Kenza eBookz
Cover art for HIYAAM  HAUSA NOVEL PAGE

Post

HIYAAM HAUSA NOVEL PAGE

.....you need a story that I started writing since 2/5/2025, I am not sure if it will work for you but I have a fight, you will not read it. Whatever happened to the life of the moon or someone, promise me that it was an investigation that brought this, I am your journalist, please forgive me, parents of the country, forgive me and those who are involved, what you have done, I will bring it back. Mothers who hold household responsibilities, this is also yours. It is a fiction but the story of the tribe that you will hear and some things that look like fiction are all real, I just added a little more on others and will tell later. THANK YOU: Before I start, I would like to thank the writers who helped me gather information together. Writers definitely tried for me, Lubnasufyan, Sumayya takori, Zuwairiyyah Adamu gerie, Autar manya, Mai dambu, MeerahGee thank you all they tried for me while collecting information and seeing that I completed everything. BRIGHT PENS: Dear Ayushercool, thank you very much my zizi Zee Kumurya, may God give you paradise, I love you dear friends 🤭... And my.....

Standalone post6,518 words

*H I Y A A M*

Page 1 Bright pens

More pages on ArewaPen. Ku yi searching sunan littafin za ku samu.

Yota/001

Bari na yi amfani da wannan damar na yi miki godiya Yaɗɗo am, kina daga cikin alherin da media ta bani, Ubangiji Ya cika miki muradanki ya raya miki zuri'a Falmata 😂Every time I see you, I see you as family, even though you're the one I love. You'll always be my favorite person, Yaɗɗo, and my best friend forever. Even if I’ve never said it before, I can proudly shout it to the world through a loudspeaker: you're so special to me. Daga farko har ƙarshe wannan littafin sadaukawa ce a gare ki Jikar Nashe. Dedicated to NAZEEFAH SABO NASHE. Fans ɗinta zanga adadin capacityn da za ku nuna mini a tafiyar HIYAAM.

NOTE: A baya ban taɓa faɗa ba, a yanzu na ce, duk wanda ya sake ya yi mini amfani da littafi a YouTube Shari'a zata rabani da mutum in sha Allah, ban fara ba sai dana samu Copyright. Ta kowacce fuska kar a juya mini littafi.

MY WORDS: Wani labari da zai yi dai-dai da abin da kuke buƙata wani labari ne dana fara rubutawa tun 2/5/2025 bani da tabbacin zai muku amma ina da yaƙinin ba za ku yi danasanin karantawa ba. Duk abin da ya yi dai-dai da rayuwar wata ko wani ayi mini lamunin cewa bincike ne ya kawo haka, ƴar jarida daku nake a yi mini afuwa, iyayen ƙasa ayi mini afuwa da masu ruwa da tsaki abin da kukai makkuwa ne na dawo dashi, idan kina sake da addu'a ko tarbiyya ba ki wahala ki zo mu sasanta lamarin tare. Iyaye mata wanda suka riƙe responsibilities na gida wannan ma naku ne. Ƙirƙira ce amma labarin ƙabilar da za ku ji da wasu abubuwan masu kama da almara duk gaske ne, kawai na yi ƙari kaɗan akan wasu kuma zuwa gaba zan faɗa.

THANK YOU: Kafin na fara zan godewa marubutan da suka taimaka mini wajan haɗa information waje guda, na sha wahala na kasa sukuni akan tattara bayanai ganin kar a baku abin da hankali ba zai ɗauka ba. Marubuta sun mini ƙoƙari tabbas, Lubnasufyan, Sumayya takori, Zuwairiyyah Adamu gerie, Autar manya, Mai dambu, MeerahGee thank you all sun mini ƙoƙari wajan tattara bayanai da ganin na kammala komai.

BRIGHT PENS: Dear Ayushercool na gode sosai my zizi Zee Kumurya Allah Ya baku aljanna ina son ku sadidan yan'uwana abokan🤭... Da na ce ba zan rubutu ba sai 2027 sune suka tasoni gaba😄. My pple YOTAWA dangina duniya da lahira Allah ya sakawa jama'ar Young talented writers association wannan page ɗin naku ne.

_Bisimillahir Rahmanir Rahim_

A ƙa'ida a kuma tarihi, maza ne kawai suke yin aiki a gidan, sun tsani mata basa son su sam, suna ganin alaƙa da matan da suka ƙetare iyaka daka waje zuwa cikin gidan, kamar zai zama tubalin rusa dukkan wani al'ada, tsafi, ƙarfin ikon da sukai shekara da shekaru suna ginawa, domin kyautata goben da har yanzu suke zaman jiran ganinta. Kakanninsu ne suka damƙawa iyayensu, bayan sun cinye wa'adin da ƙaddara ta shimfiɗa wanda kowanne mai numfashi a ƙirji yake rayuwa tare da zanen tasa ƙaddara, mai kyau ko akasin hakan, sai suka tattara ragamar komai suka damƙawa ƴaƴansu, wanda ƙarfin iko, isa, izza, jinin ƙifaɗin dake gudana a jikinsu ya zarce waɗanda suka shuɗe. Sun rayu akan mafarki, sun wanzu da tsoron da mafarkin ya saka musu, wanda kuma shine zai zame musu jagoran da zai sanya su samu haske a cikin duhun da suke. A bisa wannan tsoran suka zartar da hukunci na ma'aikatan da za su dinga hidima a cikin TAJMAHAR. Jadawalin maza kusan 150 ne masu aiki kowacce rana, safe da yamma.

Suna amfani da maza ne, domin kafin haihuwarsu an sanar musu mace ita zata zama hujjar rarrabuwar kan su gabaɗaya.

Kamar kullum yau ma ma'aikatan sun yi layi a babbar ƙofar da zata fitar da su daka cikin Tajmahar, jerin maza ne, sanye da kaya iri ɗaya wanda ke bawa wanda ya kalle su, tabbacin uniform ne.Kowanne akwai numbersa a jikin rigarsa, duk wanda zai fita akan caje shi domin tabbatar da bai yi sata daga ciki ba zuwa waje. Zuciyarta ce ta cigaba da bugawa a ƙirji, wanda ya haifarwa da jikinta amsar yanayi, duk ƙoƙarinta ta kasa daurewa, a kullum da wannan tsoron take shigowa Tajmahar kuma take fita, Allah yana tarfawa garinta nono wajan fita salin alin. Sanda binciken yazo kanta numfashita ne ya ɗauke tsaf, kamar wacce wa'adinta ya yi a sa'ilin zufa na yanko mata a duk wata ƙofa da Ubangiji ya halitta a kyakkyawan jikin da wahala ta gama muzanta shi, zuwa siffa ta daban, siffar da ita kanta tsoran kallonta take yi a madubi, bata sha'awar ganin ma.

"No 089" aka nanata kiran sunanta.

Cikin hanzari ta ƙarasa tana shanye tsoran da ya gama cinye dukkan zuciyarta sai rawar ɗari take yi, a zuciyarta take furta; “Allah ya cece ta yau ma”.

Aka fara caje ta, aka cire hular kanta domin tabbatar da babu komai a ciki, aka tarar da santalelen kanta daya sha ƙwal kwabo babu tsoruwar suma ko guda ɗaya sai ƙyalli yake. Bayan an duba aka mayar da hular kan nata, aka caje har cikin takalminta har zai sallame ta, sai ya lura da ƙirjinta kamar ya tasa, tunaninsa ko wani abu mutumin ya sato, zato ko tsammani balle hasashe bai taɓa kawo masa ita ɗin macace ba, tunda ta fara aiki har kawo yanzu da sunan namiji take amsawa “TERSEER”. Ya yi mata kallon tsaf kamar zai cinye ta a dake ya furta "089"

Sannu a hankali ta jinjina kai alamar amsawa. "Cire rigarka, umarni nan take"

Ta ji umarnin har tsakiyar kanta, kamar an sanar mata da ranar mutuwarta, ƙoƙarin magana take yi, amma ta kasa, muryarta zata fallasa sirrinta na jinsin ƴa mace, ya sake yi mata tsawa "Terseer 089!" Fafur taƙi cire rigar, sauran ma'aikatan da basu fita ba, suka fara yi mata ban baki akan ta yi abin da aka ce, domin a cikin abu biyu za'ayi ɗaya, ko ta rasa ranta nan take, ko dai ta tabbata a cikin kurkukun “GBANDE AONDO”

"Guards! Guards!"

"Umarnin kira nan take......!"

Cikin ƙaramin lokaci dukkan wasu Guards da suke tsaron ƙofar suka bayyana, aka zagaye ta. Babban cikinsu ya ce "Wannan mutumin ya yi sata, akwai kaya a ƙirjinsa, a ƙwace a yi masa bulala hamsin a kore shi"

"Kashina ya bushe!" Ta furta a zuciyarta.

Kokawa suka shiga yi da ita, sai dai kasancewar ta macace ita dole ta bada kai bori ya kar boka, bugun zuciyarta ya tsananta lokacin da suka zare rigar wata razana suka yi tare da yin baya, nan take kuma iska ta fara tashi a wajan, arba da halittun ƙirjinta na ɗiya mace da suka yi a lokacin ya fi komai muni a tarihin masarautar Tajmahar, wani abu ne da ko a mafarki ba'a taɓa tunanin zai faru ba, rashin sani ga Guards ɗin, domin bayyanarta zanannen labari ne tun iyaye da kuma kakanninsu har zuwa yanzu.

Ta saka hannu wajan kakkare tsaraicin ƙirjinta, hawaye na taruwa a cikin idanunta.

Bayyanar abin da ya faru ya zama abu me sauƙi, kamar wutar daji a cikin Tajmahar, kafin ka ce wane aiki, Shugaban da kan shi da jama'arsa sun ƙarasu wajan, ya shiga bin kowa da idanu, yana ɗora idanunsa a kanta, jikinsa na matsanancin rawa da ɓari ya yar da sandan dake hannunsa ya zube a gabanta wajan ƙafafuwanta ya furta "Lale, barka da zuwa uwata, barka da zuwa Mamaa, barka" ya ce da rawar ɗari.

Allah Subhanahu wata'ala shi kaɗai ake bautawa, ita musulma ce mene ya haɗata da abin da suke yi? Su waye su ɗin? Mene hakan? Me kalma Uwata, da Mamaa suke nufi a tattare da ita? Ta shiga girgiza kai

"Bani bace, bani bace" ta faɗa a sanyaye, jikinta na rawa

"Mun fi shekaru muna dakwan zuwanki Mamaa, kar ki yi fushi damu, ki albarkaci wannan masarautar, an ce, kalmar ki ɗaya na iya sauya mana rayuwa, ki yi furuci akai na Mamaa, ki buɗe bakinki Mamaa, ki yi..,"

"Ban kasance wacce kuke nema ba"Ta rushe da kuka

"bani kuke jira ba....

Nan da nan suka fara rawa da kiɗe-kiɗe hatta Shugaban rawa ya fara cikin waƙe yake maganar "Kece ruhinmu Mamaa, kece gatanmu Mamaa, abar bautarmu kece Mamaa, kece"

Suka shiga watsa mata wasu abubuwa aka.

Sham ya ce "Mu fara tabbatarwa ita ɗin ce, an bamu haske na yadda za mu gane Mamaa, an baka umarnin kasancewa da ita a dare ɗaya, idan ka samu nasarar keta budurcinta, to ba ita ce Mamaa ba, idan alƙalaminka ya gaza keta budurcinta to tabbas Mamaa ta bayyana a wannan karon"

Jin haka ya saka ta mance da tsaraicin ƙirjinta dake bayyane, ta saki hannunta ta juya zata fara gudu ya ce "A ɗakkota, akai ta kyakkyawan gadon da nake kwajin budurci domin tabbatar da zuwan Mamaa, ku kasance a bakin ƙofa, idan kuka ji ihu to na samu budurcinta, sai a fara tunanin yadda za mu kashe ta, idan kuka ji shiru baƙin hayaƙi ya bayyana, to Mamaa ta bayyana, sai mu shirya inda zamu ajjiyeta mu dinga yi mata bauta" duk yadda ta yi ƙoƙarin kiran sunan Allah ta kasa, komai nata ya kunce ta durƙushe a wajan, wani badakaren mutum ya zo ya saɓa ta a wuya ya nufi da ita cikin ɗakin Shugaba. Ya ajjiye ta ya fito, Shugaban ya shiga jama'ar wajan sun fi ɗari suka tsaya a bakin ƙofa ana dako, tare da sauraro zuƙata cike da fatan Allah Ya sa ta kasance MAMAA ABAR BAUTA wace suke jira tsayin shekaru.

*** H I Y A A M. Littafin Haleeym Ana Daada.

Jerin kalmomi guda biyar kawai ta samu zarafin rubutawa a cikin fejin littafin dake hannunta, idan ta irga haruffa a jimilance a yau ta samu ƙarfin zuciyar rubuta harafai har Talatin cif, saɓanin baya da iya HIYAAM kawai take rubutawa a tsayin kwanaki talatin har yinin yau kenan, kalmar da a yanzu bata san me take nufi ba, bata san bigirin da zata ajjiye ta ba, ta ci karo ne da ita a cikin mafarkan data saba a kullum.

Ta shiga juya biron hannunta, tana tunanin da zuciyarta, da tambayar kanta a hikimance.

"Zan zama marubuciyar kuwa?Zan iya rubuta abin da nake ji yana mini yawo a cikin kaina wanda baya barin ƙwaƙwalwata samun nutsuwa? Wanda yake gallabar zuciyata..Haka rubutun yake dama?"

Ta ja numfashi ta sauke.

"Haka kowacce marubuciyya take ji?" Sai ta sake ɗora biron akan takaddar akaro na babu adadi, wannan karan ma haƙarta bata cimma ruwa ba, duk yadda ta saƙa zaren labarin daka farko har ƙarshe, data zo rubutawa komai yake daburce mata, ta kasa.

"Wataƙila bani da basirar zama marubuciya"

Ta furta a fili cike da sangarta da shagwaɓar da take jin kamar da ita aka haife ta, luuu ta ja manyan idanunta ta lumshe su, saboda iskar bishiyar darbejiyar dake kaɗata, wacce ta kasance zaune a ƙasanta saman tabarma.

Sai kuma ta saki dariya me sauti. "Ƙila rabon zama ƴar jarida ya daƙusar dani daga kasancewa marubuciya, irin shahararrun marubutan nan da suke tashe, amma ba masu rubutun lalata tarbiyya ba" Idan zaman banza ne da rashin abin yi ya riga ya gama zama a jikin Ana, hankali kwance cike da sabon nishaɗi ta juya bayan littafin nata, ta fara rubutu sannu a hankali.

"Sunana Ayshatul-Haleeym, da yawan mutane basu san asalin sunana na Aysha ba, irin sunan Nana Aysha Matar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama. Ban san ina Babana ya samo sunan ba, a kaf danginmu na uwa da uba babu wata mai suna Aysha....Au dangin Babanmu basa son mu na manta ban faɗa muku ba, bayan Aysha, ana kirana da Haleeym irin sunan ƴan gayu, duk da ni talauci ya ɗaurawa iyayena riga, bayan Haleeym ana kirana da ANA. Sunan Mamata INNTI, wanda ya amsa sunan uba a gare ni ana ce masa DAADA, Muna zaune a garin Kano, a cikin local Government ta Municipal, a wata unguwa da ake kira da Kankarofi. Mu biyar ne a wajan Iyayenmu, haka Innti ta haife mu duk da Talaucin da take fama dashi, amma masu kuɗi yara biyu kawai suke haifa, Babban yayanmu ana ce masa BABBAN YAYA, bayan shi ta haifi tagwaye duk maza Yaa Jaheed da Yaa Jadid, amma nafi son Yaa Jadid, saboda shi yana taje mini kaina, yana yanke mini farce, shima Yaa Jaheed ina son shi saboda yana da kirki, yara uku kenan, sai mu da muka kasance ƴan auta, tagwaye ne muma, dani da mahaɗita, rana ɗaya aka haife mu, bamu san waye babba ba, Innti ta ce bata cikin hayyacinta ta haifo mu, don haka kowa babba ne. Sunan abokiyar haihuwata IFTIHAL, wasu na ce mata Iftin Innti, ni kuma Shalelen Innti Itama sunanta Aysha, ni ANA ita IFTI...

Sai ta dakata daga rubutun tana bin jerin kalmomin da bata san yaushe ta rubuta ba, ba tare data san hakan shi ne tubalin zama marubuciya a gare ta ba, baiwar kalaman da suke fitowa daka ƙasan zuciya na zahiri.

Iskar ta cigaba ta kwasarta dara-daran idanunta ya fara lunshewa alamar bacci.

"Ina da ƙanin uba, amma fa shi ɗan daudu ne, ana kiran shi da suna Sukunbiya, don Allah ba sunan kifi ne haka ba? Bala sunansa na gaskiya... Sai kuma Yaa Sam, abokina aminina kuma yayana maƙocinmu ne, kyakkyawa ne sosai yana da grey eyes amma talaka ne irinmu, wasu da yawa suna cewa wai saurayina ne, bayan babansa ya yi masa zaɓen matar aure, kuma ni bana son ma ya zama mijina. Ina son namiji kyakkyawa,bani da burin daya shige na auri kyakkyawan namiji a duniya, fari, dogo, mai zubi da tsarin halittar Ubangiji, irin kyawun da bana damuwa ko da na Aljanu ne, talaka ne, gurgu ne, ko da me cutar ƙangamau ne (Hiv) muddin kyakkyawa ne ajin ƙarshe, irin kyawun mazan novel to zan aure shi, ko da ace zai dinga gutsirar naman jikina yana soyawa tare da cinyewa ne, kai ni ko da maye ne ina so. Wannan shine ra'ayi da tsarin ANA....

Bacci ne ya ci ƙarfinta a daf da lokacin da limamin Masallacin unguwarsu ke ƙwalla kiran sallar la'asar, haka ta cusa littafin a rigarta ta ɓingire wajan ta fara bacci.

* 1500 / 1700. TIVLAND NA FARKO

Sau tari ana cewa, idan masifu suka yi yawa a inda kuke, yin ƙaura tare da yin nisa shine yafi zama alheri, a kwanakin baya na faɗa muku asalin su waye Tiv, na san kuma kun fahimci daga ina iyaye da kakanninku suka samu tushe, Hausawa sukan ce, Tushiya masomin dawa, haka kuma kowa ya bar gida, gidan zai bar shi. Mun samu matsin rayuwa, na rashin doka, bamu da shugaba ko wanda suke jagorantarmu, kowa yana cin gashin kan shi ne, mun yi imani da Akombo fiye da yadda kuke tunani, mun wayi gari cikin fari da talauci, har muka yanke shawarar yin ƙaura, ashe Akombo ya yi fushi me tsanani damu, hakan yasa komai ya rikici mana. Muka ɗauki hanya me nisa.

A cikin wannan shekarar a hanyarmu ta yin ƙaura saboda yawan jama'a sai aka rabu kashi da kashi, kowanne rukuni suka kasance Ahhali guda, kamar yadda muma muka kasance iyali ɗaya ta hanyar kaka ɗaya daya haifi iyayenmu, ni na fito daga ɓangaren Ikur ɗan'uwana ya fito daga ɓangaren Imande, ma'ana babana shine Ikur babansa kuma Imande, muka tashi dangi biyu a bisa jagorancin kakanmu. Mun yi wannan ƙaurar saboda yawan jama'a, da kuma neman ruwa da kuma Dazuzzuka sai ƙasar da za ta iya yin noma. Akan hanyarmu ne wa'adin mutuwar kakanmu ya yi, dare ya tsala babu gida gaba, babu baya, muna tsakiyar daji ne. Mun yi kukan rashi sosai, domin shine muke gani matsayin Dattijon da yake jagorancin Ikur da Imande. A cikin wannan daren muka fara shirin bikin jana'izar kakanmu, muna yara amma har yanzu ina hango yadda al'amarin ya faru.

Aka haɗa ganye da ruwa da ƙasa, aka fara watsawa gawar kakanmu tare da wasu kalamai na tsafi, an lulluɓe shi da farin yadi.

Ba'a ɗauki minti biyar da fara wannan tsafin ba, mu kaga kakanmu ya miƙe saman ƙafafuwansa, na ɗauka idan mutum ya mutu shikenan tashi ta ƙare, bisa ga mamakina sai na ga gawa ta miƙe da ƙafafuwanta tana tafiya, haka muka dinga binsu gawa na tafe muna bayanta ana kiɗa da waƙe, har zuwa inda aka haƙa ramin, kakanmu na zuwa zai shiga cikin kabarinsa, sai mu kaga ya tsaya cak, wani baƙin hayaƙi na fita ta cikin idanunsa, wanda alama ce na cewa, yana son bayar da saƙo ne kafin ya kwanta a cikin kabarin nasa, wanda zai zama gidansa na ƙarshe, sai idan dalili ya zama babban dalili za'a iya tayar da shi ya bamu haske akan abin da ya shige mana duhu muka kasa samun mafita mai ɓullewa.

Ya yi shiru daga basu tarihin kakansa, ya dubi ƙananun yaran da suke gabansa, basu fi shekara biyar biyar ba, sai namiji da ba zai fi shekara biyu ba a cinyarsa ya yi luf yana bacci. Yana shafa kan wata mace ya ce

"Na san kuna son jin me kakana zai ce ko a lokacin?" Suka jinjina masa kai alamar "eh"

Ya ɗora da; Ikur da Imande, muna tsaye muna kallon kakanmu, Iyayenmu na kallon mahaifinsu suna sauraro daga gare shi. Cikin abin da bai gaza daƙiƙo ba, gawar kakanmu ta buɗe bakinta cikin damuwa da murya irin ta kuka da tashin hankali, ta ce

“Haƙiƙa kun karya dokar Akombo, bala'i da masifu za su faɗo muka, ba za ku taɓa samun sauƙi ba, har sai UWA MAMAA ta bayyana, zata bayyana ɗauke da TSAV, kalmarta ɗaya waraka ce a tattare daku, albarkarta ceto ce a wajanku, kada ku neme ta, ita da kanta zata kawo kanta inda kuke, domin bata kasance ɗaya daga cikinmu ba, tana wata uwa duniya, wata nahiyar ta daban, kar ku neme ta, zata zo har inda kuke ta same ku, duhu da iska,da baƙin hayaƙi da kukan Akombo shi ne zai baku shaidar cewa, MAMAA tazo, kalmanta shi ne misali na biyu, babu yankan shakku a duk wani furucinta, harshenta bala'i ne ga ƴan'uwanta, ku kuma haske da tabarraki ne a gare ku, idan kun samu MAMAA kar a yadda a kuskura ta kasance da ɗa namiji, balle ta ɗauki ciki, MAMAA tsarkakkiya ce, na san Ikur da Imande da maitar mace. Akwai alama ta uku da zata sake bayyana zuwan MAMAA, idan an yi mata gwajin budurci, Alƙalamin ba zai taɓa shiga jikinta ba, babu wani daya isa ya amshi kimar MAMAA, zaku sadaukar da budurcinta ne zuwa ga Akombo, Tsav ɗinta zai cece ku”

"Kaka mene Akombo da Tsav?"

Anum ta yi tambayar cikin rashin fahimtar tarihin kakan nasu na zamanin daya shige.

Ya dubi Anum ya ce "Anum, Akombo yana nufin ikon ruhaniya da aka gada daga kakanni, yana warkar da cuta, kariya daga bala'i, gano me laifi, warware rikicin dangi a taƙaice Akombo shine haskenmu da muka yi imani da shi Anum. Tsav shi ne ikon sihiri mugun iko a al’adar Tiv. Ana danganta shi da Mayu, masu shan jini, masu cutarwa ta ɓoye ana cewa Tsav yana cikin jinin mutum ko ruhinsa. Ba kowa ke da Tsav ba masu Tsav suna iya, haddasa cuta, kashe mutum a ruhaniya, rikitar da al’umma hakan na faruwa ta harshensu, a kalamansu"

Ya cigaba da basu labarin asalinsu; Bayan mun kammala sauraran Kaka, yana gama faɗa ya faɗa cikin kabarinsa muka binne shi. Muka cigaba da nausa tafiya a tsakiyar daren har muka samu yada zago a gaɓar wani ƙogi. A lokacin Itayo daga ɓangaren Imande shine ya amshi jagorancin tafiyar. A hannunsa akwai ganye da aka ɗaure da zare,da ƙasa a ƙaramar ƙwarya, da ruwa daga kogi. Ya durƙusa a wajan yana duba ƙasa kamar me nazari cikin girmamawa ya ce

“Ba mu mallake ku ba” ya faɗa a hankali. “Ku ne kuke riƙe mu.” Ya ɗauki ɗan gishiri ya zuba a ƙasa. Ya shafa ruwa a ganyen, ya ɗora su a gefen wuta. Murmushi mu kaga yayi, akan hadayar da ya yi wa Akombo.

Itayo ya ce "Akombo ya yarda da zamanmu a nan, bai amince da zubda jini ba, duk wanda ya karya doka bala'in Akombo zai saukar mana, don haka a kiyaye kun ji?"

Ikur da Imande sun yanke shawarar a zauna a nan, saboda ruwa mai yawa, mun samu ƙasa me laushi da albarka ga kuma sauƙin noma. Aka kafa tanti Ikur suka keɓe haka Imande, muna murna mun samu makoma me kyau muna tsaka da bacci, wata mummunar masifa ta afko mana, wanda ya haddasa mana rashin mutane wajan ashirin a cikinmu, farmakin da ƙabilar Jukun suka kawo mana.

1976. TIVLAND.

Shigowar Dooshima ne da sauri ya dakatar da Kaka daga Tarihin da yake bawa jikokinsa na asalinsu wanda yake bin tarihin shekara-shekara na abin da komai ya faru, tunda daga asalin Tiv har zuwa yanzu da yake shekarar da sukai ƙaura a 1500/1700. Kaka ya bi ɗansa Dooshima da idanu, shima kallon mahaifin nasa yake kafin da hanzari kuma ya ce "A ɓoye mata da ƙananun yara"

"Ɓoyewa? Dooshima lafiya?"

Kaka ya tambaya da tsoro saboda gudun wani bala'in da Akombo zai jefo musu.

Anum na ɗan juya fararen idanunta masu kyau da tsari irin na mahafinta Dooshima.

Dooshima ya kalli Kaka ya ce

"Sojoji ne, sune sukai mana ƙawanya kar su sake kashe mu, kamar yadda Junkun suke bin mu kowacce farar asuba su kashe mu"

"Na rantse da Akombo babu abin da zai faru da dukkan jinin Ikur alƙawarina ne wannan, ka hanzarta ɓoye yaran nan yanzu"

Anum ta ce "Kaka me ya saka za'a ɓoye mu?" Ya shafa kan ta cike da damuwa ya ce

"Za mu iya rasa ku a yau ɗin nan Anum ɗin kaka, jeki wajan Babanki ya ɓoye ki kin ji?"

Rashin yadda ya bayyana a tattare da Anum, ita a dole sai ta fita taga Sojojin da ake magana akai. Haan ne ya shigo hannunsa ɗauke da baka da kibbau, yana ganin ɗan'uwansa Dooshima ya furta

"ka shirya?"

"Zan ajjiye Anum da Jarumi"

Tashin hankali ya wanzu a saman fuskokinsu, tsoro suke ji da gaske, sun ɗauka sun samu ƴancin kai bayan zuwan turawan Biritania, amma hakan duk ya tafi a busar sarewar Audu. Haan ya furta

"Yaushe za mu daina fuskantar matsi da rikin ƙabilanci, anya ba za mu yi magana da gawar Kakanku ba Ortyom?"

Kaka ya ce "Ba za mu daina shiga masifa ba, har sai MAMAA ta bayyana wacce za mu samu TSAV a tattare da ita, dole sai ita"

Cikin gwaranci Anum ta ce

"Kaka yaushe Mamaa zata zo?"

"Yau ne, gobe ne, jibi ne ko gata, wannan shekarar, wannan zamanin ko sai bana raye ban san yaushe ne Mamaa zata bayyana ba, amma komai daran daɗewa Uwa Mamaa zata zo, kuma za ta cece mu" ƙarar Kibbau suka ji, da sauri Haan ya yi waje yana kare ƙofar shigowa gidan duk da a tsakiyar dokar daji suke a gaɓar kogin da bashi da suna.

Da hannu ɗaya Dooshima ya saɓa Anum a kafaɗa, ya saka hannunsa ya ɗauki yaron dake wajan kaka yana bacci ɗan wajan Haan. Can cikin gidan ya shiga wajan wani ramin ƙasa inda suke ɓoye mata da yaran, Anum na kuka da ihu haka ya dannata cikin ramin ya ɗauki Jarumi ya saka mata a cinya, ya mayar da ƙofar ya rufe tare da ƙaton dutse, cak ya tsaya yana goge hawayen idanunsa bayan ya zubawa ramin ido, yana jin kukan Anum dake ratsa kunnunwansa, babu tabbacin zai sake sanyata a cikin idanunsa. Ya ɗaga kai sama ya ce "Na bar Anum da Jarumi a hannunka Akombo, an yi maka laifi har yanzu Uwa bata bayyana ba, waɗannan ɗin yara ne ka kula dasu Akombo" yana faɗin hakan ya fice da sauri yana tushe kunnunwansa daga jin kukan Anum ɗinsa.

*** Mafari. 11/8/2025. KANKAROFI/ KANO MUNICIPAL.

Kankarofi na daga cikin tsofaffin unguwanni da ke cikin birnin Kano. Tana cikin Kano Municipal LGA. Yammacin ranar Asabar ne wanda ya yi dai-dai da Shaɗaya ga watan takwas, shekara ta dubu ashirin da ashirin da biyar, kasancewar watan Nuwamba ne, farkon shigowar sanyi ya saka iska me daɗi da sanya nutsuwa take kaɗawa a lungu da saƙo na cikin garin, har zuwa unguwar Kankarofi da mutane shige da fice.

Ƙarar ihunta ne ya ja hankalinsu zuwa ga ƙasan bishiyar da take kwance tana bacci a saman tabarma, ba ihun ke basu mamaki ba, face yadda take kiran sunan Anum da dukkan ƙarfinta zufa na yanko mata, bayan sunan Anum har sunan jarumi take kira.

"Kar ku bar su a ramin nan, shikenan za'a kashe Anum na shiga uku, Anum, Anum...

Wanda yake alwala ya juyo ya kalle ta, sai ya girgiza kai ya ce "Ina fa'ida a baccin La'asar daman, ba dole mutum ya yi mugun mafarki ba, tai ta bacci kamar kasa haba"

Matar dake ta tsinke zogale da ya yi kore shar saboda rani, ta ajjiye zogalen tare da zuba tagumi sannu a hankali kuma take bin yarinyar dake ƙwance wacce bata fasa kiran sunan Anum da Jarumi ba da kallo, can ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Tashe ta daga baccin nan Jaheed" ya ajjiye butar hannunsa. Tsaye ya yi a kanta, fuskarta ta yi sharkaf da zufa ta kuma yi ƙyalli ya saka ƙafa yana shurinta a hankali

Ya ce "Ana"

Jadid ya kalli Jaheed yana dariya ya ce

"Wannan uwar baccin, da shegen nauyin bacci kake wa wannan kiran Jaheed?"

"Wallahi takaici ne ya kamani, wannan ihun kamar mahaukaciya sabon kamu har ina"

Jadid ya ce "Ko kuma sabuwar amaryar da ake shirin sawa a lalle ba, zaune zaka tashe ta, idan ba haka ba, ba tashi za ta yi ba".

Duk yadda Jaheed ya yi ƙoƙarin tashin Ana kasawa ya yi, ya juya ya kalli mahaifiyarsu data mayar da kai zuwa ga aikin tsinke zogalen ya ce "Innti taƙi tashi, anya lafiya?" Bata kalli Jaheed ba ta miƙe zuwa inda Haleeym ke bacci da sambatun kiran sunan Anum da Jarumi, ta zubawa kyakkyawar fuskar yarinyar idanu kamar tana karantar yanayin da take ciki, ta fara kiran sunanta.

"Ayshatul Haleeym!"

Ta nanata "Ana, Haleeym"

Sallama ya yi a nutse cikin kamala ya shigo gidan, amma duk basu san ya shigo ba, ya jima tsaye hannunsa cikin aljihu ya watsa idanunsa akan fuskar Ana ganin yadda Innti ke ta kiran sunanta amma ko motsi ba ta yi. Ya juya zuwa bakin rijiya, ruwan da ya gani a cikin bokici ya ɗakko tare da ƙarasuwa wajan da suke, duk suka matsa shi kuma ya ɗaga bokicin ya sheƙa mata ruwan.

Ruwan sanyin da aka kwarara a jikinta ya haddasa mata farkawa daga nauyayyen baccin yamman daya ɗauke ta, ta shiga mustsikka manyan idanunta, ƙoƙarin komawa take yi ta kwanta tana surutai irin magagin baccin nan wanda bai gama sakin mutum ba, daman gata da nauyin bacci.

A fusace ya ɗauke ta, ya dire a wajan. Ganin ta tsaya akan ƙafafuwanta ya saka ya juya ya zauna akan Benci yana duba agogo.

Littafin dake rigarta ya faɗo ƙasa

"Wayyo Anum, ki yi shiru kin ji jikalle" cikin magagin baccin ta sake furta hakan idanunta na lunshewa jikinta na zubar da ruwan daya kwara mata saboda yadda ta ishe su da ihun ana saka Anum da Jarumi a cikin rami, garin kayan takaicinta ta kwasuwa kanta mutanen ɓoye ita kaɗai ta sani sai Allah, yin duniya ta tashi daga bacci amma fafur taƙi sai mimmiƙe hannu take.

Daga gefe aka ce "Wai uwar wace Anum ɗin nan, da kika cika mana gida da kiran sunanta a cikin baccinki? Ƙawarki ce ko?"

Jadid ya girgiza kai ya ce.

"Ko kuma ta yi rigima da wasu, suka biyo yammaci wajan shaƙe wuyanta wallahi"

"Babu mamaki" in ji Jaheed.

Sai kuma ya miƙe yana kakkaɓe yadin da yake jikinsa da furta "Duk hankalina ya tashi, na ɗauka Shalelen Innti aka kawo wa hari, gashi na rasa jami'in la'asar dole a gida zan gabatar na yi na koma shago yanzu"

"Kar ka sake ka yi mini sallah a gida" Innti ta furta a sanyaye idanunta zube akan yarinyar da aka tayar daga bacci. Sai ɗacin rai take yi tana kukkumbura kamar wata kububuwa, fuskar nan na ƙyallin kyakkywar baƙar fatarta ga shatin tabarma da ya yi mata zane a kumatu

Jaheed ya ce

"A gafarce ni Innti"

Ya furta yana ficewa daga cikin gidan.

"Mutum yana baccinsa me daɗi kawai sai a katse shi fisabilillahi? Kun san me nake gani?" Jadid da Innti suka zuba mata idanu, wanda ya tashe daga baccin kuwa har yanzu ko tari bai yi ba, bai ma sake kallon inda take tsaye ba, tuni ya koma ya zauna ya cigaba da duba wayar hannunsa daya kunce. Ta juya ta kalli Jadid suna haɗa ido ta murguɗa masa bakinta, ta kalli Innti ta ce

"Innti wanne me tsautsayin ne ya tashe ni?"

"Gashi can" Jadid ya bata amsa yana nuna bayanta. Ta juya zata fara masifa idanunta ya sauka akan Baban yaya, nan take ta ji zufa na karyo mata duk da iskar bishiyar darbejiya dake kaɗawa tana bada yanayi me daɗi. Ta haɗiye yawon baccin daya tarar mata a baki. Ta nufi tabarmar zata zauna ta ji kamar daga sama ya yi gyaran murya.

Sai ta kwaɓe fuska ta ce

"Nifa aka zalunta bance komai ba, kun san a tarihin gidan nan ko Tv ta wasa ba'a taɓa yi ba, balle ta gaske ɗan kallon nan dake saka nishaɗi ba'ayi, kowa keyboard ce a hannunsa, shikenan na samu ana haska mini film a cikin baccina sai a tashe ni saboda mugun abu? Yanzu ba lalle na sake yin wannan sa'ar ba, gashi ina son sanin yadda ƙarshen abu zai kasan da rayuwar Anum data Jarumi...," bata ƙarasa maganar ba, ta miƙe a zabure ta yi cikin ɗaki ganin Babban yaya ya ciro darbejiya tasan tsaf zai zane ta, ba imani ne dashi ba wallahi ga mugun abu.

Ganin ta shige cikin ɗakin ya nufi hanyar waje, bai jima da shigowa ba tun safe amma har zai sake ficewa.

"Tafiyar kenan?" Inji Innti.

Ya jinjina kai alamar "Eh"

"Allah Ya tsare hanya Babban yaya, kar ka yi dare don Allah bana son kaiwa daren nan ka ji ko?" Jiki a sanyaye ta yi furucin.

Bai amsa ba, ya saka kai ya fice.

"Babban yaya kike cewa kar ya kai dare? Shine fa babba a gidan nan, babban wa magajin uba ne Innti a ɗan raga masa"

Hararar wasa ta yi masa kafin ta fara ƙwalla kiran sunanta. "Ana kika bari na shigo ba ki fito kin ɗauki buta a gidan nan kin yi sallah ba, mai rabani dake sai Allah ki cigaba da saka ni kumfar baki a gidan nan" Ita kam tuni ta yi nisa a tunanin da take yi, game da rayuwar mutanen da aka haska mata a cikin baccinta, waɗanda bata san su waye ba, ƙilama basa duniyar, domin rayuwar da taga sunayi irin ta labaran almara ne da hikayoyi da kuma da tsuniyya, koma yaya ne, ita a Film ta ɗauke shi, kallon ya yi mata daɗi sosai, domin taga abubuwan daba kowa ne ya san dasu ba.

"Jadid shiga ka fito mini da yarinyar nan"

Fit ta fito daga ɗakin, kai babu ɗan ƙwali sumar kan nata a hargitse gashi tubarakallah kamar Buzuwa har ƙasan wuyanta baƙa suɗik da ita. "Ki cigaba da shiga banɗaki babu kallabi Ana, in sha Allah sai na saka Babban yaya ya aske mini rabin sumar nan taki, kamar wata Bunzuma" babu abin da take so sama da sumar kanta cikin sauri ta fusge hular kan Jadid ta kifa a nata kan. Ta yi cikin banɗakin

Ya ce "Kika shafa mini kwarkwata a hula na daina koya miki komai, me kama da chocolate"

"Yaushe ka fara yin halitta ne Jadid?" Ya ce "A gafarce ni Innti, fatar Ana ce ke bani mamaki wallahi, ko mai take shafawa ne?" Innti ta ce "Sai ka tambayi Babban yaya, domin naga kalarsu iri ɗaya ce ko shine yake sammata man da take shafawa, bata da kuɗin siyan mai"

Jadid ya yi saurin yin shiru jin ta sako Babban yaya a lamarin nasu. Ganin ya yi shiru ya saka ta ce "Kasha maganinka ne?"

Ya ce "E, saura na dare in sha Allah"

"To, Allah Ya sa kaffara ne Jadid"

Ganin ta fito da gudu daga cikin banɗakin ya saka suka juya suna kallon ta, ta saka hannu ta tushe hancinta ta ce "Wanne ƙazaminne ya gundura mana kashi a ruɓaɓɓen banɗakin nan sai uban wari, kana gani ka san kashin gardi ne wallahi" Jadid ya ce "Waye gardin? Babban yaya? Bari ya shigo gidan zai ji komai in sha Allah" Tsuke fuska ta yi, bata sake magana ba ta cigaba da ɗaura alwala cike da nutsuwa da tarbiyyar da Innti ta ɗora yaranta akai.

***

“Labaran rana, a ranar 25–26 Disamba 2025, Amurka ta kaddamar da harin sama da ake kira da airstrikes a yankin arewa‑yammacin Najeriya, musamman jihar Sokoto. Wannan aiki ya kasance tare da haɗin gwiwar sojojin Najeriya Harin ya shafi sansanonin ƴan ta’adda masu alaƙa da ƙungiyar Islamic State (ISIS)musamman irin waɗanda ake kira Lakurawa a yankin. Sojojin Amurka sun yi amfani da makamai masu daidaitaccen GPS daga jiragen sama masu iko da na teku, inda suka kaddamar da harbe‑harbe kan manufofin da aka gano suna da alaka da ISIS. Babu cikakkun bayanai kan adadin mutane da suka mutu, amma gwamnati ta ce an kashe ƴan ta’adda da dama. Harin ya faru ne da yardar gwamnatin Najeriya ta wancan lokaci. Me rahoto Ahlam Abdallah Zango, mita 116 BRIGHT FM”

Cigaba da sauraron Redion ya yi yana murmushi cikin nutsuwa da kamala.

“An saurari rahoton tsaro daga abokiyar aiki Ahlam Abdallah Zango. Yanzu za mu koma ɓangaren wasanni, me rahoto Anees Adeel Yakasai" kashe Redion ya yi ya ajjiye a gefe ya ɗan murmushi tare da kallon ta ce ya ce

"Madam"

"Na'am Abban Mufeed"

Ya furta "Ina jin daɗin yadda kika taimaka mini muka tsaya kai da fata wajan cikawa Ahlam burinta na zama ƴar jarida".

"Abban Mufeed, Ahlam amana ce a gare mu, kafin mahaifinka ya rasu kai ya bawa wasiyyar kulawa da Ahlam, a matsayina na matarka dole ne na tayaka kulawa da ita, da wannan wasiyyar, ka duba muryar Ahlam ce muke saurara ni da kai a Redion yanzu haka" ta ce tana riƙe hannunsa.

"Ba iya ni dake ba, duka garin Kano suna sauraron Amanata, ita ɗin Golden voice ce"

Idanunsa ya kawo ruwa, sai kuma ya ce "Ni tana ina ne ma? Wani labari na ji ɗazon nan ta zo na faɗa mata amma sai ta bada abin sadaƙa" cikin tsokana Jiddah ta ce

"Haba ranka ya daɗe uban Mufeed, yayan Ahlam mijin Hawwa'u a gaza mana"

Daidai nan Ahlam ta fito tana gyara hular kanta, bata gama dawowa daidai daga baccin da take ba, Mufeed ya je ya uzzura mata ganin yayanta ya saka ta zauna cikin shwagaɓa ta ce "Yaya kaga Mufeed ko?"

"Babu ruwan Yaya, ki faɗawa babarsa"

Cikin sauri Jiddah ta miƙe tsaye ta ce "A'a sun fi kusa, harshe da haƙori kunga hanyata" ta haura sama tana musu dariya.

Engineer ya ce "Na biyo hanya na ci karo da taron mata, har zan shige na tuna ina da suda a gida, na tambayi meke faruwa aka ce wata kishiya ce ta ɗauki jaririn amayar mijinta ta cilla a ruwan zafin..," ko gama bata labarin bai yi ba, ta zabura ta miƙe duk da hannunta ɗaya da yake shanye ta ce

"Yaya wacce unguwa ce don Allah"

Ya ce "Kawo abin sadaƙa"

Cikin shwagaɓa ta ce "Ina son ka, sosai da sosai yayana abin alfaharina, you're my 001"

"Daɗin baki, babu komai da haka kike yin nasara akai na. A Gandun Albasa ne"

Ɗaki ta koma, ta ɗauki jakar kayan rahotanni cikin sauri ta fice tana waving yayanta. Ya lumshe idanunsa ya ce

"Allah Ya tsare"

*** Jifanta ake yi da duwatsu yara sun taru maza da mata ana kallon yadda take durƙushe, tuni yaron da aka kama shi da ita acikin lungun yana taɓa mata ƙirji ya gudu. "Nifa gwara da asirinta ya fito fili, ba zata zauna ta ɓata mana yara ba, uwa uba gata mayya dole ne tabar mana cikin rugar" bata fahimtar me suke cewa, wani irin kartawa cikinta yake mata saboda saɓar yunwa.

Fincikota aka yi da ƙarfi. Jamila ta ce "Babu mamaki ita ta cinye jaririyar Zabba'u tun tana ciki. Wannan ai irin masifa ne"

Rinannun idanunta kawai Batty ta ɗago tana binsu da ido da ƙyar ta ce "E ni mayya ce, amma wallahi bani na ci jaririyar Zabba'u ba, daman Zabba'u bata da ciki ƙarya kawai ta yi muku. Ga cikinta nan lafiya lau babu alamar ɗa ya taɓa zama a ciki, kayan cikinta gwanin sha'awa" Jamila ta ce

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Wannan wacce kalar masifa ce ai dole ki bar rugar nan kafin ki cinye mu gabaɗaya" tusa ƙeyarta suka yi zuwa gidan me gari.

***

Ganin Shida ta kusa ya saka ta ɗan ƙara saurin da take yi akan nada, kanta a ƙasa tana tafiya cike da nutsuwa kamar kazar da ƙwai ya fashewa, addu'a take yi Allah Ya sa Babban yaya bai dawo ba, yanzu sai ya haɗa mata Malaman jikinta. Daga can nesa ta ji an ce "Ifti" cikin sauri ta juya.

Zaune ta hango shi a ƙasan bishiya, shi da abokansa suna ta faman karta hayaƙin taba na tashi, ya ɗan ya fito ta da hannunsa ta ƙarasa "Na'am Dadaa" ta amsa tana durƙusawa. Ya dube ta sosai yana sake zuƙar tabar yana busawa a gefe ya ce "Ina Ana na ganki ke ɗaya?"

Ta ce "Ana na gida, kitso na je na yi"

"To nawa kika samu a can?"

Ta ware hannunta, yaga curarriyar ƴan dubu guda biyu, ya kwashe kuɗin yana faɗin "Jeki gani nan zuwa gidan, hanzarta Ifti, kar Ana ta biyo sahunki"

Kan ta ƙasa hawaye na cika idanunta ta ce

"To Dadaa"

Bayan ta yi gaba, wani Dattijo wanda a ƙalla zai yi shekaru 62 bakinsa fal goro da ƙaton tumbin daya kwanta masa, ya saɓa babbar rigar jikinsa ya ce "Kar ka ce mini ɗiyar wajanka ce wannan?" Dadaa ya bushe da dariya yana juyawa wajan kallon Ifti ya ce

"Alhaji Baita, kar dai ka ce baka san ƴar taka ba, ai Tagwaye ne su, Ayshatul-Ana, da Ayshatul-Ifti, wannan Ifti ake ce mata, ta gidan kuma Ana, yarana ne"

"Ka ce kawai dukiya na gida a ajjiye"

In ji Alhaji Baita.

Ya ɗora da "Ina da shawara, Miliyan goman dana saka na caca, kai kuma ka saka keken ɗinkin matarka, yanzu na ƙara miliyan goma akai ya zama miliyan ashirin, ina son ka saka Ifti ma'ana Iftihal a cikin cacar, idan ka ci zan baka miliyan ashirin kash, idan na ci, zaka bani Iftihal....

Idan labarin ya yi muku a duk inda kuke ku nuna alama a tayani sharing saboda Allah.

Team Bright pens 08164069385 08082101373 Read on Arewa