Kenza eBookz
Cover art for FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 18

Post

FARASHIN IZZAH BOOK 1 PAGE 18

.....t turned and looked at Firdausi. "How come you knew I needed rest and lied to my supervisor?" Firdausi smiled. "Zahra, if I don't know you, I don't deserve to be your friend." She stopped for a while and said, "Zahra, now start the car and let's leave the school." Zahra started the car and started walking. For a moment there was silence in the car. Then Firdausi looked at her. "Zahra, what's wrong with you?" "Nothing." Firdausi laughed and shook her head. "Zahra, we are not used to this, you say, let's not start." Zahra was silent, looking at the street. "Kema, you know I know you're not like that," Firdausi said softly. "I left you at school because I don't want the Asians to understand anything." Then she lowered her voice, "You are with Ibrahim, right?" Zahra took another breath. She slowly said, "Firdausi... my heart will beat." Firdausi quickly turned and looked at her. "What happened?" "Ibrahim will kill me..." her last voice trembled. Firdausi quickly said, "Oh Zahra! Stop talking like that." Tears filled Zahra's eyes. "By God, I don't feel good... since yesterday." She bit her lips trying to stop her crying "I started to fear what I see and what I don't see..." Immedia

Standalone post2,533 words

FARASHIN IZZAH

Book 1 Chapter 18

Bayan sun fito daga lecture ɗin ne aka sanar musu cewa supervisor ɗinsu yana neman duk 'yan group ɗinsu.

Zahra na tsaye tare da friends ɗinta amma ko kaɗan bata ma fahimci me aka ce ba. Firdausi ce ta matsa kusa da ita ta maimaita mata a hankali.

"Supervisor na neman 'yan group dinku Zahra"

Kai Zahra ta gyada kawai ka.

Firdausi ta riƙe jakar hannunta sannan suka fara tafiya a hankali suna bin bayan sauran 'yan group ɗin.

Bayan sun isa office ɗin, supervisor ɗin ma kallon Zahra kawai yake yi. Daga gani ba cikin normal state take ba kwata-kwata. Ko fara'ar da aka santa da ita babu.

Firdausi tayi saurin magana kafin ya tambaya.

"Sir bata jin daɗi ne, kuma zata tafi antenatal."

"Okay," ya amsa yana kallon Zahra. "You can go. Duk gyaranki zaki gani a hardcopy ɗinki."

"Nagode sir," Zahra ta amsa da ƙyar.

Daga haka suka fito tare.

Tun daga office ɗin har zuwa parking lot babu wanda yace uffan

Sai da suka isa wajen motar Zahra suka shiga.

Zahra na saka seat belt ta juya tana kallon Firdausi. "Ya akayi kika san I need rest har kika ƙirƙiri ƙarya wa supervisor na?"

Murmushi Firdausi tayi. "Zahra idan ban san ki ba, ban cancanci na zama kawa a gareki ba."

Ta ɗan tsaya sannan tace, "Zahra yanzu tada motar mu bar makarantar nan."

Ba musu Zahra ta tada motar suka fara tafiya. Na ɗan lokaci shiru ne ya mamaye motar.

Sai Firdausi ta kalleta. "Zahra meke damunki?"

"Nothing."

Dariya Firdausi tayi tana girgiza kai. "Zahra bamu saba haka dake ba, kar mu fara."

Shiru Zahra tayi tana kallon titi.

"Kema kin san nasan ba haka kike ba," Firdausi ta ƙara faɗa cikin tausasawa. "Na zame ki ne a school saboda bana son su Asiya su fahimci wani abu."

Sai ta ɗan rage murya "Akan ke da Ibrahim ne ko?"

Wani numfashi Zahra ta sauke. A hankali tace, "Firdausi... zuciyata zata buga."

Firdausi ta juya da sauri tana kallonta. "Me ya faru?"

"Ibrahim zai kashe ni..." muryarta ta ƙarshe tana rawa.

Da sauri Firdausi tace, "Haba Zahra! Ki daina irin wannan maganar."

Hawaye suka cika idanun Zahra. "Wallahi bana jin dadin raina... tun jiya."

Ta ɗan cije lips ɗinta tana ƙoƙarin hana kukanta fita "Na fara jin tsoron abubuwan da nake gani da wanda bana gani..."

Nan take Zahra ta fara bata labarin komai.

Tun daga yadda suka dawo daga gidan Mama cikin so da kauna, yadda Ibrahim ya nuna mata kulawa har ta tausaya masa ta manta da damuwarta na ɗan lokaci akan reaction din Mama

"Mun dawo gida lafiya..." Zahra tace tana kallon gaba. "Har naji maybe ina overthinking ne..."

Firdausi bata katseta ba, sai kallonta take yi.

"Yana toilet ni kuma na tsaya a kitchen kafin na haura sama." Ta haɗiye wani abu mai nauyi a maƙoshi. "Da na shiga ɗaki... sai naga wayarsa na ringing."

"Hmm..." kawai Firdausi ta iya cewa

Zahra ta ce "An yi saving number ɗin da... 'Lovie Dovie.'"

Firdausi ta ɗan zaro ido. "What?"

Kai Zahra ta gyada a hankali.

"Da farko ma bansan me naji ba. Kawai zuciyata ta tsinke, har Call ɗin ya yanke sai kuma wani ya sake shigowa."

"Kin ɗaga?" Firdausi ta tambaya

"A'a... na kasa." Ta amsa

Ta share hawayen da suka zubo mata.

"Yana fitowa daga toilet ya sake ganin call ɗin. Wallahi Firdausi yadda ya tashi da sauri ya ɗauki wayar... sai ya mayar silent ya saka a aljihu."

Firdausi ta haɗe gira. "Then?"

"Ya fita daga ɗakin, shine abun daya bani mamaki"

"Ya dawo?"

Kai Zahra ta girgiza mata.

"Har ƙarfe goma sha ɗaya ban ganshi ba. Daga baya ma bacci ya ɗauke ni. Da asuba na tashi... har lokacin baya ɗakin."

"Subhanallah..." cewar firdausi

"Tun da muka shirya bayan dawowata gida, Ibrahim bai taɓa barina ni kaɗai a dare ba. Sai jiya..."

Muryarta ta fara rawa. "Da safe ma babu explanation. Babu inda ya ce ya je. Kawai ya shigo ɗaki kamar babu abin da ya faru."

Firdausi tayi shiru tana sauraronta.

"Bayan wani lokaci ma ya fita. Ni kuma na shirya zuwa school..." ta sauke numfashi. "Kawai naji ƙarar gate."

"Shi ne?"

"Eh. Na buɗe curtain naga yana fita da mota." Hawaye suka sake cikowa idanunta. "Wallahi Firdausi kamar an dasa ni a wajen. Ko sallama bai min ba fah, just imagine...."

Firdausi ta ɗan dafe kanta. "Ya Salam..."

"Shiyasa nace miki zuciyata zata buga." Zahra ta ƙara faɗa cikin kuka. "Bana son yadda nake jin kaina yanzu. Bana son tunanin da nake yi."

Firdausi ta kama hannunta. "Shhh... calm down."

"Ki gaya min idan ba wani abu bane me yasa zai fita haka? Me yasa zai ɓoye min wayansa? Me yasa zai kwana a waje?"

Shiru Firdausi tayi na wasu seconds kafin tace, "Kin tabbatar ba wata business issue bace?"

"Da ace haka ne ai zai gaya min." Zahra tace da sauri. "Ibrahim ba irin mutanen da suke waya da mace suna saving number da 'Lovie Dovie' saboda business ba."

Wani shiru ya cika motar.

Sai Zahra ta runtse idanunta tana kuka a hankali. "Firdausi bana jin zan iya ɗaukar wani ciwon zuciya daga Ibrahim..."

Firdausi tayi shiru na ɗan lokaci tana tunani, sannan ta juya tana kallon Zahra sosai.

"Pls kiyi kokari ki nemo number ɗin."

Zahra ta ɗan haɗe gira. "Number ɗin wa?"

"Wancan 'Lovie Dovie' ɗin."

Gabanta ya faɗi ta ce "Firdausi kar dai kiranta zaki yi?"

Firdausi ta ce da sauri. "No!!! Just find her number ki turomin immediately. Kuma kar ki bari Ibrahim ya sani."

Zahra ta gyada kai a hankali. "Amma me zakiyi da number ɗin?" ta tambaya cikin damuwa.

"Ke dai ki samo min ita." Firdausi ta bata amsa a takaice

Kai ta sake gyadawa.

Sai kuma ta sauke numfashi tace, "Firdausi ina zan kaiki yanzu?"

"Ki kai ni gida kawai."

"Toh."

Zahra ta juya steering tana canza hanya.

Dukansu suka yi shiru na ɗan lokaci, amma wannan karon shiru ne wanda dukkansu fadawa duniyar tunani suka shi

Firdausi na kallon Zahra lokaci zuwa lokaci. Yadda hannunta ke rawa saman steering ya tabbatar mata cewa kawarta tana cikin wani irin hali.

Firdausi ta ce "Zahra..."

"Hmm?" Cewar Zahra

"Kar ki fara conclusions yanzu."

Sai Zahra tayi murmushi mai ciwo. "Yaya ba zan yi ba?"

Firdausi ta sauke numfashi. "Saboda baki da complete answer tukuna. Kuma idan kika bari tunani ya rinjaye ki yanzu, zaki cutar da kanki ne."

Zahra bata amsa ba, kawai ta ci gaba da driving tana jin zuciyarta na mata wani irin nauyi da bata taɓa ji ba.

A haka Zahra ta kai Firdausi gida.

Kafin ta sauke ta, Firdausi ta sake riƙe hannunta tace, "Please ki kwantar da hankalinki. Kuma ki tuna abinda nace miki."

Kai Zahra ta gyada mata kawai. Ta sauka sannan suka yi sallama

Daga haka ta juya motarta ta nufi gida.

Tana shiga compound ta samu Farida zaune gefen flowers tana gyara su a hankali. Ganin Zahra yasa tayi saurin miƙewa tsaye.

"Ina wuni Hajiya."

"Lafiya," Zahra ta amsa a taƙaice.

Bata tsaya wata magana ba ta wuce ciki kai tsaye.

Yau ko baccin rana ma taji bata son yi. Wani irin cunkoso take ji a zuciyarta.

Kai tsaye ɗakinta ta wuce. Toilet ta shiga tayi wanka, sannan ta fito tayi sallah.

Bayan ta idar ne ta ɗauki magungunanta zata sha, sai kuma ta tuna cewa ko breakfast bata yi ba, a hankali ta sauke magungunan.

Sai ta sauka ƙasa ta ɗibo abinci kaɗan. Ko yunwar ma bata ji sosai ba, amma tasan dole ne ta ci saboda maganin. Bayan ta gama ci ta koma sama.

Maganin ta sha sannan ta kwanta akan gadonta.

Tana lumshe idanunta kuwa, nan take bacci ya ɗauke ta saboda gajiyar tunani da damuwar da ta cika mata zuciya.

Wajajen ƙarfe huɗu na yamma Zahra ta farka daga bacci.

Da ƙyar ta buɗe idanunta saboda yadda kanta yake mata nauyi. Amma first thing data fara yi shine ta miƙe ta nufi labulen ɗakinta.

Da sauri ta buɗe curtain ɗin tana kallon compound. Babu motar Ibrahim to her own surprise, abin ya bugi zuciyarta sosai.

Ta tsaya tana kallon wajen kamar zata ga motar ta shigo a lokaci guda, amma shiru.

Wani irin faɗuwar gaba taji, da sauri ta fita daga ɗakinta ta nufi nasa ɗakin dan tabbatarwa.

Tana shiga kuwa... babu shi, Komai a yadda ya bari yake.

A hankali ta juya ta koma ɗakinta, wayarta ta ɗauka hannu na rawa ta kira Firdausi.

Tana ɗagawa kawai Zahra ta fashe da kuka.

"Firdausi..." ta kira sunan cikin wani irin kuka mai cin rai.

"Zahra lafiya!" Firdausi tace a razane.

"Bai dawo ba..."

Rasa abin cewa Firdausi tayi ta ce "Wa?"

"Ibrahim..." ta faɗa tana kuka sosai. "Har yanzu bai dawo gida ba"

Firdausi tayi shiru tana sauraron kukanta.

"Kw... kwana biyu bayan mun shirya..." Zahra ke magana da ƙyar. "Da wuri yake dawowa... ko biyu bai wuce yake gida..."

Ta share hawayenta amma suka ƙi tsayawa.

"Amma yau... har yanzu baya nan."

"Shhh... calm down."

"Firdausi zuciyata zata tsaya wallahi..." ta ƙara faɗa tana kuka. "Ina jin kamar wani abu na faruwa a bayana."

Firdausi ta runtse idanunta tana tausaya mata sosai.

"Please ki daina kuka haka. Kin gwada kiransa ne?"

Kai Zahra ta girgiza duk da bata ganinta. "Bana son ya gane ina tracking ɗinsa."

"Okay... toh ki kwantar da hankalinki yanzu. Maybe yana office ne."

"Da ace office ne ai zai min magana..." muryarta cike da ciwo. "Tun safe babu call... babu message... babu komai."

Da ƙyar Firdausi ta samu ta lallabata.

"Listen to me," tace cikin tausasawa. "Kar ki bari tunani ya kashe ki kafin ki gano gaskiya. Ki nutsu farko." Firdausi tayi shiru, tasan kawarta tana cikin wani irin hali.

Saboda ita kanta ta fara jin tsoron yadda Ibrahim ke canzawa Zahra a hankali. Ya

Duk maganar da Firdausi ke mata, Zahra ko kaɗan bata ɗauka ba. Kuka kawai take yi kamar zuciyarta zata fito.

"Zahra ki kwantar da hankalinki mana... Amma ina....

"Firdausi wallahi bana jin daɗi..." ta faɗa cikin kuka. "Ina jin kamar zan haukace."

Firdausi ta dafe kanta. Tasan idan ta barta a haka, zata iya cutar da kanta da yawan tunani.

"Okay listen," tace cikin ƙoƙarin ɗauke hankalinta. "Ba mun gama plan ɗinmu ba ko? Zaki samo number ɗin toh..."

Sai Zahra ta sake fashewa da kuka.

Kamar ma maganar ta ƙara tunzura ta ne

"Firdausi ya ya kike so nayi?" ta faɗa tana sheshsheƙa. "Ni yanzu bana ma son ganin wayarsa..."

A nan Firdausi ta fahimci ba waya ce zata iya kwantar mata da hankali ba.

"Okay..." tace a hankali. "Ki kwantar da hankalinki. Zan sake kiranki."

Bata jira ƙarin magana ba ta katse kiran.

Nan take ta miƙe daga kan gadonta ta fara shiri cikin sauri.

Tana gamawa ta fito parlorn.

"Mama zan je gidan Zahra," tace tana ɗaukar handbag ɗinta.

"Lafiya kuwa?" Mahaifiyarta ta tambaya.

"Eh... tana ɗan jin babu daɗi ne."

"Toh Allah ya sauƙaƙa."

"Ameen."

Daga haka ta fita da sauri ta nufi gidan Zahra, zuciyarta cike da tausayi da damuwa kan halin da kawarta take ciki.

Bayan mai gadi ya leƙo ya gane Firdausi ce, sai ya buɗe mata gate ɗin.

Da sauri ta shiga ciki.

A parlorn ƙasa ta haɗu da Farida. Bayan sun gaisa, Firdausi bata tsaya wata magana ba ta wuce sama kai tsaye zuwa ɗakin Zahra.

Tana buɗe ƙofar kuwa ta shiga.

Zahra dake zaune bakin gado ta ɗaga kai dan ganin wanene.

Da ganin Firdausi, nan take ta miƙe da sauri ta ƙarasa wajenta ta rungumeta.

Ba kaɗan ba Firdausi tayi mamakin ganin har lokacin Zahra na kuka. Idanuwanta duk sun kumbura sun yi ja.

"Ya Salam Zahra..." ta faɗa tana riƙeta. "Har yanzu kina kuka?"

Zahra ta ɗago tana share hawaye. "Ba kinga har ƙarfe biyar yayi ba? Bai zo ba.... Muryarta na rawa ta karasa,

"Nasan suna tare ne..."

Firdausi ta ɗan ja baya tana kallonta. "Wa da wa?"

"Ibrahim da ita mana..." ta faɗa tana ƙoƙarin hana sabon kukan da ke tasowa. "Wallahi Firdausi zuciyata na gaya min haka."

"Haba mana..."

"Tun safe fa!" Zahra ta katseta. "Tun safe babu call babu message. Ni ma bansan inda yake ba."

Firdausi ta kamo hannunta suka zauna bakin gado.

"Ki nutsu ki saurare ni."

Kai Zahra ta girgiza. "Bana iya nutsuwa."

"Okay... kin gwada kiransa?"

"A'a." Ta ce da sauri

"Why?"

"Saboda bana son ya ga kamar ina binsa ne." Ta runtse idanunta. "Amma kuma bana iya daina tunani."

Firdausi ta dafe kanta a hankali. "Zahra kina cutar da kanki haka."

"Me kike so nayi?" ta tambaya cikin kuka. "Tun jiya nake jin kamar bana cikin hankalina."

Firdausi ta rungumeta kaɗan tana shafa bayanta.

"Shhh... please ki kwantar da hankalinki."

Sai Zahra ta ɗago tana kallonta da idanuwan da suka kumbura saboda kuka.

"Firdausi idan har Ibrahim ya koma wajen wata mace..." muryarta ta karye. "Wallahi zan mutu."

Firdausi ta gama ruɗewa gaba ɗaya. Ta rasa wani tunani zata yi.

Ta sani ƙwarai Ibrahim na cutar da Zahra, amma bayan duk abinda ya faru tsakaninsu not long ago na kama shi da wata.... shine zai sake komawa irin halinsa?

Wani numfashi ta sauke tana kallon kawarta dake kuka kamar ranta zai fita.

"Zahra..." ta kira a hankali.

Ta ɗago tana share hawaye.

"Yanzu idan ya zo ya ga idanunki sun yi ja zai san saboda shine kika yi kuka. Kinga zai ji daɗi."

Kai Zahra ta girgiza. "A'a wallahi ba zai ji daɗi ba..."

"Ki bar wannan." Firdausi ta katseta. "Namiji idan ya ga mace na rushewa saboda shi, wani lokacin sai ya ƙara jin yana da power akanki."

Zahra tayi shiru tana sauraronta.

"Sannan secondly..." Firdausi ta kama hannunta. "Ciki jikinki yana buƙatar ki kwantar da hankalinki. Wannan yawan kuka da tunani bai Kama ce ki ba a halin yanzu"

Wani sabon hawaye ya sake zubo wa Zahra.

"Ki duba yadda kike rawa..." Firdausi ta ƙara faɗa cikin tausasawa. "Wallahi kina bani tsoro."

"Na kasa controlling zuciyata ne..." Zahra tace da ƙyar. "Ina son Ibrahim sosai Firdausi."

Firdausi ta runtse idanunta na ɗan lokaci.

"Nasan ki na sonsa. Kowa ma ya sani. Amma ki tsaya ki fara son kanki farko ma"

Sai Zahra ta sunkuyar da kai.

Firdausi ta ɗan matsa kusa da ita. "Yanzu tashi ki wanke fuskarki. Kar ya zo ya same ki haka."

"Bana ma son ganinsa..."

"Ko baki so ba, dole ki haɗa kanki." Firdausi tace. "Ki nuna masa kina da ƙarfin zuciya."

A haka Firdausi ta zauna tare da Zahra har suka yi sallar Maghrib, tana ƙoƙarin lallashinta da rage mata yawan tunani

Bayan sun idar, har yanzu Zahra ba ta huce ba. Idanunta sun kumbura, zuciyarta kuma cike take da wani nauyi mai wuyar kwatance

Can kuma sai suka ji ƙarar buɗe gate.

Firdausi ta yi saurin leƙawa ta window. Sai ta juya a hankali tana kallon Zahra.

"Wallahi shi ne..."

Zahra ta ɗago kai da sauri. "Firdausi..."

"Ni kam wallahi zan tafi." ta faɗa cikin sauri tana ɗaukar jakarta da wayarta. "Please kar ki yi kuka, kar ya gane."

Zahra ta miƙe da sauri ta nufi toilet ba tare da ta ce komai ba, tana ƙoƙarin ɓoye kanta daga yanayin da take ciki.

#jiddatulkhyar writes #08110615256