Kenza eBookz
Cover art for HIYAAM  HAUSA NOVEL PAGE 2

Post

HIYAAM HAUSA NOVEL PAGE 2

.....yes, one part of his teeth are all eaten, and the rest are decorated with walnuts, they are red when talking and the smell of walnuts comes out, the doors of his house are locked with his four wives, his children, and his grandchildren like peanuts because of the pain of the number they have. His house is like that, like life in a barracks. "You put Iftihal in this lottery that Alhaji Baita made for you, you are looking at how you have combined friendship with poverty" said Dahe, throwing the card on the ground with a malicious smile. Really, Daada and poverty are like twins, they came from the same mother, either he saw the end of this poverty, or the poverty saw the end of Daada and took him to a place of no return if he died. Seeing that Daada was silent, he was smoking his cigarette, he put away the cards they were playing, and Malam Dahe put his hand to Daada's shoulder and shook it, a sign of confidence in his decision, which is not a fraud in trust, he said "Keep it in your heart, your daughter is your investment" "That's her benefit" He repeated while bowing his head, a sign of confirmation of his words to Daada. "Women's children are a treasure, an asset to keep a sec

Standalone post5,475 words

*H I Y A A M*

Page 2 Bright pens

Yota/001

Dedication to Nazeefah Sabo Nashe

Bai sani ba ko yana da gwaggwaɓar riba a sanya ɗiyarsa Ifti a cikin cacar, idan ma ya barta mene amfaninta da kuma tasa ribar, banda galaulawar kula da ita, shi ƴaƴa mata a marasa amfani yake kallon su, bai taɓa saƙawa a ran shi suna da wata rana a wajansa ba. Gwara ya sata a cacar ya ciyo Miliyan ashirin a kanta, bashi da wata asara.

"Zan saka Ifti a cacar na ci Miliyan ashirin, ita kuma Ana zan kai ta wajan wani Alhaji da zata dinga kwana a can yana bani kuɗi"

Ya yi zancen a ƙasan zuciyarsa.

"Idan bai ci cacar ba, hakan yana nuni da cewa zai damƙa Ifti a hannun Alhaji Baita?"

"Ko kuma aikin gida zata dinga masa, tunda matansa huɗu yana haddace dasu a kan shi" ya yi shiru yana nazari, me gobe zata haifar. Ifti ta yi ƙanƙanta da auren Alhji Baita ya yi mata tsofa tuƙuf, to me zai yi da ita?

Bashi da masaniyyar yadda rayuwar Ifti zata kasance idan tsohon ya mallake ta a caca, domin mutum ne me shekaru 62 a duniya, kaso ɗaya daga cikin haƙoransa duk a cinye suke, sauran kuma goro ya yi musu ado da lalle, sun yi jawur ko magana ya yi warin goro ke fita, ƙoƙofin gidansa, kulle suke da mata huɗu cif, yaransa, da jikokinsa kamar gyaɗa saboda azabar yawan da suke dashi.

Haka gidansa yake, kamar rayuwar bariki.

"Ka saka Iftihal a cacar nan da Alhaji Baita ya yi maka ta yi, kana kallon yadda ka haɗa zumunci da talauci dai" cewar Ɗahe yana cilla kartar a ƙasa da murmushin ƙeta

Ƙwarai da gaske, Daada da talauci kamar tagwaye ne, suka fito daga mahaifa guda, ko dai yaga bayan talaucin nan, ko kuma shi talaucin yaga bayan Daada ya kai shi zuwa inda ba'a dawowa idan anje.

Ganin Daada ya yi shiru, yana ta jan sigarin hannunsa, ya ajjiye kartar da suke bugawa, ya saka Malam Ɗahe miƙa hannunsa zuwa kafaɗar Daada ya jijjigata, alamar tabbaci akan shawarar da yake basa, wacce babu zamba cikin aminci a tattare da ita ya ɗora

Da "Ka saka a ranka, ɗiyarka ce jarinka"

"Amfaninta kenan" Ya nanata yana jinjina kai, alamar tabbacin maganarsa ga Daada.

"Su yara mata dukiya ne, kadarar rufawa kai asiri, ka amince ka saka Ifti a cikin cacar nan, sai ka ga ta ciwo maka maƙudan kuɗaɗe kuma yanke talauci wlh"

Garba ya riƙe zancen daga wajan Malam Ɗahe, yana sake yi wa Dadaa ingiza me kantu ruwa wajan sanya ɗiyarsa mai hankali da nutsuwa da kamala, kyau da tsarin halitta. Dadaa ya yi shiru yana tunani, idan abin da yake buƙata ne a zuciyarsa, bai shige kuɗi masu ɗumbin yawan da zai iya sake dulmiya su a cikin cacar ya sake cin ninkin su ba, yana son kuɗi fiye da duk wani abu da yake cikin wannan duniyar, ƙamshin jaka guda kaɗai dagula masa lissafi yake yi balle yaga fara ƴar shehu, mulmulalliyar dubu ɗaya, ko notikan kansa basu kunce ba, da ƙyar yake iya hattama nutsuwarsa ya daidaita zuciyarsa gudun murna da zumuɗi kar su yi masa illar da zai gaza ganin bayan dubu ɗayan. Ya dube su, yana nazari.

Yana buƙatar lokaci,lokacin da zai tantance mene yafi muhimmaci a gare shi, a tsakanin ɗiyarsa Iftihal da dukiyar da ake magana akan ta, sai ya nutsu, yadda zai tantance

Me ake nufi da zuri'a ta ƴaƴa mata, Me ake nufi da arziƙi masu rufin asiri.

"Ina buƙatar lokaci"

Ya furta yana miƙewa tsaye.

"Wanne lokaci kuma kake buƙata, ƴa dai taka ce, kana da iko da rayuwarta, kamar yadda miliyan ashirin ɗin nan suke jiranka"

"Malam Ɗahe, a bani lokaci, bari zan je na dawo sai mun haɗu zuwa tsakiyar dare ko safiya ko kuma war haka yammacin nan"

Wani irin maƙetacin murmushi Alhaji Baita yake wanzar dashi a fuskarsa, murmushin da indai a kaga ya yi a cikin abu biyu ne za'a samu guda, wanda ya zama zakarar gwajin dafi. Ko dai budurwar zuciyarsa ta hango masa kyakkyawar matashiya wacce zai huta ya more tsofansa a jikinta, ko kuma an yi masa batun caca, me kawo ruwan kuɗi.

Musamman da idan ya rufe idanunsa yake hasaso tsanain kyawun fuska irin na Iftihal

Da faffaɗan ƙugunta,wannan mazaunan daya zauna das, ta cikin hijabin daya kwanta a bayanta ya hango hakan. Yabi Daada daya shige ya bar wajan da kallo, tare yin kwana ya ɗauke idanunsa yana kallon Garba ya ce

"Garbati"

Cikin rawar jiki Garba ya amsawa Alhaji Baita da murmushi a fuskarsa

"Ni kaɗai na ga yarinyar nan ƴar wajan Daada, ko kaima ka ganta don Allah?"

"Alhaji wai Iftihal kake nufi? Daman baka da labarin tagwayen yaransa, Ana da Iftihal? Ai kaf unguwarsu babu yara masu kyawun ɗiyoyin Daada" Garbati ya shiga labartawa Alhaji Baita bayani akan su Ana da Iftihal "Ita wacce ta shige ita ce Iftihal ana ce mata Ifti, ɗayar ta gida kuma sunanta Haleeym ana ce mata Ana, kyawawa dasu"

Wani yawo ne ya taro a ƙasan maƙoshin Baita cike da zalama ya ce "Kasan da yarinyar nan baka taɓa bani labarinta ba?"

"Alhaji tuba nake, na gansu ƙanana ne yanzu fa suke aji uku na Sakandire"

"Irin waɗannan sabbin ƙinƙisar nake so, a ganin farko yarinyar nan ta dagula mini lissafi sai tsiyaya nake ta yi ta ciki"

Garbati ya shanye mamakinsa, wajan yin amfani da tafin hannunsa zuwa bakinsa ya rufe, ya sauke muryarsa a ƙasa kamar wanda wani zai ji me zai faɗawa Alhaji Baita ya ce "Ko zaka ƙara miliyan goma akan ashirin ɗin nan, yadda za mu samu damar shawo kan Daada ya afka cikin cacar, ina da yaƙini kai zaka lashe tunda ka fisa iya yin wasan nan nesa ba kusa ba, idan ka cinye sai ka yi gaba da ƴarsa ka more abinka, amma wani hanzari ba gudu ba, ka rufe ƙofofin gidanka, kar wankin hula ya kai mu zuwa dare, babu abin da ya rage maka na jerin ɗakuna huɗun nan sai dai ka haƙura" da wani irin yanayin da yake nuna Alhaji Baita yaje ƙarshe, irin wa'adin da ba zai iya tausasa zuciyarsa har ya gamsar da ita akan ta yi haƙuri da Ifti ba, ya ce

"Sai na buɗe ƙofa ɗaya, ka ga an samu sarari zaman Iftihal a ciki ko?'

Ya yi furucin yana kallon Garbati.

Caraf Garbati ya ce "Wannan ma ya yi"

***

Duk yadda Ifti ke sauri kar Babban yaya ya rigata cimma isa gida kamar yadda idanunsa ya nuna gargaɗi a gare ta, tafiya take yi cikin ɗan karsashin da ya yi mata saura a matsagaicin jikin nata, ta na yi tana juyawa ko Daada ya biyo bayanta, sai taga babu komai dake biye da ita sai ƙurar iskar bazarar dake tashi, a haka ta dinga bin jigin bango tana gujewa kwatocin lungun data shigo cike da taka tsantsan, kamar bangon da take bi zai tsake ta shige ciki, tana karyawa lungun da zai kai ta gida, tun a bakin hanyar ɗaya lungun wanda ya kasance yana da mahaɗa biyu ta hango shi yana tafiya, kamar baya son takawa, idan ya cire ƙafa ɗaya sai ya mayar da ɗaya, hannunsa duka biyun ya adana su cikin aljihun wandonsa, hular tsakin daya saka ya ɗan karkatar da ita zuwa gefe guda a kan.

Buɗewar farar manyan idanunsa, da yadda ƙwayar idanun ta juya a cikin gurbinta, ya bawa Ifti tabbaci yake bata akan zai ci ubanta idan ya rigata ƙarasawa cikin gidan.

Sai ta ƙarawa tafiyarta sauri, wuf kamar iska ta ƙarasa shigewa da gudunta tana haƙi.

"Ass... Assalamu alaikum"

"Wannan gudun ke kuma na mene? Gudu kina ɗiya mace haba ƴar albarka irin arziƙi a bari don Allah"

Innti ta faɗa bayan ta amsa sallamarta.

"Wallahi Babban yaya na gani"

Ta ce da ƙyar tana juya idanunta, sai kuma ta zare hijabin jikinta ta rataye saman igiya tare da ƙarasawa kusa da Innti dake bakin murhu tana tuƙa towon masara. "Barka da gida Innti, kawo na ƙarasa miki aikin ki wuta kin ji uwata?" Innti ta girgiza kai ta ce

"Jeki abinki ki huta ƙasan bishiya kafin a kira sallar magariba ku tafi makarantar dare ko"

"Allah sarki uwata, Ubangiji Ya yi mini arziƙin da za ki huta, Allah Ya kula mini dake Sahibata" murmushi kawai Innti ke yi.

"Mutuniyar abin ƴar haka ne? Innti kawai kika gani a taskar gidan ashe?" Cewar Jadid

"Tuba nake Yaa Jadid"

Ta ce tana ƙarasawa ƙasan bishiyar da yake zaune saman tabarmar da Ana ta yi bacci akai, labari sosai Ifti ta shiga bawa Jadid suna tafawa kamar ba yayanta ba.

"Sannu da dawowa yaya"

Suka haɗa baki ita da Jadid wajan faɗa suna daidaita nutsuwarsu, jinjina masu kai kawai ya yi sanda ya shigo ɗin, a hankali kuma ya durƙusa daidai inda Innti take yin aiki yana ɗan lumshe idanunsa saboda hayaƙi, ta juyo ta kalle shi, shima ya ɗan kalle ta, da body language ya yi mata magana sai ta ce "Sannu da hanya yaya, kaga ka riga Jaheed shigowa yau, shima na san yana hanya duk inda yake, wataƙila bai kammala sallamar mutane ba, tunda uban gidan nasa ya ce kamar ya yi tafiya shi kaɗai ne a katin yau"

Shiru Babban yaya ya yi.

Da nutsuwa kuma ya miƙe ya shige cikin ɗakinsu, wanda suke kwana su uku a ciki.

"Innti wai ina Mahaɗita ne?"

"Wai Shalelen Innti?"

Maganar Jaheed ta riga shi shigowa cikin gidan, ya ƙarasa maganar sanda yake durƙusawa a kusa da Innti cike da ladabi ya ce "Sannu da aiki Innti" cikin kulawa ta amsa masa "Yanzu nake maganarka yaron kirki"

"Sai gani ɗan halak yaƙi ambato"

"Ma sha Allah, Allah Ya yi muku albarka ya kare ku daga dukkan sharri da abin ƙi"

"Amin"

Da ita suka amsa.

"Innti wai ina Mahaɗita?"

"Sannu kashin awakai, tana cikin ɗaki kin san yau da miskilanci ta tashi, gashi ana abokin gaban nata, ƙato da kwat" inji Jadid.

Dariya sosai Jaheed ya yi kafin ya ce

"Tuwo da miyar kuka"

Duk kiran da Ifti ke yi wa Ana ƙin fitowa ta yi, sai da aka kira sallar magariba sannan ta fito tana kame fuska taƙi yi wa kowa magana, tana shirin ɗaukan buta ta ji an zabga mata ranƙwashi a kanta, zafi da raɗaɗin da ta ji ya sauka har tsakiyar ƙwaƙwalwarta, yatsun ƙafafuwanta suka shiga rawa da kakkarwa, jikinta ya dinga tsuma kamar ya watsa mata ruwan sanyi, da wani irin rawar jiki ta ɗago har wani ruwa ne yake kwanciya a cikin manyan idanunta wanda suka samu surki da wata zaiba, blue- blue haka cikin idanun Ana suke, kodayaushe kamar an yi mata ado da kwalli haka suke nuna wa, saboda wani ɓaki siriri daya zagaye ƙasan idanunta da saman idanun wanda ya ƙarawa ƙwayar girma wai da aniyya, girmansu ya yi daidai da tsarin zagayyiyar fuskarta. Ganin Babban yaya tsaye da buta a hannunsa ya saka ta yi sak.Curarriyar girarta ta tattare waje guda.

Ta kafe shi da idanun da lokaci ɗaya suka fara surkawa, gefenta ya bi ya shiga banɗaki abinsa ba tare daya sake bi ta kanta ba, Ana tabi hanyar da yabi da kallo.

Ruwan daya taro a cikin kwarmin idanunta ta haɗiye su, tare da mayar dasu ta hana su zuba a saman fuskar da babu tabo ko guda.

Butar ta saki ruwan ya mamale ta shige ɗaki abinta, sai da duk suka fita zuwa masallacin su uku, kana ta fito kanta babu kallabi ta shige banɗaki, a bakin banɗakin ta yi addu'a ta shiga. Alwala ta ɗaura ta yi sallah a sakar gida kusa da Mahaɗinta wato, 'Ifti'.

Bayan sun idar sun yi azkar wanda Innti take nanata musu muhimmancinsa, sukai sabuwar shimfiɗa aka saka Tuwon a babban faranti da ruwa a babban kofi wanda ake sha ɗaya bayan ɗaya. Ana sai tsinewa Tuwon albarka take yi, wanda takaicin ya saka ta miƙe ta shige ɗaki bacci ya ɗauke ta.

Ɗabi'ar zuri'ar Innti ce, cin abinci a faranti ɗaya tare da iyalanta, safe, rana da dare.

"Innti, Daada ya amshi kuɗin kitson dana bawa Mahaɗita ta siyo taliya ƴar murji"

"Daada?"

Jaheed da Jadid suka maimaita.

Ita dai Innti ba ta yi magana ba, kalmar Daada kawai ya tsayar da bugun zuciyarta na wani lokaci, a ƙarƙashin tsayuwar bugun zuciyar, ta nemo fargaba da tashin hankali, zullumin abin da zai biyo baya, akan abubuwa da suka riga suka shuɗe ya sakata tsame hannunta daga cikin jerin hannu huɗun da yake faranti, biyar cif idan aka haɗa da nata hannu. "Ifti, kici abinci ki bar Ana kawai, samu ne wanda yafi rashi ɓarna, ganin Tuwon ya saka take wannan, da Allah bai hore na ɗora tukunyar bafa?" Ifti za ta yi magana, yatsun Babban yaya daya motsa ya saka ta yi shiru.

Har akai sallar issha'i Ana na bacci, da ƙyar ta miƙe ta fito kan nan babu ɗan ƙwali gashi sumar ta mimmiƙe kamar sabon kamu, bata kitso bata son dukkan wani tashin hankali da zai saka a taɓa mata kai, kamar me gyambo a kan, suka zuba mata idanu, Babban yaya kallon ta kawai yake yi ya ƙudurce abin da zai mata idan ta shiga banɗakin babu kallabi, Innti ta tsaya da tatsuniyar da take basu, da labarin iliya ɗan me ƙarfi. Ana ta nufi banɗaki bayan taja ruwa a rijiya, a magagin bacci take ko addu'ar shiga banɗaki ba ta yi ba, tana saka ƙafafuwanta cikin banɗakin, ta yi arba da me kama da ita kwabo da kwabo zaune a banɗaki ta zuba mata manyan idanunta.

Da fari ta ɗauka Ifti ce, sai ta tuna yau ba kaya iri guda suka saka ba, Ana ta murza idanunta, sai taga matar itama ta murza nata idanun, ta ɗauka ko bacci take yi har yanzu, tana a duniyar mafarki ne wataƙil

Sai ta girgiza kanta sumar ta baje.

Nan take matar itama ta girgiza kanta.

Wani gigitaccen ihu Ana ta saki sanda ta tabbatar gamo ta yi a banɗakin, ta zube a wajan a sume babu numfashi a ƙirjinta.

Babban yaya, ya riga su miƙewa, taku ɗaya biyu dugwayen ƙafafuwansa suka ƙarasa dashi banɗakin,a bakin ƙofa yaga Ana bata motsi, ya zuba mata idanunsa da suke iri ɗaya sak da nata kafin ya saka hannunsa ya ɗakko ta zuwa harabar gidan. Salati Innti ta fara a gigice tana ɗaukan carbi, cikin rikicewa Ifti ta fashe da kuka, Jaheed da Jadid suka rufu a kanta suna kiran sunanta. Hijabin Innti dake gefe Babban yaya ya ɗauka ya zurawa Ana, a zuciyarsa ya dinga addu'a yana tofa mata, da yayyafa mata ruwa a fuskarta zuwa wuyanta sosai

Ajjiyar zuciya ta sauke me ƙarfi. Sai kuma ta zabura tana sambatu da surutai, suka danne ta suna sake yi mata addu'a a haka har ta dawowa daidai.

"Yau naga abin da ya ishe ni, sau nawa zan ce ki dinga saka kallabi a kan ki Ana?"

Inji Innti tana riƙe haɓa.

Jaheed ya ce "Babu mamaki gamo ta yi"

"Idan gamo ta yin ma ai da sauƙi muddin basu shafe ta ba, yarinya ce da shegen taurin kai da miskilancin jaraba kamar matar kuturu, ƙila ko addu'a ma ba ki yi ba"

Wata uwar harara ta watsawa Jadid. Ya ce

"Oh, hararata ma kike?"

Ya juya yana kallon Innti ya ce "Anya Innti Shalelenki ce wannan ko wata ce daban?"

"In sha Allah ita ce. Tashi maza ɗiyar albarka ki yi sallah ki ci abinci kin ji Shalelen Innti"

Ana ta miƙe kamar ka ce mata ƙyat ta gudu saboda tsoro, ta marairace fuska ta ce "Mahaɗita rakani banɗakin don Allah?"

"Ai ya zama dole rabin jiki"

Ifti ta ce tana miƙewa, bayan ta yi alwala ta yi sallah yin duniya aka yi taci abinci amma taƙi a haka bacci ya ɗauke ta, bayan ta shiga ɗaki Ifti baccin itama ta yi, Innti dake tsaye a ɗakin ta bisu da kallo, a hankali ta zauna gefen katifar da rabi duk ya cinye, kallon fuskar Ana take yi, kyawun fuskarta tsoro yake bata, wannan tsoran shine yake cin zuciyarta, wannan tsoran shine yake damunta, dashi take kwana take yini, wannan tsoron shine yake hanata sakin jiki da fitar Ana, shine yake hanata sakin jiki da barin Ana ta yi ƙawaye, wannan tsoron shine yake sawa bata barinta fita waje. Ta ja numfashi me ɗauke da damuwa da yawa, na makomar yaranta, da tarbiyyarsu. Ta jima tana yi musu addu'a sosai ta shafa musu sannan ta fice daga cikin ɗakin. Sannu a hankali suka juya a tare, Ifti da Ana, suka rungume junansu cikin bacci.

Basa iya bacci sai sun yi wannan rungumar kamar ibada, wannan numfashin junan. Shine ke riƙe da zuciyoyinsu.

Ɗakin mazan ta shiga ta tarar Jaheed ya yi bacci, Jadid riƙe da azkar, Babban yaya na duba wata waya a can gefe wajan shimfiɗarsa, ma kwanci biyu ne a ɗakin.

Jadid da Jaheed, sai ta Babban yaya.

"Jadid"

Ya ce "Na'am, wani abin zan miki Innti?"

Ta zuba masa idanunta wanda suke faɗar abubuwa da yawa a hankali ta ce

"Magani"

"Kasha maganinka na dare?"

"Ina cin abinci na sha ai Innti"

Ta ce "Ma sha Allah, Allah Ya ƙara lafiya"

"Amin Ya Allah, Allah ya ja kwana Innti"

Ta yi masa murmushi.

"Yaya" ta kira sunan Babban yaya.

Fararen idanunsa sune suka fara shiga cikin nata kafin kyakkywan duhun fatar fuskarsa, ya yi jim ta ce "Zo, ka saman a waje" tana fita ya bi bayanta a nutse

A tsaye ya sameta tsakiyar hasken wata, haskensa da yake nuna cewa ya shiga 14 ko 15. Ya durƙusa har ƙasa cike da ladabi.

"Yaya, kai ne Babba bana son yi maka faɗa a cikinsu shi ya sa na rabu da kai, kar ka sake ranƙwashi Ana a tsakiyar kanta, ita macace tarbiyyar mace akwai wahala a wannan matakin bana son ka yi mata sabon duka, idan ya zama dole gwara ka ɗauki bulala ka zane ta akan ranƙwashi nan ka ji?"

Ya jinjina kan shi alamar “Eh" Dubansa ta yi da kyau bata san me ya sa shurunsa ke ninka maganarsa ba, yana yaro kamar karsashinsa yafi haka. Hannunsa ta riƙo cikin nata ta damƙe, ajjiyar zuciya ya sauke saboda wani daɗi da nutsuwa da ya ji, ya ɗauki hannunsa ya ɗora a nata. "Hausawa suka ce babban wa magajin uba, ina jiye maka kula da tarbiyyar Ana zuwa ɗakin miji idan haka zaka dinga mata, na san kana da zafin zuciya wacce a lokutan baya har tsoro nake ji, na ji da ɗabi'arka ta sauya. Ka yi haƙuri Yaya ka sake haƙuri watarana sai labari, za kaga babu Ana babu Iftihal duk suna ɗakin mazajensu, kaima kana tare da matarka wataƙila da yara, be patient yaya"

"Har Ana? Itama auren kenan za'a mata?" Ya shiga zance a zuciyarsa ransa kuma ya ɓaci nan take. Ta ce

"Saboda lafiyar idanunka, ya kamata ka kwanta don Allah, kar na leƙo naga kana wani aikin na daban kuma yaya"

Tsoro Innti take ji! Taka tsantsan take yi! Tana ƙoƙarin tilasta musu yin bacci, bayan dole sai sun farka kamar kullum.

Ya sake bata tabbacin zai kwanta ta hanyar jinjina mata kansa kana ya miƙe ya koma ɗakinsa. Tsakar gidan ta dawo da zama hannunta riƙe da carbi zuciyarta sai bugawa take yi, na rashin sanin dalili gashi bata jin bacci sam, kamar wacce akai wa farraƙu dashi, tunawa ta yi tana da ɗinki sai ta ɗakko atamfar da almakashi ta fara yankawa.

Tana zaune Yaa Jaheed ya fito hannunsa riƙe da waya zai nufi ɗakin su Ana. Innti ta ce "Jaheed me za ka yi a ɗakinsu a yayin da suke bacci" ya yi sak sai ya ce "Ana zan bawa wayar ne Ana nemanta" kallon wayar ta yi har za ta yi magana kuma ta fasa. Ta miƙe ta amshi wayar shi kuma ya juya zuwa ciki. Kamar me jiran wayar haka Innti ta samu Ana zaune akan katifar ta ɗora kan Iftihal a cinyarta tana shafa kanta a hankali, idanunta yana kallon sama ta yi shiru.

"Shalele me ya farkar dake yunwa ko?" Sai ta girgiza kai a hankali cikin sautin muryarta mara ta ce "Sumar kaina Innti don Allah kar Babban yaya ya aske mini na san halinsa da ƙeta wani lokacin, ina son sumar kaina ba zan samu mijin aure me kuɗi da kyau ba idan bani da gashi wallahi"

"Oh! Wannan kyau da kuɗi Ubangiji ya sa ya zame miki alheri Aysha. Wani kyawun masifa ne"

Ta ɓata fuska kaɗan "Ki yi mini addu'a kawai Sahibarmu, addu'arki kaifiyance. Yanzu da Daada yana da kyau sosai irin na mazan novel da Zainab Alƙali take karantawa a redio wallahi da wani takaicin nasa bai sarƙi zuciyarki ba, da ya shigo kinga kyakkyawan mijinki ko yunwa kike ji za ki mance"

Innti bata san lokacin da ta yi murmushi ba ta ce "Au yanzu idan na ganshi bana farincikin kenan Shalele" ta ce tana ɗan jingina da ƙofar yin hira da Ana na sata nishaɗi yana ƙara mata son yarinyar. "Nifa ban taɓa ji kince masa I love you ba, kinga Miftaa na cikin littafin Allah Yana gani matarsa kullum sai ta ce masa I love you, shi ma ya faɗa mata ai soyayya duniya ce Babarmu"

"Oh really?"

"Wallahi Innti"

"Allah Ya kula mini da rayuwarki Shatuna, Ubangiji Ya miki zaɓi da mafi alheri ke da ƴan'uwaki gabaɗaya. Riƙe ana nemanki a waya" wayar ta bata ta amsa ita kuma ta juya zuwa inda take yankan atamfa.

Sannu a hankali ta manna wayar a kunnenta tana lumshe idanunta, shima shirun ya yi saboda gabaɗaya ya ji hirar da suke yi da Innti. Ciki ciki tana kumbura fuska ta ce

"Hello.....

"Assalamu Alaiki"

Muryarsa me cike da kamala ta sauka a kunnenta ajjiyar zuciya ta sauke tana jingina da bango. Bai jira ta amsa ba ya ce

"Me kike buƙata?"

Shiru taƙi amsawa.

"Nanaah....."

Ya kirata da sunan da yake kiranta, madadin ta amsa sai ya ji kamar tana ɗan shessheƙar kuka. "Nanaah mene?"

"Ni yaushe zaka dawo kuma ka ƙi kirana sai yanzu"

Ya yi jim yana jin damuwarta na sauka a ransa kamar ba zai ce komai ba sai ya ce "To ni da ba kyakkywa ba mene za ki ƙwarzaɓi ranki don ban dawo ba?" Bai bari ta amsa ba ya ɗora da "Ba zan dawo ba, ki faɗa mini me kike so zan aiko miki dashi, idan kinga dama ki yi ta yin rashin kunya Nanaah. Kina faɗawa Innti ke handsome kike so"

"To kai ma ka ɗan fara shafa man bilitin mana, kana saka kaya masu kyau ni kawai.....,"

Cikin tsawa ya ce "Heee queit!" Yana faɗa ya kashe kiran gabaɗaya ta ji tsawar har cikin kanta tabi wayar da kallo tana tura bakinta gaba zuciyarta kuma ta ji babu daɗi.

***

Ahlam na zaune a parlour tana bawa yayanta labari na rahotan da ɗazo da taje ɗauka, cikin sanyin muryarta me ɗauke da wani 'sounds' wanda duk ƙarshen harafi sai ka ji kamar tana fitar dashi da sauri ne.

Tana da ƙin-ƙina sosai a saman harshenta, wata baiwa ta Ubangiji muddin akan aikinta ne ko karatun Alkur'ani bata yin ƙin-ƙinar.

"Yaya wai me kishiya ta ɗauki abokiyar zamanta ne? Wasu mutanen basu da imani da tausayi sam a cikin lamuransu yaya"

Ya murmusa kawai ya ce

"Ahlam me kika gano ne?"

Cikin damuwa ta ce "Yaya ɗazo da naje ɗaukan rahoto, wata ce mijinta ya yi mata kishiya, yanzu kishiyar ta haihu sai ta ɗauki jaririn ta saka shi a cikin ruwan zafi, kar kaso kaga babyn gabaɗaya ya saɓule"

Engineer ya ce

"Subuhanallahi!"

"Babu kyan gani, da ƙyar bai mutu ba" Anty Jiddah dake zaune kusa da mijinta tana sauraran hirar yaya da ƙanwa cikin raunin murya da damuwa irin ta uwa ta ce "Ai wasu matan basu da imani, wannan ya fita daga kishi ya koma hauka ya kamata hukuma ta shiga cikin lamarin a bi mata haƙƙinta, ban san yaushe ne mutane za su yi hankali ba a wannan rayuwar, kodayaushe wa'adinmu ƙarewa yake, yanzu zaka mutu, yau ne, gobe ne bamu sani ba, da muna da masaniya wataƙila mu yi hankali da wasu abubuwan rayuwar" Ahlam idanunta ya cika da hawaye muryarta na rawa ta ce "Anty abin baƙin ciki mijin yace muddin tai ƙarar kishiyar zuwa hukuma a bakin aurenta, duk wanda ya shigo cewa ake yi ruwan zafi jaririn ya faɗa, mace ɗaya ce abin ya faru akan idanunta ita ce wacce ta fito da maganar ta fara hawa iska kamar wutar daji, da ƙyar ta bani haɗin kai na yi Recorded muryarta, kuma na ga hakan ma babu fa'ida kar na saka a Redio na yi sanadin aurenta, auren fari ne"

"Allah buwayi gagara misali, Allah mun tuba. Zata iya sauya miji amma ɗanta fa?"

Ahlam ta kalli Anty Jiddah.

"Bari kawai Anty, ina ganin goge recorded ɗin zan yi, kar tsautsayi ya saka na turawa News editor" Alhaji Abdallah ya dubi Ahlam cikin nazari da tunani da nutsuwa ya ce

"Amma wannan kamar opportunity ne kika samu da za ki moving level ɗinki a gidan rediyon naku, nasan kece kika fara samun rahoton jaririn, ya kamata ki kai musu"

"Yaya...

"Yaya ina jin tsoro ne"

Ta fashe da wani irin raunataccen kuka, jikinta har rawa yake yi nan da nan hankalin yayan nata ya tashi, ya dawo kusa da ita yana riƙota da kulawa, ganin yadda shanyayyen hannunta ɗaya ya fara rawa shi kaɗai. "Tsoron me kuma kike Ahlam, ki tuna ina tare dake a koyaushe dukkan abin da kike buƙata ko kike so zan miki, ke ƴar jarida ce, matakin farko a fara aikinki, ki tuna daga shigarki kika samu award a 2024, ina ganin wannan labarin zai iya sawa ki samu wani award ɗin a ƙarshen shekarar nan, ki ƙarfafa zuciyarki, ki cire tsoro, daman kun saba ɗaukan kasada, tsoro ko ja da baya bana ɗan jarida bane, wannan mafarkinki ne, burinki ne, ba daga sama kika samu aikin ba, karanta kikai, karatunki ya kai ki wannan matakin, kar ki sare kin ji?"

"Idan na yi mata sanadin igiya uku fa? Idan na yi sanadin aurenta a gidan mijinta fa?"

Ya yi jim, sai ya ce "Hakan ba zai faru ba"

"Idan ya faru fa? Zaka aure ta?"

Anty Jiddah kallon Ahlam kawai take yi tana girgiza ƙafarta hannunta rungume a ƙirjinta ta cije leɓenta, zafi da ɗanɗanon da ta ji ya shiga cikin bakinta, ya bata tabbacin ta datse leɓen da haƙoranta, ta jiwa kanta rauni ne. Miƙewa ta yi da murmushin data ara ta shimfiɗa a fuskarta ta ce "ƴar gatan yaya rigima ake ji yau, ni dai mu kwana lafiya" Abdallah ya bi bayanta da kallo har ta shige cikin part ɗinsu kafin ya sauke nauyayyiyyar ajjiyar zuciya yana kallon ta

Ya ce "Ki je ki kwanta, kinga gobe da wuri za ki tashi, idan na kunna rediyo ina son na ji wannan rahoton daga cikin golden voice ɗinki" rarrashinta ya dinga yi har ya rakata ɗakinta ta je ta kwanta tana tunanin yadda ta bar jaririn matar a saɓule tas ko asibiti anƙi kai shi. A daren ta turawa Editor recorded ɗin tana son amincewa daga wajansa

*** Tsaye ta yi a gaban room ɗin hotel ɗin cikin shigar after dress data ɗora a saman kayan jikinta, ta rufe fuskarta da face mars. Babu jimawa aka buɗe ƙofar da fararan idanunsa ya bita da idanu kafin ya yi baya wajan bata waje ta shige ciki.

"Na fara gajiya da wannan mu'amalar, ni ba matarka ba ni ba budurwa ba nama kasa gane ina muka dosa. Yaushe ne zaka daina yi mini barazana jikina ya fara gazawa"

Jallabiyar jikinsa ya zare ya zago ta bayanta ya rungumeta yana ɓalle after dress ɗin ya ce "Kin samu abin da kike so, nima dole ki bari na yi yadda nake so, tunda nine na kai ki matakin da kikai kai. Don haka quiet ki haɗiye duk wani complain ki bani farinciki a nan" ya ce yana nuna mata gadon ɗakin.

"But sir....

"But what? Fitowa kike so na yi na ce ba ki cancanta ba, ko kuma ba karantar ɓangaren kikai ba, ko kuma ana daƙile wasu ne saboda ke"

Sai ya girgiza kai da faɗin "I'm not in the mood ne sir" yana shafa fuskarta ya ɗan murmusa kaɗan "Never mind, zan dawo dake mood yanzu" yana faɗin hakan ya kashe hasken room ɗin

***

Cikin dare Ana ta dinga firgita saboda gamon da ta yi a banɗaki ta hana Ifti bacci sam, sai ta dinga rungumeta tana mata addu'a kuma taƙi kiran Innti bata so ta dame ta. Har kusan 1:36 na dare Innti na zaune a tsakar gidan tana yankan ɗinki.

Garam! Sautin bugowar ƙofarsa ya bayar a cikin kunnenta, addu'a ta fara idan ka shiga tsoro da firgicin gamuwa da wata halitta ta Ɗan'Adam. Jin bata ji motsin shi ba, ya saka ta juya a hankali bayan ta ajjiye yadin landin ɗin da take saita kafaɗa zata yanka, zumbur ta miƙe tsaye, a tsakanin miƙewa da tsayuwar bugun zuciyarta na wani lokacin ba zata lissafa wanne ya zarce wani ba.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"

Ta furta a gigice da sautin daya cika gidan ganin Daada tsaye a tsakiyar gidan zigidir haihuwar uwarsa, idan ya miƙe tsaye sai ya sake yanke jiki ya faɗi yana layi da tangaɗi, ko irin ɗan kamfan da maza suke sawa babu a jikinsa, bata san tun yaushe ya kasance tsirara ɗin ba, wandonsa da zabgegen tazugen wandon da yake lilo har ƙasa, ya yi amfani dashi wajan ɗaure wuyansa da tunanin al'aurarsa ya rufe, furfurar kan shi da wacce hazo ya ƙara masa sun yi haɗin gwiwa wajan sake fito da tsofan nasa.

Sambatun giyar bata sake shi ba, a cikin can tsakiyar kan shi jijiyoyin da suke sarrafa tunanin Ɗan'Adam, su sanar da ƙwaƙwalwa halin da gangar jiki take ciki, sune suke aikinsu a tattare da Daada, ya ɗauka har yanzu yana cikin ɗakin Tani suna aikata abin da suka saba. Wani mokaɗe kwankwaso yake yi yana tura shi gaba zuwa bawa.

"Tani ke duniya ce, Tani zumata, me zaƙi, Tani kin fi reza kaifi, Tani kinfi Innti amfani da garɗi!"

Jerin baitocin waƙar duka a kunnen Babban yaya da Ana dake ƙoƙarin buɗe ƙofa ta fito waje, cikin sauri Babban yaya ya saka headphone a cikin kunnensa yana juya zaibar idanunsa zuwa shimfiɗar su Jadid da Jaheed, yaga bacci suke yi ɗaya ya yi filo da hannun ɗaya, abin mamaki hannunsu damƙe dana juna a haka suke yin baccin

A gigice Innti ta nufi ƙofar ɗakinsu Ana tun kafin ta fito, karo suka yi. "Ana"

"Na'am" ta faɗa a hankali.

"Me za ki fito yi cikin daren nan?"

"Innti na kasa ganin film ɗinsu su Anum da Jarumi a ɗaki, zan kwanta ƙasan bishiya ne"

"Ƙasan bishiya?"

Ta ce da mamaki "Ana anya ba zan kwana ina faɗawa Ubangiji lamuranki ba?"

Innti ta maimaita tana buɗe mata idanu.

"A daren nan? Bakya tsoron mutanen ɓoye ashe ba ki ɗauki darasi a banɗaki ba Ana?" Ta zubawa Innti manyan idanunta masu saƙar baƙi kamar me son karanto gaskiyar maganar Innti a fuskar tata.

"Koma cikin ɗaki"

Da ƙyar ta ce "Bari na sha ruwa"

"Aysha!" Ta kira sunanta a tsawace jikinta ya fara bayar da ita wajan amsar rawar da zuciyarta take yi mata ganin tamboɗan Daada na ƙara ƙaimi, ya kwanta a ƙasa yana wasu abubuwa kamar wanda yake tare da mace wajan auratayyar aure.

Macen ce, da macen yake tare.

Tani ce ke yawo cikin kansa!

Tura Ana cikin ɗakin ta yi,ta janyo ƙofar ta ɗaure da igiya kana ta dawo tsakar gidan.

"Menene? Me ya sa ta hanaki fita"

Ifti ta tambaya tana murza idanunta, Ana taƙi magana sai waje guda data kafe da kaifafan idanunta, Ifti zata sake yin magana suka jiyo ihu da kururuwar Innti, a kiɗime Ana ta miƙe ta fara jijjiga ƙofar haka ma Ifti amma sun gagara buɗewa saboda ta rufe su ta waje, suna jin yadda Daada ke ɗaukan Innti yana bugata da ƙasa.

Ihunta ya farkar da Jadid da Jaheed daga bacci, Babban yaya duk da ya saka abu kunnensa bai hana shi jin kukan ba, gabaɗaya kwantattun gargasar ƙirjinsa suka mimmiƙe reza ce a hannunsa yana yanke wata waya, bai san yadda aka yi ya dunƙule hannunsa ba, sai jini ya gani yana tsiyaya daga cikin tafin hannunsa, raɗaɗin zuciyarsa yafi na yadda rezar ta kekketa masa hannu, idanunsa kamar zasu zazzago ƙasa saboda tsabar yadda suka buɗe. Jadid kuka ya saka yana kiran sunan mahafiyarsu, ashe suma ta rufe su ta waje da kwaɗo....

Akwai page 3 da 4 a ArewaPen ku yi searching sunan littafin HIYAAM za ku samu. Ku yi following account ɗina domin samun notification a duk sanda na yi positng.

Bright pens 08164069385 08082101373