Kenza eBookz
Cover art for KOMAI YA YI FARKO  HAUSA NOVEL 3

Post

KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 3

.....he went out of her mind at the same time. Now, always in the istighfari rake and the prayer of God, he took her life when he accepted her, not when he was angry with her, her future is in danger now since the world has already collapsed for her. Life did not hurt Humaira anymore until Kamis went to talk to his friends about what happened to her, and then the word spread in their neighborhood in a way she did not expect. First of all, when she goes out to go to Islam, she sees people following her and looking at her, sometimes even pointing fingers at her in town, on her head or on her body, because she knows she hasn't done anything wrong. Humaira was lying at her mother's feet and was teasing her, Farida's mother and Farida greeted and came in. Farida is Humaira's best friend who grew up together since primary school. Mom smiled and said; "Good morning, now I'm saying let me finish teasing her and we'll come to your house and check on you." Mamam Farida sat next to Inna and said; "The body is too light." Humaira stood up from where she was lying at Inna's feet, hugged Farida's mother a little, and said; "Mom, I'm sleeping, you body?" "Healthy beauty, body and ease, Mama's dau

Standalone post2,142 words

https://chat.whatsapp.com/CGm8zTMQDDO1e9sf3BmDKQ?mode=hqctcla

KOMAI YA YI FARKO

PAGE 3

Alhaji Mai canji wani hamshaƙin mutum ne dake anguwar mu, matarsa biyu amma ɗa ɗaya tak Allah ya azurta shi dashi, shine LUKMAN. Lukman ya kasance hatsabibin yaro tun yaranta, ya taso babu kwaɓa, duk abinda yake so shi ake masa, hakan yasa ko da ya girma bai ganin kowa da daraja, kuma duk abinda zai yi to fa daidai ne a wajen mahaifinshi, sau da dama ya ɓata wa yara mata rayuwa, amma babu wanda ke iya kai ƙararsa saboda tsoron Alhaji mai canji da kowa ke yi a anguwar.

Tun daga ranar da Kamis ya rabu da Humaira, ta shiga cikin sabon ƙunci da baƙin ciki, ta rasa ɗan ƙarfin gwiwa da ta ba wa kanta na cigaba da rayuwa kamar komai bai faru ba.

tana tafiyar da rayuwanta ne cikin ƙuncin rayuwa, result ɗin SSCE ɗinta ya yi kyau sosai saboda ta yi ƙoƙari sosai wajen ganin ta mayar da hankali a karatunta.Amma despite kyau ɗin result ɗinta, ba ta tunanin za ta iya cigaba da karatu, saboda yadda komai na duniya ya fita mata a rai lokaci guda. Yanzu kullum cikin istighfari rake da addu'ar Allah ya ɗauki ranta a lokacin ya yarda da ita, ba a lokacin da yake fushi da ita ba, Lahiranta take tattali yanzu tunda duniyar ta riga da ta ruguje mata. Rayuwa ba ta ƙara yiwa Humaira zafi ba sai da Kamis ya je ya yi hira da abokan shi akan abinda ya sameta, daga nan kuma maganar ta yaɗu a anguwar su ta yadda ba ta yi tsammani ba, wasu ma cewa suke ƙarya take ba fyaɗa aka yi mata ba, da son ranta aka yi. Da farko idan ta fita za ta je islamiyya ko aike sai ta gan mutane suna ta bin ta da kallo, wani lokacin ma har nuna tai da yatsa ake yi a gari, itako ko a jikinta, saboda ta san she haven't done anything wrong.

Humaira na kwance a ƙafar Innarta tana yi mata tsifa, Maman Farida da Farida suka yi sallama suka shigo. Farida ƙawar HUMAIRA ce da suka taso tare tun daga primary.

Inna na murmushi tace; "Sannunku da zuwa, yanzu nake ce bari na gama mata tsifa mu zo gidanku na duba ki."

Mamam Farida ta zauna a gefen Inna tace; "Jiki ya yi sauƙi ma ai." Miƙewa Humaira tayi daga kwancen da take a ƙafar Inna, ta ɗan rungume Maman Farida, tace; "Mama ina kwana, ya jiki?"

"Lafiya ƙalau, jiki da sauƙi ƴar Mama" ta faɗa tana shafa kanta.

Sannan ta ce; "Ku ɗan ba mu waje, zan yi magana da Innar ki." Humaira ta ɗauki hularta ta rufe gashinta baƙi ƙirin mai cika da tsawo sosai, ta miƙe ta fita tare da Farida. A tsakar gida ta shimfiɗa mu su tabarma, ruwa ta ɗeba a kofin silva ta kai wa Mama a ɗakin, sannan na ɗebowa Farida, ta miƙa mata, girgiza kai ta yi, tace; "Ƙawata Allah ya sa abinda nake ji a gari ba gaskiya ba ne." Kallonta Humaira ta yi da mamaki, ta ce; "Me kike ji a garin?"

Numfasawa Farida ta ɗan yi, tace; "Kwana biyu kenan magana ke ta yawo a gari wai an yi maki fyaɗe, dalilin zuwan Mama ma kenan."

Wani ɗaci-ɗaci Humaira ta fara ji a maƙwogwaronta, zufa ya fara keto mata lokaci guda, da kyar ta iya ɗaga ido ta kalle Farida, ta ce; "A ina kika ji wannan maganar Farida?" Farida ta ce; "Asha, maganar da ya baza gari, ko ina fa maganar ake yi."

Humaira ta gyaɗa kai tace; "Na gan alama, ashe wannan shine dalilin da ya saka da na fita kowa ke bi na da ido." Ta share hawayen da ya gangaro mata, tana sharewa wasu na ƙara gangarowa, kawai sai ta rungume Farida ta fashe da kuka. Iya kiɗemewa Farida ta kiɗime, she just don't want to believe cewa abinda take ji gaskiyane, amma sai ta yi wani tunani, 'Ma zai sa Humaira kuka idan ƙarya ne.'

Cireta ta yi daga jikinta, bakinta na rawa tace; "Please my friend kar kice min gaskiya ne, this can't happen to you."

Share hawayenta Humaira ta yi da bayan hannu, ta ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali, ta ce; "ƙawata ƙaddara ta riga fata, tabbas an yi mini fyaɗe." sai ta fashe da sabon kuka, tana jin baƙin cikin cin amanar da Kamis ya yi mata, don ta san bayan ƴan uwanta da suka san abin nan sai Kamis da ta faɗawa don ta ɗauke shi a matsayin masoyi, ashe dai ba hakan bane, ƴan uwanta kuma tana da tabbacin ba za su yi mata wannan fallasar ba, tunda aka yarda akan a rufe maganar ta san ba za su tona ba, gaskiya Kamis ya cuceta, ya ɓata mata suna a gari, ya sa ta zama abin kallo. Farida ta rungumeta, tana bubbuga mata baya ta ce; "It's ok ƙawata, ki daina kuka, wannan ba shine karshen rayuwarki ba, duk wanda ya yi miki hakan zai gan sakamakonsa tun a duniya." Kuka kawai ta cigaba da yi tana rungume a jikin Farida, duk yadda Faridar ta so ta daure kar ta yi kuka hakan ya gagara, kukan tausayin ƙawarta itama ta fara yi. “Kamis ya cuce Ni, Na fi kowa son maganar nan ta bayyana idan za a kwatar min haƙƙina, amma na san ba za a yi hakan ba, to me amfanin fallasa Ni wa duniya don kawai na kunyata, ban taɓa tunanin haka daga gare sa ba, amma duk wanda ya yi mai kyau don kansa.“ Share hawayenta ta yi, ta tafi randa, ruwa ta ɗeba ta wanke idanuna tsaf, by all means ba ta son ta bar maganar nan ta damenta, don ta san idan ta shiga damuwa kowa a gidan nan zai shigeta. Tabarmar ta dawo ta zauna, Farida ma ta goge hawayenta ta sakar mata murmushi, murmushin itama ra ƙaƙalo, kwantar da kanta na yi a ƙafafun Farida, sai ta zame hular kanta, ta cigaba da yi mata tsifar da Inna ta yi rabi. Sunna tsaka da tsifar Inna suka fito tare da Mama, Inna ta bi Humaira da kallo zuciyarta fal tausayinta, murmushi ta sakar mata pretending as if bata san komai ba, kamar Farida ba ta faɗa mata dalilin zuwarsu ba, saboda ta gaji da ganinta cikin damuwa ta dalilinta.

Ƙarfi da yaji fita ya nemi ya gagare HUMAIRA, saboda duk inda ta saka ƙafa a unguwar sai an nunata, dole ta daina fita kwata-kwata, hatta islamiyya ta daina tafiya, su Yaya da Abba ke yi matq karatu a gida, kullum Inna na cikin kwantar mat da hankali, tana ƙoƙari wajen ganin ta saka ta walwala, ba ta barinta ta shiga tunani.

Humaira ta rage yawar magana sosai duk da tun da ita ɗin ba mai yawar magana bace, Kullum daga ɗaki sai banɗaki, Yau ta yi wa kanta faɗa akan yawan zama da take yi a ɗaki da wata rana zai iya saka ta cikin wani hali, hakan ya sa ta miƙe daga kwance da take, waje ta fita tsakar gida da take jin hirar mutanen gidan suna ayyukarsa. Bakin randa ta tafi, ta ɗebi ruwa ta wanke fuskarta tsaf, kafin ta zo ta samu waje a gefen Innarta ta zauna, hannu ta saka ta fara tayata tsintar shinkafa da za a dafa na dare. suna tsaka da tsintar shinkafar ana hira, Abba ya shigo tare da Yaya Kabir ɗauke da sallama a bakunansu. Bayan sun gaisa da mutanen gidan, Ya Kabir ya zauna a gefen Humaira ya ɗan ja kumatuna, yana murmushi yace; "Humairar mu yau ke kenan za ki yi mana girki?"

Gyaɗa masa kai ta yi, ta ce; "Shinkafa da wake zan yi wa Abba mai danƙaran daɗi."

Ya Kabir ya naɗe hannunsa a ƙirji, ya mata wata kallon kin ma isa, yace; "Mu kuma sai mu ci wannan ƙaton kan naki?" Ya faɗa yana mai dungure mata kai. Hannunsa ta riƙe, tana murmushi tace; "Ni kam ba ni da wani ƙaton kai wallahi, kuma wai kishi kake da Abban?"

Taɓe baki ya yi, yace; "Ba zan biye miki ba." Hannu ya saka shima ya fara tsintar shinkafar, yana yi yana zolayarta, tun tana kulasa pretending to be fine, har dai da gasken ta fara jin wani farinciki na ziyartata, ta fara jin walwalar da zuciyarta ta kwana biyu rabonta da ita tana dawowa. Tabbas ta gan farincikin da ke idon dukkan mutanen gidan da suka ganta cikin farinciki, hakan ya sa ta yi wa kanta alƙawarin no matter what zata yi ƙoƙari ta kasance cikin farin ciki by all means. Saboda tsabar yadda Abba ya kasa controlling farincikin da yake ciki, fita ya yi daga ɗakinsa, ya zo ya zauna tare cikinsu a tsakar gidan ana hira da raha da shi. Suna cikin wannan yanayin sauran ƴan uwa suka zo suka same su a hakan, aka ɗora hirar da su, Auta Bilki na maƙale da Humaira duk inda na saka ƙafa, daman ita ɗin ta hannun damarta ce. Daidai ana kiran sallar Maghrib Humaira ta sauke tunkunyar abinci, daga gefen murhun ta ajiye tunkunyar, sannan ta fita daga kitchen ɗin. Mama Lantana kawai ta iske a tsakar gida, kowa ya shige yin Sallah, ita ɗin ma alaular take, butar da ta iddar da alaular ta miƙawa tana faɗin; "Sannu da aiki Humaira." Murmushi kawai ta yi mata, ta karɓi butar, ta ce; "Na sauke abincin, idan kin fito sai ki raba."

"Toh Nagode, Allah ya yi miki albarka."

"Aameen." ta furta a hankali.

Bayan Abba da samarin gidan sun dawo daga masallaci, Mama Lantana da ita ke da girki, ta shimfida babbar tabarma a tsakar gidan da ke share tsaf, Abincin Abba ta fara kawowa, sannan ta kawo na Inna, Humaira ta taimaka mata ta kawo na samarin, da kuma na Mama Hafsatu, a tray ta zubowa Humairan da ƙanenta mata, duk suka fara cin abincin cikin shiru da nutsuwa. Bayan mun kammala cin abincin su Bilki da Imrana suka tattara kwanukan suka kai wajen wanke-wanke. Suna zaune a tsakar gidan suna ɗan hirarakin duniya hara aka kira Isha, kafin kowa ya watse. Ko da mazan suka dawo daga masallaci, kowa sun shige ɗakinsu, Inna na zaune akan darduma tana jan carbi, Humaira kuma ina zaune a bakin gado ina linke kayan su da Inna ta wanke da safe, ta kuna rediyon wayar Inna tana sauraro. Inna na iddar da addu'o'inta ta zo ta zauna a gefenta tana taya ta linke kayan suna jera a ɗan ƙaramin wardrobe ɗinsu dake ɗakin.

Gidansu HUMAIRA madaidaicin gidane mai ɗauke da ɗakuna biyar daga ciki, sai ɗaya daga zaure. Dakin zauren shine na Abbansu, na farko daga gefen dama kuma a ciki shine na samarin gidan, na gefensu shine na Inna, na tsakiya na Mama Hafsatu, na gefenta na Mama Lantana, na ƙarshe shine na Umman Salamatu, tun bayan rasuwarta Abba ke ajiyar amfanin gonarsa da kayan tsaronsa a ciki.

Humaira da Inna suke kwana a ɗaki ɗaya, Imrana kuwa tana kwana da Bilki a ɗakin Mama Hafsatu, a ɗakin Mama Lantana kuwa, ita kaɗai ke kwanciyarta tun bayan auren Ya Khausar. Kan ƴaƴan gidan duk a haɗe yake, Abba na tsaye akan duk abinda ya shafe gidansa, bai ba wa ko wacce mace damar raba masa kan ƴaƴansa ba, yana kuma iya ƙoƙarinsa akan ci, sha, suttura da kuma makarantar ƴaƴansa, Yaya Kabir ya haɗa degree ɗinsa a Computer engineering, Yaya Kamal ma yana da degree a civil engineering, Ya Khausar na da diploma a Mass communication, Khalid da Yusuf suna SS2, Humaira ba ta daɗe da yin Candy ba, Bilal na Jss3, Bilki da Imrana suna primary 6.

Bayan sun gama jera kayan tsaf a wardrobe, Humaira taa kwantar da kanta a cinyar Innarta, tana sosa mata kaina dake tsefe a hankali, lumshe ido taa yi, ta buɗe a hankali, tace; "Inna..."

"Na'am ƴar Inna." Ta amsa tana cigaba da sosai mata kai.

Gyara kwanciyarta ta yi, ta ce; "Daga gobe zan ci-gaba da tafiya islamiyya, zan cigaba da rayuwata yadda nake da, ba zan sake bari maganar mutane ya ƙara tasiri a kaina ba, I will live my life to the fullest, saboda na sama wa kaina da ku farinciki, saboda na lura farincikin ɗayan mu shine farincikin mu baki ɗaya, haka zalika baƙin ciki."

Ɗago da ita Inna ta yi, tana faɗin; "Tashi tashi ƴar albarka." Rungumeta ta yi tsam a jikinta, sai kawai Humaira ta fara jin yadda hawayenta ke gangara a dokin wuyata, a hankali ta fara magana; "Kin yi shawara mai kyau ƴata, Allah ya yi miki albarka, ya bi miki haƙƙin ki, Allah ya ba ki ikon cinye wannan jarabawar, Tabbas kin tabbata musulma kuma mumina mai imani da ƙaddara."

Humaira na rungume a jikin Inna tana sauraron yadda take suburbuɗa mata albarka har bacci ya ɗauketa.

SHIN KUNA GANIN HUMAIRA ZA TA IYA ABINDA TA ƘUDDIRA.

#JIKARGARBA 07048694211.