikina, yunwa....yunwa zata kai ni lahira"

Babangida ya yi saurin ɗauke kai jiki a sanyaye, haka dattijon ma ya bar wajan.

Jaheed ya ce "Bari na koma shago Yaa Sam"

Yaa Sam ya jinjina kai. A hankali ya juya tare da bin bayan Ana ganin ta yi gaba ya ce "Madam, takalmin fa?" Sak ta yi sai kuma ta juyo a nutse bata yarda ta kalle shi ba, ta fito da kuɗin hannunta ta miƙa masa. Yatsun hannun Sam ya bi da kallo ganin wasu kwantatun gargasa kwance a kowacce gaɓa ta yatsun hannunta, sun yi kyau sosai gwanin sha'awa. Ya san nufinta da baƙar zuciya saboda ya ce ta tsallaka yaron shi ne ya gogawa kan shi laifi. "bata son kuɗin ta fasa siyan takalmin kuma" haka yanayinta ya nuna. Sai ya tattara ya yi watsi da ita tare da yin gaba duk yadda yaso ya yi magana da ita. Ita ma gida ta nufa zuciya ba daɗi. Ana bata san abin da take ji a zuciyarta ya yi ƙarfin da zai saka ta rasa sukunin zuciya ba, sai da ta ji kamar damshin hawaye a saman fuskarta, a hankali ta miƙa hannunta zuwa ga zagayayyiyar fuskar tata, ba hawayen bane domin ƙarfin abin bai kai girman da zai saka ta zubar da hawaye a banza ba. Amma me ya sa yake cin zuciyarta har haka? Bata sani ba, amma hakan baya rasa nasaba da yadda aka aibata mata uba a gabanta.

"Me ya sa zan ji zafi har haka? Me ya sa zan ɗauki lamuran Daada na ƙwarzafi raina da shi na hana zuciyata sukuni?" Ita da zuciyarta suke wannan taɗin, tana cilla ƙafafuwanta ba tare data san inda suke samun masauki ba, ta ji zafi tabbas.

Ta kuma ji raɗaɗi tabbas.

Bata san ta ƙarasu ƙofar gidansu ba, sai data na ƙoƙarin shigewa ta yi gaba ba tare data sani ba ta ji an yi saurin riƙo hannunta. Bata firgita ba, saboda dakkakiyar zuciyarta sometimes, rigima kuma a jininta kawai take.

"Daga ina? Yaushe kika fara haka?"

Idanunta ta watsa a saman fuskar Jadid ta dube shi na wani lokaci kafin ta tabbatar a ƙofar gida take ta raɓa ta gefensa ta shige. Wani abu na musamman dake sanyaya zuriyar Ana ganin abin data fi so a rayuwa.

Yanzu ma tana ɗora idanunta akan Innti da Iftihal ta ji ta nemi dukkan damuwar data cushe mata a tsakiyar ƙirji ta rasa. Iftihal ce ta kalle ta kafin ta ce "Mahaɗita ko dai mu tattara ki kawai ki koma gidansu Yaa Sam?"

"Da kin duba mini, ko babu komai zan huta da cin arne da kwat. Ya kike Mahaɗita?"

Iftihal ta ce "Ba lafiya ba, bani da lafiya"

A ɗan rikice Ana ta dafe ƙirjinta saboda wani azababben bugawa da ya yi mata, wani tsoro ya lulluɓe ilahirin ƙofofin zuciyarta, idan ba ta yi ƙarya ba, har wani zazzaɓi ta ji ya fara saukar mata. "Mene ya same ki? Me kike so? Ina ke miki ciwo, mene damuwar?"

Yadda ta rikice kawai Iftihal ke kallo tana jin wata sabuwar soyayyar abokiyar haihuwar tata yana sake samun gurbi na musamman a zuciyarta. Idanunta ya kawo ruwan hawaye ta sake tabbatar idan bata raye Ana zata samun bugawar zuciya, yanzu ma idanunta ya zama kamar ba nata ba, jikinta sai faman rawa da kakkarwa yake yi.

"Ayshatul-Haleeym!"

Innti ta kira sunanta da ƙarfi tana jijjigata, amma tuni ta fara rasa nutsuwarta daidai lokacin Babban yaya ya shigo cikin gidan shi da Jadeed tsayawa suka yi, Jaheed ya dubi Ifti, Babban yaya kuma Ana da ake jijjigawa ya zubawa kasalallun idanunsa masu kyau.

"Shalelen Innti... Ana.... Ayshatu....."

Innti ta faɗa a gigice.

"Babban yaya duba mini ita, Yaa Jadid ɗebo mini ruwa me sanyi a randa ka ji"

A kiɗime Jadid ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ko dai aljanu ne suka shaƙe mata wuya, ko ta yi faɗa da wasu ne?"

Bata iya bashi amsa ba, gabaɗaya ta rungumeta a jikinta bata taɓa ganin girman yaranta, Iftifal fashewa da kuka ta yi tare da durƙushewa a wajan ta riƙe hannun Ana gam a cikin nata, cikin kuka take faɗin "Ki yafe mini mahaɗita, ba zan sake ba, ba zan kuma yi miki irin wannan wasan da zuciyarki zata kasa ɗauka ba, ki yi haƙuri" sai a lokacin Babban yaya ya fahimci abin da yake faruwa da kuma dalilin shigar Ana halin da take ciki, wato a kowacce haihuwar tagwaye akan samu mugu ɗaya da zai dinga gallazawa ɗayan, Iftihal ba mugunta take wa Ana ba, amma tana raunata zuciyar yarinyar da soyayyarta, jin cewa Ifti babu lafiya ya saka Ana fita daga hayyacinta.

A hankali ya durƙusa dab da fuskar Ana ya miƙa yatsun hannunsa guda biyu na tsakiyar ya shafi fuskarta kaɗan kafin a hankali ya sauke a gefen ƙirjinta ya danna a nutse. Ajjiyar zuciya ta sauke me nauyi jikinta ya saki a jikin Innti bata motsa ba, bacci ya ɗauke ta a nan jikin mahafiyarsu.

Innti ta dubi Iftihal ta ce "Iftihal....

"Na'am, Innti"

"Shin ba ki aminta da son da Ana ke miki bane? Ba ki yarda cewa zata iya rasa ranta idan bakya duniya ba? Ba ki yarda ba ko?"

"Na yarda Innti, wasa nake mata"

Innti ta ce "Wasa? Wasa da rayuwarta ko zuciyarta? Bari na faɗa miki za ki iya yi mata wannan wasan, wasan da har abada zai iya rabaki da ita, kar ki kuma na faɗa miki"

Cikin kuka da murya a raunace har ta fara dashewa ta ce "Na tuna Innti, ki yafe mini don Allah ba zan kuma ba in sha Allah"

"Shikenan, Allah Ya yi muku albarka gabaɗaya, Ubangiji Ya duba gabanku da bayanku ya tsare kima da mutuncinku"

"Amin" Iftihal da Jadid suka amsa.

Babban yaya ɗaki ya shige abin shi ba tare da ya ce komai ba, Jadid ya yi shiru ya zubawa Innti idanunsa kamar me buƙatar wani abu. Suna ta zaune har Ana ta farka, ko data farko ta manta da abin da ya faru ta ce "Gaskiya daga yau kullum a cinyarki zan dinga bacci uwata, kin ji laushi? Ubangiji Ya yi mini arziƙin da zan saka ki ji daɗi ki huta ki daina jin tuwo kwata-kwata, ki ce amin" Girgiza kai kawai Innti ta yi tana amsawa da "Amin" a zuciyarta. A hankali ta ja idanunta ta lumshe tana jin fresh air ɗin wajan na sake saukar mata da nutsuwa, abubuwa da yawa take son yin tunani akan su, na farko yadda zata rayu har abada ita da Innti da Iftihal, na biyu tunanin rayuwar mutanen da take gani a cikin baccinta, ta rasa dalilin da ya sa take mafarki dasu, ta rasa su waye, bata kuma iya hango haɗinta dasu ba. “MAMAA? UW?” ta furta a sanyaye domin sai a lokacin ma sunayen ya faɗo mata. Abu na uku alaƙarta da Daada ta rasa tudun dafawa domin har yanzu ta kasa gasgata cewa, shi ɗin mahafinsu ne, bai dace da uba ba sam.

Tattara maganar ta yi waje guda ta watsar. Ta juya ta kalli Innti ta kalli Iftihal sai ta ce

"Ni dai ku dinga saka ni a addu'a, Allah Ya bani miji kyakkyawa ko da maye ne shi" Ta yi maganar hankalinta kwance.

Iftihal murmushi kawai ta yi.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Innti ta zabga uban salati tana riƙe haɓa. Kafin ta ce "Ubangiji Ya miki zaɓi da mafi alheri a rayuwarki daku duka gabaɗaya ya nisanta ku daga abin ƙi, Allah Ya rabaku da auren maye. Maita babu daɗi" Ana ta yi shiru saboda tuna dramar ɗazo da aka yi da aka ce mata mayya.

Jadid ya ce "Daman gata nan kamar kazar mayu saboda rashin kuzari, tatsa ɗaya zai mata ya suɗe abin shi, ji jaraba wai maye?"

Idanunta a lumshe ta ce "Allah idan na auri mummunan miji zan iya haɗiyar zuciya, ina son abu me kyau, ina son kyakkyawan miji ko Aljani ne...," bata ƙarasa faɗa ba Babban yaya ya fito yana kallon ta, itama kallon shi ta yi ƙwayar idanunsu suka shiga cikin na juna ya ɗauke kai yana yin waje abin shi.

"Innti kin gama ɗinkin atamfar nan?"

"Wanne ɗinki? Abin duniya duk ya daman bayan kin ce ya yi kyau kin fita daga nan na rasa meke faruwa dani, komai ya lalace gashi yanzu atamfar jama'a ta yi kaca-kaca"

Miƙewa ta yi ta nufi inda taga atamfar tana ɗauka ta tuntsire da dariya ta ce "Daman abu ya fiya kyau masifa ne, Allah ya kyauta"

***

Bayan ya kammala gyarawa wani wayarsa da ta ci screen ya ajjiye sannu a hankali ya zubawa gefe guda idanu, ya ɗan girgiza kai sai asalin kamannin da yake dashi na zubi da labarabawa suka fara bayyana, yana tsoron wannan sauyin yanayin a cikin jama'a kar su dinga gudunsa, shi kan shi bai san meke faruwa da rayuwarsa ba, tsakanin baƙar fatar da farar fatarsa me sheƙi da ɗaukan idanu wacece asalin halittarsa? Ya miƙe a hankali ya shiga takawa ya ƙarasa jigin bango madubin dake maƙale ya kalla, daya kalli fuskarsa shi da kan shi ya ji tsoron ace shine wannan domin kyawun fuskar ya yi masa yawa, kyawun da zai zame masa bala'i ne. Waye shi idan ya ɗauke cewa shi Babban yaya ne? Ya tattara maganar ya watsar yaje ya zauna saboda gajiya da yunwa tunda uban gidan nasa ko kwabo har yanzu bai bashi ba. Bacci ne ya ɗauke shi a wajan.

Babu jimawa ya ji iska na kaɗa shi, sanyin ruwa na ratsa jikinsa ga ƙarar tsuntsaye na tashi alamar yana cikin daji ne. Ya buɗe idanun, bai san alaƙar da yake da ita a wannan wajan ba, bai san me ya sa yake zuwa nan ɗin ba. Numfashi ya ji yana sauka a fuskarsa kafin ya gama buɗe idanunsa ya ji siriyar murya ta shiga kunnensa an ce.

"Kaɗo....

Ya yi saurin janye fuskarsa, sai ta kuma matso da tata har goshinta na sauka a nasa, ta washe fararan haƙoranta masu kyau ta ce "Kai kaɗo ne ko? Kai kyakkywa ne zaka zo a yi mana aure irin wanda ake yi?" Nan ma bai magana ba sai kallon ta kawai da yake yi, ya zame kaɗan ya yunƙura ya tashi sai a lokacin yaga ɗanyen barkonon data yatsar a wajan.

"Wayyo Allah, kana da kyau kai kyakkywa ne, amma baka da lafiya shi ya sa baka da kuzari"

Ya yi mata shiru.

"Me kake yi a nan? Kai ma ɗan gidan Moddibo ne? Ina naggenka? Ina Innarka ta mutu ko tana raye? Kuma kai ma kana ganin kayan cikin mutane? Mutum nawa ka taɓa ci? Ka taɓa fita maitar dare? Wa aka taɓa cewa ka kawo aci? Kai kaɗai kake kama kurwa ko haɗin gwiwa kuke yi?" Tambaya take ta yi masa daga wannan zuwa wannan, shi kuma ya juya mata baya.

Ɗan zabura ya yi kaɗan jin ta cakume shi sai ta yi baya. "Innalillahi!" Ta lumshe idanunta "Jikinka laushi kamar burudin da Saleh yake bani idan ya taɓa ƙirjina" Sannu a hankali ya juya ya kalle ta, don tsayi tana da tsayi amma bata kai Anarsa tsayi ba, kyau kuma bai san waye yafi wani ba, wannan akwai surutu kamar aku, ana kuma maganarta a sanyaye take kuma babu ƙuruciya a tattare da Ana magana cikin hikima take yi. Ana ta zama budurwa completely, wannan yanzu take girman.

"Baffana makaho ne, amma sarai da idanunsa Yaaye ce ta makantar dashi saboda ta kasa cinye shi, ta ɗora masa lalura ita a tunaninta duk ban sani ba, ta manta muddin mayu suka kama mutum idan ɗan'uwansa ya gani yana gane tambarin mayen" ganin ko tari bai ba, ya saka jikinta yin sanyi ta ce

"Laa kaɗon baya magana Allah Sarki"

Ta zuba tagumi ta tallafi haɓarta. "Ka dinga shan ruwa sosai zaka samu kuzari da ruwan zogale ka saka madara a ciki

*** BRIGHT FM REDIO.

Ta gefen ido ya sake watsawa Ahlam wani irin miskilin kallo wanda yake nuna kin rainawa kan ki hankali. Ita kam gabaɗaya jikinta wani irin rawa yake yi yana ƙoƙarin bada ita, da yadda tsoron MD ɗin ya bayyana ƙarara akan fuskarta, ta kasa ɗago kai ta kalle shi, gashi zuwa yanzu tasan Yussy ta fara karanta labaran, gashi bata son ta saka auren matar can a cikin matsala.

A hankali ta ɗago kai kamar zata kalli fuskar MD ɗin sai kuma ta yi saurin mayar da idanunta zuwa gefensa, ta shiga kame jikinta da tattauna laɓɓanta wanda ta gama jiƙasu da yawon bakinta ba tare data sani ba. A iya tsayin lokacin data shafe a BRIGHT FM ɗin bata taɓa kallon cikakkiyar fuskarsa ba, bata da wani dalilin da zata kama wanda zai zama hujjar ƙin kallon fuskar ta MD.

Kawai dai tana da yaƙinin bata da alaƙa dashi da dukkan abin da ya mallaka a ciki har da fuskar da zuwa ke janta wajan kala, ko zata iya yango bambancin da yake tsakaninsa da sauran maza, wanda ya saka shi irin wannan ƙifaɗin da jin kai har haka.

MD da yake tsaye kamar an dasa shi wayarsa kawai yake dannawa, yatsunne kawai suke operating wayar, amma duk wani motsi na Ahlam yana ankare dashi, tare da sanya su cikin ma'adanan sirrin shi.

"Don Allah....,"

Ta kasa yin maganar a lokacin daya ɗago idanunsa ya watsa a saman fuskarta, jiran abin da zata ce yake yi, sai kawai yaga ta fashe da kuka ta haɗe kai da jikin ƙofar Studio ɗin jikinta na wani irin ɓari tana girgiza kai, a firgice kuma ta juya tare da zubewa a wajan ta haɗe hannunta biyu waje guda ta ce "Sir don Allah, don girman ka tsayar da Yussy daga karanta labaran nan, na shiga uku idan ta karanta na kaɗe har ganye na" da ƙyar take yin maganar ma. "Bana son matar nan ta rasa igiyar aurenta akan son raina, akan son ɗaukakata don...,"

"Baby mene haka? Get up please"

Anees ya furta yana ƙarasawa wajan idanunsa ya rine saboda ɓacin rai da ganin yadda Ahlam ta durƙusa a gaban MD ta zama wulaƙantacciya a wajan mara gata.

Girgiza kai ta yi ta ce "Ya zan yi Anees?"

"Wataƙila idan na durƙusa za'a fi fahimtata"

Anees ya ce "Ba dole sai kowa ya fahimci ki ba baby, saka labarin nan baya nufin tsayuwar rayuwarki, wani ko wata basu isa su yi miki abin da Ubangiji bai ƙaddara ba"

Hannu Anees ya miƙa zai ɗagota ganin yadda shanyayyen hannunta yake ta rawa shi kaɗai, shi dai sosai yake jin tausayin Ahlam har ƙasan zuciyarsa ba tare daya san wani dalili ba. Kafin ya saka hannunsa Md ya yi baya kaɗan da waya kare a kunnunsa

Ya ce "Idan room zaka kama mata a hotel bani da damuwa, Bright Fm bai zama dandalin ƴan iska na mamajos ba Please"

Daga Anees har Ahlam wani abu suka ji ya tokare musu a maƙoshi ya tsaya waje guda, wani irin duhu kawai Ahlam take gani, ta rasa dalilin daya saka MD yake mata kallon ƴar iska ko kuma me buɗewar ido, bata san abin daya taka ba da yake jin ko a gaban Ubangiji zai iya maimaita wannan kalaman masu muni a gare ta dama rayuwarta gabaɗaya. Ko dai ya taɓa kamata tana aikata abin da ba shikenan ba? Ko wani namijin ya taɓa gani ya rungumeta, ko ya sumbace ta, ko kuma kamata ya taɓa yi turmi da taɓarya? Tana buƙatar sanin dalilin wannan ƙazafin wanda yake shirin rusa mata dukkan farincikin rayuwarta.

Mijinta take wa tanadin kanta, jikinta na wanda Allah ya bawa ita ne matsayin mata

Da ƙyar ta miƙe tsaye, kanta a ƙasa daidai nan Yussy ta fito daga Studio kuma ya yi wa'adi da lokacin da HR ya ƙarasu wajan.

HR ya ce "Na je office ɗinka baka nan, so you're here ashe. Na ji kana kirana?"

"HR daga yau kar ka sake ɗaukar mana shirmammun mutane a gidan rediyon nan, waɗanda basu san komai ba sai shirme da tsoro, wanda basu da wani amfani sam"

Cikin girmamawa HR ya ce "In sha Allah"

MD ya juya a hankali, Yussy ma ta yi wa Ahlam wani irin ƙasƙantaccen kallo kafin da sauri tabi bayan MD tana riƙe masa hannu da faɗin "MD yaushe aka mayar da taron?"

Ahlam tabi bayansu da kallo, ta dubi yadda shafaffen ƙugun Yussy ke mannewa ita a dole murguɗa shi take yi, sannu a hankali kuma ganinta ya sauka akan hannun Yussy da yake cikin na MD. "Ɗan iska akwai" Ahlam ta furta a sanyaye tana jin cewa daman ɗan iska ne kawai ke yi wa wasu kallon ƴan iska. Da ƙyar Anees ya rarrashe ta suka nufi office ɗinsa tana ta murmushi tare da juya manyan idanunta, bayan sun shiga office ɗin ya ja mata kujera ta zauna.

"Anees"

"Na'am baby"

A hankali ta ce "Anees ina buƙatar ɗaukaka a aikin jarida kota wacce hanya ce, ina buƙatar na samu ɗaukaka ko hakan zai saka Yussy ta daina yi mini kallon da take yi mini na wacce ba zata iya ba, ina son nunawa duniya nakasa ba zata taɓa zama kasawa ba" ta ƙare maganar a hankali tana yin ƙasa da kanta saboda kallon da Anees yake mata.

Shiru ne ya biyo baya, tun tana jiran ta ji amsar da Anees zai bata har ta gaji ta miƙe ta nufi ƙofa zata fita tana ƙoƙarin buɗewa

Ta ji ya ce "Ahlam"

Cak ta tsaya kuma bata juya ba, tana jin sanda ya miƙe ya tsaya a bayanta ya ce

"Wata ɗaukakar masifa ce, ki yi addu'ar samun abin da yafi zame miki alheri. Aikin jarida ba abu bane me sauƙi, yanzu kika fara ba balle ki fahimci me nake son faɗa miki ba. Amma ɗaukaka ga ɗiya mace hatsari, kar ki damu da abin da Yussy ke miki, ki mata uzuri na wani lokaci kin ji?"

A hankali ta jinjina kai ta ce

"Thank you Anees"

"Bari na ajjiye ki a hanya nima tafiya zan"

Office ɗin ya rufe fuska fito tare, tunda ta fito Baba driver yake mata kirari irin wanda ya saba. "Allah Ya taimaki Golden voice, maƙiyanki fadawanki an buga dake an barki sarauniyar murya ta Bright Fm gabaɗaya"

Ta murmusa ta ce "Duk ni kaɗai Bana?"

"Haka za'a ganki a bar ki, bangon sigari kowa ya jingina dake sai ya lasa Wallahi"

Anees ne ya ciro walet ɗinsa ya ce

"Wannan kirarin ya zama dole na biya"

Jiki na rawa Baba driver ya saka hannu ya amshi kuɗin yana faɗin "Sarauniya sai da Sarki, Allah Ya baka Golden voice ka ji"

"Amin Ya Allah, Amin Ya rabb"

Anees ya furta cikin sauri yana lumshe idanunsa, cikin sauri Ahlam ta kalle shi sai ya yi saurin kashe mata ido ya yi waje.

Ta saman bene MD ya hango shigar Ahlam cikin motar Anees har suka fice sai kawai yaja siririn tsaki yana mai da sunglasses ɗinsa zuwa saman fuskarsa.

*** Ya murmusa kaɗan ya ce "Giɗaɗo ikon Allah masu Gwamantin da kan su, to ya ake ciki ne?" Wanda aka kira da Giɗaɗo ya gyara zaman shi a nutse fuska a kame cike da kwarjini ya ce.

"Barde, Gwamnati ai taku ce" Barde ya jinjina kai yana faɗin

"Shi ya sa naga nine na hannun daman Gwamna. Na ji abin arziƙi na offers data fito daga hukumar Ma'aikata ta Jiha, kuma dai kai ne Kwamishinan ilimi, dole na yi kamun ƙafa da akai" Giɗaɗo ya buɗe fararan idanunsa ta cikin glasses ya kalli Barde kamar ba zai magana ba, sai ya ce "Mun tattauna da Indabawa jiya, an ware naku da za ku bawa iya family ɗinku, Offer ɗin me kyau ce, hatta salary duk da ba'a kammala yanke nawa za'a bada ba. Waɗanda za'a bawa Allowance ma daban suke. Don haka za'a dinga siyar da Offer ɗin akan dubu ɗari uku, ba zamu rabawa yaran talakawa a aikin banza ba, ba sanin darajar ilimin sukai ba duk sune ƴan iskan gari"

Barde ya ce "Allah mutumina? Shi ya sa nake yinka ba, masu Gwamanati da kan su" Giɗaɗo ya miƙe tsaye yana gyara zaman suit ɗin jikinsa wacce ta yi masa kyau sosai.

"You're not nice Barde. Zuwa anjima zan shige Qatar dani da Madam, wai tana buƙatar hutun sati biyu ne kawai a can"

"Dole Madam ta huta da yawa, kuɗi yazo Alhaji" taɓe baki Giɗaɗo ya yi, mutum ne me ji da kan shi uwa uba ilimi da izza professor matakin ƙarshe kuma Dr. Suka ɗan fito harabar babban wajan. Barde ya ce

"Yanzu airport zaka shige kenan Giɗaɗo?"

"Nop, ina da meeting da Kwamishinar kuɗi, domin tattauna batun gina sabbin makarantu a jihar. 2 weeks zan yi na dawo akwai zama a Executive Council Majalisar zartawa"

Sallama suka yi ya shiga bawan haɗaɗɗiyar motarsa driver ya ja shi.

*** Tsoro ya hana Batty komawa gida saboda bata san wanne irin hukunci za ta yi mata ba na zuwa gaɓar kogi da take yi, tana tafe tare da wawwaro idanunta hannunta riƙe da sanda jikin nan babu kayan arziƙi sai kayan Fulanin dake jikin, kanta a buɗe babu kallabi, gashi dare tuni ya kawo kai. Cikowar mutane ta gani ga kiɗe-kiɗe na tashi akwai samari maza da mata da kuma ƙananun yara, cikin sauri ta washe jerarrun fararen haƙoranta cikin jin daɗi da nishaɗi ta ƙarasa wajan, wasu Ƴan'mata ne suke rawa a tsakiya ana musu kiɗa ga wasu samari na yi musu liƙi, Batty ta shiga girgiɗa kai saboda bata taɓa jin nishaɗi da kiɗa irin wannan ba.

Wuf ta faki idanun jama'a ta shige wajan tare da kutsawa tsakiyar matan dake rawa, rawa ta shiga yi tana girgiza tare da yin fari da idanunta da wani irin salo yadda take rawar kamar wacce ta saba da yin rawar dandali. Kafin wani lokaci matasan rugar Biya sun rufe Batty ana yi mata liƙi ta ko'ina.

Mado, ɗan gidan Moddibo shugaban rugar shine ya tako a hankali shi da abokansa ya tsaya a gaban Batty yana ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa, yarinya ce sosai akan yadda ya san matan birni, amma a rugar Biya tuni ta isa shiga ɗakin miji.

Tunda da yawansu a gidan miji suke irgar dangi, duk da itama bashi da tabbaci ko ta fara. Kuɗi ya fara watsa mata a jiki, Batty ta ɗauka yin rawar abin arziƙi ce ta shiga banƙaro ƙirji ana malƙwasa har Mado ya gama yi mata liƙin. Cak ta tsaya daga rawar saboda ƙwayar idanunta daya hango mata kasasshiyar kazar daya gama ci ko gama narkewa a cikinsa ba ta yi ba, ta rufe ido ta buɗe tana sake hango komai da yake cikinsa har da fura da nonon daya sha.

Cikin sauri ta biyo bayansa yana cewa

"Kaɗo, kaɗo hai kaɗo"

Mado ya tsaya a inda yake yar Batty ta ƙarasu wajan tana zuwa wajan ta ce masa

"Nima ka bani kazar da kaci"

Da mamaki yake bin bakin maganar da kallo na rashin fahimta. "Har da fura da Nonon"

Ta sake kashe shi da mamaki da faɗar Fura da nono. Mado ya numfasa ya ce "To"

"Amma sai gobe ko?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a yunwa nake ji, tun safe ban ci abinci ba, ko kazar ce ka bani"

Ya ce "Ya akai kika san na ci naman kaza?"

Dariya ta ƙyalƙyala ta ce "Wai ma, gata nan ina kallonta gwanin sha'awa ka siya mini"

Ya share maganarta, domin a shirme ya ɗauki zancen Batty babu mamaki taga lokacin da yake ci ne, tunda a nan ya siya ɗin. "Me kike da ba ki ci abinci ba har kawo shigowar dare?" Ta yi shiru sai kuma tadai "Yau aka kawo ni nan gidan Ƙanin Baffana, kuma matansa basu bani abinci ba, ina can baƙin kogi ina wasa ni ɗaya da ruwa sai barkono ɗanye da na ci in faɗa maka"

Mado ya buɗe ido ya ce

"Subuhana, harkokin kuma?"

Sai kawai ta jinjina masa kai tana murmushi.

"To, ina ne garinku?"

"Rugar Yari"

"Me ya sa aka kawo ki nan?"

A hankali ta ce "cewa akai wani kaɗo yana taɓa mini ƙirji wai nono ya fito mini"

Da wani irin mamaki da tashin hankalin surutun yarinyar Mado ya buɗe baki ya rasa ma me zai ce, tashin farko tsoro maganar ya dinga bashi, yanzu kuma ita ɗince take bashi tsoron ba wani ba. "Kuma da gaske ne?" Ta juya idanunta na rashin fahimta

Ta ce "Me ɗin?"

"Shi kaɗon ya taɓa?"

Ta jinjina masa kai.

Ya ɗaure fuska babu wasa ya ce "Allah sai ya saki a wuta yarinya, kike buɗe masa jikinki ko? To me ya taɓa ɗin? Me kike ji?"

Kai tsaye ta ce "Nono ya taɓa, zafi na ji"

Mado ji ya yi zufa na yanko masa ta ko'ina a jikinsa. Batty ta ce "Kai ma idan sai ka taɓa zaka bani kazar na buɗe ka taɓa kaɗan, sai ka siya mini abinci shima kaɗon abinci yake siya mini, saboda a gida ba'a bani komai. Bana cin komai sai duka da azabar zagi da kiwo, shine shi kuma yake.....," hannu ya ɗaga mata fuska a ɗaure ya ce "Ya isa"

Ya ciro kuɗi ya bata ya ce "Duk abin da kike so ki mini magana amma duk sanda na ji labarin kin sake buɗe jikinki sai na yanka ki"

Batty ji ta yi kamar fitsari na bin ƙafafuwanta, kisa? Irin kisan da aka yi wa Innarta? Me ta yi masa? Ko shima me sace nagge ne? Jikinta ya yi sanyi ta amshi kuɗin shi kuma ya yi gaba abin shi. Tsire ta siya me zafi ta ci ta sha ruwa kafin ta ɗauki hanyar gida hankali ƙawance. Sanda ta shiga a waje ta same su Kulu nata kuka saboda jikin yaronta da ya yi zafi sosai baya ko numfashi, an rasa abin da yake damunsa Sadiatu sai banbaki take yi amma taƙi shiru.

Gana na zaune gefe tana yin kaɗin Audiga.

Babu wanda ya kula da Batty har ta shige ƴar bukkar da aka bata tana shiga ta yi kwanciyar babu jimawa bacci ya ɗauke ta me nauyi ko sallah ba ta yi ba. Cikin bacci ta fara wani irin mugun mafarki wanda bata taɓa yin irinsa ba, ita sam bata mafarki.

Wani waje ne babba, yana kama da gari gudu ko masarauta, bata taɓa ganin girman gari da jama'ar garin da suke wata kala ba irin waɗannan mutanen da take gani a gabanta. Bata san mene ya kawo ta garin ba, tana cikin tafiya kawai ta ji an kamata an ɗaure da sarƙa an sanyata a cikin jerin matan da aka kama, sai muzurai take wani babban tashin hankalin ma, ganin yadda ake kwantar da mace a tsakiyar filin wajan ana rabata da budurcinta su yi mata kaca-kaca, kamar masu neman wani abu jikin matan, idan suka amshi budurcin nan take suke kashe yarinya su cillata ruwa ko a bawa dabbobin da suke wajan su cinye.

Batty ji ta yi fitsari na bin ƙafafuwanta, ita bata san ma'anar yadda ake danne mace ƙato ya hau kanta ba, kuma namiji ɗaya ne yake yin wannan ta'asar yadda yarinya ke kuka da ihu yake bawa Batty tabbacin ko ma me ake yi tabbas abu ne me ciwo da azaba.

Ta fashe da wani irin matsananci kuka tana jin kamar ƙasa ta tsage ta shige ko kuma ta mutu kafin azo kanta. Mutumin ne ya ce

"Ko duka matan duniya za su ƙare ba za mu saurara sai UWA MAMAA ta bayyana ta cece mu daga halaka, sai ABAR BAUTA ta bayyana"

Jin abin da ya ce ya saka Batty fashewa da kuka da ƙarfi ta ce "Do Allah idan akwai ɗiyar data san sunanta UWA MAMAA ta fito, walle bana son abin nan da ake yi kowa"

Daga daga cikin dakarun wajan ya zube a ƙasa yana ɗaga hannu ya ce "Ya shugabana shin babu wata alama da za'a iya haska mana yadda za mu UWA cikin sauƙi haka?"

"Akwai"

"Sanar dani Shugabana"

Ya shaƙi iskar wajan, yana wani irin ɗaci da raɗaɗi da yake cin zuciyarsa, ya dubi yarinyar dake kwance cikin jini har yarinya idan ya lissafa ya lalata budurcinta mata kusan arba'in kenan amma har yanzu haƙarsa bata cimma ruwa ba, da ƙyar ya ce

"Akwai wasali UKU da aka bamu na farkon sunanta, a ciki ɗaya akwai wasalin daya fara da sunan UWA MAMAA shine kawai"

Farinciki ya kama duka jama'ar wajan.

"Ka bamu sunayen wasalin?"

A hankali cikin taƙama ya ce

"Akwai A akwai F da H"

Ajjiyar zuciya Batty ta sauke jin babu wani wasali da ya yi iri ɗaya da BA tunda sunanta BATTY ne sai ta samu nutsuwar zuciya.

A haka aka dinga tambayar sunansa aka dinga ware wanda farkon sunansu ya yi ɗaya, a nan ne Batty ta hango wata mata a cikin babban keji da ƙaton ciki a jikinta tana kuka da ihu tana kiran Batty tare da yi mata alama ta gudu ko kuma dai tazo ta taimaka mata. Daidai nan kuma layi yazo kan Batty.

"Ya sunanki?"

Ta ce "Batty"

A hankali ya maimaita sunan "Batty"

Tun kafin ya yi magana ta ce "Amma na gaskiya Fatima ne kuma mayya ce ni....

Akwai page 6&10 a ArewaPen ka yi searching sunan littafin, ta appao a ko ta wesbio. Arewapen.com sai ka yi register ko log in.

Share fisabilillahi 🤲🏻

For information Chat dis number via WhatsApp 08082101373 08164069385