
Post
KOMAI YA YI FARKO HAUSA NOVEL 4
..... she started to come out, smiling and said; "Hello, Humaira, the king of work." She smiled back at her, and she crouched down to greet her. Mama Lantana looked in the middle of the house where she was cleaning, and the bowls were overturned in the basket, she saw the heat from the side of the stove, and then she saw the water boiling on the fire, she just nodded and said; "God bless you Humaira, you should have raised your younger brother to encourage you with some work, but you did everything alone." She smiled and said; "There is not much to do, Mom." Koko sat in the big plastic bag, covered it with a lid, looked at Mama Lantana, and said; "Here's Mom's food." "Take yours and eat it. When the Falmatas come out, they will eat theirs." Said Mama Lantana who was sitting in the squatting chair outside the kitchen. Humaira shook her head and said; "I just woke them up." Mama Hafsatu went to her room, said hello and opened the curtains and entered. Hafsatu's mother was sitting on the carpet, she was drinking coffee and she was singing, when she greeted her, she said; "I will wake them Bilki and we will eat." Hey, Mama Hafsatu shook her head and said; "Get up and let them hear your
KOMAI YA YI FARKO
PAGE 4
Cikin dare HUMAIRA ta farka, ta ganta kwance akan gadon Innarta, ta luluɓeta da bargo, ita kuma tana kan darduma tana sallah, tocin wayarta ya ba wa dakin ɗan haske, miƙa ta yi, ta ɗan sosa idonta, A hankali ta sauka daga kan gadon, ta ɗauki wayar Inna dake gefenta a ƙasa yana haska ɗakin. Buɗe ƙofar ɗakin ta yi, ta ajiye wayar daga gefe yana haska tsakar gida, alaula ta ɗora, sannan ta koma ɗaki. A gefen Inna ta shimfida dardumanta ta kabbara Sallah, a lokacin da ta iddar har Inna ta kammala addu'o'inta ta kwanta ko, Addu'o'i ta yi a daren sosai, tana roƙon Allah ya ba ta ikon cika burinta, ya kuma ƙara mata dangana, ya ba ta damar fuskantar rayuwa a duk yadda ta zo mata, a kan darduman ta ƙara bigewa da bacci, bacci da sai sallar asuba ce ta farkar da ita.
Bayan ta idar da sallar asuba, ta fito tsakar gidan ta kama aikace-aikacen gida, sannan ta ɗora musu ɗumamen shinkafar jiya da suka ci da daddare, ɗayan murhun kuma ta ɗora ruwan dama kamu. Mama Lantana ce ta fara fitowa, tana murmushi tace; "Sannu Humaira Sarkin aiki." Murmushin itama ta mayar mata, ta ɗan tsuguna ta gaisheta. Mama Lantana ta kalli tsakar gidar dake share tsada, da kwanukan da aka kife a basket, ga ɗumame daga gefen murhu, sannan ga ruwa na tafasa a wuta, sai ta kada kawai, tace; "Allah ya yi miki albarka HUMAIRA, ai da kin tashi ƙanen ki su taya ki da wani aiki, amma kika yi komai ke kaɗai." Murmushi ta yi, tace; "Aikin babu wani yawa ai Mama."
Koko ta dama a babban roba, ta rufe da murfi, ta kalle Mama Lantana, ta ce; "Ga abincin Mama."
"Ki ɗeba naki ki ci, idan su Falmata sun fito za su ci nasu." Cewar Mama Lantana dake zaune a kujerar tsuguno dake daga wajen kitchen ɗin.
Girgizar kai Humaira ta yi, tace; "Bari dai na tashe su."
Ɗakin Mama Hafsatu ta tafi, ta yi sallama sannan ta yaye labulen ɗakin ta shiga. Mama Hafsatu na zaune akan darduma, tana jan carbi tana gyangaɗi, gaisheta ta yi, sai ta ce; "Zan tashe su Bilki ne mu ci abinci."
Kai Mama Hafsatu ta gyaɗa mata, ta ce; "Ki tashe su ƙilla su ji taki don ni kam babu yadda ban yi da su su tashi su taya ki aiki ba, amma sai ƙara duƙunƙunewa suke yi a cikin bargo."
Bargon da suka lulluɓu da shi, Humaira ta cire, mari ta fara dalla wa Imrana a cinyar, a firgice ta tashi tana zazzare ido, sai ta dalla wa Bilki ma nata, ihu ta yi, tace; "Mama na ce miki kai ɗaya fa zan yi." Buɗe idon da za ta yi ta gan Humaira ce a tsaye kanta, sai ta sosa gashinta dake wargaje, tace; "Ina kwana Ya Humai." Tana sosa cinyarta da ta sha mafi, hararar su Humaira ta yi, tace; "Za ku tashi ne ko yaya?"
A gaba Humaira ta saka su Bilki suka fita daga ɗakin. Tray ta ɗauko ta zuba musu abincin suka ci suka yi naƙ, Bilki da Imrana suka kai kwanukan wajen wanke-wanke, Humaira kuma ta ɗebi ruwa ta shiga wanka.
Ƙarfe goma daidai Humaira ta shirya tsaf cikin uniform ɗin islamiyyar asabar da Lahadi riga da wando blue sai farin hijjabi da ya sauka sosai, rabonta da islamiyyar tun ranar da Kamis ya yi mata tonon asiri a gari, amma yau ta kuddiri aniyar ko me mutane za su faɗa ba zai hanata yin rayuwarta yadda ta tsara ba, neman ilimi shine priority ɗinta a rayuwa, don haka ko menene ya samu rayuwarta ba ta tunanin za ta iya watsar da neman ilimi ba. Inna dake zaune daga bakin gado tana kallon Humaira dake sanya safa a ƙafa, tace; "Masha Allah, Humairata kin yi kyau sosai."
Murmushi Humairan ta yi, ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta, tana appreciating kyaun halittar da Allah ya yi mata, halittar ta daban ne da na sauran mata, she's just 17 amma tana hade cib abinta, tana da diri mai kyau da ko cikin hijjabi zaka fahimci hakan, Tana nan fara sol da ita fatarta fresh sai sheƙi ya ke, daga gaban goshinta kuma gashine baƙi mai tsantsi har wadda daga kallo zaka fahimci ita ɗin mai gashi ce, tana da full eyebrow baƙi ƙirin mai kyau, tana dogayen eyelashes da suka ƙara fito da kyaun dara-daran idanunta da suke nan fari ƙal, sai ɗan ƙaramin bakinta kamar ta baby, she's average in height. Murmushi ta ƙara sakar wa kanta, a zuciyarta tana faɗin; "Ni ba butulu bace, dole na gode maka ya ubangiji na bisa ga wannan kyaun halittar da ka yi min, Alhamdulillah." Sai ta kalli Inna, tace; "Duk kyaun Humaira ba za ta kama ƙafar Innarta ba."
Inna tace; "Wannan kuma zance kike." Ta miƙawa Humaira niƙab ɗinta tace; "Ɗaura ki tafi kar ki yi latti, Allah ya tsare ya dawo dake lafiya Humairata."
Humaira da ta gama ɗaura niƙab ɗinta, tace; "Aameen Innar Humaira."
Tunda Humaira ta fita daga gidansu ta lura da yadda mutane ke binta da kallo, amma sai ta yi kamar ba ta lura ba ta cigaba da tafiyarta cikin nutsuwa. Despite niƙab dake fuskarta duk wanda ya riga da ya santa sai ya ganeta, saboda yanayinta ba mai ɓoyuwa bane, da kuma yadda take tafiya ɗaiɗaiya kamar hawainiya, idan baka fahimceta ba zaka ɗauka yanga take amma nature ɗinta ne hakan.
Tana shiga ajinsu a islamiyyar, ta zauna a kujeransu da suka saba zama da Farida, tana jin yadda ƴan ajin suka fara ƙus-ƙus tunda ta shigo, ongoing ɗinsu ta yi, ta ɗauki ƙur'aninta ta fara bitar haddar da aka ba ta. Tana cikin karatun ta ji ƴan seat ɗin bayansu suna hirarta, ɗayar mai suna Falmata tana ba wa ɗayar labarin wai daman bin maza Humairar take yi sai ta rinƙa wani saka dogon hijjabi tana rufe fuska da niƙab kamar ta Allah, wannan karon ma Allah ne ya toni asirinta, duk yadda Humaira ta so ta kawar da hankalinta daga jin hirarsu, amma ta kasa saboda ba a hankali suke maganar ba, they were talking to her hearing. Miƙewa ta yi ta fita daga ajin saboda malaminsu bai shigo ko ba, kusan cin karo suka yi a bakin ƙofa da Farida, ja da baya Farida ta yi, ta ce; "Humaira..." Ta ɗan kalleta ta ce; "Daman za ki zo?" Humaira ta raɓa ta gefenta, ta yi gaba, Farida ta bi ta a baya tana tambayarta; "Me ya faru?"
Massallacin dake gefen classes ɗinsu suka shiga, Humaira ta kwance niƙab ɗinta ta fashe da kuka, Farida ta daafa kafaɗarta, tace; "Haba ƙawata, kukan na menene? Ba dai maganganun ƴan ajin kika ji ba kike wannan kukan?" Ɗago kai Humaira ta yi, ta kalleta, tace; "Tun kafin na zo ake maganata kenan?"
Gyaɗa kai Farida ta yi, tace; "Ai kin san dole ƴan gulma su yi sana'ar, munafukai ma har sauya ainahin maganar suka yi, amma ina tunanin tunda kika samu courage ɗin zuwa kamar kin shirya yin kunnen uwar shegu ne akan duk abinda za ki ji. Humaira..." Humaira ta ɗago ido ta kalli Farida, Farida ta riƙe hannunta cikin ba ta kwarin gwiwa ta ce; "Is time for you to be deaf and dumb, duk abinda za ki ji ki yi kamar ba ki ji ba, sannan you don't owe anyone an explanation, wasu za su iya zuwa su yi miki tambaya akan abinda ya faru don gulma ba wai don su taya ki jimami ba, don haka zip your mouth, kar ki faɗawa kowa komai."
Niƙab ɗinta Farida ta ɗaura mata bayan ta goge mata hawayenta tas, tace; "Be strong komai zai wuce, Tashi mu tafi aji." Ta taimaka mata ta tashi suka koma ajin. Malamin su ma da ya shigo ajin, satar kallon Humaira ya rinƙa yi har aka tashi, he still can't believe maganar da ke yawo a gari akanta, Humaira da duniya ta ba ta shedar kamilalliyar ƴace, wacce ta ba wa neman ilimi muhimmanci sosai a rayuwarta, tunda ya fara jin jita-jita a gari yake mata addu'ar Allah ya wanketa.
Malam Ɗalha na fita daga class, ƴan matan ajin suka zagaye seat ɗinsu Humaira, Babbar ajin mai suna Jamila, itace ta bi Humaira da matsiyacin kallo, tace; "Ustadha Humaira ashe abinda ya faru kenan? Kai Allah ya kiyaye na gaba, Amma ya akayi hakan ta faru ne?" Farida ta rinƙa binsu da kallo zuciyarta na tafarfasa kamar ta janyo Jamila ta wanka mata mari, amma she's trying hard kar ta saka baki, she want to learn how to speak for herself.
"Uhmm? muna sauraron ki." Jamila ta katse shirun.. Humaira da ta gama tattara takardunta, ta saka a jaka ta zuge zip ɗin, ta tashi tsaye, tace; "Ban son na yi maganar." Ta bi ɗan space da suka bari za ta fita, Jamila ta ja jakarta, cikin isa tace; "Abinda dai ake faɗa a gari shine gaskiya, tunda gashi kin kasa faɗar komai."
Humaira ta juyo, ta kalle Jamila a cikin ido, firmly ta ce; "Kina da damar yadda da duk abinda kika ji, ke wannan ta shafa." Ta toshe jakarta daga hannun Jamila, fuuu ta fita daga ajin Farida na bin ta a baya. Ƴan ajin suka bi su da kallo, wasu daga cikinsu na Allah wadar da hali irin na Jamila da ƙawayenta, ace babban abu ya sami ɗaya daga cikinsu su ɗauke shi abin farinciki, amma babu wacce ta yi gangancin yi wa Jamila magana saboda itace babbar ajin kuma babanta hamshaƙin ɗan kasuwane, hatta wasu malamai tsoron shiga harkarta su ke.
Su Humaira na fita daga ajin ta sauke numfashi, don Allah kaɗai ya san irin jarumtar da ta yi har ta iya faɗawa Jamila abinda ta faɗa, Farida ta yi mata thumbs up, tace; "Kin yi ƙoƙari ƙawata, I never saw this coming."
Guntun tsaki Humaira ta ja, suka shiga Masallaci. Sallar Azahar suka yi, sannan suka fita suka nufi gida, adaidai ƙofar gidansu Humaira suka tsaya, Farida ta ce; "Gobe zan biyo ta nan sai mu tafi tare."
Humaira da ba ta mood ɗin magana sosai tace; "Allah ya kaimu." A takaice, sannan ta shiga gida, Farida kuma ta ƙarasa gidansu.
Humaira na shiga gidan ta ji ko ina shiru, ba ta yi mamaki ba don a lokuta irin haka ahalin gidan sukan yi baccin rana zuwa lokacin sallar La'asar, ɗakin Mama Hafsatu ta fara leƙawa don wasu lokutan Imrana da Bilki ba su baccin, ɓarna suke yi a lokacin da kowa ke bacci, tana shiga ɗakin kuwa ta iske su da robar sugar a tsakiyar gado suna kashewa, Mama Hafsatu kuma tana kwance a darduman da ta yi sallah tana bacci. Saɗaf-saɗaf Humaira ta yi sanɗa ta shiga ɗakin, suna ganinta Bilki da ta fi Imrana wayyo ta yi saurin ɓoye robar sugan a bayanta, Humaira ta ƙarasa zuwa bakin gadon ta zauna, Imrana dake zazzare idon rashin gaskiya tace; "Sannu da dawowa Ya Humaira." Bilki kuwa murmushi ta ƙaƙalo, trying hard not to look suspicious, itama ta yi mata sannu da zuwa. "Fito da abinda kike ɓoyewa." Humaira ta faɗa ba tare da ta amsa sannun da suka yi mata ba, Imrana ta fito da gorar sigar kamar za ta fashe da kuka, robar Humaira ta ƙarba, ta ɗan yi dube-dube a gaban mirror ɗakin, ta ɗauki wani leda, sigar ta ɗan zazzage a leda, ta miƙawa su Bilki sauran, tace; Idan Mama ta kama ku babu ruwana." Sannan ta fita daga ɗakin. Bilki ta harare Falmata, tace; "Kin fiye tsoro, Ni na san babu abinda Ya Humai za ta yi mana tunda itama tana lasar sugar Inna."
Falmata tace; "Ai Ya Humai tama fi mu shan zaƙi." Dariya suka yi harda tafa hannu.
Humaira na shiga ɗakinsu ta iske Inna na bacci, rataye jakarta ta yi a wani ƙusa da aka buga a jikin bango don rataya jakukkuna, kular da ta gani a gaban mirror ta buɗe, ɗan wake ne a ciki da kulin maggi da yaji a gefe, a gabar mirror ɗin ta zauna, ta haɗa ɗan wakenta ta fara ci, kaɗan ta ci ta ture kular don ba ta kasance mai ci sosai ba, sai ta shimfiɗa sudaden katifarta ta kwanta itama.
Cikin bacci ta ji Inna na mita; "Tashi ki yi sallah, na hana ki kwanciyar wannan suɗaɗen katifar kin ce ba za ki ji ba ko, ki yi duk abinda kika gan dama, amma ranar da za ki ce min jiki na miki ciwo zaki gan abinda zan yi miki."
Zumɓura baki Humaira ta yi, ta tashi ta naɗe katifar, tar̃4 tura shi a ƙarƙashin gadon Inna, tana shan ƙamshi ta fita daga ɗakin don yin alaula, Humaira ba ta son ana tashinta a bacci da masifa. Alaula ta yi ta zo tayi sallar La'asar, tana idarwa ta fito don taya Mama Hafsatu tuwon dare.
https://chat.whatsapp.com/CGm8zTMQDDO1e9sf3BmDKQ?mode=hqctcla